masa riga malam masallaci."
Muka yi dariya ni da Nafisa.
"Allah dai ya sauwakc." Nafisa ta fada.
Bayan na sanya kasct din ne na koma na zauna
tare da daukar littafina domin in ci gaba da karatun.
Muryar da karet din ya amayar ne ya sanya mu daga kai gaba dayanmu lokaci guda muka kalli juna, muryar
yayana ne yana baiwa su T.j. kashedi akan kar su kuskura su saurara mini, wato dai kaset fin da na baiwa baba Musa ne ya daukar mini a ranar da su T.j. suka ziyarci gidanmu. Na tashi nayi hanzarin cire kaset din zuciyata cike da al'ajabin yadda hakan ya faru. Sai a
17
lokacin na lura domin tabbas ba shi ne kaset din Celine
Dion din ba, dan shi fari ne wannan da nakc rike da shi
kuwa baki ne, lallai ido gululu ne hankali ne ke gani ba
shi ba, dan kuwa shi ma yana kan redio a ajiye gefe
guda hade da 'yan makullaye guda biyu su ma ajiye.
Na so in manta in da na taba ganinsu, sai dai cikin ikon
Allah na tuno cewa na safe din yayana ne da ke dakinsa
na sama. Su Uzaifat su ma sun riske ni suna masu farin
ciki marar misaltuwa.
"Ubangiji yana bayan mai gaskiya yaya. ba ga
shi ya sanya shi mantawa da keset din ba anan, ina
kyautata zaton garin sauri ne ya manta su." In ji Uzaifat
"Har da makullin safe dinsa ga shi." Na fada ina
nuna masu.
Take muka nufi dakinsa. mun sha
gwagwarmaya sannan muka bude dakin. Safe din dam
yake da kudi rafa-rafa na dari bibbiyu.
* ** *
Har yanzu tunanina bai wuce yadda aka yi
yayana ya manta da kaset din da ya karba a hannuna
tare da dan mukullin safe din sa ba, duk da na san babu
yadda ubangiji ba ya ikonsa, to maganganun Uzaifat ma
sun sake sanyawa na sadudu domin a yadda ta fada ta
nuna cewa ubangiji yana bayan mai gaskiya, kuma ba
zai taba fora mai karfi akan raggo ba, hakazalika ba ko
zai taba dora azzalumi akan na-gari ba, in ko har yayi
hakan to tabbas hakan ya so domin kuwa wata shari'ar
sai lahira.
"Kamata yayi muyi saurin faukar mataki. in
kuwa ba-haka ba duk sanda ya farga bai ga kaset din
18
nan da dan mukullinsa ba, to wallahi zai farma na tunda
a tabbata yanzun tuni labari ya isar masa cewa kun
dawo gida." Nafisa ce ta katse mini tunanina.
Na ja numfashi na ce "Tabbas hakan zaa yi.
amma before that ina son muyi hanzarin zuwa Abuja
wajen Hajiya tun kafin ya dawo kamar yadda ta fada.
Suka nuna amincewarsu hade da murna. Ko ni
ina farin cikin sake hada ido da Hajiya Maryam wacсе
na rika tamkar mahaifiyata tun bayan rasuwar iyaycna.
Cooker Gas na janye daga mazauninsa na sanya dan
mukullin hade da kaset din a bayansa, sannan na mayar
da shi mazauninsa ya zauna tsaf kamar ba'a taba wajen
ba. Nayi hamdala ga ubangiji sannan nayi dakina.
* ** *
Washegari bayan mun karya muna zaune akan
dining kowannenmu na saka nasa zaren a zuciyarsa na
daga abinda yake tunani. Na katse musu tunaninsu da
cewa "Na yanke shawara wacce nake ganin ita ce mafi
dacewa a tare da mu." Na ja na tsaya tare da lura da
fuskokinsu, ganin sun ba ni hankalinsu ainun yasa na
samu kwarin gwiwar ci gaba "A ganina bai kamata
muyi gaban kanımu mu ce zamu tafi gidan yaya ba tare
da sanin hukuma ba, domin kuwa sanin kanku ne cewa
babu yadda za'a yi ya zauna ya sakankance ba tare da
kasancewa cikin shiri ba alhalin ya san yana cikin
hatsari, dan haka zan nemi taimakon Inspector Kabir
saboda ba na son mu fauki law into our hand."
Shakka babu su kansu sun san cewa wannan
shawara tawa ingantacciya cc, danhaka suka ba ni
goyon baya, sannan wani matashin murmushi ya biyo
19
baya, wannan kuwa sako ne daga SAHIBATA. Na dauki kan waya na danna lambobi. Ba tare da 6ata
lokaci ba ta fara ringing, zuwa dan wani lokaci aka
dauka, na amsa da cewa "Ina son inyi magána da Inspector Kabir."
Sagent ya sanar da ni ya fita amma in sake
bugowa nan da awa daya.
Garin yayi lub-lub kamar furkar angon da ke
sauraren zuwan amaryarsa, da ma tunda Asuba aka
tashi da sanyi mai ratsa jiki, domin kuwa saboda sanyin
yayi yawa ma har sai da hazo yayi kaka-gida inda har
ya hana jirage tashi, kamar yadda aka sanar a labarani,
bakwai na safe. Danhaka mun rufe kowacce kafa da
muke tsammanin sanyin ka iya shigowa, sannan na
mike na danna Heater inda falon ya fara amsar/bakon
dumi. Award din India muke kallo wanda
SHARUKHAN ya lashe. Su Uzaifat, sai faman zabga
musu suke yi, ni kuwa dariya kawai nake yi, musu. In
suka jeho mini tambaya akan waya fi gaskiya cikinsu,
sai ince Uzaifat ce. Kai har Nafisat dai ta hakura da
musun tana fadin "Ni ma Allah ya kawo mini nawas
masoyin da ba zai taba ganin laifina da karyata ba,
domin kuwa wallahi yaya ka nuna mini son kai."
Na tuntsire da dariya na mike na nufi Telephone
domin sake neman Inspector Kabir. Nayi sa'a kuwa ya
dawo, bayan na sanar da shi bukatarmu ne ya yaba da
hankalina tare da ba ni goyon baya akan shi da kansa
ma zai bi mu, hade da cewa zai zo gidan, namu ma
yanzun. Nayi masa godiya, sannan na ajiye kan wayar.
Ina cikin sanar da su Nafisa yadda muka yi ne aka yi
20
wani irin buga Kofa wanda ya gigitamu. Cikin hanzari
na tambaya "Waye ne haka?"
Amma shiru ne ya biyo baya, sai ma wani
bugun da aka sake yi. Mamaki ya kama ni, ni dai na ga
cewa akwai Bell da ake dannawa a bakin kofar, mai zai
hana mai shiga ya danna cikin mutunci? Take zuciyata
ta tabbatar mini cewa ai kuwa tunda ake irin wannan
bugu tofa rashin mutunci ne ya kawo sa. Su Nafisa duk
sun yi tsuru-tsuru yayin da aka ci gaba da buga kofar.
Cikin sanyin murya Nafisa ta ce "To wai shin ina baba
Musa yake ake irin wannan bugu?"
Na amsa mata da "Ai tunda kika ga haka sai dai
Allah ya kiyaye shi kawai zamu ce."
Gaba faya aka ci gaba da girgiza kofar. "Wallahi kowaye sai dai ya balle kofar ba za a
bude ba." Uzaifat ta fada ranta a басе.
Muna tsaye kikam muna kallon sarautar ubangiji kofa na barazanar 6allewa, take na nufi
Telephone domin na sanar da Inspector Kabir halin da
muke ciki don yayi saurin kawo mana agaji, amma sai
me? Ai tuni an tsinke layin ban da shuuu! babu abin da
kan wayar ke yi. Ajiye kan wayar da nayi yaya daidai
da fadowarsu falon kowannensu na muzurai. Sanye yake da bakar shirt mai gajeren hannu da koren wand
hannunsa rike da karamar Pistol. Mutuniynta ko
wannan karon shigar da tayi sai ka rantse da Allah idan
a kasa sa ta a masallaci za tayi limanci, bakar abaya ce
a jikinta hade da mayafinta, wannan karon arnan takalmin nata ba baki ba ne shudi ne, Sussy kenan wanda Gulawa mutum ciki da takalmin nan nata ba
21
wata tsiya ba ce, hannunta nke vake ita ma da Pistol.
Shi. ma cikon na ukum masu wani katon gaske ne
fuskarsa sai naso take tana maiko kamar kosai ya ji
man gyada, wanda a zahirı nayi tsammanin cewa уa
dade da shekawa barzahu an jela gawarsa a teku kifaye
sun cinye, abokin harkar T.j kenan wanda ya keta rigar
mutuncin mahaifiyar Uzaifat wanda take nemansa ruwa
a jallo da gidauniyar mutuwarta wato Chiko kenan.
Fuskarsu sam babu utunci, suka ci gaba da
tsayawa a yayin da mu kuma suka yi mana umarni da
mu zauna, duk mun žauna face-izaifat da ta ki zama ta
ci gaba da kallon Chiko bå ko kakkautawa.
"Ke ba da ku ake magana ba ne, ko kin fi sauran
ne da suka bi umarni?" Sussy ta daka mata tsawa.
T.j. ya kalli Sussy ya ce "Take it casy baby aí ba
sai kin daga murya ba, in san cewa ba fada ko
ta'addanci ne ya kawo mu ba amma duk da haka ba
zamu yarda da taurin kai ba." Yayi shiru sannan ya ci
gaba da "dan gyara mata-tsayuwar kuncinta may be she
will obey."
Kafin ya rufe baki Karar saukar mari ya dira a
dakin, wanda saboda tsananin Karfinsa sai da Uzaifat ta
kife kasa. Nayi yunkuri domn kai mata agaji amma
ina! Takalmin Sussy ne ya maida ni baya, na rike cikina
ina salati.
Nafisa ko také ta saka ihu tana kuka "Wayyo
Allah mun shiga uku." Ta fada.cikin murya mai cike da
ban tsoro.
"Cool down." Chikova fada.
22
"Samari da yan mata ku kuka jawo hakan ta
faru, mu abinda ya kawo mu daban in har kun ba mu
shikenan you are very free." T.j. ya fada muryarsa cike
da gargadi.
Uzaifat na kwance tana nishi amma dan taurin
kai irin nata sai da tayi nagana "Wallahi koma mene ne
ba zamu baku shi ba, sai dai ku yi duk wacce zaku yi.
Ta fada muryarta na rawa.
"Fine" T.j. ya ce yana murmushi. "Duk da haka
gara dai mu tambaye ku, kuna gwamma dai ku ba mu
kafin mu nemi oga a waya ya ba mu izinin saba muku
kamanni." Yayi shiru "Kaset din da ya manta shi a falo
hade da dan makullin safe dinsa, sannan sai Film din
da ke cikin Camera da ka fau hotonmu wato Nagetive
kenan, su zaku ba mu mu juya muyi tafiyarmu cikin
mutunci mu barku cikin aminci."
Na ja numfashi na ce "Mu ba mu ga komai ba
domin shikaran jiya muka dawo sai dai in wani ne ya
shigo ya dauka, camera kuwa tun a ranar da ya riske ni
a daki rabona da ganinta."
"Kai kar ka kawo mana rainin hankali mana ka
ji? Ku fito mana da shi tun kafin ran kowa ya baci."
Chiko ya fada yana muzurai.
Ni dai banda addu'a babu abin da nake yi, na
ubangiji ya kawo mana wanda zai agaza mana.
"Wai kai gwari ne?"" Uizaifat ta fada tana kallon
Chiko, sannan ta ci gaba "in ba gwari ba ai maka Hausa
ka kasa fahimtar me ake fada' Mun ce ba mu ga komai
ba sai ku fice ku bamu waje.
23
Chiko yayi kanta, a yayin da T.j. ya dakatar da shi "Rabu da su dama ce suka samu, amma duk za su
gane kuskurensu yanzun nan, jeka mayar da wayar nan
mu yi kiran Oga mu sanar da shi don ni wannan raini ya ishe ni."
Take Chiko ya fice. Tj. ya nufi gindin
"Telephone din ya kara a kunne, zuwa can waní lokaci
sannan ya danna lambobi "Hello Oga mu ne...ch nuna
nan din amma sun Ki ba mu hadin kai Oga..., Haba
mun yi iya kokarinmu Og To sbikenan dama
umarninka mu ke jira mu ji, yanzun nan zamu cika
aiki." Ya ajiye kan wayar yana murmushin keta "Baby
Ogu ya ba mu izini ko ta halin Kaka mu karßar masa
sakonsa Even if it takes a lifo."
Cabana ya yanke ya fadi da jin kalamansa, dan
na san yayana sarai zai iya fadin hakan. Lokacin da
Sussy ta auni Rafata da Pistol dinta, to a lokacin ne
wata siririyar murya ta ratso fafon "Hold on! Kutsaya a
position dinku ba tare da motsi ba in kuwa ba haku ba
ranku yana bakin wanan bindigar tawa.
Shirun da muryar tayi ne yayi daidai da harbin
da ya dira akan fanka, wanda hakan ya sanya su T.j
zubewa a Rasu tare da fatali da bindigoginsu.
Kwanciyar da suka yi a Rasa ne ya baamu damar ganin
wannan mai magana. Fara ce kynkkyuwa mai
matsakaicin tsaho, hannunta rike da Pistol, tayi
murmusbi hade da fadin "Ku tashi ku kwashe
bindigoginи,"
Muna Kokarin mikewa zuciyarmu cike da farm
ciki, a lokaci guda murnarmu ta koma ciki, Chiko ne ya
24
kara mata bindiga a kunnenta yana fadin "Ajiye bindigar ki ko in fasa miki kwanya."
Cikin nutsuwa tayi wurgi da bindigar.
Jin muryar Chiko ya sa su T.j. mikewa
kowannensu ya dauki bindigarsa, sannan Chiko ya
ingizo wannan kyakkyawar budurwa ciki yana dariya.
Ganin haka ya sanya ni yanke hukuncin ba su dukkan
abinda suka bukata, tunda sun ce babu abinda za su yi
mana, in ya so ubangiji shi ya san yadda zai yi da su
kawai kar taurin kanmu ya sanya su kashemu a banza.
Tunanina ya tsaya cak! A lokacin da su Inspector Kabir
suka shigo kusan su bakwai, kowanne da zungurazunguran bindiga.
"Your hands up." Inspector Kabir ya fada.
Gaba dayansu suka daga hannayensu, 'yan
sandan suka karbi bindigoginsu sannan suka sanya
masu Handcuff, lokaci guda Inspector Kabir ya ba su
umarnin suyi cikin mota da su yana zuwa. Bayan mun
gaisa nai masa godiya ne yake sanar da ni cewa "Ai
makotanku zaku yiwa godiya, domin su suka yi mana
waya cewa gidan nan babu lafiya, dama ai mun yi da ku
zan zo, har na fito Sajen ya biyo ni ya sanar da ni sakon
wayar da ya aiko, to ganin haka ya sanya na bugo maku
waya, sam! layin ya ki shiga alamar an yanke wayar, to
ganin haka ya sanya na dada tabbatar da gaskiyar
lamarin."
Muka sake yi masa godiya, sannan yayi mana
sallama ya tafi hade da sanar da mu cewa yana jiran mu
a can Police Station din. Bayan tafiyarsu ne
kowannenmu ya nemi guri ya zauna, zuciyarmu cike da
25
godiya gurin ubangiji hade da hamdala da fatan cowa
InshaAllahu karshensu T.j. ya zo, saura ogan nasu.
Sallama muka ji daga can harabar gidan, na shaida mai
muryar makocinmu ne Alhaji Mudi mai zarc wanda
Inspector Kabir ya ce gidansa akai musu waya. Bayan
na fita mun gaisa nayi masa godiya, shi kuma yayi mini
jaje. "Ai a bandaki nake ina wanka kamar an ce in juya
in ga, kawai sai na hango su uku kowanne da Pistol a
hannunsa suna kokarin shiga dakin Musa mai gadinku,
to shi ne na tabbatar cewa babu lafiya domin kuwa
Barayi yanzun sun tayar mana ba sa sati ba su shigo
layin nan ba. To ko wankan ban gama ba na fito daga
bandakin na sauka falon kasa, shi ne na sanar da 'yan
sanda."
Sai yanzun na tuna da Baba Musa, duk a
tunanina ko ya fita ne a lokacin da abin yake faruwa, to
amma yanzun kuma da Alhaji Mudi yayi maganar cewa
ya gan su suna kokarin shiga dakin sai zuciyata ta fara
bugawa a hankali hade da razana. Na nufi dakin a
hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, nan na
bar Alhaji Mudi a tsaye yana bi na da kallo. Bayan na
tura kofa ne na saki uban salati hade da fadawa dakin
baba Musa. Sai bayan da na kwance masa daurin da
suka yi wa bakinsa hade da hancinsa, sannan Alhaji
Mudi shi ma ya shigo ya taya ni kwance masa daurin
hannunsa, jikina na rawa na fada bandakinsa na debo
ruwa a cikin karamin bokiti na fito. Alhaji Mudi ya
amsa a hannuna yana salati yana yayyafa masa. Ai
tunda na ga jini yana gangarowa daga kofar hancinsa,
zuciyata ta sallama domin sun yi masa dauri ne ba na
26
wasa ba. Alhaji Mudi ya ajiye bokiti hade da taba
Jijiyar wuyan baba Musa, ya sake yin salati cikin murya
mai cike da ban tausayi ya ce "Uzaif sai dai mu dau
hakurin Musulunci domin kuwa Musa rai yayi halinsa,
Allah ya jikansa da rahama."
Ai ban san sanda nà daka tsalle nayo waje a guje
ina ihu ina kuka kamar wani dan yaro, wanda dalilin
yin hakan ya sa su Uzaifat bazamowa waje. Suna
taradda abinda ya faru su ma suka soma kuka da kyar
Alhaji Mudi ya lallashe mu hade da sanar da mu illar yi
wa mamaci kuka, haka dai muka hakura ba dan zuciya
ta so ba. Take na shiga na bugawa Inspector Kabir
waya na sanar da shi rasuwar baba Musa, yayi mani
ta'aziyya hade da sanar da ni cewa shi ma yana nan
tafe.
Muna tsaye a harabar gidan Inspector Kabir ya
iso tare ua 'yan sanda biyu, bayan sun shiga dakin baba
Musa sun yi 'yan dube-dubensu ne suka fito, ya sake yi
mini ta'aziyya sannan yayi wa su Nafisa. Lokaci guda
ya ci gaba da kallon wuyan Nafisan take kuma ya shafa
nasa, komene ne dalilin yin hakan ba zance ba. Kallon kurillan da yake yi wa Nafisan kamar sai a lokacin ya
taba ganinta ne ya sanya ta sunkuyar da kai hade da
kunce dan kwalin da ta daura a kanta ta yafa a kanta
hade da wuyanta, kasancewar jikinta ba hijabi kamar yadda ta saba sawa a dalilin rudanin da muka shiga.
Can kuma kallonsa ya koma ga bakuwarmu wacce har yanzun ba mu san ta ba ballantana dalilin zuwanta, sai
dai tabbas ina yi mata kallon sani, yayi mata murmushi fuskarsa cike da mamakin ganinta.
27
"Yallabai na iya suturta mamacin yanzun ko?"
Alhaji Mudi ya tambaya.
Inspector Kabir ya dago kai ya ce "Tabbas! Sai
ku hanzarta domin yamma tayi kar a bari lokaci ya
Kure. Zan koma Station na rubuta Statement, ba zan
samu damar halartar jana'izar ba domin daga nan zan
wuce gida in kai mahaifina asibiti."
"Assha bai ji dadi ba ne?" Na tambaya.
"Eh ba shi da lafiya ne."
Muka yi masa sannu hade da fatan Allah ya ba
sa lafiya. "In mun gama karbar ta'aziyya ka kai mu mu
gaida shi." Na rufe da ina mai nuna damuwata domin
kuwa Inspector Kabir ya taimakawa rayuwarmu saboda
haka ya cancanci yabo.
7
An yi jana'izar baba Musa mai gadi da fatan
Allah ya ba sa Aljannatil Firdausi, amin. Bayan sallar
Magarib ne muna zaune a falo, na kalli bakuwarmu na
sake yi mata sannu da zuwa hade da tambayar ta ko ita
wace ce.
Ta yi murmushi hade da fadin "Da farko dai
Moda nake kamar yadda mutane ke kirana, amma
ainihin sunana Nafisat Abdulmalik, wanda na san kana
da labarin rasuwar mahaifina daga bakin Hajiya, a
takaice dai ni ce 'yar Hajiya da ke Zariya."
28
Haba! Hajiya Maryam ce kamar da na gani a
jikin bakuwar, tabbas da ita tayi kama. Lallai Hajiya ta
sanar da ni rasuwar mahaifin Moda bayan an haifeta da
wata uku. Nafisa tayi tsalle ta fada kanta tana murna, ni
ma na ji dadin zuwanta kwarai da gaske. Na tambayc ta
vadda aka yi ta san nan gidan.
"Kakata ce ta ba ni address, wato mahaifiyar
abana.
Ta tambaye mu labarin labarinsu T.j. Bayan
un ba ta labari tun daga farko har karshe, ta sanar da
nu cewa ita C.I.D. ce. "Yanzun ma yadda zamu sadu
da Hajiyar a Abuja müke shiryawa."
Bayan sallar Isha'i muka kai Moda gidan Hajiya
Tsohuwa mahaifiyar Hajiya. Mun tarad da ita tana
kadin auduga a fakinta, daga yin sallamarmu ta dau
murya "A'a ku shigo, sannunku da zuwa sai yàu a
gari?"
Nayi dariya na ce "Haba Hajiya wallahi harkoki
ne su kai yawa shi ya sa."
Tayi murmushi "To ai shikenan, ya gida? Ya su
Hajiya?"
Nayi saurin amsa mata, gudun kar wata daga
cikinsu ta sanar da ita abinda ake ciki "Suna nan lafiya,
ai tana Abuja tafiyar ce ta zo cikin gaggawa shi ya
sanya ba ta samu zuwa ba, amma duk sanda ta yi waya
tana aiko da sakon gaisuwa, muma gobe muke son mu
je Abujan shi ya sa na ce gara mu zo mu yi miki sallama. Wannan ma Moda ce wato Nafisa 'yarta da
take Zariya yau ta zo."
29
Hajiya tsohuwa ta kalli Moda tayr mormashi
hade da jin dadin ganinta. "Y'anzun nan daga zowata
ko dan kwana biyu ba zata yi mini ba. zata wuce Ta
fada tana kallona.
"Haba ai kwana daya za můyi ko biyu. zata
dawo mana tayi miki ko da sati daya ne.
Tayi dariya "To Allah ya sa.
Bayan wani lokaci muka vi sallama muka fito.
Moda kuwa ranta duk a bace ba ta so ta rabu da kakarta
ba, domin kuwa wannan shi ne karo na farko da suka
sadu tun bayan da kakarta ta wajen uba ta zo ta dauke
ta, lokacin Hajiya na shirin auren yayana dan ba ta ti
shekara daya da 'yan watanni ba a lókacin.
"A ce mutum yana da yan'uwa da dangi anuņa
ganinsu ya gagara? Tunda nayi wayo nake son in hadu
da sauran 'yan'uwana na wajen uwa, amma Gambo lu
hana, tana ganin in na taho ba za a bar ni na koma ba,
wallahi wannan zuwan ma sai da muka kai ruwa rana
sannan da 6acin rai ta ba ni address na taho." Moda ta
fada tana matse hawayc.
Hakuri muká ba ta ta ci gaba da fada mana
halayen kakarta na rashin son ta rabi dangin uwarta.
Washegari bayan mun karya sai na fuskanci
Uzaifat na cikin damuwa, don haka nayi kiranta muka
kebe na tambaye ta meke damunta? Ta so ta boye mini,
amma sai na ce da ita "Haba Uzaifat yanzun har akwai
abinda zaki boye mini? Tun dazun fa na lura cewa you
are not yourself why?"
Idonta ya kawo hawaye lokaci guda ta sa hannu
ta goge "Am really sorry Uzaif, wallahi ba haka ba ne
30
tunanin alhalin da mahaifina yake cike kawai nake yi.
wallahi na matsu in gansa, gaskiya ain feeling bad."
Na tausar da muryata na ce "Ki yi hakuri ai dole
ne mu san inda yake tunda su Chiko din sun zo hannu.
bayan haka ni ma abin ai yana damu na ko tsammaninki
ke kadai ce 'yar abban?"
Tayi murmushin jin dadin lafazina.
"Ki bari zan bugawa Inspector Kabir waya ya
tuhumar mana su, in ya so Abujan mu bari sai gobe.
Zuwa an jima sai mu je Station fin mu ji yadda zata
kasance."
* ** *
Na sanar da su Nafisa sakon Inspector da ya ce
ba sai mun zo ba, mu bari sai gobe da safe kamar karfe
tara mu zo gaba faya a wuce Abujan. Sannan ya sanar
da mu mutuwar Sussy wanda ban so hakan ba, na so а
ce ta er bakar wähala sannan ta gangara. Sannan a
fadarsa su 1j-da Chiko sun nuna taurin kai matuka.
don har electric aka sa musu a jikinsu kan su fadi inda
mahaifin Uzaifat yake. amma sun ki fada.
"Kar ka samu damuwa Uzaif am ready to help
you, ba su gagare ni ba. ka bari sai mun dawo daga
Abuja za su gane kuskurensu." Ya ce da ni.
Yayin da ya ajiye kan wayar. Nafisa ta nuna
farin cikinta sosai da jin tafiyarmu Abuja da su
Inspector, domin a ganinta abin zai zo da sauki.
Kwamishinan da aka canja sam bai yi mini ba,
domin na fuskanci yana da girman kai tare da
wulakanci, idan ka lura da irin kallon biyu ahun da
yake yi mana: Mun riske su da Inspector Kabir a
31
harabar Station din suna zantawa, bayan mun gaisa ne
Inspector ya gabatar dà mu gare shi, sannan ya kara da
cewa "Shi ya sa nake son na bi su can tare da yara
kamar uku ko biyar domin taho da Alhaji Yusuf din,
don yana da dukkan proof da ake bukata kuma tun jiya
na karbi warrant din arresting nasa.
Kwamishinan ya bata rai hade da fadin "To ai
ba komai sai in ce a dawo lafiya."
Ganin wannan shan Kanshi da yake yi ne ya
sanya Uzaifat fidda 1.D. Card dinta ta nuna masa hade
da fadin "Ni sunana Uzaifat as you can see am a
professional doctor."
Ita ma Nafisat nuna masa nata 1.D. Card din,
ganin haka ya sanya Moda tura hannu cikin jakar da
take rataye a kafadarta ta fidda nata Card din ta ce
"Nafisat Abdulmalik C.I.D."
Ai da ganin haka fuskar mutuminka ta sauko ya
dan yi murmushi ya ce "Commissionar Faruk Salami
you are highly welcome." Ya juya suka yi magana da
Inspector Kabir wanda ba nace ga abin da suke fada ba.
Bayan sun kammala yayi mana sallama ya shige cikin
Station din, na kalli su Uzajfat nayi dariya.
Nafisa ta ce "Yaya dariyar me kake yi haka?"
Tùn kan nayi magana Uzaifat ta amsa "Ba dole
yayi dariya ba, ya ga mun fito da kimar mu kar a raina
mana hankali mana wani shankanshi haka kamar а
kansa aka saba kai wani matsayin mukami."
Duk suka kwashe da dariya.
Inspector Kabir ya ce "A'a kar a yagewa Ogana
fa a gabana, kar in sa ayi cikin cell da ku yanzun nan:
32
Gaba daya muka dada kwashewa da dariya.
Motarmu na gaba ta su Inspector Kabir na baya
hat muka isa kofar gıdan yayana. Ni kadai na fito daga
cikin motar na waiwaya na kalli motarsu Inspector nayi
masa alamar'su dakata daga nan baya kar su karaso.
domin ban manta ba Hajiya ta sanar da'ni a wasikarta
cewa ya zuba masu gadi a gidan, to in har kuwa haka ne
ba za a shiga gidan ta dadin ba, sai dai da dabara. Na
nuff-Rofar Gate din na kwankwasa na ji shiru, na sake
kwankwasawa a karo na biyu, sai a garo na uku ne na
ga an bude wata yar kafa da ke jikin Gate din.
Puskarsa na da kauri idan ka yi la'akari da kumatuna
zaka yarda da hakan.
2eAssalamu alaikum." Nayi masa sallama.
geb Bai amsa ba, dan haka sai nayi tunanin ko arńe
ne Ko kưwở ma ba bahaushe ba ne. Shiru yayi yana
kallona. kuma yana kallon motarmu, amma ban yi
amnlanin ya hango motarsu Inspector Kabir ba, dan
ltaka-sar navi masa nuni da motarmu na ce shi "Dan
Allah-imu bakíne mun zo gun Hajiya ne"
Ed Ya kailf Kwayar idona a fusace ya ce "Wa ya ba
kü izimin Anwa?"
ub Awaka cé dan iska da kana jin Hausar? Na fada
a zuciyata. Da ya ga nayi fan shiru ban ce komai ba ya
sake magana a fusace Kai mallam ku bacebmana da
gain saboda Strangers are not welcomo herelit sZarmañda abün ya rufé nayi saurin tsayar da shia
Hajiya Maryam dm ce tarce mu zo, ta san da zuvanmu
ka tambayo ta ka ji:
33
"Ko ma Hajiya wace ce babu halin ganinta." Ya
fada muryarsa na tabbatar mini da maganar da ya fada
har zuciyarsa haka yake nufi, Ganin zai Bata mana
lokacı ya sa na ce da shi "To yallabai in ba zaka damu
ba zan baka sako ka kai mata.
Yayi jim kamar bai amince ba, can sai ya ce in
kawo. Zuctyata, küwa saka tunanin yadda zan bullo
masa kawa ta ke yi. Na Karasa gindin motarmuna
sanar da su Uzaifat yadda muka yi da shi. Nafisa ta ce
"To ar-ina