Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels REAdeN's Media FagGe Rashin MutunciBinta Rabi'u Ali Laraba Agage Copyright : B.A.R.A. Agege. Hakkin Mallaka (m): B.A.R.A. Agege. Shekarar Bugawa2007. BUGAWA A COMPUTER B.T.H. COMPUTERS 080-62218701 GODIYA DA MANUFA Alhamdulillahi Rabbil Alamina. Wassalatu was salamu ala Asharaful Mursalin Sayyadina wa Nabiyyina Muhammad S.A.W. Godiya mai yawa ta tabbata ga Ubangijina mai kowa mai komai, wanda yayi ni yayi ku, sannan ya kwararo mana da manufa daban-daban a zukatanmu. Ina godiya ga Ubangiji da ya nufe ni da rubuta ci gaban wannan littafi mai suna RASHIN MUTUNCI wanda kuka dade da karanta na dayansa, a dalilin wata 'yar matsala da na samu wanda nake fatan Ubangiji ya tsayar da ita kenan. Bayan haka manufata ga rubuta littafin nan yana da yawa, to amma wanda yake shakiki a ciki shi ne, ba wai na rubuta shi ba ne saboda wani ko wata, sai dan kawai abinda ke faruwa a al'ummanmu 'A YAU'. Na rubuta RASHIN MUTUNCI nc domin fayyace gaskiyar abinda ke faruwa a tsakanin 'yan'uwa kai hatta wadanda suke ciki daya wanda kansu na wallafa wannan littafi. Kar jama'a su ta'allaka akan cewa sai lallai 'yan'uba ne ke bakin cikin junansu, wanda sam!! ba haka ba ne. Saboda haka jama'a sai a lura a gane cewa zumunci ya fi gaban wasa, in ba a yi sa anan duniya ba, to wallahi ża'a yi sa a lahira. Da fatan duk wanda ya karanta littafin nan zai dauki abubuwan da zasu yi masa amfani a ciki yayi aiki da su, ya watsar da wanda ba su da amfani, domin kuwa no one is perfect no matter how expert you may be. Sannan kayi tunanin karshenka in har ka kasance mai irin halin Alhaji Yusuf. TUKUICI GA: Kannena Zainab, Hafsat, Sani, Salis Tahir Mande. SADAUKARWA NE GA: Kannena Amina Rabi'u, Sagir (M.S), Yakub, Muhammad, Hassana, Husna Tahir Mande. KYAKKYAWAN FATA GA: Iyayena H.Binta Tahir Mande(Asabe), A. Tahir Mande, da A.Bashir Mande, dawana Auwal Tahir Mande. KYAUTARWA NE GA: Hajiya Hauwa'u Bashir Maude (Naira Power), da amarvarta Anty Amina, da yaransu gaba daya, Allah ya raya mana su, aminMUSAMMAN DON: Yarana Tahir A. Rabi'u (MD), Ibrahim Rabi`u Halilullahin Furera: Rabiu (lhsan Smatt Eondoner), sannan mahartinsu Alhagi Rabr'u Ali Usman (Sweetheart). GODIYA TA MUSAMMAN GA: Kawayena Shafiya Alhaji Tanko Mai Rago (Mrs Bakure), Hadiza A. Lawan (Maman 'yar Baka), Hadiza Sani Shuaibu (Hajiyayye), makociyata Hajiya Nana A. Papi (Maman Ummita). Bana iva suya na manta da albasa Hajiya Binta Sani Shuaibu ilnnan Fahad) babbar yaya kenan, Allah ya bar mana ke amin. Ubangiji va kara zaman lafiya Sakanınkr da kishiyarki Hajiya Binta Sani Shu`aibu (Inna Haw Ya raya maku zmyarku. Hajiya Binta Rabi'u Shu athu Innai bán mnua da ke ba. t bangin ya Kata miki hakur kkka yi. Ya sa kuma ajanna ce akomarsa) 3 5 ogi hade da radadin da suka addabe ni ne yа Z sanya ni na farka daga wahalallen barcin da nake yi, sam na kasa bude idanuwana saboda nauyi da suka yi mini, sannan hankalina gabaki daya a tashe yake a dalilin mummunan mafarkin da nayi. Tabbas mafarkin ya firgita ni ainun, domin ganin yadda mutanen biyu da suke tsaye a kaina suke shirin zare robar da aka sanya mini a baki hade da hancina ta oxygen domin taimakawa numfashina. Kuma suna sanye ne da kayan likitoci. A zahiri na farka amma zuciyata ba ta daina dukan uku-uku ba. A hankali na fara kokarin bude idanuwana da tuni na dan fara jin saukin nauyinsu, ga mamakina sai kuwa na ga mutaen nan biyu a tsaye a kaina fuskarsu a Taure. Baki dogon ciki yana rike da sirinii In, yayin da gajeren ya mika masa wata yar karamar kwalba mai dauke da ruwan magani. Gabana ya yanke ya fadi, na kasa motsa ko'ina a jikina saboda tsananin razana. Zuciyata kuwa ta kasa tunato komai na game da addu'a, sai salati kawai na ke yi. Gajeren ya matso daidai kaina ya yaye mayafin da aka lullube ni tun daga iyaka wuyana har kafaduna, sannan ya karbi sirinjin ya daga sama yana matsawa, ruwan ya dan yi tsartuwa, sannan ya nufo wuyana yana kokarin danna mini. Cak! Ya tsaya hade da kallon dan'uwansa, lokaci guda suka faďa wata kofa dake cikin fakin suka rufe. Lokaci guda na ji an murda kofar shigowa dakin 4 マ hade da sallama. Dr Idris ne ya shigo fuskarsa cíke da fara'a yana murmushi. Na ja wani gwauron numfashi na ajiye hade da hamdala. Ya lura da yanayina, saboda haka sai na tsince shi yana fadin "Uzaif ka farka? Ya jikin naka?" Na kalle shi na kauda kaina. Ya zauna a gefen gadon ya ci gaba da magana "Komai fa sai a hankali kar ka ce zaka dinga damun kanka, in sha Allahu Every thing will be o.k." Ni dai hankalina duk yana can kofar da wadannan mugayen mutane suka shiga, domin ba ni da tabbacin ko ina ne kofar da suka shigan, dan na fahimci kofar da Dr Idris ya shigo an rubuta Special Ward, sannan ta bandaki an rubuta Toilet, ita kuwa wannan kofa da suka shiga babu komai a rubuce a jikinta. Take na daga hannuna ina yi masa nuni da kofár. Ya kalle ni ya ce "Fitsari zaka yi?" Na girgiza kaina. Ya sake cewa "Bayan gida zaka yi?" Na sake girgiza kai hade da nuna masa kofar ina yunkurin mikewa. Yayi saurin maida ni izuwa kwanciya hade da mikewa, ya ce "In shiga wannan kofar kake nufi?" Na yi saurin kyada kaina. Take ya bude kofar a hankali hade da tura ta, ya shiga ciki ya maida kofar ya rufe, ya kusa minti biyar da shiga sannan ya fito yana share gumi da farin hankicin da ke hannunsa, bai ce da ni kala ba ya nufi Computer da ke ajiye akan karamin tebur din da ke 5 gefen gadona yayi 'yan tabe-tafensa sannan ya zare mini robar oxygen din. Cikin kaguwa na ce da shi "Dr kashe ni za su yi, su biyu ne sun shiga wannan kofar." Ya kalle ni ransa a bace ya сe "Ka kwantar da hankalinka Uzaif insha Allahu babu abinda zai sami rayuwarka anan. Tabbas na shiga, amma kafin na karasa garejin tuni sun tashi motarsu sun yi gaba." Ya dan yi shiru, sannan ya ce "Nayi mamaki kwarai domin kuwa wannan kofar ba a bude take ba, don ba a amfani da ita, haka ta sauran Special Ward din da ke asibitin, domin kuwa na tabbata duk cikin mu likitocin da ke aiki a asibitin babu wanda yake rike da ko wane dan makulli na kofofin dakunan da ke cikin asibitin. Ita wannan kofa tana leading ne izuwa gareji saboda inmajensi (Emergency), kenan da an taho da marar lafiya cikin gaggawa za ayo nan da shi Special Ward; sannan a take a ba shi treatment ingantacce kamar yadda akai maku. To a tsammanina bayan kawo ka ne aka manta ba a rufe kofar ba, ko kuwa mukullina aka samu ta hanyar maciya amana da ba su san darajar aikinsu ba, amma dole ne in sanar da M.D. domin a dauki mataki na musamman. Duk wannan bayani da yake yi, yana yi ne idonsa kur a kaina yana mai nuna tsabar tausayawa. Ya danyi gwaje-gwajensa ya mike yana mai yi mini Allah ya kara sauki hade da nufin barin dakin. Cikin sanyin murya nai kiran sunansa, ya waiwayo hade da tsayawa cak sannan ya amsa. Na yi shiru kamar in fasa tambayarsa abinda nayi niyya. Ganin haka ne ya sa ya 6 juyo sosai ya sake nufo ni, ya sa hannu ya shafa kaina "Haba Uzaif na ce da kai babu komai Insha Allah za mu nemi taimakon 'yan sanda ma in har hakan zai faranta ma rai." Ya dan yi shiru. Shi a tunaninsa ko har yanzun tsoro nake ji, bai san gaba daya tunanina ya koma kan masoyiyata ba "Dr wallahi ni ba wannan nema yake damu na ba." Na dan yi shiru. "Come on Uzaif talk mana. Na kalli gefe guda sannan na ce "Dama tunanin jikin Uzaifat kawai nake yi, don ban san a matsayin da takc ba." Ya ja numfashi ya ce "Babu komai jikin nata da sauki kamar naka, kuma tana Next Ward." Nayi farin cikin jin haka "To kana ganin zan iya ganinta?" Yayi murmushi ya ce "Ka kara hakuri dai Uzaif, domin ba ku gama kwari ba duk kanku, ina so sai ka fara taka kafafunka sannan." Ya kare maganarsa da murmushi, sannan yayi waje. * ** Tun fitar Dr Idris zuciyata ta nutsu cikin tunanin Uzaifat take na fara tunanin tun daga ranar da na bupi ido na ganta a NAGARTA HOSPITAL har zuwa ranar da yayana ya ritsa ni a dakina. Tabbas an ce ka so mai sonka ko ba komai rayuwa tai maka dadi. Uzaifat ta zama wani bangare na jikina wanda ba za a taba gani ba ballantana a yanke a yar "Zuciya" kenan. Ta yi risk din rayuwarta a kaina, ta sadaukar da ranta a kaina, tayi mini abinda ba kowa ne zai iya yi mini shi a rayuwan 7 nan ba. Uzaifat ta cika mace a cikin mata, kuma ta cancanci yabo. Tabbas da lafiyata lau ba yadda zan yarda in wayi gari in tsinci mai kaunata na mawuyacin hali in kasa agaza mata. Sallamar da na ji ce ta yanke mini tunanina, na daga kaina hade da amsa sallamar. Ta nemi guri ta zauna jikinta na rawa, jefi-jefi kuma ta kan yi ajiyar zuciya mai cike da nuna alamun tayi kuka har ta gode Allah. Ganin ba ta da niyyar yin magana ne ya sa gabana dukan uku-uku, zuciyata kuma tuni ta dauki haramar bugawa. "Nafisa, lafiya kuwa?" Tayi shiru ba ta amsa ba. "Haba Nafisat ya zaki zo mini da wannan suffa? In wani abu ne ya faru ki sanar da ni mana." Shiru ta sake yi ba tare da tace da ni kala ba. Na yunkura zan mike, na kasa. Ganin haka ne ya sa ta ta tashi ta matso kusa da ni idanunta na zubda hawaye, sannan ta ce "Ka yi kwanciyarka yaya, da ma tambaya ce na zo in yi maka, amma dan Allah you have ta tell me the truth." Ta yi numfashi mai zafi wanda tururinsa ya daki fuskata "yaya please tell me su waye iyayena?" Kaina ne ya fara sarawa sannan gabana ya ba da gudunmawar faduwa, zuciyata kuwa sai da tayi wani irin bugu wanda ba ta taba yinsa ba. Tambayar ta girgiza ni ainun, saboda ban taba tsammanin wannan tambaya a rayuwata ba. "Yaya ka sanar da ni kawai, saboda 6oyewar ba ta da wani amfani tunda tuni Daddy ya sanar da ni cewa in nemi iyayena a gaba in bar masa gidansa......" Ba ta 8 Karasa maganarta ba ta barke da kuka mai ratsa zuciya. na dangana yaya, wallahi na dangana!!! Jikina gaba daya yayi sanyi na kasa katabus. Da na ga kukan nata sai ci gaba yake yi ne na bude baki da Kyar ina fadin "Haba Nafisa, wane irin zance ne wannan? Idan zuciya ta bata ina ce hankali ne kc nemo ta? Ni dai ban sån wasu iyaye naki da suka wuce Hajiya da yayana ba domin kuwa..... Kallon da tayi mini mai cike da rashin amincewa ne ya sanya ni dakatawa. "Ni dai yaya ni na san abin da kunnuwana suka jiye mini, wallahi ko ka sanar da ni gaskiyar al'amari kamar yadda Daddy ya umarce ni da in zo ka sanar da ni. ko kuwa inna tashi daga nan in bi uwa duniya in huta da wannan bakin ciki da ya addabe ni." Jin haka ya sa ni daka mata tsawar da ban yi niyya ba "Ba ki da hankali ne Nafisa? Ki bi duniya kamar yaya? To koma mene ne ki bari sai na samu sauki mun koma gida." Ba ta tanka ba kuka kawai ta ci gaba da yi. * Ni da kaina na tabbatar da cewa Dr Idris ya dauki tsattauran tsaro a kaina, domin kuwa duk wanda ya zo dubiya gurina sai da amincewata zai shigo, idan har kuwa na ce ban san mutum ba to ta zauna sai dai ya hakura ya koma, in ba haka ba kuwa ya fuskanci tashin hankali. Hankalina har yanzu bai yi daidai ba domin matsaloli biyu da ke addabar raina. Na farko sam Dr Idris ya ki bari in ga masoyiyata daidai da minti daya balle in san halin da take ciki ko zuciyata ta yi sanyi. 9 Duk sanda na tuntube shi sai dai ya kawo mini Excuse, Na. biyu kuwa Nafisat, domin ban san yadda zan yi da ita ba in na koma gida, domin kuwa tashin hankali ne a tare da mu gaba daya in sanar da ita cewa ba su yaya ba ne iyayenta, to shin ina zamu nemo nata iyayen? Tabbas yaya yayi kuskure da ya sanar da ita wannan Magana, dan kuwa laifina bai kamata ya shafe ta ba. Sallamar da na ji ce ta yanke ni daga tunanin da nake yi. Dr Idris ne ya shigo wannan karon su biyu ne shi da wani mutum mai kirar 'yan ibo amma a zahiri bahaushe ne. Bayan yayi gwaje-gwajensa ne yayi introducing din Sa'id Muhammad a matsayin sabon likitan da suka sake yi a asibitin, ya sanar da ni a yanzun haka ma yana kaisa Ward-Ward ne domin ya ga tsarin asibitin da yadda suke gabatar da ayyukansu. Sa'id Muhammad mutum ne mai fara'a hade da barkwanci, wanda hakan ya sa har muka dan saba a tsakankanin wannan lokaci. Har sun juya nai kiran Idris na ce da shi ina da magana. Yayi murmushi hade da fadin "Malam Uzaif kenan ni dai na san zancen gizo baya wuce na koki." Ya kwashe da dariya a daidai lokacin da suka fice daga dakin. - Bayan dawowar Dr Idris sai da muka dauki wani lokaci muna fafatawa akan ya bar ni in je in ga Uzaifat amma ya ki, sai da ya ga na nace ne yake sanar da ni cewa "Ba wai ba na son ka ganta ba ne Uzaif, dalili kuwa shi ne tunda aka kawo ku sai da Uzaifat ta kwashe kusan kwana uku ba ta cikin hayyacinta а sakamakon buguwa da kanta yayi, sannan ko da ta 10 lartado da sunanka ta budi bakr. Ita ma haka ta damu akan tana son ganinka, sar da na tabbatar mata da ce%2 kana nan lafiya sannan ta hakura, Da ma tunanina bzi wuce in ga duk kun samu sauki vnai ba, domin in har zaku fuskanci junanku a cikin yanayin da kuke lo fa tashin hankali zai zame muku, amma tunda kon amu sauki zan sa Nas ta kawo ta nan wájenka tunda kafarka har yanzun da sauranta. Na ji dadin maganarsa kwarai na yi masa godiya. Ya mike yanayi min dariya. Fitarsa ke da wuya na ji an bude kofa da sallama. Nas ce ta riko hannunta suka shigo, ta nemi guri ta zauna a bakin gado. Bayan Nas din ta fita ne muka kalli juna zuciyarmu cike da farin cikin ganin juna. Tabbas Uzaifat ta ji jiki in ka yi laakari da bandejin da aka daura mata aka da kafafunta. Na tashi zaune ina mai tausaya mata. "Czaif sannu yaya jiki?" Ta tambaya-muryara na rawa. "Haba Czaífat ai ni zan tambaye ki jiki." Ta yi hishiru tana kallona fuskarta duk a kumbure. Ta fashe da kuka a lokacin da ta kurawa kafafuna da suka sha bandejí ido. "Ba komai Ľzaif Allah zai yi mana sakayya." "Da ma kin san Any disappointment is a blessing." Na fada ina kallonta ido cikin ido. ban ankara ba na tsinci Dr. Idris a bakin kofa. 11 Mun samu wata-uku a asibiti sannan aka sallamé mu a sakamakon warkewar da aka tabbatar mun yı. Bük tsawon wannan lokaci babu duriyar Hajiya balle na yayana. Ko da yake Nafisa ta sanar da ni cewa bayan sun dawo daga asibiti yayana ya tare su ya sanar da ita cewa ba shi ne ya haife ta ba ta je ta nemi iyayenta, sannan kar ta kuskura ta tunkari gidansa. Ita da kanta Hajiya garin ba da hakuri sai da ta shå wawan mari. Abun farin ciki kuma shi ne Nafisa ta sanar da ni ceWa Hajiya na da juna biyu a sakamakon zuwansu asibiti. Na taya Hajiya farin ciki da fatan Allah ya sauke la lafiya ganin cewa shekararsu ashirin da 'yan kai"da yayana amma sai yanzun ubangiji yayi musu arzikin haihuwa.. Muna kan hanyarmu ta komawa gida Nafisa ta sanar da ni cewa gida ba kowa daga ita sai Baba Musa, yayana tun a ranar da abun ya faru ya dauki Hajiya suka bar gida. "Faduwar gaba asarar namiji." Na fada ina murmushi. Sai a lokacin ne na sanar da su yadda na danawa yayana tarko, da yadda ya ritsa ni. "Amma ga shi komai ya tashi a banza, tunda komai ya koma hannunsa." Uzaifat ta ce "Ba dai komai ba, domin tabbas lokacin da na riske-ku har ya make ni, kafata ta buği wani abu kamar rikoda kamar camera yayi Rarkashin firij. 12 Dadi ne ya mamaye mini zuciya hade da fatan ubangiji ya sa yayana bai ga lokacin ba ya dauke. Bayan ham din da muka yi baba Musa ya bude mana Gate muka shiga. Ya karaso yana murmushi hade da yi mini sannu "Ban sami damar komawa ba tun da na je sau biyu na tarar kana bacci. Barayi ne suka takurawa unguwar yanzun, shi ya sa bana fita ko'ina, jiya ma sai da suka shiga gidan malam Muttaka." Nayi salati na ce "In ce dai ba suyi masa komai ba ko?" Baba Musa ya fada dakinsa yana fadin "Haba Uzaif ai malam Muttaka ya ga ta kansa, domin su yi masa wulakanci wai dan ba su samu kudi mai yawa ba suka harbe masa yara biyu har shi kansa ba su bar sa ba sai da suka harbe sa a kafar dama." Labarin ya girgiza ni, nayi wa yaran addu'ar Allah ya jikansu, shi kuma Allah ya ba sa lafiya, sannan nayi nufin shiga ciki wanda dama tuni su Nafisat sưn shige dan sun san surutun baba Musa baya karewa. Kira na da baba Musa yayi ne ya sa ni na dawo, hannunsa rike da Brown din Envelop yana murmushi ya miko mini "Ga shi wani yaro ne matashi ya kawo, kuma ya sanar da ni cewa in ba kai ba kada in bawa kowa hatta Alhaji." Na karba hade da tambayar "Wai in ji wa?" "Bai fada ba, amma ya ce akwai muhimmin bayani a ciki." Nayi masa godiya na shige ciki. Na tarar da su Uzaifat a zaune akan kujera kowacce da kofin ruwa a hannunta. Na nemi waje na zauna ina jujjuya Evelop 13 din hannuna. Nafisa ta mike a yayin da ta nufi kicin gami da tambayata ko ina na sami sako? Nayi shiru ina kallon Envelop din har ta fito daga kicin din ta sake neman waje ta zauna. Na kalle su na ce "Wallahi wasika ce baba Musa ya ba ni, amma har shakkar bude יי ta nake yi saboda ban san me zan tarar a ciki ba." Uzaifat tayi hanzarin cewa "Akan me za kai shakka? Ko fargaba kake yi kar irin ta Dele Giwa ta kasance maka?" Muka tintsire da dariya, sannan na ce "To in dai wasika ce aka kawo ba tare da wanda ya aiko ya fadi sunansa ba, shi ma dan aiken ya ki fadawa baba Musa wanda ya aiko. Haka dai na daddage na bude wasikar na fara karantawa. Daga wacce take a matsayin mahaifiyarka. Bayan gaisuwa da fatan alheri, ya bayan saduwa? Ka san ce mai karanta wannan wasikar. Sauki ya tabbata a gareka, Allah ya sa hakan amin. Ya su Nafi da Uzaifat, ita ma ya nata jikin? Ubangiji ya baku lafiya tare da kara muku juriyar hakuri. Bayan haka Uzaif ba komai ne ya sanya na rubuto maka wannan wasikar ba, illa in ba ka hakuri kuma in tausasa maka zuciyarka akan abinda yayanka ya aikata gareku. Uzaif abu daya nake son ka sani cewa fa shi ubangiji ba azzalumi ba ne, duk abinda da mutum ya aikata imma hairan ko sharran to ubangiji yana kallo, kuma zai yi hisabi a ranar da dan'adam ba shi da wata katabus sai aikin alherin da ya aikata, saboda haka Uzaif kuyi hakuri ubangiji zai saka maku saboda ni da 14 kansab yaneh Hа bыdarda dewayayüika shi ne kd gindinedakanfbddk&afkiwaa gard ka har a thasoy4yarkaliewato Uzalfatsaboda haka Uzaifkakakа nki wani mata Ka barwa abangijn koihđi đon Shi ne'ntai sakayya domin in HiarsA hajioyifuskanci kid Shitih aikata wahi abti gare shi, to wallahi ka san ya tara 'yan iska wadanda zasu iya ikand komiai saboia bamun abur duani kuma rayuwarku ita ce muhimmiye gare i! Hakurl Shi ne yaskartneu kaihadeda adit'a a kowanne lothei! Magana ta biyu kuwa ita ce akan Nafisa konmai runtsi kar ka sanar da ita komai akan Background dinta, doino yinrhakanař zome makd babbah thstin hankali. A ranar daA ajt onyi mhne Wayau ya tirar nlagi hartyalaikata malk annan hummuhar abu, y ae achanyalya eiwa Naft mitunel ya kama faf körhkr ganet Ua Kiahtl WandaakalJ ARUBISHI sherara batantanaus o arna, unihdiana itsanfP haka ku Abufa nay tiik haP Th en Gidansa nacwbuja a aaska sahi Han üah ajiye shananvya Nanga thasugadikapy i fita, hunzafta zuwa Rathoya Uwo Yath ANANRila he is fi nabig sbud sat asy a Taku har abada Hajiya Maryam. a 15 Ina kammala karantawa na mayar da wasika na mike ina shirin maida ta cikin Envelop gudun kar Nafisa ta ga ma ke ciki. Amma kafin na aikata hakan, ta wurgo mini tambaya "Yaya wane ne ya aiko da ita?" Ni da kaina na san cewa 6atan basira ne ya sanya ni na ce da ita "Hajiya ce ta aiko mana da gaisuwa." Ai nan take ta mike ta nufo ni tana dariya "La wallahi sai ka ban na karanta ni ma."יי Kafin na ce me tuni ta firge takardar daga hannuna. ** ** Mun lallashe ta ne da kyar bayan mun daukar mata alkawari zamu ziyarci Abuja very soon, tare da alkawarin cewa duk inda iyayenta suke sai mun taimaka mata wajen nemansu. Na tashi na nufi dakina ina taka matattakalar bene hade da yiwa Hajiya addu'a domin a rayuwata ban taba ganin mace mai hankali da nutsuwa hade da sanin ya kamata ba irinta. 'Ubangiji ka sauke ta lafiya, hade da raya mata abin da zata haifa." Na fada a raina a lokacin da na murda mubudin dakin na shiga. Gabana ya fadi lokacin da na riski anyi wa dakin tsinke duk an hargitsa shi, amma cikin ikon Allah ba a taba firij ba, dan haka na sunkuya na leka karkashi, ga mamakina can na hango ta kwance tana ta walkiya kamar ba ta shafe wadannan watanni a wajen ba. Na sa hannu na dauko ta lokacin da fuskata ta fadada izuwa murmushi, nayi godiya ga ubangiji. Bayan na bude gidan Film din na tarad shi ma yana nan 16 a mazauninsa yana shakatawa. Na bucfe akwatina na jefa ta ciki hafe a hargitsa lambobin. * Sautin amon wakar shahararriyar mawakiyar nan Celine Dion ne ke tashi wato Think Twice sannu a hankali, falon yayi tsit duk sun nutsu akan nazarin mujallar da ke hannunsu ta Daily News Paper illa ni kadai kawai da ke rike da littafin Hausa na Hajiya Binta A. Rabi'u Ali Agege wato Tsautsayi ko Kaddara? Na fara jin dadin littafin ainun, amma saboda matukar son wakar ya sani ajiye littafin na nutsu wajen saurare. Kaset fin ya kare na tashi na nufi wajen redio domin juyawa izuwa daya bari. Uzaifat ke tambayana inda na ajiye mata Mixmac dinta maganin ciwon cikin da take amfani da shi in ya murda mata. Na ajiye kasct akan redio ba tare da na sa ba, na nufi bayan babbar kujera na dauko ina fadin "Ya fara yi miki ciwo ne cikin?" Ta amsa da "Yana dai so ya fara ne, shi ya sa zan yi

Chapter 1 of 6