da su T.J suka yi wani yare wanda ban fahimce shi ba.
Bayan kamar minti biyar wannan saurayi na tsaye kamar sanda ni
kuma ina dag ajikin bango mahailiyata kuma tana jikin gado sai T.J ya
shigo ko ina ya kai mahaifina Allah kadai ya sani. "Ke juya jikin
bango". Wannan saurayin ya umarce ni, ba shiri na bi umarninsa.
Fuskata na jikin bango na ji kamar ana kikiniyar fada, ina son na juya
amma bahu dama. Can da na ji abin ba mai karewa ba-ne sai na juya. ai
kawai na karyata abin da idona ya gani domin shi wanna saurayi ne ya
ke kokarin kwantar da mahaifiyata a kan gado amıma ta ki yarda. Can
da ya ga ba ta da niyyar yarda sai ya rotsa mata gindin bindiga a ka,
tuni ta fadi a kasa sumammiya don haka sai ya mai da ita kan gado. T.J
bai lura da na juyo ba sai da na gama kallon duk abinda ke faruwa
tukunna. "Ke ba cowa aka yi ki juya ba?". Na juya fuskata jikin bango
a daidai lokacin da hawaye ya gangaro mini, na riga na san abin da zai
faru. Bayan 'yan mintoci sai wannan gayen ya umarce ni da na juyo,
ina juyawa na ga yana gyara wandonsa ita, kuma mahaifiyata tana
kwance a kan gado ba ta san inda kan ta ya ke ba na dai riga na san ya
riga ya keta mutumcinta. Cikin hawaye na sake kallonsu. T.J na girgiza
kai. "Ai saura kuma ke". Da jin haka gabana ya fadi nan na dinga
tunanin yadda zan tsira. Saurayin ya fara matso ni a hankali nima na
fara matsawa da baya, da na shammace su sai kurum na ratsa ta
Isakiyarsu da gudu na nuli hanyar fakina. Suma suka biyo ni da gudu,
"Tsaya, tsaya", Suka soma umarta ta, amma ina ai ko rage gudu ban yi
ba. halle na Jsaya, kalin na karasa kofar dakina sai na ji saukař bindiga
a Kafata. duk da radafin da na ke ji sai da na karasa daki na yi sauri na
51
mai da kofa na rufe. Suka zo suna ta bubbuga kofa, da suká ga cewa kansu za su 6atawa lokaci sai suka yi gaba. Bayan tafiyarsu na duba agogona karfe uku da rabi don haka sai na dauki dankwali na daure
inda suka harbe ni daga nan kuma sai bude ido na yi na ganni a asibiti.
Sai da na yi jinyar wata uku da kwana hudu sannan na samu sauki, ka ji dalilin yawona da bindiga 1..tina duk inda na ga su T.J sai na harbe
su a kan abin da suka yi min shi ya sa na shiga.nemansu ruwa a jallo.
Tun da yanzu na san in da suke sai na far musu bazata, na yi kaca-kaca
da rayukansu sannan na shiga neman Alhaji. Sa'arsu daya na samu
mahàifina da rai to zan iya ramgwanta musu in tura su ga hukuma,
amma in har ya mutu wallahi duk kansu sai sun bakunci lahira da
wanna bindigar tawa, ba zan fasa ba tun da har na dauki alkawari. To
ka ji d...ilina".
Na yi ajiyar zuciya na kalli Uzaifat duk hankalina a tashe, na cе
"Ki kwantar da hankalinki duk za su zo hannu tunda kin san
ma6oyarsu". Uzaifat ta dube ni ta 'ce "Sai dai kawai mu far musu ba
tare da hukuma ta sani ba". Nafisa ta kalle ta ta ce "Haba kamar
wadannan gungun mutane mu ce za mu far musu mu kadai? Ai sai duk
kanmu sai mu bakunci lahira. Shawarata a nan shi ne mu bari idan
lokaci ya yi mu je mu samu inspector Kabir mu shaida mishi kun ga sai
ya hada mu da 'yansanda, ko me kuka ce?". Dukkkanmu muka amsa da
"Haka ne". Da Nafisa ta ji Uzaifat bata ci gaba ba sai ta ce "Yana ji kin
yi shiru". Sai Uzaifat ta ce "Ai shi ke nan". Nafisa ta kalle ta ta yi
murmushi ta ce "Haba ba dai shike nan ba, saura haduwarki da su T.J".
Sai Uzaifat ta ce "Ai ba yanzu zan bayar ba sai Uzaif ya kammala min
labarinsa tukunna, za ku ji yadda na hadu da su da wuyar da na ci da
yadda na gudu". Da yake Nafisa ba ta san na bawa Uzaifat labari ba sai
Nafisa ta ce "Tun da. ni na san wannan labarin bari in je in yi nazari,
idan ya so in za ki ci gaba da naki sai in zo". Har Nafisa ta tashi da
yake Uzaifat ba ta son su rabu sai ta ce da ita ta zauna ita za ta ci gaba.
Murna ta ishe ni domin ta hutar da ni. Har za ta fara bada labari sai
Hajiya ta shigo hannunta, rike da wata bakar leda. "Nafisa ta shi na
aike ki gidan yayana Mukhtar, ki kai mishi wannan ki ce ina kuma
gaishe da Hajara da yarta Aisha. Shi kuma Abba ki ce da shi idan ya
samu dama gobe ya leko". Nafisa ta karbi kaya duk ranta a 6ace har za
ta fita sai Uzaifat ta ce za ja raka ta kannan ta dan saki fuska. "Mukillia
Daewoo za ki dauka fa". Nafisa ta çe "To". Tun da suka tafi ba su suka
52
ka dawo ba sai goma da kwata na dare. To dana ga lokaci ya yi sai na
ce da su bari sai gobe a ci gaba da labarin tun da dare ya yi. Nafisa ba
da son ranta ta yarda ba.
**** **** ****
Bayan mun yi sallama da su Uzaifat kowa ya nufi dakinshi sai na
fara tuna abinda nake shirin aiwatarwa. Shin ya zan cimma burina? Na
tambayi kaina domin yau su T.J. za su zo. "Kada ka yi sake wannan
dama da ka samu ta wuce ka domin wannan ita ce damarka ta.karshe,
idan kuma ka yi wasa ta wuce ka to shike nan ba za ka kara samun
wata ba ". Ina cikin tunani agogon dakina ya buga karfe goma sha
daya. Nan da nan na mai da hankali a kan abinda na ke shirin fuskanta,
domin saura sa'a daya mugwayen su kasance a kofar gidan mu. Da me
zan fara? Na tambayi kaina. Watadabara ta fado mini don haka sai na
dauki rikoda ta na nufi kofar gida.
Ina zuwa harabar gida na tarar da Baba Musa yana zaune a kan
benci hannunsa rike da tocilan. Yana ganina ya dallare mini ido da
tocilan, nasa hannuna na kare domin hasken ya yi yawa. Na karaso
wajensa, ina masa murmushi shima yana yi mini dariya, "Malam Uzaif
kai ne da tsakar dare haka?" Na ce da shi "Wallahi baba Musa kasa
barci na yi shi ya sa na fito mu yi hira maiyiwuwa daga bisani idan na
köma ya yiwu na yi barcin". Baba Musa yace "Ai yana da kyau amisa
masa a daidai lokacin da na zauna kusa da shi. Mun fara hira ba mu yi
nisa ba na tura hannu a aljihu na zaro kudi na fara kirgawa. "Bara na
kirga sauran kudina domin yau na yi siyayya da dama".
"Haka fa". Baba Musa ya amsa. Dariya ta kama ni amma sai na
dake na ci gaba da kirgan wa-zo-biyoyi. Na kalli baba Musa ta
wutsiyar ido sai na ga ya kurawa kudin ido ko kibtawa ba ya yi. Da na
fuskanci haka sai na yi godiya ga Allah dòmin hakana ya kusan cimma
ruwa. Na kalli Baba Musa muka hada ido ya yi mini yake a nufinsa ya
yi murmushi. "Baba Musa ya kamata na yi maka alheri ko?". Ya amsa
da sauri múryarsa na karkarwa. "Babu shakka". Na yi dariya cikin
gudun kada ya gane gadar zaren dana ke shirin shirya masa. Na kirga
wazobiya guda goma sha biyu na bashi, tun kafin ya karba ya ke ta
hadiyar yawu. Ya karba don murna har da hawaye da na ga haka sai
na ce da shi. "Haba Baba Musa dan na yi maka wanna yar kyauta? Ni
53
da
"Sabon
na ke shirin siya maka keke mai fitila a gaba? Ya sake tambayata me ka ce?". "Sabon keke mana ko ba ka so?" Ya kalle ni ya ce "Ka ji dannan me ya fi wannan alheri a gare ni?. Kai amma Allah Ya saka maka". Na ce "Amin". Dana kalli agogon hannuna na ga shadaya ta wuce da minti ashirin da biyu sai na mai da hankalina ga ba ba Musa domin na yi abinda ya kawo ni. Ina kallonsa na ga hankalinsa duk yana kan kudin da ke hannunsa sai na yi gyaran murya na ce "Baba Musa". Ya yi firgigit ya amsa "Na'am". Na kura mishi ido na ce "Don Allah za ka iya tuna mutanen da suka zo nan kwanaki uku da suka gabata?. Ya daga kansa sama da alamun tunani ya ke yi. Da ria ga idan ban wayar mashi da kai ba zan Gatawa kaina lokaci saina kara da cewa "Da misalin karfe goma sha daya suka zo su biyu nan da nan ya ce "Ayyo wadannan namijin da macen da suka zo wajen Alhaji?". Na amsa cewa "Su fa". Na ce "Shin ko ka saurari abin da suka tattauna a kai?". Ya ce "Ina ai ina sallama da Alhaji Ya ce da ni na fita waje idan sun gama na shigo shi yasa Ban ji hirarsu ba". na ce "Da kyau". Kannan na ci gaba. "Baba Musa don Allah wani aiki nake bukatar ka yi mini...", ban karasa ba ya katse ni. "Uzaif ai kawai ka fada kanka tsaye ko mene ne zan.yi maka". Na ja gwauron numfashi "Wato alkawari na daukarwa
wannan macen kuma na ke son in sauke. Makaranta da ya muka yi da
ila sai muka saba har ta zamo kawata. Bayan mun kammala makanta shi ne kowa ya kama gabansa to shi ne muka dade ba mu hadu da ita ba. Ranar da muka tashi haduwa sai muka hadu a kofar kamfanin Alhaji, bayan mun gaisa sai ta ce da ni gurin mai kamfanin ta je. Muka -çi gaba da hira har na ce da ita a gidan mai wannan kamfanin na ke sai
ta ce idan anan na ke me ya sa da ta zo ba ta ganni ba? Sai na ce me yiwuwa na yi barci a wannan lokaci, sai na karyata ta na ce idan har ta
zo ai zan san da zuwanta, to a nan ne ta ce da ni za ta kara zuwa gidan, idan kuma na ganta to ta yi mini alkawarin mota, da yake iyayenta
masu kudi ne shi ya sa na yarda za ta iya bani. To yanzu shi ne na ke
son na nuna mata cewar karewar sanin zuwanta har abin da ta ce na ji. Shi ya sa na kawo maka wannan rikodar domin ka boye mini a inda babu avanda zai gani, ka daukar mini maganarta". Baba Musa ya ce "Babu laifi, wannan ai karamin aiki ne". Na kara da cewa "Ka bari sai
sun zo kafin su shigo sai ka boye, kuma idan sun tafi kada ka yi saurin daukowa sai Ka ga Alhaji ma ya shiga har ya rufe kofa tukunna, Idan har ka aikata hakan gobe sai na dada kara maka wasu wazo-biyoyin".
54
Daga nan na nuna masa inda zai kunna da kuma inda zai kashe, kana
muka yi sallama na shiga gida na barshi a nan. Ina shiga daki na dubi
agogon bango domin har na manta da na hannuna don murna. Agogo
ya nuna karfe goma sha biyu saura minti bakwai, nan da nan na dauko
kemarata na cire gurin filasha domin kada in dauke su a hoto haske ya
tonamini asiri, abin 6oye ya fito fili. Daga nan na fito daga dakin na
shiga kicin na boye ina jiran fitowar Alhaji.'
Baba Musa mai gadi ya manyanta domin zai kai shekara hamshin
da bakwai a duniya fari ne dogo tsamirarre, kamar goyon yunwa
fuskarsa kullum a daure take kamar wanda ya ga mala'ikan mutuwa.
Na fuskanci baba Musa ya yi sabo da takardun kudi shi ya sa na shir ya
mashi wannan tuggun. Na san zai yarda da abin da nace da shi, ko da
kuwa bai yarda ba to tabbas zai yarda da takardun wazobiyoyin da zan
rudeshi da su shi ya sa na bashi su kamar yadda na ce ya yi sabo da
kudi ban yi karya ba domin a duk inda ya ganka da kudi ko da kuwa
wazobiya daya ce sai ka ga kamar zai kwace daga hannunka.
"Salamu Alaikum! Salaumu Alaikum". Muryar baba Musa
maigadin can kuma aka amsa "Alaikumussalam". Daga jin muryar na
shaida ta yayana ce. Ya fito yana sanye da rigar bacci, suka rankaya
suka fita tare. Gabana na ta faduwa kafata na ta karkarwa kamar ba za
ta iya daukar gangar jikinaba, da haka na karasa har bakin kofa cikin
fargaba da tsoro na yi sa'a kuwa a inda suka zauna kwanaki wannan
karon ma nan suka zauna. Ina lekawa na ga'yayana ya yi hannu da
sussy na yi sauri na daukesu a hoto, suka karayin hannu da T.J. a daidai
lokacin da ya ke yi mishi murmushi, amma sai yayana ya dake baya ko
fara'a can bayan ya zauna sai ya fara fadace fadace har yana nuna su da
yatsansa daga nan na nufi dakina. Ina shigowa abakin gado na zauna
ina dariyar murna na doki cinyata na ce "Asiri ya tonu ai wannan shi ne
(open secret), wato dai an yi shuka a idon makwarwa kenan ba a sani
ba". Can sai rikoda ta fado mini a rai,na ce "Allah ya-sa baba Musa ya
yi mini (as I want) da farin ciki na ya fi haka". Daga nan na gyara
shinfida na kwanta Ina tunani lallai mutum mugun ice ne wai ace
yayana jinina shi ya ke cunkusa ni acikin wahala? Hawaye ya gangaro
mini, ba komai ya sani fitar da hawaye ba sai dan tausayawa yayana da
na yi domin shima ba karamar wahala zai shiga ba. Shi ya ke hada ni
da T.J. da abokin harkarsa chico ashe? Amma sai ya yi kamar bai san
da komai ba wani sa'in har hawayen karya ya ke yi, kai amma Allah Ya
55
tsinewa pretender. Ban san lokacin da 6arawon ya sace ni ba sai ji na yi
ana kiran assalatu, na yi mika kannan na shiga bandaki.
Kamar yadda muka saba haduwa cin abinci haka muka hadu a
wannan rana ta asabar. Kowa ya zauna sai harrakawa cikinsa ya ke yi.
kowa yayi shiru, ni kuwa sai satar kallon idon yayana na ke yi. Na lura
da hankalinsa ba a jikin shi yake ba amma ban darħu ba tun da shi ma
ba damuwa ya yi da ni ba ballantana ya kaunace ni, haka ni ma idan
akwai wanda ba na kauna a duniya to bai wuce shi ba. Tuno da karin
maganar bature da ya ke cewa ("Care for who love not who hale you").
Haka kuma na tuno da addu'ar sa da yake cewa ("Oh God let my
enemy stay long and see what you shall let be tomorrow"). Duk
gaskiya banasare ya fada don haka sai na mai da hankali gurin cin
abinci. Bayan an gama sai na tashi na koma kan kujerar falo na zauna
ina kallon wasan bebi (Catoon) na (Tom & Jerry) ina cikin kallo ita ma
Uzaifat ta zo ta zauna muka ci gaba da kallo. Mun dan viisa da kallon
sai Hajiya ta fito daga cikin daki tana sanye da wani leshi (cofion) mai
ruwan dorawa bayan ta kuma Nafisa ce tana sanye da boyal fari kanta
yafe da bakin mayafi mai shara-shara, tana rike da bakar leda. Hajiya
ta shaida mana cewa za su je unguwa amma ba za su dade ba, muka yi
musu a dawo lafiya suka ansa da Amin. Bayan fitar su Ilajiya da Nafisa
da kamar minti talatin shi ma yayana ya yi shirin tafiya aiki. Da ya
gama sai ya fita, gida ya rage mu biyu daga ni sai Uzaifat. Na ji dadin
hakan domin zan samu damar jin kaset ba tare da wani ya kawo min
cikas ba. Nafisa ce ke hana ni sákewa bini-bini tana daki ga to gashi
kuma bata nan sai Uziafat, ita dama ba kasafai take shigowa ba sai
dalili. Dan haka si na mike na nufi wajen baba Musa domin na karbi
rikodata.
Zuwana na tarad da shia bakin kofarsa a tsaye, yana ganina sai ya
fara yi mini murmushi ganin haka na san cewa komai ya yi zanzan, da
na karasa sai na ce "Anyi nasara ko?" Ya ce dani "Ba dole ba". Ya
shiga cikin dadins aya dauko miri rikoda na kaarba na tura a aldjihu
kanna an zaro wa-zo-biya goma sha biyu na fashi shima ya karba ya
tura a aljihun kannan na juya na shiga cikin gida. Inna shiga falo na
faråd Uzaifat ba ta nan. Saboda haka na yi shigewata daki ba tare da na
damu da irin gurin da ta shiga ba. Inna shiga daki na turo kofa dan
zumudi ko kulle kofar ban yi ba. Na tariyo kasęt kanna na danna
(play.)
56
P
Kaset ya fara aiki kamar mutanen ne da kansu suke kusa da ni suke
magana, kaset ya dinga amayo abinda ke ciki, hankalína ya yi bala'in
tashi da na ji irin maganganun da ke fitowa daga bakin yayana ban san
lokacin da hawaye ya dinga zubo mini a kunci ba. Wani irin bakin ciki
ya cunkushe mini a makwagoro. Gabana ya yanke ya fadi da na ji
maganar mutuwat babana abakinshi, Rirjina ya yi bugun uku-uku, wato
dai dasa hannun yayana wajan kisan mahaifinmu. Na kashe kaset na
sake yiwo baya da shi a zatona ya yi kuskure ne, amma sai na sake jin
ya maimaita abin da ya fada da farko. Nan na fashe da kuka dana tuna
da irin kisan da yaya.na ya sa aka yi wa mahaifinmu. Kaico! Wannan
irin *RASHIN MUTUMCI* har ina? na tambayi kaina. Da na ji ba zan
iya jure jin sauraron abin da kaset ya kunsa ba sai na kashe na sunkuyar
da kaina ban da hawaye babu abin da ke zuba a idona. "Ni da kudi na
daga na tambaya sai kuma a dinga gana mini azaba?".
Gabana ya yanke ya fadi keyata ta amsa makogwarona ya yi sama
sannan ya yo kasa a daidai lokacin da na daga kaina na kalli kofar na
ga yayana a tsaye idon shi babu sauran alamun imani. Ya kalle ni ya
zuro mini idonsa kamar zai zazzago da shi. Idon kuwa ya kada ya yi
jawur, ya ce da ni "Au dama abin da ka shirya kenan? Ashe kai
karamin dan iska ne?". Ni dai na yi shiru sai kar karwa na ke yi kamar
mai jin sanyi. Ya gyara tsayiwarsa kana ya ce "To zan nuna maka cewa
na fika, wato duk abinda na ke yi kana lura da ni, kuma kana bina a
gindi-a-gindi, ko? to ka sani cewa ba za ka kai labari ba". Ya yi huci
kamar rikakken kumurci. Ya ci gaba "Amma kafin na aiwatar da
komai zan so ka ci gaba da jin kaset din domin bai kare ba". Ya zuro
mini ido na yi sauri na sunkuyar da kaina domin ganin idonsa zai iya sa
mini ciwon kai. "Baka ji?" Tsawarshi ta dawo da ni daga tunanin da na
fada. Na kalle shi na bude baki zan yi magana amma sai naji bakina
gam! Kamar an rufe da makulli. "To tunda kaki jin sauran yanzu zan
aiwatar maka da duk abinda na-ga dama, amma kafin haka, zan dada
tunatar da kai cewa ni na sa aka kashe Alhaji ba don komai ba sai don
ya fi nuna damuwarsa akanka fiye da ni, kuma na bukaci kudi a
wajensa ya hana ni shì ya sa na sa aka kawar da shi. Yanzu ba gashi ina
cikin dukiyar ta shi ba? Dama saboda kai na tura su Hajiya asibiti
kuma na dawo daga wajen aikina domin cika alkawarin da na dauka
jiya da daddare,. na kashe ka na kuma kashe bakar shegiyar da ta ke
taimaka maka, tun da na riga na sa mahaifiyarta ta bakunci lahira,
57
sannankuma na yi jiran lauyar da ta daure maka gindi, shegiyar cikin. kwali, wato na raya ta ta tashi shine zata saka mini da rashin mutunci
ko? To ba za ta yiwu ba. Tunda ka gagari su T.J to ba zaka gagar eni ba
kuma ina tabbatar maka cewa idan na kashe ku na kashe banza, domin
babu abinda zai faru. Don na mallaki abin da duk wani tajiri ke bukatar
mallaka,. Za ka iya kawo maganar hukuma a ranka to wallahi mu ne
hukuma sabo da haka yanzu za ka bakunci lahira".
Da na ji irin maganganun da yake fada sai na yi zaton ya tabu
domin idan ba wanda ya tabu ba babu mai irin wannan magana. Duk
da haka šai na ji maganganun sun kona mini rai saboda haka sai na ji
duk warfi tsoro da ya shige ni ya fita daga zuciyata. Dan haka sai na
mike tsaye daga inda nake a zaune na yi murmushin "RASHIN
MUTUNCI" na ce "Yaya ai kunyar mara kunya asara ce, bansan da
haka ba sai yanzu, tunda ka debo da zafi sai a yi ta ta kare. Ban san
haka ka ke da muguwar aniya ba. Idan ka sa an kashe Baba to ya zo ne
da karar kwanansa domin kai ba ka isa ka kashe shi ba. Haka ni ma
idan ka ga na mutu to kwanana ne ya kare.
Na ji ka ce idan ka kashe ni ka kashe banza, to Wallahi (You are
telling a big lie) Domin yadda ka fitar mini da rai haka za a fitar
maka. ." Kafin na karasa ya tura hannu a cikin aljihunsa ya
zaro wuka mai tsinin baki da bindiga. "Dan iska za ka gane kurenka na
fada mini bakaken maganganu". Ya ce da ni.
Da na ga ya fito da wuka da bindiga sai tsoro ya shige ni fart ta daya, ban san lokacin da na koma na zauna ba. Ina zaune duk tsoro ya
dabaibayeni sai addu'a na ke yi, shi kuwa yayana sai dada gyara bindigarsa yake yi domin ya harbe ni.
Ya daga hannunsa kenan sai na ga an damke hannun ta baya,
murta na shige ni duk da cewar ban san wanda ya rike hannnun nasa
ba, abin mamaki kuma sai na kasa tashį. Sai yanzu ne na gane wanda
ya rike hannun nasa, Uzaifat ce domin na hangi leben zaninta. Ya yi ya yi ya kwace hannunsa, amma ya kasa sai kawai ya kwase ta da kafa,
sai ka ga ta a kasa rigib. Da mamakina sai na ga ta mike ta sake rike
hannunshi kafin ya farga. Ya yi kokarin fidda hannunsa na dama ya naushe ta a fuska, sai ga jini ya fara zuba daga hancinta. Sannan ya hankadeta amma bata fadi ba, da ya ga haka sai ya gyara wukar hannunsa, tana kara tana karą kusanto shı sai ya caka mata wukar a
kafada, ya zare cikin gaggawa ya sakę soka mata a daya kafadar, ya
58
sake zarewa zai soka mata a kahon zuciya ke nan sai na taso na yo kansa da gudu, amma ina kafin na karaso ya yi gaggawar sakar mini harsashi a kafa ta ta dama. Na yi wata irin kara mai razanarwa, nan take na fadi kasa, a daidai lokacin da na daidaita a dandagaryar kasa ne na jiwo ihun Uzaifat cike da razanarwa kana ita ma ta zube a kas.
Mu Hadu a littafi na gaba.
Musamman don:
Taheer A. Rabiu Ali Agege
(Abba)
59
"Wato duk abin da nake yi kana lura da ni, kuma
kana bina a gindi a gindi ko? To ka sani cewa ba za ka
kai labari ba". Ya yi huci tamka rwani rikakken kumurci, ya ci gaba, "Tun da ka gagari su T.J. ai ni ba za
ka gagare ni ba, kuma ina tabbatar maka cewa idan na
kashe ku na kashe banza".
Ina zaune na kasa aiwatar da komai domin tsoro
duk ya bi ya ishe ni, addu'a kurum na ke ta zubawa a
zuciyata, yayin da shi kuma yayana sai kokarin
daidaita bindigarsa ya ke yi domin ya harbe ni.
Numfashina ya dauke a daidai lokacin da na
tsinkayi bakin bindigar yayana na barazanar saitinruwan cikina...
Babu shakka Malama Binta ba karamin kokari ta
yi ba wajen ganin ta fitowa da al'umma dinbin basira
a fannin rubutun zube na harshen Hausa, ta kowane
bangare, ta yi matukar taka rawa a fagen soyayya ta
gaskiya, sa'annan kuma hannunka mai sanda ne ga
dukkan al'umma. A gaishe da Binta Agege.
B.A.U. Reader,
Marubucin Komai Rintsi.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk