na kurba na sake kurba sannan na ce "To bisimillah
sai ki fara ba ni labari" ga mamakina sai na ga ko tanka
mini bata yi ba, don haka sąi na sake maimaitawa, sai ta
ce "Ka yi hakuri domin sai na fara jin naka labarin” ina
jin haka sai nima na share kawai na bar zancen.
Bayan na kwana biyu a asibiti Uzaifat ta yi mini
dawainiyar nemo yayana ranar asabar da misalin karfe
goma saura ya zo tare da matarsa Hajiya Maryam. Bayan
sun yi mini sannu sai muka kama hirar yadda abu ya
kasance, dana kammala fada musu Hajiya har hawaye sai
da ta yi don tausaya mini. Yayana kuma cewa ya yi duk
inda suke sai ya sa an nemo su.
Hajiya ta ce wai su wadannan mutane ba za su rabu
da kai ba ne? yanzu kusan shekara biyu kenan suna binka?
Ko so suke yi su raba ka da duniya ne?" na ce "Haba
Hajiya ai ba su isa su kashe ni ba domin sai kwanana ya
kare zan mutu sai dai kuma idan ranar karshe ta zo mini,
kin san hausawa sun ce "Wuya bata kisa". "Haka dai muka
ci gaba da hirar mu har Uzaifat ta shigo. Bayan sun gaisa
da su Hajiya sai yayana Alhaji Yusuf ya kara yi mata
godiya kan irin taimakawar da takc yi mini, daga nan suka
yi mana sallama suka tafi.
* *
Satina biyu na samu sauki na koma garau kamar ban
taba yin ciwo ba sai Uzaifat ta fara shawarar sallamata
domin duk ciwukan jikina sun warke. Bayan ta dada tabbatarwa na warke sai ta rubuta mini takardar sallama,
na yi farin ciki kwarai da gaske. Na yi mamaki da naga Uzaifat bata bukaci ko mai da sunan kudin magani ko
7
a kudin gado ba. Don haka nima sai na sakc yi mata godiya
ta musamman amma sai ta ce "Not to bother" Bayan na
kammala harhada kayana sai Uzaifat ta ce da ni in tsaya
ita zata kaini gida, don haka sai na nemi guri na zauna.
Ina zaune Uzaifat ta shigo ta ce da ni "Uzaif ka
saurareni zuwa minti ashirin domin an kawo wata haihuwa
kuma haihuwar na son kawo gardama shi ya sa I have to
make it my self" na ce da ita "Ba komai" sannan ta fita.
Bayan fitarta da kamar minti talatin sai ta shigo hannunta
rike da hankici tana share gumin fuskarta. Ta umarce ni da
in tashi mu tafi, har na dauki jakata sai Uzaifat ta karba
nayi-nayi da ita a kan ta bari in dauka amma taki.
Mun shiga motar Uzaifat kirar ACURa Intgra muka
nufi hanyar gida. Muna tafiya muna hira a nan Uzaifat
take fada mini irin kirkin Ilajiya Maryam har nima na ce
da ita "Ai abin da take yi mini ko 'yarta Nafisa bata yi
wa" muna cikin sharar gudu sai Uzaifat ta kalli madubin
mota ta ce da ni "Uzaif kaga motar da ke bayanmu kamar
mu take bi" cikin sauri na kalli madub kana na yi ajiyar
zuciya na kalli Uzaifat na ce "Yanzu idan mu suke bi yaya
zamu yi? ta bani amsa ba tare da ta kalle ni ba "To sai me
idan mu suke bi? Ta fada a sanyayc sai dai fa kai har ka ji
tsoro ko? Amma bari na tababtar naga idan mu suke bi
din" saboda haka sai Uzaifat ta kara giyar mota ta manna
da gudu. Ga mamakina sai na ga wannan motar kirar
HONDA ita ma ta sharo da gudu tana binmu. Daga nan sai
hantar cikina ta kada hade da juyawa. Nan take na fara
tunani "Lallai wadannan su T.J. ne ba wasu ba yau ina zan
sa kaina? Da fitowata daga asibiti kuma zasu nemi komar
da ni?".
Gaskiyar Hausawa da suka ce rikicin duniya da mai
rai ake yi. T.J.!!! yanzu ba zai bar bina ba sai ya ga ya
hallaka ni? Lallai yau ake yinta wai ansa mage a lalle....
Maganar Uzaifat ce ta katseni "Uzaif mu fa suke bi" na ce
"Yanzu ya kenan? Ta ce "Ya ke nan kuwa ai sai mu zuba
hausawa dai sun ce inda ba kasa..." Ni dai na yi kasake
8
ina jin ta domin duk a tsorace nake. Ta sha kwana a daidaj
lokacin da ta bude wani dan guri a jikin murfin kofar
wajenta, ta fauko karamar bindigarta sannan ta kara gudu
ba ji ba gaı kamar wata barauniya "Kada ka damu ka saki
ranka insha Allah zamu tsira da yaddar Ubangji". Kana ta
yi wani fan murmushi.
Ni dai gabana sai faduwa yake yi duk da yake bayau
na taba hoduwa da T.J. ba yau dai naa tsorata da shi
macen bon ba haduwa da ita ba haduwarmu ta farko ita
ce ta kainı ga kwanciya a asibiti to shi yasa nake tsoron
ha fuwarmu ta biyu kada ta kaini ga kwanciya a kabari. Ba
wani abu ke bani tsoro da macen ba illa kawai wannan
arnen takalmin da take sawa mai tsinin tsiya.
Hankalina ya dawo ne a daidai lokacin da na ji harbin
bindiga. Ba kowa ya yi harbin ba illa su T.J. sun yi ne
domin su sace mana tayar mota ganin bamu da niyyar
Isayawa. Nan da nan Uzaifat ta gyara tata bindigar ta leka
ta taga ta sakar musu harsashi amma bata yi sa'a ba domin
kuwa babu harsashi a cikin bindigar. Cikin sauri ta kalle
ni "Uzaif ka iya tukin mota? Cikin tsoro da razana na
kallcta" na-iya- amma a gaskiya yanzu ba zan iya ba don
kuwa sai na fada rami domin na gama tsorata.
Ta kalle ni fuskarta babu alamar fara'a "To dinga juya
mini sitiyarin ni zan yi sauri na zuba harsashi a bindigar
"Na karbi sitiyarin mota na fara juyawa cikin faragaba.
Bayan ta gama zuba wa sai ta karbi sitiyarin ta ci gaba da
juyawa. Kai lallai idan mutum ya ga bala'i sauyawa yake
yi. Na yarda da haka ne ganin yadda fuskar Uzaifat ta
sauya babu ko alamar imani. Aka dada yin harbin ita ma
Uzaifat ta harba tata bindigar, ai fa daga nan aka fara bude
wuta har abın ya fara ba ni tsoro. Da Uzaifat taga basu da
niyyar barin harbi sai ta waiwayoni da sauri "Uzaif koma
kujerar baya ka kwanta".
Cikin firgita na ce da ita "Haba hauka nake yi? zaki
taimake ni sannan na koma bayan mota na kwanta?
"Uzaif" ta ce da ni cike da damuwa. "na'am" ta ci gaba
9
"Na san da haka amma zamanka a nan hatsari ne domin za
su iya harbi ya sameka" na ce "Kece idan suka yi bazai
sameki ba.... Ban karasa ba ta yimini magana cikin ihu
"Uzaif sunkuyar da kanka za su yi harbi.... Ita ma bata
Karasa ba harsashi ya bi ta saman kanta ya fasa mudubin
gaban motar, Allah ya yi bai same ni ba.
Cikin fushi ta ce "ai ga irin ta nan, ka koma baya na
ce" "Wallahi ba zan koma ba sai dai in rasa raina". Na
fada a gaggauce. Da ta ga ihu ba zai yi mata ba sai ta
koma lallashina tana ba ni hakuri. Duk da haka naki
komawa da ta ga ba ni da niyyar komawa sai ta ce da ni
"To tunda kaki sai ka sunkuyar da kanka kasa har sai ka ji
na ce ka dago" nan ma sai da muka fafata da kyar na yarda
na sunkuyar da kaina, duk abin da muke yi motar mu tana
sharar gudu haka suma masu bin mu gudu suke don neman
cim mana.
Duk da sunkuyar da kaina da na yi ina satar kallon
Uzaifat wacce duk ta bi ta dibirbirce. Uzaifat ta karya
kwana sannan ta rage gudun da ta ke yi. suma su T.J. sun
rage gudu na lura da haka ne a sakamakon fakar idon
Uzaifat dana yi na leka tagar motar. Uzaifat ta cire
mayafin dake kanta ta goge gumin dake tsattsa owa daga
fuskarta, Tasa hannu ta danna na'urar sanyaya n ta bayan
haka ta sake mannawa da gudu. Wata sabuw ta dada
aukuwa domin su T.J. suma sai suka kara giyar motarsa
suka yi wo kan motarmu da gudu, irin gudun da su T.J.
suke yi na san suna nufin ayi ta takare ne domin saura kadan su cimmana.
Ashe Uzaifat tarko ta dana musu sai da ta bari duk
sun saki karfin motarsu sun zo kusa da ita sai kawai ta
taka birki suka wucemu da gudu. Kalin ta yi ribas tuni sun
sake yiwo baya sun tarar da mu suna zuwa daf da mu sai Uzaifat ta daga bindigarta ta sakar wa T.J. harsashi amma
sai ya sunkuya don haka sai ta zarce la samu abokiyar
harkarsa a kafada. Ta yi wata irin kara wadda ta firgitar da T.J. har ya so ya saki sitiyarin. Duk na lura da haka ne a
sakamakon daga kaina da na yi ina mai kallon komai ita da kanta Uzaifat ba ta lura ba.
Bayan Uzaifat ta harbi mcen sai ta manna da gudu ta
bar motar su a wajen a tsaye shi kuma T.J. yana jinyar
kafardar 'yar'uwarsa. Tun da muka bar gurin babu wanda
yace kala balle mu kai ga yin hira, sai da muka isa gida.
Bayan mun fita daga cikin mota sai muka shiga cikin gida,
muna shiga gida Hajiya ta taso ta taryemu cike da farin
ciki. Muka nemi wuri muka zauna. Bamu dade da zuwa ba
iga yayana ya fito daga cikin daki, muka gaisa shi ma
mi guri ya zauna.
Bayan kowa ya nutsu sai na fara bawa su Hajiya
labarin gamuwarmu da su T.J. da suka ji labarin nan fa
suka dinga yi wa Uzaifat godiya har yayana ya bata kudi
mai dimbi yawa ya ce tasai gilashin mota, amma taki
karba. Yayi-yayi da ita taki, nima na sa baki amma duk
banza. Hajiya ta yi mata addu'ar Allah ya biya mata da
gidan aljanna ta amsa da amin.
a
Bayan ta yi sallama da su Hajiya sai na yi mata rakiya
zuwa bakin motarta. Ta jingina da murfin mota ta kalle ni
ta ce "UUzaif yaushe zaka samu dama mu zauna mu
saukewa kanmu nauyi? Na daga kaina sama wanda hakan
ya nuna cewa ina tunani "Me zai hana jibi, don gobe ina
son in huta" ta ce "Yauwa, ya kuwa yi daidai da abin da
nake tunani domin nima gobe zamu je mintin (meeting)"
la ci gaba "A ina zamu hadu domin bana bukatar tawowa
nan na yi murmushi karo na farko ke nan tunda muka
baro asibiti "Ina kika ga ya dace mu hadu? amma bana son
guri mai nisa kin san cewa inna cikin hatsari" tayi mini
kallon kai matsoraci ne sannan ta ce "Na san da haka to
mai zai hana ka je gidanmu?
Na nisa kańa na cc da ita "Ai ba hawan ba saukar" ta
ce "Ban gane ba hawan ba saukar" na ce "Ba zuwa gidan
naku ba vadda zan je din" ta yi mini wannan murmushin
nata ma Kosar da mayunwaci “Kai dai matsoraci ne, in be matsorav .... na tari numfashinta "Haba Uzaifat wane
mahaluki ne ba zai yi dari-dari da ransa ba? Na tambayeta
ta ce "I know, but yours is too much" na ce da ita "Thank
you amma duk da haka ni dai ba zan je gidanku ni kadai
ba" "To naji zanzo in dauke ka da kaina, ya yi hakan? Na
ce "wannan babu laifi" muka yi sallama da ita ta shiga
mota ta yi gaba ni kuma na juya na shiga gida.
Ranar da muka yi da Uzaifat ta zo tunda misalin karfe
goma sha daya saura minti goma ta zo. Bayan sun gaisa a
Hajiya sai muka fito muka rankaya cikin mota. Data tashi
mota ba mu tsaya a ko'ina ba sai a DAULA ta ja burki ta
tsaya a kofar wani katafaren gida mai fenti shudi da fari.
Muka bude kofa muka fita ta yi mini jagora har cikin
gidan. Lallai gidan ya kawatu matuka domin harabar
gidan nasu ma abin kallo ne. Gidan akwai shi da yawan
lunguna da lankwashc-lankwashe domin mun lankwasa ya
fi sau hudu. Lankwasawar karshe da muka yi shi ya kai
mu ga bakin bene. Na kalli Uzaifat na ce "Wannan gida
naku na rufin asiri ne" ta ce "Uzaif wanc gida ne bana
rufin asiri ba?"
na ce da ita a daidai lokacin da muka hau benen "Ba hakа
nake nufi ba wato ina nufin cewa ya cika lunguna, kafin
barawo ya shigo ko ya fita tuni an kama shi tunda ba gane
hanya zai yi ba" "Haka ne amma sai dai kawai mu ce
Allah ya kare mu domin hausawa sun ce maso abinka..
na karashe mata "Ya fika dabara" "Ka gani ko? Sai dai
kawai mu ce Allah ya kare mu" na ce "Amin".
Muka shiga wani makeken falo kawatacce mai kyaun
gani, kujeru sun zagaye shi sannan ga wani tebiri round a
tsakiyar falon muna shiga na'urar sanyaya faki ta yi mini
maraba. Uzaifat ta yi mini umarni da na zauna, na nemi
kujera na bi lafiyarta. Sannan itama ta zauna. Bayan mun
nutse cikin kujera sai Uzaifat ta kalle ni ta ce "Uzaif Allah
ya kawo mu dama an ce rana bata karya sai dai uwar diya
12
יי
ta ji kunya saboda haka sai ka bani labari amma before
that ina zuwa bari n'a je na dawo" ta mike ta nufi wata
kofa ta bude ta shiga. Bayan kamar minti bakwai da
tafiyarta sai ta dawo ta ce da ni ""Uzaif Momy dina ta ce
kaje ku gaisa" nan take mamaki da kunya suka rufe ni. Na
mike na bita ina tafiya kamar kazar da kwai ya fashe wa a
ciki. Ta bude kofar data shiga dazu.
Ashe bene ne ba daki ba, koda yake dama gidan hawa
biyu ne saboda haka ban yi wani mamaki ba. Bayan mun
hau bene sai gamu wata 'yar hanya siririya sai muka bita
wannan hanya muka fada wani makeken falo wanda ya yi
wanda muka fara shiga uku. A can gefe mahaifiyar Uzaifat
ce a zaune tana sanye da alkebba baka mai ado a gaba.
Tana kallon wani kaset na America NO WIIERE TO RUN,
na durkusa gwuiwa biyu-biyu na gaishe da ita, ta amsa
cikın murna da lallausar murya.
Da ganin Hajiya mahaifiyar Uzaifat kasan barewa ba
zata yi gudu 'yarta tà yi rarrafe ba, domin kuwa sun yi
matukar kama. Bayan mun dan yi hirar da bata wuce minti
goma sha uku ba sai na yi wa Hajiya mahaifiyar Uzaifat
sallama, daga nan muka koma falon farko.
13
2
a bude baki kenan zan fara baiwa Uzaifat labari, N
sai wata irin kara mai razanarwa da ban tausayi ta
bayyana kunnuwanmu. Gabadayanmu muka mike
da dai naga Uzaifat ta yi hanyar kofar bene sai nima na
bita da sauri muka rankaya izuwa falon mahaifiyarta. Abin
da idon mu ya gani mun so mu karyata shi, wato yankan
rago aka yi wa mahaifiyar Uzaifat, wuyanta sai shatatar da
jini yake yi. Uzaifat ta nufi wajenta a guje ta jata a jiki
tana kuka mai ban tausayi.
Ni kuwa sunkuyar da kaina kasa na yi domin al'ajabin
yadda abin ya faru bamu sani ba. Shin yaya aka shigo aka
yi wannan aika-aikar? Ko dama an a binmu a baya ne? ko
su T.J. ne suka yi wannan aikin ganin cewa Uzaifat na
taimaka mini? Amma babu amsa duk wadannan
tambayoyi. Don haka sai na daga kaina don na tambayi
Uzaifat ko akwai wata hanya banda wacce muka biyo.
Amma sai na raina idona, domin kuwa babu Uzaifat babu
alamarta amma mahaifiyarta na nan a kwance cikin
maliyar jini. Na tashi da sauri ina kiran sunanta Uzaifat!
Uzaifat!! Amma babu amsa. Dana tabbata Uzaifat bata
cikin gidan na fa na fara tunanin shin idan ba a ga Uzaifat
ba wa za'a ce ya yi kisa? Dole idan aka tarar da ni a cikin
gidan a ce ni na yi domin babu Uzaifat babu wanda ya yi
kisa. Lallai idan ban san inda dare ya yi mini ba saina
shiga tarko babba.
Gabana ya yanke ya fadi, hantar cikina ta kada hade
da juyawa miyan bakina ya kasa hadiyuwa a daidai
lokacin dana ji jiniyar motar 'yansanda. Shike nan ta faru
ta kare an yiwa mai dami daya sata. "Shin wa ya sanar da
'yansanda? Babu amsa. "Ko dai tarko aka dana mini ne?
na sake tambayar kaina. Don tsananin tsoro da razana sai
na kasa tabuka komai, in gudu na kasa in tsaya waje daya
na kasa sai safa da marwa nake yi a tsakiyar wannan katon
falo. Na yi hanzari na koma na boye a bayan wata kwana
14
kusa da wani daki, dana ji gudun mutane a kan matattakala.
A inda nake a boye zai yi wuya mutum ya gane ina wajen amma ni duk abin da ake yi ina gani. Wani mutum dogo baki sanye da kananan kaya riga da wando na Jeans ya shigo hannunsa rike da waya mai amfani da iska wato salula. Ya shigo ya tsaya a kan gawar mahaifiyar Uzaifat, ya kalleta ya girgiza kai cikin takaici.
Wadansu mutane su shida suna bayansa sanye da kayan 'yan sanda wanda hakan ya dada rikitar da ni" In
fito ne ko in ari kafar kare? Na tambayi kaina. Sannan na
bada amsa -gwanda na yi tsayiwata domin na shiga ban dauka ba bata fitar da barawo. Bare kisan mutum"
maganar wannan mutun ce ta katse ni. "Ku shiga ku dudduba dakunan ko za'a yi dace a samu imformation
"Suka kame sannan suka amsa "yes sir" kana kowa ya kama diretion dinsa.
Ni dai banda tunanin yadda zan tsira babu abin danake yi. Bayan 'yan mintina ‘yansandan nan suka fito
suka shaida cewa babu wani imformation a cikin gidan.
Wannan mutum dana fahimci Ogansu ne sai ya ce "Kun tabbata kun duba ko ina? Suka amsa bayan sun kame
"Mun tabbata" ya tsaya yana kallon kasa yana bubbuga salular hannunsa a baki wanda hakan ya nuna cewar tunani
yake yi, ya ce "kwa iya tafiya nima ina zuwa within three
minute". Wani irin dadi ya shiga zuciyata ya ketata, don
murna sai da na yi murmushi.
Har 'yansandan nan sun juya za su sauka sai ya ce da
su "au kun duba wancan 6angaren? daya daga cikinsu ya
amsa "No sir" ya ce "To ai sai ku duba don mutabbatar wa
da kanmu babu komai a cikin gidan" hudu suka juyo suka
nufo inda nake. Ai nan da nan murna ta koma ciki na fara
tafiya da baya, sai dana dan yi nisa da tafiya sannan na
juya domin na san inda na nufa 'banyi taku shida ba na ji
an gargade ni "tsaya inda kake in ba haka ba kuma ranka
yana bakin wannan bindiga "cikina yabada wani irin kara
15
kululu !!! sai kawai naja na tsaya domin in ceci raina,
mutumin da ya umarceni da na tsaya dayaga na tsaya sai
ya taho a hankali yarikemini kugu tabaya zatonsa ina da
makami. Ya hura husir sau uku kafin kace me! Tuni
'yansanda sun zagaye ni. Duk da haka dansandan bai
yarda ba sai da ya ce a cajeni tukunna.
Wani guntu fari da fuska kamar alkubus ya caccaje ni
da ya ga bani da komai sai yave da su "He has nothing"
nan na fahimci yarensa. Aka buga mini ankwa a hannu
sannan aka tunkuda keyata zuwa waje inda motarsu take.
Muna sauka da dai sauran 'yansanda suka ga an fito da ni
har da ankwa sai dukkansu suka gyara bindigar hanaunsu,
suka daidaitoni da ita. Mototcin da suka kawo ya iaban
shida, sanan su da kansu sun kai goma sha hudu.
Kai! Allah ka rabamu da sharrin "Ba mu ji ba ba mu
gani ba", Ogan 'yansandan nan ya turani cikin mota,
'yansanda uku suka shigo biyu na hannun haguna daya
kuma yana hannun dama. Mutanc kuwa sun cika sai
kallona suke yi suna nunani. Abin da ya fado mini ina
zaune a kan kujerar cikin mota shi ne shin ina Uzaifat ta
yi? wa ya shaidawa 'yansanda? Yanzu idan ba'a ga Uzaifat
ba na kade har ganyena domin za'a iya cewa ni nayi
wannan aika-aika. Innalillahi wa inna ilaihirraji'un... na
fada a daidai lokacin da na ji yawun bakina ya kafc.
Naga tashin hankali domin irin marin da kwamishina
ya yi mini saida naga taurari bakwai sun wuce. "Kaidan
iska ba zaka fadi inda sauranku suke ba ko? Wato kun
kama mai gidan duk da haka bai yi muku ba sai da kuka
ga kun kashc matarsa ko? Zaka dandana kudarka" wannan
ma gana ta kwamishi na ta girgizani kwarai, kuma ga shi
yaki bari na nayi magana sai dukana yake yi batare da
laifin tsayc ba balle na zaunc.
Da na ga idan ban yi da gaske ba kashe ni za su yi saj
na fara magana da ihu "na fada muku ban san da komai ba
domin wannan shi ne karo na na farko da naje gidan kuma
tare da 'yar mai gidan muke... ban karasa ba kwamishina
ya dakatar dani da hannunsa, "Isa" ya kira wani dansanda.
Ya sara "Yes Sir" "Kwance shi tukunna" Isa ya nufo ni yaа
kunce ni domin daure ni suka yi a kan wani benci sai jigba
ta suke yi kamar Allah ya aikosu.
Kwamishina na zaune a kan kujera ya yi mini umarni
da na zauna a kasa. Bayan na zauna sai ya ce da ni "Ка се
baka san da komai ba?" na amsa "Wallahi ban san da
komai ba" ya kalle ni ya yi murmushi mai cike da alamun
bai yarda da abin da na ce ba. "Kai nan ba gurin rantsuwa
ba ne". ya gargade ni. "Baka san da komai ba me ya kaika
gidan? Kuma aka sameka a dakin da aka yi kisan sannan
ita wacce kace tare kuke me yasa ita bata nan sai kai aka
taras?
Na ja gwauron numashi sannan na ce "Yallabai muna
tare amma sai na nemeta na rasa" Ya kalle ni cike da
mamaki ya ce "ka nemeta ka rasa? Na amsa "Haka ne
yallabai" ya ce "Kana nufin ka ce ta yi layar zana ke nan?
Na amsa "Bang e ba yallabai ni da kaina ma I can't just
understand yo ci gaba "Kana nufin wannan magana taka
mai hankalı zui yarda da ita? Ya za'ai kana tare da mutum
ka ce ka neme su ka rasa? Gwanda ka sake tunani domin
nan da sati za'a gurfanar da kai a gaban kotu tun da an
kamaka da hujja kwakkwara guda biyu, na farko dakin da
aka yi kisa you was there.domin kuwa ba'a ga komai ba,
kuma an kamaka ne a lokacin da kake kokarin guduwa"
Na yarda da duk abin da yace dmin babu karya a ciki
amma duk da haka sai na ce "Yallabai abin da nake son ka
lura a nan shi ne babu yadda za a yi ka dauki ran mahaifin
wanda kai ya ceto naka ran daga halaka. Saboda haka
Uzaifat ita ce shaidata ta fili Ubangiji kuma shi ne na
boye domin bani na yi.... na kasa karasawa don tsananin
17
bakin ciki da takaici na kai hannu na goge hawayc daga
fuskata.
Shi da kansa Kwamishina jikinsa ya yi la'asar, don
haka sai na sake marairacewa inna mai tbbabatar masa da
gaskiyar al'amarina. Kwamishina ya ja numfashi sannan
ya ajiye "Shike nan na ji tun da ka ce tare kuke da Uzaifat
ni zan maka kokari daya insa a yi investigation a nemota
as possible as I can, kafin a gurfanar da kai a kotu"
Maganar Kwamishina ta da dada mini rai matuka, amma
abin lura anan shi ne ina za'a samu Uzaifat?
Kwana biyu a gidan yari sannan yayana Alhaji Yusuf
ya zo shi da matarsa Hajiya Maryam. Da ya zo ne yakc
shaida mini cewa ya yi tafiya ne zuwa Abuja shi yasa bai
san an kama ni ba sai da ya dawo Hajiya ta ce. "ai ni a
ranar da kuka bar gida da Uzaifat Alhaji ya bugo waya zai
je Abuja to sai na ji tsoron fada mas gudun kada ya tsurc.
Jiya sai da muka yi ta bilinbituwar neman police station
din da aka kawo ka amma bamu yi sa'a ba sai da magariba
tukunna aka ce kana nan, to da muka zo sai me tsaron ya
ce ba zamu samu haduwa da kai ba sai dai mu dawo yau"
yayana ya yi kasake yana jin mu bai ce komai ba.
Bayan mun yi 'yar hira sai suka yi mini sallama suka
tafi ni kuma na koma gadirum dina na fada cikin tunani,
ina cikin tunani na ji an bude kofa, na maida kallona
izuwa inda kofar take, kurtun dansanda mai lura da ni ya
shigo hannunsa rike da jar roba. Bayan ya ajiye mini sai
ya fita abinsa, na kalli abin da ya kawo mini naga garin
kwaki ne fal a robar don haka sai na janyo robar gabana na
tsoma hannu na cikin garin na debo, ina kaiwa bakina na
fito da shi don tsananin gishirin da ya kame mini baki.
Na zubar da yau yafi sau biyar don tsananin kame
bakina da gishirin ya yi. Daga nan na fara nadamar rashin
fadawa su Hajiya a dinga kawo mini abinci, koda yake ban
san irin wannan mugun abinci za su dinga bani ba. Domin
jiya ma wake suka kawo mini. Ina cikin wannan hali sai
na ji an bude kofa wannan kurtun dansandan ya karа
18
shigowa ya ce "Ka yi bakuwa" ko tsayawa bai yi ba ya yi
ficewarsa. Na fara tunanin inda na san wata har da zata
kawo mini ziyara a jarum ba'a gida ba. Da naga tunani ba
zai kai mini ba sai na mike tsaye na yi mika sannan na
nufi kofa.
Ta yi mini murmushi a daidai lokacin da muka hada
ido da ita. Nima na yi mata yake don bana ce murmushi
ba. Koda yakt ban yi mamakin ganinta ba tunda nasan ta
tafi kasar waje karo ilimi a kan cause dinta. Tana sanye da
riga da wando na fakistan kanta yafe da wani dan mayafi
shara-shara na fakistan din ta kalle ni "Yaya sannu" na ce
"Yauwa Nafisa" "Yaushe kika dawo? Ta ce "wallahi yau
na dawo" ta sunkuyar da kai "Yaya wallahi ban ji dadin
labarin da na tarar ba domin ya yi matukar razana ni”"