na
kalleta "To yaya za'a yi Nafisa? Kin san abin da Allah ya
kaddara" ta karasa mini "sai ya afku".
Idonta ya cicciko da hawaye "Yaya ya aka yi wannan
abu ya faru?" na ja dogon numfashi sannan na fara bata
labari tun haduwarmu da Uzaifat har zuwa ranar da na zo
hannun 'yansanda. Ta sa ahannu ta share hawayen da ke
kwaranya daga idonta "Babu komai, yanzu abin da nake so
da kai shi ne ka kwantar da hankalinka kada ka damu ko
kadan ni zan vi kokari in nemo ta insha Allahu. Idan
kuma ban ganta ba zan tsaya tsayin daka a kotu in ga na
kwato ka. Ka dal se ronka a inuwa kawai”.
Ban yi manakro fadin hakan nata ba, domin na san
zata iya yin abın da ya fi haka. Ta ci gaba "amma ina son
ka tabbatar mini da gaskiya" na kalleta "Haba Nafisa sai
ki ce baki san halina ba? Ta ce "Na sani amma ai komai na
son gaskiya" na ce Gaskiyata ke nan "To shi ke nan Allah
Ya taimaka mana" na ce amin.
Bayan mun dan yi hira sai mai tsarona ya ce lokaci ya
yi don haka sai muka yi sallama. Har ta fita sai na kwalla
mata kira domin sai yanzu na tuno da maganar abinci. Da
ta zo sai na shaida mata ta fadawa Hajiya a dinga kawo
19
mini abinci domin ban gane wa na nan ba, ta amsa da
"To".
Bayan na koma jarun ina zama maganar yayana ta
fado mini a rai da ya ce an fara yadawa a labarai a kan
kisan da a kayi kuma da sunana a kai amfani. Nan fa na yi
ta shabar kuka ina mai cewa a raina lallai idan ba'a ga
Uzaifat ba karshena rataya domin hukuncin da aka ajiycwa
duk wanda aka kama da laifin kisan kai ke nan. Why? Na
tambayi kaina, hawaye ya gangaro mini na sa hannu na
goge. Yanzu shike nan duniya ta gama daukar sunana.
Uzaifat ta fado mini a rai na ji zuciyata kamar ta fashe don
tsananin kunci da takaici.
Dana ji takaicin ya yi mini yawa sai na fara karanto
wata addu'a da mutum zai iya karantawa idan ya fada
cikin bala'i "Allahumma inna na uzu bika min jahadil
bala'i wa darkish-shi ka'i wa shima tutul a'a da'i" na
shafa da amin. Daga nan na yi addu'a Allah ya sa aga
Uzaifat, domin rashin ganinta musiba ne a garc ni.
Kwamishina tare da wasu 'yan sanda guda biyu suka
shige cikin kurkukun da nake. Yana sanye da kayan
'yansanda a wannan karon, sun shigo sai ga wani saurayi
da ba zai fice shekara ashirin da takwas ba ya shigo yana
sanye da kananan kaya farare kansa ya dora hular FACIN
CAP. Saurayin nan ya nuna ni da danyatsa ya ce "Shi ne
wannan? Kwamishina ya amsa "shi ne"
Murmushi ya bayyana a fuskar Kwamishina. Ya dan
tura hannu a cikin aljihunsa kana'ya ce "Uzaif kamar
yadda na yi maka alkawarin neman Uzaifat to na sa an
binçika amma ba mu yi sa'a ba" ai nan da nan fuskata ta
hade "Ba a ganta ba? Na tambaya cike da damuwa. Ya dan
gyara tsayiwarsa "Yanzu dai sai ka zo mu je ofis domn na
fi yi maka bayani dalla-dalla yadda zaka gane" ni dai na yi
shiru kamar wanda ruwa ya ci, na kasa cewa komai sai da
naga sun juya sun fita kana nima na bisu a baya. Ina mai
tunanin inda Uzaifat ta shiga, idan ba a ga Uzaifat ba
lallai na kade har ganyena.... Ban karasa tunanina ba na ji
an yi mini magana "Nan zaka shigo, ina kuma ka nufa? Na
waiwayo kana na yi ajiyar zuciya na bi bayan su zuwa
cikin ofis din duk jikina a sanyaye.
Muna shiga ofis Kwamishina ya nemi guri ya zauna a
kan kujcrarsa ta alfarma, shi ma wannan saurayin ya nemi
guri ya zauna a kujerar da ke kallon ta Kwamishina. Ya yi
mini nuni da hannu wanda hakan ya nuna cewar na zauna,
na jawo kujera na zauna na kasa kunne domin na ji labarin
rashin ganin Uzaifat. Ya yi gyaran murya kana ya fara
"Kamar yadda na fada maka tun farko mun yi kokari a kan
mu ga mun samo Uzaifat amma abu ya ci tura.
Na sa an yi bincike amma shiru kamar an aika
bawa garinsu, to bayan kwana biyu da binciken Uzaifat
ba'a samu labarinta ba, kwatsam labari ya zo mana cewa
akwai wani gida a dokar wanda a nan ne wadansu 'yan
aika-aika sukan yada zangonsu watau suke baza kolinsu.
To amma bara dai ka ji daga bakin Inspector Kabir". Ya
tsaya kanan ya gyara wata farar takarda dake barazanar
fadowa a dalilin fankar dake kadawa ba kakkautawa
tamkar iskar bazara.
Inspector ya kalle ni kana ya fara nasa labarin "wato
da muka samu labarin cewa suna can dokar daji sai muka
-shirya muka nufi wajen da motoci hudu, kusan mu ashirin
muka je amma mu goma sha daya ne muka dawo dalilin
6arnar da suka yi mana Ya kasance a lokacin da muka je
ba mu samu kowa a gidan ba don haka sai muka je can
wani gefe da ban muka boye motocin gudun kada suga
motocin idan sun dawo su juya. Bayan mun boye su sai
muma muka nemi waje muka buya.
Ba mu fi minti talatin da buya ba sai ga su sun dawo
kusan su goma sha hudu. Suna fitowa daga cikin motarsu
kafin su shiga cikin gida tuni mun far musu, ashe suma
suna da bindigogi nan fa aka dinga wuta, to dai sai da
21
suka kashe mana mutane tara mu kuma mun kashe kawas.
Shida sun zo hannu dauke da munanan raunuka.
Bayan mun gama kame su muna shirin tafiya sai ga
wata karamar SPORT CAR nan ta danno da ganin mu sai ta
juya ta figa da gudu. Muka dinga harbin tayar motar amma
a banza domin ba mu same ta ba". Ya dan dakata yana
kallon Kwamishina, kana ya mai da kallonsa gare ni. "da
muka dawo sai na sa aka ganawa sauran shidan da muka
kamo azaba domin su shaida mana inda sauran suke. Tun
basa son fada har dai wani da ya ga wuyar ta yi yawa sai
ya ce suke nan amma motar ogan su ce ta zo daga baya shi
da wata abokiyarsa da kuma wata budurwa.
Dana tambayi sunan su sai ya ce T.J. da Sussy amma
bai san dayar ba. Na kara tambayarsu ko suna da wani
gurin da ya wuce wannan sai ya ce sudai gurin buyar su ke
nan amma Ogansu yana da wani gurin wanda suda kansu
basu san gurin ba, to kaji yadda abu ya faru".
"Da jin cewa Uzaifat na hannunsu T.J. na san ta faru ta
kare an yi wa mai dami daya sata. Tun da su T.J. suka ga
'yansandan sun far musu to fa kashe Uzaifat za su yi. Idan
suka kashe Uzaifat yaya zan yi da raina? Ban baiwa kaina
amsa ba maganar kwamishina ta ratsani "Insha Allahu
gobe za'a kaika wajen wadannan 'yan fashi domin mu
dada tabbatarwa da kanmu cewa baka cikinsu, kasan fa
aikin mu ne we just have to do it, duk da dai mun san
kana da kanshin gaskiya. 6
Amma ni har yanzu inan kan bakana na sai na samo
maka Uzaifat insha Allahu" Inspector Kabir ya ce "ai da
ganinsa ka san ba zai aikata haka ba domin Hausawa sun
ce alamar karfi tana ga mai kiba" ni dai na yi shiru ina
sauraronsu domin jikina ya yi, sanyi. Na ja wani gwauron
numfashi tare da ajiyar zuciya na kalli kwamishina muka
hada ido, na dauke kallona daga gare shi izuwa ga
Inspector Kabir, wani irin hawaye ya gangaro min na
sunkuyar da kaina kasa "Allah ya sa a dace". Na fada a
cikin sassanyar murya, suka amsa da "amin".
22
Gari na wayewa Inspector Kabir ya sa aka fito da daga cikin kurkuku. Bayan mun fito waje sai Kabit
tsaya tare da kwamishina suna magana wacce bana ce
abin da suke cewa ba. Kamar minti biyar da tsayiwarsu s
Inpector ya sarawa Kwamishina kana ya juyo ya nufo ni. Yana zuwa muka shiga mota ba mu tsaya ko ina ba sai
ofishin 'yansandan da aka kai wadannan 'yan fashi. Dukkanmu muka sauka daga cikin mota muka bi Inspector
Kabir a baya har zuwa cikin ofishin 'yansandan. Muna
shiga 'yansanda dake wajen duk kansu suka mike tsaye
suka kame kana suka sarawa Inspector. "Mu'azu mike ka
bude min kofar wajen 'yan iskan nan".
Mu'azu ya mike ba tare da bata lokaci ba ya ciro
mukullin a jikin bango ya yi gaba mu kuma muka bishi a
baya. Muna zuwa ya bude kofar ya ce da su “duk ku fito"
jikinsu babu riga duk bayansu ya yi rudu-rudu don duka,
fuksarsu kuwa ba'a magana don tsananin kumbura da ta
yi. inspector ya kalle su daya bayan daya ya yi tsaki
sannan ya ce "Ku kalli wannan mutum da kyau ko kun san
shi? Kallon da dukkansu suka yi mini ke da wuya sai abin
ya bani mamaki da tausayi, ganin cewa hudu daga cikinsu
abokaina ne a lokacin da muke makaranta domin a wannan
lokaci babu abin da ke raba mu har bacci. Duk suka
sunkuyar da kai don kunya. "Ba mu san shi ba". Za ku ce
ba abokin harkarku ba ne" ya ce yana harararsu.
Daya daga cikinsu ya yi tsaki ya ce "Yallaba ba mu
san shi ba muka ce" inspector ya murtuke fuska ya kalle
shi. "Kai ka iya harshenka idan kuma ba haka ba yanzu
nasa a kaddamar maka, ni ka ke yiwa magana haka? Gayen
ya ce "Haba yallabai ai ban isa in fada maka magana ba”. Ni kuwa dadi ya kashe ni ba su nuna sun sanni ba. Nan na
fara tunanin ko na yiwa abokan nan nawa magana? Sai na
yi tunanin gwanda na kyale su kada na jawo wata sabuwa
a wajen Inspector, su da kansu kunyar ta hana su magana.
23
Daga nan Inspector ya yi umarni da a mayar da su har
sai ya bukace su. Mu kuma muka ſito muka shiga mota
bamu tsaya a ko ina ba sai a ofishin 'yansandan da nakc
tsare. Muna isa inspector ya ce mu zarce ofishin
Kwamishina, da muka shiga sai kowa ya nemi wajc ya
zauna. Daga nan Inspector ya kwashe duk abin da ya ya
faru ya fadawa kwamshina ya yi farin ciki da jin hakan.
Kwamishina ya kalli Inspector ya сс "Kа ga kc nan
wannan ya tabbatar mana da cewa shi ba dan fashi ba nc
kamar yadda muka yi kokwanto, yanzu saura fuskantar
alkali domin ya zama dole tunda za'a yi mana yan
tambayoyi tunda shi aka samu a dakin da aka samu gawar
Hauwa A. Lauya Saleh" Inspector ya ce "Ba shakka".
Bayan na tashi zan koma dakin tsarona sai inspector ya
shaida mini cewa gobe za'a kai ni kotu. Na ce Allah Ya
kaimu goben lafiya.
Na zauna na hada kai da gwiwa ina tunanin yayana da
kuma dalilin da ya hana shi zuwa yau kusan sati daya da
kwana biyu, tun da ya zo sau daya. Shin abin da ya yi
kuwa ya kyauta? Kai ina ganin akwai abin da ya faru a
gare shi, ga shi kuma gobe za'a kaini kotu a kan laifin da
ban aikata ba..... ban karasa ba na ji an bude kofa. Kurtun
dansandan nan tsamurarre ya shigo "Ka yi bakuwa" ya
juya ya fita, wannan karon ban yi mamakin jin cewa na yi
bakuwa ba. Don haka sai na mike na nufi kofa. Ina fita na
yi tozali da ita, tana sanye da jallabiya shudiya da
mayafinta. "Nafisa lafiya?" na tambayeta domin naga
alamar damuwa a fuskarta.
"Lafiya kalau" ta ci gaba "Na yi kokari a wajen
neman Uzaifat amma na rasata sai kuma na ji cewa gobe
za'a gurfanar da kai a kotu shi ne nazo domin na shida
maka cewa ka kwantar da hankalinka ni zan tsaya a kotu
domin ba zan yarda a aza maka laifin da bana ka ba". Та
goge hawayen da ke idanunta. Da na ga hankalinta ya
tashi sai na sauya darasi "Su Hajiya kuwa suna nan? Ta
24
amsa "suna nan jiya ma yaya ya shaida mata sakonka m
gaisuwa ina jinsu a lokacin inna nazarin wani littafi.
Abin da na ji daga bakin Nafisa ya bani mamaki don
har kasa magana na yi. dana ji ta ce yayana ya zo har na
ba shi sakon gaisuwa. Ta ce da ni "yaya zan koma sai
goben domin ina son in je in yi nazari". Na cc ai babu
damuwa "Ki gaishe da su Hajiya". Ta ce "saji" ta tafi ni
kuma na koma cikin kurkuku. Tunanin duniya duk ya bi
ya ishc ni. Na tuno da son da mahaifana suke-yi mini har
da yayana da kuma irin mutuwar da su kayi cspecailly irin
kisan da aka yi wa mahaifina hawayc ya gangaro mini.
Ban san lokacin da na fashe da kuka ba don bakin ciki na
yi kwafa kana na hada-kai da gwiwa kai!! Lallai dunya
rawar yan mata сс.
25
un isa kotu karfe tara da kwata. 'yansanda kusan M
dozin suka take mana baya ni da Inspector Kabir.
Suka tura keyata gaba har cikin kotu kamar wani
gagarumin danfashi, muna shiga aka bani kujera na zauna
idon mutane kuwa duk ya yi kaina. Sabonda kunya da
fargaba kasa daga kaina na yi, kotun babba ce kuma cike
take da mutane ba iyaka. Daga tsakiya wani katon teburi
ne zagaye da kujeru, a kan kujerun kuma lauyoyi ne su
hudu. maganar wadansu mutane ce ta dakatar da ni daga
tunanin da nake yi. Daya daga cikinsu ya ce "Kai Hadi
wannan saurayin daga ganinsa kamili ne kuma gashi shiru
shiru ba shi da alamar mugunta" dayan kuma sai ya ce
"Kai Ya'u rabu da shiru-shirum mutum ka ji? nan ba
gamuwa muka yi da wani kamilin mutum ba? Da muka
yarda da shi ba kwace mana fan talatin ya yi ya gudu ba?
Yanzu ai shiru-shirun mutum ya fi mugunta kai dai rabu
da halin dan'adam" haka dai suka ci gaba da hirarsu.
Fitowar Alkali ne yasa kotun ta yi shiru kamar ruwa
ya ci ta. Kowa ya mike bayan Alkali ya zauna sai kowa ya
nemi guri ya zauna. Wani gwarzon mutum fari dogo mai
bille a kumatu lauya ya mike ya karanto shari'a bayan ya
gama ya koma ya zauna. Alkali ya yi umarni da na shiga
ckin kanta, na shiga ciki na daga kaina duk idanun mutane
yana kaina, na yi sauri na sunkuyar da kaina ta faru ta
kare na fada a raina. Alkali ya ce da ni "Uzaif ka ji laifin
da ake tihumarka da shi na kisan matar Lauya Saleh ko
kana da ta cewa? Zan, yi magana sai wani luya baki dogo
ya mike ya yi gaisuwa kana ya gabatar da kanshi a
matsayin lauyan da dangin mahaifiyar Uzaifat suka dauka
shari'a, kana ya matso ni ya ce "Kana da ta cewa?"
"Ranka ya dade bani na yi kisa ba". Na fada ina
kallon Alkalin
Ya ce "Zaka iya nuna shaida ko kuma hujjar hakan?"
yana magana ransa a bace.
26
"Ina da shaida amma kuma bata kusa" na ce da shi,
"Ko kotu zata iya sanin shaidar taka?"
"Why not? Uzaifat Salch shaida ta amma an rasa inda take".
"Ban da ita wace alama zaka nuna da zata gamsar da
kotu ba kai ka yi kisa ba? Na kara kallon sa cike da
mamakin nacewar da na ga ya yi". "Ni bani da wata alama
da zata nuna bani na yi kisa ba illa Uzaifat".
Ya yi ajiyar zuciya da ya ji ina amsa tambayoyina daidai.
"A lokacin da 'yansanda suka je har suka kamaka ka
yi niyyar gudu ne ko kuwa?" "Gakiya bana ce ban yi
niyyar gudu ba". Nıshare gumi daga fuskata.
"Mene ne dalilin yin hakan alhali ka tabbatarwa kanka
cewa baka yi laifi ba?
"Saboda tsoron kada hukuma ta kamani" na dan
yamutse fuska.
"Ba kai ka yi kisan ba yaya zaka ji tsoron kada a
kama ka?"
'Kai wannan da tambayar tsiya yake'na ce a zuciyata.
"Ka san Hausawa sun ce na shiga ban dauka ba bata
fitar da barawo shi ya sani na ji tsoron kada a kamani a
kan gawar especially ma da banga Uzaifat ba".
"Tun da baka da bayyananniyar amsa kotu zata yanke
maka hukuncin da ya yi daidai da kai". Kaina ya sara kwakwalwata ta yi wani irin kara kamar an karkada
kararrawa. Zan yi masa magana ke nan sai Nafisa ta mike
cikin isa da takama da ji da kai. Hankalina ya dan kwanta ganin zan samu mafita ko da dai ba da yawa ba. Та
_ gabatar da kanta a matsayin mai kare ni kana ta nufo ni ikin nutsuwa. Bayan ta zo inda nake sai ta dafa jikin _antar dana ke ciki ta kalle ni kana ta maida hankalinta ga Alkali. "Allah ya gafarta malam ina ganin bai dace a ce an nkewa wannan bawan Allah hukunci a kan laifin da bai ba, domin ya kamata ayi bincike dalla-dalla kafin a
_vatar da komai gare shi in har shi ya yi laifin".
27
Nan da nan naga hankalin sauran lauyoyin ya yiwo
kanta. Ta kalle su ta kauda kai "Dalilin fadin haka shi ne
su masu tambayar shi ko kuma ince ma su dora masa
laifin ina son su nunawa kotu hujjar da ta nuna ccwar shi
ya yi kisa". Wannan lauyan fari ya mikc da sauri ya ccс
"Kotu zata iya yarda da shi ya yi kisan musamman idan
aka yi la'akari da cewar shi aka samu a dakin da abin ya
faru". "Wannan ba shaida ba ce' ta fada tana mai kallon
Alkali. Ta ci gaba "Tun da ba'a samu makami a hannunsa
ko kuma a inda aka yi kisan ba to kuwa ba za a ce shi ya
yi kisa ba". Nan da nan wannan lauyan mara imani ya
mike tsaye yana fadin "Karya ne shi ya yi kisan mc yasa
zai gudu idan ba shi ya yi kisan ba?Ya daka mata tsawa.
Nafisa bata ce masa komai ba amma ta yi masa kallon
Baka isa a yi da kai ba wanda ya sa shi ya girgiza matuka.
Ta sake maida kallon ta ga Alkali "Allah ya gafarta malam
zan so a yi binciken wannan magana tawa da kyau domin
bai dace a muzanta mara laifi ba, saboda haka zan so kotu
ta bamu dama mu yi binciken wannan yarinya tunda ya
nuna cewa ita kadai ce shaidar sa, idan kuma kotu ta yarda
da ni a matsayin lauyar da zata iya belin Uzaif" Lauyoyin
nan suka mike cikin hanzari suna muzurai dayan fari ya ce
da Nafisa yana harararta "Bamu yarda ba, ba za a baku
wannan damar ba".
Nafisa ta yi murmushi ta ce "Sai ihu kuke bayan hari
ku kawo shaidar ku mana wacce ta nuna shi ya yi kisan".
Suka koma suka zauna suna haki kamar wadanda suka yi
tsere da zomo. Alkali ya yi gyaran murya kana ya ce "Kotu ta baku wata dayar cur ba kari ku nemo shaidarku,
an baki belin,Uzaif akan dalili daya kada ki sake ya gudu idan hakan ta faru to kinsan abin da zai biyo baya domin
yana cikin littafin doke". Nafisa ta ce "godiya muke ranka
ya dade". Ta koma wajenta ta zauna. Murna zan yi ko
kuka? Zan so mai karatu ya ba ni wannan amsa domin na
rasa abin da zan yi cikin biyun.
28
Bayan Alkali ya mike ya shiga wni daki sa mutane
suka dinga sowa suna yin mini fatan Allah ya sa inga
Uzaifat ka min wannan lokaci wadannan lauyoyi kuwa
banda kallon banza babu abin da suke yi mini. Muka fito
bakin titi neman tasi, ko dadewa ba mu yi ba muka samu.
Bayan mun fara tafiya sai na tambayi Nafisa dalilin
da ya hanata taho da motar gida. Ta shaida mini cewa
yayana ne ya fita tun da safe shi ya sa, kuma makullayen
duka suna hannunsa. Nan fa na tuno da yayana kome ya
hana shi zuwa kotu? Shin yayana yana kaunata kuwa? In
har yana kaunata mai zai hana shi zuwa kotu ya ji yadda
zamu karke? Tsayiwar mai tasi ce ta dawo da ni daga
tafiya dana yi fagen tunani. Bayan mun sauka sai Nafisa ta
sallami dan tasi ya yi gaba mu kuma muka shiga gida.
Hajiya na ganina ta taso da sauri ta rike mini hannu
tana kuka. Ta goge hawayc da leben zaninta "Uzaif lafiya
ko?" ta tambaye ni tana hawayc. "Hajiya ai Alhamdu
lillahi domin babu abin da ya samu lafiyata". Ta yi ajiyar
zuciya "To ai shike nan amma sai Allah Ya saka maka
domin duk wanda ya shirya maka wannan tuggun
muguntar shi ma yana tare da wahala babba". Na ce
"Hajiya ai babu komai Allah ya fisu kuma yana bayan mai
gaskiya, ki daina kuka". "Ba dole na yi kuka ba Uzaif?" ai
kuka ya zamar mini dole".
Muka zauna muka ci gaba da hira. Ashe duk abin da
Hajiya ke yi bata lura da Nafisa ba sai da taje ta dauko
mini abinci tukunna bayan ta dawo sai Hajiya ta lura da
kayan dake jikinta.
Duk gidan babu wanda ya san aikin da Nafisa zata yi
sai ni. Hatta yayana ma bai san aikin da zata yi ba sai dai
karbi kudi wannan ta karbi kudin wancan amma ba zaı
taba tambayarta aikin da take karanta ba. Nima da kyar ta
barni na san cause dinta". "Nafisa" Hajiya ta kira sunanta;
S
ta rike baki cike da mamaki sannan ta ce "Wannan kayan
kuma fa? Nafisa ta yi dariya ta ce "don Allah ji yadda
Hajiya ta rike baki, ai kayan aiki na ne". Hajiya ta ci gaba
"Shi ne baki sanar da mu ba? Kwanakin baya da na
tambayeki aikin da zaki yi ashe karya kika yi mini na
cewa aikin banki zaki yi?" Hajiya na fadi haka ne don
kada ku katse mini hanzari ke da yaya shi ya sa na yi
muku karya". Yanzu ki rasa aikin da zaki yi sai aikin
lauya? Aikin marasa gaskiya ne fa aikin lauya, aikin da
karbar cin hanci da rashawa ya yi wa kanta? Lallai baki yi
tunanin arziki ba wallahi, gwanda da baki fada ba".
Nafisa ta cire hular da ke kanta ta gyara zama ke nan t
*afara bawa Hajiya labarin aikin lauya "Hajiya ki kwantar
da hankalinki domin ni ba zan kasance mai cin amanar
talakawa ba, ina wannan aiki ne domin na karbar musu
hakkinsu a dalilin gani da na yi an danne musu. A inda
zaki gane aikin lauya sai ansa kai ake karbar cin hanci da
rashawa shi ne yanzu idan wani ya kawo mini cin hanci ba
sai na ga dama zan karba ba? Idan ban karba ba zai tilasta
šini ne? Kinga ai ba zai tilasta mini ba. Kinga aikin lauya
yana da amfani musamman yanzu idan wani abu ya faru a
dangi ai ba sai an yi wahala ko kuma asarar kudin nemo
lauya ba.
Ba gashi yanzu na yi kokari na yiwo belin yaya ba?
Kina nufin idan wani ya je za'a ba shi? Ai sai lauya dan'uwanmu ko kuma babban dan sanda” haka dai ta ci
gaba da baiwa Hajiya haske har itama t gamsu kuma t ayi
mata addu'a tare da bata goyon baya. Ni dai ina jinsu sai harraka abinci nake yi a cikina.
Da yamma bayan na yi wanka nasa rigata 'Kano State' da wando sầi na nufi falo na tarar da Nafisa tana kallon wani kaset na yaran Amurka LUCKY SEVEN'don haka sai nima na zauna muka ci gaba da kallon. Muna kallon muna hira
kama
yayana ya dawo daga wajen aiki. Yana gani na ya kame-kame yara fada mini dalilin da ya hana shi zuwa wajena. Da ya gama tsarinsa sai na ce da shi ai babu
komai daga nan ya shiga daki mu kuma muka ci gaba da
kallo. Na lura da ran Nafisa ya 6aci amma sai na yi kamar
ban lura ba, a haka har muka gama kallo kowa ya yi nashi
waje.
Tun daga ranar da na dawo gida naga yayana ya canja
ba kamar da ba, babu wálwala a fuskar shi sannan 'yar
hirar da muke yi ma yanzu an daina. Saboda haka sai na
yanke shawara in je in tambayi Hajiya ko tana da
masaniya. Dana isa dakinta sai na tarar da ita tana sakar
rigar sanyin yara da inji.
Na zauna a kan kujera dake dakin na tambaye ta
amma sai ta ce "Yadda k tsinkayi Alhaji haka nima na.
tsinkaye shi" na ce da ita "To Allah ya yi mana magani".
Тa се “Amin" daga nan na fita daga dakin na nufi falo. Ina
zuwa na tarar da Nafisa zaune ta yi tagumi, tana ganina ta
dago kai da sauri kana ta tambaye ni ko na san abin da ke
damun yayana. nIma sai na yi ta bakin Hajiya "Yadda kika
gan shi haka nima na gan shi". Nan muka fara sakawa
muna kwancewa ko zamu gane abin da ke damun sa amm
mun rasa.
Daga nan Nafisa ta fara bani labarin dawainiyar da
take yi mini wajen neman Uzaifat amma abin ya ci tur.
"Allah ka taimake mu" na ce da ita ta amsa da "amin".
Yanzu na tabbatar Nafisa na son taimakata, domin irin
dawainiya da wahalhalun da take yi wajen neman Uzaifat
amma shiru kake ji kamar an jefa kwai a ruwa. Wani sa'in
idan Nafisa ta fita tun safe sai yamma ko magariba zatı
dawo. Na kan yi mata fada a kan ta dinga samun hutu
amma ta yi kunnen uwar shegu da ni yau gashi saura
kwaga goma sha daya mu koma kotu amma babu duriyar
Uzaifat. Na tambayi kaina wai idan ba a ga Uzaifat ba
wane irin hukunci za'a yanke mini? Kisa...! Na ji tamkar
wani ya bni amsa.
Na yi nisa a cikin tunanin da nake yi şai karar tarho ta
katseni, na yi firgigit na mike, na duba inda Nafisa take na
ga bata gurin a nan na fahimci cewa ta fita ne. ina zuwi
nasa hannu na dau wayar "Hello who's talk?'Na tambaya,
amma memakon a bani amsa sai nima aka yi mini tambaya
"Who are you?"Maganar shi t abani