tsoro domin kamar
zata fasa kan wayar ta huda mini dodon kunne.
Da naga zai bata mini lokaci sai na cc "Wa kake
nema?" "Alhaji na nan?" Ya tambayeni da wata katuwar
murya kamar kukan shanu. "Baya nan wa ke nemansa idan
ya dawo a fada masa?"Ya amsa ta daya bangare "Wake
magana ne?". Da na so na fadi sunana amma kuma sai na
fasa tunda shima bai fadi sunan sa ba. "Ya'u ne yake
magana". Sai na ji ya yi wata katuwar tsaki ya ce "Kai ba
kai ake nema ba Alhaji ake bukata". Sai na ce "Ka fadi
sunanka tunda baya nan idan ya zo sai na shaida masa....?
ban karasa ba na ji ya dakatar da ni "Kai idan ya dawo ka
ce an bugo masa waya amma ya bugo”. Kawai sai na ji ya
ajiye kan wayar gwaram!!!
Nima na ajiye kan waya na koma na zauna ina tunanin
wannan abu mai ban al'ajabi na kin fadin suna da kuma
sakon da ya bari mara m'ana. Sai yanzu nake tunanin inda
na taba jin wannan murya can bayan na yi zurfi cikin
tunani kwatsam sai T.J. ya fado mini a rai, babu shakka
wannan muryar T.J. ce. In dai har wannan T.J. ne meye
gamin yayana da shi? Zan iya tuno da abin da ya ce mini a
lokacin dana daki sussy abokiyarsa "Zaka san ka nausheta
nan gaba ba zaka kara wannan karanbanin ba”"
Wannan murya hakika ta yi kama da wadda aka bugo
waya yanzun nan. Haba har na tsaya batawa kaina lokaci?
Ai wannan muryar ta T.J. ce shin me ye gamin yaya da
wannan mugun? Zuciyata ta ce da ni "Kada ka dauki hakin
yayanka wannan murya bata T.J. ba ce, me ma zai hada
wannan rikakken dan fashi da yayanka? Na yarda da
maganar karshe amma ban yarda da ta farko ba domin babu makawa wannan murya ta T.J. ce tunda ba wannan
karen na taba jin muryarsa ba. Ko ya yi batan lamba ne?
Da na sani na tambayi sunan Alhajin da yake nema. Ina
cikin wannan tunani na ji an bude kofa ina waiwayawa
32
2
uka hada ido da Hajiya ina ganinta na tashi na shiga
akina.
Can da yamma ina zaune a dakina, aka kwankwasa
ofa na amsa da a shigo. Nafisa ta shigo ta nemi waje ta
auna tana nishi, na kalle ta na ce "Lafiya na ganki haka?"
a kalle ni ta ce "Wallahi daga gidan su Hadiza Adam
ake tun dazun da na fita can na nufa sai yanzu na dawo,
nota ce ta yi mini tsiya a kan hanya ta lalace da kyar na
amu wani mutumin arziki ya kawo ni gida". Na ceе "То
cuma motar a ina aka barta?"Na tambaya Ta ce "Ina za'a
arta da ya wuce gurin gyara?"Na kara da "Lallai wannan
nutumi ya kyauta kwarai". "Kar ka so kaga yadda na ji
dadi kamar na hadiye shi kuma ga shi da fara'a". Nafisa ta
gyara zama kana ta ce "Yaya wallahi daga gidan su kawata
Hadiza Adam nake dazu mahaifiyarta ta sa aka yi kirana.
Wato ni na rasa abin da ke damun mu musamman mu
mata akan kishi. Ko mene ne amfaninsa idon't know why.
Sai ka ga mace da zarar mijinta ya yi mata amarya to an
daina zama lafiya daga fada sai muguwar aniya. Alhali
kuwa Ubangiji ya umarta a yi aurarraki idan har ana da
ikon yin. To shi ne don an yi miki daya kacal shi ne wani
tsiya?"Ni dai na yi shiru ina saurararta daga nan ta bani
labarin yadda kishiyar kanwar mahaifiyar kawarta ta hada
mata gobara a jiki duk ta bi ta salibe tana asibiti rai a
hannun Allah, to shi ne aka dauketa shari'a domin
mahaifiyar Hadiza Adam ta ce bata yarda ba sai an kai
magana kotu. Na yi ajiyar zuciya na ce "To yanzu ya za'a
yi?ta ce "Sai jiba za'a gurfanar da ita kishiyar a kotu.
Yanzu ma tana hannun hukuma” na ce "Yauwa ai haka ma
ya fi domin wannan ba kishi ba ne ya zama hauka".
Bayan na ji dawowar yayana sai na shiga bandaki na
yi wanka da na fito sai na dauki jalabiya ta mai ruwan
hoda na sa na taje kaina sannan na nufi falo domin na idar
da sakon da aka bari. Ina isa falo na tarar da yayána da
Hajiya suna zaune suna hira, na zauna a kan darduma na
33
yiwa yayana sannu da zuwa, zan bude baki na fara magana
ke nan sai Nafisa ta shigo falo itama ta nemi guri ta zauna.
Bayan ta zauna sai na ce da yayana "Da safe wani ya
bugo waya amma ya ce in fada maka cewa ya bugo bai
sameka ba amma ka buga. Kafin hakan sai dana tambayi
sunansa amma yaki fada". yayana ya fara muzurai yana
cewa "Waye shi? Ban san shi ba kuma ban fahimci abin da
kake nufi ba". Nan dai na kuma yi mishi bayani amma ya
nuna bai san wanda ya bugo wayar ba.
Na kyale shi na mike zan koma daki. Mike wata ke da
wuya Nafisa ta ce da ni "Yaya saura kwana hudu mu koma
kotu" na ce "Ina sane". Na yi shige wata daki. Bada
dadewa ba sai ga Nafisa nan ta shigo nan fa muka kama
hirar duniya har magariba daga nan muka mike muka yi
sallah sannan muka nufi dinnin table domin mu bawa ciki
hakkinsa. Da muka gama cin abinci sai muka dada kafa
wata majalisar hirar har da Hajiya a wannan lokacin. Da
isha'i ta yi sai kowa ya mike domin ya je ya gaida mai
duka.
Bayan na gama salla sai na tuno da wani littafin hausa
da wata budurwata da muka yi makaranta daya ta bani
domin na karanta amma ban samu damar karanta wa a
wannan lokacin ba. Saboda haka sai na mike na shiga
bincike a cikin littattafaina, sai da na yi nema har na gaji
sannan na samo littafin. Ba tare da 6ata lokaci ba na fara
karanta Rikicin Duniya.
Bayan na gama karanta littafi na daya sai na dauko na biyu na fara karantawa. Har misalin karfe goma sha daya ina karatu tun da na yi sallar isha'i. Da na gama karatuna
misalin karfe goma sha daya da minti goma sai na ji ina bukatar shayi don haka sai na mike na nufi kicin domin na jona ruwa a heater. Dana jona sai na koma falo domin na
zauna kafin ya tafasa.
34
a
a
a
Gidan ya yi shiru wanda hakan ya nuna cewar kowa
ya yi nisa da barci. Zamana ke da wuya sai na ga kofar da
za'a bi a shigo falo daga kofar gida ba'a kulle ta ba. Abia
ya bani mamaki domín na san ba'a taba barin ta a bude ba.
Ganin hakan ya sa na mike domin in je in kulle "Y anzu da
Allah bai fito da ni ba sai dai kofar ta kwana a bude. Har
na janyo kofa zan rufe sai na ji magana sama-sama. Don
haka na leka don in gani ko Baba musa mai gadi ne ya
samu abokin hira. Lekawata ke da wuya na maido da kaina
da sauri, gabana ya yanke ya fadi, numfashina ya dauke
jiri ya dauke ni na yi tangal-tangal zan fadi, na yi karfin
hali na rike karfen dake jikin kofa. Na yi kokarin kawo
nunfashi amma abu ya faskara, sai da na yi kamar minti
hudu
da
a cikin wannan hali sannan na dawo cikin hayyacina
Ba wani abu ne ya sa na girgiza ba illa su T.J.
Sussy dana gani suna tsaye shi kuwa yayana yana zaune
kan motar sa kirar DEAWOO. Gashi hira suke yi har
dariya, wannan abu ya girgiza ni ainun. Na gyan
tsayiwata na kara makalewa domin in ji abin da hirar su
kunsa. Abin da na ji daga bakin yayana da wani ne ya fad
mini ya ce ya ji daga bakinsa to da sai mun yi rigi
kuma na kai kararsa, amma sai gashi na ji da kunned
Ashe haka dan Adam yake? Wai ace kamar yayana wam
yake salihi kuma n yarda da shi yake yi min hab
Gaskiyar Hausawa da suka ce 'mutum'mugun ice ne
yanzu na yarda da wannan karin magana ta masui
magana.
Wata magana da na ji daga bakin yayana ita ta firg
ni ta razana ni ta rikitar mini da kwakwalwa, sai yanzus
dada jin sunan wannan 'yarta'addar sosai "SUSSY", lall
ta dace da sunanta in ma bata dace da wannan suna ba
babu ko shakka shegen takalmin na náta ya dace
wannan sunan.
Sai da na gama jin hirar su kaf sa'annan na juya
nufin in koma cikin gida, ina daga kafa ta sai na ji na ta
wani abu mai laushi kuma murdadde, don haka sai na k
8
8
8
idona kasa domin in ga abin dana taka, ina duban kasa ban
san sa'ilin da na kwalla wani wawan ihu ba, na nufi cikin
gida da gudu na shiga daki na kashe fitila na nufi gado na
kwanta. Wani irin katon maciji na gani bakikkirin da shi
ko ya mutu ko kuwa da ransa? Allah kadai ya barwa kansa
sani. Duk da rufa da bargo da na yi ina iya ganin haske ya
gauraye dakin, ko raba daya biyu ban yi ba na san yaya na
ne ya shigo, ba tre da bata lokaci ba sai na soma
minsharin karya, bayan ya gama 'yan dube-dubensa
sa'annaan ya kashe fitila ya ja kofa ya fita.
Fitar ke da wuya na yaye bargon da na rufa kana na
taşhi zaune, dukkan wadannan abubuwan sun afku ne a
cikin dan lokacin lokacin da bai fi minti talatin ba, sai
yanu ne na tuna da ruwanzafin da na jona a heaater, cikin
gaggawa na mike na nufi kicin, na iske ruwan da na jona
har ya kone yayin da 'heater ke ta faman kauri, cikin
haanari na kashe domin gudun jawo gobara. Na koma daki
na kwanta,amma kuma kash! Yadda na ga rana haka na ga dare.
Gari na wayewa bayan kowa ya kammala karin
kumallo, a falo na iske yayana yana shirin fita aiki sai na
ce ya bani kudi zan yi wani abu da su. Ya tambayeni ko nawa
nake bukata na ce da shi dubu biyu,ya kirga kudi ya bani
dana amsa, sai na kirga, amma sai na ga naira dubu daya ta
hau kai sai na mayar masa da abinsa ya ce na barshi na yi
wata hidimar da shi amma sai na ki karba na ce wannan ma
ya yi min ba sai ya kara min ba. Ya amsa ya bawa Nafisa
kaman ya wuce wajen aiki.
a
Bayan Alhaji ya fita sai na ce da Nafisa ta zo ta kaini
wani waje, ba tare da ta amsa ba ta karbi makulin mota
gurin Hajiya, ba mu zame ko ina ba sai a wani shagon saida kayan alatu kamar su rediyo da bidiyo.
Ina shiga wajen Chukudi da yake mutumina ne na saba siyan kaya a wajensa. Ina shiga na duba wata 'yar karamar rikoda na siya, kana a na kara siyan wata CAMERA hade da fim. Na kirga kudi naira dubu daya da dari tara da hamsin na
36
cuk
J72
an
ak
a
ay
k
T
ba shi kanana na ce da shi ya barka yan awajensa gobe ya
kawo min gida da magariba kuma kada ya bari kowa ya gani,
muka yi sallama na nufi inda motarmu take, bayan mun isa
gida sai Nafisa ta tambayeni abin da na yi a gurin Chukudi
sai na shaida mata cewa na biya shi bashin da yake bina ne.
Da ganan na zarce daki na fara wasa da computer game'dina
wanda mahaifina ya siya min kafin ya rasu.
Washegari kamar yadda muka yi da Chukudi sai ga shi
da misalin karfe bakwai saura ya kawo min rikoda da kamara
hade da fin din. Bayan na yi masa godiya ya tafi sai na shiga
cikin gida ban zame ko ina ba sai dakina. Ina shiga na yi
alwala na gaida Ubangijina ka nan na ja kofa na rufe. Domin
na duba lafiyar kayan dana siya.
Bayan .na duba lafiyar kamara sai na ajiyeta na dauko
rikoda na saka mata wani tsohon kaset dina kana na danna
gurin daukar magana na fara magana a ciki. Ban kai wani
lokaci ba na kashe kaset din na dawa da shi baya kana na
danna gurin magana, muryata ta fara fitowa ras kamar ni nake
magana a wannan lokaci. Dana ga komai ya yi dai-dai sai nà
mayar da su na boye a cikin adakata. Na fada kogin tunanin
yadda zan bullowa al'amarin idan har na aikata abinda nake
shirin yi lallai bakaramar nasara zan samu ba.
Ina cikin irin naji an kwankwasa kofa, na mike na nufi
kofar ina zuwa na bude. Ta shigo sanye da hijab fari ba zaka
zo ka ci abinci ba? Na kalleta kana na ce 'Har lokaci ya yi
ban sani ba?" Mai kake yi da baka san lokaci ya yi ba?
Bayan ta fita sai na canja kayan jikina kannan na nufi
falo. Na zauna kamar yadda na saba na ci abinci.
Bayan na gama cin abinci zan koma daki sai Hajiya ta
dakatar dani. 'Uzaifa ga shi gobe zaku koma kotu babu shaida
yake nan?"
Na gyara zama na kalli kwayar idon yayana na kawar da
kai cikin takaici.
'Hajiya babu komai Allah yana tare da mu zan fita daga
wannan kangi insha'Allahu domin gaskiya ta kusan bayyana.'
37
A
Nafisa ta tambayeni cike da mamaki. Yaya ban gane gaskiya
ta kusan bayyana ba.'
Na ce 'Zaki ji komai sai nan gaba.' Nafisa tayi-tayi akan
na gayaa amma naki domin bani da cikakkiyar hujjar da zan
nuna mata amma idan na gabatar da hujja ta hanyar daukan
magana da hoto to, a wannan amma lokaci sai na nuna mata
kuma dole ta yarda. Haka ta hakura amma ba don ta so ba.
Na lura da yayana na yana kallona kallon mugunta amma
ban damu ba wai an fadawa kurma bakar magana.
Na koma dakina na ci gaba da tunani irin nasarar da
zamu yi in har abin nan ya samu, sai na ji an kwankwasa
mini kofa haushi ya kamani domin kuwa ina jin dadin
tunanin da nake yi.
'Waye? Shigo' Na ce a cikin fushi. Nafisa ta shigo ta cе
min 'Yaya me ya sameka na ga kana fushi? Na ce da ita ba
tare da na daga kai na kalle taba 'Ba abin da ya sameni ta dan
tsagaita da kallona kana tace "Baba Musa ne ya leko ya cе
ana sallama da kai a kofar gida.' Cikin mamaki na ce da ita
'Waye shi?' Ta ce 'Ban sani ba nima kallo na keyi a falo ya
leko ya fada min. Na ce 'to shike nan gani nan zuwa.' Ta fita
ta barni a cikin tunani. Ko Inspector Kabir ne? Na tambayi
kaina na tashi na nufi kofar gida.
Da fitata na zarce dakin Baba Musa mai gadi. 'Baba
Musa wake sallama da ni?"
Ya ce 'Wata mace ce nake gani ma ba a cikin hankalinta
take ba.'
Na bude baki. 'Ba a cikin hankalinta take ba? Na kara
maimaita maganarsa. 'Me ka gani ka ce haka?
Ya ce 'Yadda naga yanayinta na. Ya yi min kwatance da
dan yatsansa inda take. Na nufi wajen cikin faduwar gaba.
Ina zuwa wajen na karyata abin da kwayar idona ta nuna min.
Tana tsaye kai babu dan kwali kafa babu takalmi riga duk a
yayyage.
'Uzaifat,na kira sunanta muryata na rawa.
'Na'am.' Ta amsa idonta ya cicciko da hawaye, ina
matsawa kusa da ita ta fadi kasa sumammiya. Na yi sauri na
ciccibeta na yi cikin gida da gudu ina kiran Nafisa.
Nafisa! 'Nafisa!! 'Nafisa!!! Fito ki gani.
Nan da nan Nafisa da Hajiya suka fito, har baba Musa
sai da ya shigo. Hajiya cikin rudewa ta ce 'Wace ce wannan?
Na bude baki na ce. 'Uzaifat... amma sai na kasa
karasawa don rudewa. Debo ruwa Nafi. In ji Hajiya Nafisa ta
nufi kicin da gudu ta debo ruwa a cikin kwanon sha tana
zuwa ta watsa mata a fuska kana ta durkusa tana daddanna
mata kirji, ni kuwa ban da addu'a da nake yi ina shafa mata a
fuska babu abin da nake yi.
Hajiya ta kasa komai sai kallonmu take yi kamar bebiya.
Uzaifat ta yi ajiyar zuciya ai nan da nan wani murmushin,
farin ciki ya bayyana a fuskarmu.
'Ruwa! ruwa!! zan sha,' wannan shi ne abin da ke fitowa
'daga bakinta, amma sai wanda ya kasa kunne ne zai ji. Na
dauki ragowar ruwan dake kwanon sha na bata, ta sha kana ta
ce 'Ya isa.' Na cire ruwan daga bakinta amma idona na kanta
bai bar kallonta ba.
,Bayan hankalinta ya dawo gareta sai ta tashi daga
kwanciyar da ta yi ta dan jingina da kujera.
Bayan mun yi shiru wani dan lokaci sai Uzaifat ta ce
'Uzaif ina son in dan gyar ajikina.
Uzaifa ta mike kafin ta daga kafa Hajiya ta ce. Sanny
'yar nan, karonna far ko ke nan da ta yi magana tunda ta ce
Nafisa ta debo ruwa. Uzaifat ta amsa da 'vauwa.' kana ta bi
Nafisa a baya suka nufi dakinta.
Muka hada 'ido da Hajiya na ga idonta ya cicciko da
hawaye ta ce, 'Allah sarki Uzaif yanzu Uzaifat ce ta zama
haka? Ji yadda ta bi ta fada lallai wadanda suka tafi da ita sun
gana mata azaba kwarai da gaske. Kai! Allah Ya saka muku A
baki daya.'
Na ce 'Hajiya ki daina kuka ai tunda Uzaifat ta dawo
gaskiya ta bayyana.' Na tashi zan koma daki na ji an ce Allah
Ya kiyaye gaba. Na waiwayo sai na ga Baba Musa, ni har na manta da yana wajen na amsa 'Amin'sannan ya juya ya fita.
Ina zaune a daki a kan gadona na ji an turo kofa, duk da na san wadanda za su shigo wannan bai hana ni juyawa wajen domin na ga
masu shigowa ba. Tana sanye da rigar fakistan mai ruwan kwai kanta rufe da wani mayafi shara-shara bayanta kuma, nafisa ce suka shigo Uzaifat tà zauna akusa da ni ita kuma Nafisa ta zauna a kan kujerar da ke kusa da firjin. Ta yi min murmushin nan nata mai cike da alamar so,
nima na mayar mata da murmushi mai cike da nuna kauna. "Uzaif ya
bayan saduwa?" Na yi mata yar dariya "Sai dai wuya zan ce ba alheri
ba." Dukkanmu muka kwashe da dariya na ce "Uzaifat ya kuma na nemeki na rasa a wanan rana kuma mai ya faru?"
Ta yi mini wani irin kallo mai cike da damuwa ko kuma in ce cike
da hushi. "Uzaif kai dai bari, zancen yana da tsawo sosai sai mun nutsu
tukunna. 'Bau laifi'. Gumi ya gangaro min na sa hahnu na share muryata na rawa na ce."Baya ta dan huce sai na ke fada mata abin da
ya faru bayan bata nan. Da yadda yan sanda suka kamani da zargin da
ake yi mini da kuma shari'ar da aka yi duk na kwashe na fada mata, ta yi tsaki ta ce"Ai duk wannan mai sauki ne tunda na yi excaped". Bayan
mun dan yi hira sai Uzaifa ta fara gyangyadi "Barci kike ji ne?". Та се
"Ai dole". Na ce "Ai sai ki tashi ki je ki kwanta ko?". Ta ce "To". Har
ta mike sai ta ce "Uzaifat gobe zan so kai da Nafisa ku raka ni gida zan
dauko wai abu which 'is very important on this case". Na ce "Ai-babu
damuwa in dai ba zai kawo deley ba".
4
ayan sun fita na tashi a rufe kofata kana na kashe fitila na. BKwanta cikin farin ciki da annashuwar dawowar Uzaifa, Dama
hausawa sun ce "Idan dadi ya yi wa mutum yawa sai ya rasa
abun yi ko kuma ya ce Allah kashe ni dan dadi". To haka ne ya
kasance a gare ni domin kasa barci na yi, don murna, sai da agogon bangon dakiná ya buga karfe uku sa'annan barawon ya sace ni, ba ni na
farka ba sai karfe shida, bayan na tashi sai na shiga bandaki, na yi wanka kannan na yi alvala na yi sallah na fauki rigata shirt da wando
baki, ąa sn, mislain karfe bakwia na isa teburin cin abinci, na tarar
kowa da kowa ya hallara sai dai na yi mamakin rashin ganin yayana.
40
Amma sai na'basar domin so da Kaunarsa ma bana yi, balle ganinsa.
Bayan mun kammala cin abinci, sai Nafisa ta ce mu ta shi mu raka
Uzaifat kada lokaci ya wuce dukkan mu muka mike muka nufi harabar
cikin gida, muka shiga mota, bamu zame ko ina ba sai daula, muna
zuwa kofar gidan muka tarar da yansanda guda hudu suna zaune a kan
benci.
Muna fitowa daga cikın mota duk suka tashi tsaye suka gyara
bidigoginsu; daya daga cikinsu ya nufo mu tun kafin mu isa wajensu
"Tsaya kai malam, daga ina ku ke, kai ba kai ne Uzaif ba?" Kafin na yi
magana sai uzaifat ta dauko wani dan karami kati mai hade da hotonta
ta nuna mashi, ya ce"Tuba na ke". Daga nan muka shiga cikin gida
Uzaifat na gaba muna binta a baya, ta bi da mu wani dan tsukukun
lungun da ya kai mu ga matattakalar bene da muka hau sai ta kaimu
wani dan karamin daki mai bala'in duhu, kamar kabarin kafiri, can sai
na ga haske ya gauraye fadin dakin sakamakon fitilar da Uzaifat ta
kunna. A cikin dakin akwai wata 'yar karamar talabijin tamkar
'computer', ta sa hannu ta danna wani abu mai jan kai a jikin talabijin
din wani kaset ya fito daga ciki, ta sa hanu ta ciro shi, sannan ta kara
kunna wani abu gurin ya koma ya rufe kamar ba a bude ba. Muka fito
daga wannan daki muka nufi waje, bayan mun isa kofar gida muka yi
wa wadanan yansanda sallama, sannan muka shiga mota sai gida.
Mun isa gida misalin karfe takwas saura ashirin bayan mun zauna
muna hutawa, sai Uzaifat ta ke bamu labari a kan wannan kaset da
muka raka ta ta dauko. "Kaga Uzaif shari'a zata yi mana sauki idan har
basu yarda da shaidar da zan bayar ba, kasan lauya mugum mutum ne
sai ya iya mai da baki fari". Na yi dariya kana na ce da ita "Haka ne,
amma menene dalilin fadin hakan?". Ta ce "Abin da ya sa kaga domin
irin haka mahaifina ya sa wata na'ura mai hade da bidiyo wadda duk
abin da aka yi a wannan gida wannan na'ura zata yi rikodin dinshi, ka
ga kenan za a ga wanda yà yi kisan, ko ba haka ba?". Na sakeyin
dariya "Haka ne".
Bayan karfe takwas ta wuce sai nafisa ta shiga daki, jimawa kadan
ta fito sanye da kayan aikin lauya a jikinta, sannan ta yi mana umarni
da mu tashi mu tafi, sai da hajiya ta yi mana addu'a gami da fatan Allah
Ya bamu sa'a, dukkanmu muka amsa da amin. Bamu zame ko ina ba
sai kotu, muna zuwa muka shiga ciki mun tarar da kotun cike makil da
mutane, muka samí wuri muka zauna. Bayan alkali ya fito sai aka yi
41
wata shari'a akan rancen kudi wacce.har ta kai ga kisan kai, kannan aka karanto tamu shari'ar alkali ya sa aka tsayar da ni cikin kanta, ina cikin
kanta ina kallon Nafisa, sai wannan lauyan fari dogo ya tashi ya yi
gaisuwa ga alkali, sannan ya nufo ni, ya yi min yake mai nuna alamar kurewa.
"Malam Uzaif ka ce zaka kawo shaidarka ko?".
"Na zo da ita". Na amsa masa.Nan da nan fuskarsa ta canza ba ma
shi kadai ba har daya lauyan. "Ka zo da ita?" Ya sake tambarta cike da mamaki.
"Hakane yallabai na zo da ita". Na sake bashi amsa.
"Ya sunanta?". Na ce "Uzaifat A. Saleh"
Ya yi kiran Uzaifat ta fito jama'a sai kallonta suke yi. Ta tsaya a
daidai wurin da ake bukatar mai bada shaida ya tsaya.
'Malama Uzaifat". Daya daga cikin lauyoyin nan ya soma yi mata
magana.
Nà'am', ta amsa.
"Kotu na son ki fada mata wurin da ki ke ranar asabar misalin
karfe goma sha daya na safe".
"Ina gidan mahaifina tare da Uzaif a wannan rana kuma a diadai
wannan lokaci".
"Ko zaki sanar da kotu abin da ku ke yi a wannan lokacin?".
Ta kalle shi kallon tsana. "Hira mu keyi". Ta amsa cike da kwarin gwiwa.
'Shin me hirar taku ta kunsa?'. Ya tambaya.
Kafin ta yi magana Nafisa ta mike 'Allah Ya gafarta malam ina gani bai dace dan'uwana ya tambayi wannan maganar ba domin bata shafi abin da zargi ba, ban da haka maganr zaza ta iya kasancewa sirri a
tsakaninsu'.
Alkali ya kalli wannan lauyan ya ce. 'Ka sake tambaya wanan ba ta nufi shari'a ba". Nafisa takoma a zauna.
Lauya ya mai da kallonsa ga Uzaifat ya yi dariya a zuwan bai damu ba, kana ya ci gaba 'Kotu na zargin Uzaifat da laifin kisan kai, ko zaki iya bada shaida da zata nuna cewar ba shi ya yi kisan ba?". "Tabbas ba shi ne ya yi ba". Ta fada cikin babbar murya. "Kina da hujjar da ta nuna cewar ba shi ba ne?"
42
E
"Na ce ba shi ya yi kisan ba ne domın muna zaune a falo muka ji
kara daga sama kuma gabaki daya muka mike muka nufi sama, shi ya
sa wanan kawai ya nuna cewar ba shi ya yi kisan ba"
Lauyan ya koma wajen zamansa ya zauna, sannan wannan mara
imanin ya taso ya yi gaisuwa kana ya juya zuwa ga Uzaifat.
'Malama Uzaifat mun' ji bayaninki, amma ba wannan ba ne zai sa
kotu ta yarda cewa ba Uzaif ba n ya yi kisan domin a lokacin da aka je
gidan shi kadai aka samu a ciki ba kya nan kuma da aka ganshi a
kokarin gudu yake yi. To, ke a ina ki ke a wannan lokacin, kuma ban
da haka ai zaku iya hada baki just to save him! Ihu-ihu ta kalle shi nan
da nan ta harzuka ta fara yi mishi magana.
'Haba lauya! Ya za a yi na daurewa wanda ya kashe mahaifiyata
gindi ta hanyar hade baki da shi?, Ai