fitsari ta cewa Salama
"Wallahi Salama fitsari nake ji, ya matseni
matuka kamar ya zubo kuma naje bandaki
na tadda layi yanzu ya zanyi?"
Wani irin kallo ta yi mata shekekek
sannan ta ce mata
"To ya kikeso na yi miki? Ko bakina
kike so na bude ne ki yi fitsarin a ciki?
Suma da kike gani a layin ai a matse
suke amma kuma dole suka hakura, don
haka ke ma hakurin zaki yi har azo kanki
shiyasa ake so a gasa maka cibiya sabida
ka dinga rike fitsari."
114
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Wani takaici ne ya turnuke ta,
kallonta kawai ta yi ta girgiza kai sannan ta
fice daga dakin da kyar take takawa domin
ko yaya ta taka sai ta ji kamar fitsari zai
zubo gaba daya.
Tana isa gurin layin ta tadda na ciki
ya fito wani kasurgumin kato, ganinsa ya
tsorata ta, amma sai kawai ta matsa kusa
da masu bin layin ta karyar da murya ta ce
musu.
"Don Allah ku taimakeni ku barni
na shiga wallahi na matsu kar fitsarin ya
zubo.
Gaba daya suka harareta cike da
mamakin raina musu hankalin da take
neman yi.
Delu ce ta kalleta ta yatsina fuska
sannan ta ce, "yau nake jin karfin hali barawo da sallama, mu da muke bin layin
an gaya miki ba a matse muke ba?"
115
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Kande ta amshe tana rike da kugu
cike da takaici ta ce "To matsuwa kuma ta
nawa?"
Ta nuna wata dake durkushe ta ci
gaba da cewa "Wannan da kike gani
gudawa takeyi tun dazu take murkususu
amma dole ne sai ta bi layi domin haka
tsarin gidan yake, mu bamu iya kashin
dankali ba, na sama ya danne na kasa, don
haka yi azama ki bi layi kar wata ta zo ta
shige gabanki."
Wani irin takaici ne ya turnike Mero
bata iya cewa komi ba illa komawa da ta yi
jikin bango ta rakube tana zubda hawaye
mai zafi na takaici.
A nan a tsaye ta ji fitsarin na jikinta,
babu yanda zata iya domin bata isa ta
maidashi ba, sai da ta gama fitsarin sannan
ta bi jikinta da ruwa ta wanke ta bar gurin
ta nufi daki tana jin mutanen gidan suna
mitar anyi musu fitsari a tsakar gida amma
116
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE2
ta yi biris bata ko tanka musu ba domin
abin yayi mata yawa matuka.
Bakin kofar dakin kawai ta je ta
zauna tana ci gaba da zubda hawayen dana
sani.
****
Can gudansu Mero kuwa hankalin
Baba Kande ne kan diyarta,kullum
damuwa ta rashin sanin inda diyar tata
take, tana so ta yiwa Baba Idi magana
amma tana gudun taşhin hankalinsa.
Izuwa yanzu dai kam damuwar tata
takai makura don haka ta yi karfin halin
tinkararsa da maganar.
A zaune suke bisa tabarma suna hira
jefi jefi da karfin hali ta yunkura ta ce
masa "Mai gida yanzu yarinyar nan ba za
a bincika a ji inda take ba, da kanka fa
kace kaje gurin mijinta ka bashi hakuri
117
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
yace maka bata dawo gidansa ba, anya
kuwa ma zuba idanu?"
A fusace ya dubeta sannan yace
mata "To ai sai ki tafi neman nata tunda ke
kin damu da ita, yarinyar da muka koreta
amma sabida bamu isa ba memakon ta
koma dakinta ashe tanada inda yafi gidan
Ubanta dana mijinta."
To ni ba tsohon banza ba ne, idan da
ya gujeni ba zan tafi nemansa ba domin
shine ke neman albarka a gurina amma ba ni ke neman albarka a gurin sa ba, don
haka ga hanya nan daga nan har bayan duniya ki tafi neman diyarki amma ba da
yawuna ba."
Hukuncin da ya yanke ya yi mata tsauri amma babu wani abu da zata iya yi domin tana matukar shayin mijin nata,
sannan tana girmama aurenta na shekaru
masu yawa tun bata san kanta ba.
118
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Don haka ta rangwadar da kanta
kawai ta ce "Shi kenan Allah ya bayyanata
a duk inda take."
Amma cikin ranta ta kudire cewar
zata dage da addu'a kuma zata sanya a
tayata da addu'ar Allah ya bayyana mata
inda diyar tata take."
Cikin halin halin ko in kula yace
mata "Kuma dai, ai ni ba hanaki zuwa
nemanta na yi ba, amma dai nace ba da
yawuna ba."
Bata sake ce masa komi ba illa
mikewa da ta yi tana fadin "Allah ya
kyauta."
Ta nufi dakin girki domin fara
aikace aikacen ta na gida, cikin ranta tana
addu'a Allah ya kawo mata karshen
wannan al'amari ya bayyana mata
diyarta."
Ita kuwa Mero tana can gidansu
Salama tana faman shan wahala, yau kuma
119
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
da ciwon ciki ta ta shi, don haka take ta
murkususu tana fama shafa cikin nata ita
kadai tasan wahalar da take sha.
Salama ta kalleta shekeke cikin daga
murya ta ce mata "Wai ke Mero me ke
damunki ne kike ta faman murkususu?
Ko cikin naki ne ke miki ciwo? Ai
gashi nan kinga abin da ya sameki ai ba
irin gargadin da ban miki ba akan kar ki
yarda da mutumin nan baki yarda ba,
gashinan kina fama da dirkeken ciki shi
kuwa yana can zai bare sabuwa dal a leda
ko tunawa da ke bayayi."
Wata kwallar takaici ce ta fito mata
cikin shesshekar kuka ta ce mata "Yunwa
ce ke damuna Salama tun farau farau din
da na sha dazu shikenan a cikina, kuma
kin san ba ni kaďai bace."
Kwabe baki ta yi ta yatsina fuska ta
ce. "Mero kenan to ke da wai kina nufin
nice zan dinga ci da ke? Tabdijan nima sun
120
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CЕ-2
Inna da za su tafi ba su barni da komi ba
illa rai da lafiya, ni ke fita na yi 'yan shige
da ficena na ci da kaina, kin sani kuma ba
sana'ar komi nake yi ba, in zaki saida
kadara ki samu abinçi to, in kuma zaki
zauna ki bushe ke da dan cikin naki duk
dai ke ya ragewa."
Wani irin daci ta ji kan harshenta
sabida bakin ciki da takaici, ba zata iya
magana ba, illa ci gaba da shafa cikinta da
ta yi wanda ke azalzalarta, tamkar dam
cikin zai fito.
Cikin ranta take fadin "Lallai maza
basu da tausayi, duk da dai tasan ta yi laifi
amma ai bata cancanci wannan hukuncin
ba ko don cikin dake jikinta, wai yau ita ce
abincin da zata ci ya gagareta, hawayen dai
ke sake biyo idanuwan nata, ta sanya
hannunta ta share tausayin kanta da na dan
cikin nata ya mamayeta.
121
AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CЕ- 2
Ita kuwa Salama tsaki kawai ta yi ta
wuce ta barta a nan tana fadin "Yau na ji
karfin hali dana baki gurin da zaki zauna
ma ai nayi ca nake iyayenki ne suka koroki
ni na rufa miki asiri na karbeki shine kuma
zaki zauna ki saki baki na baki abin da za
kicin? Lallai Mero baki da lissafi sam.'
Shi kuwa Alhaji Sadik kamar kullum
yana gaban gimbiyar tasa ya sanyata a
gaba tamkar zai lasheta, ita kuwa sai wata
ran gwada take yi tana yin abubuwab da
tasan yana tafiya da imaninsa.
Cike da kulawa ya kalleta daga sama
har kasa ya saki murmushi cikin tausasa
murya yace mata "Dafatan dai duk abin da
bai yi maki ba ki fada sai a sauyashi."
Wani fari ta yi masa sannan ta zari
idanuwa ta ce masa "Haba ranka ya dade
ai wallahi komi ka yi hidima kwarai, Allah
ya saka da alkairi ya bamu zaman lafiya."
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE 2
Maganganun nata sun ratsa shi sosai
wani dadi ya ji ya mamaye ko ina nasa
domin ba abin da yake kauna a duniya irin
ya faranta mata don haka cike da jin dadi
ya amsa mata da "Ameen, ko dama
godiyar da kike ta yi mini a waya kenan?"
Ta rangwadar da kai abin da ke kara
daukar hankalinsa sannan ta ce "Eh mana
kai da baka gane ba? Ai Inna ma ta ce na
yi maka godiya sosai, kana jin yanda
aurenmu ya zama abin yadawa a gari?"
Dariya ce ta subuce masa, ya amsa
da cewar "Ai haka ake so dama, domin
kyakkyawa kamarki abin da ya dace ayi
mata kenan."
Gaba dayansu suka yi dariya Sadiya
ta sake rangwadar da kai ta yi masa wani
irin fari da ya aikata shi sannan ta ce masa
"Amma godewar da kike min kamar ta yi
yawa, ai ban kaiyadda kake fada ba."
123
AWITYA WADA ISA- YAR ALJANNA CE
Maganar tata ta ratsa ruhinsa cikin
kasalalliyar murya ya ce mata "Sadiya
kenan ai komi naki ya yi, ba kya kallon
kan ki ne a madubi shiyasa inajin baki san
kanki aba, amma mu da muke kallonki ko
yaushe ai mun san bamu ce komi ba a
yabawa halittarki da iya tsara kwalliyarki,
shi yasa nake jin kamar gC ACI na janyo kwana
biyun nan da suka rage na ganki a
dakina." iseoe gvibog sAsπ
Wani irin dadi ta ji ya mamaye ta
domin ba abin da take kauna a ranta illa ta
ji cewar ta tafi da imanin Alhaji don haka
ta zaro idanuwanta da suke dauke hankalin
Sadik sannan ta yi dariya ta sunkuyar da
kai kasa kana ta ce, "Uhum Alhaji kenan,
gaskiya kana da zumudi dad yawa.
cikin mutuwar jiki Alhajin yace mata
"ke kinsan kanki kuwa?sb aswabog smmA"
Ai dole nayi zumudi akan ki, ke ni
ko ma na shiga gurin Inna ne yanzu nace a
124
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
fasa yin taron bikin kawai ki sanya
mayafinki yanzu na tafi dake."
Da sauri ta zaro idanuwa ta bude
baki, sannan ta juya ta nufi gidansu tana
fadin "Tabdijan bari kaga tafiyata tun
kafin mafarkina ya tabbata."
Ya bita da kallo tana matukar jan
hankalinsa tamkar wani magana disu take
tare da shi, cikin kasalar murya yace mata
"Ko sallama ba zaki tsaya muyi ba
Sadiya?"
Tana zuwa dai dai kofar shiga cikin
gidan nasu ne ta bashi amsa da cewa
وو" Mayi a waya.
Tana gama fadin haka ta shige cikin
gidansu.
Tsayin lokaci yana tsaye yana kallon
kofar gidan nasu sannan daga bisani ya
hakura dolensa ya shiga motarsa jikinsa a
sanyaye yana jin tamkar ya bita cikin
gidan nasu.
125
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
****
Ita kuwa Mero duk ta yi baki. ta
rame, idanuwanta duk sun fada sunyi zuru
zuru, sai ciki a gabanta tororo.
Suna zaune ita da Salama a cikin
dakinsu wata jaka ta fado daga kan tsirin
kayan da ke kan dakin, wani yariin gwal
ne ya fado daga cikin jakar dukkansu
idanuwansu suka hadu a kan kallon yarin.
Mamaki ya cika Mero, don haka da
sauri ta kalli Salama ta ce mata "Salama
wannan yarin da ke kusa dake naki ne?"
Wani irin kallo ta yi mata a
wulakance sannan ta masą mata da cewa
"Nawa ne mana ji wata irin tambaya, tunda
kika ganshi a kayana ai kinsan nawa ne.
Da sauri ta dauko yarin tana kallonsa
a hannunta tana dubawa san a ta ce mata
126
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE2
"Ashe kina da irin yarina da ya bata amma
ban taba ganinki da shi ba sai yau?"
A fusace Salama ta ce mata "Ban
gane me kike nufi ba, kina nufin yarinki ne
daya bata ni kuma na sace kenan ko? 3
Tunda dama ke kadai aka Kerawa
irinsa ko? Kuma ni talauci ba zai barni na
2
mallaki yarin gwal ba sai ke matar Alhaji.'
A sanyaye Mero ta ce mata "A'a
wallahi ni ba haka nake nufi ba, da ga nace
irin nawa?"d iv i emsta2 n
Tamkar wacce aka tsaikara sai kawai
ta mike ta tsaya akan Mero a fusace tana
fadin "Haka kike nufi mana Mero, wallahi
haka kike nufi, yau na ji masifahaka kawai
na jajibo ki har gidanmu zaki zo ki kala
min sata kiri-kiri ina ji ina gani."
anoy Mero ta mike jikinta na kyarma ta ce
"Haba Salama menene na yi mini gori
akan 'yar wannan maganar?"
127
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
Cikin daga murya ta ce, "Ke ce kika
dauketa 'yar magana ni babba ce a gurina
domin sharrin sata bashi da dadi, don haka
ni kam ba zan iya zama da ke ba kina yi
mini sharri bayan ci dake da nake yi da
baki makwanci."
Wani irin tashin hankali ta ji cikin
ranta, da kyar ta iiya mikewa jikinta ba
kwarin jiki na daukarta ta janyo mayafinta
ta yafa ta janyo akwatinta sannan ta ce.
"Shi kenan Salama ki yi hakuri insha
Allah yanzu zan bar miki gidanki."
Daga nan bata sake cewa komi ba
illa janyo akwatinta da ta yi tsakar gida.
Ita kuwa Salama tuni idonta ya gama
rufewa da masifa don haka cikin daga
murya take fadin.
"Ey aje Allah ya raka taki gona
Umma ta gaida Assha, ba zan lamunci
sharrin sata ba ko kadan, abi wani sarkin
kuma."
128
AWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNA CE 2
gidan mijinta, Allah ya rufa mata asiri bata
99
gane ba, gashi nan ta tonawa kanta.
Delu ta amshe da cewa To ai jiki
magayi, mu din nan da muke cikin talauci
da wahala ma bamu yi wasa da aurenmu
ba, ballantana wanda ke cikin daula irin ta
Mero.
Ita kuwa Mero jan akwatinta ta yi ta
nufi kofar fita, tana zuwa daidai kofar ta
juyo ta dubi Salama kamar tana wani
tunani sannan ta gyada kai kawai ta juya ta
fita, ita kuwa Salama fadi take.
iAje dai Allah raka taki gona haka
kawai zan daukowa kaina ruwan dahuwar
kaina, ina zaune cikin rufin asirina, ba zata
sabu ba bindiga a cikin ruwa."
Da kyar take daga kafafuwanta tana
jan Trolly din nata hawaye na bin idonta
ita kanta bata san ina ta dosa ba.
Nima na dakata anan. mu hadu a
littafi kashi na üku insha Allah. y dallA
130 S
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
ALAWIYYA WADA ISA
(maman twins)
08033472866
DAGA TASKAR SARAUTA
08034255307
TALLA! TALLA!! TALLÁ!!
"Abban Ilham yau ina zuwa ne da sanyin
safiya haka.?"
Ya dubi Agogon Bangon dake dakin tara
da 'yan mintuna. "Me ki ka ga ni.?"
Shi ma ya tambaye ta.
131
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
"Na ga ne ka ci ado kamar wadda za ka
fita wani taro na musamman."
"An ce ba kullum ake kwana a gado ba,
kuma haka ne wadannan masana fadin magana
sun fadi gaskiya, yau kai ne a can gobe kai ne a
nan."
Ta bishi da kallon mamaki domin amsar
tasa bata fuskanci ainihin abin da take son ji ba."
"Uhm sai an karya min harshe kuma, ni
dai tambaya na yi amsa nake bukata kawai ina
zuwa yau da safe.?"
"Neman aiki.?"
Ta jima ta na kallon sa da mutukar
mamaki.
"Neman Aiki.?'
Ta fada da mamakinta.?"
132
AWITTA WADA ISA- YAR ALJANNA CE2A
"Zan je neman aiki ne saboda al'amura
sun fara yawa, duniya ta na da girma, haka
hanyoyin samu na da fadi, babu mamaki idan can
ta ki ka koma can, fadi ta shi dai dama bawa bai
isa ya ce yafi karfin yi ba, in har ina busar
numfashi. Zan je ko Allah zai sa a dace."
"Me ne ka rasa.?" rude of sa
nennsw, sh iy unn os sy ofcoaр ок eр t ad edog
"Me ne na samu.?"sxinub sh nioelol WUYBI
Ya dawo mata da tambayar ta kai tsaye. sd Tsyinub Ita kuma ta saka masa ido cikinmutukar
mamakin kalamansa.
S Ba samu komai 318h smmA
samu komai ba, Hafsa dan ki ka
auna cewar idan Allah ya ba mu aron rai gobe ba
irin yau ba ce jibi ba rin gobe bace haka gata
citta, don haka ya zama dole na shiga duniyar
neman abin rufin asiri abubuwa sun cunkushewa
rayuwa ta, na ga alamar baki san da haka ba." nsW
EBW sWtun an ibsi Ta mike daga in da take ta dawo kusa da
shi "Mai yasa kake yanke kauna da daukaka ta.
133 E
AWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE 2
(
t
(
Ya zuba mata ido kafin ya ce komai
sannan ya gyara murya ya ce, "Daukaka lokaci ne
da ita, ki na nan za ta zo ta turmeshi ki, kuma
kada ki manta ba a rayuwa a dakushe."
"Kamar yaya.?"
"Da ni na ke shuhura, yanzu kuma ke ce,
gobe ba fa ba ke bace, to ya za mu yi da wannan
rayuwa, lokacin da duniya take yi da kai, lokacin
jama'a ke yi da kai. In kin ji an ce duniya. To ba
duniyar ba ce jama'ar cikinta ne. Ranar da
jama'ar suka koma kan wata, kaka ke nan.?"
"Amma dai ka san duk lalacewar dan zaki
yafi karfin kadangare, ko da a ce ban da wani abu
da zan tabuka mahaifina mai kudi ne, ba kuma
zai hanani duk abin da nake bukata ba."
Ya dora hannuwansa a kai, daga bisa ni
wani murmushi ya kubuce masa "Da a ce zan
fadi na mutu. Wannan shi ne abu mafi soyuwa a
cikin zuciyar iyayen ki, ni kuwa don me zai sa na
134
시
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE-2
zauna ina barautar abin da za su ba ni, wadanda
ko kauna ta a raye ba sa su. Hafsa ki rike
daukakar ki, ni ma zan je na nemi abin da zai
rufamin asiri, daga rana irin ta yau na rabu da
harkar rubutu, har Abada kuma ina mai nadamar
kasancewa ta marubuci.
Tirkashi, in ba ka yi ba ni guri. Wani
kasaitaccen labari, mai sa ka zubar kwalla, mai
dauke da wata sha'umar soyayya, wannan labarin
ya kasaitu ya samu ingancin aiki, sabon salo a
cikin rubuce rubucen zamani, ka da ka saki a
baka labarin wannan kasaitaccen littafi mai suna.
BA ALJANNA BACE.
Matashiyar marubuciyar nan 'yar uwa ga Hadiza
Adam shi shitu wato Rabi'atu wacce ta rubuto
littafaina kamar haka
BAKIN JINI NA.
135
ar
a
AWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNA CE- 2
TAKAICINA FARIN CIKINA.
MURAIDIN RAINA
DAN KUKA
ALKIBLATA
NI CE NA DACE
ZANEN DUTSE ТА КARA YUNKURAWA
TA KAWO SABON LABARI MAI SUNA ...BA
ALJANNA BACE, KI NEMI NAKI А
KASUWA DA ZARAR YA FITO. Kada ku
manta da sunan BA ALJANNA BACE
136
Littartafan marubucivar:
SHARRIN ZUCIYA
...RABIN JIKI
GUGUWAR ZAMANI
RUWANIDO
DUNIYAR MAKARANTA CЕ
YAR ALJANNA CE
YarAljanna Ce
ALAWIYYA WADA ISAH
BUGAWA DA YADAWA:
Printing & Publishing by:
SARAUTA PUBLISHERS
08034255307
Cover Graphics
Anka-Graphics fagge 07030319787
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels