ma ya
fada tsakanin kujeru, kinga kuma in hakane
55
AWIYYA WADA ISA- YAR ALJANNA CE2
ba za ki ganshi ba sai sanda aka balle kujerun
don haka ki bar neman nan kawai ki zo mu
wuce ni wallahi ke nake ji ba ni kaina ba, ni
ko kwana zanyi a tafe ba ruwan wani da ni ke
kuma fa?"
Mero ta ce "To ai ni abin ne ya yake
daure mini kai, domin ba yanda za ayi yarin
nan ya fada cikin kujera don na sha ajiye shi a
nan kuma na dauki abina inda na ajiye.
Salama ta dubeta shekeke ta ce mata
"Af! To yanzu wa ya daukeshi? Ko kuma ni
kike zargi? "Ta fada cikin bata fuska.
Mero ta kalleta ta ce, mata "A a ni
wallahi ni ba haka nake nufi ba, muje kawai
dan na dawo na dubashi cikin tsanaki."
Salama ta juya ta nufi kofar fita tana
fadin "Ato da dai ya fi miki."
Itama Mcron ta bi bayanta suka fice
zuwa kasuwa.
56
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE 2
Tafe yake a kan hanyarsa ta zuwa gida
daga office, wata zuciyar ce ta raya masa
ccwar ya kamata yaje gurin Auwalu don haka
ya juya kan motarsa zuwa majalisarsu domin
yasan a wannan lokacin a nan ne kawai zai
iya samun Auwalu.
Kansu na kasa sun dukufa suna faman
karta, har ya tsaya da motarsa ya fito sannan
suka kula da zuwansa, ya yi musu sallama
sula amsa sannan ya tambayi Auwalu.
Babu wani gamsasshen bayani na ina
yake don haka ya yi musu sallama ya juya
zuwa motarsa.
A daidai kan hanya suka ci karo da
Lado daya daga 'yan majalisar tasu, da zolaya
yace masa "Ango ka sha kamshi, shima yayi
dariya ya amsa masa da cewa "Lado kartagi
uban 'yan karta, an taho sana'ar ne?
Suka sake yin dariya, Lado yace masa
"Saddiku baka da dama ina amarrya?"
Sadik ya ce "Amarya tana can gida
abinta."
57
AWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE 2
Lado yace "Ko da yake dazu 'na shiga
kasuwa na gansu ita da wata kawarta sunyi
siyayya ko da yake dai basu ganni ba amma
ni na gansu, ai abokina ka iya kiwo yarinya ta
yi kyau ta yi 6ulbul da ita haka.
Alhaji Sadik ya katseshi cike da
mamaki yace masa "Kasuwa kuma Lado ko
dai wata ka gani ba ita ba?"
Lado ya yi murmushi yace masa "Haba
Saddiku ai Mero ba zata bace mini ba,
yarinyar da ta taso a gabanmu? Ai a sanin
Mcro daga Auwalu sai ni ke rufa masa baya."
murmushin Alhaji Sadik ya kakaro
yake da niyyar rufawa kansa da iyalansa asiri
yace masa "Hakane Lado ka sanni da
mantuwa, na tuna ta sanar dani zata je siyo
abubuwan da suka kare a gidan.
Lado ya yi dariya yacc masa "Ai kai
Saddiku tsufanka da kallo, nan da na sai kacе
ka manta abu, kuma har ma abin da ya shafi
aurenka? Allah ya yaye maka, ni dai na san
Mero na gani yarinya ta yi kyau abinta amma
dai duk da haka ban kasa ganeta ba."
58
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Alhaji Sadik bai ce komi ba domin tuni
ya kure da takaici da kunar rai musamman
yanda Lado ke bayyana matarsa, don haka
motarsa kawai ya nufa yana fadin "Gaskiya
bari na koma sai anjima."
"To sai anjima Allah ya kiyaye, Lado
ya amsa masa sannan ya nufi gurin 'yan
uwansa 'yan karta, shi kuwa Alhaji Sadik
tashin motarsa ya yi da sauri ya dagawa
sauran abokansa hannu ya wuce zuciyarsa na
yi masa kuna tana azalzalarsa.
Kai tsaye gida ya wuce, cike da bacin
rai ya dire a falo yana kwalawa Mero kira,
cike da yauki ta fito daga cikin dakinta tana
yatsina tana bata rao, ganin halin da take ciki
ne ya sanyata mamaki ta zo ta tsaya kawai a
gabansa.
A fusace yace mata "Wai ke don Allah
wacce iri ce? Ke wai bakya son zaman lafiya
ne a rayuwarki?
Na auroki don na huta amma banda
takaici da bacin rai da bakin ciki ba kya haddasa mini komi?
59
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE 2
Da mamaki ta dubeshi ta ce masa "Me
kuma na yi kake mini wannan tashin hankalin
daga shigowarka ko zama baka yi ba?"
Ya sake hasala ya dubeta da bacin rai
yace mata "Kinji irin rashin da'ar taki ko?
Waye ya baki izinin fita daga gidannan
ki ka je kasuwa ba tare da sanina ba?"
Kwabe baki ta yi ta yatsina fuska ta cе,
"Af wannan 'yar karamar fitar da nayi har
munafukai sun je sun sanar da kai?
To da sunyi hakuri ma ai da zan sanar
da kai cewar na dan fita.""
Nan take ya hau huci tamkar wani Zaki
sabida Kara masa bacin rai da ta yi, cikin
karaji yace mata "Ok wato kina ma tabbatar
mini da kin je kenan inyaso duk abin da zanyi
na yi ko?
Wai ke wacce irin tarbiyya aka yi maki
a gidanku ne?"
Kuka kawai ta saki, cikin kukan take
fadin "Af abin har ya kai ga zagin Iyayena?
Daga na dan fita kuma nace dma zan gaya
maka, me Iyayena suka yi mak
60
AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE 2
Cike da takaici yace "Mata to biyayya
cc basu yi maki yanda ta dace ba, ko kuma
basu sanyaki a Islamiyya ba domin da kinsan ilimin Addininki da dole zaki san cewa
matar aure sai da izinin mijinta take fita ko
ina nc.
Kara ci gaba ta yi da kukan, ta juya
kawai ta nufi cikin dakinta tana fadin
"Wallahi ba zan yarda ka dinga zagar mini
lyayena ba domin alheri suka yi maka da suka
haifeni har ka samu ka aura.
Tana kaiwa nan ta shige cikin dakin,
shi kuma kawai binta yayi da kallo cike da
takaici da bacin rai ya dafe kansa idanuwansa
sunyi jawur sabida takaici.
Ji yayi ba zai iya zama agidan ba domin
zuciyarsa tafarfasa kawai takeyi don haka ya
mike ya dauki mukullinsa ya nufi motarsa ya
tasheta ya fita, yana tafe kan titi amma bai san
ina ya nufa ba, haka ya dinga tafiya a kan titi
ba shi da gurin zuwa har sai da dare ya soma
yi masa sannan ya juyo ya dawo gida.
61
AWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNА СЕ- 2
Haka nan 'dukkansu suka kwana kowa
ransa babu dadi, washegari har ya nufi ofis ko
motsin Mero bai ji ba, balle ya saka ran
fitowarta.
Sanda ya taso daga ofis sai ya ji yana
bukatar ganin Hajiyarsa don haka sai kawai
ya nufi gidannasu kai tsaye.
Da sallama ya shiga ya taddata zaune
tana hutawa a falo, sai da suka gaisa sannan ta
fara yi masa da cewa "Kamar kasan ina so na
ganka sai gashii Allah ya kawo mini kai, ka
bani mamaki matuka, har yaushe aka yi auren naka da har matarka zata fara kawo mini
karar ka?
Kuma abin takaici da 6acin rai wai
Iyayenta kake zagi, abin da ban sanka da shi
ba, na ji ciwon wannan abu sosai, domin ya
nuna baka daukar hudubar da nake yi maka a
kullum akan matarka.
Maganganun Hajiyar tasa sun daure
masa kai, mamaki ya cikashi.
62
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Da sauri ya yace mata "Hajiya wallahi
ba haka bane, ni nafi so ki saurareni na gayа
miki yanda komi ya kasan.....
Da sauri cikin fada ta katseshi da cewa
"Rufe mini baki, bana so na ji komi daga
bakinnka, wannan yarinyar 'yar albarka mai
ganin girma da mutuncin mutane, ba za ta
taba shirya abin da bai faru ba ta zo ta fadi,
yarinyar da babu sawa ba fitarwar me zata yi
wa mutum na 6acin rai."
Dagowa kawai ya yi ya kalleta cike da
6acin rai ya girgiza kai kawai.
Cikin fada Hajiyar ta ce, Ai dama sai
dai ka kalleni din amma baka da ta cewa,
wato ka fara biyewa zigar abokai ko?
Sunga Allah ya rufa maka asiri shine
suke so su shirya maka gadar zare, su kai
ka su baro, to wallahi ba zan lamunta ba,
sam kar ka bari na sake jin wani abu
makamancin wannan ya sake faruwa.
Cike da karfin hali ya girgiza kai
kawai ya ce mata "Shi kenan Hajiya Allah
bayyana gaskiya komi daďewa.
63
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
"Yo ga gaskiya nan ta tabbata ni dai
na gaya maka ka kiyaye."
Kansa na kasa ya ya amsa da cewa
"Shu kenan Hajiya Allah ya kiyaye gaba."
Da "Amin ta amsa, shi kuma yayi
mata sallama ya fito ransa na yi masa
Kuna.
Yana tafe bisa hanya ne wayarsa ta
hau kara, Auwalu ne don haka ya saka
handsfree suka fara magana.
Bayan sun gaisa ne Auwalu yace
masa "Dama na kiraka ne na isar da sako,
su Ahmad ne suke so za su zo gidanka su
ga amarya, shine suka ce na sanar da kai,
to ni kuma zata iya kasancewa su zo bana
nan don zan danyi tafiya, shine nace bari
na gaya maka ta waya don kar na manta."
Duk da gabansa ya fadi domin ya
san yanayin da gidansa yake ciki amma
hakan bai hanashi amsawa ba.
64
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Cikin karfi hali yace masa "To
shikenan Allah ya kaimu, zamu shirya
zuwan nasu insha Allah, akwai maganganu
da yawa da nake so muyi amma sai mun
hadu sai mu tattauna.
Auwalu ya amsa da "To ba komi, ni
yanzu na saita hanyar tafiya, amma Insha
Allah idan na dawo zan lalubeka sai mu
tattauna din."
Alhaji Sadik ya ce "To shi kenan
Allh ya tsare, suka yi sallama suka ajiye
wayar.
Jikinsa babu kwari ya shiga cikin
gidansa. A zaune ya taddata a falo tana
kallo, ya nemi guri ya zauna ko kallonta
bai yi ba.
Sannu da zuwa ta yi masa gami da
zuwa kusa da shi ta zauna, ko kallonta bai
yi ba illa sake dauke kansa da yayi ya
sauya tashar da yake son ya kalla.
65
AWIYYA WADA ISAYAR ALJANNA CE2
Yana ajiye remote din ne ta sa hannu
ta dauka ta sauya tashar sannan ta sake
maida kallonta gareshi.
Juyowa ya yi ya harareta sannan ya
dauke kansa, kamar ba zaice mata komi ba
sabida zafinta da yake ji, amma sai ya
daure yace mata "Yanzu ke abin da ki ka
yi ya dace kenan?
Da sauri ta yi dariya ta ce masa "Mе
kenan na yi? Canja tashar da na yi ne ban
kyauta ba?"
A fusace ya fizge remote din da ke
hannunta yace mata "Yanzu ke tsakaniinki
da Allah ni ban kai ki kara ba sai kece zaki
je ki shirya mini sharri kice wai na zagi iyayenki?
Anya kuwa kina tsoron Allah
kuwa?"
Kanta na sunkuye tana wasa da yatsunta ta amsa masa da cewar "Ai sako
Iyayen da ka yi ne ya bani haushi, amma
66
AWIGYAWADAISA YAR ALJANNAICRA
tunda Hajiya da bani hakuri komi ya wuce
nia gurina har ma na manta anyi
Kansa kawainya girgiza yácet Allah
sya kyautanyanzu abin da nake so na sanar
imiki shinewgobe insha Allah abokaińa ża
su zorsu tayamu murna sabida basa nan
akaniyin bikinmu don haka ina neman
alfarma da hadin kanki, ki yi musu.duk
rabin da ya dace wanda zamu fita kunya."
isl si Gike da gamsuwa tace masaBa
kominAllah yakaimu za ayi komisinsha
ilahys iss sbu nice Test Star 6
вгnollsAmsar tata ta sanyashi farin cikirdon
haka yayi murmushi yace "Shi kerian
Allah yayi miki albarka, Allah yásáłki dore
a haka ki igane gaskiya." A E2707ETINTE
пнсо Миmushi kawai ta yistarmikeita
nufi kan tebur domin hada masa abincin da
zai cin shilkansa abin mamaki yake bashi,
Gikin mransa yake fadin "Anya ukuwa
yarinyar nan bata da iskoki?( g
67
AWIYTA WADA ISA- ‘YAR ALJANNÀ CH
Yau birkice gobe ta koma daidai.
Haka nan ta yi ta tarairayarsa tana
kula da shi, har lokacin baccinsu.
Yau kam har bisa shimfidarsu, ta
bashi mamaki domin abubuwan da ta yi
masa bata tabayi masa ba irinsu ba,
wannan ya sanya ya kwana cikin farin ciki
marar misaltuwa."
Washegari da safe hatta ruwan
wankansa itace ta hada masa, sai da ta kai
masa wajen shiryawa sannan ta nufi tebur
ta hada masa abincin da zai karya. Shi
kansa tamkar a mafarki yake kallonsa
abin."
Haka ta yi ta kula da shi da
tarairayarsa har sai da ya tafi izuwa gun
aiki sannan ta dawo gida ta shiga kokarin
gyaran gidan da sauran ayyukan gida.
Da yamma ya shigo gidan cike da
zumudi, dadi ya sake kamashi domin tun
daga waje wani kamshi ya daki hancinsa a
68
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE2
cikin gidan kuwa tamkar komi na gidan
sabo aka sake don kyau, domin ta goge
komi ta kuma gyare komi sai daukar ido
yake yi.
Tana jin motsinsa ta fito da sauri
tana yi masa barka da zuwa, ita kanta ta yi
kyau tamkar wata 'yar tsana, sai daukar
ido take yi, dadi ya sake cikashi, bai san
sanda murmushi ya subuce masa ba yace
mata
"Ko ke fa Mero, yanzu don Allah da
haka kikeyi yaushe zamu dinga fada dake?
Lallai yanda kika gyara gidannan
tsaf, ki ka yi komi yanda na umarce ki,
gaskiya yau kin fiddani kunya, Allah ya yi
miki albarka, bari kawai na juya na shigo
da bakin domin tun dazu sun min waya
suna jirana."
Bai saurari amsarta ba kawai ya juya
ya fice, ita kuwa binsa kawai ta yi da kallo
tana murmushi.
69
AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE2
Bayan 'yan mintuna ne suka shigo
tare da abokan nasa, su uku dukkansu cikin
fara'a suka yi sallama suka shigo.
Mero ta amsa musu gami da yi musu
barka da zuwa, cike da zolaya Umar yace
mata "Amarya kinsha Kamshi."
Ahmad ya amshe da sauri yace mata
"Amarya kuma? Ai yanzu ta zama uwargida, ka sani ma ko har an samo
kyautar daki?"
Shehu ne ya amshe da cewar "Nima
dai abin da nake so nace kenan ka rigani,
ka san yanzu tamkar tuntube ake dashi a
bakin kofar daki."
Gaba daya suka yi dariya, Alhaji
Sadik ya dubeta ya ce mata " kina ji suna yi maki tsiya amma kinyi shiru? Baki da
amsar da zaki basu?"
Da sauri ta mike ta nufi hanyar daki
tana fadin "To me zance?"
70
AWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNA CE-2
Alhaji sadik ya bita da kallo yana
fadin "Ya kike tafiya daki ne baki sauki
bakin ba?
Juyowa kawai ta yi tana nuna wajen
da tebur yake ta ce masa "Ai ni na gama
saukar baki, komi yana bisa tebur.
"Tana gama fadin haka ta shige cikin
daki."
Bai ce komi ba illa mikewa da ya yi
ya nufi kan teburin yana fadin "Ku taso
mana kuci irin girkin amarya."
Kai tsaye suka mike suka nufi kan
teburin suka zauna suna sauraron a basu
abin da za su ci din."
Alhaji ne ya hau bude kwanikan da
ka jera don ya taimaka musu wajen zuba
abincin.
"Sai me?
Ga mamakinsa kowanne kwano ya
bude sai ya ga danyen abinci ba dafaffe
ba, na farkon danyar shinkafa ce a ciki, na
71
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE 2
biyun kuma kayan miya ne danyu aka jera
a ciki, hakan dai duka sauran kwanukan
suka Kunsa.
Nan take hankalin Aliyu ya tashi, idanuwansaaa suka rune suka yi jawur, su
kuwa abokan nasa ta sjii kawai suka yi
daya bayan daya suka yi masa sallama cike da mamakin abin da Mero ta aikata,
suka fice.
Ko sallamar ta su bai iya amsaea ba, illa kwalawa Mero kira da ya yi cikin 6acin rai da tsananin bacin rai, kai tsaye
dakin nata ya nufa domin ba zai iya jira ta fitoo ba sabida tsabar 6acin rai da takaici.
Zaune bisa gado ya taddata idonsa a
rufe ya hau fadin "Wai ke Mero wacce irin dakikiya ce ne? ki rasa sanda zaki tozarta
ni sai a gaban abokanaina? Yan zu ni ban
isa ki dafa mini abin da zanci a gidana ba?
Sannan idan na kawo baki suma
haka? Ban isa ki fiddani kunya ba? Sannan
72
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ» 2
karin takaici da bakin ciki da tozarci wai
sai ki zuba danyen abinci cikin kwanuka,
ni kam wallahi na gaji da wannan auren
naki, na yi dana sanin auren domin ba
komi a cikinsa sai 6acin rai da tozarci."
Muryarsaa rike ya karasa maganar.
Ita kuwa yatsina fuska kawai ta yi ta
ce masa "Haba Alhaji menene na wannan
ta da jijiyar wuya haka.
Na sha gaya maka wallahi ba zan iya
girki ba, na ji ma da larurar da take jikina,
ko kamshin abinci na ji amai nake yi,
kuma kaine ka jawo, don haka ni wallahi
ba zan iya ba."
Kansa ya dafe kawai sabida takaici,
ya koma falo ya zauna cike da tashin
hankali, kansa na sunkuye yana zubda
zazzafan hawaye, cikin ransa yana fadin
"Wacce irin masifa na daukowa kaina har
cikin gidana?
73
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Kuma na kashe kudina da kaina na
dauko abin da zai aur
Hawayen nasa ne suka karu, nan
yaci gaba da tunane-tunane barkatai har ya
nemi hawayen ya rasa. Don haka ya tashi
ya nufi dakinsa yana ambaton Innalillahi
wa inna ilaihirraji'un, da haka bacci ya
dauke shi.
****
Washegari da sassafe ya fice kai
tsaye gidansu ya wuce, yaci sa'a ya
sameshi a kofar gidansu bisa dakali yana
zaune.61
zeDa sauri ya taso ya tareshi kan
dakalin suka koma suka zauna, bayan sun gaisa ne Alhaji Sadik ya fara dacewa
"Nasan za ka yi mamakin ganina yan zu?
Auwalu ya ce "Babu mamaki nasan
halin rayuwa ai, wani abin zai iya taso
74
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
mutum ba tare da shiri ba, kuma bahaushe
ya ce labarin zuciya a tambayi fuska, tunda
na ganka fuskarka ta bani labarin halin da
kake ciki."
Alhaji Sadik ya yi gyaran murya
sannan ya ce, "Wato Auwalu na rasa ta
inda zan bullowa lamarin yarinyar nan
domin wulakancin da ta yi mini da
tozarcin da ta yi mini a jiya a gaban
abokaina gaskiya ba zan iya dauka ba
Auwalu, ina ganin gara na hakura da ita
kawai, na kaddara kawai ban dace da aure
ba, don haka zan saketa kawai..."
Da sauri Auwalu ya katseshi da
fadin "Haba abokina kar ka yarda zuciya
ta yaudareka ka aikata abin da ba shikenan
ba. Jiya da na dawo da daddare Ahamad ya
gaya min duk yanda aka yi to amma abin
da yasa banyi maka magana ba sabida
nasan kana cikin 6acin rai, sai na kyaleka
sai ka huce tukunna.
75
AWIYYA WADA ISA-"YAR ALJANNА СЕ 2
Ka yi hakuri abokina wallahi na fika
tashin hankali da 6acin rai domin nine na
kawo Mero. Yanzu abin da nake so da kai
ka daure ka janye maganar saki domin
yanzu mutane na jin ka saketa ba kowa ya
san matsalarku ba sai ace kudi yasa kake
so ka fara auri saki, ko kuma dama so kake
ka yi auren dandano kawai, ni kuma bana
so a sanyaka a baki domin baki bashi da
dadi."
Cike da damuwa Alhaji Sadik ya ce
"To ya kake so nayi Auwalu? Tunda na
auri yarinyar nan ban huta ba, sai na zauna
99 neman kudi bai bani matsala sai mace.
Auwalu ya gyada kai ya се,
"Hakane, amma nafi so ka sauya matakin
da ka ka shirin dauka, amma ba wannan
ba."
Alhaji Sadik cikin sanyin jiki yace
"To ina sauraronka bani shawarar matakin
da zan dauka?
76
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Auwalu ya nisa sannan ya ce, "Ai
shawara bata wuce ka kara aure ba domin
ina tabbatar maka duk tsiyar da take ji ko
take takama da ita, daga zarar ta ji zaka
auro wata to daga sannan zata shiga taita
".yinta وو
Alhaji Sadik cikin rashin gamsuwa
da shawarar Auwalu ya ce, "Haba Auwalu
wannan kuma wacce irin shawara ce? Na
yi auren ban huta ba, kuma sannan na
karowa kaina wata? So kake su sanya mini
hawan jinin da ban shirya ba.
Auwalu ya dan yi murmushin yake
yace "Ba haka bane abokina, ai duk wanda
ya san lagon mata, da zarar ya ga matarsa
zata bashi matsala to sai kawai ya laluba
ya samoo wacce ta fita hankali ya uaro, shi
kenan sai kaji shiru ta shiga taita yinta ta
koma gasar yanda za ta zama tauraruwa a
tsakanin su biyun."
77
AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE 2
Alhaji Sadik ya gyada kai sannan
yace. "Ka gwada mana ka gani abokina,
musamman da mahaifiyarka ke goyon
bayan Mero bata son laifinta kuma yanzu
ka je kace zaka saketa, ko ka saketa, kai
kanka kasan akwai rikici ba karami ba,
amma idan kace aure zaka yi ba wanda zai
hanaka domin Allah ma ya baka damar ka yi."
Da alamun maganganun Auwalun
sun fara ratsashi don haka ya danyi
murmushi sannan yace "Ka zo da shawara
mai kyau fa abokina, amma kuma sai na
duba ta sosai sanan zan yanke hukunci, in
har na ga zata bulle mini to Insha Allah
zanbita domin wallahi sai na rama
takaicin da Mero ta hadani da shi."
Auwalu ya yi faffadan murmushi
sannan ya сe, "Kо kai fa abokina, kuma
ina tabbatar maka wallahisromon da ke
78
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
cikin hada mata biyu sai ka yi sannan zaka
bani labari da kanka."
Mikewa ya yi yana dariya yana fadın
"Allah ko abokina."
Shima Auwalun mikewa ya yi yana
fadin "Allah kuwa abokina kaje dai ka yi
tunani, ni nasan insha Allah za a dace.
Da haka suka yi sallama da juna,
Alhaji Sadik ya tafi gun aikinsa cike da
tunani akan shawarar da Auwalu ya ba shi.
Zaune take a falo bisa kujera cikinta
ya fara girma, yana daga cikin daki ya jiyo
wayarsa na kara, da sauri ya fito ya nufi
kan teburin da ke gaban kujera, a daidai
lokacin da Mero ke shirin sanya hannu ta
dauka ne ya ture hannunta da sauri ya
dauke wayarsa, yana ganin sunan da ke
79
a
AWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA СЕ- 2
jikin wayar ne ya danna ya hau amsa wayar.
Cike da zumudi yake fadin "Hello ai
ina nan tafe insha Allah yanzu nake shirin
fitowa daga gida Insha Allah."
Kashe wayar ya yi ya nufi cikin
daki ya sanyo wata hadaddiyar shadda sai
kyalli take yi da daukar ido, takalminsa da
hularsa har agogonsa kalar zaren da aka
dinka shaddar ne, sai tashin kamshi yake yi.
Tana nan zaune ya zo ya wuce, ta
taho da sauri zata sha gabansa tana fadin.
Malam ni fa bangane ba wai ina
kake shirin zuwa ne haka?
N a kula yanzu ka tsiri wani sabon
salo na yin kwalliya ka fita da daddare sai
sanda kaga dama sannan ka dawo."
Bai san sanda dariya ta subuce masa
ba ya ce "To sai me don kin gane hakan?
1
80
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE-2
Zamanki nake yi da zan zauna ba zan fita
ba sai sanda kika bani izini?
Kema da kike zamana ni ne na ajiye
ki ba kya tambaya ta neman izini na idan
zaki fita, ballantana ni da babu wanda ya.
ajiyeni?"
Wani irin takaici ne ya turnike ta
don haka da sauri ta nufi bakin kofar ta
babbake tana fadin "To wallahi nima ba
zan zauna ni kadai ba, haka kawai 'yar
jira ka maida ni.?"
Dariya ya sake yi yace mata "Ai
kuwa zaki yi jiran nan domin dama da shi
aka sanki, banda abinki Mero ai mace ta
zaman gida ce dama."
Bai jira amsarta ba ya sanya hannu
ya janyeta daga jikin kofar ya hadeta da
jikinsa ya sumbaçe ta cikin kunnenta ya ce
mata "Sai na dawo kinji ki kula da kanki."
Ya bude kofar ya fice sannan ya rufe
mata kofar.
81
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СE 2
Ita kuwa durkusawa kawai ta yi anan
tana faman zubda hawaye domin da
alamun harsashenta na nemman tabbatuwa
ya zama gaskiya.
A kofar gidansu ya yi parking ya
kirawota a waya bayan 'yan mintuna ta
fito cike da yauki take takawa kamar ba
zata taka kasa ba, tana matukar burgeshi
da daukar hankalinsa domin ta iya
kwalliya matuka, kuma kwalliyar na
daukar jikinta komi na ta das-das tamkar a
jikin nata aka kirkireshi.
Da zazzakar muryarta ta yi masa
barka da zuwa, tuni ta tafi da tunaninsa,
firgigit ya yi ya amsa mata sannan ya bude
motar ya fito.
Idanuwansa kyar bisa kanta ya се
mata "Komi naki birgeni yake Halima
kullum kara kyau kike yi tamkar wata 'yar
fulawa."
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Maganganunsa sun birgeta don haka
ta yi dariya sannan ta ce, masa "Kai kuma
fa gaka nan ka yi kyau kamar wani
basarake amma baka ganin naka kyan sai
na wani?"
Gaba dayansu suka yi dariya, Alhaji
Sadik ya nisa sannan yace mata "Kinga
hukuncin Allah ko Sadiya? Karamar
magana na neman zama babba."
Sadiya ta yi dariya ta ce, masa
"Wacce karamar maganar ce ke nema ta
zama babba Alhaji?"
Alhaji ya yi murmushi yace mata
"Tamu mana ni da ke Sadiya, kamar yau
muka haďu ga shi soyayya mai karfi na
Kara kulluwa a tsakaninmu.
Cike da yauki ta dago idanuwa ta
dubeshi sannan ta ce, "Muka hadu kuma?
Ai ni kawai ganinka na yi kazo zance
gidan mu, mma ban san a ina ka sanni ba
koma ka ganni."
83
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Dariya kawai yayi sannan yace "kin
tuna wata ranar asabar da karfe biyar na
la'asar kika je wani super market kika yi
siyayya?"
Jim ta yi alamar tana tunano lokacin,
sannan daga baya tayyi dariya ta ce, "Haka
ne na tuna, kana kufin anan ka taba
ganina?"
Alhaji Sadik ya gyada kai yace
"Kwarai da gaske anan nayi tozali da
wannan kyakkyawar fuskar sai kawai na ji
kin tafi dukkan tunanina da hankalina, don
haka sai kawai na saita motata na biyo
adaidaita sahun da kika hau, har gidanku,
sai da kika shiga cikin gidanku sannan na
juya.
Tun daga wannan rana na fara shirya
ranar zuwa zance, gashi kuma cikin yardar
Allah na samu karbuwa."
Kanta na kasa ta yi dariya amma ba
ta ce komi ba.
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Wata tambayar ya sake watso mata
"Kin san wani abu kuwa Sadiya?
Ta gyada kai ta ce, "A'a sai ka fadi."
Murmushi ya yi sannan yace "Ni fa
kinsan ana gani na a kofar gidansu yarinya
to aure ne ya kawo ni, don haka tun yanzu
ki fara shirin zama amarya, kuma ki fara
sanarwa a gidanku.
Cike da mamaki ta zaro idanuwa,
amma bata iya cewa komi ba, shi kuwa
gogan girgiza kai yayi alamar jaddada abin
da ya fadı sannan yace mata "I da gaske
nake, don ba zan bari ai min sakiyar da ba
ruwa ba, kuma kinsan na sanar da ke ina
da mata ko?
Ko dai ba kya son mai mata ne ya yi
miki tsufa?"
Da sauri ta gyada kai ta ce, masa
"A'a wallahi ai tun sanda ka gaya mini ma
ni bani da wata damuwa a kai kowa ai da
habarsa zai yi tagumi, ko Innata ma da na
85
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE-2
gaya mata cewa ta yi ita tafison hakan
domin mai mata yafi rikon aure.
Dariyar farin ciki ce ta subuce masa
ya ce "Alhamdulillah haka nake sonki
Sadiya, shi yasa nake jin kaunarki ta yi
yawa cikin raina domin ina da yakinim
zaki kawo mini farin ciki a rayuwata,
wannan dalilin kuma ya sanya na ji ina
Kaunar Innarki dari bisa dari."
Dariya kawai ta yi ta sunkuyar da kai
tana wasa da yatsunta, shi kuwa gogan
bandir din kudi ya dauko har biyu ya mika
mata yana fadin "Gashi ki kaiwa Inna
daya, daya kuma na kine ki kara siyen
kayan kwalliya don na dinga ganinta
kullum kala kala a jikinki.
Ta risina ta amsa tana godiya ya
katseta da fadin