"To ni zan koma amma fa
ki sanarr a gidanku cewar a satinnan zan
aiko ayi maganar aurenmu domin da,
domin da sassafe ake kama fara."
68
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA E 2
Zaro ido ta yi cike da mamaki da
tsoro, amma sai ta kasa cewa komi kawai
ta sunkyar da kanta.
Alhaji ya dubeta da kulawa yace
mata "Sadiya ko baki amince da aurena b
ne?
Gara ki sanar da ni kar nayi zurfi na
zo na shiga wani hali sakamakon
rasaki."cikin sanyin jiki yake maganar.
Tausayinsa ne ta ji ya mamayeta,
Kaunarsa ta karu cikin ranta ta dubi kudin
da ke hannunta sannan ta tuno irin hidimar
da ya yi mata daga haduwarsu zuwa yanzu
don haka cikin sanyin murya ta ce masa
"Ba wani abu, Allah yasa hakan ya zama
alkahiri a garemu baki daya."
Wani dadi ne ya cika zuciyarsa
tamkar ya hadiyeta haka ya ji, cike da
zumudi ya ce mata "Ina godiya matuka
Sadiya bari na je sai munyi waya insha
Allah."
87
AWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE2
Idanuwanta ta dago suka yi ido
hudu, da ido ta amsa masa sallamar tasa,
sannan ta juya ta nufi gida, tuni ta kashe
masa jikinsa kasa motsi ya yi har sai da ta
6acewa ganinsa sannan ya lallaba ya shiga
motar ya tadata ya tafi.
Ita kuwa Sadiya tana shiga gida ta
tadda Innarta tana zaune bisa tabarma a
tsakar gida tana sauraron Radio, don haka
ta nufeta da sauri ta fada bisa cinyarta cike
da murna.
Innar tata ta yi saurin dago ta tana
fadin "Ke lafiya kika fado jikina haka me
ya faru?"
Cike da zumudi ta ce, mata "Inna ki
kashe Radio nan don Allah ki ji labari mai
dadi, wanda ya zarce na Radion da kike
sauraro.1
Da sauri ta kashe Radion ta ce, mata
"To me ya faru gaya mini mana.
88
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Bandir din kudi guda biyu ta dora
mata bisa cinyarta tana zare ido ta dauki
kudin tana juyawa, sannan ta ce mata "Ke
waye ya baki wannan kudin haka tamkar a
mafarki?
Domin ni dai har zuwa yau ban taba
rike irinsu ba, haka mahaifinki har ya bar
duniya bai taba taba kamarsu ba."
Dariya ce ta subuce mata sannan ta
ce, "Inna Alhajin ne dai da yake zuwa
yana bani kudinnan kina cewa ke
hankalinki ya na kansa? To shine ya bani
wannan makudan kudin, sannan kuma
yace na fadi a gidanmu zai turo Iyayensa."
Zaro idanuwa ta yi cike da mamaki
hadi da murna ta ce, "Dagaske kike
Sadiya?
Wannan fa shine tsuntsu daga sama
gashasshe, lallai Allah ya kashe ya bamu,
shiyasa duk da bani da hali nake kokarin
na tsara miki kwalliya domin kina da
89
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СЕ- 2
kyawun sura, masu yi dani cewar ina yin
abin da yafi karfina yanzu zasu gane inda
na dosa, domin dama burina mu samu mu
rabu da wannan talaucin da ya addabe mu
tunda muka fara rayuwa."
Hannunta ta daga sama tana fadin
"Allah nagode maka da ka cika mini
burina."
Sadiya ce ta katseta da fadin "To
Inna idan ya tambayeni maganar aikowa
me zan ce masa?"
Da sauri ta amsa da mata da cewar
"Kice masa an bashi kawai, tana sake juya kudin."
Da mamaki ta amsa mata da cewar
"An bashi kuma, kuma tun bai turo ba?
Innar ta ce, "Bari ke dai Sadiya kice
wallahi kudi ne suka rudani, ki ce ya turo
da gaggawa.'
Sadiya ta yi dariya ta ce, "Kai Inna
ki kwantar da hankalinki ki samu nutsuwa,
90
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE-2
ceniada zan shiga gidansa ma gaba daya, ai
kudi har sai kin gaji da rikesu. Insha
Allah."SO
іv в Dа sauri ta rungume Sadiya tana
fadin"Allah kuwa Halimatu, haihuwar
maierana shiyasa bahaushe ya ce ko kana
igudu haifi ka yar, Allah ya nuna mini
wannan rana Halimatu."
so sy isSadiya ta amsa da "Amin Inna,
sannan ta mike ta nufi cikin daki. Ita kuwa
sbInnar nan ta zauna tana ta juya kudin tana
al'ajabi ko kirgasu ma ta kasa yi
oballantana ta san nawa ne, ita dai tasan sun
samu kudin da dasu yanke musii talauci
iss insy sb nereb i sls erianay аH зикs
Tsugune yake a gabanta kansa na
skasa yana sauraron hukuncin da ta yanke
enmasa kan batun aurensa, bayan ya je ya
sanar da ita cewar zai yi auren, cike da
919
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
babbar murya take kara jaddada masa
cewar.
"Ina kara jaddada maka ban yarda ka
yiwa Mero kishiya ba, har yaushe aka yi
auren da har zaka fara jajibe-jajibе?
Wato ąbin da nake gudun shi ke
bibiyata ko? Shawarar abokai ita kafi
fifitawa fiye da komi.
Cike da ladabi ya girgiza kai ya ce
"Ba haka bane Hajiya, mai daki shi yasan
inda yake masa yoyo, ni nasan halin da
nake ciki....
Da sauri ta katseshi da fadin "Yoyo?
Ta ina dakin yake yoyo?
Yarinya mai kirki mai girmama mu
da kaunarmu, ita ce zaka ce tana bata
maka? Har yaushe aka yi daren da gari zai
waye?"
Bude baki yayi zai yi magana, amma
Hajiya ta hanashi da fadin "Bana son na
92
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNА СЕ- 2
kara jin komi ni dai na riga na yanke
hukunci kawai."
Tana kaiwa nan ta mike ta bar shi a
nan zaune, cike da kunar rai da nadama.
Ya dauki lokaci a haka sannan ya
mike ya fita jiki a sanyaye sam babu
kuzari da kyar yake iya daga kafarsa ya
fice waje, a soron gidan wayarsa ta hau
kara ya duba Auwalu ne don haka ya daga
wayar cikin rashin kuzari yace "Daga
gurin Hajiya nake yanzu domin tuni na
fuskanci an kai mata gulmar batun aurena
don haka kawai na sanar da ita, amma ina
gaya mata ta ce ita sam bata wannan
zancen ba, in dai tana raye bata yarda na
yiwa Mero kishiya ba.
A firgice Auwalu yace masa "Haba
dai, ita Hajiya bata san me ake ciki ba ne?
Alhaji Sadik yace "Yaushe ta bari
ma aka gaya mata halin da ake ciki, tana
93
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE-2
goyan bayan Mero, wai har ta zabi Mero
fiye da dan da ta haifa.
Kasan wani abu Auwalu? Wallahi in
har ta hanani auren nan to sai na saki Mero
kuma sai na hakura da aure a duniya har
abada, ai ni na kawo Meron sannan har
suka ganta suke sonta ko?"
Cikin rashin jin dadi Auwalu yace
"A'a abokina kar ka yi haka, ka dai lallaba
har a samu ta amince ka san Iyaye abin
lallabawa ne.
Alhaji Sadik ya amsa masa da cewar
"Auwalu ka kyaleni kawai na riga na kai
makura a 6acin rai zaka jí labarin abin da
zai faru."
Yana kaiwa nan ya kashe wayar ya
fice daga soron ya nufi motarsa ya tasheta,
da karfi ya tada kura ya wuce.
Ita kuwa Ramla tana labe a soron
tana jin wayar da Sadik din ke yi don kala
94
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СЕ-2
da gudu ta nufi cikin gidan gurin Hajiya ta
isa, bisa kujera ta taddata.
Hajiya ta yatsina fuska ta ce, "Ke
kuma lafiya zaki shigo mini da gudu
haka?"
Ramla tana haki ta ce mata "Hajiya
don Allah ki kyale Yaya Sadik ya yi
aurensa, wallahi yanzu na ji shi a soro
yana waya da abokinsa yana cewa "In har
baki barshi ya yi auren nan ba to sai ya
saki Anti Mero kuma ba zai kara auren ba.
Ciki ne da ita Hajiya idan ya sake ta
a haka ai ya cuceta.
A rude Hajiya ta ce, "Saki kuma?
Au wato bai ji abin da na gaya masa ba zai
bula mini kasa a ido kenan ko? Abin da
nake ji yana faruwa a gari nima shine zai
faru a kaina kenan, yanda 'ya'ya ke
bijirewa iyayensu akan mace, ni ma an
jajibo mini wacce zata rabani da dana?"
95
AWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE- 2
Ramla ta ce mata "Hajiya ba haka ba
ne, babu fa haramci a aure, ya kamata ki yi
hakuri ki daure ki barshi ya auri wacce
yake so, idan fa ya saki Mero za a fara
yadamu a gari ne ana cewa muna auri saki.
Sai da ta yi dogon tunani sannan ta
nisa ta ce mata "Ni abin da ma yafi daga
mini hankali kenan, ace dana ya yi saki,
sannan kuma yace babu shi babu aure ai ya
jawo mini abin fada a duniya."
Ramla ta amshe da cewa "Kuma
Hajiaya kin dai san halin Yaya Sadik, yana
da biyayya sosai da hakuri amma fa idan
aka kaishi bango to ko wanne hukunci ya
ga damar dauka yyake yi don haka ki yi
gaggawar nemo shi kar ya je ya saki 'yar
mutane da ciki."
A rude Hajiya ta ce, "To kiyi sauri ki
kirawo shi mana."
Ramla ta ce,"Hajiya ya riga ya shiga mota
ya tafi, sai dai ki nemeshi waya.
96
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ 2
Da sauri ta lalubo wayarta ta mikawa
Ramla ta na fadin "Ungo lalubo mini shi ki
99 ce maza ya zo yanzu ina nemansa.
Ramla ta ce "Haba Hajiya wanne
irin kina nemansa ai an sa lokaci, ki се
وو kawai kin amsa maganar aurensa.
Hajiyar ta ce, "Kirawo shi to mana.
Sai da ta yi ringin ta katse bai daga ba, don
haka ta kara kiransa ringing biyu ana uku
ya daga, ta yi saurin mikawa Hajiyar ta се
"Gashi ya daga."
Da sauri ta karba ta ce masa "Kana
ina ne?" bai iya ce mata koli ba illa shiru
da yayi kawai.
Bata ji haushin shirun nasa ba illa da sauri
ta sake ce masa "Ba wani abu kar ka damu
na amince da aurenka, Allah ya sa ya zame
mana alkairi.
Tamkar a mafarki yake ji haka ya I
maganar Hajiyar tasu, sama ta ka, wani
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
dadi ya cikashi, bai san sanda ya ce mata
"DaKI
UI gaske Hajiya kin amince?" Bima
Gashi kuwa na gaya maka? Ni dai
fatana kada ka wulakanta uwargidanka."
Da sauri ya ce mata “Hajiya nagode
matuka, Insha Allah ba zan wulakanta
Mero ba."
Bai ko saurari me ta sake cewa ba, nob sd
sai kawai ya kashe wayar, cikc da zumudi
ya nufi gurin Auwalu domin su fara tsara,
yanda komi zai kasance."egsb sy ules
****
unine alii sd ilol stem eс svi ind "Son ani
iswsx ivBy sD
Yana zaune a falonsa ne yana kallon FURA SD 1 50 TIBI, OETI Mero K taKSL shigo gU tana takawa a hankali
sakamakon cikin da ke jikinta. A bisa
kujera ta je ta zauna. BAEM
Ta gefen ido ya dubeta sannan yace
mata "Wato ke Mero ba da aiki sai kai
Karata ko? To a wannan on dai hakanki
98
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Da sauri ta lalubo wayarta ta mikawa
Ramla ta na fadin "Ungo lalubo mini shi ki
99 ce maza ya zo yanzu ina nemansa.
Ramla ta ce "Haba Hajiya wanne
irin kina nemansa ai an sa lokaci, ki cсе
kawai kin amsa maganar aurensa.
Hajiyar ta ce, "Kirawo shi to mana.
Sai da ta yi ringin ta katse bai daga ba, don
haka ta kara kiransa ringing biyu ana uku
ya daga, ta yi saurin mikawa Hajiyar ta ce
"Gashi ya daga."
Da sauri ta karba ta ce masa "Kana
ina ne?" bai iya ce mata koli ba ilfa shiru
da yayi kawai.
Bata ji haushin shirun nasa ba illa da sauri
ta sake ce masa "Ba wani abu kar ka damu
na amince da aurenka, Allah ya sa ya zame
mana alkairi."
Tamkar a mafarki yake ji haka ya I
maganar Hajiyar tasu, sama ta ka, wani
97
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE-2
dadi ya cikashi, bai san sanda ya ce mata
"Da gaske Hajiya kin amince?" вістей
Gashi kuwa na gaya maka? Ni dai
fatana kada ka wulakanta uwargidanka."
Da sauri ya ce mata "Hajiya nagode
matuka, Insha Allah ba zan wulakanta
Mero ba."
Bai ko saurari me ta sake cewa ba,
sai kawai ya kashe wayar, cike da zumudi
ya nufi gurin Auwalu domin su fara tsara
yanda komi zai kasance."
****
Yana zaune a falonsa ne yana kallon
TIBI, MeroKH taROL shigo tana takawa a hankali
sakamakon
25
cikin da ke jikinta. A bisa
kujera ta je ta zauna.
Ta gefen ido ya dubeta sannan yace
mata "Wato ke Mero ba. da aiki sai kai Karata ko? To a wannanon dai hakanki
98
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA СЕ- 2
bai cimma ruwa ba, domin aure sai na yi
shi babu fashi."
Nan take ranta ya baci ta yatsine
fuska, cike da takaici ta ce masa "Ni kake
gayawa aure ba fashi Alhaji? Wannan ai
cin fuska ne ka dinga gaya mini azncen
aurenka kiri-kiri."
Dariya ce ta subuce masa sannan
yace mata "Af to in ban gaya miki da
kalmar ba wa zai gaya miki? Kuma
menene ya yi kama da cin fuska a ciki?
Ni da zan aikata halak ba haram ba.
Kema da kike cin mutuncin aurenki, an
hakura da ke, ballantana ni da babu sabon
Ubangijina a tattare da abin da zai aikata."
Cike da takaici Mero ta ce, "Af haka
ma kace ? shi kenan ni kuma wallahi ba
zanci gaba da zama da kai ba, in har zaka
auro mini wata a gidannan, har yaushe ka
auroni da har zaka ce zaka kawo mini
wata?
99
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE-2
Tana gama fadin hakan ta fashe da
kuka, shi kuwa Alhaji ko ajikinsa cewa ma
ya yi mata "Ki je duk inda zaki je mana ga
hanya nan mana ai a share tas babu kuma
wanda ya hanaki tafiya tunda haka zaki
zabarwa kanki."
Kukan nata ne ya karu, ta mike ta
nufi dakin baccinta.
Bayan 'yan mintuna ne ta fito da
mayafinta lilli6e bisa kanta hannunta rike
da Trolly tana turawa ta zo ta wuce ta
gabansa ta fice.
Shi kuwa bai ki tanka mata ba, illa
cikin zuciyarsa da yace "Ki je duniya zata
koya miki hankali."
Kai tsaye gidansu ta wuce ta shiga
da sallama tana janye da Trolly, a tsakar
gida ta iske mahaifanta zaune bisa
tabarma, a gefensu kuma kyandir ne ke
haskaka tsakar gidan sakamakon rashin
wutar da ake fama da shi.
100
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Ta yi musu sallama suka amsa mata
sanyaye, itama sam babu kuzari a jikinta
ta samu guri ta rakuбе.
Baba Kande ce cikin mamaki ta се
"Ke lafiya kika zo mana da wannan daren
kuma har da akwati?
Sannan baki ce komi ba kin samu
guri kawai kin zauna.
Cikin shasshekar kuka take fadin
"Shi shine...ya ce..wai na taho gida.!
A rude Baba Kande ta ce "Ki tahi
gida kuma ina shedar fadin hakan?"
Baba Idi ya katseta da sauri yace
"Dakata Kande kada ki rude, muna
sauraronki me ya faru ya ce ki taho gida,
ko'sakinki ya yi ko kuwa?"
"A 'a wai aure zai yi shine yace' ni
na taho gidanmu." Cikin kamannin rashin
gaskiya take maganar.
Baba Idi ya kara cewa "Sai ya baki
takarda yace ya sake ki?"
101
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
"A'a bai bani takarda ba, bai ce ya
sake ni ba."
Baba Idi yayi murmushin yake yace
"Towo na gane, kishi ne ya sanya kika ga
ba zaki iya zama a gidan ba sabida za a
auro wata shine kika fito daga dakinki
ko?"
A tsorace ta ce, "A'a Baba wallahi ni
ba haja ba.......
A fusace Baba Idi ya ce mata "Rufe
mini baki munafuka, kina nufin bamu san
duk wainar da kike toyawa ba ne a gidan
naki, idan kin boye mana wani ai wani
abin muna sane da shi, amma abin da yasa
muka sanya miki ido mun san akwai ranar
da zaki yi gangancin cewa ba ba ri ki baro
dakinki gashi kuwa tazo, to ina tabbatar
miki wallahi ba a gidana ba."
Yana kaiwa nan ya mike a fusace ya
dauko muciya ya nufi inda take. Da gudu
ta tashi ta nufi waje tana kuka, da sauri ya
102
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
bita har waje ya korata sannan ya jefe mata
trolly dinta yana fadin "Idan na sake ganin
kafarki a gidannan wallahi sai na nakasta
ki, ya juyoo kofar gidansa ya rufe.
Baba Kande ce ta zo ta iske shi tana
fadin "Maigida wai korarta ka yi?
A fusace Baba Idi ya ce mata
"korarta na yi mana, haba Kande, ki duba
kiga halin da muke ciki a gidannan, in an
samu abin da za aci yau gobe haka za a
wuni, tunda Allah yasa suka yi aure da
yaron nan shi kenan muka yi sallama da
wannan Kaka ni ka yin, shine kuma yanzu
kwatsam sai ta dauko jiki ta taho gida, ta
zo ta zauna mu koma 'yar gidan jiya."
Baba Kande ra rangwadar da kai ta
ce, "To ai maigida wai sabida dare da an
وو barta ta kwana gobe sai a mai da ta."
e A fusace yace mata "A gidana?
Allah ya tsareni da kwana da mai yaji a
gidana, wacce irin nasiha ce ban yiwa
103
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
t
yarinyar nan ba, lokacin da za a kaita,
amma duk ta saka kafa ta shure, to wallahi
ba zan haifi da yafi karfina ba, ta je bayan
duniya ma karewa amma ba a gidana ba."
Haka nan dole Baba Kande ta hakura
ta kyaleshi domin ta san ita kanta idan ta
matsa akan maganar zai iya saba mata, don
haka dole tabi shi kan hukuncin da ya
yanke amma cikin ranta tana jimamin halin r.
da diyar tata zata shiga cikin wannan daren d
duk da dai tasan Meron bata kyauta ba,
n
kuma tasan halin mahaifin nata.
a
n
d
Haka ta kwanta cike da jimami har
sai da bacci barawo ya zo ya dauke ta.
d
m
di
ta
Kai tsaye gidansu Salama ta wuce,
gidan ya kasance gidan haya ne mai
dakuna rututu da mutane rututu.
104
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
bita har waje ya korata sannan ya jefe mata
trolly dinta yana fadin "Idan na sake ganin
kafarki a gidannan wallahi sai na nakasta
ki, ya juyoo kofar gidansa ya rufe.
Baba Kande ce ta zo ta iske shi tana
fadin "Maigida wai korarta ka yi?"
A fusace Baba Idi ya ce mata
"korarta na yi mana, haba Kande, ki duba
kiga halin da muke ciki a gidannan, in an
samu, abin da za aci yau gobe haka za a
wuni, tunda Allah yasa suka yi aure da
yaron nan shi kenan muka yi sallama da
wannan. Kaka ni ka yin, shine kuma yanzu
kwatsam sai ta dauko jiki ta taho gida, ta
zo ta zauna mu koma 'yar gidan jiya.
Baba Kande ra rangwadar da kai ta
ce, "To ai maigida wai sabida dare da an
barta ta kwana gobe sai a mai da ta."
A fusace yace mata "A gidana?
Allah ya tsareni da kwana da mai yaji a
gidana, wacce irin nasiha ce ban yiwa
103
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE2
yarinyar nan ba, lokacin da za a kaita,
amma duk ta saka kafa ta shure, to wallahi
ba zan haifi da yafi karfina ba, ta je bayan
duniya ma karewa amma ba a gidana ba."
Haka nan dole Baba Kande ta hakura
ta kyaleshi domin ta san ita kanta idan ta
matsa akan maganar zai iya saba mata, don
haka dole tabi shi kan hukuncin da ya
yanke amma cikin ranta tana jimamin halin
da diyar tata zata shiga cikin wannan daren
duk da dai tasan Meron bata kyauta ba,
kuma tasan halin mahaifin nata.
Haka ta kwanta cike da jimami har
sai da bacci barawo ya zo ya dauke ta.
****
Kai tsaye gidansu Salama ta wuce,
gidan ya kasance gidan haya ne mai
dakuna rututu da mutane rututu.
104
AWIYYA WA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Datsdama ta shiga, sannan ta nufi
kofar dakn Salama. A zaune ta taddata
バイ
bisa tabarn tana sauraron Radio, ta kunna
aci bal bal wacce ta sanyata a gefen inda
take zaune
Та сазо da sauri cike da mamaki ta
ce, "Kamaf muryar Mero nake ji da
wannan daren?"
Cikin sanyin jiki da rashin kuzari
Mero ta ce Nice Salama.'
Da sauri ta gyara zamanta ta ce,
"Lafiya Mero kike tafe yanzu me kuma ya
faru?
Bata iva ce mata komi ba illa kukan
da ta sake fashewa da shi, sai da ta
numfasa sanman ta ce, "Wai Alhaji ne zai
yi aure, shine nace ni ba zan zauna da
kishiya ba, shine yace to na tafi duk inda
zani, naje gida Baba ya koroni." Kuka ya
kara dawo mata.
105
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Wani dadi ta ji cikin ranta, farin ciki
ya mamayeta amma a fili sai ta nuna
damuwarta matuka, rungumeta ta yi tana
rarrashinta tana fadin "Bana so ki dinga
bata hawayenki Mero, yanzu akan wannan
kike kuka?
Ki kwantar da hakalin in dai dani a
duniya ba zaki tozarta ba Mero, ki zo mu
zauna anan dama su Inna sun tafi kauye,
insha Allah da kansa zai zo yana magiya
akan ki koma gidansa kina ja masa aji.
Ta hau share hawayen da ke bin
idonta, cikin muryar kuka ta ce, "Alhaji ba
zai zo ba Salama, ba irin mazan da kike
nufi ba ne."
Salama ta ce mata "To ki sa ido
mana ki gani, ai mu kowa yaci tuwo damu
miya ya sha, wallahi namiji bai isa ya
wulakanta mu ba komin taurin kansa ko a
mutanen farko ya fito."
106
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Mero ta hau murza idanuwa da
alamun gamsuwa da maganar Salama
sannan ta ce, "Nagode Salama Allah ya
kara zumunci."
Dariya kawai ta yi sannan ta ce, "Ai
ba komi Mero ciwon 'ya mace ai na 'ya
mace ne, taso mu shiga ciki. Ba tare da ta
ce komi ba ta bi bayanta.
Ta daukar mata Trolly din kayanta ta
shigo mata da ita dakin.
Sai me? Tana ganin cikin dakin
gabanta ya fadi domin ba komi a ciki sai
shimfidar tabarma sai 'yan kayan
amfaninsu gefe guda kuma jakar Ghana
must go ce inda suke zuba kayansu na
sakawa.
A zatonta ta zaci izuwa yanzu
Salama yanzu ta gyara dakin nasu domin
ta dauki tsayin lokaci bata zo gidansu
Salama ba, ashe yana nan a yanda yake.
107
1
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNА СЕ 2
Sai da ta ajiye akwatin sannan ta
3 gyara shimfidar tabarmar ta dauko wani
C
yagulallen zanin gado ta shimfida mata
I
"Ga shimfida nan na yi miki Mero sai ki
E
1
kwanta anan don ni a waje nake kwana
saboda zafi."
Gabanta ya sake faduwa ta kalli
C
2
i
a
1
2
n
n
n
W
n
C
shimfidar ta sake duban dakin cikin ranta
ta ce, "Yan zu nan zan kwana? Tuni
tunaninta yayi nisan kiwo ya dawo mata da
hoton lafiyayyen dakinta da lintsimemen
gadonta, ba zafi ba duhu balle sauro domin
ko ba wuta Alhaji ka'ida ne zai kunna
inji..."
Sallama ce ta katseta daga dogon
tunanin ta ce, "wai har yanzu tunani ki ke
yi ne?"
Mero ta gyada kai ta ce, "A'a ba
tunani nake yi ba na dai gaji ne kawai."
Salama ta ce "To ki kwanta ki huta
mana Allah ya bamu alkairi."
108
AWIYYA WADA 18A 'YAR ALJANNA CE2
Bata tsaya ta sake sauraronta ba ta
fice ta nnufi makwancinta.
Ita kuwa Mero kasa bacci ta yi sam,
domin ji ta yi kamar akan Raya take
kwance jikinta duka ciwo yake yi domin ta
manta iyakar shekarun rabon da ta kwanta
a kasa, ga sauro tamkar kuda ga kuma zafi
gumi sai kwaranya yake a jikinta kamar an
kwara mata ruwa.
Ta shi kawai ta yi ta zauna tana
hawaye domin sam baccin ba zai tabа
yiwuwa ba.
Haka ta kwana tana kuka da takaicin
rabuwa da dakinta sai da asuba ta yi
sannan ta samu ta dan runtsa sakamakon
sanyin asuba da ya dan busa, shimma ba
wani baccin kirki ta yi ba, kwaramniyar
gidan ta tashe ta, domin sarakan sammako
ne matuka.
Shi kwa bangaren Alhaji Sadik
hidimar aurensa ce kawai a gaban sa, suna
109
AWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE-2
1
t
t
1
3
1
i
t
t
6) zaund a falo shida Auwalu suna tattaunawa
ga saitinan akwantina a gabansu guda
ugoma sha biyu.
Auwalu ne ya dubeshi cikeda
5J mamaki yace, "gaskiya mutumina ka
hbirgeni ka tabbata namiji, gwarzo ma
kuwa, wato duk wannan rikicin bai sa ka
s kaja da baya ba ko ka saurara, wannan irin
kaya da ka shirgo na alfarma haka? Kana ji
Gruda Sadiyar nan gaskiya.
söst isx Alhaji Sadik ya yi dariya ya ce masa
"To kai da me kake nufi? UWIY
micisist Nace na fasa? Ai me hanani wannan
iv auren sai ubangijin da ya halicceni.uds
пожвтDariya ya yi sannan ya ce masa
sd Amma dai ka yi hakuri ka je bikon Mero,
16yko don albarkar juna biyun da take dauke
olida shi."s
Da sauri ya girgiza kai gami da 6ata
ibfuska ya ce "Ni naje? Sai dai idan wani
snaka sake mai irin sunana amma ba dai ni n
110
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE 2
ba, ai dain an je biko na kara bata lasisin ci
gaba da abin da take yi, amma yanzu idan
ta dandana zaman gidansu sai ta banbance
tsakanin gidansu da gidan aurenta wanne
ne yafi?
Ni bata san tafiyar ta ma kamar an
yaye mini takaici ba, musamman idan ina
tareda Sadiya ina kallon kyakkyawar
surarta, ba abin da nake doki illa na ga an
kawo mini Sadiya cikin gidana."
Girgiza kai kawai ya yi domin abin
ya girmameshi, cike da sallama yace
"lallai abokina ka yi nisa na kula akan
fushinka kake har yanzu don haka zanje na
samu Hajiya in yaso da yawunta sai ni naje
bikon."
Da sauri ya katseshi gami da nuna
shi da yatsa "A'a kar ma ka soma abokina
domin a gidan namu ma nayi kashedin
cewa kada a sake a je bikon Mero, duk
kuwa wanda ya je to in ta dawo zata zauna
111
AWITYA WADA ISA- YAR ALJANNA CE2
a karkashinsa amma ba dai ni ba, a kyaleta sai saida ta horu da kanta ta dawo."
Auwalu ya gyada kai cikin sanyin jiki ya ce "To shi kenan Allah ya zaba abin
da yafi alkairi, yanzu wannan kayan yaushe za a kaisu?"
Da sauri ya amsa "Gobe ne fa, na
gaya mata, dama abin da yasa na dan ja lokaci sabida itama Meron zan yi mata kayan lefen kuma banyi niyyar banbanta
komi a tsakaninsu ba, to sai Allah ya hutar
dani ta tafi gidansu."
Alhaji Sadik cike da fara'a ya amsa da ameen, sannan ya mike yana fadin
"Yanzu tasowa za ka yi mu dauki kayan
mi kaisu gidan Hajiya, abin da babu mu
bata kudi su karasa kasan mata da bidi'a to
kaga mun huta sai gobe kawai mu basu
motoci su tafi."
112
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Bai ce komi ba illa mikewa da ya yi
ya fara daukar akwatunan shima din Sadik
din dauka ya yi suka nufi mota.
Sai da suka kwashesu tas sannan ya
rufe gidan ya tada motar suka fice.
A bangaren Mero kuwa izuwa yanzu
ta samu kwanaki a gidansu Salama, ita
kadai ta san irin azabtuwar da take yi a
gidan har ma ta fara sabawa.
Wata safiya ce ta tashi fa sassafe
domin izuwa yanzu itama ta fara sabawa
da sammakon da mutanen gidan suke yi,
abinka da mai ciki fitsari ne ya cika mata
mara ya kulleta kamar ya zubo don haka
da sauri ta dauki buta ta nufi bandaki, sai
me?
113
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Layine dogo wajen mutum goma
tsaye maza da mata kowa na jira a zo
kansa ya shiga.
Nan take hankalinta ya tashi, ga shi
ta matsu matuka, ta rasa yanda zata yi don
haka ta koma daki tana matse-matse.
A dakin ta tadda Salama tana yatsina
saboda matsuwar