zumudi ya ce mata "zanyi miki
kyakkyawan tanadi kuwa, bari na fita don
kada na makara."
28
AWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNA CE 2
Cikin yauki ta mike ta bi bayansa, ta
raka shi har gurin mota, sai da ta ga tashinsa
sannan ta dawo gida ta zauna a falo tana
kallon talabijin.
Karar kwankwasa kofa ta ji, don haka
ta tabbatar tana da bako ta tashi da sauri ta
bude, suka yi ido biyu da ita, cike da farin
ciki suka rungume juna sannan suka nufi
kujera suka zauna.
Mero ce ta dubeta cike da murna ta cс,
"Yar halak kin ki ambato yan zunnan na
gama zancenki cikin raina har ina tunanin
buga miki waya, ashe kina tafe.."
Salama ta yi murmushi tana sake kallon
hadadden lafiyayyen falon ranta na yi mata
kuna, amma a zahiri babu alamu ta ce mata
"Uhum ina tafe amarya kin san ba yanda za
ayi yau ta wuce ban zo ba, na dai bari ne mai
gidan ya fita kin san hirarmu ba za ta yi dadi
ba idan yana nan."
Da dariya Mero ta mike ta nufi firij
tana fadin "Gaskiya ne kawata ba sakewa
kam."
29
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Salama ta bita da kalloo ranta ya biya
matuka da matsayin da ya kai Mero, ta hadiyi
yawu mukut mai hade da takaici sannan ta
dake.
Mero ta dauko lemon kwali da kofi ta
kawo ta ajiye bisa teburin da ke gaban
kujerun ta bude ta zuba mata sannan ta
fuskanceta ta ce mata "Ga lemo nan ki
sanyaya makoshinki don na ga kamar yau ana
zafi-zafi."
Salama ta gyada kai ta ce "Nagode
amarya, kinsha kamshi ina angon naki?" ta
watso mata tambayar daidai lokacin da take
kurbar ruwan lemon.
Mero ta yi dariya ta amsa mata "Ango
yana nan sumul ya fita gurin aiki, wai ana
sauke masa wasu kaya don haka dole ne ya je,
ba don haka ba ma ai a gida zaki same shi."
Cike da mamaki Salama ta dubeta ta cе
mata "A gida kuma? A lallai ciniki ya fada
kenan, na ga sai wani rawar kai kike yi wa
mijin."
30
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
Mero ta kwabe baki ta cc mata "Haba
dai wanne irin ciniki kuma? Ba sai anga'haja ciniki yake fadawa ba? Idan kuma ba a gani
ba fa?"
Mero ta yi dariya sannan ta ce mata
"To kwana gida daya ai ba kwana daki ba ne,
kamar yanda kike kwana a gidanki ni kuma
na kwana a nan gidan to haka muka kwana a
gida, dayan yana Katsina ina Daura."
Dadi ne ya cika zuciyar Salama a rude
ta ce mata "Allah da gaske kawata? Ta cc,
"Wallahi."
Da sauri ta rungumeyta suka yi shewa,
tana fadin "Amma kin burgeni kawata haka
nake sonki mai daukar shawara, lallai kina so
ki yi daraja a gurin miji, ki sa ido ki gani
kullum sai ya zamo mai dokinki domin abin
da baka samunsa ko yaushc ka fi
marmarinsa."
Mero ta yi dariya suka sake tafawa, ta
ce mata "Ai kuwa baki ga yanda ya rude ba,
amma dai yau nayi masa alkawarin zan bashi
mamaki."
31
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Salama ta yi dariya ta ce mata "To ai
sai bada himmar bayar da mamakin, ni ai na fi
son kullum ki bashi mamakin kinji kawata."
Suka sake yin dariya suka tafa suka ci
gaba da tattaunawarsu da hira irin ta aminai
har yamma sannan Mero ta yi shirin tafiya.
Bayan sunyi Sallama Mero ta juyo
zuwa gidan ta sake kiranta ta ce mata "Kar fa
ki manta ki bada mamakin nan kamar yanda
kika yi alkawari.
Dariya suka yi gaba dayansu Mero ta
cc "Kar ki damu kawata zaki sha labarin
yanda ta kasance, cike da jin dadi suka yi
sallama suna kewar juna, ta nufii gidansu, ita
kuma ta koma cikin gidanta ta kulle.
Wata irin hadaddiyar kwalliya taci
cikin riga da siket da suka fiddo da surarta
sukai mata kyau ga wani kamshi mai daukar
hankali na tashi daga cikin jikinta, fuskarta ta
yi kyau matuka, ta kama gashin kanta ta
matse shi da rubon ta saki sauran a baya.
Tana zaune a falo tana kallon Tibi ya
shigo ya taddata, da sauri ta mike tana yi
32
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
masa barka da zuwa ta amshi ledójin da ke
rike a hannunsa ta nufi kan teburin abinci da
su,
Kamshinta ya doki hancinsa ya bita da
kallo wani dadi ne da farin ciki suka
mamayeshi, cike da kulawa ya sake dubanta
suka yi dio biyu cikin tausasa murya ya се
mata "Amarya kinsha kamshi, irin wannan
kwalliya haka mai daukar hankali, ga kamshi
na ta shi ta ko ina, gaskiya kin matukar
faranta mini zuciyata."
Wani dadi ta ji cikin ranta domin yabon
da ya yi mata, ta saki murmushin jin dadi ta
ce masa "Ai duka nayi ne domin na faranta
maka maigidana.""
Maganar tata ta matukar bashi mamaki
don haka cikin mamakin ya bude baki ya ce
mata "Masha Allah ko yanzu na fara ganin
kadan daga mamakin da kika yi alkawarin
zaki bani."
Dariya kawai ta yi ta sunkuyar da kai,
shi kuwa gogan idanuwansa na kan ta da
alamaun yana raya wani abu cikin ransa.
33
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Dakinsa ya wuce yana fadin "Bari 'na
na je na watsa ruwa na yi sallah sai na zo
muci abincin ko?"
Bai tsaya ya saurari me zata ce ba
kawai ya wuce cikin dakin ya cire kayansa ya
nufi bandaki ya fara wanka.
Sanda ta shiga fakin tuni har yayi nisa
a fara wankansa don haka ta bude durowa ta
zabo masa wata sassaukar jallabiya ta dauko
turare ta feshe masa ita da shi, nan take dakin
dukkansu ya hau wani kamshi mai daukar
hankali.
Sai da ya kammala sannan ya fito ya
taddata zaune bisa bakin gadon tana tsumayin
fitowarsa, hakan ba karamin dadi yayi masa
ba, don haka cike da fara'a a fuskarsa ya
dubeta da kulawa ya ce mata "Allah yayi miki
albarka Maryama kina ji dani matuka, irin
wannan kulawa haka?"
Dariya kawai ta yi sannan ta dauko
jallabiyyar ta mika masa, karba kawai yayi ya
sanya bai iya cewa komi ba domin ta kai
matuka a bashi mamaki, kai tsaye bai tsaya
34
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
6ata lokaci ba ya hau bisa abin sallah ya tada
sallah.
Tare suka fito daga dakin kowannc a
cikinsu fuskarsa cike da walwala da farin ciki,
kai tsayc kan teburin abinci suka wucc.
Farfesun kayan ciki ne da miyar Kaza
da kuma shinkafa da taliya sai hadadden salat
da kabeji.
Tana budewa kamshi ya doki hancinsa,
nan take yawunsa ya tsinke sai da ta gama
zuba masa ta mika masa sannan ta zubawa
kanta.
Loma daya kawai yayi ya hau santi, ita
kuwa sai dariya take ta yi masa, sai suka
kammala cin abincin sannan ya umarceta da
ta bude ledojin nan ta kwashe kayan ciki ta
saka firij.
Ba tare da musu ba ta bi umarninsa,
kayan marmari ne irinsu Apple da Ayaba da
Lemo da Abarba da sauransu.
A falo ya taddata don haka yace mata
"Bari naje waje na siyo katin waya, sabida ba
35
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
kudi a wayata kuma kin san bana son kwana
ba kudi a waya saboda dare."
Ta yi murmushi ta ce masa "To sai ka
dawo, Allah ya tsare." Ya amsa da "Amin."
Ya fice.
Ita kuwa tunda ya fita maganganun ke
dawo mata cikin kwanyarta musamman
gargadinta na karshe don haka da sauri ta
mike ta nufi cikin dakinta ta kulle kofar ta
cire mukullin.
Tana jin shigowarsa amma ko da wasa
ba ta gwada fitowa ba, ya hau duba ko ina bai
ganta ba sai kawai ya samu guri ua zauna
abinsa yana jiran ya ga ta inda zata fito.
Yana,nan zaune har ya gaji da jira don
haka ya tashi ya nufi dakin yana kwala mata
kira, ko motsinta bai ji ba don haka ya murda
kofar dakin zai shiga ya ga ko me ke faruwa,
ga mamakinsa kofar ba zata budu ba, domin
an kulleta da mukulli, ya sake murda kofar
jaro na biyu amma sam taki buduwa sai
kawai ya buga kofar dakin cike da takaici da
36
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
kunar rai amma har yanzu dai shiru babu ko
motsi.
Wata zuciyar ce ta bashi shawarar ya
lcka ta taga, don haka kai tsaye ya nufi tagar
yana fadin "Mero! Mero!! Ki bude mini
dakin mana na dawo fa, idan wasa kikeyi don
Allah ki daina, ki bude mini, ki tuna fa
alkawarin da kika yi min na yau ya dace ki
zamo mai cika alkawari a matsayinki na
cikakkiyar musulma musamman akan
mijinki."
Cike da kasala ya karasa maganar.
Ga mamakinsa sai kawai ta zo ta saki
labulen tagar ta zuge glass din tagar ta ciki.
Wani irin mamaki ne ya cikashi don
haka kawai, ya saki baki yana kallon tagar
cike da takaici idanuwansa sun kada sunyi
jawur tamkar zai zubda hawaye sabida
takaici.
Bai iya yin wani cikakken motsi ba illa
wuccwa da ya yi cikin dakinsa sam babu
sauran kwari a jikinsa tamkar wani dan giya
san tangadı yake yi.
37
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE-2
Yana isa kan gado ya fada a kai tamkar
bugagge, idanuwansa sunyi jawur kamar
garwashi, silin din dakin kawai ya zubawa
idanuwa, wata kwallah mai matukar zafi ta
fito daga cikin idanuwansa, haka nan ya yi ta
juyi bisa gado tamkar wanda ya shekara yana
bacci, hakika ba don bacci karfinsa ya kai
karfi ba da bai isa ya daukeshi ba amma a
hakan ya fi karfinsa ya yi awon gaba dashi.
****
Washegari bai ko saurari tashunta ba
domin izuwa yanzu baya kaunar ganinta ma
domin ganin nata kara yi masa fami yake yi
kan bakin cikin da take kunsa masa don haka
ya fice da wuri ya bar mata gidan.
A restaurant ya tsaya ya karya sannan
ya wuce ofishinsa duk da yau akwai saukin
aiki amma yafi bukatar ya kasance aofishin
nasa don yafi sámun saukin bacin rai fiye da
gidansa.
TE
38
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Sai yamma sannan ya fito daga ofishin
kai tsaye ya saita motarsa zuwa majalisar da
sukan zauna da abokansa don yin hira.
Suna zaune a majalisar suna karta, ya
iso ya same su. A gefe ya ajiye motar sannan
ya nufi inda suke aiune ya yi musu sallama,
Auwalu na zaune cikinsu suka dakata da
kartar suka amsa masa cike da zolaya suna
fadin "Ango ka sha kamshi, shi kenan kuma
sai ka bace ko gaisuwar babu?"
Dariyar yake yayi ya amsa musu da
cewa "To so kuke yi na dawo ina zama a
cikinku bayan ni Allah ya suturtamin. Zaman
majalisa ai sai mai kwanan zaure."
Gaba daya suka yi dariya, Auwalu ne
yace "Mu ma dai mun kusa yin auren nan a
dainyi mana gori.
Sadik ne ya katseshi da fadin "Kai
cakwaikwaiwa gurinka fa nazo kar ka dameni
da surutu, taso muje akwai maganar da
zamuyi da kai."
Ba tare da ya ce komai ba ya ajiye
kartar yana murmushi ya bi bayansa sai da
39
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
suka je har jikin motarsa suka jingina da
motar suka fuskanci juna.
Auwalu ya dubeshi yace masa "Ya akai
ne ango dafatan dai alheri ne ya same mu mai
tarin yawa."
Fuskarsa ba yabo ba fallasa ya amsa
masa "To lafiyar kenan, Auwalu ka san irin
yarinyar da ka hadani da ita kuwa?
Gabansa ya fadi cike da rudewa ya yi
saurin tambayarsa "Kamar yaya Sadik har ka
sanya gabana ya fadi, me ya faru Sadik daga
yin aure yau kwana biyu?"
Cike da damuwa ya bashi amsar "meye
ma bai faru ba Auwalu?yarinyar nan ta maidani tamkar wani dan aiken gidanta
amfanina a gurinta kawai na fita na nemoo
sannan kuma nai mata bauta na kawo mata
taci ta sha ta zauna cikin ni'ima, amma ni
idan dare ya yi sai ta rufe mini kofa ta barni
na kwana a falo? Tamkar wanii baran gida, ina cikin damuwa matuka Auwalu.
Innalillahi wa innah ilaihirraji'un ya
fara amfata sannan yaci gaba "Alhaji bani da
40
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE2
maasaniya akan wannan halayyar tata, domin
wallahi ni na sani iyayenta mutanen ne, kuma
sunyi mattarbiyya, ban san kuma a inda ta
samo wannan mummunan dabi'ar ba."
Sadik ya yi ajiyar zuciya sannan yace
"Wannan shine abin da na dinga jin tsoro da
yin aure shiyasa na baka wuka da nama don
ka samar mini mace ta gari, gashi nan ina
neman yin gudun gara zai haikewa zago.
Auwalu ya ja dogon numfashi sannan
yace"Hakane amma inaso ka kwantar da
hankalinka abokina, wannan ba zai taba zama
matsala ba Insha Allah matso kaji yanda zaka
yi duk ka magance wannan matsalar, in tasan
wata ai bata san wata ba."
Ya matsa kusa da shi ya yi masa rada a
kunne, yana gamawa suka dubi juna suka yi
dariya, cike da fara'a Sadik yace masa "Allah
abokina haka za ayi.
Auwalu yayi dariya yace masa "Wallai
kuwa abokina kaje kaa gwada ka gani lokacі
daya zaka yi maganin iskancinta da ka sameta
41
1
S
t
i
n
in
fa
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE
lokaci daya kuwa ka gama da ita karyarta ta
gama karewa, sai kazo ka bani labari."
Alhaji Sadik cikin fara'a yace masa
"To kai shiru da bakinka kawai, bari naje na
kammala abubuwan da ke gabana don na
koma gidan akan kari."
Bai saurari amsar sa ba yayi saurin
bude motar ya shiga ya tadata, Auwalu na yi
masa sallama, shi kuwa daga masa hannu
kawai ya yi ya wuce ya barshi a nan tsaye.
Kamar yanda ta saba tarbarshi kullum
yau din ma hakan ta yi masa sannu da
zuwanta kawai ya amsa, sannan kai tsaye ya
wuce dakinn barcinsu, sai da ya kammala
komi a dakin sannan ya sanya rigar bacci
marar nauyi.
Sam babu walwala a fuskarsa, bisa
bakin gado ya zauna, ya dubi Mero yace mata
"Ki zubo min Kaza da kuma Lemo shikenan
abin da nake bukata ci yau.
Da sauri ta mike tana fadin "An gama
ranka ya dade. Ya dubeta yace "Sai kacc
42
AWIYYA WADA ISA- YAR ALJANNA CE
gaskc da a gaban wani nc sai yace ai biyayya
kike yi mini sau da kafa."
Kasa ce mata komi ta yi illa wucewa da
ta yi ta nufi falo don cika umarninsa.
Sai da ya kammala cin abincin sannan
yatashiyacbshiga bandaki don wanke
hannunsa da bakinsa. Ita kuwa sai ta kwashe
kwanukan ta kaisu kitchen, sannan ta ta dawo
dakinta sam babu kuzari a tare da ita.
Tana ganinsa ya wuce kofar dakin
tamkar fita zai yi, sai kawai taga ya janyo
kofar dakin ya kulleta da mukulli, ya juyo da
mukullin a hannunsa.
Gabanta he ya fadimatukar faduwa
dama ta kula akwai abin da yake shirya yi
mata, shi kuwa ko kallonta bai yi ba, kan wata
kujera kawai ya nufa ya zauna. sollel sgnil
Ita kuwa can kuryar gado ta nufa ta
kwanta jikinta a kankamė ta tákure, kallonta
kawai yayi dariya ta subuce masa amma -bai
bari ta bayyana ba. a sur
A
43
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
Sai da ya dan dauki lokaci sannan ya
taso ya nufi inda take yana fadin "Mero kenan
yau dabarar taki ta kare kenan?
Bata iya ce masa komi ba illa sakc
takurcwa da ta yi ta kankame jikinta, sannan
ta janyo bargon da ke kusa da ita ta sake
Kudunduncwa ciki, bai san sanda dariya ta
subuce masa ba.
A bakin gadon ya zauna yana shirin yin
magana ta ce, masa "Ka fita ka bani guri
Alhaji, wai shin ma me kake nema a gurina ne
da har kake mini wannan bibiyar?"
Dariyar mugunta ya saki sannan ya
matsa inda take yana fadin "Mero kenan, to
ke da kina zaton na aureki ne kawai tamkar
wata flawa abar ado da zan jerata a gidana na
dinga kallonta kawai don ta kawata mini
gidan?"
A hankali ya fara janye abin da ta rufa
da shi, yana sake matsawa kusa da ita, ita
kuma tana sake ja da bayaa, da haka dai har
ya cimma burinsa a kanta tukunna ya kyalcta,
44
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
P
tun tana hawaye har ma ta nemi hawayen ta
rasa.
A haka Mero ta kwana cikin takaici.
Shi kuwa gogan ko ajikinsa domin sautin
munsharinsa kawai take ji yana fita daidai da
alamun baccin na matukar yi masa dadi,
tamkar ta dookeshi haka take ji cikin ranta
musamman ita da baccin ya kaurace mata.
Washegari Alhaji Sadik ya tashi cikin
walwala da jin dadi, kai tsaye bandaki ya
wuce ya yi wanka, sannan ya fito.
Ita kuwa Mero ta kasa ko da motsi sai
faman zubda hawaye take yi.
Bai ko kula da kukanta ba illa shiryawa
da yaci gaba da yi, sai da ua kammala shirinsa
tsaf sannan tukunna ya koma ga Mero, cike
da walwala ya dubeta ya ajiye ambulan a
gabanta yace mata "Wannan kyautarki се
Mero ta kasancewarki kamilalliyar mace,
nagode Allah ya bamu zuriya dayyiba."
Wani irin takaicii ne ya turnuko mata
cikin zuciyarta, da sauri ta wurgo ambulan zin
cike da kunar rai, kukanta ya karu tana fadin
45
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE 2
"Dauke tsiyarka bana so me zaka gaya mini
bayan ka riga ka 6ata mini tsarin rayuwata."
Har ya nufi hanyar fita dariyata suбисе
masa ya juyo ya kalleta yana fadin "Mero
kenan, to ke da wai a gidanku ba a sanar dake
menene aurc ba ne? To idan baki sani ba
99 wannan shine aure.
Yana gama fadin haka ya juya ya ficc
ya barta a nan.
Takaicinta ya sake karuwa, ta yi kwafa,
sannan cikin muryar takaici t ace, "Ba komai
in kasan wata ai baka san wata ba.
Shi kuwa Alhaji Habu kai tsaye
motarsa ya nufa, daga kallon fuskarsa kasan
ya koshi da farin ciki, har wani kuzari yake ji
na musamman, ya bude kofar motar ya shiga
ya tada ta cike da kuzari ya fice daga gidan.
Wayarsa ce ta fara ringin dan haka ya
dauko ya duba fuskar wayar murmushi yayi
ya danna gurin amsawa ya sanya a kunnensa
ya ce "Abokina an tashi lafiya?"
uwat riuse ebstisAicus nikic
46
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
"Lafiya kalau abokina, ya nakc jin
karar tafiya kamar kana hanya wai kana
nufiin har ka fito ne?"
Alhaji Sadik yayi dariya yace "Na fito
mana abokina, ai kasan lokacin fita ta ya yi,
musamman kuma yau wata babbar ran ace a
gareni domin ina cikin walwla da nishadi.
Auwalu ya yi dariya ya ce masa "To fa!
Abokina ko dai an dace ne?
Alhaji Sadik ya sake yin dariya yace
massa "Tun yaushe ma abokina, ai wannan
tarihin ya wuce sai dai wani kuma sabo kai
dai kawai sai mun hadu abokina."
Dadi ya cika Auwalu yace "To ai ni
abokina na fika murna. Allah yasa daga yau
damuwa ta kare."
Sadik ya amsa da "Amin abokina' sai
anjima kasan bana son ina tuki ina waya.
Suka yi sallama suka ajiye wayar.
Kai tsaye gidansu ya wuce domin
gaishe da Hajiyarsa.
Zaune ya taddata a falo tana kallo, ya shigo da sallama, cike da fara'a ta amsa masa,
47
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CЕ-2
ya risuna ya gaisheta sannan ya zauna a
kujerar da ke fuskar tata.
Cike da kulawa ta sake duban dan nata
ta cc masa "Dafatan dai kuna lafiya ba wata
matsala?"
Shima cike da fara'a ya amsa mata
"Lafiya kalau muke Hajiya.
Cike da gamsuwa ta amsa sannan ta ci
gaba da cewa "To dama inaso na gargadeka,
ka rike matarka da kyau, kada ka yarda a
zigaka akan matarka, mutane yanzu ba so
suke Allah ya rufa maka asiri ba, dole kuma
sai hada da hakuri, domin yarinya ce, shi
99 kuma dama aure rabinsa hakuri ne.
Gyada kansa kawai yayi ya ce mata
"Insha Allahu zan kiyaye Hajiya.
Hannunsa ya sanya a aljihu ya dauko
kudi ya mika mata sannan ya mike ya yi mata
sallama.
Cike da jin dadi ta amsa tana yi masa
fatan alheri da addu'ar Allah ya sake tsareshi
yayi masa albarka.
48
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE-2
Ya amsa da amin sannan ya fice ya nufi
gurin aikinsa. Ko a can gurin aikin yau kowa
ya fahimci Alhaji yana cikin walwala matuka,
har rabon kudı ya yiwa kananan
ma'aikatansa.
A bangaren Mero kuwa said a ta ji
ciwon jiki ya ishcta sannan ta tashi ta lallaба
ta nufi bandaki, sai da ta samu ruwa mai dumi
ta gasa jikinta da shi sosai sannan ta dan ji
dama dama, bayan ta idar da sallah ne kuma
ta hada shayi mai dumi sannan ta hada da
maganin ciwon jiki da paracetamol ta sha,
duk wannan abin da take yi kuma cikin ranta
tana jin takaicin abin da ya faru da itane,
musamman idan ta tuna da hudubar Salama.
Wata zuciyar ce ta dinga zigata akan ta
duba ambulan din da Alhaji ya bata, don haka
ta dauko ta buda dan taga menene a ciki?.
Da mamakinta sarka ce ta gwal
dankareriya kirar dubai 'yar kwance, wata
irin kara ta yi sabida murna da farin ciki,
domin a rayuwarta tana matukar kaunar
sarkar gwal musamman kirar dubai, don haka
49
AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE-2
ta yi ta murna tana gwada sarkar, tuni ma ta
riga ta manta da wani ciwon jiki ko wani
6acin raid a Aliyun ya haddasa mata.
A gajiye tikis ya dawo daga gurin aiki,
don haka kawai bisa kujera ya fada sabida
tsabar gajiya, tsawon lokaci bai ji ko motsin
Mero ba don haka ya hau kwala mata kira.
Bata ko amsa ba illa fitowa da ta yi
tana faman dacin rai, a gabansa ta tsaya
kerere babu ko risinawa.
Dubanta kawai ya yi tana faman girgiza
tana bata rai ta ce masa "Wai ba kiji
shigowata ba ne Mero?
Na dawo a gajiye memakon ki zo ki
tarbeni sai kuma ki zamanki a daki?"
Kwabe baki ta yi tana faman girgiza
tana bata rai ta ce masa "Shi kenan dama
dalilin da yasa ka kira ni? Ka katse mini
hutun da nake cikin daki na? to idan na ji
shigowar ta ka sai kuma me? Me zan maka?"
50
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Da mamaki ya sake dubanta ransa na yi
masa kuna ya ce mata "Bangane sai me ba?
A matsayina na mijinki ba zaki zo ki
bani hakkina ba, ki bani ruwa da abincin da
zanci, sai kawai ki kyaleni, kuma na yi
magana kice wai sai me?"
Kada kai ta yi ta ce masa "Ruwa da
abinci?" Tabdijan, ni wallahi ban girka ba, ai
abin sai yai min yawa, ni komi nice zan maka
sai kace wata baiwarka?
Kuma ai kaine ka zabi abin da ka fi so
a tare dani, tunda ka samu ai sai ka nemi mai
tarairayarka in ka dawo da kuma dafa maka
abinci ko? Ammaba dai ni ba."
Tuni zuciyarsa ta ciko da takaici da
kunar rai, cikin bacin rai yace mata "Haka
kika ce ko Mero?"
Juyawa kawai ta yi ta girgiza jiki tana
fadin "Zancen kakeso, ni ka ga tafiyata, in
zaka nemi mai dafa maka abinci ka nema
domin ni abin ya min yawa.
Tana kaiwa nan zata shige daki shi
kuwa dafe kai yayi kawai cike da takaici ya bi
51
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
ta da kallo, ya ma rasa me zai ce mata, bai
sakc bi ta kanta ba illa dauko Kazar da ya
shigo da ita da kayan marmari ya sanya su a
gaba yana ci tamkar magani sanbida tsabar
yunwar da yake ji, ga kuma takaici da ya
cunkushc masa zuciya.
Washegari haka ya fita babu ko
sauraron tsayawa karyawa domin 'yar mulkin
tasa bata ma ko tashi ba balle ya saka rai,
kuma ko ta tashi ma yasan ba zata damu da
bashi abin da zai karya din ba, don haka ya yi
wanka kawaiya shirya ya fice.
Ita kuwa Mero sai da ta yi baccinta mai
isarta sannan ta tashhi ta yi wanka ta shirya
tsaf, ta hada lafiyayyen shayinta hade da
soyayyen dankali da kwai, da kuma farfesun
kayan ciki ta zauna ta cika cikinta tsaf, sannan
ta hau bisa kan doguwar kujera ta kwanta tana
kallon Tibi.
Wayarta ta hau kara alamar kira ya
shigo, ta yi sauri dubawa, sunan Salama ne
akai don haka da sauri ta dauka cike da fara'a
ta ce "Salama kawata ya kike?
52
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Salama ta amsa da cewa "Lafiya kalau
nake kawata, gani nan zuwa gidanki daga nan
zan wuce kasuwa?
Da sauri ta amsa mata "To sai kin zo
ina sauraronki dama wallahi kewa ta ishcni ta
zama ni kadai babu abokin hira."
Dariya Salama ta yi ta ce mata "Gani
nan zuwa kawata na debe miki kewar, suka yi
dariya suka ajiye wayar.
Bayan mintina kadan Salama ta
bayyana a gidan Mero, kar kaso kaga murnar
da ta yi da zuwanta, nan take ta baibayeta da
kayan ci da sha iri-iri."
Sunyi hira mai dan tsawo, sannan
Salama ta ce mata "Dama ina sha'awar zuwa
kasuwar nan kawai don nayi kallo idan naga
abin saye kuma na siya zama guri daya ya
isheni wallahi."
Salama ta yi dariya sannan ta ce "To ki
zo mu wuce mana Mero menene a ciki?
Ni fa da kike ganina wallahi banga
abin da zai takura mini ya hanani yin abin da
nake so ba."
AWIYXA WADA ISA, TAR ALIANNASENа
Mero ta zaro idanuwa cike d tsoro ta
e mataA Salama ban Sanaida
maigidana ba, kinga kuwa banda damar fitaES
Salama ta kwaße baki tosaiki yi ta
zama ai ki zama daddawar daka mai doyini
kam banga namijin da zai tsareni a gida shi yà
dinga fita harkokinsa ba haka kawai wai da
sunan aure Tabdijan.Podob sn siswsl swuS SN
Mero ta gyada kai taceWallahi
Salama aure yana da takurawa, yanzu da dane
mayafina kawai zan dauka mu zaga duk inda
muke so ba fargaba balle tunani, amma yanzu
wai idan zaka fita ma sai ka nemi izinin wani
wannan abu yana kona mini rai ivnu2
Salama ta yi Isaki ta . Ni dadina
dake rashin ganewanewakitaso kiedauko
mayafinki, mu wuce kila ma har ma dawo k
ma huta a gidanki bai san kin fita ba, in kuma
kinga kina jin tsoro ne to sai kiyi ta zama ki
rube a cikin gida ni kinga lafiyata.orw um os
Mero na ganin haka sai ta mike tana
fadin "Bari na dauko mayafina sai mu tafi.
Da sauri ta nufi cikin dakinta."р ог эрн
54-
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CЕ 2
Nan fa Salama ta faki ido ta hau dagedagen matasan kujera a zatonta ko zata yi
arba da kudi, ai kuwa sai ta yi ido hudu da
yarin gwal, da sauri ta dauke ta jefa a jaka ta
hau gyaran matasan kujerar.
A daidai wannan lokacin ne Mero ta
fito daga dakinta da mayafi bisa kanta ta
sakale jaka a kafadarta, da sauri ta hau daga
matasan kujerar tana neman yarinta na gwal
wanda ta cire da zata kwanta a kan kujerar
don kar ya dameta, yanzu kuwa za ta saka ta
fita.
Salama ta yi kamar bata san me take
nema ba, ta ce mata "Mu tafi ko Mero kinsan
fa baki da isasshen lokaci."
Mero tana ci gaba da duba ta ce, mata
"Yarina na gwal na cire na sanya karkashin
kujerar nan shi nake nemma na sanya sai mu
tafi.
Salama ta bude baki da mamaki ta ce,
mata "Yari kuma? Kema banda abinki ai nan
ba wajen ajiye yari ba ne, yanzu haka