An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Sarauta Publishers
Yar Aljanna CeALAWIYYA WADA ISAH
AWIYYA WADA ISA 'YAR ALJANNA CE- 2
onyislise sb aabi alamd
eYARALJANNA CE 2
daya bangaren kuwa, tunda ta wdaina ganin kyalln motar su ta tsaya nan a soro cike da tunani,
cikin ranta take fadin "Gaskiya mutumin nan
ya burgeni matuka, na dade banga saurayi da
ya hada komi da ake bukata kamar wannan,
lallai Auwalu ya kawo mini babban Kifi.
Ta saki murmushin jin dadi wanda ya
ratsa zuciyarta da ruhinta, wata irin iska ta
daban ce ta ratsa ta, ta juya ta shiga gida don
kar wani ya shigo ya taddata.
seaKai tsaye alwala ta dauro ta hau kan
abin sallah tana dakon ta ji kiran sallah domin
lokacin yayi, can kasan ranta kuwa tunani
Sadik ne zokar cikin ranta ta dade tana ganin
maza kala-kala suna neman auren ta amma ba
ta ga wanda ya hada komi, kuma ya kwanta
mata a rai lokaci daya ba. 5M sb Kiran sallar da aka yi ne ya katse mata s UGIUsus KIKO
tunaninta, sai da aka kammala aka-tada salbab GE GIKG TDI B
sannan ta mike ta bi jam'i.
3
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE-2
Bayan sun kammala idar da sallah ne ta
koma kan aikinta na abinci wanda dama ita kc
yi da aka yi sallama da ita ne Babuita ta karba
taci gaba dayi.
Tana Kokarin kada miyar ne kamar
daga sama ta jiyo sallamar aminiyarta da sauri
ta juyo suka hada ido ta sakar mata murmushi
gami da fadin "Salama yanzu kike tafc?
Barka da zuwa, kamar kin san ina nemanki."
Salama ta yi dariya, ta ce mata "Ki сe
nazo a dai-dai, Allah ya sa dai babbar
samuwa ce.
Suka yi dariya sannan ta nufi inda
Babar Mero ke zaunc tana lazimi, ta durkusa
ta gaishcta, sannan ta nufi inda Mero take.
Da sauri ta ajiyc abin kadin ta rufe
tukunyar miyar sannan ta marci Salama da su
shiga daga cikin daki. Kan wasu kujeru
yagulallu da suka sha jiki suka zauna, suna
fuskantar juna cike da zumudi Salama ta ce
da Mero "Kawata bani labarin abin da ya faru
kike nemana, Allah yasa dai babbar karuwa
ce?" ta fadi cike da zolaya.
4
AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE-2
Mero ta yi dariya ta ce mata "Kc daí
bari kawata ai na yi babban kamu yau dinnan,
na samo zankafedc kuma mai hali, hatta
motar da ya zo a cikinta abar kallo ce, ga kudi
ga kyau ga kuma daukar wanka.
Nan take fuskar Salama ta sauya, ta
harareta da gefen ido gami da kwabe baki
ta ce, "Shine duk kika firgice haka akan
namiji?"
Mero ta yi saurin bata amsa "Haba
kawata ya ba zan firgice ba kuwa? Na
tabbata ko kece kika sami irinsa sai kin
ruďe."
Salama ta sake harararta sannan ta ce
"Haba Kawata kar ki zubda ajinki a gurin
namiji mana ki tuna fa ko ke wacece, ki
tuna yanda maza ke karakaina akanki,
amma yau kina nema ki firgice akan
mutum daya, gaskiya wannan ba girmanki
bane, kar dai ki manta halinsu, in suna son
su aureki tammkar su hadiyeki ko su sake
naki sai don so, amma da zarar sun sameki
5
AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE-2
bukatar su ta biya, to sai kuma wulakanci
da mugun hali ya bayyana.
Da alamun maganganun Salama sun
fara tasiri a gareta don haka jikinta
sanyaye ta ce mata "To ya kike ganin za
ayi Salama? Ko dai ma na sallame shi ne
kawai na huta tun ba ayi nisa ba."
Maganar kawar tata, ta yi mata dadi
cikin ranta dama da haka take samun
lagonta ta dinga sarrafata, don haka sai ta
6oye jin dadinta ta ce mata.
"A'a ni bance ki shareshi ba Mero,
amma ni dai shawara ce na baki ki rage
wannan zumudin, wallahi ina tabbatar
miki namiji ko aurensa kika yi ki iya
takunki da shi, in kuwa ba haka ba sai kin
koma abar tausayi a cikin jama'a. domin
yana gama cin Biredi zai yaga ledar ya
watsar a kwandon shara, ya barki da
takaici, shiyasa ni kin ganni nan tsakanina
da namiji sai dai na karbe abin hannunsa
6
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
na barshi da hamma amma ba dai nayi
zakwadi akansa ba."
Tana kaiwa nan zata mike tsaye tana
fadin "Kinga tafiya ta ina da abubuwa da
yawa da zanyi a gida kada na shantake
anan.
Itama Mero mikewa ta yi jikinta ya
gama yin sanyi ta ce mata "Shikenan
Salama na ji shawararki kuma Insha Allah
zanyi aiki daita BY ol
ollWani dadi ta ji cikin ranta, har dadin
ya bayyana kan fuskarta, cike da fara'a
tace mata "Yauwa Aminiyata shiyasa nake
sonki wallahi domin kina daukar
shawarata matuka."
Mero ta yi dariya, ta bi bayanta
sallama kawai ta yi da Baba da sauri ta fice
tana
233
fadin "Mero sai munyi waya.
Haka nan ta barta cikin tunani da
saka da warwara, ko ishasshen bacci ranar
bata samu ba domin abin ya zame mata
7
AWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE- 2
cankacakare, tana matukar jin kaunar
Sadik fiyc da komi cikin ranta amma kuma
hudubar Salama na yi mata yawo cikin
kwanyarta wacce ke neman yi mata tarnaki
a cikin tafiya.
Shi kuwa gogan bai zame ko ina ba
sai gidansu, a falo ya tadda Hajiya Saudc
zaunc ita da kanwarsa Ramla suna kallon
tibi.
Da sallama ya shiga suka amsa masa
cike da fara'a, kai tsaye ya nufi kujerar da
ke kusa da Hajiya ya zauna.
Bayan sun gaisa ne, Hajiya ta
dubeshi cike da damuwa tace masa "Wato
maganar auren nan dai da na yi maka ka sa
kafa ka shureta ko" na kula ko hira muke
yi idan na sako maganar auren sai kawai
8
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
ka bata rai ka tashi ka fice, wai me ke
damunka ne?"
Murmushi ya yi sannan da sauri yace
mata "Hajiya ki kwantar da hankalinki
dama can lokaci ne bai yi ba, to yanzu ina
mai sanar dake cewa na samo matar da zab
aura, a takice ma naje har gidansu mun
gana, don haka sai ki shirya ki bimu da
addu'a domir ba wani lokaci za a dauka ba
komai zai kasance.
Bata san sanda dariyar farin ciki ta
subuce mata ba, farin ciki bayyananne
akan fuskarta ta ce masa "Haba ko kaifa,
gaskiya yau ka faranta mini sosai, to ina yi
maka fatan alkaíri, Allah ya sa albarka ya
sa an dace da ta gari."
Da sauri Sadik ya amshe shima farin
ciki bayyane a fuskarsa "Amin, Hajiya."
Ramla ce ta matso kusa da shi cike
da zumudi ta ce masa "Yaya dafatan dai ka
9
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
dauko mana wacce ake ya yi kalar zamani
wacce zamu shiga ko ina da ita ba raini."
Gaba daya suka yi dariya Hajiya ta
ce mata "Kai Ramla baki da dama, wato
kenan kina layin masu cewa su dai fara ko
mayya ce ko?"
Suka sake yin dariya, Sadik ya mike
daga kujerar sannan yace wa Ramla, "Ki
kwantar da hankalinki Ramla idan na
koma zan dauko miki hotonta a waya sai
kiga irin zabin Yayan naki."
Suka yi dariya sannan yayi sallama
da su ya fice, Hajiya na yi masa addu'a
Allah ya tsare.
Washe gari tun da la'asar yake
zumudin tafiya gurin Mero. Karfe shida
dai dai ya fito tsaf cikin wata shadda
Getzner 'yar Dubai kalar sararin samaniya
ta yi masa kyau matuka, zaren da aka yi
dinkin shaddar dashi kalar blue ne don
haka ya saka hula da takalmi blue. Turaren
10
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
out wood na maza ya feshe jikinsa da shi
sai tashin kamshi yake yi.
Ramla ce take zolayarsa tana fadin
"Yaya da alama yau gurin Yayar tawa za
kaje na ga sai zumudi kake yi ga wata
kwalliya ta musamman ka dauka haka...."
Ya katseta ta hanyar kai mata
mangara yana fadin "Kaji marar kunyar
yarinya, kina nufin bana yin kwalliya irin
יי
wannan sai yau.
Wata kara ta saki ta nufi Hajiya ta
buya a bayanta. Ita kuwa Hajiyar dariya
kawai ta saki tana fadin "Kar ka dokar
mini 'ya, ai ba cewa ta yi baka yi ba,
amma dai ba a irin wannan lokacin
la'asariyya ba."
Kwafa ya yi kawai ya girgiza kai ya
fice cikin daga murya ta ce masa "Yaya
kar ka manta ka taho mini da hoton nata."
Bai ko tanka mata ba ya nufi motarsa
wacce ta sha wanki da guga sai daukar ido
11
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
take yi. Ya tada ita ya hau bisa titi yana jin
wani irin nishadi yana ratsa shi har cikin
ransa.
Kai tsaye shagon da ake saida
wayoyi ya nufa, sai da ya samu wacce ake
yayi mai tsada sannan ya siya, yana fitowa
ana kiran sallar magriba, don haka ya
karasa masallacin da ke kusa ya sauke
farali, sannan ya kama hanyar zuwa gidan
Mero.
A kofar gidan ya ajiye motar tasa ya
aika yaro kamar yanda ya saba.
Cikin 'yan mintuna ta fito tana
sanye da wata atamfa wacce ta dansha jiki
ta yafa mayafinta bisa kafada.
Duk da ba wata kwalliya ta yi ba
amma ta matukar birgeshi domin ko yaya
ta yi kyau take yi.
Ya bude motar ya fito fuskarsa cike
da walwala suka hada ido gami da sakarwa
12
AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE 2
juna murmushi, ya birgeta matuka komi na
sa daukar hankalinta yake yi.
Ta risina ta ce masa "Barka da zuwa,
dafatan kana lafiya."
Daddadar muryarta ta doki kunnensa
wani dadi ya ji ya ratsa shi, idanuwansa
kyas a kanta ya amsa mata "Barkanmu dai
Maryamu dafatan kowa da komi lafiya?"
Kanta a sunkuye ta amsa masa
"Lafiya kalau ya mutanen gida?"
"Suna lafiya suna gaisheki. Da
sauri ta dago cike da mamaki ta dubeshi ta
zaro idanuwa amma ta kasa cewa komi.
Dariya kawai ya yi domin ya gano
me take so ta ce don haka ya taimaka mata
wajen fadi tunda ita ta kasa "Kina mamaki
ko? Don nace mutanen gida na gaisheki?"
Ta gyada kai sannan tace masa "To
ai naga basu sanni ba ne ya za ayi harsu
san zaka zo gurina kuma sucea gaisheni?"
13
AWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA СЕ- 2
Ya saki faffadan murmushi sannan
yace mata "ke ce kike tunanin haka
Maryam amma labarinki ya riga yaje inda
bakya tsammani domin ni bana yin abu da
wasa, da ace babu wani kudiri mai karfi a
gareni ba zan taba zuwa kofar gidanku ba
don haka idan ma kina kallon abin da wasa
gara ma ki daina ki mai da shi babba."
Girgiza kai kawai ta yi, cikin ranta
kuwa mamaki ne ya cikata domin bata
taba haduwa da mutum mai magana daya
kai tsaye ba irin Sadik.
Motarsa ya bude ya dauko mata 'yar
karamar leda mai kyau, ita kuwa kanta na
kasa tana wasa da 'yan yatsunta.
"Gimbiya ga wannan wata 'yar
kyauta ce na kawo miki, kin san bahaushe
yace tukwicin so kyauta."
Ta amsa cike da murna duk da bata
san ko menene be ta hauyi masa godiya.
14
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE-2
Ya ce mata "Bana son wannan godiyar
יי taki, ki bude dai kiga ko menene.
Nan take ta bi umarninsa ta
bude,hadaddiyar waya ta gani wacce ko a
mafarki bata taba tunanin mallakarta ba,
cike da mamaki ta bude baki tana kallon
wayar, bata san sanda ta zube a kasa don ta
yi masa godiya ba, da sauri ya dagota yana
fadin na gaya miki bana son godiyar nan
amma kin ki ki daina."
Cike da kunya ta mike, ya amshi
wayar ya hau nuna mata yanda zata yi
amfani da ita, a haka har dare ya soma yi,
ya yi sallama da ita ya nufi gida ba tare da
zukatansu sun so rabuwa da juna ba, sai
dai don babu yanda zasu yi, amma fa sun
raba dare suna magana a waya, suna
musayar kalmomin soyayya, har sai da
`bacci yaci karfinsu sannan suka hakura..
15
****
AWIYYA WADA ISA-‘YAR ALJANNA CE-2
Zaune suka a falo shida Hajiya da
alama suna tattaunawa ne akan wani
muhimmin al'amari, dukkansu sun maida
hankalinsu guri daya suna fuskantar juna.
Bayan shiru na dan sakanni ne Sadik
ya cewa Hajiya "Ni abin da nake gani
Hajiya klu zauna ke da Ramla ku tsara duk
abin da ya dace a siya, inyaso sai mu sanya
lokaci daya muje mu siyo komi a zo a
hade su guri daya, ni nafi bukatar a kai
komi rana daya kar a tsaya wani rabe-rabe
inyaso da ankai ranar biki kawai za a dawo
a sanar dani."
Hajiya ta girgiza kai ta ce masa "Ni
kaina na fika bukatar hakan domin akwai
halin yin hakan, amma abin da nake hange,
an sanar da lyayen yarinyar domin gani
nake zasu ce anyi gaggawa, da an bari sai
nan da wata biyu, kaga idan ya cika na uku
sai ya zama shine na bikin ko kuwa?"
16
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Sadik ya girgiza kai yace mata "Haba
Hajiya na yi maki bayanin nan fa tun farko,
sai da na jaddadawa yarinyar tace babu
matsala, kuma na je mun gana da mahaifinta
ya ce ai ba komi, su albarka kawai suke
bukata, shiyasa na ce miki aje kawai a
tambayo sanda za a kai kudi, da an kai sai
kuma batun kai kaya shikenan ni gaskiya ba
zan juri har wata uku ina zuwa gidansu
yarinya da sunan soyayya kawai ba.
Dariya Hajiya ta yi sannan ta ce, "Ikon
Allah, Ashe dama matar ce bata zo ba,
shiyasa kake gudun zancem aure, yanzu da
matar tazo gashinan har kafi kowa zakwadi
da zumudi, to ai shikenan Allah ya sanya
alkhairi tunda Iyayenta sun amince ai magana
ta kare."
Bai kara ce mata komi ba illa mikewa
kawai da ya yi yana fadin "Ina sauraronku
zuwa yamma don na san me ake ciki."
Yana fadin haka ya fice, ita kuwa
Hajiya Saude binsa kawai ta yi da kallo cike
da jin dadi cikin ranta, tana kuma godewa
17.
AWIYYA WADA ISA. ‘YAR ALJANNA CE-2
Allah da ya nuna mata wannan rana da dan
nata ke zumudin aurensa har yana nema ya
fita.
Maganar aurc kam ta kankama domin
an kammala komi na aure, an kuma saka
ranar aurc uzuwa yanzu saura sati guuda don
haka kowanne bangare suna cikin hidima
Amarya kan ta sha gyara ta fito fes sai
daukar ido take yi, ga kamshi na binta ta ko
ina, nera kam ta yi kuka domin Sadik ya yiwa
Mero 6arin kudi kamar debo su kawai yake yi
ba nemansu yake yi ba. Hakan ba karamin
batawa Salama rai ya yi ba, a fuskarta ne
kawai take yake ake ganin kamar tafi kowa
murna, amma cikin ranta baki ne kirin domin
ji take yi kamar ta maida auren Sadik kanta ba
Mero ba, a ganinta itace tafi cancanta. тв1
dirAcikin taron bikin kuwa duk inda
Mero ta saka kafa Salama ke bibiyarta har
lokacin da za a kaita dakinta ob srrunGY.BWUS
Fes ta fito cikin wani swiss lace pink
mai zanen manyan flawers blue, duwatsun
jiki suma kalolin. r iio ibeb nij sb
18
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA СЕ 2
Ya matukar amsarta dinkin da aka yi
masa tamkar dama a jikin ta aka halicce shi,
ya bi jikinta lif, tun daga mayafinta kuma har
yarin kunnenta da sarka zuwa abin hannu, da
takalmi da jaka duka kalar Blue ta sanya,
hakan ya sake fiddo da kyawunta karara.
Tana zaune bisa kujera ta lulluße kanta
da mayafi, Salama na kusa da ita tana gaya
mata wasu maganganu a kunnenta wanda ba
kowa ke iya jinsu ba.
A haka Baba kande ta shigo ta same su
tana fadin "Ke Mero ke ake jira tun dazu anzo
daukar amarya mutane duk suna waje suna
dakon fitowarki."
Da sauri Salama ta amshe cike da
99
fara'a "To Baba bari mu fito yanzu.
Ta kamo hannun Mero tana fadin "Та
so muje amarya kar a gaji da jiranki.
Ta shi kawai ta yi ta bita ba tare da tace
komi ba, hawaye na bin idanuwan Mero tana
waiwayen mahaifiyarta haka ta fito daga
mahaifarta.
19
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNА СЕ-2
Har suka isa cikin dakinta Salama ce
dai ke rike da ita, sai da ta zaunar da ita bisa gadonta sannan itama ta zauna kusa da ita.
Irin gadon da taga an kawo Mero a
matsayin gidan aurenta, ya tsaya mata a rai, domin gidane wanda zaka iya mantawa da
talauci idan har ka shigeshi.
Duk wadanda suka rako amarya sunyi
mata fatan alkairi sun tafi, illa Salama da
wasu daga kawayenta da suke jiran ayi sayen baki suma su kama hanyarsu.
Ba dadewa angwaye suka bayyana a
gidan, Auwalu ne a hannun damar ango
sannan wasu daga abokansa don haka bayan
sunyi masu sallama sun gaggaisa. Sannan
Auwalu ya fara da fadin "Alhamdulillah yau
Allah ya kawo mu auren Sadik da Maryam,
masoyan da suka kafa tarihi a wannan yankin
namu, don haka muna musu yi musu addu'a
Allah ya basu zaman lafiya da kuma kazantar daki."
Dukkansu suka yi dariya sannan suka
amsa masa da "Amin."
20
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
Auwalu ya sake duban ango cike da
zolaya yace masa "Ango ai ka bude kan
amaryar taka don muyi sauri mu tafi mu baku
waje ko? Don na tabbatar yanzu kafi kowa so
mu tafi mu baku gidanku."
Dukkansu suka sake dariya, Sadik da
sauri yace masa "Wallahi abokina kamar ka
shiga zuciyata dama zaku kyale siyan bakin
nan na sayi abina da kaina da yafi.
Mamaki ya cika Auwalu, da sauri ya ce
masa "Af haka kace" To shikenan bari mu
tashi mu barku tunda korarmu kake yi.'
Zai yunkura ya ta shi daga inda yake
zaune, da sauri Salama ta ce masa
'Haba dai ka zauna mana Auwalu a
karasa ai shima zolayarka yake yi kawai."
Auwalu ya yi murmushi sannan yace
"Ai nima na san zolayar tawa yakeyi. Ya
dauko kudin siyan bakin ya mikawa Salama
yana fadin "Ga kudin sayen bakin ki nan, da sauri ta amshe bandir din kudin, amma ranta
yana tafarfasa da takaici.
21
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE- 2
Ta daga kudin ta juya sannan ta ce, "То
mun amince ango ya bude fuskar amaryarsa.
Gaba daya suka yi dariya, shi kuma
Sadik cike da zakwadi ya hau cire mayafin
kan Mero a hankali, tana dago idanuwanta
suka yi ido hudu, sannan suka sakarwa
junansu murmushi.
Auwalu cike da fara'a yace "To amarya
ga amanar ango nan, kaima ango haka, mu
zamu wuce yanzu don mu barku ku sake don
nasan zuwa yanzu kana kan gwiwa tamkar
mai nakuda.
Sadik ya yi dariya ya ce masa "Kai dai
baka rabo da zolaya, amma ba komi zan rama
ne.
Suka yi sallama da su ya tafi ya rakasu,
ita kuwa Salama matsawa ta yi kunnen Mero
ta sake yi mata huduba, sannan daga karshe ta
ce mata "Kar fa ki 6ata mana shirinmu."
Mero ta girgiza kai sannan ta ce mata
ina sane kawata kar ki ji komi.
Sai da ta jiyo karar horn din mota
sannan ta fito da gudu ta same su suna jiranta.
22
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE 2
:Sai da suka fice aka rufe kofar gidan
sannan ya koma cikin gidansa cike da
zumudin mallakar Mairamunsa a matsayin
matarsa ta sunna.
id:Kai tsaye dakin Mero ya nufa amma
abin mamaki sai ya ga kofar dakin nata а
rufe, ya murda cikin kwarin gwiwa amma
sam kofa bata bude ba, hankalinsa ya ta shi
ya hau buga kofa yana kiran Mero, amma
shiru.
fsRaiCikin daga murya ya ce "Mero ya ka yi
kofar ta rufe da ke? Ki jeho mukullin ta taga
na budeki."
110
oav Shuru dai ba wani motsii, ya ci gaba da
kiranta yana fadin "Ko bandaki kika shige ne
Mero?
Har tsawon mintuna amma shiru babu
ko motsi, wannan abu ya matukar daurewa
Sadik kai, don haka ya hau buga kofar da
karfi yana kiran sunanta amma san babu
alamarta.
Cike da dacin rai ya hau za gayawa falo
yana faman huci, ya dunkule hannunsa ya
23
AWIYYA WADA ISA. 'YAR ALJANNA CE2
doki dayan yana furzar da hucin bacin rai da
takaici.
A haka har ya gaji ya kwanta bisa
doguwar kujera cike da dacin rai, sakamakon
gajiyar da ke jikinsa ne bacco ya dauke shi а
nan, haka ya kwana cikin bakin ciki da
taraddadin rashin sanin dalilin faruwar hakan.
****
Alhaji Sadik yana dai zaune bisa kan
gadon Asibitin yana fuskantar Alhaji Aliyu,
ya na kaiwa nan ya yi ajiyar zuciya sannan ya
יי
rufe idanuwansa ya sake budewa kana yace
Haka nayi aurena na farko babu bincike na
dai biyewa son zuciyata ne kawai da kyale
kyale sannan kuma na sake samun goyon
baya daga gidanmu wadanda ke fifita kyau da
יי
wayewa fiye da komi a wajen aure.'
Alhaji Aliyu ya girgiza kai cike da
jmami yace masa "Wannan shine kuskuren ka
na farko Alhaji Sadik."
24
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE- 2
Ya sake yin ajiyar zuciya sannan yaci
gaba da daga inda ya tsaya.
****
Washegari da safe Alhaji Sadik ya
gama shiryawa tsaf ya fito falo ya zauna cike
da jimami da takaicin abin da Mero ta aikata
masa jiya.
Motsin tahowarta ya dinga jiyowa daga
dakinta, ya sanya ido bisa hanyar, ita din ce
kuwa, a shirye tsaf cikin wasu engllish wears
da suka amsheta matuka, ta yi matukar kyau.
Da sauri ya dauke kansa daga inda take ya
koma kallon film din da yake kunne a falon.
Kusa da shi ta zo ta zauna cike da
fara'a tana gaisheshi.
Harararta kawai yayi ya kawar da kansa
gefe ya ci gaba da kallon da yake yi.
Ta rusina har kasa tana sake gaishe shi,
cike da takaici ya sake kallonta, sake kawar
da kansa gefe yace mata "Yanzu ke dan Allah
abin da kika yi jiya kin kyauta kenan?"
25
AWIYYA WADA ISA-'YAR ALJANNA CE- 2
Ta sunkuyar da kai kasa ba tare da tacc
masa komi ba, ya sake tambayarta cike da
damuwa "Kiyi magana nace kin kyauta kenan
haka ya kamata kiyi ko?"
Ta girgiza kai ba tare da tace komi ba.
Ya sake watso mata tambayar tya ce
"To me ya sa kima aikata abin da kika san
bai dace ki aikata ba?"
Cikin muryar neman afuwa ta ce, masa
"Ka yi hakuri ba zan kuma ba Insha Allah
kuskure ne nayi."
Ya girgiza kai gami da kwaße baki
yace mata "Allah yasa abin da kika fada
gaskiyane."
Ya duba agogonsa sannan yace "Ai ya
kamata mu karya domin ni da wuri nake son
na fita sabida ana sauke kaya yau."
Mero ta marairaice murya ta ce, masa
"Da wuri kuma Alhaji? Ko hutun aure ba za
ka yi ba? Duk ango yana hutawa a gidansa
amma banda kai."
Cike da mamaki ya dubeta yace mata.
"Mero kenan, kina bukatata ne a cikin gidan
26
6
AWIYYA WADA ISA- ‘YAR ALJANNA CE 2
na? ki kyaleni na tafi gurin aikina mana sai
kifi sakewa a gidanki ko? Tunda bakya
bukatata a kusa da ke."
Girgiza kai ta yi sannan cikin shagwaба
tace masa "Wallahi ba haka bane, don Allah
ka yi hakuri ka zauna mu wuni tarc."
Bai tsaya sauraronta ba kawai ya mike
ya nufi kan teburin cin abinci.
Ta bi shi a baya tana isa ta hau zuba
masa karin kumallon sai da ta kammala ta
bashi sannan ta zuba nata ta zauna ta fara ci.
A tsanake yake dubanta cike da kulawa
ya ce mata "Amarya kinsha kamshi kinyi
kyau matuka sai daukar ido kike yi sai dai
rowar kyan naki kike yi."
Dago kanta ta yi suka hada ido ta sakar
masa murmushi tana fadin "Kaima aika zuba
kyau tamkar wani Dawisu."
Ya saki murmushi da alamun
magannarta ta faranta masa ya ce mata
"Dagaske kike?"
99 Ta girgiza kai tana fadin "Sosai ma."
27
AWIYYA WADA ISA- 'YAR ALJANNA CE 2
Alhaji Sadik yace mata "Amma kike
nema ki kawo mana cikas a farin cikinmii da
cikar burinmu."
Ta sunkuyar da kanta a kasa ta ce "Ai
ba zan kuma ba."
Cike da fara'a ya ce mata "Ko ke fa,
banda abinki kin taba ganin a wannan
zamanin mace na gudun mijinta? Musamman
99 wadan da suka yi auren soyayya.
Murmushi ta yi ta sunkuyar da kanta,
kar ka damu zan baka mamaki."
a
Wata dariya ce ta subuce masa mai
bayyanar da jin dadinsa da farin cikinsa a fili,
daidai lokacin da ya ke mikewa daga kan
teburin yana kallonta "Allah yasa da gaske
kike yi.'
Murmushi kawai ta yi ta ce masa "Zaka
tabbatar da gaske nake yi idan na shayar da
kai mamakin."
Cike da