har ta iso inda yake zaune,
muryarta ta yi kasa sosai, ta yi mashi sallama ya
amsa yana murmushi, ya ce "Sorry Naja'atu, na
takura ki ko.?" Ta dan saki fuska sannan ta ce mashi
"Ina yini.?" Ya ce, "Lafiya lau, ya ya karfin jikin.?"
Nan ma ta amsa mashi a sanyaye, ya ce "Kiyi hakuri
dani Naja'atu kada kiga laifina, duk wani da namiji
da ya san ciwon kanshi, mace irin ki yake nema, don
ta zamo uwar 'ya'yanshi, don haka duk wata zalama
ko naci da zaki ga na nuna akanki, ba kallonta yana
son yaga yarda ta karbi maganarshi. To babu laifi ba
damuwa a tare da ita, haka nan ba ta sakar mashi
fuska ba, yarda shi yake so, to wannan bai dame shi
ba, yasan sai a hankali ya sani irin su Naja'atun
wuyar samuwa ke gare su.
Ya nuna mata dayar kujerar dake kusa dashi ya
ce, "Zauna mana." Bata yi musu ba ta ja ta zauna, ya
ce "Yanzu ta ina kike ganin za'a fara.?" Ta sarda kai
bata san me zata ce ba, sai ya gyara zama yana
kallonta, ya ce "Bari in fadi mani abin da ya dace ki
tambaya, tunda baki so ki sani sunana Dr. Khalid
Musa, asalin iyayena 'yan Kano ne a unguwar Hotoro, ba zani 6oye miki komi ba, iyayena talakawa
ne likis, don haka ban tashi cikin rayuwar dadi ba,
karatuna gaba ki dayanshi nayi shi ne a makarantun gwamnati, tare da rufin asirin Allah, saboda abubuwa da yawa suna yi mani wahalar samu, da haka har
76
Allah ya taimake ni na kare karatun sakandire, don
zaman da na yi gida kafin jarabawarmu ta fito na yi
sana'o'i daban-daban, domin taimakon kaina da na
kanne na, cikin sa'a lokacin da jarabawarmu ta fito na
samu gagarumar nasara da ya dace ace na ci gaba da
karatun, amma rashin galihu ya sanya dole na hakura
ina kallo abokaina da yawa suka ci gaba da karatunsu
ni ina zaune gida.
Sai da na shafe shekaru biyu zaune gida, sannan
Allah ya hada ni da Ubangidan kirki, Alhaji Buba
Usman, shi ya yi tsayin daka a kaina ya fiddo
kudinshi ya biya mani kudin karatu, in da na samu
digiri akan fannin lafiya, kamar yarda kika ganni.
Cikin ina karatun ne Allah ya yi ma mahaifina
rasuwa, don haka nauyi ya kara yi mani yawa, saboda
nine babba sai Kanwata mai bi mani Zulaihatu sai
Sadiya, karaminmu namiji ne Sulaiman yanzu haka
yana nan tare dani yana karatu a Gwagwalada, yayin
da Zulaihatu da Sadiya suke aure a can Kanon.
Bayan rasuwar mahaifinmu da shekara hudu,
itama mahaifiyarmu Allah ya yi mata rasuwa, don
haka ni na aurar da su Sadiya baki daya, tun kafin su
kare karatunsu na sakandire, saboda idan na barsu
gidan su kadai hankalina baya kwanciya, kin san
yarda rayuwa ta canza, don haka na gwammace in
barsu su yi auren. 77
Da na kare karatuna a A.B.U Zaria, na yi bautar
kasa, ban zauna ba na ci gaba da fadada ilimina a
Jami'arm Ibadan, kuma da taimakon. Allah na kai
wannan matsay in da nakc. Yanzu ina aiki a National
Hospital, sai kuwa Part time a wannan asibitin da na
haďu dake. Kamar yarda na ce ba zani iya boye maki
komi ba, iya tsawon rayuwata ban taba son wata diya
mace ba, gaba ki daya ban fara tunanin aure ba sai
cikin wannan lokacin ko da yaushe addu'at Allah ya
hada ni da mata ta gari, wadda zata taimaka mani in
ci gaba da kula da 'yan'uwana, to kuma cikin sa'a sai
gashi Allah ya hada ni dake, na yarda dake da dabi'unki, don haka kika ga na tako takanas na zo
gare ki ina ji a jikina ke alkairi ce gare ni, da fatan za
ki bani dama mu fahimci juna." Nan ya tsaya yana kallonta.
Haka nan sai ta rinka jin tausayinshi, duk da
cewa itama cikin talaucin ta tashi, a kalla ita gaban
iyayenta take, kuma babu abin da ya gagare su
daidai. Ta dube shi a hankali ta yi murmushi shima
ya taya ta, ya ce "Kin gamsu da abin da na fadi maki?
Ko kuma akwai wani abu da ki ke son ji.?" Ta girgiza kai ta ce "Babu." ya ce, "To na gode da ki ka yarda ki ka bani dama na fadi maki manufata akanki, don haka bari in barki ki huta, kiyi nazari sosai sai na sake dawowa."
78
Ta yi mashi sallama ta nufi cikin gida yayin da
shi kuma ya nufi motarshi kirar Pcogeout 307 baka
sabuwa dal, ya bude sif din baya, ya fiddo manyan
ledoki biyu, ya kira maigadi ya ba shi ya ce ya shigar
ma Naja'atun da su." Kayan kwalama ce da na shafeshafe. Yaja motarshi ya tafi, ya yi haka ne saboda ya
fahimci halayyarta, idan ya ce zaya bata hannu da
hannu ba zata karba ba, 6ata mashi lokaci zata yi, ireiren abubuwan da ke kara mata kima kenan, sam bata
da zalama da zakewa irin ta wasu matan. Insha
Allahu zaya ci gaba da lallabawa yana bin ta har sai
ta amince da shi.
To Allah yasa hakan.
Mai karatu ka biyo ni zuwa littafi na biyu don
jin yarda zata kaya, shin Daddy ne ko Likitan.?
Alhamdulillahi!
Taku har kullum
Anty Uwanin Kankia.
79
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels