"Na barki ki yi nazari sosai,
Allah ya kara sauki."
Ya juya yana shirin fita ta budc idanuwanta tar
tana kallonshi, ta ce "Ba wani nazarin da zani yi ka bar
maganar ba ni so." Ya yi murmushi ya dubec ta cikin ido
sai ta ji nauyinshi ta sarda kai ya ce "Ban yi maki musu
ba, sai dai abu guda ne zaya sanya in iya hakuri dake,
idan da kin ce mani kina da aure ko kuma wanda na
ganku tare saurayinki ne, to gaskiya sai in yi hakuri,
saboda na ga ya damu dake yana nuna kulawarshi sosai,
to kin ce yayanki ne, kinga zancen in bar ma wani ke
ma bai taso ba, don haka ki kwantar da hankalinki, idan
kika fahimce ni za ki nine mijin da ki ke jira, Allah ya
bamu alkairi." Bai jira ya ji ta bakinta ba, ya sanya kai
ya fita, Naja'atu ta rumtse ido tana mamakin wannan
wane irin mutum ne Allah ya hada ta dashi.?" Daga
ganin sarkin fawa shi kenan sai miya ta yi zaki.?"
60
To amma wani abun mamaki sai ta samu zuciyarta
da karkata wajen sha'awar wasu abubuwa da ta fahimta
a tare dashi, kai gaba ki daya ma sai ta ji tana
ra'ayinshi, muryarshi mai taushi tsab-tsab da shi. A
hankali ta rufe fwayar idonta tana kallonshi yana yì
mata murmushi, sai ta saukar da ajiyar zuciya bata san
me zata kira wannan al'amarin ba, amma a bangare
daya kuma sai kaunar Daddy ta rinka neman fizgarta
har tana jin ba zata iya amsa tayin Likitan ba.
Daddy ya murda kofar ya shigo, Ibrahim yana
biye da shi sai Hajiya, Ga ba ki daya suka shigo suna yi
mata sannu Hajiya ta kalli farin ruwan ya yi nisa sosai,
don hala suna sanya ran cewa zasu tafi gida a ranar.
Nan suka zauna ana ta jinya Ibrahim ya cc ma ta ga
wayarta nan ya taho da ita Mas'ud yana ta kira, amma
ya sanar da shì tana asibiti." Hajiya ta ce, "Ka kira shì
sai ka bata su gaisa, kada hankalinsu ya tashi gashi ta
samu sauki. Don haka Ibrahim ya kira sannan ya bata
suka gaisa da Masud, ta sanar dashi zazzabi ne kawai,
amma ta samu sauki, karin ruwa ne aka yi mata da
zaran ya kare kuma zasu tafi gida." Ya cc., "To Allah ya
kara sauki, Inna na gaida ki." Ta cc. "Ina amsawa, ka
gaida su duka har da Baba." Ta yi sallama ta rufe
wayar.
Babu laifi ta dan samu sauki, suna magana da
Ibrahim, Hajiya na zaune gefe daya shi kuma Daddy
wayarshi ta yi kira, don haka ya bude dakin ya fita
tasan mutuniyar ce ta yi kira, ya cika damuwa da
wannan Faridar, sai ka ee ta asirve whi. Suna nan zaune
har ruwan ya Rarc, don haika Doiddy ya fita ya kirawo
Nas din tazo ta cire ya сc. "Ta je ta nemo Likita ya
sallame su" Amana sai Nas cin ta ce "Likita ya (tafi,
Ruma yaoc kada a sallame ta sai da safc." Naja'atu ta
kalle ta da sauri, to sai dai ta san manufarshi, don kada
ta taftne hai samu abin da yake so ba to ko kwanan tayi
ha abin da zaya samu zaya gaji da fwafwarshi ya rabu
da ita. Ta maida kanta ta kwantas yayin da su Hajiya ke
ta korafin don mi zaya ce sai da safc alhalin gashi ta
smau sauki kuma da kanshi ya ce ba zata kwana
Hajiya ta kalle ta ta cc. "Yanzu yaya za'ayi
kenan?" Daddy ya yi sauri ya ce. "Rabu da shi kawai
Hajiya, tafiyarmu zamu yi tunda gashi ta samu sauki."
Hajiya ta oc. "Ba'a haka Daddy, idan mun tafi yanzu
wani abun ya sake tasowa kana ganin zasu saurare
mu?" Ya ce "Ga asibiti da yawa a gari, sai mu camza
wani" Naja'atu ta coc. "Babu komi mummy ku tafi zani
kwanan da safe sai a dawo a dauke ni
Hajiya ta cc, "Yaya za'a barki ke daya a asibiti
Ta cc, "Ga Nurses dim su nan, suna kulawa sosai, Allah
kuwa babu komi." Hajiya duk tabi ta dmau, ta cc ""Sai
dai nì in tsaya mu kwana tarc." Ta cc, "Yaya za'ayi ki
kwana nan Mummu? Ke ma fa har yanzu ba ki ida
warwarcwa ba, Allah babu wani abu.
Hajiya ta jima tana kallonta, sai kuma ta jinjina
kzi ta oc, "To tashi kici abinci, gaya nan." Naja'atu ta
tashi zaunc, yayin da Hajiyar ta zubo mata abincin ta
bata tana ci, su duka suna nuna kulawarsu gare ta.
Daddy ya fita ya kira wata Nas da zata kwana ya сс,
"Don Allah ta rinka kula da Naja'atun." Ta cc, "Babu
damuwa, insha Allahu zata kula." Ita kuma Naja'atun
ya rinka bata hakuri, gani yake yi kamar sun yi mata ba
daidai ba, to sai dai matsalar maza ba su jinyar mata, da
ya tsaya tarc da ita, tunda babu macen da zata zauna da
ita, Zainab ce tana makaranta, amma cikin satin suke
sanya ran zuwanta. Naja'atu ta yi murmushi, tana
kallonshi ta ce, "Allah kuwa babu komi Daddy, awa
nawa ne."
Shima ya zuba mata ido ya ce, "Kin tabbata.?" Sai
ta yi dariya, tana kallon Hajiya, itama Hajiyar
murmushi take yi, yanzu hankalinta ya kwanta, tunda
taga Naja'atun bata damu ba." Karfe goma suka yi mata
sallama suka tafi. Ta kwanta shiru, duk sai ta ji ta dan
takura, ta lalubo wayarta, ta bude sai ta kunna kira'a, da
ta dauka ta aje wayar gefe daya tana bi a hankali
zuciyarta ta samu nutsuwa tana tunanin kamalan Likita
da abin da ya yi mata, kome yake nufi.?" Karatun ya
tsaya yayin da kira ya shigo, ta lalubo wayar tana kallo,
sunan Daddy ne faro-6aro bata yi mamaki ba, kila
Ibrahim ne ya sanya mata lambarshi, ta Glo, to amma
shi ina ya samu lambar?"
Ta danna wayar ta amsa mashi da sallama ta ce,
"Har kun isa gida.?" Har ma na yi wanka na kwanta
amma sai na kasa barci ina tunanin wane hali kike, baki
takura ba ko.?" Ta ce, "Eh." ya ce "ko dai in zo in
63
dauke ki yanzu.?" Ta yi murmushi a hankali, ta ce kada
ka samu damu, zani kula sosai, sai da safc." Ya cc,
"kora ta kike yi kuma?" Ta ce, "Ba haka ba ne, naga
dare ya yi sosai, ya dace ka kwanta saboda tafiya ofis
da safc." Daga in da yake ya lumshe ido, muryar nayi
mashi dadi, tana cikin abubuwan da yake so a tarc da
ita. Ya yi murmushi ya cc, "kin san wani abu.?" Ta yi
shiru tana saurarenshi, ya ce "Ni kuma nafi jin dadin
wannan hirar da muke yi akan barcin da zani yi, yanzu
haka kwance nake amma na kasa yin barcin, tuninki ya
hana ni zama lafiya, gani nake kamar kina nan cikin
damuwa, da kamar namiji na jinyar mace, wallahi ba
zani barki ki kwana ke daya ba cikin asibiti."
Naja'atu ita daya cikin daki, mamaki ya cikata,
"Me ke damun Daddy yau? Kalamanshi sun fara zarta
hankali." A bangaren shi ya yi shiru yana sauraren ya ji
abin da zata fada, shiru ba ta ce komi ba, ya yi gyaran
murya ya ce, "Naja'atu kina jina kuwa.?" Ta ce, "Ina
saurarenka." Ya ce, "To yaya baki ce komi ba.?" Та сс,
"To me zani ce maka? Na lura yau hirar ka ke ji, me
zaya hana ka kira Farida kuyi." Yana saurarenta ya yi
shiru, to sai dai shima da ya yi nazarin kalaman da ya.
fada, sai yaga ba shi da hujjar fadi mata haka, to sai dai
abin da zuciyarshi ta kudurta kenan, me yiwuwa wani
sirri ne na daban a cikin zuciyarshi, yake neman
bayyana kanshi." Sai yaga kamar bai kyauta ba, amma
kuwa a wani 6angaren bai yi nadamar maganarshi ba,
saboda kullum rana kima da martabar Naja'atu karuwa
64
yake yi cikin zuciyarshi, wani lokacin idan yana
tunaninta sai yaga matsayinta yana neman kai wani
matakin da shi kanshi bai san yarda akai haka take
neman faruwa ba.
Muryar Naja'atu tadawo dashi, in da ta ce, "Daddy
ka aje ne, na ji shiru.?" Ya yi murmushi yana shafa kai,
ya ce "Shi kenan bari in barki ki huta, na ji kin fara
korata kada ki kai ga rufe wayar." Ta ce, "lah! Ni fa ba
korarka nake yi ba, kayi hakuri idan kuma kana ganin
mu ci gaba da hirar to bissimillah, ba matsala, ni dai
gani nayi doguwar hira ta ma'abota soyayya ce, don
haka na cc ka nemi Farida." Ya cc, "kina son ki fadi
mani ke ba ki soyayya?" Ta cem "Ban ce ba, sai dai
komi lokaci ne, idan yazo zani yi." Daddy ya rinka
kyalkyatar dariya ya ce, "Ashe mu zuba ido zam,u ga
takun soyayya.?" Ta ce, "Amma fa mai tsabta, ba wai ta
rashin hankali ba." Ya ce, "Ashe har soyayya ke akwai
ta rashin hankali.?" Та се,"Sosai ma." Ya ce "Kamar
wace kenan.?" Ta ce, "Kasan kowa da irin yarda ya
dauki soyayya, to ni abin da na dauke ta wani abu ce
mai muhimmanci, da ta dace ayi ta da wanda ya
cancanta, wai don mutum yazo ya ce yana sonka, ba shi
ne so ba, sai ka natsu ka fahimci menene dalilin son da
yake yi ma? Wadanne abubuwa ya duba har yazo ya сe
yana sonka, haka nan menene manufar son da yake yi
maka. A ra'ayina ba zani taba tsayawa in yi soyayya da
wani ba, sai wanda ya cancanta kuma naji ina sonshi,
na yaba da dabi'unshi da manufarshi a kaina, kuma
65
wanda nasan a Karshen soyayyarmu aure zamu yi mu yi
rayuwa ta har abada Kaga wani zaya iya zuwa yа се.
yana sona amma ba manufarshi ya aure ni ba, kawai
don acc wance budurwarshi ce, ko kuma don ya saka ki cikin lissafin 'yanmatan da ya nema wani ma kai tsayc
wani abu ya hango tare dake yazo kaga wannan ba so
ba ne, don haka idan na ce maka yanzu ina soyayya
nayi karya, saboda har yanzu ban samu wanda ya
cancanta in yi ma irin son da kai kake magana ba."
"Na Daddy ya saukar da ajiyar zuciya, ya ce,
fahimce ki Naja'atu, kuma abubuwan da kika fada sune
suka dace akasari ma'aurata su rinka dubawa kafin su yi
aure, nima na karu da nasihar ki, idan kin dawo gida
zani yi wata shawara dake, na gode, Allah ya bamu
alkairi." Ya rufe wayar, ya aje gefe daya sai ya sanya
hannu ya tallabe kanshi daga kwance yana kallon silin,
tunani barkatai a ranshi. Can itama ta kwanta tana
tunanin Daddy da kuma dangantakarshi da Farida,
akwai abubuwa da dama da ya kama ta ya duba
matsawar dai yana son suyi aure mai dorewa. A hankali
tunaninta ya dawo kan Likitanta, "ko me ye sunanshi
ma.?" Ta lumshe ido tana sauraren kalamanshi, amma
data tuno yaudarar maza sai taji sam ta tsane shi, balle
kuma ga jin zafin abin da ya yi mata na rike ta asibiti,
sai ta share tunaninshi, a haka barci ya dauke ta.
Da safe karfe bakwai da rabi, tana kwance Likitan
ya shigo fuskarshi a sake yana murmushi, ya ce, "Good
mornin my dear, yaya jikin? Naja'atu ta daure fuska
66
sosai, bai yi fushi ba yana kallon kwayar idonta, ya сс,
"Ayya na yi laiti ko? Kiyi hakuri kada kiga laifina, na
san idan ba haka na yi ba, idan kika tafi jiyan ba zani ji
abin da nake so ba, daga gare ki, don haka na ba da
umarnin kada a sallame ki so ki yi hakuri dani." Duk ya
marairaicc yana kallonta, sai ta yi murmushi ta ce,
"Amma kasan ba ka kyauta ba, jiba yarda ka janyo
mani kwana cikin asibiti a takure." ya ce, "Na sani na yi
laifi, amma kiyi hakuri yanzu zaki tafi gida, muje in kai
ki da kaina don inga in da ki ke." Ta kalle shi da sauri,
shima kallonta yake yi da salon yaudararshi, sai ta
sauke kwayar idonta tana girgiza kai ta ce, "Gaskiya ba
zani bika ko ina ba, za'a zo a tafi-dani yanzu."
Daddy ya murda kofar ya shigo, idanuwanshi na
kanta, sai kuma ya juya kan Likitan yana tuhumarshi,
amma shi Likitan sai ya washe ya mika mashi hannu
suka gaisa, ya na bashi hakuri kan rashin sallamar su
jiyan. Daddy ya ce, "Ba damuwa, ta wuce gashi har
garin ya waye." Ya dubi Naja'atun, yayin da itama take
kallonshi da shirinshi na tafiya ofis, akasari dama ya fi
sanya fut, to yau ma tsanwaye ne jikinshi sunyi mashi
kyau. A hankali ya isa gaban gadon yana tambayarta
jiki, ta ce "Ya yi sauki." Insha Allahu gida zata yanzu,
ai naga jikin ya yi sauki sai dai za'ayi allura daya." Su
duka suka yi dariya. Likitan ya duba ta ya kara rubuta
mata wasu maganin da zata ci gaba da sha. Daddy ya
karba ya sanya aljihu ya ce, "Zaya taho mata da su,
idan ya taso daga ofis. 67
Don haka ta zama cikin shiri, direba na nan zuwa
da Mummy zasu dauke ta, ya duba agogo lokaci yaja,
gashi akwai tazara zuwa ofis dinsu, don haka ya yi
mata sallama ya fita. Ta bishi da ido sai da ya fita,
sannan ta sauke kwayar idonta akan Likitan shi kuma
ita yake kallo, suka yi murmushi baki daya, ya ce,
"Yanzu ina magana ta tsaya.?" Tа сс, "Tо ai ka ji dai
za'a zo a dauke ni yanzu." Ya ce, "To ki bani address
din ki zani zo." Ta girgiza kai ta ce "Na fadi maka ka yi
hakuri ni fa ba zani yi wata soyayya ba." Ya zuba mata
ido ya ce, "Saboda me.?" ta ce, "Ba ni da ra'ayinta ne.?"
ya dan yi shiru, amma kuma sai ya ce, "Ni kau sai nake
lura da man din nan kamar yana nufin wani abu
akanki." Naja'atu ta kalle shi da sauri ta ce, "ban
fahimce ka ba." Ya watsa hannayenshi, akwai alamar
damuwa a fuskarshi, sai dai yana kokarin boyewa, ya
dan cije lebenshi yana kallonshi ya ce, "Mu maza muna
da wani sirrin kishi a ranmu, wanda idan ba mu ba babu
wanda zaya iya fahimtar hakan, bari in tambaye ki wani
abu, shin cikin ku daya da shi.?" A hankali Naja'atu ta
sauke kwayar idonta tana kada mashi kai, ya yi
murmushi ya ce, "Nasan a rina, wai an saci zanin
mahaukaciya, to amma tunda ku duka kuna kokarin
6oyewa, shi kenan ni dai ba zani 6oye maki ba, ki
saurari zuwana gare ki koda wane lokaci, me yiwuwa
rabon nawa ne don haka ya tsaya kauron baki."
Naja'atu ta tashi zaune tana kallonshi ta ce, "Kaga ni fa
babu wani abu tsakanina da Daddy, yana da yarinyar da
68
zaya aura kowane lokaci za'a ya sanya lokacin
aurensu."
Ya cc, "Shi kenan, nima sai kiyi mani kokari mu
fahimci juna, yarda zata kaimu ga irin wannan
matsayin." Naja'atu ta yi shiru tana jin shi bata taba
ganin mutumin da ya iya naci irinshi ba, ga baki da
wayaun tsiya, duk ta in da ta bullo mashi sai ya san
abin da zaya ce mata, ya jima tsayc yana kallonta, bata
ce mashi komi ba, sai ya ji muryarshi ya cc, "Shi kcnan
bari in barki ki huta, sai kin ganni." Bai jira amsa ba ya
bude kofa ya fice, ta bi kofar da kallo, sai ta saukar da
ajiyar zuciya, ya ta iya da rayuwarta?.
Bai jima da fita ba, sai ga su Hajiya sun iso ta
godc ma Allah da ya sanya basu samu Likitan ba, tasan
Hajiya zata yi tsammanin wani abu, ko shi Daddyn ta
lura dashi bai gamsu da abin da ya gani ba, tana lura
dashi yana tuhumarta da ido, to ita kanta ba damuwa ta
yi bashi ba bata san dalili ba, sam bai burgeta ba illa dai
kawai bata iya fitowa fili ta yi mashi, rashin kunya, to
kuma ta wulakanta shi, amma zancenta tsaya ta sauran
ra'ayinshi ma bai taso ba jininsu bai hadu ba ba irin
mutumin da take so ba nc. Amma da ta natsu tana
tunani sai taga idan ba ta so shi ba, ta so wa? Zuciyarta
ta rinka raya mata "Dady." To sai dai da kanta tasan
Daddy ya fi karfinta, wannan shi ake ce me son maso
wani.
Suka gaisa da Hajiya tana yi mata sannu yayin da
direba ya shigo da kayan kalaci ya ashe, sannan ya yi
69
mata sannu, Hajiya ta ce, "Amma dai yanzu jikin ya yi
sauki ko.?" Ta cc, "Sosai ma, tun jiya ban sake jin
zazzabin ba." Hajiya ta cc, "Allah ya kara sauki, bari in
je in samu Likitan ya sallame ki mu koma gida, zaman
asibitin babu dadi." Naja'atu ta cc. "Ya shigo ya
sallame ni, Daddy ya tafi da takarda d ata magani ya ce,
in jira zaku zo yanazu sai mu tafi gida: yana sauri zaya
tafi ofis." Hajiya ta ce, "Au! ya biyo ta na kenan?
Naja'atu ta daga mata kai tana kallonia ta ce, "To ai shi
kenan, kiyi kalaci sai mu tafi." Naja'atu ta ce, "Mummy
idan mun je gida na ji bakina babu dadi ban yi brush
ba." Hajiya ta ce, "To shi kenan tashi ki lallaba mu tafi
kije ki yi wanka kin fi jin dadin jikin." Ta umarci
direban ya dauki kayan da ya shigo da su ya kai cikin
motga ya dawo ya dauki sauran sannan suka fito.
Daga nesa ta hango direban suna magana da
Likitan ta ji haushi sosai, tasan abin-da taki fadi mashi
ne yake tambaya, kuma tasan fadi mashi zaya yi, sai ta
daure fuska ta kauda kai kamar bata gansu cikin
zuciyarta ta ce, "makwakwanci." Da suka isa in da
mota take, tana shirin shiga idanuwanta suka kai
kanshi, a hankali ya dan daga matga hannu yana
murmushi, sai ta sharc shi suka shiga direban yaja suka
nufi gida.
Da ta shiga bata zauna ba, sai da ta yi wanka da
ruwan dumi ta ji dadin jikinta sosai, ta zauna gefen
gadon tana shafa mai. Mas'ud ya kirata ta waya, ta
dauka suka gaisa ta sanar da shi ta dawo gida, kuma
70
jikinta ya yi sauki. Ya yi mata fatan alkairi. Ta rufc
wayar ta ta aje gefe guda, sannan ta ida shiryawa cikin
wata shadda mai jinin kare, siket da riga ta sha aiki
dinkin ya tsaru, dan madaidaici daidai jikinta, Anty
Aisha cc ta yi mata kyautarsu sabbi ne, ta dinka suka yi
mata kadan. Ta yi kyau daidai gwargwado ta gyara
gashinta ta daura sannan ta tuke shi ta tura ciki, ta
maida kallabin kayan ta daura fuskar tasha kwalliya
daidai gwargwado, jikinta ma na kamshi mai sanyi
zuciyarta fes, kamar ba ita ce ta kwana asibiti ba, babu
abin da ke damunta sai dan ciwon da wurin da aka yi
mata karin ruwa yake yi, shi kuma tasan a hankali zaya
daina.
Da ta fito kai tsaye kicin ta nufa, ta hada tea kofi
daya ta dauko biredi ta dawo falo ta zauna tana kalaci.
Mummy ta fito daga cikin daki, tana kallonta sai ta yi
murmushi, har kullum idan Naja'atu ta yi kwalliya
burge ta take yi bata gajiya da kallonta, Allah ya yi ma
yarinyar kyhaun diri, komin munin kaya idan ta sanya
su jikinta zasu karbe ta, insha Allahu ko burinta bai
cika ba, watau Daddy bai aure ta ba, tasan a sannu wata
rana zata samu miji na gani a fada, in da zata huta ta
taimaka wa iyayenta.
Ta shigo cikin falon suka dubi juna da Naja'atun,
sai suka yi murmushi baki daya, Hajiya ta ce, "Da kyau
Naja'atuna, kin yi kyau sosai kamar ba kece kika dawo
daga asibiti ba." Naja'atu ta yi murmushi ta ce "Da na yi
wanke sai na kara jin karfin jikina sosai." Hajiya ta cc
71
"Ai wanke rahama ne, amma tea zaya rike maki ciki?
Ki yi kalaci sosai mana." Ta yi murmushi tana kallon
Hajiyar ta ce "Mummy idan na ce zani ci abinci sosai
amai zani yi sai a hankali zani warware." Hajiya ta
jinjina kai ta cc "Babu damuwa, Allah ya Kara sauki ai
kina kokari." Suka ci gaba da hira Hajiya na kara janta
jikinta, sai ka yi tsammanin ita ta haife ta.
Da aka yi sallar azuhar, Mummy ta shirya ta tafi
unguwa don haka itama ta shige cikin daki ta kwanta
jiya bata yi barci ba sosai, duk a takure ta kwanta, don
haka da ta kwanta ta samu barci sosai, ga shi ta rufe
wayarta don haka babu wanda ya tada ta, Ibrahim ne da
ya taso daga makarantga ya shigo yaga tana barci bai yi
mata magana ba, ya fita to shima Daddyn yau da wuri
ya dawo, tun karfe hudu ya shigo gidan shiru shima
Ibrahim yana cikin dakinshi, ya yi waya da Mummy ta
ce mashi bata gida, don haka yasan itama Naja'atun
tana cikin dakinta, don haka bai takura kowa ba, shi
kadai ya yi hidimominshi ya dan watsa ruwa sannan ya
dauro alwala yayi sallar La'asar ya sanya wando trosser
baki da shirt mai dogon hannu ruwan madara ya dawo
falo ya dan zauna shiru yana duba jarida, sai kuma ya
aje ya nufi taburin cin abinci ya zuba yana ci.
Lokacin itama Naja'atun ta fito daga cikin daki, da
nufin ta samu dan abin da zata iya ci, saboda har yanzu
bakinta babu dadi. Da ta hango Daddy sai ta nufi in da
yake tana murmushi ta ce, "Wai ashe ka shigo, ban ji
ba." Ya zuba mata ido kawai bai san dalili ba zuciyarshi
72
ta cika damuwa da lamarin yarinyar duk sadda ya
kalle ta sai yaga abin da ya burge shi, kwakwarta ta
yi mashi kyau, ya aje cokalin yana kallonta ya ce "An
ya Naja'atu ciwon da kika yi na gaskiya ne.?" Ta
tsaya tana kallonshi da mamaki, ya yi murmushi ya
ce "kin yi kyau ne kamar bake ce kika kwana asibiti
ba." Ta yi dariya ta isa taja kujera ta zauna ta cе
"Mummy ma haka ta ce, ni kuwa ji nake yi duk na
rame jikina babu karfi." Ya ce, "Babu wata rama, sai
dai ki ce rashin karfin jikin."
Ta yi murmushi kawai ta debi abinci kadan tana
ci haka nan ba don dadi ba. Da ya gama shi kuma ya
tashi ya fita, sai ga shi ya shigo da ledoji, ya zube
mata bisa tebur, ya ce "Ga magungunan nan da kuma
karin ciwo." Ta dube shi tar cikin ido, shima ya zuba
mata nashi, ta ce "Don mi ka dora ma kanka wata
wahala haka, ina laifin maganin ma.?" Ya'ci gaba da
kallonta ya ce, "Ni bani tare da wahala, kuma nasan
ba rokona kike yi ba, nine na sanya kaina, ko ba haka
ba?" ta daga mashi kai ya ce "To kiyi mani godiya ko
kuma kiyi shiru." Ta yi murmushi ta ce, "To na gode,
Allah ya kara arzuki, sai dai naga kamar ranka ya
baci, ni kuma gani nayi kudin da yawa." Ya yi
murmushi ya ce, "Amma kinsan wanda ya cancanta
ake yi ma kyauta ko? Haka nan ban ga laifin ki ba,
sai ma burge ni da kike yi idan na yi la'akari da yarda
halayyar 'yan matan yanzu ta lalace, ba ke ba su ba
73
ma roko suke yi kamar zasu shiga aljihun mutum,
idan ma kyautar ka yi masu babu godi bare na godc,
sai ka ce sun ba mutum ajiya, idan ba ki sani ba wani,
lokaci godiyar da kike yi mani, ina jin dadi shi yake
nake yawan yi maki kyautar, idan naji kina yi mani
godiya, burge ni kike yi sosai, wannan shi ne halin
dattaku da kawaici."
Naja'atu ta jinjina kai, ta ce "To ai godiya ba,
saboda Mummy da abin da ta ke yi mani zani iya
gode maka ai duk dan halak ya san an yi mashi." Ya
ce "Haka ne, yanzu yaya kike jin jikin.?" Ta ce "Jiki
Alhamdulillahi, ya yi sauki sosai." Ya ce, "To idan
kin gama cin abincin ki fara shan maganin gaya nan."
Ta jinjina kai, yayin da shi kuma ya koma cikin falo,
ya dauki jaridarshi yana dubawa, itama da ta gama
nan ta dawo har da Ibrahim suna hirarsu a mutunce.
Yamma ta yi sosai, Mummy ta dawo suka tarbe
ta tana tambayar jikinta, ta ce ya yi sauki, ba ta zauna
ba kowa ya nufi Sallah, magariba ta gabato. Karfe
takwas kowa ya dawo falon suna nan ana ta hira har
da Mummy, maigadi ya kwankwasa kofa, Ibrahim ya
tashi yaje ya bude ya ce mashi, wani bako ne yake
son ganin Naja'atu." Ibrahim ya saki labulen ya dawo
ya zauna, ya ce, "Anty Naja wai bako ne kika yi."
Wuta ta dauke mata, ido cike da tuhuma, itama
Hajiyar kallonta take yi tana murmushi, ta ce, "Waye
ke nemanki Naja'atu.?" Ta kalle ta a marairaice, ta ce
74
"Nima ban san shi ba." Hajiya ta dubi Ibrahim ta ce,
"Je ka gano waye.?"
Ibrahim ya tashi ya fita, ita kau Naja'atu kamar
ruwa ya cita, ga Daddy ya hada rai sosai bata san
abin da yake nufi ba, koda bata san mai kiran ba,
tasan ba ya wuce Likita, idan ba shi ba bata san kowa
ba. Ibrahim ya dawo yana dariya ya ce, "Ok, Doctor
din nan ne da ya duba ki jiya." Daddy ya dube shi a
fusace ya ce, "Je ka kace mashi bata zuwa." Hajiya ta
dube shi da sauri ta ce, "Don mi? Wannan ba mutunci
ba ne, ina laifin wanda ya taso takanas yazo in da
kake, kuma kasan abin da ke tafe dashi?" Daddy ya
yi sukuti, Hajiya ta dubi Naja'atu ta ce, "Tashi kije ki
ji abin da ke tafe da shi wulakanci babu kyau."
Kamar zata nutse don kunya, haka nan ta daure
ta tashi, idan bacin kada Hajiyar ta ce "ta watsa mata
kasa a ido ita kam da ra'ayin Daddyn ta bi ba za ta
fita ba, to sai dai bata son yi ma Hajiya gardama, don
haka ta shiga cikin daki ta dauko mayafi tazo ta raba
su ta fita. Yana zaune cikin harabar gidan bisa kujerar
roba, kananan kaya ne jikinshi, sun fito da sigar
kyaunshi kamar koda yaushe fuskarshi dauke da
murmushi, sai ta ji zuciyarta ta dan yi sanyi ba zata
iya wulakantashi ba, Mummy ta yi gaskiya da ta ce
"Babu kyau wulakanci, to ita kam kwarjininshi ma ba
zaya bari ta samu kafar fadi mashi komi ba.
75
A hankali take tafiya