nata ya canza, tun a lokacin ya fara
dasa ma zuciyarshi kaunarta, lokacin ta gama karatun
sakandire tana shirin ci gaba da karatu. Wayewarta da
komi sun karu, don haka bai ji shakkar fadi mata sirrin
zuciyarshi ba, a wani dare da suka kawo masu ziyara
tare da mahaifiyarta, lokacin yana shirye-shiryen
komawa, kuma bai samu matsala ba, Farida ta amince
da bukatarshi, a take suka daukar ma kansu alkawurra
da dama.
Satinshi uku da zuwa, ya tarkata ya koma London,
ya ci gaba da karatunshi, da farko yakan dan samu
matsala wajen rashin jin komi daga gare ta, amma da
wayar hannu ta yawaita sai ya samu sauki yana hira da
ita koda yaushe yana sane da komi nata, kuma itama
Farida ta rike alkawari, duk irin gwagwarmayar da take
yi a makaranta ba ta yarda ta yada alkawari ba, ta tsaya
kan Daddy dinta bata sauraren samari, matsalarta daya
46
miahaifinshiatana karkashi ta haka ne suka san juna ita
dida Mummy suna mutunci sosai, idan tazo gidansu tare
didå Farida da kannensu yama janta wasa, sabodá lokacin
didaataná karama ta yi kyau sosai ga baki tana da yawan
surutukdon hakaatakel da farin jini wajen mutanc, duk
wanda yazauna da ita cikin dan lokacisaieta shiga
ranshil da irin haka ne suka saba da ita cikin fan lokaci
ssaistaishiga ranshil daririn haka ne suka saba da Daddy,
ididantsuka zo gidan koda yaushe tana wajenshi yana
ishalawar abubuwanata Iokuta da dama idan suka zo ba
ata atafiya sai ta yi kwana biyu a gidan, Hajiya ma na
sonta, yauda gobe da ta yi girma ne ta rage zuwa gidan,
amma dole da haka akwai fahimtar juna tsakanin zuri'ar
biyu, mahaifinta matukin jirgin sama ne.
Lokacin da girma ya farfa zo ma Farida ne ta fara
muna jink kunyar Daddy shik kuma hakan yaddauki
hhankalinshi ya fara nuna ra'ayinshi akanta, Hajiya na
lura datshi da ta tsare shi tana tambayarshi bai ji kunya
iba, ya fito fili ya sanar da ita da gaske yana sonta, kuma
cin Allah ya yarda ita ce matar. Hajiya dariya ta rinka yi,
saboda tana ganin abin har da yarinta, amma a hankali
yau da gobe sai ga soyayya ta fara kafuwa tsakaninsu,
to gaskiya lokacin ta tsorata ganin cewa su duka basu
kaiwwani matsayihba da/za'a ce tsun maidak kaioga
soyayya irin haka don haka ta gargadi Daddy da ya bi a
sannu saboda Farida yarinya ce, a kalla su duka akwai
karati gabansu, bai dace ace sun tsaya wata soyayya ba,
445
to Daddy ba ya da taurin kai don haka ya bi umarnin
mahaitiyarshi ya yi kokarin kauda abun a ranshi.
Lokacin da yake shirin fita karatu duka Farida na
aji daya na babbar sakandire SS1, don haka basu tsaida
wata kwakkwarar magana ba, ya tafi. Duk lokacin da
suka yi magana da Hajiya yakan tambayi labarin
Farida, Hajiya dauriya take yi ta ce tana nan lafiya lau."
Shekararshi biyu da tafiya, Allah ya yi ma mahaifinsu
rasuwa, sakamakon wani mummunan hadari da suka yi
kan hanyar Katsina zuwa Abuja, to lokacin ne ya samu
zuwa gida, ya yi mamaki kwarai da ya ga girman da
Farida ta yi, komi nata ya canza, tun a lokacin ya fara
dasa ma zuciyarshi kaunarta, lokacin ta gama karatun
sakandire tana shirin ci gaba da karatu. Wayewarta da
komi sun karu, don haka bai ji shakkar fadı mata sirrin
zuciyarshi ba, a wani dare da suka kawo masu ziyara
tare da mahaifiyarta, lokacin yana shirye-shiryen
komawa, kuma bai samu matsala ba, Farida ta amince
da bukatarshi, a take suka daukar ma kansu alkawurra
da dama.
Satinshi uku da zuwa, ya tarkata ya koma London,
ya ci gaba da karatunshi, da farko yakan dan samu
matsala wajen rashin jin komi daga gare ta, amma da
wayar hannu ta yawaita sai ya samu sauki yana hira da
ita koda yaushe yana sane da komi nata, kuma itama
Farida ta rike alkawari, duk irin gwagwarmayar da take
yi a makaranta ba ta yarda ta yada alkawari ba, ta tsaya
kan Daddy dinta bata sauraren samari, matsalarta daya
46
cc da ta biye ma kawaye tana shafe-shafen mayuyyuka
na bleching da suka canza ma ta fuska baki daya, haka
nan 6angaren sutura ma wani dinkin har da na banza ta
kara gashin kanti babu kwaba nan kawai take da
matsala wanda ita Mummy take ganin har da laifin
iyayenta.
Gwagwarmaya cikin kawaye ta sanya idanuwanta
suka bude, wayewar har ta yi yawa, da yawa dabi'o'inta
na Turawa ne, Ibada kanta ba ta dami Farida ba, sai ta
yini zaune ba ta yi Sallah ba, kuma ko ajikinta, lokacin
da Daddy ya dawo, Hajiya ta zuba ido taga matakin da
zaya dauka kan yarinyar, amma sai taga ya rufe ido,
sun fada kogin soyayya ba-ji ba gani, da bakinshi yasha
fadi mata Farida kadai yake so, kuma ita za ya aura,
abun da daure kai, duk wani abubuwa da take gani ba
masu kyau ba ne, sai taga shima su yake so suke kara
daukar mashi hankali. Ya rikice akan Farida. Da ta yi
mashi magana, sai ya ce "Babu komi Mummy ni dai ina
sonta haka." Yarda taga ya rikice ta yi imanin komi zata
yi ba zata iya raba su ba, sai taga kara ta rabu dasu ayi
ya fiye mata alkairi, kada su dauko mata abin fadi a
gari, amma 'yan'uwanshi kansu, A'isha da Fatima ba su
yi na'am da yarinyar ba, don dai Hajiya ta ce su yi
hakuri su rabu da shi. Ita kau abin da take dubawa duk
cikin irin mutanen da mijinta ya yi hulda dasu ita kadai
ke biye su ta damu dasu, bai dace ta yi mata haka ba.
Duk da cewa ta hakura akwai wasu halayen
Farida da ta tsana a ranta, wadanda ba al'adunmu ba ne,
47
Hausa Fulani, rashin kunyarta da rashin kawaici yana
damunta, lokuta da dama ita ke zuwa wajen Daddyn ba
wai shi ke zuwa ba, idan tazo sai ta yini kuma cikin falo
suna hira, bata jin kunyar nuna mashi so ko gaban
waye, dole sai dai Hajiya ta shiga daki ta bar masu
falon. To ire-iren abubuwan da. suka sanya ya fara
tsanar yarinyar kenan, yanzu kuma da ta ke zaune da
Naja'atu tana lura da takunta da halin dattaku, sai take
ganin irin macen da ta dace ta zamo surukarta kenan ba
wai Farida ba, ko ba komi Na'ajatu akwai asali da halin
kwarai, haka nan idan ma biyayyar aure ce yarda zata
bi shi, Faridar ba zata yi mashi ba, don haka ta fara
addu'ar Allah yasa hankalinshi ya karkato kan
Naja'atun, ta yi tuwona maina, zata fi samun kwanciyar
hankali da natsuwa, to gashi shi kuma ya watsa mata
kasa a ido, yaya zata yi kenan?.
Kwana biyu tsakani, ranar asabar Hajiya ta wayi
gari bata jin dadi, da Naja'atu ta fito ta kwankwasa
kofar dakinta, sai ta murda ta shiga, tana gaida Hajiya
ta amsa da kyar, Naja'atu ta tsaya tana mamaki, ta ce
"Mummy lafiya.?" Ta ce, "Wallahi bani jin dadi
Naja'atu, na kira wayarki tun dazu ki zo ki shafa mani
magani a kafata wayar a rufe." Naja'atu cikin damuwa
ta ce, "Sannu ban bude wayar ba ne." Ta iso in da
Hajiyar take ta ce, "kafafuwan ne kadai ke ciwo." Tа
ce, "Har da zazzabi, dauko maganin gaya can ki shafa
mani a kafafuwan." Naja'atu ta dauko maganin Cream
ne ta tsugunna tana shafa ma ta tana murzawa yana
48
shiga, Hajiya ta rumtse ido tana jin maganin yana
shigarta, sai da ya bi sosai, ta dan ji sauki sai ta ce ta
bari haka nan taje ta kirawo Daddy ya sawo mata
maganin da zata sha.
Ta fito da sauri ta isa kofar dakinshi ta dan
kwankwasa ya ce "Waye?" ta ce, "Naja'atu ce." Ya ce
"Bude shigo." Ta murda kyauren ta shiga, taga dakin
ya tsaru, yana kwance kan gado, da allon kwamfuta
gabanshi ga alama akwai abin da yake yi saboda ga
takardu nan zube kusa da shi." Ya zuba mata ido yana
sauraren abin da zata ce, ta ce "Ina kwana.?" Ya ce,
"Lafiya lau Naja'atu, lafiya dai ko.?" Ta ce "Lafiya lau,
Mummy bata jin dadi, ita ta ce in kira ka ka sawo mata
magani." ya ci gaba da kallonta, ya се "Mе ke
damunta.?" ta ce "Kafafuwanta dai take kuka dasu, to ta
ce har da zazzabi." Ya jinjina kai ya ce, "Shi kenan gani
na fitowa." Ta juyo ta fito ta koma dakin Mummy ta
sanar da ita yana zuwa. To sai Hajiyar ta ce, ta ci gaba
da murza mata kafafuwan, don haka ta koma ta
tsugunna tana danna mata a hankali.
Ya murda kofar ya shigo, idanuwanshi na kan
Hajiya ya ce "Mummy baki jin dadi.?" Ta ce, "Wallahi
kuwa Daddy jiya ban yi barci ba, ciwon kafar nan ne ya
dawo, sai dandaka suke yi ga zazzabi, kuma ina jin
jiri." ya ce, "Sannu Allah ya sauwake, to amma
Mummy ba kara muje asibiti ba.?" Ya zuba mashi ido
ta ce, "Yanzu.?" ya cc, "Eh, kara muje tunda rana ta yi,
ya fi ace aita magani haka nan." Hajiya ta ce, "Shi
49
kenan." Ya cc, "To ku shirya, bari in duba motar." Ya
fan kalli Naja'atu yayin da ita kuma ta mike ta bude
wardrof ta fiddo ma Hajiya kaya, sannan ta dawo tana
taimaka ma Hajiyar zata tashi. Sai ya yi murmushi yana
jin dadin yarda yaga tana nuna damuwarta da kulawa
ga Hajiya.
Naja'atu na rike da Hajiya, suka shiga kewaye ta
yi brush, sannan suka fito ta taimaka mata ta shirya,
sannan ta barta nan ta shiga dakinta ta sanya hijab dan
Karami fari, ta fita waje ta samu Daddy, ta ce "Ka gama
mu fito.?" Ya ce, "Eh." Sai ta dawo ta kamo Hajiyar
kafar nayi mata ciwo sosai, don haka da kyar take
takawa, Naja'atu ta rinka lallabata har suka- fito waje,
Daddy ya bude motar sannan ya taimaka mata ta zauna
cikin motar, ya rufe ita kuma Naja'atu ta zauna gaba
gefenshi yaja suka tafi.
Asibitin da suke zuwa ya kai ta, ya shigar da
katinta aka fiddo fayil din ba babba sannan suka bi
layin Likita, da yake sun fito da sauri basu yi zama
sosai ba, layi yazo kan Hajiya shi da Naja'atu suka
kama ta suka shiga, Likitan fan kabilar Igbo ne, ya
saba da Hajiya, ya san matsalarta, don haka bai tsaya
wasu tambaye-tambaye ba, ya shiga duba ta. Sai dai da
ta sanar da shi matsalar da take samu ta jiri, sai ya
gwada jininta nan ya samu ya hau sosai, ya yi mamaki
tunda yasan Hajiya bata da matsalar hauhawan jini, ya
san dai yakan dan yi sama amma ba wai na matsala ba
irin haka. 50
Ya rinka yi mata tambayoyi yana son ya ji dalilin
hawan jinin nata, shima Daddy mamaki yake yi, ya
zuba mata ido cike da mamaki, ya cc, "Mummy me ke
damunki haka, baki sanar da ni ba, har gashi za ki samu
matsala?." Ta girgiza kai ta cc, "Babu wani abu da nake
6oyc maka Daddy, matsalar hawan jini yanzu ta zama
ruwan dare, kananan yara ma yanzu jininsu hawa yake
yi. Su meye matsalar su.?" Daddy ya zuba mata ido, shi
kam ya shiga damuwa, baya son yå ji an ce wani abu
yana damun Hajiyarshi, to ganin haka ya sanya Likitan
da kanshi ya rinka kokarin kwantar mashi da hankali,
ya ce, "Kada ya samu damuwa, yawan shekaru ma yana
-janyo hauhawan jini, kuma ba wai ya kai matsayin da
ba za a iya magance shi ba ne, idan dai za'a kiyaye
ka'idoji to zata komo normal, don haka zaya kwantar da
ita ta samu a kalla awa ashirin da hudu tare da su, tana
samun kulawa insha Allahu zata warware.
Sai lokacin ya dan samu kwanciyar hankali, ya
zuba ma Naja'atu ido, itama hankalinta ya tashi tana
kallon Hajiyar cike da damuwa, da ta dube shi sai suka
yi murmushi. Likitan ya danna kararrawa, Nas ta shigo,
ya bata umarnin ta taimaka Naja'atu su shiga da Hajiya
daki, yayin da Daddy ya tsaya yana jiran a ba shi
takardar sayen magani.
Lafiyayyen daki aka basu mai kyau, gado biyu da
kujeru uku ciki, sai talabijin da firij ga kewaye a cikin
dakin, ko'ina fes-fes babu kazanta, Hajiya ta kwanta
kan gado Naja'atu nayi mata sannu, suna nan sai ga
51
Daddyn ya shigo da magunguna ya sawo. Naja'atu ta ce
"Amma fa bata yi kalaci ba." Ya ce, "Ko.?" Ta daga
mashi kai, ya сe, "To yanzu yaya za'ayi.?" Naja'atu ta
zuba mashi ido, tana jiran taji abin da zaya ce, sai ya
ciro waya daga cikin aljihu ya kira Aisha, yana yi mata
bayanin halin da suke ciki, yace ta taho da ruwan zafi
da kayan tea, ta fara shan ko tea ne." Ta cc, "Su jira ta
tana nan isowa yanzu." Don haka suka ci gaba da zama
tare da Hajiya, Naja'atu na danna mata kafar yayin da
kuma Daddy yake zaune bisa kujera, idanuwanshi kan
Hajiya cike da damuwa.
Lokaci-lokaci ya kan kira A'isha ya sanar da ita
suna jira, to ita ma iya bakin kokarinta take yi, ta
tabbatar mashi cewa tana bisa hanya. Da ta iso ta kira
shi ta waya, ya fita ya same ta cikin mota sai ta dauki
danta karami Yazid, ita kuma ta dauko kayan tana
tambayar shi, abin da ke damun Hajiya. Ya ce, "Ciwon
kafar nan ne dai, to wai kuma yanzu mun zo da Likitan
ya auna jininta sai ya ce ya hau ban san me ya janyo
hakan ba." Cikin damuwa Aisha ta ce, "kasan halin
Mummy, abu kadan sai ya dame ta, kuma bata yin
magana sai ta barshi a cikinta." ya ce, "To amma Aisha,
menene zaya damu Hajiya wanda ba za ta iya fadi mani
ba?"
Da haka suka iso cikin dakin, Aisha ta aje kayan
ta isa tana yi ma Hajiyar sannu. Ta dubi Naja'atu ta ce
"Sannu Naja." Suka gaisa tana tambayarta jikin
Hajiyar, Naja'atu, ta ce "Da sauki." yayin da ta tashi
52
taje tana hada ma Hajiya tea, da ta kawo Aisha, ta amsa
ta mike sannan ta zubo dankali ta kawo mata, tana ci su
duka kowa yana nuna kulawarshi ga Hajiya, sai ta rinka
jin tausayinsu, sun damu kwarai. Da ta koshi ta ce "Ya
isa." Sai Daddy yaje ya kirawo Likitan ya nuna masu
yarda za'ayi amfani da magungunan. Naja'atu ta amshi
na shafawar tana shafa mata, yayin da A'isha ta rinka
bata na shan.
Cikin dan lokaci kadan, barci ya fara dibarta, ba'a
jima ba ta samu barci. Daddy ya dubi Naja'atu yacc
"kinyi kalaci kuwa.?" Sai ta yi murmushi ya ce, "Matso
mana da shi muyi, nima yunwar nake ji, don haka suka
zauna suna kalacin har da A'isha, itama ta ce tashinta
kenan taji wayar Daddy. Karfe daya yace zaya je gida
ya yi wanka ya dawo. To itama Aishar sai ta ce zata je
gidan yara sun kusa tasowa makaranta, zuwa anjima
zata dawo, tare suke fita aka bar Naja'atu tana kula da
Hajiya, to har zuwa lokacin barci take yi cikin
kwanciyar hankali saboda maganin data sha akwai mai
sanya barci..
Da ya. dawo da yamma Hajiya ta tashi kuma
akwai alamar sauki kafar ma ta ce da sauki, zaune take
suna hira, hankalinsu ya dan kwanta, Daddy ya rinka
lallaßata, bai son ciwon Hajiya ko kadan. Wayarshi ta
yi kira, Farida ce ta dauka suka gaisa yana yi mata
bayanin cewa yana asibiti ne, Mummy bata jin dadi ta
jajanta mashi ta ce zata fito ta duba ta ya gaida ta. Da
ya rufe wayar ya juya yana sanar da Hajiya sakon
53
Farida. Ta yi murmushi ta ce, "Ina amsawa." A hankali
ya sauke kwayar idonshi akan Naja'atu, yanayin ta ya
dan canza, amma ta rinka kokarin sakin ranta, bai се
mata komi ba, ya jefa wayar cikin aljihu, suka ci gaba da hira.
Da daddare Farida tare da Kawarta Zainab da
Kanneta biyu suka zo cikin matar Mamansu, ita ke jan
motar. ta kawo ma Hajiya kayan ci da lemuna iri-iri.
Tunda suka shiga taga Naja'atu, sai ta dauke kanta, ko
kallon sashin da take bata yi ba, kai tsaye ta nufi wajen
Hajiya tana gaida ta tare da tambayar jikinta. To ita
Naja'atu, ta iya jan ajinta, sai ta share ta suka gaisa da
Zainab, bata sake kula su ba suka ci gaba da magana ita
da Ibrahim, amma cikin zuciyarta mamaki take yi sosai,
bata san daukar da yarinyar ta yi mata ba, ko kishiyarta
ce sai haka ta cika nuna jin zafi da tsana akanta, to
kuma sai aka yi dace tun farko dama itama bata
ra'ayinta.
'Yan mintuna kadan suna cikin dakin da taga ba
tafiya zasu yi ba, sai ta yi ma Ibrahim magana suka fito
daga cikin daki, suka zauna cikin wani dan falofalo,
suna hirarsu, amma fa ta ji zafin abin da Faridar ta yi
mata, tunda tana ganinta sai da kalle ta tsab cikin ido
sannan ta dauke kanta, ai ko ba komi tunda ita tazo inda
take ita ce ya dace ta fara yi mata magana ba wai ita ta
yi mata ba, sannan wani abu da ya dan taba mata
zuciya, shi ne yarda ta lura Daddy na rawar jiki akanta,
ita kam bata ga abin so ba kila har da haka ya sanya
54
take yi mata kallon banza, ta tabc baki ta danja tsoki."
Ibrahim ya zuba ma ta ido ya ce, ke da wa Anty Naja?
Ta ce "Waccan sakaryar Faridar, sai tai ta daga ma
mutane kai sai ka ce tafi wani, jaba fa yanzu ta shigo ta
same mu, amma ba zata yi ma mutane magana ba, tana
tsammanin mu zamu fara yi mata.?"
Ibrahim ya yi murmushi ya ce, "Share da wannan
Anty Naja, ni dama ko ta yi mani magana tasan ko
kallo bata ishe ni ba, kila fushina ne ya shafe ki."
Naja'atu ta yi murmushi, amma ita tasan dalilin wannan
fushin da take yi, tsammani take yi Daddy zaya iya
cewa yana sonta, ba komi ne matsalarta ba, illa zafin
kishin kuma taji da abinta. Suna nan zaune sai gasu sun
fito har da Daddyn, Farida ta dauke kanta, sai Zainab се
ta yi masu sallama, to wani karin haushi shi Daddyn sai
ya tsaya yana kallon Naja'atun, ya ce, "Wai nan ku ka
dawo.?" Ta kalle shi kawai, ya juya yana kallon Faridar
dake tafiya ko juyowa ba ta yi ba, bai yi mata magana
ba, ya ce ma Naja'atu, zo muje ki raka ni ayi masu
rakiya."
Ta dube shi cikin sigar nuna kin jinin abu, ta ce,
"Daddy na gaji da yawa, kaje kawai sai ka dawo." Ya
zuba mata ido bai yi magana ba, ya tafi. Sai da suka fita
sannan su Naja'atu suka koma cikin dakin. Karfe tara
da Likita ya dawo ya duba jikin Hajiyar sai yaga jininta
ya sauka sosai, don haka ya ce zasu iya tafiya gida
amma ta kula da shan magani bisa ka'ida, haka nan ta
rage cin gishiri, ta kuma cire damuwa a ranta. Hajiya ta
55
ce, ita ba wani abu da ta sanya cikin zuciyarta, ya ce shi kenan Allah ya kara sauki, bayan kwana biyu zata iya dawowa ta duba jikin.
Bayan ya fita, Naja'atu ta shiga hada 'yan kayan da suka aje, amma ko kallon ledar da Farida ta kawo
bata yi ba, Daddy na lura da ita sai ya yi murmushi ya
girgiza kai ya rasa matsalar yaran kö kadan Farida bata
son Naja'atu, har fadi mashi ta yi tana kishin ta ko
yanzu da suka fita sai da ta yi mashi korafi akanta, to
ya lura ita kanta Najar ba damuwata yi da Faridar ba,
kamar dama da azazjiya tsakaninsu. Shi ya dauki ledar
ya ce, "Naja'atu ta dauko sauran kayan suka suka kai
cikin mata, sannan ta dawo ita da Ibrahim suka kuma
Hajiya, suka tafi.
Kwana biyu suna jinyarta, Naja'atu ta yi tsayin
daka kan kula da ita, magani akan kari bata bari lokaci
ya wuce, haka nan na shafawa koda yaushe cikin
hidimarta take, idan Aisha ta zo duba Hajiya tana
yabawa kwarai saboda wani abu ne da ya dace ace ita
zata yi shi, Naja'atun ta dauke mata gaskiya tana jin
dadi sosai kuma, tana gode mata, to shi kanshi, Daddyn
sai ya ji yarinyar ta kara shiga ranshi ta nuna tana da
wayau, yana lura da ita damuwarta har ta fito fili, ko
zama suka yi falo ba'a dadewa zata tashi ta shiga cikin
daki, ta duba ta sannan ta dawo ta zauna. Irc-iren
abubuwan da take yi suka sa ma mata matsugunni cikin
zuciyarshi, yanzu kam ya amince yana kaunar Naja'atu,
matsalar dai kawai ba zaya iya barin Farida ba saboda
56
ita kaunar Farida daban ce, cikin zuciyarshi ta ratsa duk
wani sassan jikinshi kai shige ni ma yake yi ba zaya iya
yin gamsasshiyar rayuwa ba idan ba dda ita ba, don
haka dai ya yi tsayin daka akanta.
Ranar Litinin da ya fita aiki, sai yamma ya dawo,
kamar kullum ya shigo gidan shiru bai ji motsin kowa
ba, ya rinka sallama bai ji an amsa ba sai ya zauna
falon yana hutawa, aikin su ya cika tsanani, babu hutu
sai zuwa can Hajiya ta fito daga cikin daki ta ce,
"Daddy ka dawo?" Ya ce "Wallahi kuwa, ina ta sallama
shiru, Naja'atu fita tayi ne.?" Hajiya ta cc, "Naja'atu na
daki kwance ba lafiya." Ya dubi Hajiyar da sauri ya ce
"Me yake damunta.?" Hajiya ta ce, "Zazzabi ne tun
dazu amai take yi don haka ta galabaita sosai, na cc ta
fito direba ya kaita asibiti ta kiya, wai bata son allura."
Sai ya jinjina kai ya tashi yaje ya kwankwansa kofar
sannan ya shiga yayin da Hajiyar ke biye da shi, suka
tsaya kanta ta kudundune tana rawar dari, Hajiya ta dan
bude jikinta ta ji ya yi zafi sosai, su duka suka rinka yi
mata sannu.
Daddy ya ce, "Sannu Naja'atu shirya sai mujc
asibiti ba zani bari ayi maki allura ba." Ta dube shi a
sanyayc idanuwanta sun kada sun yi jajir, sai ya ji
tausayinta ya rinka yi mata sannu, shi da Hajiya suka
hadu suna lallashinta akan ta yarda su tafi asibiti, to
gaskiya ganin yarda Hajiya ta damu ne ya sanya ta
yarda, ta tashi zaune Hajiya ta kama ta zuwa bayi,
amma ta kasa taba ruwa sai da ta zuba ruwan dumi,
57
sannan ta wanke fuskarta ta fito Hajiya ta bata tafkekiyar suwaita ta sanya suka fita tare da Daddy.
Cikin motar ma baya ta kwanta, sanyi ya rinka kada ta, don haka ya Kara sauri suka isa asibitin,
Likitan da suka samu Bahaushe ne dan asalin jihar
Kano, Dr. Musa ya amshe su hannu bibbiyu duk abin
da ya dace ayi mata yayi, sai dai Naja'atu ta kafe kan
cewa bata son allura, don haka Likitan ya maida duka,
magani ban da allura to sai dai da ya lura da yanayinta,
jikinta ya yi laushi sosai saboda aman da ta yi, sai yace
ta yi hakuri sai an kara mata ruwa. Naja'atu duk tabi ta
damu, Likitan da Daddy suka taru suna bata hakuri,
amma ta kafe sam bata so lallai tana tsoron allura har
hawaye ta rinka yi masu.
Daddy ya dubu Likitan ya ce, "Doctor ka janye
maganar karin ruwan shi kenan, tunda bata so." Likitan
ya yi murmushi ya ce, "Ba ka son uwargida ta wahala
ko.?" Daddy ya lumshe ido yana murmushi, sai ya
sauke kwayar idonshi akan Naja'atu, ita kuma ta daurc
fuska ta dauke kanta yayin da Likitan ya ci gaba da
cewa, "Hakuri zaku yi idan da na san karin ruwan ba
dole ba nc, tun farko ba zani fara rubuta shi ba, to nasan
ko na bi son ranku na barku kun tafi to fa zaku dawo
ne, matukar tana so ta smau karfin jikinta." Daddy ya
jinjina kai yana kallon Naja'atu, sai ya ciro waya ya kira
Hajiya yana yi mata bayani. Hajiyar ta cc, "A bata
Naja'atun." Ya mika mata wayar ya ce "Ga Hajiya." Sai
ta amsa, amma kafin tayi magana ta fara shesshekar
58
fi
kuka. Hajiya ta ce, "Naja'atu ba ki son lafiyarki ko? Kin
son kiyi ta fama da ciwo, ta ce "A'a" Ta ce, "To kiyi hakuri duka awa nawa nc za'ayi a gama.?" Та се
"Amma fa ni Mummy ba znai kwana asibiti ba." Hajiya
ta yi dariya ta ce "Ba za ki kwana ba, yau za ki dawo." Ta ce "Shi kenan."
Sai ta mika ma Daddy wayar tana kallon Likitan a
tsorace, su duka suka rinka yi mata dariya. Ta daure fuska sosai haushin Likitan take ji.
An sanya mata ledar farko, Daddy ya ce, zaya jc gida ya dawo ta ce, "Babu matsala ya je." Yana fita ta kara ruwan yana shiga da sauri bata son dare ya yi ace
ta kwana asibitin. Bai fi awa daya ba, ledar farko ta kare, don haka aka sanya mata ta biyu. Nas din ta rinka yi mata fada, akan budewar da tayi yana shiga da sauri, don haka yanzu da ta sanya ta biyun sai ta zauna tana
kula da ita. Har aka yi sallar magariba Daddy bai dawo ba, to bata ga laifinshi ba, tasan ko abinci bai ci ba, ga
kuma lokacin sallah ya yi. Ta kwanta shiru ita daya zazzabin ya fara sauka, yanzu zufa ke ta barko mata don haka ta yi ma Nas din magana ta kunna mata fanka
tana yi a hankali.
Likitan ya shigo, dogo ne sosai, fari yana da bille
a gefen fuskarshi yana da sakin fuska babu laifi ya duba yarda ruwan yake tafiya, yana tsokanarta ya ce, "Saura
allura ko.?" Naja'atu ta daure fuska ba ta son ta ji anyi
maganar allura. Sai ya jawo kujera ya zauna gaban gadon ya ce "Mutumin da ku ka zo tare yayanki ne ko
59
maigidanki.?" Ta zuba mashi ido tana son ta ji dalilin
wannan tambayar, sai ta girgiza mashi kai ta cc.
"Yayana ne." A hankali ya sauke kwayar idonshi
akanta yana murmushi ya ce, "Har kin sanya hankalina
ya kwanta." Naja'atu ta ji zuciyarta na bugawa da sauri
"Me mutumin nan yake nufi.?" Ta zuba mashi ido ta cс
"Da aka yi mc.?" Ya ce mc kila nine zani zama
maigidan idna dai kin yarda." A hankali ta sauke
Kwayar idonta kasa, sai ta lumshe ido tana wani tunani,
anya kaunar Daddy zata barta taso wani da namiji а
rayuwarta." Ba ta ce komi ba yayin da Likitan ya mikc
yana shirin tafiya, ya ce