yi fushi ba." Ya
zuba ma Faridar ido, ya cc, "Wai haka ne.?" Ta dan
tsuke bakinta, tana yatsuna fuska ta cè "Ban ce ba." Ya
ce "To ki zuba abinci ki ci, ai ba bakuwa ba ce, idan
kuma laifi nayi kiyi hakuri." Ya zuba mata ido da sigar
zolaya, sia ta yi murmushi ta zuba abincin dan kadan ta
ci. Naja'atu dai bata sake sanya masu baki ba, har ta
gamaci, ta tashi ta basu wuri. ta dawo cikin falo ta ta
zauna. Sai ga Ibrahim ya shiga lesson ya tafi tun safe,
nan ya zauna suna hira, sai da su Daddy suka gama
sannan ya tashi ya nufi cin abincin.
To suma ko da suka dawo, basu dade da zama ba,
Farida ta ce, "Tafiya zata yi." Ya dubi Naja'atu ya ce,
"Shiga ki gaya ma Mummy Farida zata tafi." Ta tsaya
kawai tana kallonshi, sai ka ce yarinyarshi, amma ita
kanta ta kagara yarinyar ta tafi, sai wani cika take yi
tana batsewa, don haka ta shiga cikin dakin Hajiya ta
sanar da ita, daga nan ta fito da kwanonin da ta ci
abinci, ta nufi kicin. Sai da suka fita sannan ta dawo
suka ci gaba da hira ita da Ibrahim.
A can kuma suna fita waje, Farida ta daure fuska
sosai, Daddy ya zuba mata ido, ya ce, "Wai me yake
33
damunki, tun dazu naga kin canza.?" Ta dan zobari
baki, ta ce, "Daddy kasan ina da tsananin kishi a kanka
ko? Ya ci gaba da kallontga ya ce, "Uhm." Ta ce, "To
gaskiya bani jin dadin yarda naga kana jan yarinyar nan
da wasa.?" Ya saukar da ajiyar zuciya ya ce "To me
hakan yake nufi.?" Ta ce, "Shi ne ban sani ba, amma ni
na san matsawar ku ka ci gaba da tafiya haka, wani abu
zaya iya biyo baya." Ya ce, "Kamar me.?" Itama ta
zuba mashi ido, ta ce "Wannan kai za'a tambayà." Ya yi
murmushi ya ce, "Dadina dake kenan Farida, kin cika
zargi da kawo abu a ranki, yarinyar nan 'yar'uwata ce
ko." Ta ce "Amma kuma ba cikinku daya ba." Ya
jinjina kai-ya ce, "Haka ne.?" Sai dai abin da na ke so ki
fahimta shi ne, abin da ke ki ke tunani ba zaya taba
faruw ba, zuciyata ke kadai take so, sannan yarinyar
nan ina jin duka jiya ne ma muka fara magana da ita,
tun a Katsina fada muke yi, sannan ba zaya yiwu ba ace
muna zaune gida daya kuma 'yar'uwata ce, amma ace
ba mu magana tsakaninmu, Mummy ba zata ji dadi ba,
kuma itama yarinyar ba zata sake ba, don haka ki kaga
ina shiga harkarta, ba wai don wani abu ba."
Ta ce, "Amma kai kanka kasan abin da ka yi dazu
ba ka kyauta ba.?" "Da na yi me.?" Ta ce, "Yarda ka
rinka janta da wasa a gabana har da daukar abincinta."
Ya yi murmushi ya ce, "Har yanzu dai kin kasa fahimta
ta, Farida akwai wani abu a tare da Naja'atu da nake
so.?" Ta dube shi da sauri, ya ce, "Ba wai ina nufin
wani abu daban ba ne, tana da saurin fushi ne don haka
34
ki ka ga ina janta, don kawai ta yi fushin." Ta dan cije
lefenta tana jinjina kai, ba ta ce komi ba, ya yi mata
rakiya da nisa babu nisa zuwa gidansu cikin unguwar
daya ne, duk da haka dai Farida ba ta sa ki fuska ba
sosai, ita dai tana zargin wani abu to shima bai sake
tada mata maganar ba, suka yi sallama ya yi mata
godiya kan zuwan da ta yi yima Hajiya sannu da zuwa.
'Yan kwanaki kadan Naja'atu ta warware cikin
Abuja, koda yaushe tana like kicin tare da Mick tana
koyon girki kala-kala, tun Hajiya na yi mata fada akan
ta rinka zama tana hutawa, har ta gaji ta rabu da ita, to
sai ta samu littafi duk girkin da aka yi wanda ya burge
ta zata rubuta. Tana jin dadin zaman gida, babu in da
Hajiya ta rage ta idon zata fita unguwa takan fita tare da
ita taga gari to shi kanshi Daddy yana son ya rinka fita
da ita ita ce dai taki amincewa sau daya ta bishi suka je
gidan Aisha diyar Hajiya dake aure nan Abuja, daga
nan koya nemi su fita ba ta binshi ita kau ba don komi
ba sai don ganin yarda yake neman makale mata, duk
in da take zaune shima yana nan, yana jifarta da
mayataccen kallonshi wanda ita kanta bata san
dalilinshi ba, cikin faki ne kadai take shiga ta samu
lafiyar shi, idan ma ta shiga dakin Hajiya ta rinka
jajenta kenan tana tambayarta abin da ke damunta, ko ta
ce babu komi duk da haka sai ta dan damu.
Yanzu haka duk wasu hidimominshi ya dauko ya
dora mata, ko abinci zaya ci idan ya shigo zaya kwalla
mata kira, duk in da take sai ta fito ita zata zuba mashi
35
abincin kuma ya tsare ta sai ta zauna a gabanshi zaya ci
abincin.Abun yakan daurc mata kai, idan ta yittunani
shi ba fitowa ya yi ya sanar da ita wani abu ba, amma
duk ya bi ya daure ta, ita ba abun ta kai karar shi wurin
Hajiya ba, to ta ce mata mi? Tunda ba wani labu ya cc
mata ba. Lokuta da dama idan suna zaune yakan kira
Farida ta waya ko kuma ita ta kira shi gabanta za su yi
hira yana fadi mata kalaman soyayayya da matsayinta
cikin zuciyarshi, kai ko wajenta yajc ya dawo zaya ba
ta labarin hirar da suka yi, don haka nc take ganin
kamar yana neman ya maida ta sakarai, to sai ta rinka
daure mashi, amma duk da haka a banza, bata smau
lafiyarshi ba, sai da ya koma bakin aikinshi, idan ya fita
tun safe, shi da gida sai dare, sai kuma ta rinka tausaya
mashi baya da hutu sai Asabar da lahadi.
Abu guda ne ya ke damunta rashin jin labarin gida
ta damu kwarai, rannan ba zato Hajiya ta fita cikin gari
da ta dawo sai ga waya sabuwa fil ta kawo mata mai
kyau, da gani za ta yi kudi, don murna Naja'atu rasa
abin da zata ce ta yi, to itama Hajiyar ta hanata yin
godiya, ta shige cikin daki ta barta da Ibrahim suna ta
dannar wayar. Cikin jikkarta ta laluba ta fiddo Diary
dinta, ta duba lambobin dake gare ta na kawayenta ta
loda cikin wayar har da ta kaninta Mas'udu ta rinka
neman layin shiru ba ta samu ba, ta damu kwarai amma
can da daddare da ta sake kira, sai ta ji wayar ta shiga ta
tsaida hankalinta wuri daya tana dokin ta ji ya dauka,
kuma cikin sa'a yana kusa ya amsa da sallama. Ta cе,
336
ki ka ga ina janta, don kawai ta yi fushin." Ta dan cije
lefenta tana jinjina kai, ba ta ce komi ba, ya yi mata
rakiya da nisa babu nisa zuwa gidansu cikin unguwar
daya ne, duk da haka dai Farida ba ta sa ki fuska ba
sosai, ita dai tana zargin wani abu to shima bai sake
tada mata maganar ba, suka yi sallama ya yi mata
godiya kan zuwan da ta yi yima Hajiya sannu da zuwa.
'Yan kwanaki kadan Naja'atu ta warware cikin
Abuja, koda yaushe tana like kicin tare da Mick tana
koyon girki kala-kala, tun Hajiya na yi mata fada akan
ta rinka zama tana hutawa, har ta gaji ta rabu da ita, to
sai ta samu littafi duk girkin da aka yi wanda ya burge
ta zata rubuta. Tana jin dadin zaman gida, babu in da
Hajiya ta rage ta idon zata fita unguwa takan fita tare da
ita taga gari to shi kanshi Daddy yana son ya rinka fita
da ita ita ce dai taki amincewa sau daya ta bishi suka je
gidan Aisha diyar Hajiya dake aure nan Abuja, daga
nan koya nemi su fita ba ta binshi ita kau ba don komi
ba sai don ganin yarda yake neman makale mata, duk
in da take zaune shima yana nan, yana jifarta da
mayataccen kallonshi wanda ita kanta bata san
dalilinshi ba, cikin daki ne kadai take shiga ta samu
lafiyar shi, idan ma ta shiga dakin Hajiya ta rinka
jajenta kenan tana tambayarta abin da ke damunta, ko ta
ce babu komi duk da haka sai ta dan damu.
Yanzu haka duk wasu hidimominshi ya dauko ya
fora mata, ko abinci zaya ci idan ya shigo zaya kwalla
mata kira, duk in da take sai ta fito ita zata zuba mashi
35
abincin kuma ya tsare ta sai ta zauna a gabanshi zaya ci
abincin. Abun yakan daure mata kai, idan ta yi tunani
shi ba fitowa ya yi ya sanar da ita wani abu ba, amma
duk ya bi ya daure ta, ita ba abun ta kai karar shi wurin
Hajiya ba, to ta ce mata mi? Tunda ba wani abu ya cc
mata ba. Lokuta da dama idan suna zaune yakan kira
Farida ta waya ko kuma ita ta kira shi gabanta za su yi
hira yana fadi mata kalaman soyayayya da matsayinta
cikin zuciyarshi, kai ko wajenta yaje ya dawo zaya ba
ta labarin hirar da suka yi, don haka ne take ganin
kamar yana neman ya maida ta sakarai, to sai ta rinka
daure mashi, amma duk da haka a banza, bata smau
lafiyarshi ba, sai da ya koma bakin aikinshi, idan ya fita
tun safe, shi da gida sai dare, sai kuma ta rinka tausaya
mashi baya da hutu sai Asabar da lahadi.
Abu guda ne ya ke damunta rashin jin labarin gida
ta damu kwarai, rannan ba zato Hajiya ta fita cikin gari
da ta dawo sai ga waya sabuwa fil ta kawo mata mai
kyau, da gani za ta yi kudi, don murna Naja'atu rasa
abin da zata ce ta yi, to itama Hajiyar ta hanata yin
godiya, ta shige cikin daki ta barta da Ibrahim suna ta
dannar wayar. Cikin jikkarta ta laluba ta fiddo Diary
dinta, ta duba lambobin dake gare ta na kawayenta ta
loda cikin wayar har da ta kaninta Mas'udu ta rinka
neman layin shiru ba ta samu ba, ta damu kwarai amma
can da daddare da ta sake kira, sai ta ji wayar ta shiga ta
tsaida hankalinta wuri daya tana dokin ta ji ya dauka,
kuma cikin sa'a yana kusa ya amsa da sallama. Ta ce,
36
"Mas'udu ni ce Naja'atu." Shima murna yake yi va ce.
"Yaya Naja mun yi missing din ki sosai, kulluna sai
mun yi maganarki, ba'a gaisawa ba wani labari yaya
Abujar?"
Ta rumtsc ido tana jin dadi, ta ce "Alhamdulillahi,
komi lafiya. Mas'ud yaya Baba da Inna.?" Ya ce, "Duk
suna nan lafiya, gasu nan ma kusa ga Inna ku fara
gaisawa." Cike da doki ta gaisa da Inna, Inna ta ce.
"Yaya Hajiyar.?" Ta ee "lafiya lau, ita ce ma ta sai mani
waya yau, shì ne na ce bari in kira Mas'ud mu gaisa пa
yi kewarku Inna." Inna ta ce "To ai komi lafiyha lau
dai.?" Ta ee "Wallahi lafiya lau Inna, sai dai godiyar
Allah, ba ki ga yarda Hajiya take yi mani ba, ko ita ta
haife ni sai haka, yanzu tana cikin daki ne, amma idan
ta fito zani kira ku gaisa." Inna ta ec, "Shi kenan Allah
ya saka mata da alkairi, ga Malam nan ku gaisa." Shima
tikin doki suka gaisa har da su Badiya sai da aka ba su
suka gaisa, gaskiya ta ji dadi waya rahama ce, sai ta ji
duk wata damuwarta ta warware.
A hankali ya murda kofa ya shiga, hannunshi
daya rike da kwat dinshi, yayin da dayan hannun ya na
rike da allon kwamfuta (laptop) daga ita har Ibrahim
suka maida idanuwansu akanshi, suna yi mashì sannu.
Akwai alamar gajiya sosai a tare da shi, sai ta ji tsikar
jikinta yana tashi a hankali ta sauke kwayar idanuwanta
kasa, ta rasa abin da yake damunshi cikin ta wahin han
har ba ta so ya shigo gidan, sai đai yanzu da ta lura da
yanayin aikinshi tausayi yake bata ba tare da ta kalle
37
shi ba, ta ce "Sannu." Ya saki fuskarshi ya ce, "Yauwa Naja'atu yaya gidan.?" ta ce "lafiya lau." ya ce "Mc ki ka aje mani da zani ci.?" Ta dube shi tar cikin ido, ta се
"Kamar me.?" Ya ce "Abinci ko.?" Ta ce "Akwai
abinci." Ya jinjina kai ya ce "Shi kenan bari in shiga in
dan watsa ruwa sai in fito ki bani."
Ya huce zuwa dakinshi, sai ta saukar da ajiyar
zuciya a hankali tunanin da take kokarin danne wa, ya
dawo mata cikin zuciya cikin 'yan kwanakin nan tana
wahala sosai dangane da abin da zuciyarta take neman
janyo mata, sai dai duk iya kokarin da take yi wajen
ganin ta kawar da abun, ya faskara saboda wanda ake
abun dominshi kullum rana kara iza wutar abun yake yi
tana ruruwa cikin zuciyarta ko shakka babu ta sani
Kaunar Daddy ce ke wahalar da ita, wanda ita kanta
tasan cewa bugun iska take yi. Daddy ba nata ba ne,
satin da ya shige ta ji Hajiya da mahaifiyar Farida suna
maganar sanya lokacin aurensu, kuma shi ma ya
amince babu yarda za'ayi ya dawo gare ta, sai ta rinka
jin tausayin kanta, yaya aka yi haka ta faru gare ta? A
duk iya tsawon rayuwarta bata taba yin soyayya ba, don
mi yanzu ta fara da son maso-wani? Tabbas tana cikin
wahala.
Wasu siraran hawayhe suka sauko bisa fuskarta,
bata ankara ba sia dai taji muryar Ibrahim akanta, ta
sanya hannu tana share fuskarta ya ce, "Anty Naja
lafiya.?" Ta yi murmushi ta ce, "Lafiya lau Ibrahim."
Ya ce, "Naga kin yi shiru." Ta ce, "Babu komi wani
38
tunani ne nake yi." Sai ya zauna suka ci gaba da danna
waya, yana gwada mata yarda komi yake.
Suna nan zaunc Daddy ya fito, ya watsa ruwa
yana sanye da jallabiya fara sol, mai gajeren hannu.
Naja'atu ta zuba ido ta ce, "kan tabur zaka ci abincin ko
a kawo maka nan.?" Ya ce, "Kawo mani nan, na gaji da
yawa." Ta tashi a hankali ta zubo ta kawo mashi,
sannan ta je ta kawo mashi rujwa ta samu har ya fara
cin abincin, don haka tà aje ta zauna, to shi Ibrahim sai
ya tashi. Ya tafi dakin karatu yana da Assignment.
Naja'atu ta zauna shiru, yawanci ta fi maida hankalinta
kan akwatin talabijin, yayin da shi kuma Daddy ya
tsare ta da kallo, wanda ita kanta ba ta san dalilinshi ba,
yana damunta da yawa. Tun tana daurewa har ta kai ta
yunkura ta mike tana shirin tafiya. Ya ce, "Ina za ki
kuma.?" Ta ce, "Ina cikin daki." Ya cc, "Zauna hira
zamu yi, duka yanzu karfe nawa.?"
Bata yi musu ba ta koma ta zauna, ya gyara zama
yana kallonta, ya ce, "Wai in tambayc ki, kin gama
NCE din ki ko.?" Ta ce, "Eh." Ya ce, "To yanzu sai me
kuma za ki yi.?" Ta dube shi tar cikin ido ta ce, "Me fa?
Duk abin da Allah ya kawo shi zan yi." Ya ce, "Kamar
me.?" Ta yi murmushi ta ce, "Ka cika tambaya Daddy."
Ya rinka kyalkyatar dariya, ya ce, "Abin da ka damu
dashi Naja'atu shi kake tambaya kanshi, yanzu bani
labarin saurayinki." Ta dube shi da sauri, ta ce, "Na
ina.?" Ya ce, "Kina nufin ba ki da saurayi.?" ta ce,
"kusan haka ne, bance maka bani da samari ba, ina da
39
so sat dai babu wanda nake so, don haka zani iya ce
maka bani da shi.""Ya ce, "To wane irin miji kike so.?"
Ta ce "Bani da zabi sai abin da Allah ya yi." Ya се,
"Kina ganin ba matsala, idan ni na samo maki.?"
Ta yi dariya ta cc, "Ce maka na yi ina nema.?" ya
cc. "Ba ki ce ba sai dai ni ina ganin ya dace ace kina da
shi." Ta kada kai ta ce, "To ban sanya ka ba, saboda ba
dole ba ne in so abin da kai kake so." Ya zuba mata ido
a hankali ya ce, "Ko.?" Jikinta ya ida mutuwa sai tga
sarda kai bata ce komi ba. Shima cin abincinshi yake yi
yana kallonta, har ya kare bai sake magana ba. Hajiya
ta fito ta zauna, Naja'atu ta zubo mata abinci ta zauna
tana ci suna hirarsu gwanin ban sha'awa, akwai fahimta
sosai tsakaninsu haka nan Hajiya na kokarin hada
kansu a bangare daya kuma wani tunani ta soma yi,
yanzu da take zaune da Naja'atu ta yaba da kyawawan
dabi'un yarinyar, tana kaunarta har cikin ranta, sai ta
rinka sha'awar dama ace ita Daddy yake nema ba wai
Farida ba, ta kowane fangare ta auna Naja'atu sai taga
ta yi ma Farida fintinkau, kyau ne, asalin kyaun hali, da
sanin ciwon kai, sai dai kai ya ce don ita Naja'atu
iyayen talakawa ne kuma bata waye ba irin Farfida
haka nan ta 6angaren ilimi ita kanta Faridar yar
Diploma ce ta kulla, to ita ba ta damu da talaucin
iyayen Naja'atu ba idan dai zaya amince da ita duk abin
da iyaye zasu yi ma diya ita mai yi mata ce tana son
halin dattakun yarinyar. To shi duk duk baiga wannan
40
ba, ya rufc ido baya ganin wata diya mace da mutunci
idan ba Farida ba.
Cikin 'yan kwanakin han tana nazarin takunshi da
Naja'atu cikin gidan, sai take jin dadın yarda suka kara
kusantar juna, tana fatan Allah ya karbi addu'arta, idan
haka ta faru sai tafi kowa farin ciki, ko ba komi ta yi
sarakuwa ta gari kuma ta yi imanin zamansu zaya yi
dadi, duk wannan sabanin da suke samu ba ta dauke shi
matsala ba, da zaran sun fahimci juna shikenan. To sai
dai lura da yanayin da ake ciki yanzu ba a yi ma 'ya'ya
dóle, sai ta zuba ido taga iya gudunsu, kullum dai
addu'arta guda Allah ya sanya burinta ya cika.
Karfe goma daidai, Naja'atu ta mike-zata tafi ta
kwanta ta yi ma Hajiya sai da safe sai ta juya tana
kallon Daddy wanda shi ma ya zuba mata ido, ya ce
"Barcin ne ko.?" Ta yi murmushi kawai ta ce, "Sai da
safe." Ta nufi daki ta yi shirin kwanciya ta kashe fitila,
ta kwanta tana karanto addu'o'i, tunanin hirar ta da
Daddy ya tsaya mata a zuciya, "Wai shi ne zaya nemo
mata saurayi? To ko dai ya gane cewa tana sonshi? Don
haka yake zolayarta? Ta rinka jinjina magar, cikin
zuciyarta. Dole ne ta bi a sannu kada ta bada kanta abun
ya kaita ga cin fuska, to amma kuma da ta tuno Farida
da matsayinta sai ta tabbatar da bugun iska take yi, me
yiwuwa shi ba ya ra'ayin diyar talakawa irin ta, haka
nan waycwarta bata kai ta Farida ba, kai nazarin da ta
yi mashi ma ya damu da Faridar sosai, ba ya shakkar
yin hira da ita ko gaban waye, haka nan da wuya su
41
zauna a waje ba ta ji ya ambace ta ba, tabbas yana
Kaunarta, don haka da wuya ya dawo gare ta, sai ta
rinka jin tausayin kanta ta fada tarkon son maso wani.
Can falo kuma da Naja'atu ta tashi Daddy ya bita
da kallo, har ta shiga daki, sai ya yi murmushi yana
kada kai, da ya sauke kwayhar idonshi sai yaga Hajiya
na kallonshi, to sai ya dan ji nauyin ta, ya yi. Hajiya ta
yi murmushi ta ce, "Ya ya ko nan zaka dawo ne.?" Ya
shafi kanshi yana dariya, ya ce "Mummy in yi yaya da
Farida.?" Та сс, "Кana namiji zaka tsaya tambayar
yarda zaka yi da 'yan mata duka biyu, gurbin hudu fa
ke gare ka fa". Ya kyalkvace da dariya, ya ce "Haba dai
Mummy sai ka ce mutumin karkara? To ai ko kauyen
ma yanzu gudun tara matan suke yi, balle ni da nake
mijin mace daya".
Hajiya ta yi dariya ta ce, "Cika baki dai, kada fa a
wayi gari wata rana in ga ka hada hudu cikin gida." Ya
ce, "Allah ya kyauta, mu bar maganar nan Mummy,
bakin uwa saurin kama da take yi, kada abun fa ya
tabbata, da na bani." Hajiya don dariya har tuntsuwa
take yi, shima ya tayata ta ce "Muyi maganar sosai
Daddy, da gaske fa nake yi idan dai kana ganin zaya
yiwu, to ka dawo in baka diyata, yarinyar na da kyaun
hali, kuma naga kamar hankalinku ya hadu."
Ya zuba mata ido yana nazari, sai kuma ya girgiza
kai ya ce, "Kiyi hakuri Mummy ba zaya yiwu ba, ina
son Farida kuma kin sani itama tana sona, mun yi ma
juna alkawari da dama daga ciki har da na aure, idan na
42
ce yanzu in rabu da ita, na ci amana, ba zata ji dadi ba,
kuma maganar gaskiya, ni ita kadai nake so. ba zani iya
barinta ba in koma ma wata." Hajiya ta dan cije lebe,
sai kuma ta ce, "Ni kau sai nake ganin Naja'atu na da
halayc managarta, da duk wani da namijin da ya san
ciwon kanshi zaya so ace ya mallake ta matsayin mace
a gidanshi wadda zata zamo uwar 'ya'yanshi, ta samu
tarbiya mai kyau haka nan idan kyau ne ba za'a nuna
mata komai ba, ka dubi takunta tasan abin da take yi,
zaka yi alfahari da aurenta."
Ya yi murmushi ya ce, "Mummy duk nasan
wannan, sai dai abin da za ki duba shi ne, ina son
Farida-sosai, mun yi alkawarin aure ysakaninmu, kuma
maganar nan ba wai tsakaninmu ta tsaya ba, kin san
maganar nan haka iyayenta sun sani, yanzu haka ko jiya
da naje gidansu munyi magana da mahaifinta ya ce in
turo ayi maganar lokacin auren, maganar da nake son
muyi kenan dama, to kuma Mummy sai in zo yanzu in
kawo wata maganar, ko kuma suga na janye mata,
daukar me zasu yi mani? Ke kanki za ki ji nauyin abun.
Kiyi hakuri insha Allahu Naja'atu zata yi miji, wanda
ya dace da ita." Hajiya ta jinjina kai, ta ce "Shi kenan."
Ya zuba mata ido da sigar lallashi, ya ce "Amma
don Allah Mummy kuyi hakuri kada kiyi fushi dani, gaskiyar abin da ke cikin zuciyata ne na fadi maki, idan
na ce maki zani iya rabuwa da Farida saboda wata nayi Karya." Hajiya ta yi murmushi ta ce, "Shi kenan Daddy
na fahimce ka, yanzu ina magana ta tsaya.?" Ya dube ta
43
yana murmushi ya ce, "To Mummy yarda duk ki ka
gani su dai sun yi mani magana he." Ta ce, "Nima şun
aiko mani, don haka yanzu ka tsaya kan haka.?" Ya
jinjina mata kai, yana murmushi. Ta cc, "Babu
damuwa, Allah ya tabbatar mana da alkairi, zani samu
lokaci in je gidan Babanku, in ji yarda zamu yi.
maganar gidan nan na Arca II, ka ce ka basu Notice din
ko.?" Ya oc, "Eh, tun katin in tafi hutu." Ta ee, "To nan
zaka zauna, don haka sai ka maida hankali kaga sun
bada gidan, yarda za'a yi gyaranshi sosai, ina ganin ya
fi sauki akan ace a gina wani, kuma kaga dai gidan
yana da kyau." Ya ce, "Ya yi sosai Mummy." Ta watsa
hanu ta ce "Shi kenan sauran shiryc-shirye kuma sai
yadda muka yi da Babanka, shi kenan hankalinka ya
kwanta.?" Ya yi dariya kawai.
To amma da ya shiga cikin daki, sai ya rinka juya
maganar Hajiya, "Tabbas yana son Naja'atu, akwai
wasu abubuwa a tare da ita wadanda yake so, yana son
ya kasance tare da ita, ko ba komi takan sanya
zuciyarshi nishađi, to sai dai a ganinshi son da yake yi
mata bai kai matsayin da zaya ce ya zabe ta matsayin
matar da zaya yi rayuwa ta har abada da ita ba, yana da
wadansu ra'ayoyi na daban da ya ruga ya gabatar ma
Farida dasu, kuma ta karance su, don haka take saurin
samun kanshi. So daban ne yaso Farida tun bata kai
matsayln mace ba, mahaifinta Banufe ne, sai dai
mahaifiyarta Ibra ce, su duka ma'aikatan Gwamnati ne,
ita mahaifiyarta Hajiya Hafsatu sun yi aiki ofis daya da
44
mahaifinshi tana karkashi ta haka ne suka san juna ita
da Mummy suna mutunci sosai, idan tazo gidansu tare
da Farida da Kannensu yama janta wasa, saboda lokacin
da tana karama ta yi kyau sosai ga baki tana da yawan
surutu don haka take da farin jini wajen mutane, duk
wanda ya zauna da ita cikin dan lokaci sai ta shiga
ranshi da irin haka ne suka saba da ita cikin dan lokaci
sai ta shiga ranshi da irin haka ne suka saba da Daddy,
idan suka zo gidan koda yaushe tana wajenshi yana
sha'awar abubuwan ta lokuta da dama idan suka zo ba
ta tafiya sai ta yi kwana biyu a gidan, Hajiya ma na
sonta, yauda gobe da ta yi girma ne ta rage zuwa gidan,
amma dole da haka akwai fahimtar juna tsakanin zuri'ar
biyu, mahaifinta matukin jirgin sama ne.
Lokacin da girma ya farfa zo ma Farida ne ta fara
nuna jin kunyar Daddy shi kuma hakan ya dauki
hankalinshi ya fara nuna ra'ayinshi akanta, Hajiya na
lura da shi da ta tsare shi tana tambayarshi bai ji kunya
ba, ya fito fili ya sanar da ita da gaske yana sonta, kuma
in Allah ya yarda ita ce matar. Hajiya dariya ta rinka yi,
saboda tana ganin abin har da yarinta, amma a hankali
yau da gobe sai ga soyayya ta fara kafuwa tsakaninsu,
to gaskiya lokacin ta tsorata ganin cewa su duka basu
kai wani matsayi ba da za'a ce sun maida kai ga
soyayya irin haka don haka ta gargadi Daddy da ya bi a
sannu saboda Farida yarinya ce, a kalla su duka akwai
karati gabansu, bai dace ace sun tsaya wata soyayya ba,
45
to Daddy ba ya da taurin kai don haka ya bi umarnin
mahaitiyarshi ya yi kokarin kauda abun a ranshi.
Lokacin da yake shirin fita karatu duka Farida na
aji daya na babbar sakandire SS1, don haka basu tsaida
wata kwakkwarar magana ba, ya tafi. Duk lokacin da
suka yi magana da Hajiya yakan tambayi labarin
Farida, Hajiya dauriya take yi ta ce tana nan lafiya lau."
Shekararshi biyu da tafiya, Allah ya yi ma mahaifinsu
rasuwa, sakamakon wani mummunan hadari da suka yi
kan hanyar Katsina zuwa Abuja, to lokacin ne ya samu
zuwa gida, ya yi mamaki kwarai da ya ga girman da
Farida ta yi, komi