ni zo gidan nan ba." Inna ta yi dariya ta ce,
"Na yarda da laifina ayi hakuri, ku shigo ciki. Hajiya ta
ce, "A'a, ciki zafī, kawo mana tabarma tsakar gida mu
sha iska." Naja'atu ta shiga cikin daki da sauri ta dauko
tabarma sabuwa ta shimfida Hajiya ta zauna, sannan
itama Inna ta zauna kusa da ita, yayin da Malam Abdu
yake zaune bakin kofar dakinshi bisa shimfidarshi. To
itama Naja'atu sai ta nemi kujera ta zauna gefe daya
tana sauraren yarda za'ayi, da yinin da ta yi tarc da
Hajiya ta ji tana kaunar matar, tana da dadin zama,
zama da ita kanshi wata makaranta ce ko ba komi zaka
fahimci wasu abubuwa na rayuwa, wadanda idan ba
wajen irin su ba, da wuya mutum ya same su.
Badiya da Fatima suka zo suka gaida Hajiya suka
koma cikin daki in da suke linke kaya, sannan suka
shiga gaisawa ita da Hajiya korafi take yi ma Inna kan
cewa ba ta son zumunci, to ita Inna abin da take
dubawa shi ne, yau da gobe sai Allah, sannan haye ma
masu kudi, yana da wuya, idan mutum bai yi a sannu
ba, sai ya wulakanta, ita kau abin da take gudu kenan
wulakanci.
Sai da suka natsu sannan Hajiya ta juya wurin
Malam Abdu, ta ce "Zuwa na yi a bani aron Naja'atu ta
zauna hannuna kwana biyu, tun da dai ta kare karatu."
Malam Abdu ya yi dariya ya ce, "To ai ba wani abu ne
18
ba anima dai ga mahaifiyarta nan ku sasanta." lapv
tta dubi Iuna ta oc, "To kin ji don baka ya ya ki ka cc.
Itama Innar ta yi murmushi ta cc, "To ai shi kenan, har
kwana mawa.?" Hajiya ta cc "Eh to, ina ganin zuwa
Asabar in Allah ya kamu zani wucc Abuja, kuma tare
zamu taf don haka dai sai kin ganmu." Naja'atu n
zauna gefe daya, tana jin maganar da suke yi, mamaki
take yi wai ita zata Abuja abin da ba ta taba tumani ba."
Sai đai taddi kuma ta yi murna da tafiyar, sai dai
wani abktike dubawa shi ne. Inna zata dan takura
msammsa yake ta saba tana dan dauke mata wasu
ayyukan cikin gida, yanzu idan ta tafi ita zata rinka yinm
komi sai idan su Badiya sun dawo daga makaranta. To
sai dai Iunar ta ce babu komi ta shirya su tafi, ina laifin
wanda ya nuna sha'awar zama da naka, a ganinta wani
ci gaba ne ga ita kanta Naja'atun, zama da mata irin su
Hajrya Halima alkairi nc, ko ba komi zata koyi
abubuwa da dama na rayuwa, kuma ma dai babu dach
yarda ta taso takanas ta tambaya ace ta hana wasu masu
kudin ma gudun 'yan'uwansu suke yi
Naja'atu ta shiga cikin daki ta fidda 'yan sababbin
kayanta masu haske, kala bakwai ta diba ta fita zuwa
dakin Mas'udu, ta ci sa'a ya shigo ta ce ya bata jikkarshi
farama ta zuba kaya, ta sanya kayanta, ya cc, "Ina za ki
kuma. Ta yi murmushi ta ce, "Ba ka ga mota ba a
waje, tare da Hajiya Halima mu ka z0, tafiya zata vì
dani gidan ta, daga can zamu wuce Abuja." Mas'ujdu
ya jinjina kai ya cc. "To ni na ga mota, amma ban yi
19
tsammanin baki muka vi ba, na dauka dai ko wani ne
ya ajc ta ya shiga wancan lungun, sai ki cc ke lafiya
lau." Naja'atu ta yi dariya kawai, ya fidda kayanshi
daga cikin jikkar ya ba ta suka fito tare zuwa cikin gida,
ya zauna gefe daya yana gaida Hajiya, yayimn da ita
kuma Naja'atu, ta shiga cikin daki ta zubá kayanta da
'yan abubuwan da zata bukata, ta zage ta ta aje gefe
guda, sannan ta fito. Hajiya ta dube ta ta cc, "Kin gama
ko? Mu tati dare nayi."
Ta koma cikin daki ta fiddo jikkar Mas'udu ya
taso ya karba, yayin da ita kuma ta zuwa wurin
Babansu ta dan tsugunna gabanshi tana yi mashi
sallama, ya cc, "Sai ki kula ki bi a sannu, ba ni son
karambani, kuma ban da gardama, kinga dai arziki ne
ya sanya ta nuna sha'awar tafiya dake, to don Allah ki
iya kanki ki tsaya matsayinki, kada ki kuskura in ji
wani abu na rashin kyautawa ta taso daga gare ki, Allah
ya kiyaye hanya." Ta jinjina kai, sannan ta taso ta yì ma
Inna sallama, har suka fito Inna na gargadinta akan tabi
a sannu, ban da karambani, yayin da ita kuma Hajiya ta
cika su da iyayen kudi, kowa da nashi, haka suka rabu
cikin dadin rai, Malam Abdu ya rinka nanata mata
kalmar ta yi hakuri zama da yaro sai an kai zuciya nesa.
Lokacin da suka isa gida karfe goma saura, Daddy
ne kadai kwance bisa kujcra, yana kallon wasan
kwallon kafa. Hajiya ta nuna mata dakin dake kusa da
na ta ta ce ta shiga da kayanta ciki, nan zata zauna, ta
wuce da jikkarta cikin dakin ta ajc, dakin yana da
20
girma talkeken gado ne na ba kin Karfe cikin dakin sai
madubi da kujera daya itama ta bakin karfen, akwai ba
yi a ciki ta bude dirowar bango ta saka kayan gefe daya
saboda akwai manyan jikkuna ciki ga alama nan ma
kayan sanyawa nc. Da ta ajc ba ta fito ba, sai da ta yi
sallar Isha'i, sannan ta cire hijabin ta linke ta aje gefe
daya, sannan ta fito cikin falon in da Hajiya take zaune
ita da Daddy, ko kallonta bai yi ba, haka itama ba ta
damu da shi ba, shi kadai ne take ganin zaya zame
mata matsala a gidan, to shi din ma ba damuwa ta yi da
shi ba, ai sai dai ta shiga harkarshi ne zaya yi mata.
Kafin ta zauna Hajiya ta ce ta shiga kicin ta fiddo
masu abinci, sai lokacin ta tuna-ba su ci abincin dare
ba, rayuwar gidan dabance, kalaci sai sha biyun rana,
haka na rana sai wajen la'asar. Suka ci shi, yanzu kuma
na dare sai karfe goma. Kan tabur ta shirya kayan
abincin, sannan ta koma kicin dauko ruwa, da ta dawo
daga Hajiya har Daddyn sun hau tebur din suna
zubawa, ta aje farantin itama ta zauna sai da suka gama
diba sannan itama ta zuba kadan Hajiya ta rinka yi
mata fada, kan ta saki jiki ta ci abinci nan gida ne ba ta
son zama da yunwa musamman ta dare.
Naja'atu ta ce, "Allah kuwa Hajiya wannan ya ishe
ni." Ta ce, "Shi kenan." Ta rufe sauran suka ci gaba da
cin abincin, tana lura da Daddy ya daure fuska sosai, ba
ya magana sai ita da Hajiya ke hira jefi-jefi.
Zuwa can wayarshi ta yi kira, ya dauka ya duba
sai ya yi murmushi ya dauka yana magana a hankali
21
cikin kwantar da hankali ya cc "Kada ki damu, insha
Allahu ina nan tafe gobe, nima Katsinar ta ishe ni." Ya
dan yi shiru, sai kuma ya yi dariya yana shafar kai, а
hankali ya yi satar kallon Hajiya ba ta damu da
harkarshi ba, ya ce "Ke ki ke ganin haka, kiyi hakuri
idan na iso zamu tattauna komi, baye bye ok good
night." Ya rufe wayar yana murmushi ya ce da Hajiya,
"Mummy Farida ce ta ce a gaida ki." Hajiya ta skai
fuska tana murmushi ta ce, "Ina amsawa, nasan dama
saboda ita ne kake ta wannan rawar jikin tafiyar ka tafi
ka barni ni daya." Ta dubi Naja'atu tana dariya, ta ce,
"To ai nima ga tawa diyar nan na dauko, sai ka tafi
Allah ya kiyaye hanya."
Bai sake cewa komi ba har suka kare cin abincin,
Naja'atu ta kwashe kwanonin ta maida kicin, sannan ta
dan zauna falon kadan amma barci ya taho don haka ta
yi ma Hajiya sai da safe, ta raba ta gefen kujerar da
Daddy yake zaune ya bita da ido kawai, ta bude daki ta
shiga abinta. Sai ya cije lebe yana kada kai mamakin
daukar da yarinyar ta yi mashi ya ke yi ta raina shi da
yawa, duk sarda ya kalle ta sai ta yi mashi, kallon
banza, to baya son ta raina shi ne don haka baya biye
mata.
Washe gari tunda safe ta tashi, bata saba da irin
wannan barcin ba, mutum yai ta kwanciya har rana
cikin daki ta tsiri goge-goge ta wanke kewayen dakin
wai duk don ta rage lokaci, har karfe tara ta fito bata ji
motsin kowa ba, Hajiya ba ta tashi ba, to ita kam ta gaji
22
don haka ta fan zauna cikin falon shiru, to sai kuma ta
shi ta isa wajen da kayan kallo suke, ta rinka binciken
kasasuwansu, ta ci sa'a ta samu DVD, na kira'a sai ta
hada wuta ta kunna kira'ar tana fita a hankali, muryar
Shcik Ahmed Sulaiman cc, ta koma ta kwanta tana bi.
Karatun yana yi ma ta dadi, ta shagala sosai, lokacin
shima ya fito daga cikin dakinshi, har yazo ya zauna ba
ta sani ba, sai dai ta ji muryarshi yana magana kan
waya, a hankali ta sauke hannuntà da ta rufe fuska tana
kallonshi, shima ita yake kallo, sai ta tabe baki ta maida
idanuwanta ta rufe.
Har ya kare wayar yana kallonta, yanzu ya daina
mamakinta dariya take neman sanya shi ya rasa dalilin
wannan fushin da take yi mashi, ta cika riko abu baya
wucewa wajenta koda yake wasu abubuwan da take yi
harda yarinta, amma shi bai ga laifinshi ba, a nan, ya
rufe wayar ya saka cikin aljihu, yana kallonta ya ce,
"Ke." Ta. sauke hannunta tana kallonshi ya ce, "Wai ke
ba ki iya gaisuwa ba ne.?" Ta zuba mashi ido kawai, ba
ta ce komi ba, ta yunkura ta mike tana shirin tafiya, da
saurinshi yasha gabanta har ta ji tsoro ta tsaya tana
kokarin maida lumfashi, ya tsare ta da idanuwanshi
babu wasa ya ce, "Ina yi maki magana, shi ne za ki
tashi." Ta sarda kai ba ta ce komi ba, ya ce, "Wai me
kika taka ne? Da za ki rinka hararata, ni fa ba abokin ki
ba ne kin sani."
Тa сe, "Тo in kasan haka tunda ban shiga harkar
ba, kaima sai ka fita tawa ka yi harkarka, ko ko nace
23
dole sar ka tanka mani?" Ya girgiza kat yа ссe, "Вa ki
ce ba, amma tunda gashi Allah ya hada mu zama wuri
daya dole ne in yi maki magana don ni ban iya gaba ba,
sai dai kuma dole ne ki shiga hankalinki, tunda gaba na
ke da ke." Ta yi shiru ba ta ce komi ba, ya tsaya kawai
yana kallonta, mamakin yarinyar yake yi, tana cin
sa'arshi ya ce, "Yanzu shiga ki fadi ma Hajiya na ce na
fito." Ta tsaya shiru kamar ba za ta je ba shima bai sake
magana b a ya koma ya zauna yana kallonta to itama da
ta duba sai taga abin da take yi bai dace ba, ko ba komi
gabanta yake, haka nan yanzu a karkashinsu take
zaunc, dole ne ta rinka daratta shi, in dai tana son ta
zauna lafiya, sai dai zancen shiri tsakaninshi da ita babu
shi har abada, ra'ayinsu bai zo daya ba.
Ta sanya kai ta dan kwankwasa kofar dakin
Hajiya ta shiga har yanzu kwance take a hankali ta
bude ido tana kallon Naja'atu, yayin da ita kuma ta dan
rusuna tana gaida ta, ta ce, "Naja'atu lafiya dai ko.?" Та
cc, "Lafiya lau, Daddy ne ya ce a fadi maki ya fito."
Hajiya ta yi murmushi ta ce, "Ni wallahi har na manta
da tafiyar shi, shi kenan ki ce mashi ya dan jira ni, bari
in yi wanka gani nan fitowa, sai ki shiga kicin ki sama
mashi abin da zaya ci, ba ni son ya hau hanya da
vunwa." Ta amsa "To." Ta fito, yana nan zaune in da ta
bar shi, sai ta dan dafa kujera tana kallonshi, ta ce, "Та
ce ka jira tana fitowa yanzu." Bai ce komi ba. Abin da
tafi tsana kenan rainin wayau, yarda ya nuna kamar ba
da shi take magana ba, alhalin shi ne ya aike ta, don
24
haka ne ta ke yi mashi haka, don in ta ce zata rinka
binshi tana kwantar da kai yarda yake so to wahalarshi
zata sha.
Da wannan tunanin ta shiga kicin ta yi tsaye tana
kalle-kalle ba ta san ta ina zatga fara ba, sai ta hango
files din ruwan zafi ta duba, cike yake da ruwan zafi ta
aje gefe daya, ta hada kayan tea da bread, ta dauko tazo
ta ajc mashi, kallonta yakc yi kawai ta koma ta dauko
filas ta aje mashi tana shirin tafiya, ya ce "Ni ki ka
kawo ma wa:?" Ta daga kai, sai ya yi murmushi karo
na farko kenan da ya dan sakar mata fuska, ya ce "To
amma sai ki kawo kaya ki aje mani kamar kin kawo ma
kurma, ba bayani."
Ta kara faure fuska tana kallon wani sashin, bai
sake magana ba, don haka itama ta yi tafiyarta cikin
daki tga kwanta, tana jin shi da Hajiya suna sallama,
har ya tafi bata sake fitowa ba, sai ta ji gidan ya yi mata
dadi, dama shi ne matsalarta, ta saki jiki sosai yayin da
Hajiya ta rinka nuna mata gata tana janta jikinta, a kalla
sai da ta yi mata sabbin dinkuna kala biyar masu tsada,
sannan ta kara mata wasu cikin diyarta Ummi da ke
karatu A.B.U ai don da nan Naja'atu ta kara zanzarewa,
ta fito sosai kamar ba ita ba, hutu ya samu Hajiya ba ta
so taga tana aiki cikin gidan fada take yi, ta ce "Meye
amfanin 'yan aikin da suka aje, ba ta dauko ta ba ne don
ta yi mata wahala." Ita kau Naja'atu ba ta saba da
zaman ba ne, to tun zaman na isarta har ta kai ta fara
sabawa, itama ko ta tashi ba ta fitowa sai rana ta yi,
25
amma duk da haka takan yi wasu 'yan aiyukan da basu
taka kara suka karya ba, kullum rana ita ke gyaran
dakin Hajiya da kewayenta, to da yake ba yara gare ta
ba, ko ina fes yake, sai dan abin da ba'a rasa ba.
Kwananta takwas gidan Hajiya ta ce, "Ta yi shiri
washe gari zasu tafi Abuja, da daddare ta sanya direba
ya kai ta gidansu ta yi sallama da iyayenta, daga Inna.
har Babansu suka taru suna yi mata nasiha tare da
gargadinta, akan ta aje rayuwarta matsayinta kada ta
dauki girman kai rawanin tsiya ne." Ta yi masu
alkawari, suka yi mata fatan alkairi, gaba ki daya suka
yo mata rakiya, ta shiga dankareriyar motar gidan su
Hajiya, suka taho tana daga masu hannu. Washe gari
kuma sai karfe sha biyu suka bar Katsina zuwa Abuja,
ita ke zaune gaba kusa da direba, yayin da ita kuma
Hajiya take kwance baya, sanyin A.C na ratsa su, yayin
da direban ke ta aikinshi, sai zuba gudu yake yi, amma
tafiyar a natse. Karfe biyu suka tsaya Zaria, makaranta
wajen Ummi, sai dai ba su bata lokaci ba suka dauki
hanya, gaskiya Naja'atu ta yaba da halayyar yarinyar, ta
karbe ta hannu bibbiyu bata da girman kai irin na
Daddy, tana da son mutane yun kafin Hajiya ta yi mata
bayaninta ta fara tambayarta, sunanta. Hajiya ta fadi
mata ai shi kenan ta rinka janta da hira, har tana
rokonta akan kada ta tafi sai tazo hutu. Hajiya ta yi
dariya ta ce, "Kwantar da hankalinki Naja'atu ta dawo
hannuna kenan sai aure zaya raba mu." Tana kallonta
tana dariya, to itama dariyar kawia tayi, bata san irin
26
daukar da matar ta yi mata ba, tana nuna mata kulawa
sosai, don haka itama har cikin ranta kaunar matar take
yi.
An gama sallar Isha'i suka shiga garin Abuja,
gaskiya birnin ya kayatar da Naja'atu, ta rinka mamakin
tsarin garin, lallai kam an ci gaba sosai a Nigeria, ba ta
yi tsammanin haka ba, ta saki ido sosai ta na kallekallenta ba ta san in da akc zuwa ba, sai dai ta ji an
tsaya bakin wani gida ana yi hon. Maigadi ya bude get
yana yi masu sannu da zuwa, yayin da motar ta shiga
ciki, bakin kofar shiga gidan ta isaya lokacin Daddy ya
fito daga cikin gidan shi ya bude ma Hajiya kofa ta fito
yana yi mata sannu. Naja'atu ta kalle shi kawai, ba ta cсе
komi ba, ya kamo hannun Hajiya suka shiga ciki, yayin
da ita kuma ta tsaya ta dauki jikkar Hajiya ta hannu da
'yan tarkacen da ke kusa da ita, sannan ta bi bayansu
zuwa cikin falon, shima ya kayatu sosai ba sai an yi
bayani ba.
Hajiya ta nuna mata wata kofa ta ce, "Shigar mani
da jikkar ciki, sai ki ciro mani wayata daga cikin jikkar
ki taho mani da ita." Ta amsa "To." Ta shiga dakin,
shima ya tsaru wani dunkulallen gado ne dan Italiya, ya
yi kyau komi ya tsaru babu tarkace, kai lallai masu kudi
na jin dadi. Ta aje jikkar ta fiddo waya ta dawo falon
lokacin direban yake shigowa da kayansu, don haka ta
kwashi na Hajiya ta kaisu cikin dakinta da ta fito
Hajiya ta nuna mata wata kofar ta ce, ta kai nata ciki,
fakin Ummi ne, ta shiga shima fakin ya tsaru gadon iri
27
daya ne da na dakin Hajiya, ta shirya kayan ba ta fito
ba sai da ta watsa ruwa, ta dauro alwala ta yi sallolin
dake kanta, to sai ta sanya jallabiya marar nauyi,
sannan ta fito falon Hajiya ta cc, "Da kyau Naja'atu, har
kin yi wankanki ko? Ta yi murmushi kawai ta dubi
Daddy kallonta kawai yake yi ba ta ce mashi komi ba,
Hajiya ta ce, "Bari nima in shiga in dan watsa ruwan in
fito mu ci abinci.
Ta tashi ta shige cikin faki, don haka suka zauna
su kadai cikin dakin. babu wanda ya yi ma wani
magana tana nan zaune Hajiya ta kwalla mata kira, ta
shiga dakin da sauri ta ce, "Kice ma Daddy yaje ya
dauko Ibrahim yanzu." Ta-fito ta same shi yana kallon
Kwallon kafa, ta ce, "Hajiya ta ce kaje ka dauko
Ibrahim." Ya yi shiru kamar bai san tana magana ba, ta
dan tsaya tana kallonshi, tasan dai ya ji abin da ta fada,
to sai ta rabu da shi ta yi zamanta, shiruj-shiru bai tashi
ba ta sake yi mashi magana, ta ce, "An ce fa ka je ka
dauko Ibrahim." Ya juyo yana kallonta, muryarshi a
hankali ya ce, "Wai don Allah me ki ka dauke ni, tunda
ki ka zo gidan nan baki yi mani magana ba sai yanzu."
Ya yi shiru, sai kuma taga kamar bata kyauta ba, ta cе,
"To amma Daddy daure mani fuska kake yi yaya kake
so in yi da kai.?"
Ya cc,"Ba wani daure fuska, ki dai ce kin raina ni
ne kawai." Ta yi murmushi ta ce, "wallahi har abada
babu raini tsakaninmu, ban ga fuska ba ne, idan na
kalle ka naga ka daure fuska, sai raina ya baci, don
28
haka kaga ina yin shiru." Ya girgiza kai ya cc, "To
gaskiya ba ni jin dadin abin da ki ke yi mani ki daina."
Ta jinjina kai, ya ce "Yanzu muje ki raka ni a dauko
shi, gidna wani kanin babanmu ne yake can Maitama."
Ta yi murmushi ta ce, "Don Allah kayi hakuri, na gaji
da yawa." Ya zuba mata ido, sai kuma ya jinjina kai ya
aje remote fin dake hannunshi kan kujera, ya dauki
makulli ya fice yana ce mata "Sai na dawo."
Ta zauna shiru tana mamakin halayyar Daddy,
miskili kafi mahaukaci ban haushi, yau kuma 'yan
kirkin yake ji. Hajiya ta fito ta sanya ta fiddo kayan
abinci daga kicin kukun gidan ne ya girka, abinci
lafiyayye tuwon shinkafa miyar agushi, yasha naman
kaji da na sa tsoka zalla ga kuma kifi, naman har ya fi
karfin miyar, ta rinka mamaki a ranta sai ka ce abincin
Yarabawa, suke irin wannan hadin. Suna tsakar cin
abinci su Daddy suka dawo tare da Ibrahim ya kama
Hajiya ya rike gam yana murnar dawowarta itama ta
rinka shafa kanshi cike da kulawa tana lallashin dan
auta, da banne ga alama ana ji dashi. To ranar hirar ta
dan yi ma Naja'atu dadi, saboda Daddy ya saki jiki
sosai ana hira da shi, duk da cewa ba ta cika sanya
masu baki ba, idan ya yi magana yana kan sako ta, haka
nan idan an yi abun dariya tana taya su. Hajiya ta ji
dadi sosai da taga tana sakin jikinta sai da dare ya yi
sosai, sannan suka kwanta, sai lokacin ta gane abin da
ke sanyawa suna yin barciu da safe, ashe basu
kwantawa da wuri. Ga mamakinta itama da kyar ta
29
tashi ta yi Sallah da asuba, ta koma ta kwanta ga gajiyar
tafiya don haka barcin ta yi sosai sai sha daya ta tashi.
Mamakin barcin da ta yi ta yi, da kyar ta shiga
kewaye ta yi wanka, sannan ta shirya ta fito. Hajiya na
zaune cikin falon da wata yarinya ta ida rufe kofar ta
iso in da suke, tana gaida Hajiya, Hajiya ta yi
murmushi ta ce, "Naja'atu duk gajiyar ce yau ta kwantar
dake, ke da ba ki barcin safe." Ta yi murmushi tana
kallon yarinyar, kyakkyawa da ita fara sai dai da gani
idanuwanta a bude suke, haka nan sai taji jinintga bai
hadu da ita ba, amma ta daure ta gaida ta, itama kallon
Naja'atun take yi, Hajiya ta ce mata "Farida ga Naja'atu
diyata ce daga Katsina na taho da-ita." Ta juya kan
Naja'atu ta ce "Wannan ita ce Farida, in Allah ya yarda
ita ce matar Yayanki Daddy." Naja'atu ta kara kallon
yarinyar a karo na biyu, sai ta dan yi murmushi ta cе
mata "sannu." Itama dai babu wani sakin fuska ta amsa.
Sai ga Daddyn ya fito daga cikin daki, ta gaida
shi, Hajiya ta ce, "kije ki yi kalaci, mun yi tun dazu."
To sai ta nufi teburin cin abinci ta zauna tana kalacinta,
yayin da shi kuma Daddy ya zauna don haka Hajiya ta
tashi ta koma cikin daki, ta bar su suna hirarsu. Naja'atu
ta ci gaba da kalacinta tana satar kallon su Daddy, sam
ita dai yarinyar ba ta yi mata ba, wayewar ta ta yi yawa
tun akan suturar dake jikinta, ta raina mata, a ganinta
ko tana sanyawa tunda zata zo gidan surukai ya dace ta
sanya kayan kirki, wani material ne bula a jikinta, daga
einkin siket din har na rigar sun matse mata jiki kamar
30
zata kare a ciki, gashi dinkin an bi an yayyaga shi sai
kacc tsumma, kuma babu mayafin kirki ga gashin kanti
a kanta, kamar kwancen hauka. Da ta kare mata kallo
tsab,m sai taga hatta farin nata ta kara shi da man kanti,
tana jin maganarta daga in da take babu wani kamun
kai, sar kace fiyar yare." Ta taße baki ta ci gaba da cin
abinenta abin da babu ruwanka ciki, babu ruwanka har
abada ita dai 'yar kallo ce.
A hankali ta sauke kwayar idonta akan Daddy,
yana kallonta da wani irin yanayi, sai ta ji gabanta yana
faduwa, ta sauke kai amma duk sai taji ta takura da
kyar ta kare cin abincin ta tashi ta koma cikin daki. To
har aka yi sallar azahur Farida na gidan, suna hira da
Daddy cikin falo, Naja'atu ta rinka mamakin wannan
wace irin rayuwa ce? Mai da kai bayan har ya yi yawa,
ba zata bari yaje gidansu ba, sai ita ce zata zo? Kuma
ko kunya babu ta yi zaune, koda yake ta lura shima
yana sonta, don haka duk abin da zata yi ba zaya ga
laifinta ba. Bayan ta gama Sallah, cikin daki ta dan
murza ma hannuwanta mai ta gyara fuskarta ta fito ta
raba su, ta shiga kicin in da kukunsu Mick yake aikin
abinci, nan ta zauna tana kallon tsarin girkinshi, suna
hira a hankali idan taga abin da bata gane ba, sai ta yi
mashi tambaya shi kuma ya bata amsa cikin dan lokaci
suka shaku ta shiga cikin harkar girkin tana taimaka
mashi. Yana da kirki da sakin fuska, don haka ba ta
samu matsala ba, ta kwantar da hankalinta tana daukar
darasin girki, itama wata makarantar ce.
31
Da aka kammala, ta rinka jidowa tana shiryawa
bisa tabur, har yanzu suna nan zaune, Daddy na kwancc
bisa kujera, yayin da ita kuma take zaune bisa kujera
karama, bata da alamar tafiya. Idan ya kalli Naja'atu sai
ta dauke kanta kamar ba ta ganshi ba, sai da komi ya
kammala sannan taje ta dan kwankwasa kofar dakin
Hajiya, ta bata iznin shiga, ta shiga ta sanar da ita
abinci ya kammala, Hajiya ta ce, "Ina Daddy yakc.?"
Ta yi murmushi ta ce, "Suna nan zaune cikin falo."
Hajiya ta dan tabe baki, ta ce, "Wai Faridar bata tafi ba
har yanzu.?" Та се, "Тa na nan." Hajiya ta jinjina kai ta
cc, "To Allah ya kyauta, wannan bayar da kai har ina?
Ji ki zuba mani abincin, ki kawo mani kema ki zauna ki
ci kada ki biye masu."
Ta dawo falon ta shirya mata abincin akan faranti,
ta dauka ta kai mata, sannan ta fito, to kuma sai taga
kamar bata kyauta ba idan ta zauna tana ci ba tare da.ta
yi masu magana ba, don haka ta isa in da suke, Daddy
ya zuba mata ido, ta ce, "Ga abinci idan kun tashi cі."
Ba ta jira amsa ba, ta tafi ta zauna tana zuba abincin."
Sai gasu sun taso, da ta gama zuba nata, ta aje masu,
Daddy ya ce, "Ba ki zuba mani ba." Ta yi murmushi ta
ce, "Ba aikina ba ne." Ta dubi Farida tana murmushi
amma sai taga ta daure fuska, yayin da shi kuma Daddy
ya sanya hannu ya dauki wanda ta zuba ma kanta, bai
yi magana ba ya fara ci, ta bishi da ido kawai, ya share
ta sai ta girgiza kai ta dauki wani filed din ta zuba ta
nuna ma Farida abincin ta ce, "Bissimillah." Amma sai
32
ta girgiza kai ta ce, "Alhamdulillahi." Daga ita har
Daddy suka zuba mata ido yanayinta ya canza-sosai, ya
yarda duk wanda ya dubc ta zaya gane.
Daddy ya ce, "Lafiya zaki ce kin koshi, alhalin ba
ki ci komi ba." Naja'atu ta ce, "Laifinka ne, ita ce
bakuwa ita ya kamata ka fara ba, amma ka janye nawa
kana ci, kanka kadai ka sani ba dole ta