Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels SIRRIN ZUCI NA SA'ADATU SAMINU KANin (Mrs. Sani Abbas) SIRRIN ZUCI - 1 T a bata lokaci sosai ckin daki, sannan ta fito tsakar gida inda Inna ke tankaden garin tuwo. Inna ta dago kai ta kalle ta, ta ce, "Har kin fito.?" Ta се, "Eh, yamma ta yi kuma ba ni son in yi dare." Ta се, "To ga kukar can, ki gaishe mani da ita, ai za ki iya ganc gidan ko.?" Ta ce, "Eh." Inna ta cc, "To sai kin dawo." Naja'atu ta duka ta dauki ledar da Inna ta zuba kuka dakakka, ta yi mata sallama ta fita. Sanye take da atamfa fara sol, da adon furanni kanana, ta saka hijabi fari da takalmi baci, jikinta yana kamshin turare mai sanyin kamshi, daidai gwargwado, Naja'atu natsattsiyar yarinya mai hankali da wayau, ta samu kyakkyawar tarbiya da kulawa, ga ilimin addini da na boko, duk da cewa iyayenta talakawa ne likis, sun yi iya bakin kokarinsu wajen bata ilimin boko yanzu haka ta kammala karatunta na N.C.E a kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Katsina, haka nan a fannin karatun Alkur'ani, ta sauke Alkur'ani mai girma, har ta harda ce haka nan tana da sani sosai akan wasu litattafan don haka ba karamar baiwa Allah ya yi ma Naja'atu ba. Mahaifinta Masinja ne a karamar hukumar Katsina. Daidai gwargwado suna samun rufin asiri, mahaifiyarta Salamatu ita kaďai ce matar Malam Audu watau mahaifin Naja'atu, ita ce babba cikin 'ya'yanshi, sai kannenta maza biyu ke bi mata, Rabi'u da Mas'udu, 4 ko wane yana fafutukar karatunshi, sai 'yan mata biyu Badiya da Fatima, su kuma duka Primary suke. Rayuwar gidan Mallam Audu, rayuwa ce mai ban sha'awa, saboda duk da cewar ba hali ke gare shi ba, amma akwai wadatar zuci, tun daga kofar gidanshi da ke cikin unguwar tudun wada zaka fahimci haka saboda 'ko da yaushe zaka samu kofar gidan fes fes haka ma cikin gidan da mutanen dake cikin gidan ba dai ka gansu da kazanta ba, haka nan yaran gidan na da natsuwa da girmama na gaba, don haka da yawa jama'a suke kallonsu da kima da daraja. Gidan Malam Audu ginin kasa ne dan madaidaici, amma ya shafe shi da siminti, dakuna uku ne cikin gidan sai daya cikin zaure in da su Rabi'u suke zaune, akwai dan fili da ya kebe in da suke kiwon dabbobi, nan ma koda yaushe fes yake ya kiblace shi babu kazanta. Malam Audu ba ya da wnai buri sai na iyalanshi, ya yi tsayin daka akan rayuwarsu, yana tsare masu mutuncin kansu, hakan ta sanya ya toshe kunnuwanshi ya tura Naja'atu makaranta ta ci gaba da karatunta bai kula ďumin da 'yan'uwanshi suka rinka yi mashi ba, kan ya dace a aurar da ita, to shi dai yasan shi kadai ne mai aurar da Naja'atu, kowane irin yanayi ta samu kanta sai ya fi kowa ji, don haka ya zabi bata ilimi mai kyau, akan ya aurar da ita, kuma Naja'atu ta yi mashi halarci ta yi karatunta tsakani da Allah, ba ta samu matsala ba, har ta kare lafiya. A ganinshi iya 5 gatancin da zaya yi mata kenan, musamman ganin ita cc babbar diyarshi, wata rana ita zata tallafi gidan duka. To kuma Alhamdulillahi, ya samu yarda yake so, kwalliya ta biya kudin sabulu, shima Rabi'u yanzu yana Jami'ar Baycro Kano, cikin shekararshi ta biyu yayin da shi kuma Mas'ud ya zabi fannin lafiya, (School of Nursing) ya ke nan Katsina, da zaran ya dawo kuma ba zama, zaya fita in da suke aikin kafin bakin kofar Durbi, tun ya na dan kamawa, har ta kai yanzu shima ya kware aikin suke yi sosai, don haka dan abin da yake samu, da shi ya ke yin hidimar karatunshi har ya na taimakon mahaifinshi da wasu abubuwan, rayuwarsu babu wuya, kuma babu dadi irin wancan haka nan basu dauki rayuwar da zafi ba. A hankali Naja'atu take tafiya cikin unguwarsu, har ta fito bakin hanya, ta tsaida Taxi ta shiga zuwa Layout, gidan Hajiya Halima, in da Inna ta aike ta. Hajiya Halima 'yar'uwar Inna ce, mace ce mai kirki da son zumunci, mijinta Alhaji Ummaru babban ma'aikacin Gwamnatin Tarayya ne, ya yi arziki sosai, sai dai shekara biyar kenan da rasuwarshi ya barta da 'ya'ya biyar, uku ne mata sai maza biyu. Daga cikin matan biyu sun yi aure, sai daya ce gida itama ba ta cika zama ba, saboda karatu yanzu tana Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, sai dan autansu Ibrahim, da ke Secondary, babban namijin Daddy bai cika zama Katsina ba tun bayan ya dawo daga London in da ya yi karatunshi ya tare gidansu na Abuja can yakc aiki. 6 To itama Hajiyar ba ta cika zama Katsinan ba sa lokaci-lokaci, rayuwarsu tafi karkata can Abuja. Yanzu ma wani biki suka zo shi ne suka hadu da Inna, ta yi mata kyautar kudi masu yawa, tana yi mata tsegumin ba ta son zumunci, ba ta zuwa gidanta, kuma ba ta tura mata yara su gaida ta. Inna ta bata hakuri dalilin haka ne ya sanya yanzu ta ce Naja'atu ta shirya taje ta gaido Hajiyar. Da mota ta sauke ta bakin hanya, sai ta gangara da kafa, a hankali tana tafiya zuwa gidan, akwai tazara tsakanin gidan da titi, amma da yake tana yin tafiyar da natsuwa, bata gaji ba. Ta kusa isa gidan, wata mota baka mai kyau tazo wucewa, ba zato mai tukin motar ya fada cikin wata kwata da gudu, ai kuwa gaba ki daya kwatar ta fallatso ta bata mata jiki gaba ki daya. Haushi, mamaki da takaici, gaba ki daya suka rufe ta, sai ma ta yi tsaye tana, kallon motar har ta rasa abin da zata ce." To shima mai tukin motar ya lura da abin da ya faru, don haka ya ja ya tsaya daga gefe, sannan ya fito ya nujfo in da take, dogo ne sosai fari, daga ni dan gayu ne yana ji da kanshi, kunnenshi manne da Earphone na wayarshi. Naja'atu ta rumtse ido cike da takaici, cikin bala'i ta dubi mutumin ta ce, "Wannan wane irin rashin mutunci ne, da rainin hankali? Ji bi yadda ka 6ata mani jiki, don takamar kana da mota, shi kenan don Allah ya ba ku dukiya sai ku dauki talaka kamar bawa, ku rinka taka shi yarda kukc so?" Mutumin ya tsaya kawai ya na 7 kallon ta, sai dai zuciyarshi ta tabu, kan irin bala'in da ta tsaya tana yi mashi, sai ka ce yaronta, alhalin gashi har ya fito don ya bata hakuri. Ya dan gyara tsayuwarshi yana kallonta cikin bacin rai, ya ce "Amma ba gashi na tsaya don in ba ki hakuri ba? Shi ne za ki rinka gaya mani magana irin haka.?" "An fada, ka kira Soja da 'Yansanda su raba ni da rayuwata, tunda na bata maka rai, ko ko shi kenan sai a yi mani in rasa nuna bacin raina, don ina tsoronka, to bari ka ji ni ba ni tsoroń kowa sai Allah." Tsaye ya yi yana kallonta cike da mamaki, bai ga dalilin da zaya sanya ta tsaya tana gaya mashi magana yarda take so ba, to sai dai bai iya fitinar ba balle ya biye mata su yi, don haka da saurinshi ya juya ya bude motarshi ya shiga ya yi tafiyarshi. Naja'atu ta kara kulewa, a ganinta take hakkin ya yi yawa. Kamar za ta yi kuka saboda facin rai, wani gida ta shiga nan kusa ta roki arziki ta wanke jikinta da hijabin, abin da ya dauke tsawon lokaci kenan, matar mai kirki sun jima suna hira da ita, tana bata labarin yarda abun ya faru. An kusa kiran Sallar Magaruba ta yi ma matar sallama ta fito, ba ta je gidan Hajiyar ba, gida ta koma, lokacin da ta isa an gama sallar Magariba, ta yi sallama ta shiga Inna na cikin dakinta don haka itama ba ta shiga daki ba, sai da ta yi alwala sannan ta shiga dakinsu ta cire kayan jikinta ta canza wasu ba ta yarda ta tsabtarsu ba, sannan ta yi sallah da ta gama ta umarci Badiya ta dauki kayanta taje ta daurayc mata su da 8 ruwa ta shanya, sannan ita kuma ta tashi, ta shiga dakin Inna, in da take zaune ta gama sallah tana lazumi. Тa zauna bisa kujera sai da Inna ta shafa addu'a sannan ta juyo kanta ta ce, "Yaya kin dawo.?" "Eh." Naja'atu ta amsa "Kin same ta kuwa."?" Inna ta tambayc ta Naja'atu ta fan tabe baki har yanzu akwai bacin ran a tare da ita. "Ban je ba, sai dai gobe in Allah ya kaimu:" Inna ta zuba mata ido, ta ce "Kamar yaya, to ina ki ka tsaya tun tafiyarki.?" "Har unguwar naje, wani mutum marar mutunci yazo wucewa ya wuce da gudu ta cikin wata kwata duk ya bata mani jiki, sai dai wani gida na samu na shiga na wanke jikina da hijabin, to kafin hijab din yasha iska magaruba ta taho, don haka ban isa ba na taho gida kada in yi dare." Inna ta jinjina kai ta ce, "To Allah ya kyauta, in jin dai ba ki biye mashi kun yi rigima ba, na san ki ba ki da hakuri." Naja'atu ta yi murmushi ta ce, "Ai kau na gaya mashi magana, da yake yasan ba ya da gaskiya ai baice komi ba, don ba ki ga yarda jikina ya 6aci ba ne, komin hakurin mutum dole ne ya yi magana tun da ai yana ganina kuma yasan da kwatar da yaga yazo wurin ba sai ya rage gudun ba, amma sai ya wuce kamar yana shirin tashi sama, shi ga mai mota." Inna ta ce, "Ke dai ba ki da hakuri, Naja'atu rayuwar duka guda nawa ce?" Naja'atu ta yi dariya ta cce, "Inna mutanen nan sai fa mutum yana nuna masu 9 yasan 'yancin kanshi, idan ba haka ba sai su rinka taka mutanc kamar bayi, don takamar suna da arziki." Inna ta ce, "Shi kenan dai Allah ya tsare, goben sai kije, ba ni jin dadin yarda take yawan yi mani tsegumin bani zuwa kuma ba ni barin ku kuje." "Insha Allahu zan je." Naja'atu ta cе. To washe gari da wuri ta fita, karfc sha biyu na rana taxi ta sauke ta bakin hanya, sannan ta taka a natse zuwa gidan su Hajiya Halima. Bakin get ta gaisa da maigadinsu, sannan ta wuce cikin gidan. Ta yi sallama cikin katafaren falon, wani ni'imtaccen kamshi ya bugi hancinta, ta lumshe ido ta san da gidan Hajiya Halima, karshen kallo kenan gare ta, duk wani abun kawa na zamani nan gidan take fara ganinshi. Gidan shiru kamar babu mutane ciki, sai da ta yi sallama sau uku sannan wata yarinya ta fito daga sashin kicin, suka gaisa ta sanar da ita Hajiya take nema. Yarinyar ta nuna mata kujera ta ce ta zauna, don haka ta isa ta zauna bisa kujera, yayin da yarinyar ta murda wata kofa ta shiga. Naja'atu ta bude ido tana kallon tsarin falon, komi a tsare babu tarkace sosai, hatta allon talabijin jikin bango yake manne sai 'yan sauran tarkacen na kasa kan wani irin teburi shi kanshi abun kallo ne kala daya da jikin talabijin din da rikoda da manyan sifikon da ke girke gefe, ga alama gabaki daya tare suka fito ta jinjina kai ko da yake ba abun mamaki ba ne tunda akwai abun yin hatta labulolin falon abun kallo ne. 10 Yarinyar ta murda kofa ta fito, ta ce, "Ta ce ki jira tana zuwa." Ta koma cikin kicin, ba'a dade ba sai ga faranti ta kawo mata da kayan karin kumallo, ta juya ta yi tafiyarta. Naja'atu ta zauna shiru, ba ta sake jin motsin kowa ba, babu yaro a gidan Ibrahim kanshi yana Abuja can yake zaune yana karatunshi, haka itama Zainab tana makaranta Zaria. Don haka babu kowa gidan sai Hajiya da 'yan aikinta, suma kowa yana can bakin aikinshi ta sauke kwayar idonta kan farantin da aka aje mata, nauyi take ji a zo á same ta tana cin abinci daga zuwanta, alhalin ko ganin wadda tazo wurinta ba ta yi ba. Tana nan zaune ta saka wannan ta kwance wancan, a kalla ta yi minti ashirin zaune sai ga Hajiyar ta fito tana ganin Naja'atu ta saki fuskarta sosai tana dariya ta ce, "Wai yau Naja'atu ce gidan mu? Lallai yau za'ayi ruwan sama garin nan." Naja'atu ta yi murmushi ta zamo dağa kan kujera, ta na gaida Hajiya Halima, mace mai kirki da mutunci tasan ciwon kanta tana Kaunar 'yan'uwanta ko ya ya suke bata raina talaka tana jansu jikinta, don haka 'yan'uwanta suke kaunarta sosai. Ta iso in da Naja'atu take zaune, itama ta zauna ta се, "Ban san ke ba ce ai da kin shiga ciki, lokacin na fito wanka, sannu kin sha zama, yaya Innar taku.?" Naja'atu ta sake sosai ta ce, "Lafiya lau ta ce a gaishe ki kafin tazo." Hajiya tayi dariya ta ce, "Ina amsawa, amma nasan ba zuwa zata yi ba, tunda dai na ganki ai na ji dadi, yaya babanku.?" Naja'atu ta ce, "Shima lafiya 11 lua." Ta ce, "Yaya karatunki, kin yi nisa ko.?" Naja'atu ta yi murmushi ta ce, "Ai na gama karatu Hajiya." "Allah Sarki, amma kin kyauta, yanzu kina nan gida kenan.?" Hajiya ta tambaye ta "Eh." Naja'atu ta amsa. Suka ci gaba da hira cikin fahimta, Hajiya ta dubi kayan kalacin da aka aje mata ta ce "Yaya ba ki ci abinci ba ga shi an kawo maki, ki saki jiki nan ma gida ne." Naja'atu ta yi murmushi kawai, sai ga yarinyar nan ta sake fitowa da wani farantin tazo ta ajc ma Hajiya kalacinta ne. Hajiya ta ce, "Sannu Lami." Yarinyar ta yi murmushi kawai, ta ce, "Daddy ya fito kuwa.?" Та сс, "A'a, bai fito ba." ta ce, "Je ki kwankwasa mashi kofar ya fito ya yi kalaci, rana ta yi sosai, ta amsa "To Hajiya." Sannan ta nufi wani dan lungu ta tsaya bakin wata kofa ta kwankwasa sau biyu ta juyo ta koma in da ta fito. Hajiya ta tsarc ta suna yin kalaci tare, tun dai tana dari-dari da Hajiyar, har ta kai ta saki jikinta, idan ka ganta ba ka cewa ta aje yara da yawa, yanzu ma sanye take da doguwar riga da wani lallausan leshi baki, mai adon farin zare dinkin zamani. Ya yi kyau da jikinta, kwalliyarta a saukake ta zuba awarwaro guda hudu makimanta da zabba biyu, kunnenta dan kunne ne zagayayye yana da girma sosai, Naja'atu ta natsu tana kallonta, duk abin da ta yi burge ta take yi. Bayan sun gama kalaci, ta kwashe kayan zata kai cikin kicin, Hajiya ta rinka kwabarta ta bari Lami tazo ta kwashe amma ta ce, "Babu komi." Ta kwashe ta kai kicin. 12 Tana fitowa ba zato suka yi ido hudu da abokin rigimarta na jiya, yarda ta tsaya tana mamaki shima haka mamakin yake yi, ya zuba mata ido cike da tsana, jiya ta bata mashi rai da yawa, a ganinshi yasan ya fata mata, amma tunda har ya tsaya ya fito don ya bata hakuri ai ya dace ta tsaya ta saurare shi, amma sai ta rufe ido ta rinka fadi mashi magana son ranta, kamar dama jiranshi take yi. Ya dan lumshe ido tare da jan wani siririn tsoki. To ita kuma mamaki take yi, sai yanzu ta gane shi babu shakka shi ne "Daddy dan Hajiyar, to sai dai itama har yanzu zarginshi take yi da nuna izgilanci da gadara ga talaka, sam bata yi nadama ba akan abin da ya faru jiyan. Ta kara daure fuska, ba ta son ya samu damar yi mata magana kan abin da ya faru. Ta iso ta zauna in da ta tashi, yayin da shi kuma yake tsaye rike da remote yana canjin tasha a talabijin, Hajiya ta ce, "Daddy ga 'yar'uwarka ku gaisa Naja'atu, nasan ba saninta kayi ba." Ta juya kan Naja'atu ta ce, "Kinga dan'uwanki nan Daddy." Naja'atu ta dan saki fuskarta ba ta son Hajiya ta fahimci akwai wani abu tsakaninsu, don haka ta dake ta ce mashi. "Ina yini.?" Ko kallonta bai yi ba ya amsa "lafiya." Bai zauna ba yana nan yana ta danna remote tashoshin kwallon kafa yake ta nema, sai ta ji ta kara tsanarshi, idan ba cin kada Hajiya ta ce wani abu da ta yi tafiyarta, don ba ta ga dalilin da zaya rinka raina mata wayau ba. 13 Lami ta fito da kayan kalacinshi kafin ta aje уа сс, "Tajc ta aje mashi bisa teburin cin abinci." Sai da ya gama abin da yake yi sannan yajc ya zauna yana kalaci, yana kallon, Naja'atu don haushi ko kallonshi bata sake yi ba, suka ci gaba da hira ita da Hajiya idan ma ta saka shi ciki sai ta yi shiru, haka shima ba ya son maganar ya daure fuska sosai, sau daya ta juya tana kallon sashin da yake cikin sa'a shima ita yake kallo, ya wurga mata harara cike da natsa, ita kuma babu alamar razana ta murguda mashi baki ta kuma daure fuska. Har ya kare kalacin ya dawo ya zauna, ya na yi ma Hajiya magana kan cewa gobe yake son tafiya Abuja. Ta cе, "Shi kenan ba matsala nima zuwa karshen sati ina ina nan tafe Ibrahim nata tsegumin an bar shi shi kafai." Ya ce, "Nima saboda shi ne ya sanya nake son komawa, amma ai hutuna bai kare ba." A hankali ya sauke kwayar idanuwanshi kan Naja'atu, a karo na biyu ta harare shi har da murguda baki,ya kara cika da farko ya share ta ya cije lebe, yana kallon akwatin talabijin, zuwa can ya juya yana kallon Hajiya ya ce, Mummy ki yi ma yarinyar nan magana ta shiga hankalinta, idan ba haka ba dukanta zani yi." Hajiya ta tsaya tana mamaki ta ce, "Wai Lami? Me kuma ta yi maka.?" Ya ce "Ba ita ba, wannan dake zaune kusa da ke." Hajiya ta dubi Naja'atu da sauri tana mamaki, ba ta ga alamar komi a tare da ita ba, sai ta juya tana kallonshi ta ce "Daddy kanka daya? Daga zuwan yarinya me ta yi maka? Me yasa ba ka son a 14 zauna lafiya ne.?" Ya ce, "Hararata take yi tun dazu." Hajiya ta tuntsure da dariya ta ce, "Ina ta harare ka, laifin me ka yi mata.?" Ta juyo tana kallon Naja'atu, ta ce, "Wai harararshi kike yi Naja'atu.?" Ta girgiza kai ta ce, "Ni ina ruwana da shi, shi dai ke ta hararata, kuma ba yarda zaka yi da ni." Hajiya ta sassauta murya a kanshi ta ce "Me yake faruwa ne Daddy, me ya hada ku.?" Ya ce, "Jiya da yamma ba na fadi maki mun yi rigima da wata yarinya ba.?" Hajiya ta ce, "Haka ne.?" Ya ce, "To ai ita ce duk iya maganar da ta fadi mani ban kula ta ba, shi ne yanzu tun da na fito take hararata har da murguda mani baki sai ka ce abokinta." Hajiya tastuntsure da dariya, ta ce "Shi kenan dara taci gida, wa ya yi fada da kanwarshi, don haka ne nake gargadinku da ku rinka biya zumunci don gudun faruwar irin haka, yanzu meye ranar irin haka, ke Naja'atu dama jiya kinzo nan unguwar ne? Ta ce "Eh dama nan zani zo da ya ba ta mani jiki shi ne na shiga wani gida na wanke jikina da hijab din, to kafin ya bushe yamma ta yi sosai, don haka na koma gida. Hajiya ta jinjina kai, ta ce, "To yanzu dai shi kenan komi ya wuce, tunda kowa ya gane dan'uwanshi, kiyi hakuri." Naja'atu ta juya ta dube shi, ta daure fuska sosai, sai ta kara hawa itama, "Me yake takama dashi? Ita dai tasan ba ta bukatar komi wajenshi, kuma iya kacin abin da zaya yi mata bai wuce ya ce ta fita ta bar masu gida ba, to koma bai ce ba tafiya zata yi. Ta juya 15 tana kallon Hajiya, ta ce, "Ni Hajiya bani da matsala da shi, shỉ ne dai yake ganin laifina ba don na fadi mashi gaskiya, abin da ya yi ba daidai ba ne." Hajiya tana dariya ta ce, "To naji, shi kenan a rufe maganar komi ya wucc." Naja'atu ta mike tana shirin tafiya, Hajiya ta dago kai tana kallonta, ta ce, "ina za ki kuma,: Ta сc "Zani koma gida." Hajiya ta dan daure fuska ta ce, "Naja'atu haka kike da riko ko.?" Ta dan saki fuskarta ta cc, "Allah kuwa Hajiya ba haka bane, komi ya wuce." Ta cc, "To ki zauna ki na nan, ai yini ki ka zo yi min ko.?" Naja'atu ta sarda kai ta ce, "Ba yini zan yi ba, dama cewa ta yi kawai in zo in gaida ki." Та сс, "Тo ni na ce ki yi mani, yini, ta amince ko? Ai dai in kin koma ba dukanki za ta yi ba." Ba ta da zabi dole ta amince da haka, ta juya tana kallon sashin da Daddy yake zaune, ya zuba mata ido cike da tsana, sai ya aje remote din yha mike ya fice daga falon, to ganin abin da ya yi ne ya sanya ta zauna, sai taga iyakarshi. In takamarshi zafin rai, itama gidan ya tarda. Bayan sunyi sallar azahur, Hajiya ta tambaye ta idonta iya kitso ta ce mata ta iya, don haka ta zauna tana yi ma Hajiya kitson suna hira, Hajiya mace ce har mace mai son zumunci, ba ta kyamar mutane irin yarda wasu masu hannu-da-shuni suke yi, da zaran sun yi arziki sai kaga dan'uwansu ciki daya basu hulda dashi ba ya sakewa dasu bai ga fuska ba, sai wasu jayc-jayc, amma ita komi nata saukake, don haka Naja'atu ta ji 16 2 7 e dadin yini gidan ko ba komi ta Karu da abubuwa da dama. Da yamma ta yi shirin tafiya, bayan ta gama sallar La'asar cikin dakin Hajiyar, ta gyara fuskarta ta ce ma Hajiya zata tafi, Hajiya ta harare ta da wasa, ta сс, "Ki tafi ina? Wai kc ba ki sakcwa da mutane ne? To kina nan ba in da za ki, idan kin koma gidan me za ki yi, ba za ki zauna ki rinka debe mani kewa ba.?" Naja'atu ta cc, "Hajiya Inna kada ta ji ni shiru, tunda ban ce mata zani kwana ba." Ta cc, "Amma ai tasan nan ki ka taho ko.?" Ta jinjina kai, ta ce, "To ki zauna da daddare munje gidan in fadi mata da bakina, shi kenan ko.?" Babu-yarda zata yi, dole ta yi hakuri. Sai kusan karfe takwas suka fita, Hajiya ke jan motar yayin da ita kuma kc zaune gefenta, har suka isa gidansu suna hira Hajiya ta rinka nuna mata ta saki jiii da ita. Kofar gida suka ci karo da Malam Abdu mahaifin su Naja'atu, ya dawo daga Masallaci, ya tsaya yana kallon motar da ta tsaya kofar gidan shi cike da mamaki, sai da yaga Naja'atu ta fito sannan ya saki ranshi, Hajiya ta fito yana dariya ya се, "То, Hаjiya da kanki ki ka maido 'yar taki.?" Ta yi dariya ta ce, "Ga ta na dawo da ita kuma da ita zani koma in har an amince mani." Malam Abdu ya yi dariya ya сe, "To wannan kuma tsakaninki da 'yar'uwarki, in ban da abin ki Naja'atu ai taki ce." Hajiya ta yi dariya ta ce, "Ai nima haka na gani suka shiga gida suna dariya. 17 Inna na cikin daki ta ji sallamarsu, ta fito tana amsa sallamar, ta ce "Hajiya kece da kanki.?" Та се, "Gani fa, ai kafata tafi taki zumunci Salamatu, in don ta ke ne ba za

Chapter 1 of 6