cewa yaron nan da yiwa
matsafi Shamrul tambaya akan addininsu za'a yanke wa
hukuncin kisa, sai suka yaɗa labarin izuwa cikin gari, nan fa
al'ummar gari suka dinga tuttuɗowa suna cincirindo a fadar
domin su ganewa idanuwan su.
Domin a yau ne zasu tantance shin tsakanin Ubangijin
wannan yaro Imran da matsafi Shamrul wane ne na abin
bauta na gaskiya.
Sarki Ladiyas na kammala wannan batu sai sarki Ladiyas
ya koma kan karagar mulkinshi ya hakimce.
Kawai sai wani garjejen ƙato ya ɗauki yaro Imran ya ɗora a
jikin wani zagayayyan tudu a fadar sannan ya koma gefe guda
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
107
ya ja ya tsaya, sarki Ladiyas ya yi wa sarkin yaƙi Darusu inkiya
ta wutsiyar idanu dake nuna bashi umarni.
Cikin dakewar zuciya gami da zafin nama sarkin yaƙi ya
zare wata sharɓeɓiyar adda a gadon bayanshi ya durfafi inda
Imran yake domin ya datse wuyanshi.
Sarki Ladiyas, matsafi Shamrul da sauran bokayen suka
bushe da dariyar mugunta har da ƙyaƙyatawa.
Jama'a kuwa da yawan su sai suka fara zubar da hawayen
takaici da baƙin ciki
Ya yin da sarkin yaƙi ya isa daf da shi sai ya daga addar ya
ɗora akan waya yaro Imran.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga wata
kyakkyawar halitta ta keto daga saman fadar ɗauke da
waɗansu mutane guda biyu.
Ba wani bane wannan halitta da mutanen biyun ba face aljani
Hadimul-khairi ɗauke da gimbiya Lamrat matar sarki Ladiyas
da 'yarta yarinya Shuraiba.
Kafin addar sarkin yaƙi Darusu ta yanka wuyan Imran
aljani Hadimul-khairi ya ɗauko wata farar kwalba mai ɗauke da
wani koren ruwa ya watsa inda Imran da baiwa Sharifa suke,
take sarƙoƙin dake ɗaure a jikkunansu da addar dake wuyan
Imran sun narke suka zama ruwa.
Cikin matuƙar firgici sarkin yaƙi, sarki Ladiyas da sauran
jama'ar fada suka ɗaga kawunansu izuwa sama.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
108
Yaro Imran, hadima Khadijat, sarki Lazwar, sarkin yaƙi,
bawa Shamsal, gimbiya Mashlira da aljani Za'aratul-layal,
kuwa sai suka cika da matukar farin ciki maral-musaltuwa.
Aljani Hadimul-khairi ya a sauka a turba bisa diga-diganshi.
Nan fa aka shiga kallon-kallo tsakanin sarki Ladiyas, da
uwar gidanshi gimbiya Lamrat, matsafi Shamrul da yaro
Imran da hadima Khadijat wato baiwa Sharifat, sarkin yaƙi
Darusu da sarki Lazwar.
Cikin matukar ɓacin rai mai girma Ladiyas ya dubi uwar
gidanshi Lamrat ya ce "ya uwar gidana shin ina dalilin
wannan zuwa naki a cikin wannan yanayi?
Koda jin wannan tambaya daga bakin Sarki Ladiyas sai
gimbiya Lamrat ta tari numfashinshi tana mai daka mashi
tsawa, ta dube shi cikin matuƙar fushi ta ce "kai tsohon
AZZALUMI kuma la'ananne ka yi sani yanzu kan mage ya
waye, a yau ne zan ɗauki fansar jinin mai gidana maƙeri
Murrasu daka ni da 'yata Shuraiba, haƙiƙa masu iya magana
sun yi magana da suka rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai
kaya, ka yi sani cewa tsawon shekarun da ka shuɗe kana
azabtar da jama'ar birnin ISTANBUL kana yiwa mutane BAKIN
ZALUNCI, to ranar ƙin dillanci ta zo maka.
Shawarar da zan baka ita ce ka yi hanzari ka rubuta wasiyyar
da kake son bar wa jama'ar kafin mu zare maka ruhinka daga
gangar jikinka. Sannan ina so ka yi sani cewa ni da 'yata
Shuraiba tuni mun karɓi addinin yaro Imran.
A halin yanzu ni ba uwar gidanka ba ce face abokiyar
gabar ka, dama dai-dai da rana ɗaya ban taɓa ƙaunarka kawai
ina yi maka biyayya ne bisa dole don tana din gobe na".
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
109
Sa'adda mai girma Ladiyas ya ji wannan batu daga bakin
gimbiya Lamrat sai zuciyarshi takama tafarfasa tamkar zata
ƙone ya daka mata tsawa a lokacin da idanuwanshi suka
kaɗa suka yi jajur cikin kakkausar murya mai ya ce "kaicon ki
yake Lamrat haƙiƙa kin tafka babban kuskure da har kika yi
gangancin haɗa kai da maƙiya na domin farautar rai na, a yau
ne zan yi maki hukunci mafi muni ke da 'yarki Shuraiba".
Sa'adda sarki Ladiyas ya zo nan azancen shi sai ya
miƙe tsaye zumbur daga kan karagar shi ta mulki ya cire
alƙyabbarshi, take wata irin gagarumar shigar yaƙi mai
matuƙar firgici da ban tsoro ta bayyana a jikinshi. Kawai sai ya
dako wawan tsalle daga inda yake tsaye yana saman ya daga
hannunshi sama wata irin sharɓeɓiyar takobin sihiri ta
bayyana a gare shi, ya sauka bisa diga-diganshi a daf da inda
Lamrat take.
Koda ganin hakan sai yarinya Shuraiba tayi wuf ta zare kwari
da bakanta ta yi shirin ko ta kwana.
Sarki Lazwar kuwa duk da cewar jikinshi ya yi tsami akwai
manyan raunuka, amma sai ya yi wuf ya kwaci wata takobi a
hannun wani badakare ya falfala da azababban gudu izuwa
kan sarkin yaƙi Darusu
Baiwa Sharifa da yaro Imran kuwa sai suka yi ɗauki izuwa kan
matsafi Shamrul suna masu ƙwala kabbara, bawa Shamsal da
sarkin yaƙi kuwa sai suka tari dakarun dake fadar, aljani
za'aratul-layal sai ya yi girgiza take surarshi ta canja daga ta
bil'adama izuwa ta aljani kawai sai ya rufawa mai gidanshi
sarki Lazwar baya,
a lokacin ne gimbiya Mashlira sai cire hular ƙarfen dake kanta
fuskar ta ta bayyana a fili, nan fa kowa ya cika da mamaki
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
110
ganinta, kawai sai ta yi koyi da aljani Za'aratul-layal ta kaiwa
masoyinta sarkin Lazwar ɗauki.
Lokaci guda ɓangarorin biyar suka afkawa juna aka
garƙame da azababban yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro.
Wohoho! kaico haƙiƙa guguwar annoba idan ta taso
babu mai maganin ta face Allah, kuma tabbas in da babu ƙasa
nan ake gardamar kokowa, domin KARON MAZA sai
JARUMAN DUNIYA da suka ciri tuta a GUMURZUN
SHEKARA DUBU, waɗanda komai TSANANI DA UKUBA a
filin DANDAZON MAYAKA baya sa su gudu.
Haƙiƙa komai dakewar zuciyar mutum idan ya ga yadda fadar
ta yamutse da gumurzu dole ne ya ɗimauce ya fita daga
hayyacin shi domin dola ne artabun ya zamo tashin hankali.
Nan fa jama'a suka ɗimauce suka kama guje-guje da
ifice-ifice domin tsira da rayukansu
Ɓangarorin suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare
cikin matuƙar baƙin zafin nama JURIYA DA BAJINTA tamkar
jikkunan su basu kasance na bil'adama mai jini tsoka ba.
Kaico! Haƙiƙa duk wanda bai fita filin yaƙi ba to bai ga
ƙarshen tashin hankali ba,
wanda bai san shi ba shi ne yake fatan zuwan shi, ana fara
wannan ɗauki ba daɗi ne gimbiya Lamrat, yarinya Shuraiba da
Aljani Hadimul- kahiri suka fara gane cewa tabbas shayi ruwa
ne ba abinci mai nauyi ba, domin kuwa tsananin zafin naman
sarki ladiyas ya nunka nasu sai arba'in,
Nanfa ya zamana cewa mutum uku sun kasa galaba akan
ɗaya ya zame masu alaƙaƙai, duk sa'adda suka kai mashi hari
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
111
da makaman smmsu idan ya kare da takobinshi, sai kaga
makaman sun dakushe kuwa ko gezau bai yi ba.
Idan kuwa Ladiyas ya kai masu harin idan suka goce sai
ya zamana cewa duk abin da takobin ta saran sai ya yi bindiga
ya tarwatse koda kuwa gini ne.
Matsafi Shamrul, yaro Imran da hadima Khadijat kuwa tuni
labari yasha banbam, domin kuwa sun hana tsafi Shamrul
rawar gaban hantsi, har sai ya zamana cewa ya daina amfani
da makami ya dawo yaƙar su da ƙarfin sihirin tsafi, domin wani
lokacin idan Imran da Khadijah suka sare shi ta takubban su
sai su ga raunin ya koma ya haɗe sumul, wasu lokutan ma sai
ya rikiɗa ya zama haske.
Sarki Lazwar, gimbiya Mashlira da aljani Za'aratul-layal
kuwa sun wanzu suna masu kaiwa sarkin yaƙi Darusu harehare cikin gwanintar yaƙi tamkar za su cinye shi ɗanye.
Amma bisa mamaki sai ya zame masu ƙadangaren
bakin tulu suka kasa samun nasarar koda lakutar jikinshi, duk
kuwa da cewar ƙarfin mutum biyu ne da aljani ɗaya akan
mutum guda.
A ɓangaren bawa Shamsal da sarkin yaƙi ku wa sun
wanzu suna ragargazar dakarun dake fadar duk inda suka
sanya gaba sai ka ga dakarun na zubewa ƙasa matattu, nan
fa ƙarar karafniyar ƙarafa, ihun mazaje hade da hargowar
aljanu gami da ifice-ificen jama'a ya cika dodon kunne, ƙura ta
turnuƙe fadar baki ɗaya tamkar haɗari zai gangamo a kece da
ruwan sama.
Lokacin da aka ruguntsume da azababban yaƙi
tsakanin manyan sarakuna biyu, aljanu biyu, gami da jarumai
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
112
shida sai yaƙin ya zamto tashin hankali gami da ban tsoro ga
yan kallo.
Sai da aka shafe tsawon sa'a biyu ana wannan ɗauki ba daɗi
tsakanin jaruman ba tare da ɗayan su ya samu nasarar
hallaka ɗaya ba.
A bangaren sarki Ladiyas kuwa ya zamewa su gimbiya
Lamrat ANNOBA ƊARI domin duk da cewar Hadimul-kahiri na
amafni da addu'o'i domin su hallaka sarki Ladiyas amma sai
hakan ya gagara domin sai sun datse wuyanshi suna tunanin
ya mutu sai kawai su ga wani ruhun ya keto daga cikin
ƙarƙashin ƙasa ya sake shiga jikinshi.
Sai kuma a ɗora wani gumurzun, nan fa ya zamana cewa
su Hadimul-kahiri sun kashe fiye ruhika arba'in na sarki
Ladiyas.
Al'amarin da ya sanya su duka ukun suka samu miyagun
raunuka musamman yarinya Shuraiba. Haƙiƙa sarki Ladiyas
bakaramin hatsabiba ne domin ya yi nisa a halarar tsafi wanda
cimma mashi abu ne mai matuƙar wahala.
A dai-dai wannan lokaci ne yaro Imran da hadima
Khadijat suka samu nasarar hallaka matsafi Shamrul, ta
hanyar amfani da takubbansu suka soka mashi akan ƙawon
zuciyarshi, ya yin da suka hango su yarinya Shuraiba kuma
suka ga irin mugun halin da suke ciki sai suka kai masu ɗauki.
Nan fa ya zamana cewa labari ya sha bamban domin a
wannan karon sai ya zamana tasirin sihirin dake tare da sarki
Ladiyas ya fara karyewa, domin duk sa'adda hadima Khadijat
da yaro Imran suka kai mashi hari da makamansu duk inda
suka sara sai su ga sun tsarga jikinshi.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
113
Bisa taimakon Ubangijin halitta daƙyar da siɗin goshi suka
samu nasarar hallaka sarki ladiyas, ta hanyar sare mashi
hannaye da ƙafafuwanshi suka jefar da gawarshu a ƙas.
In da ace mutum ya na wannan waje a lokacin da sarki
Ladiyas da matsafi Shamrul suka yi mutuwar wulakanci dole
ne ya yi farin ciki maral-musaltuwa. Bisa ganin yadda Allah
Ubangijin halitta ya kawo ƙarshen azzalumai.
A dai-dai wannan lokaci ne su gimbiya mashlira, Aljani
Za'aratul-layal da sarki Lazwar suka samu nasarar hallaka
sarkin yaƙi Darusu.
Sa'adda al'ummar fadar da su bawa Shamsal suka yi
arba da gawar sarki Ladiyas, da ta matsafi Shamrul sai
dukkanin su suka durƙusa ƙasa bisa gwiwoyinsu suka yi
mubaya'a, suna masu cewa "haƙiƙa mun bayar da gaskiya ga
Ubangijin yaro imran
Cikin hanzari waɗansu likitoci suka shigo fadar ɗauke da
kayan aiki suka shiga duba lafiye yarinya Shuraiba, gimbiya
Lamrat,da sarki Lazwar.
Sannan yaro Imran ya ruga izuwa inda hadima Khadijat
take suka rungume juna cikin matuƙar farin ciki maralmusaltuwa bisa sake saduwa da juna da suka tsawon
shekaru.
Daga bisani yaro Imran ya janye jikinshi daga na 'yar uwarshi
Sharifa.
Ya juya ya fuskanci jama'a sannan ya buɗi baki ya ce "ya ku
al'ummar wannan birni mai albarka haƙiƙa na tabbatar da
cewa a halin yanzu zukatanku sun gamsu cewa babu abin
bauta da gaskiya sai Allah mai kowa mai komai.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
114
Saboda haka yanzu ba tare da wani ɓata lokaci ba yaro Imran
ya faɗi kalmar shahada, take ɗaruruwan jama'ar dake fadar
suka maimaita.
Sautin muryoyinsu ya cika fadar kuma ya amsa kuwwa izuwa
cikin birnin baki ɗaya.
Bisa mamaki sai Imran da hadima Khadijat suka ji sarki
Lazwar da sarkin yaƙinshi haɗe da bawa Shamsal tare
gimbiya Mashlira sun amsa kalamar shahadar.
Nan fa suka cika da al'ajabi, sarki Lazwar ya tako da
ƙafafuwanshi izuwa inda imran da Khadijat suke ya dubi
Khadijat cikin girmamawa ya ce "ya ke Sharifat Haƙiƙa rashin
sani yafi dare duhu, na zo wannan birni neman ki, ashe kina
tare da ni ban sani ba, yanzu ga shi na karɓi addinin
Musulunci shin ina makomar tafiya ta izuwa nemo abubuwan
da za su warkar da ni daga sihirin da abokin gaba ta sarki
Durwazu ya yi min, na karɓi Musulunci ne domin yadda a
zuciyata, na samu tabbacin ne a lokacin da nake fafata yaƙi
da miyagun halittun dake cikin ɗakin duhu, inda dukkan wata
dubara ta ƙwace min na nemi taimakon Ubangijin imran".
Sa'adda sarki Lazwar ya zo nan azancen shi sai
Sharifa, yaro Imran da sauran jama'a suka cika da matuƙar
mamaki.
Sharifat ta ce ''ya kai wannan sarki mai daraja ka yi sani cewa
ai shi addinin Musulunci yana shafe duk abin da ya tuve,
saboda haka a halin yanzu sihirin da sarki Durwazu ya yi
maka ya karye.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
115
Babu buƙatar sai na taimaka maka wajen mallako abubuwan
da za su warkar da kai daga sihirin, domin abubuwan da za'a
mallako dukkanin su na tsafi ne.
A halin yanzu zaka iya kusantar kowace irin 'ya mace
kuma har ka samu haihuwa ka yarda Ubangijin musulunci
kawai a koda yaushe";
Koda jin wannan batu daga bakin Sharifa wato sai
sarki Lazwar ya cika da matuƙar farin ciki wanda bai taɓa yin
kamar shi ba.
Daga wannan ne aka ɗunguma izuwa gidan sarauta domin
kowa ya huce gajiyar dake tattare da shi.
A cikin wannan dare ne hirar soyayya ta ɓarke tsakanin sarki
Lazwar da gimbiya Mashlira 'yar shugaban maridai, yaro
Imran da yarinya Shuraiba, Sharifat da bawa Shamsal.
Kuma a wannan dare ne akayi shelar naɗin sarautar
yaro Imran da wazirinshi Shamsal.
kafin wayewar gari ciki da wajen birnin Istanbul ya cika
ya batse da jama'a baƙin sarakuna daga kowa ce nahiya da
'yan kasuwa.
Tun lokacin da alfijir ya keto bayan an gabatar da sallar asuba
sai jama'a suka yi tsinke a fadar maza da mata yara da
manya.
Sarakuna da manyan baƙi an ware masu wajen zaman su
daban, haka ma na talakawa, komai dai an yi shi bisa tsari.
Sarkin fadar birnin Istanbul wani dattijo ya tashi ya gabatar da
jawabin maraba ga mahalar ta taro. Sannan ma'ajin sarautar
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
116
ya gabato da kayan sarauta da suka haɗar da alkyabba,
rawani, kwagiri, takalmi da sauaran su.
Sarkin fada Huzaifa ya ɗauki kayan ya shiga sanya
wa yaro Imran a jikin shi, bayan ya kammala ne sai ya umarci
yaro Imran ya je ya zauna bisa karagar mulki ya hakimce, nan
fa tsananin kyawun surar Imran ya fito ƙarara yarinya shuraiba
kuwa sai ta dunga satar kallon shi tana yi mashi kallo mai
nuna alamun tsantsar so da ƙauna.
Nan take jama'ar fadar suka yi mubaya'a a gare shi, daga
bisani kuma sai aka shiga shagalin ɗaurin aure mutum shida
sarki Imran da yarinya Shuraiba baiwa Sharifa da bawa
Shamsal, sarki Lazwar da gimbiya Mashlira.
A wannan rana anyi gagarumin shagalin da ba'a taɓa yin
kamar shi ba tsawon kafuwar birnin Istanbul.
Bayan an kammala ciye-ciye da tanɗe-tande, kowa ya
cika cikinshi sai sarakunan da suka halararci bikin naɗin
sarautar suka dunga zuwa, gaban sarki Imran suna karɓar
KALMAR SHAHADA tare da jama'arsu, haƙiƙa farin ciki ya
cika zuciyar kowa.
Bayan tarewar angwaye uku sarki Imran, shamsal da sarki
Lazwar.
Sai sarki Imran ya umarci aljani Hadimul-kahiri ya ɗauki sarki
Lazwar da amaryarshi gimbiya Mashlira da sarkin yaƙi haɗe
da aljani Za'aratul-layal domin ya kai su izuwa birnin
ZAWATUL-IFDAR, amma sai da aka fara zuwa ta birnin su
gimbiya Mashlira aka musuluntar da sarkin maridai da
mutanenshi kuma aka karya sihirin tsafin da aka yi masu suka
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
117
dawo ainahin siffar su irin ta bil'adama suka daina cin naman
bil'adama bisa taimakon Ubangijin halitta.
An yi shagalin farin cikin dawowar yar sarkin muridai
gimbiya mashlira. Sai da aka shafe mako ɗaya sannan aka
sake ɗungumawa aka durfafi birnin Zawatul-ifdal, amma sai
aka bar sarkin yaƙi imhal domin ya cigaba da bayar da ilimin
addini ga jama'ar birnin, kuma sarkin maridai ya naɗashi
wazirinshi.
Lokacin da aka isa birnin Zawatul-ifdal sai sarki lazwar ya
cika da matuƙar farin ciki, bisa jin labarin abin da ya faru da
magajin gari Yasiran da amarya Munirat wacce a halin yanzu
ita ce ke riƙe da karagar mulkin birnin.
Jama'a sunyi farin cikin dawowar sarki lazwar, ba tare da
damuwa ba aka sake ɗaura auren amarya Nunirat da sarki
Lazwar, sakamakon mutuwar angonta, amma da ƙyar da siɗin
goshi sarki Lazwar ya shawo kan gimbiya Mashlira ta amince
aka ɗaura auren. Sai aljani Za'aratul-layal da Hadimul-kahiri
suka koma izuwa birnin Istanbul.
Sannu-sannu bayan mako ashirin sai aka wayi gari
matayen sarki Lazwar Munirat da Mashlira suna ɗauke da
juna biyu.
Farin ciki a wajen sarki Lazwar kuwa kamar ya zautu, ya dinga
rabon dukiya da suturu na alfarma.
Tun daga wannan rana HASKEN MUSULUNCI ya
mamaye duniya baki ɗaya zaman lafiya ya wanzu, zalunci da
bautar gumaka suka rushe baki ɗaya.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
118
Ƙarshe
Alhamdulillah
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
FATAUCIN BAYI
Rubuta labari
MANSUR USMAN SUFI
Lokacin da su jaruma Nabihat suka iso izuwa bakin
tanatin, sai Nabihat ta ɗauko hodar banju a cikin aljihun rigarta
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
119
ta busa ta izuwa cikin tantin, jim! Kaɗan sai suka kunna kai ciki
suna shiga suka tarar dakaru masu dafa abinci sun kama
barci mai nauyi.
kawai sai suka cire tufafin dakarun suka maye da na sannan
suka rufe fusakunsu da hulunan ƙarfe.
Kawai sai suka matsa izuwa inda dakarun suka ɗora
sanwa akan wuta suka buɗe murafun tukunyoyin suka
zazzaga wannan hodar banju a cikin, sannan suka mayar
suka rufe ruf.
Bayan shuɗewar daƙiƙa goma sai suka zuzzuba
abincin a cikin waɗansu ƙananan akushi, suka ɗora akan
farantai na azurfa, sannan juya suka fice daga tantunan suka
shiga rarrabawa dakarun dake cikin jirgin ruwan abincin mai
dauke da hodar banjun har suka iso izuwa inda wani sadauki
yake.
Nabihat ta ɗauki akushi ɗaya ta miƙa mashi ya karɓa ya
bude ya sanya hannunshi ya yi loma ɗaya, kawai sai ya dubi
Nabihat ya ce "ya kai Himairu ya aka yi abincin nan ya yi ɗan
karen daɗi haka?
Koda jin wannan tambaya sai Nabihat ta yi murmushi
gami da gyaɗa kai, kawai sai ta huce gaba ba tare da bawa
sadaukin amsar tambayar shi ba.
Haka dai suka cigaba da rabawa dakarun abincin, har suka
iso inda suka bar saduki Hushaibu. Nabihat ta ɗauki akushin
ta miƙa mashi ya karɓa.
Har Hushaibu ya buɗe da nufin cin abincin kwai ya ji
zuciyarshi ta buga da ƙarfi, kawai sai ya yi jifa da akushin ya
durfafi madafa cikin hanzari.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
120
A dai-dai lokacinne su jaruma Nabihat suka kammala
raba abincin suka samu wata maɓuya a cikin jirgin suka laɓe.
A fusace Hushaibu ya kunna kai izuwa cikin tantin, ai
kuwa sai ya yi arba da masu dafa abincin kwance suna sharar
barci babu tufafi a tare da su.
Cikin matuƙar fushi gami da tashin hankali ya zare
takobinshi ya ruga izuwa waje yana mai ƙwallawa sauran
dakarun kira.
Al'amarin da ya janyo hankalin sadauki Sharkar kenan
ya zare takobinshi da nufin dakawa dakarun tsawa.
A dai-dai wannan lokaci ne hodar banjun da su Nabihat
suka zuba a cikin abincin ta fara bugar da dakarun suna
ɓingirewa kasa suna sharar barci.
Kafin Sharkar da Hushaibu su farga fiye da rabin dakarun
dake cikin jirgin ruwan sun kamu da barci mai nauyin gaske,
cikin matuƙar kaɗuwa gami da tashin hankali sadauki Sharkar
ya cigaba da falfala azababban gudu, yana mai kurma wawan
ihu
Nan fa sauran dakarun da ba su kai ga cin abincin ba
suka firgice suka ɗauko makaman yaƙin suka dinga fitowa
daga kowace kusurwa a jirgin.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga su jaruma
Nabihat da sauran 'yan matan fursunonin sun yo fitar burgu
daga maɓuyar su suna, suka yi ɗauki izuwa kan dakarun suna
ihu da kururuwa mai firgitarwa.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
121
Koda ganin hakan sai dakarun suka yi ɗauki kansu
suna ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA a filin
daga.
Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da
waɗannan zaratan 'yan mata su ashirin kacal! Suka tunkari
ɗaruruwan dakarun dole ne ya cika da mamaki kuma ya jinjina
masu ya tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA, mata
masu kamar maza.
Ana haɗuwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai
matuƙar muni, ban tsoro daban al'ajabi.
Nan fa gaba ɗaya jirgin ruwan ya yamutse da ƙarar haɗuwar
makaman yaƙi, gami da ihu da kururuwar mazaje.
Nanfa Nabihat da 'yan matan fursunonin suka wanzu
suna kaiwa dakarun sara da suka cikin matuƙar zafin nama
tamkar jikkunan ba su kasance na jini da tsoka ba.
Cikin abin da bai gaza daƙiƙa arba'in ya zamana cewa sun
samu nasarar hallaka fiye da mutum hamsin na dakarun sun
rauna ta fiye da ɗari biyu.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin dakarun kenan
kuma ya fusata su ainun, bisa ganin cewa a matsayin su na
GWARAZAN MAYAƘA, amma a ce 'yan mata sun zame masu
alaƙaƙai kuma GOBARAR ANNOBA.
Nan fa dakarun suka ZAGE DAMTSE wajen kaiwa su Nabihat
miyagun hare-hare.
Ana cikin wannan artabu ne wani garjejen sadauki, ya
kaiwa wata daga cikin 'yan matan wani wawan sara, da nufin
tsinke mata wuya amma budurwa ta sunkuiya cikin zafin
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
122
nama, takobin sadauki ta sari iska. Kafin ya sake mayar da
martani, budurwar ta cire wata siriyar wuƙa a damtsenta s
caka mashi a maƙogaranshi, sannan ta sanya ƙafarta ɗaya ta
daki ƙirjin shi da dukkan ƙarfin ta.
Saboda da matuƙar ƙarfin dukan sai da ya yi sama
tamkar an janye shi da ƙugiya ya faɗa cikin tekun yana mai
tsandara ihu.
Kawai sai budurwar ta sake afkawa cikin dakarun ta ci-gaba
da saran su.
Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne SADAUKi Sharkar ya
samu nasarar make Nabihat ta faɗi ƙasa, magashiyan
nunfashin ta na fita daƙyar, kawai sai ya sanya hannunshi ya
damƙo wuyanta ya tattare dukkanin karfinshi da nufin karya
wuyan Nabihat.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga Nabihat ta
dunƙule hannayen ta biyu ta girɓawa sharkar naushi a fuska.
Saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da ya yi katantanwa a
sama sau uku, sannan ya kife a ƙasa, yana mai tsandara ihu
sakamakon zafi da zugin da ya ji, haƙorinshi guda ɗaya ya yi
fitar burgu daga cikin bakinshi jini ya yi tsartuwa.
Amma saboda karfin zuciya gami da juriya irin ta
manyan GWARAZAN JIYA sai miƙe tsaye zumbur yana mai
goge jikin dake bakinshi yana mai gyara tsayuwa.
A dai-dai lokacin da Nabihat ta mike tsaye zumbur, aka sake
sabon kallon kallo,
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
123
Sannan suka sake afkawa junan da yaƙi,ana fara wannan
arbu ne Nabihat ta shammaci sharkar ta gabza masa naushi a
kirjin sa da kafafun ta biyu, saboda karfin naushin sai da
sharkar yayi tafiya a sama ta kamar dakika latalin yana mai
kurma ihu Sannan ya faɗa tekun Baharul-sawara,
Koda samun wannan nasara sai jaruma Nabihat ta ruga izuwa
inda yan uwan ta yan matan suke ta kai musu ɗauki su ka
cigaba da ragargazar dakarun.
Cikin kankanin lokaci suka hallaka su baki ɗaya.
Koda samun wannan nasara sai Nabihat ta umarci yan
uwanta fursunonin da su tuka jirgin Ruwan a cigaba da tafiya
Cikin matukar kaɗuwa ɗaya daga cikin fursunonin ta dubi
Nabihat cikin tashin hankali tace
"Yake Nabihat taya ya zamu cigaba da tafiya bayan cewa
yarinya lazimat tana cikin wannan Teku,bamu da tabbacin a
wane hali take ciki.
Koda jin wannan batu daga bakin sharimat sai idanun Nabihat
su ka ciko da kwalla, ta dubi shamirat tace cikin matukar
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
124
damuwa"yake shamirat tabbas a yanzu bani tabbacin cewa
yarinya lazimat tana raye,shin yanzu zamu tsaya ceto yarinya
lazimat ne ? Ko kuwa zamu cigaba da tuka wannan jirgin
ruwan domin ceto daruruwan jama'ar mu,yara ƙanana da mata
da tsofaffi,
Ina so ki kwantar da hankalinki idan har yarinya lazimat na
raye zamu sake saduwa da ita,
Koda jin wannan batu sai shamirat ta gyaɗa kai cikin alamun
damuwa ta matsa kusa da yan uwan ta yan matan suka shiga
tuka jirgin ruwan domin koma izuwa birnin su
A daidai wannan lokaci shugaba sharkar ya taso daga kasan
tekun fuskar sa a murtuke babu annuri,tamakar an watsa
masa garwashin wuta akanta, hannun sa ɗaya a
cire,gundulmin hannun na zubar da jini,
Sa,adda jaruma Nabihat ta cigaba da jagorantar sauran yan
uwan ta fursunoni,a bisa kan wannan jirgin ruwa, dake kan
tekun Baharul-sawara,domin gudun TSIRA DAGA HAKA.
Sai suka shafe tsawon Sa'a biyu suna tafiya babu sassauci.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
125
Lokacin da ya zamana an shafe sa,a uku, sai jaruma Nabihat
ta yi umarni aka shiga ɗaki na musamman akasan jirgin ruwan
aka ɗaukar gurasar sha'ir gami taceccen ruwan inabi,aka
shiga rarrabawa jama,ar su domin kowa ya kimtsa cikin sa.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai
aka hango waɗansu tawagar jiragen ruwa kimanin guda ashiri,
sun bayyana sun bayyana a saman tekun a kowa ce
kusurwa,wato Gabas, yamma,kudu da Arewa,
Cikin matukar kaɗuwa gami da tashin hankali Nabihat tayi
umarni aka tsayar da tafiya,
Kawai gaba sauran yan matan fursunonin suka ruga izuwa
Wani bangare a jirgin suka ɗebo makaman yaƙi, sannan suka
ruga izuwa tsakiyar birnin suna masu gyara tsayuwar su
zuciyoyin su cike da razani,
Yayin da yazamana cewa jiragen ruwan suna matso daf dasu
sai Nabihat ta sake ɗimauce wa,
Su dai jiragen ruwan suna ɗauke ne da waɗansu irin zaratan
dakaru masu kirar samudawan farko, suna sanye cikin sulken
yaƙi na baƙin ƙarfe, suna da waɗansu miguna MAKAMAN
KARE DANGI,
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
126
Tabbas waɗannan dabaru sun kasance ababan tsoro domin
babu halitta da zata arba da su face tayi nadamar wanzuwar
ta a doran kasa,
Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su jaruma Nabihat da
tawagar dakarun,
Tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali, a lokacin ne su
Nabihat suka hango shugaba Yasiran a ɗaya daga cikin
jiragen ruwan,
Shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannunsa ɗaya ɗauke da
wata sharbebiyar takobi,ɗayan hannun da yayi dungulmi kuwa
yana naɗe a cikin wani farin kyalle, fuskarsa a murtuke babu
annuri.
Al'marin da yayi matukar bawa su Nabihat mamaki kenan,
suka tambayi kansu a cikin ransu suna masu cewa, ya akayi
Yasiran ya rayu' shi ina yarinya lazimat take tana raye ne ko
kuwa ta mutu,
Amsar tambayar da suka kasa bawa kansu kenan.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
127
Kawai sai Nabihat su ka hangu dakaru masu yawa sun tsalle
daga inda suke suna ihu da kururuwa mai firgitarwa sun
tunkaro su,suna shawagi a cikin iska jitamkar sun kasance
masu fuka-fukai ,
Koda ganin hakan sai Nabihat ta daga takobin ta sama cikin
karfin hali,gami da ƙarfafawa sauran yan matan gwiwa ta
falfala da masifaffan gudu zuwa kan dakarun.
Yayin da yan matan suka ga haka sai suka yi koyi da ita, su
masu mara mata baya,
Tabbas shi ƙarfi a zuciya