bayan sarki Lazwar ya ɗora magajin gari Yasiran a bisa
sarautar shi ya shiga izuwa duniya.
Haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce,
sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'a je ba, sai ga
shi an shafe tsawon kwanaki arba'in da huɗu ana tafiya
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
53
tsakanin sarki Lazwar, gimbiya Mashlira, yarinya Shuraiba,
sarkin yaƙi ,bawa Shamsal aljani Za'aratun-layal tare da yaro
Imran.
A iya tsawon wannan tafiya shaƙuwa mai karfi ta ƙullu
tsakanin yarinya Shuraiba da yaro Imran, kuma Imran ya
bayyana abubuwan mamaki gami da ƙarfin ikon Ubangiji.
Domin sau talatin da bakwai yana ceto rayuwar su sarki
Lazwar bisa taimakon Ubangijin musulunci.
Bisa wannan dalili ne ya sanya Mashlira da Shuraiba suka
fara kwaɗayin shiga addinin.
A ranar da kwana hamsin suka cika ne aljani Za'aratun-layal
ya sauka a bisa wani daji dake kusa da birnin Istanbul, nan fa
farin ciki ya kama kowa shima aljani Hadimul-khair ya sauke
Imran da yarinya Shuraiba
Bayan kowa ya sauko sai aka shiga tattaunawa akan hanyar
da kowa zai bi wajen shiga birnin Istanbul, inda Shuraiba ta
dubi kowa sannan ta yi gyaran murya ta ce
"akwai shawarwari da zan bamu waɗanda matsawar muka
kiyaye su zamu shiga cikin birnin Istanbul lafiya kuma mu fito
lafiya sumul.
Da farko dole ne kowannen mu ya ƙaurace sanya tufafi masu
tsadar gaske, ko wada ke nuna wata alama ta mulki .
Na biyu gujewa ƙarya da ha'inci, sannan yin biyayya ga
dukkan abin da ya shafi masarauta.
Waɗannan sune shawararin da idan muka kiyaye su
zamu cimma nasara.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
54
Koda Shuraiba ta zo dai-dai nan azancen ta sai ta juya da
dubi Gimbiya Mashlira ta ce "ya ke Mashlira ya zama wajibi
idan zaki shiga cikin wannan birni na Istanbul ke rufe fuskarki
da rawani, har zuwa lokacin da zamu kammala samun abin da
muka shiga nema, domin tsananin kyawun surarki zai jawo
miki matsala.
Koda yarinya Shuraiba ta zo nan a jawabin ta sai tayi
bankwana da damisarta suna masu zubar da hawayen
rabuwa da juna, har sai damisar ta ƙule izuwa cikin daji ta
daina hangen ta.
Ko da jin wannan batu daga bakin Shuraiba sai kowa ya
gyaɗa kai cikin farin ciki, kawai sai sarki Lazwar ya karanto
waɗansu dalasiman tsafi ya nuna aljani Za'aratun-layal da ɗan
yatsan shi na hagu, take Za'aratun-layal ya riƙiɗa izuwa wani
garjejen sadauki mai kwarjini daban tsoro, sannan ya sake
karanto waɗansu dalasiman tsafin take tufafin dake jikin su ya
canja launi zuwa makasƙanta, babu wanda zai ga sarki
Lazwar da gimbiya Mashlira a wannan hali face ya cika da
mamaki bisa ganin yadda suka koma tamkar almajirai saboda
tufafin dake sanye a jikkunansu.
kaico! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka biyan
buƙata ya fi dogon buri. kuma ranar biyan buƙata rai da dukiya
ba a bakin komai suke ba.
Kawai sai aka ɗunguma aka durfafi ƙofar birnin Istanbul
gadan-gadan, shi kuwa yaro Imran sai ya matsa kusa
Shuraiba ya yi mata raɗa a kunne, sannan ya dawo da duban
shi ga hadimin shi ya ce dash ''ya kai Hadimul-khair ina ganin
ya kamata ka kasance a ɓoye, koda ka bayyana har sai
lokacin da na buƙaci hakan" koda jin hakan sai Hadimulkhair ya risina ya ce ''an gama ya shugabana, kawai sai ya
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
55
ambaci sunan Allah gami da yiwa Annabi salati take ya bace
bat, tamkar bai taba wanzu wa ba.
Wannan shi ne abin da ya faru da su sarki Lazwar
lokacin da suka iso izuwa birnin Istanbul.
BABI NA TAKWAS
BIRNIN ZAWATUL-IFDAR
Al'amarin wannan budurwa da magajin gari yasiran ya yi
umarni a kai mashi ita izuwa turakar shi kuwa, ba wata ba ce
face wata sabuwar amarya, kuma an ɗauko ta ne domin ya
keta mata haddi.
Lokacin da wannan badakaren ya isa da ita turakar sai ya
tarar da kuyangi na ƙawata turakar da kayan ƙawa da alatun
jin daɗin rayuwar duniya, wani irin daddaɗan kamshi na tashi
a ko ina.
A harabar turakar da bakin ƙofa kuwa dakaru ne birjik shirye
cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensu ɗauke da miyagun
makamai.
Ya yin da amaryar ta tsinci kanta a ciki turakar sai ta sake
fashewa matsanancin kuka mai tsuma zuciya, tsawon sa'o'i
tana cikin fargaba da tsoron abin da zai faru gare ta, kuma
tana tuna halin da angon ta ya ke ciki.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
56
Haka ta kasance a cikin wannan hali har duhun dare ya
fara nisa, a cikin wannan hali ne ta ji motsin shigowar magajin
gari Yasiran ba, nan fa tsoro ya kara kamata ainu.
Tana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani
sai kawai ta ga wani kyakkyawan tsuntsu yana fitar da wani
sautin kuka mai daɗin saurare, yana shawagi a harabar
turakar.
Cike da matuƙar kwadaituwa da son ganin tsuntsun, ta matsa
izuwa tagar dake turakar ta leƙa ai kuwa sai ta ga anyi wani
rubutu a jikin fuka-fukan tsuntsun da harshen Larabci
kawai sai ta furta a bakinta, faruwar hakan keda wuya, ai sai
ta ji dukkan baƙin ciki gami da tsoron dake zuciyarta ya tafi,
tamkar babu wani mugun abu dake shirin faruwa a gare ta.
Cikin farin ciki mara musaltuwa ta cigaba da karanta kalmomin
a cikin ranta
A dai-dai wannan lokacin ta ji an turo kofar shigowa turakar,
tana buɗe wa sai ga Yasiran ya bayyana, yana sanye da wani
mayafi na alhariri da ya rufe daga cibiyarshi izuwa gwiwarshi.
Sa'adda amaryar ta yi arba da shi saboda matuƙar tsoro
ba ta san sa'adda ta faɗi ƙasa ba, jikinta na ƙyarma tamkar
mazari, shi kuwa magajin gari sai ya nufi inda take yana mai
bushewa da dariyar mugunta har da ƙyaƙyatawa,
Lokacin da ya matso daf da ita sai ya kawai ya miƙa
hannunshi da niyyar ya cakume ta.amma
sai ya ji wani irin tiririn zafi ya tunkaro shi tamkar an yana kusa
tanderun wuta.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
57
Al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan kuma
ya fusata ainun, kawai sai ya buɗe baki da nufin ya karanta
waɗansu dalasiman tsafi.
Kaico! haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, in da ace Yasiran ya
san abin da zai faru da bai yi gangancin karanta dalasiman
tsafin ba, domin kuwa yana cikin hakan ne wata irin
gagarumar wuta ta kama a jikinshi tana ci. Nan fa magajin gari
ya shiga kurma wawan ihu yana mai kai komo a cikin turakar
domin ganin ya kashe wutar, amma duk sa'adda ya zuba ruwa
sai wutar da ƙara ruruwa.
Ita kuwa amarya munirat koda ta ga wuta ta kama a
jikinshi, sai ta ci gaba da karanta waɗannan kalmomi na
larabci da taga ni a jikin fuka-fukan tsuntsun nan a cikin
zuciyarta, kuma ta miƙe tsaye zumbur ta rugawa izuwa ƙofar
fita daga turakar.
Bisa mamaki duk ƙofar da ta tunkara sai ta ga ta buɗe da
kanta, wani abu da ya bata mamaki kuma ya ɗaure mata kai
shi ne, gashi dai ƙiri-ƙiri dakaru suna kallon ta ta tsakiyar su
take ratsawa, amma babu mai ɗaga mata yatsa ballantana ya
ce mata uffan.
Haka dai amarya Munirat ta cigaba da tafiya a cikin gidan
sarautar, zuciyarta cike da matuƙar farin ciki maral musaltuwa
gami da imani da ma'abocin waɗannan kalmomi da ta karanta
suka ce ci rayuwar ta. A dai-dai wannan lokaci ne dakarun
dake gidan sarautar suka dunga tuttɗowa suna zare makaman
su suna rugawa izuwa ɓangaren sarki, bisa jin ihu gami da
kururuwar magajin gari Yasiran da suka yi.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
58
kafin ƙiftawar idanun gidan sarautar ya hargitse da gujegujen jama'a gami da ifice-ifice tamkar an busa ƙahon BUSAR
MUTUWA.
BABI NA TARA
A can birnin muridai kuwa, sarki Zammar mahaifin
gimbiya Mashlira ya ga dukkanin abin da ya wakana tsakanin
yaro Imran da aljani Durusul-fannar.
A cikin halarar tsafin shi a lokacin da yake zaune a fadar
tare da 'yan majalisar shi.
Ko da ganin hakan sai ya cika da matuƙar baƙin ciki
maral-musaltuwa.
Wata rana sarki Zammar na kwance a cikin turakarshi da
ta ƙawatu da kayan alatun more rayuwr duniya, sai ya yi
mafarki da yarshi Mashlira tana cikin ƙoshin lafiya.
Kuma har ta gaya mashi cewa bata guje mashi domin ta
ci amanar shi ba, sai domin ta shiga duniya ta samo masu
maganin lalurar da ta addabe, su tun daga wannan rana Sarki
Zammar ya kasance cikin matuƙar farin ciki, ya yiwa 'yarshi
fatan alheri da samun nasara.
Wannan shi ne abin da yafaru acan birnin muridai.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
59
Babi na tara
Tafiyar daƙiƙa latalin kacal aka yi aka iso ƙofar shigowa
birnin Istanbul, sa'adda aka yi arba da yadda ƙofar birnin
takasance sai kowa ya cika da matuƙar mamaki, katangun
birnin sun kasance masu matuƙar tsawo, a sama da ƙasan
ƙofar birnin miyagun dakaru ne na mutum da aljan ga su nan
birjik shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayen ɗauke da
waɗansu irin masifaffun makamai
Kai koda tsuntsu ne ya zo giftawa ta wannan waje
waɗannan dakaru ba zasu bar shi a raye ba, tsananin kwarjini
mayaƙan ya isa ya ɗimauta duk wata halitta mai numfashi.
Idan har ƙofar birnin Istanbul takasance haka, to ya tsaron
gidan sarautar birnin zai kasance kuwa?
Sarki Lazwar ne ya yi wa kanshi wannan tambaya a cikin
ranshi ba tare da ya furta wani ya ji ba.
Wani narkeken sadauki mai matuƙar muni da kwarjini ya
matso daf da inda su sarki Lazwar su ke ya kare masu kallo
da yan mini-minin idanuwanshi jajaye tamkar garwashin wuta,
cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce
"ya ku waɗannan baƙi shin daga ina kuke, kuma mene ne ke
tafe da ku izuwa birnin nafi daraja a duniya?.
Ko da jin wannan tambaya sai zuciyar sarki Lazwar ta
kama tafarfasa tamkar zata ƙone.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
60
Bakomai ne ya sanya hakan ba, sai bisa jin badakaren ya
ambaci birnin Istanbul da suna mafi daraja a duniya.
Amma koda ya tuna cewa shi fa a halin yanzu sunan shi
bawa ba BASARAKE ba, sai ya danne zuciyarshi, ya dubi
badakaren ya ce "ya kai wannan badakare ka yi sani cewa ba
komai ne ke tafe damu izuwa wannan birnin na ku ba face sai
domin mu gudanar da kasuwanci, kuma a halin yanzu mun fito
ne daga nahiyar ƙasashe larabawan gabas.
Ko da jin amsar wannan tambaya sai badakaren ya
bushe da dariya sannan daga bisani ya murtuke fuska ya ce
"Za mu ba ku izinin shiga wannan birnin saboda muhimmancin
abin da ke tafe da ku. Sai dai wani hanzari ba gudu ba idan
muka samu ɗayan ku ya karya dokokin wannan birnin namu,
to zamu ƙwace dukiyarku gami da tusa ƙeyarku izuwa gidan
kaso.
Ko da jin wannan batu sai hantar cikin kowa ta kaɗa da karfi
tsoro ya kama shi.
Kawai sai badakaren ya yiwa waɗansu dakaru inkiya ta
wutsiyar idanu take dakarun suka shiga wangame kofar birnin,
ƙofar na kammala buɗewa su sarki suka kunna kai izuwa cikin
birnin zukatansu cike da matuƙar farin ciki.
Lokacin da su Sarki lazwar suka tsinci kansu a cikin birnin
Istanbul sai suka kama kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan
ƙauye ya shigo birni, kuma suka cika da matuƙar mamaki
gami da al'ajabi, bisa ganin yadda birnin ya kasance mai
matuƙar kyawun gine-gine tamkar aljannar duniya.
Kai tsaye yarinya Shuraiba ta durfafi hanyar kasuwar
birnin, amma sai sarki Lazwar ya yi caraf! ya dubi yarinya
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
61
Shuraiba ya ce "ya ke Shuraiba shin mene ne dalilin da ya
sanya za ki kai mu kasuwa? Bayan cewa ba kasuwanci ne ya
kawo mu wannan birni ba?
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai Shuraiba ta bushe da
dariya ta ce "ai bakomai ne yasanya na kawo mu kasuwa ba
sai domin kar ka manta cewa ka faɗawa dakaru masu tsaron
kofar birnin Istanbul cewa kasuwanci ne ya kawo mu, tabbas
dola ne a kowa ne lokaci dakarun sarki su kawo ziyarar
bazato, domin binciken gaskiyar maganar abin da ka faɗa
masu,
Abu na biyu kuwa shi ne a lokacin da muka shigo wannan
birni 'yan fashi da makami gami da 'yan damfara sun shaida
shigowar mu, a koda yaushe za su iya kawo mana farmaki
domin a tsammanin su za su samu dukiya mai tarin yawa a
wajen mu.
Waɗannan dalilai ne suka sanya na kawo mu kasuwa domin
babu wani waje mai ɗauke da cikekken tsaro fiye da kasuwa".
Ko da jin amsar waɗannan tambayoyi daga bakin
Shuraiba sai kowa ya gyaɗa kai alamar gamsuwa gami da
samun nutsuwa.
Lokacin da aka shiga kasuwar sai aka tarad da takasance
maƙiyaya mai faɗin gaske, tana ɗauke da gine gine cikin tsari,
rumfunan masu siyan da tufafi dabam, kayan masarufi, komai
dai an yi bisa tsari mai ƙayatarwa.
Kai tsaye aka durfafi rumfar wani dattijo, da ta ƙawatu da
kayan alatu na hatimin sarauta, da alama shine shugaba
kasuwar.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
62
Tun daga nesa Shuraiba taga ya ƙura mata idanu ko kiftawa
ba ya yi.
koda shugaban kasuwar ya yi arba da su sai ya miƙe tsaye
zumbu! Ya tarbe su cikin matuƙar farin ciki yana yi masu lale
marhaban da zuwa, tamkar ya sadu waɗansu yan uwanshi na
jini da ya jima bai sadu da su ba.
Bayan shugaban kasuwar mai suna Sha'aran ya sauke
su a bakin ƙofar rumfar, sai ya yi umarni aka kawo musu
abincin kalaci aka jera a bisa wani dogon teburi, nan fa su
sarki Lazwar suka shiga kimtsa cikinsu, har suna hannu baka
hannu ƙwarya, domin rabon su da cin irin abincin yau wata
huɗu kenan cif.
Kuma suna mamakin irin karamci da shugaban kasuwar ya
nuna masu.
Shi kuwa yaro Imran da aka fara cin abincin sai ya yi
bisimillah, loma bakwai ya yi sannan ya zare hannunshi ya
kurɓi ruwa maƙwarwa huɗu sannan ya koma koma gefe gudal.
Al'amarin daya bawa sarkin kasuwa Sha'aran mamaki
kenan, ya ƙurawa yaro Imran idanu yana so ya tuna irin
mutanen da ya taɓa gani suna irin wannan dabi'a wajen cin
abincin su, Shi kuwa aljani ZA'ARATUN-LAYAL, da a halin
yanzu sarki Lazwar ya canja mashi siffarshu dagaaljan ya
koma bil'adama, cin abincin ya yi yana santi kamar tsohon
mahaukaci.
Bayan kowa ya kimtsa cikinshi ya dawo hayyacinshi, sai
sarki Lazwar ya zira hannunshi a aljihun rigarshi domin ya
ɗauko dinare domin ya biya kuɗin bincin da suka ci, da kuma
kuɗin hayar gidan da za'a ba su.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
63
Amma sai kawai ya ga shugaban ya dube sa fuskar sa cike da
annuri ya ce "ya ku waɗannan baƙi masu daraja ku yi sani
cewa, ganin ku da nayi ya sanya jikina ya ba ni cewa ku
mutanen ƙwarai ne. Yanzu ina buƙatar ku gabatar min da
sunayen ku.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama kowa, sarki
Lazwar ya shiga gabatar da sunayen su ɗaya-bayan-ɗaya,
Amma koda yazo kan yarinya Shuraiba sai sarkin kasuwar ya
dakatar dashi ya ce "ba sai ka gabatar mini da ita ba.
Al'amarin da ya bawa kowa mamaki kenan, har Shuraiba ta ce
a cikin ranta shin me shugaban kasuwar ya sani game da ni.
Kuma me ya sanya yake ƙura min idanu tun da muka shigo
kasuwar?
Ina dalilin rashin karɓar haƙƙin aikin shi daga gare mu.
Amsar tambayoyin da yarinya Shuraiba ta kasa bawa
kanta kenan.
Shugaba sha'aran na gama faɗin hakan sai ya ƙwallawa wata
budurwa kira.
Budurwar ta bayyana a gare shi sanye da tufafi masu yalwa,
tun daga ƙasa har sama, kuma fuskarta rufe da rawani mai
ɗauke da wani hatimin sarauta idanuwanta kaɗai ake gani,
ta zube ƙasa ta kwashi gaisuwa cikin girmamawa, sannan ta
buɗi baki cikin wata irin lallausar murya mai daɗi tamkar
sarewa ta ce ''ga ni ya shugabana me ake da buƙata?
Shugaba Sha'aran ya dube ta ya ce "ya ke khadijat ki yi sani
cewa bakomai nake buƙata a gare ki ba, sai domin ki yiwa
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
64
waɗannan baƙi jagora izuwa unguwar Madinatul-dinar,
masaukin manyan baƙi, ina so ki ba su dukkan abin da suke
bukata na kulawa".
Koda jin wannan umarni sai B
Budurwa khadijat ta mayar da duban ta ga su sarki Lazwar
tana ƙare masu kallo ɗaya-bayan-ɗaya.
Ya yin da ta haɗa idanu da yaro Imran sai taji zuciyar ta
buga ƙarfi kuma tsikar jikin ta ta tashi, kamar yadda ya faru
gare ta shi ma haka yaro Imran ya ji wannan yanayi a tare da
shi, amma saboda kada wani ya fahimci abin da ke faruwa sai
khadijat ta kawar da idanuwanta a kan shi, a ɓangaren bawa
Shamsal kuwa, tun sa'adda da ya kalli idanuwan budurwa
khadijat sai ya ji hantar cikinshi ta kaɗa da ƙarfi, sannan wani
abu ya ɗar su a zuciyarshi da ya kasa gane ko mene ne.
Ita kuwa gimbiya Mashlira cikin idanun khadijat kawai ta kalla
taji kishi ya kama ta, domin koda cewar fuskar khadijat a rufe
take da rawani idanuwanta kaɗai ake gani, ta tabbatar cewa ta
shafe ta a kyawun sura ne sa ba kusa ba.
Tabbas idan masoyin ta sarki Lazwar ya yi arba da ita zahiri
zai iya karkata zuciyarshi izuwa gare ta.
Khadijat ta miƙe tsaye ta shige gaba, tana mai yafito su
sarki da hannunta, tana mai yi masu nuni da su biyo bayan ta.
Ba tare da gardamar komai ba, suka mara mata baya har
suka ƙule a cikin kasuwar, duk inda suka gifta sai jama'a su bi
su da kallo, haka suka wanzu suna ratsa saƙo da lungu na
unguwanni, har suka iso wani ƙasaitaccen gida.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
65
Kai tsaye khadijat ta durfafi kofar gidan ta na isa dakarun
dake gadi suka wangame makekiyar kofar shiga gidan suna
masu risinawa a gare ta cikin girmamawa.
Khadijah ta kunna kai izuwa cikin gidan, su sarki lazwar na
biye da ita cike da matuƙar mamakin yadda masaukin ya
kasance.
Kowanne su ɗaki aka ba shi daban mai ɗauke da gado, kushin
da kewayen wanka da sauran kayan more rayuwa.
Kuma khadijat ta shaida masu cewa duk mai buƙatar wani abu
ya sanar da ita har izuwa lokacin da zasu tafi.
kasancewar a wannan lokaci duhun dare ya fara kawo kai, sai
khadijat ta yi umarni aka kunna dukkanin fitulun dake gidan.
A lokacin da dare ya tsala sai sarki Lazwar ya shiga izuwa
masaukin kowanne ya bayyana masa cewa, dole ne su
kasance cikin shiri, domin a kowannnen lokaci za a iya kawo
masu harin bazato, kuma ba su da tabbacin cewa sarki
kasuwa Sha'aran ba shi da wata mummunar manufa akan su,
kuma a gobe da duku-dukun safiya za su shiga cikin garin
domin gudanar da abin da ke tafe da su.
A can masaukin yaro Imran kuwa bayan gabatar da
kalacen dare, sai ya shiga izuwa kewayen ya ɗaura alwala ya
dawo izuwa turakarshi ya shiga gabatar da Sallah isha'i yana
cikin hakanne ya ji an turo kofar shigowa, sai da ya idar ya yi
addu'a sannan ya juya domin ya ga kowane ne ya shigo ɗin.
Koda ya yi arba da wanda ya shigo ɗin sai ya yi turus!,
Ba wani ya gani ba face khadijat hadima ga Sarkin kasuwa
Sha'aran, tana durƙushe a gefan shi na hagu ta yi zama irin na
sallah.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
66
Cikin matuƙar mamaki Imran ya du be ta cikin girmamawa ya
ce "ya ke hidima Khadijat shin ina dalilin shigowarki wannan
masauki nawa a dai-dai wannan lokaci bakya tsoron sauran
abokan tafiya za su zargi wani abu?
Sannan jikina ya bani cewa kina kwaikwayon yadda nake
gudanar da ibadar Ubangiji na.
Shin baka tunanin hakan zai jefa rayuwarki da tawa a cikin
haɗari ba?
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai khadijat ta yi
murmushi mai taushi, sannan ta dubi Imran cikin murya mai
daɗin saurare ta ce
"ya kai wannan yaro ka yi sani cewa tun sa'adda nayi arba da
kai a lokacin da ku ka sauka a rumfar mai gidana, naji ka
burgeni sosai a zuciyata tamkar ina tare ɗan uwa na jini, kuma
lokacin da ku ke cin abincin na lura cewa duk dabi'un cin
abincin naka ya bambanta da nasu, wato naka irin na
ma'abota addinin Musulunci ne, tun daga lokacin na ji cewa na
samu ɗan uwa.
Bisa wannan dalili ne ya sanya na biyo ka izuwa
masaukin ka domin na bika sallah. Fiye da shekaru goma sha
biyu kenan tun sa'adda an fito neman ɗan uwa na, wanda shi
ne kaɗai ya rage mini da a duniya rabon da a ce na samu
jam'in sallah sai a yau,
Tabbas ina cikin matuƙar farin cikin da ba zai musaltu ba.
Haƙiƙa da zaka zauna a tare da ni da ka ɗebe mani kewar
mahaifina da na rasa.
Tsawon shekarun da na shafe ina aiki tare da Sarkin kasuwa
Sha'aran ban taɓa bayyana addini na a gare shi, saboda
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
67
gudun matsala, domin duk wanda aka samu yana gudanar da
wani addini saɓanin na birnin Istanbul hukuncin kisa ne a
ƙanshin shi.
Bisa wannan dalili ne ya sanya kai ma nake baka shawara da
ka guji bayyana hakan, har ku kammala abin da ke tafe daku
zuwa wannan birni";
Koda jin amsar waɗannan tambayoyi sai yaro Imran ya
cika da matuƙar farin ciki yaji ya yi matuƙar shaƙuwa da
hadima khadijat, kuma mamaki ya kama shi bisa jin cewa ta
fito neman ɗan uwanta ne.
Shin khadijat ita ce 'yar uwar shi da ya fito nema ?
Amma ta ya zai iya gasgata hakan bayan cewa koda yaushe
fuskarta a rufe take da rawani.
Amsar tambayoyin da Imran ya kasa bawa kanshi
kenan.
Khadijat ta katse shirun da wanzu a tsakaninsu ta
hanyar buɗar baki ta ce "ya kai ɗan uwa na idan ba za ka
damu ba, ina neman alfarma a gare ka da ka amince min
kullum na dunga zuwa wajen ka muna yin fira gami da ɗebe
kewa
Koda jin wannan batu sai Imran ya ce "na yi maki
wannan alfarma ya ke yar uwanta".
Wannan shi ne abin da ya faru a masaukin yaro Imran
ma'abocin addinin Musulunci.
A can masaukin sarki Lazwar kuwa, fira ce ta kare
tsakanin Lazwar da gimbiya Mashlira, a inda Mashlira ta ci
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
68
gaba da ba shi labarin abin da ya faru tsakanin matsafi
Sahibul-ukub da mutanen birnin akan dalilin da ya sanya
halittar su ta koma ta maridai inda ta ci gaba da cewa.
Lokacin da rundunar matsafi Sahibul-ukub suka afkawa
birnin Madinatul-Adfal sai aka ruguntsume da azababban yaƙi
mai matukar muni ban tsoro da ban al'ajabi.
Nan fa su ma mayaƙan birnin suka dinga tuttuɗowa daga
kowacce kusurwa ana yin KARON BATTA.
Nan fa sassan jikkunan bil'adama ya dinga shawagi a sama
suna zubo ƙas, hankakan mutuwa ya yi dirar mikiya a wajen
ya wanzu yana kai komo wajen ɗaukar rayuka.
JINI DA ƘASA suka haɗu waje guda, ihun da kururuwar
mazaje gami da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne.
A wannan lokaci mahaifina sarki Zammar ya shiga izuwa cikin
gidan sarautar yana shirin yaƙi, jim kaɗan sai ga shi ya fito
izuwa filin daga kawai sai ya afka cikin abokan gaba ya hau su
da sara da suka.
Yazamana cewa duk inda ya sanya a gaba sai dai ka ga
dakarun matsafi Sahibul-ukub na zubewa ƙasa matattu tamkar
yana sassabe a gonar auduga.
Sa'adda matsafi sahibul-ukub ya ga irin muguwar ɓarnar
da mahaifina ke yi mashi, sai ya ruga izuwa inda ya ke ya tare
shi suka kacame da azababban yaƙi mai matukar muni daban
tsoro.
Ana fara wannan arbu ne mahaifina ya fara gane cewa tabbas
shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin kuwa duk
sa'adda matsafi Sahibul-ukub ya kai mashi hari da takobinshi
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
69
idan ya kare harin, sai kaga ƙarfin saran ya cilla mahaifina
sama ya yi ƙundumbala ya kife a ƙasa, amma saboda juriya
da mafi irin ta GWARAZAN JIYA sai ya miƙe tsaye zumbur, ya
ci-gaba da mayar da martani
A wasu lokutan kuwa idan ya kai mashi harin ya kauce, sai ka
ga duk abin da takobin
Sahibul-ukub ta sauka a kanshi ya kama da wuta, kafin cikar
rabin sa'a Sahibul-ukub ya galabaitar da mahaifina ya faɗi
ƙasa magashiyan ya na amai na jini ta baki da hanci.
Wannan shi ne abin da ya faru a masaukin gimmbiya
Mashlira 'yar sarkin maridai da Sarki lazwar.
Kamar yadda ya wakana a masaukin gimbiya Mashlira da
sarki Lazwar haka al'amarin yakasance a masaukin yarinya
Shuraiba da aljani ZA'ARATUN-LAYAL
A inda Za'aratun-layal ya ci gaba da bawa yarinya Shuraiba
hikayar sarauniya Abidat ta birnin Sin.
BABI NA GOMA
Lokacin da wannan zakanya ta ruga izuwa inda suhaimat
da jaririyar ta ke kwance, koda taga halin da take ciki sai ta
ruga izuwa bakin wata ƙorama ta guntso ruwa a baki ta dawo
izuwa inda take ta fesa mata ruwan a fuska.
Faruwar hakan keda wuya sai suhaimat ta ja dogon
numfashi gami da sauke nannauyar ajiyar zuciya, idanuwanta
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
70
suka buɗe tarwai ta wartsake daga suman da tayi kawai sai ta
miƙe zaune.
Ya yin da tayi arba da zakanyar sai ta razana ainun ta ja da
baya tana mai ɗaukar jaririyar ta ta ƙanƙame ta a ƙirji.
Koda ganin halin da suhaimat ta shiga sai zakanyar ta
juya ta ruga izuwa cikin wannan kogon dutse dake dajin.
Cikin matukar farin ciki suhaimat ta mike tsaye taje bakin
wannan ƙorama ta yi wa jaririyarta wanka, ita ma ta tsafta ce
kazantar da ke jikin ta, sannan ta dawo izuwa ƙarƙashin wata
bishiya ta zauna ta shiga sharar da jaririyar tana mai shafa
gashin kanta, zuciyar ta cike da matuƙar farin ciki maral
misaltawa.
Kuma ta shiga tambayar kanta a cikin ranta tana cewa,
dhin wane ne ya kashe waɗannan dabaru? Ko kuwa wannan
zakanya ce?
Amsar tambayar da ta kasa bawa kanta kenen,tana
cikin wannan hali ne zakanyar ta dawo gare ta bakin ta rike da
waɗansu tarin ganyayyaki ta a jiye a gaban ta,
Bisa mamaki a wannan karon sai Suhaimat taji ko kaɗan ba ta
tsora ta da ganin zakanyar ba, bata re da fargabar komai ba ta
ta duba abin da ta kawo ɗin. Ai kuwa sai taga a she nau'ikan
kayan marmari ne dangin su ayaba da inibi, kawai sai ta shiga
kimtsa cikinta har sai da ta ci ta ƙoshi, sannan ta fasa kwakwa
ta shanye ruwan cikinta.
Zakanyar na tsaye na tsaye a gefe guda tamkar mai jiran
umarni, a sannanne Suhaimat ta lura cewa jikin zakanyar
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
71
akwai jini, take ta fahimci cewa ita ce