wani ice mai kaifi ta yanke cibiyar
jaririyar.
Tana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai ta hango
waɗansu dakaru sun durfafo inda take a bisa dawakai.
Kafin tayi wani yunƙuri ɗaya daga cikin dakarun ya ɗame
kibiyarshi ya harbe ta a gadon bayanta, saboda tsananin zafi
da raɗaɗin da ta ji bata san sa'adda ta kurma wawan ihu ba ta
sulale ƙasa sumammiya jaririyar ta shiga tsala kuka.
Har badakaren ya sake yin shiri a karo na biyu da nufin ya
sake harbin ta.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
19
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga wata
murgujejiyar zakanya ta yi fitar burgu daga cikin wannan
kogon dutse dake dajin, ta dako wawan tsalle ta daki
badakaren a kirji.
Saboda matuƙar ƙarfin bangazar sai da badakaren da dokin
shi su ka yi sama tamkar an janye su da ƙungiya, sannan
daga bisani suka faɗo ƙasa matattu ko shurawa ba su yi ba.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin zakanyar da
mayaƙan.
daga can sai zakanyar ta yi gurnani gami da hargagi sannan
ta dako wawan tsalle izuwa kan mayaƙan.
Ko da ganin hakan sai dakarun su ka ɗaga makamansu suka
yi ihu da kururuwa mai firgitarwa suka yi ɗauki kanta aka
ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni, ban tsoro
da ban al'ajabi.
Wohoho! Haƙiƙa yaƙi shi ne matattarar dukkan bala'i da
musiba, kuma idan gwani ya haɗu da gwani JURIYA DA
BAJINTA suka game waje guda, dole ne artabu ya zamo abin
tsoro.
Nanfa zakanyar ta wanzu tana hallaka dakarun, ya
zamana cewa duk inda ta sanya gaba sai dai ka ga dakaru na
zubewa ƙasa matattu, a inda za ka ga ta mako badakare faga
kan dokinshi ta bishi ta turmushe.
A duk sa'adda dakarun su ka kaiwa zakanyar hari sai ka ga ta
wurƙila haɗe da zame wa ta kaucewa saran, kafin badakare
ya sake daga takobinshi zakanyar ta dako tsalle sama ta
sanya faratanta ta tsire mashi idanu ruwan cikin ya tsiyaye,
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
20
take zai sulale ƙasa daga kan dokinshi yana mai kurma
wawan ihu.
Kai wasu lokutan idan ta daki badakare a wuya sai ka
ji wuyanshi ya ƙara ya karye ya yi ƙara ji kake ruƙus!! Ƙas! Ya
faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba.
Haƙiƙa waɗannan dakaru suna ganin tashin hankalin da ba su
taɓa ganin irin shi ba. Domin kafin cikar rabin sa'a zakanyar ta
kashe fiye da rabin su.
Nanfa ƙarar karafniyar ƙarafa da ihun mazaje, haniniyar
dawakai haɗe da gurnanin zakanyar ya cika dajin baki ɗaya,
ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke
yin turmutsutsu, kofatunsu na kartar ƙasa.
Wohoho! tabbas masu iya magana sun yi gaskiya da
suka ce wuya ko da magani babu daɗi, kuma wuya mai sa
dole.
Hakan ce ta faru ga sauran dakarun, domin koda su ka ga
cewa a kowanne lokaci za su iya baƙuntar barzahu sai suka
cika wandunansu da iska domin GUDUN TSIRA da rayuka,
sai zakanyar ta dunga ƙure masu gudu tana make su suna
faɗuwa ƙasa matattu. Kafin wani lokaci ta zubar da
gawarwakin su a ƙasa.
Kawai sai ta juya ta durfafi inda wannan mata da jaririyar ke
kwance a ƙasa tana fitar da wani irin gurnani.
BABI NA HUƊU
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
21
Lokacin da aljani da aljani Za'aratun-layal ya zo dai-dai nan a
hikiyar sarauniya Abidat ta birnin Sin sai ya ja bakinshi ya yi
shiru.
Cikin alamun matuƙar damuwa Shuraiba ta dube shi ta ce
"haba ya masanin HIKAYAR DUNIYA mene ne ya sanya za
ka yanke ba ni wannan labari mai matuƙar daɗi gami tsantsar
tausayi, haƙiƙa na matsu naji a wane hali wannan mata da
jaririyarta su ke ciki?
Kuma wace ce wannan zakanya da ta ceci rayuwar su? Shin
mahaifiyar jaririyar ta na raye ko kuwa ta mutu sakamakon
harbin kibiya da wannan badakare ya yi mata a gadon baya".
Ko da jin wannan batu sai Za'aratun-layal ya cewa da
Shuraiba ''shin baki lura da inda muka iso ba ne? Leka izuwa
kasa ki gani".
Da jin hakan sai ta sunkuya da kanta ƙasa aikuwa sai ta hangi
wani irin baƙin daji mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.
Sarki Lazwar ya dubi aljani Za'aratun-layal ya ce ''shin me ka
fahimta da wannan daji dake gaban mu?
Za'aratun-layal ya yi shiru kamar mai tunanin wani abu sannan
ya ce " ya shugabana wannan daji dake gaban mu yana
ɗauke da tsananin sanyi don haka dole ne kowannen ku ya
sanya suturun kariya, sannan kuma dukkanin daji da ya
kasance yana tattare da irin yanayin to dole ne a samu
miyagun halittu masu shan jinin bil'adama da cin naman su,
sai inda kizo ke saƙar shi ne bani da tabbacin waɗanne irin
halittu ne.
Ko da jin wannan batu daga bakin Za'aratun-layal sai
kowa yasha jinin jikinshi.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
22
Cikin hanzari sarki Lazwar ya zira hannunshi a aljihun rigarshi
ya ɗauko madubin tsafin shi da nufin gudanar da bincike,
amma sai aljani Za'aratun-layal ya yi wuf da dakatar da shi ya
ce ''ya shugabana ka yi sani cewa amfani da sihirin tsafi a irin
wannan tafiya abu ne mai matuƙar haɗarin gaske domin baka
da tabbacin cewa wanda za ka yi binciken bai fi ka karfin sihiri
ba. Sannan shin ka manta cewa kowa a gidanshi sarki ne,
mafita ɗaya ce a gare mu kowanne ku yakasance cikin shiri
tun da gashi yanzu la'asar ta riske mu, ba zamu ɗauki wani
tsawon lokaci ba duhun magariba zai gaba ce a dajin kenan
dole yaɗa zango cikin dajin dole ne domin mu kwana mu huce
gajiyar dake tare da mu.
Da jin wannan batu sai kowa ya shiga sanyawa kanshi rigunan
sanyi tun daga ƙasa har sama kuma kowa ya gyara riƙon
makamin shi.
Za'aratun-layal ya yi ƙasa-ƙasa ta fuka-fukanshi sannu a
hankali har aka sauka a bisa turba .
Sa'adda kowa ya yi arba da dajin sai tsoro ya kara kama shi.
Shi dai wannan daji yakasance gaba ɗayan shi yana
ɗauke da waɗansu irin dogayen bishiyu masu rassa masu
matuƙar kaifin tsiya masu tattare da sarƙaƙiya, babu wani waje
da mutum zai ajiye kafarshi face ya taka dusar ƙanƙara ce,
Babu abin da zai ƙara firgita mutum kuma ya jefa tsoro a
zuciyarshi sai jin shiru da ya wanzu a dajin tamkar babu wani
abu mai rai a cikin shi, kai hatta irin tsuntsaye haka a saman
bishiyoyin babu su.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
23
Nan fa aka fara tafiya a cikin ɗar ɗar domin shirin ko ta kwana,
amma bisa mamaki sai ga shi an shafe tsawon rabin sa'a ba
tare da an jiyo motsin wani abu mai cutarwa ba.
Al'amarin da ya sanya kowa ya fara sakin jikinshi kenan,
ana cikin wannan tafiya ne tsinin reshen wata bishiya ya yanki
bawa zafiyar a cinyarshi jini ya zuba a ƙasa.
Kawai sai a ka ji gaba ɗaya dajin ya kaure da wani irin gurnani
mai ban tsoro ba shiri kowa ya tushe kunnuwanshi domin
ƙarar na iya kurumtar da mutum.
Abin da su sarki Lazwar ba su sani ba shi ne zubar jini a dajin
shine alamun da halittun ke gane cewa bil'adama ya shigo
dajin.
Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu irin
zaratan muradai na fitowa daga kowacce kusurwa a dajin.
Muridan sun kasance masu matuƙar tsawo tamkar bishiyar
kuka. Jikkunansu a mummurɗe suke tamkar duwatsu suna da
rafkeken kai mai ɗauke da idanu ƙwaya ɗaya jal! Wanda ya
kasance jajur tamkar garwashin wuta, fuskokin su munana ne
babu kyawun gani, duk sa'adda su ka wangame bakunansu
sai ka ga cewa wani irin yawun mai yauƙi na dalala, a
hannayen su kuwa suna ɗauke da waɗansu irin masifaffun
makamai na yaƙi da idanu basu taɓa gani ba, a ƙalla adadin
muridan ya kai dubu uku da ɗoriya.
Lokacin da muridan suka kammala yiwa su sarki Lazwar
ƙawanya, sai aka fara kallon-kallo tsakanin ɓangarorin
biyu,tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali sai daga
bisani ne muridan su ka yi wata kururuwa mai firgita dandazon
mayaƙa a filin daga, su ka yi ɗauki izuwa kan su,
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
24
Koda ganin hakan sai su sarki Lazwar su ka yi kururuwa suka
ruga izuwa kan muridan.
Ana haɗuwa aka yi muguwar KARON BATTA.
Wohoho! Haƙiƙa tashin hankali ba'a sa mai rana, kuma
ita wutar bala'i kafin ta zo ne ake guje mata, amma idan tazo
kawai miƙa wuya ake yi a tare ta ko dai a mutu ko a yi rai.
Kaico! ana fara wannan arbu ne su sarki Lazwar suka fara
gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin
muridan sun zame masu tamkar GOBARAR ANNOBA.
Duk sa'adda ɗaya daga cikin ya kai wa su sarki Lazwar hari
da makaminshi, idan su ka goce saran ya sauka akan bishiya
sai ka ga ta rabe gida biyu ta faɗi ƙasa rikica za ta danne su.
Kafin ka ce me tuni muridan sun hallaka fiye da dakaru gami
da kuyangi fiye da guda dubu.
Al'amarin da ya yi matuƙar figita su sarki Lazwar kenen,
babban abin da ya fi dugunzuma hankalin su shi ne yadda
muridan suka kasance masu matukar zafin nama, tamkar
jikkunan su na amfani da wata na'ura dake sarrafa su.
Shi kan shi aljani Za'aratun-layal duk irin matuƙar
karfin damtsen shi sai da ya zamana muridan sun zamto
mashi ciwon idanu.
A ɓangaren yarinya shuraiba kuwa ana cikin wannan yaƙi ne
wani daga cikin muridan ya kawo mata wani wawan sara da
gatarinshi da nufin tsinke mata wuya,
Cikin wani irin baƙin zafin nama ta zille wa saran gatarin
muridan ya shige cikin ƙarƙashin ƙasa.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
25
Kafin muridin ya zare gatarin na shi Shuraiba ta ɗame bakanta
ta harbe shi da kibiya a idon shi guda, take ya fashe jini ya
dunga kwarara tamkar an buɗe kan fanfo, nan fa muridin ya
faɗi kasa yana mai kwarara ihu yana birgima zuwa wani lokaci
ya sheƙa barzahu komai na jikin shi ya dai na motsi.
Ko da yarinya Shuraiba ta ga wannan nasara da ta
samu sai ta cika da matuƙar farin ciki, kuma a sannanne ta
fahimci cewa ruhikan muridan suna cikin wannan idanu na su
guda ɗaya dake tsakiyar goshin su.
Kawai sai ta ci gaba da ta harbin muridan a idanun su cikin
matuƙar ƙware wa da zafin nama.
Wohoho! Gaskiyar masu iya magana da suka ce kyan ɗa ya
gaji ubanshi, kuma ita sadaukantaka gadon a ke yi ba wai a
kasuwa ake siyarwa ba.
Haƙiƙa babu wadda zai yi arba da yarinya Shuraiba a cikin
wannan hali face ya jinjina mata.
A ɓangaren sarki Lazwar, sarkin yaƙi da su bawa
Kuwait kuwa, sa'adda suka ga yadda yarinya Shuraiba ta
gano lagon muridan har ta na samun nasarar hallaka su sai
suka yi koyi da ita.
Ya zamana cewa suna daka tsalle sama suna hawa kan
muridan suna amfani da takubban su suna soke masu idanu.
Aljani Za'aratun-layal kuwa hannunshi ya dunƙule ya shiga
naushin muridan a idanuwansu. Duk wanda ya gabza wa
naushin sai dai ka ga ya faɗi kasa matacce.
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da
suka ce idan kiɗa ya canja dole ne rawa ta canza. Nan fa
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
26
muridan suka fara gane kuren su suna yin muguwar hallaka a
banza, komai hassadar mutum idan ya ga yadda sarki Lazwar
ke ragargazar muridan dole ne ya jinjina mashi ya tabbatar da
cewa tabbas Lazwar ya cika GWARZON DUNIYA kuma
SARKIN SADAUKAI.
Saboda yadda yake kashe muridan tamkar yana sassabe a
gonar auduga.
Lokacin da aka shafe sa'a ana wannan arbu sai ya zamana
cewa duhun dare ya fara kawo kai, nan take tsananin sanyin
dake dajin ya daɗa ƙaruwa.
Nan fa su sarki lazwar suka shiga cikin wani tashin hankali,
kuma tsawon lokacin da aka shafe ana wannan gumurzu bai
huce muridan guda ɗari kacal ba aka hallaka ba.
Koda ganin halin da ake ciki sai sarki Lazwar ya karanto
waɗansu dalasiman tsafi domin samun mafita.
Kaico! Hakikya rashin sani yafi dare duhu, inda a ce sarki
Lazwar ya san abin da zai biyo baya da bai yi gangancin
karanta dalasiman tsafi ba, domin kuwa faruwar keda wuya
sai wata irin iska ta musamman ta mamaye dajin baki ɗaya
wacce ta sanya sanyin ya kara tsanan ta. kawai sai ya ga
jama'ar ya yanke jiki suna faɗuwa ƙasa sumammu.
Ko da ya waiga bayan shi domin ya ga a wane hali
yarinya Shuraiba ke ciki.
Kawai sai ya ga wayam babu ita babu alamar ta, kafin ya
mayar da duban shi zuwa ga su sarkin yaƙi sai kawai ji ya yi
an gabza mashi wani wawan naushi a fuska take hankalin shi
ya gushe ya dai na gane kanshi.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
27
Su sarki Lazwar ba su tsinci kansu a ko ina ba sai a cikin wani
ɗakin duhu, wanda saboda matuƙar duhun shi mutum ko tafin
hannayenshi ba ya iya gani, a bisa cikin wani irin ƙaton keji da
aka yi shi da zallar waɗansu irin itace masu ƙwarin gaske.
Jim kaɗan da farkawar su sai kawai su ka ga ɗakin ya gauraye
da wani irin haske mai ban mamaki.
Sai a sannanne sarki Lazwar ya gane cewa kowannen su an
sanya shi a keji na daban ba tare da an gama shi da ɗan
uwanshi ba, hatta aljani Za'aratun-layal na shi kejin daban,
amma duk an daɗɗaure shi da waɗansu irin sarƙoƙi na baƙin
ƙarfe.
Sa'adda kowannen su ya sake buɗe idanuwan shi
tarwai ya ga babu yarinya Shuraiba da gaba ɗaya sauran
tawaga, sai hankulan su suka dugunzuma ainun, kuma aka
shiga firgici, aka fara tunanin shin ko yarinya Shuraiba da
tawaga sun rasa rayukansu ne.
Shi kanshi aljani Za'aratun-layal da bai kasance bil'adama ba
sai ya ji a ran shi yana matuƙar kewar Shuraiba tamkar da ma
sun daɗe da shaƙuwa da juna.
Tsawon lokacin ana cikin wannan hali sai daga bisani
ne sai su kaji karar buɗe sakatun kofar ɗakin.
Jim kaɗan sai Kofar ta buɗe sai ga waɗansu irin zaratan
dakarun muridan su bakwai sun shigo cikin ɗakin.
Kallo ɗaya su sarki Lazwar su ka yiwa dakarun suka sunƙuiyar
da kawunan su ƙasa, saboda matukar kwarjinin da munin
siffar su.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
28
Dakarun su ka durfafi inda su sarki lazwar suke, su na isa
gare su suka ɗauki kejin da suke ciki su ka ɗora a bisa
kafaɗunsu, wanda aljani Za'aratun-layal ke ciki kuwa dakaru
biyu suka ɗauka, kawai sai su ka fice daga cikin ɗakin, suka
durfafi wata hanya ta musamman su ka shiga izuwa cikin gari.
Nan fa su sarki lazwar suka cika da matuƙar mamaki da
al'ajabi suka kama kalle-kalle da dube dube-dube, tamkar ɗan
ƙauye ya shiga birni, shi dai gaba ɗaya birnin muridan an gina
gidajen shi da waɗansu irin manyan duwatsun wuta masu
kwarin gaske, masu matukar tsawo da faɗi.
Ko da jama'ar birnin su ka yi arba da su Lazwar sai suka cika
da matuƙar murna, su ka suka shiga tanɗe bakunansu gami
dalalar da yawu, saboda matuƙar kwadayin yau za su kalaci
da naman bil'adama.
Tafiyar daƙiƙa talatin kacal! aka yi aka iso fadar birnin.
Fadar ta kasance tanƙamemiya mai matuƙar tsawo da faɗi,
kuma gininta anyi shi ne da irin waɗannan duwatsu masu
ƙyalli, sannan an ƙawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun
jin daɗin rayuwar duniya har dama abin da idanu ba su taɓa
gani ba.
A wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a maza
da mata yara da manya, babu masaka tsinke, bisa wata
ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'an ta ta da zallar
ƙarfen jauhari, aka yi mata feshi da koren ruwan yaƙut.
Wani irin shirgegen mutum ne wanda yafi gaba ɗaya
muridan girma kwarjini da cika idanu zaune bisa wata
ƙasaitacciyar karaga. yana sanye cikin wata irin ƙasaitacciyar
shiga irin ta su ta manyan sarakai, sanye da wata alƙyabba da
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
29
aka yi mata ado da gashin ɗawisu kanshu sanye da wani
KAMBUN SARAUTA na zinare.
Zaune a gefen hannunshi na dama, wata tsaleliyar
kyakkyawar budurwa ce ta gaban kwatance.
Budurwar tana da dara-daran idanuwa farare ƙal!
Masu haske tamkar tacacciyar madarar shanu, ɗigon cikin su
ya kasance siɗik mai kwarjini, girar saman su baƙa ce siɗik
tayi luf-luf, hancinta dogo ne mai ban sha'awa, a ƙasan shi an
tsaga wani ɗan madaidaicin baki da labbanshi suka kasance
jajur, wuyanta dogo mai kyau tamkar na barewa, kirjinta kuwa
ya yi tudu a cike yake kuma a tsaye ƙyam! Bai ranƙwafa ba
tamkar nunanniyar gwanda, cikinta a shafe yake tamkar bata
taɓa cin komai ba, ƙugunta daga gaba ya tsuke daga baya
kuma ya yi tudu tamkar idan aka ɗora tuffa za ta zauna, 'yan
yatsun hannayenta da kafafuwanta sun kasance zara-zara
masu ɗaukar hankali.
Wohoho haƙiƙa Allah wannan budurwa ta cika
kyakkyawa ta kece raini, babu wani ɗa namiji mai hankali da
zai yi tozali da wannan kyakkyawar halitta face ya ɗimauce,
kuma ya kamu da matukar kaunar ta a zuciyarshi.
Ba wata ba ce face gimbiya Mashlira 'ya ga sarki muridan
Kushuful-mannar
Sarki Kushuful-mannar ya auri mahaifiyarta ne a cikin
waɗansu a yarin larabawa da aka riba to a matsayin
fursunonin yaƙi, bisa binciken da sarki Kushuful-mannar ya yi
bisa halarar tsafin shi ya gano cewa 'yar shi Mashlira ce silar
dauƙaƙar shi a duniya da ci-gaban zuri'arshi a doran ƙasa,
bisa wannan dalili ne ya sanya ya ke matuƙar kaunar ta fiye
da komai a rayuwarshi.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
30
Tun kafin dakarun da suke ɗauke da su sarki Lazwar su
iso inda karagar mulki take gimbiya Mashlira ta ƙurawa
Lazwar idanu ko ƙiftawa ba ta yi, a karon farko a rayuwar ta ta
ji wani abu ya ɗarsu a zuciyarta.
Shi kuwa sarki Lazwar koda ya ga irin kallon da budurwar ke
yi mashi sai ya ji zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya kama shi
jikin shi ya kama ƙyarma, abu na farko da jefa shi cikin
wannan hali shi ne, a iya tsawon rayuwarshi tun da yake bai
taɓa gani ko jin labarin 'ya mace mai matuƙar kyawun ta ba.
Abu na biyu kuwa shine lokacin da da ya haɗa idanu da
ita sai ya ji cewa a duk faɗin duniya babu wata budurwa da
yake ƙauna tamkar ta.
Yanzu ta ya ya zuciyarshi za ta kamu da soyayyar wata 'ya
mace bayan cewa ba zai taɓa kusantar mace ba da niyar aure
ba face ya karya sihirin dake jikinshi.
Wai shin wane tabbaci ya ke da shi cewa waɗannan
muridan za su bar shi a raye,
Sa'adda sarki Lazwar ya zo nan azancen shi sai hankalinshi
ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe.
Lokacin da ya rage sauran kamar taku goma tsakanin su da
karagar mulki sai dakarun su ka zube ƙasa, su ka kwashi
gaisuwa cikin girmamawa bayan sun ajiye kejin da su Lazwar
ke ciki.
Sarki kushuful-mannar ya shin-shina su sarki Lazwar yana
mai tanɗe baki tamkar wadda zai ci naman ɗawisu.
Sannan ya busar da iskar dake hancinshi wani irin tiririn baƙin
hayaƙi ya fita daga ƙofofin hancinshi.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
31
Kawai sai ya yi wa ɗaya daga cikin dakarun wata inkiya
ta wutsiyar idanu. kawai sai badakaren ya buɗe kejin da bawa
zailan ke ciki ya ɗauko shi ya kwantar da shi akan wani
zagayayyen tudu, sannan ya ɗauko wata zabgegiyar takobi ya
ɗaga sama ya datse wuyan bawa Zailan kuma ya shiga
daddatsa naman shi.
Koda ganin yadda aka yiwa bawa Zailan sai su sarki
Lazwar su ka kamu da matuƙar tausayin shi har ƙwalla ta cika
masu idanu.
Badakaren na kammala daddatsa naman sai ya watsawa
jama'ar dake fadar.
Tun kafin ya kai ƙasa jama'a sun wawashe sun cinye suna
ihun murna da kururuwa mai tayar da hankali.
Badakaren ya sake sanya hannuwanshi a kan kejin da sarki
Lazwar ke ciki ya buɗe sakatun, ya zira hannun sa ya ɗauko
shi ya ɗora shi a bisa wannan tudu, a karo na biyu ya sake
ɗaga takobin domin ya datse wuyan sarki lazwar.
Kafin takobin ta datse wuyan Lazwar sai gimbiya
Mashlira ta dakawa badakaren tsawa sannan ta dubi
mahaifinta ta ce "ya abbana ina neman wata alfarma a gare ka
da abar mani waɗanan fursunoni zuwa gobe, domin nima ina
so na ga na hallaka su da hannaye na domin ɗaukar fansar
kisan da su ka yiwa dakarun mu shin ko ka manta ne cewa
fiye da shekaru ashirin hakan bai taɓa faruwa ba.
Koda jin wannan batu sai sarki zammar ya yi murmushi
mai taushi ga 'yarshi Mashlira ya ce "nayi miki wannan alfarma
ya muradin zuciyata ai girma da matsayin ki ya huce haka,
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
32
gaba ɗaya jama'ar wannan birni da abin da ke cikinsu mallakin
ki ne".
Ko da gama faɗin hakan sai ya yi wa badakaren inkiya a karo
na biyu kawai sai badakaren ya mayar da takobinshi cikin
kuben ta.
Sannan ya ɗauki sarki Lazwar da hannunshi ɗaya tamkar
ya ɗauki takarda ya sake jefa shi cikin kejin ya mayar da kofar
ya rufe, sannan ya sake umartar waɗannan dakaru suka sake
ɗaukar kejinan, har suka fice da fadar gimbiya Mashlira bata
daina satar kallon sarki Lazwar ba tana yi mashi murmushi
mai ɗauke da alamar tambaya.
Al'amarin yarinya Shuraiba da damisar ta kuwa, a she
lokacin da waɗannan samudawan muridai suka samu nasarar
kama abokan tafiyarta ta rugawa ne izuwa wani ɓangare a
dajin ta laɓe domin ta ga abin da muridan za su aikata
Sa'adda ta ga muridan sun ɗauke su a cikin kejunan sun
kunna kai izuwa cikin dajin, sai ta ci gaba da bin sahun su
sannu a hankali, har sai da ta shige izuwa cikin birnin su ba
tare da wani ya gan ta ba, da yake lokacin dare ya fara duhu
sai Shuraiba ta maƙale a dai-dai ƙofar gidan da aka ajiye su
sarki Lazwar, tana zuba idanu domin ta ga wanda zai fito daga
cikin,
tana nan tsaye sai kawai ta hango waɗansu dakaru su bakwai
sun durfafo Ƙofar gidan har dakarun sun zarce gaba, sai
kawai ɗaya daga cikin su ya dubi sauran 'yan uwanshi ya ce
"haƙiƙa ni fa ina jin ƙamshin bil'adama.
Sauran suka dube shi suka ce "kwarai tabbas zancen ka
dutse, muma muna jin hakan kawai dai shiru mu kayi".
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
33
Ko da jin abin da dakarun ke tattaunawa sai shuraiba ta yi wuf
ta shiga cikin wani kwandon shara tare da damisarta, nan fa
wari da ɗoyin dake ciki ya fara galabaitar da ita ga yunwa da
addabe ta, take numfashin ta ya ɗauke, ta sulale ƙasa
sumammiya, a dai-dai lokacinne badakaren ya haska
gwandon sharar da wata fitar ice, dake hannunshi domin ya
ga menene a cikin.
Ko da haskawar ta shi sai ya ga babu komai a cikin
shawara. cike da mamaki da al'ajabi ya sake shaƙar iska dake
wajen amma a wannan karon sai ya ji ba ya jin ƙamshin
bil'adama.
Kawai sai ya juya izuwa inda yan uwanshi suke tsaye ya
tarar da su ya dube su ya ce "babu komai a wajen tamkar
yadda muke tunani, take sauran dakarun su ka cika da
matuƙar mamaki, ɗaya daga cikin su ya yi gyaran murya ya ce
cikin wata irin kakkausar murya "amma kamar yau na samu
labarin cewa dakarun mai girma Zammar masu FARAUTAR
MAZAJE sun samu nasarar kamo waɗansu fursunonin
bil'adama,'.
Wata ƙila wannan kamashi da muke ji yana da alaƙa da
bil'adaman dake cikin wannan birni namu".
Ko da gama faɗin hakan sai dakarun su ka juya suka ci gaba
da tafiya.
Kaico! Haƙiƙa yarinya Shuraiba da damisar baƙaramin
tsallake rijiya da baya suka yi ba.
Abin da dakarun ba su sani ba shi ne tabbas akwai bil'adama
a cikin sharar, kawai dai saboda Shuraiba da damisar ta sun
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
34
sume ne babu rai a tare da su shine ya sanya ba su ji ƙamshin
su ba.
Kuma bisa halayyar muridan matuƙar babu rai a jikin
bil'adama ba za su ji kamshin shi ba. Tsananin sanyin da ya
mamaye birnin bisa ketowar alfijir, shine abin da ya farkar da
yarinya Shuraiba da damisar ta, koda farkawar ta su sai suka
yunƙura suka fito sharar, nan take damisar ta fahimci cewa
Shuraiba ta galabaita ainun da alamu ƙishi ruwa ce ta addabe
ta, koda fahimtar sai kawai ta shiga tona ƙasa da ƙafarta ɗaya
jim kaɗan sai ga shi ta tarar da ruwa.
Kawai sai Shuraiba ta sunkuiya ƙasa bisa gwiwoyinta ta
sanya hannayenta biyu, tana kamfatar ruwan ta na sha, duk
da cewar ruwan yana da sanyi ƙarara har yana kama mata
hakuri, amma haka ta cigaba da kwankwaɗar shi har sai da ta
ƙoshi.
A sannanne Shuraiba ta ji ƙarfi a jikinta, kawai sai ta yunƙura
ta haye bisa gadon bayan damisar.
Sannan ta cigaba da tafiya a cikin birnin, sai dai a wannan
karon ba su haɗu da komai ba, haka dai su ka cigaba da tafiya
a sannu-sannu, tana cikin tafiyar ne ta hango wani katafaren
gida waɗansu irin dakaru tsaye a wajen, kuma shirye cikin
gagarumar shigar yaƙi rike da miyagun makamai.
Nan take Shuraiba ta sunkuiyar da kanta ƙasa tana mai
zurfafa cikin kogin tunani.
Daga can sai kawai ta durfafi ƙofar gidan, kafin ta isa
sai ta hango waɗansu dakaru na daban ɗauke da waɗansu
kejunan ƙarfe, kawai sai ta rakaɓe a wani waje tana hangen
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
35
abin da ke faru, ba wasu ba ne a cikin kejin ba face su sarki
Lazwar
Ko da ta ƙwarewa kejin kallo sai ta lura cewa ƙofofin kejin
suna ɗauke da waɗansu irin kwaɗuna, waɗanda ke nuna
cewa akwai mabudin su, wani tunani da ya faɗo wa yarinya
Shuraiba shi ne.
Yanzu idan har ta ƙyale aka shige da su sarki Lazwar cikin
gidan ba lallai ne suka kasance a raye ba, lallai dole ta yi
dukkanin ƙoƙarin da ya dace don ceto rayuwar su kafin gari
ya waye.
Gama tunanin hakan keda wuya sai Shuraiba ta hangi
wani tsuntsu a saman ta yana yana wani irin kuka da ta ga ya
durfafi wani ɓangare na musamman a wannan gida da za
shige da su sarki Lazwar, cikin matuƙar farin ciki ta dunga bin
bayan tsuntsun, ba tare da waɗannan dakaru sun ganta ba.
Koda isowar ta kusa da saitin inda dakarun suke a dai-dai
lokacinne aka iso da su sarki Lazwar za a shiga da su cikin.
Sai kawai ta ga wannan tsuntsu ya buɗe bakinshi ya busa wa
gaba ɗaya dakarun wani irin koren haske, kafin ka ce me sun
ɓingire ƙasa suna sharar barci har da munshari, kuma koren
hasken ya shiga cikin kejunan su sarki Lazwar, take suka
narke