ta kashe waɗannan
dakaru domin ta ceci rayuwar ta da jaririyar ta.
Lokacin da aljani ZA'ARATUN-LAYAL ya zo dai-dai nan
a hikiyar sarauniya Abidat ta birnin Sin da yake bawa yarinya
Shuraiba sai ya tsuke bakinshi ya yi shiru.
Al'amarin da ya sanya yarinya Shuraiba ta dube shi cikin
alamun tsananin damuwa ta ce "ya kai masanin HIKAYAR
DUNIYA shin mene ne yasanya zaka katse min wannan
daddaɗan labari? Tabbas ina so naji wace irin rayuwa
Suhaimat da jaririyar ta za su yi a nan gaba, kuma menene
dalilin da ya baro da ita daga birnin su?
Shin ma mene ne ya sanya dakarun ke farautar Suhaimat?
Koda jin waɗannan tambayoyi sai aljani ZA'ARATUN-LAYAL
ya bushe da dariya ya dubi yarinya Shuraiba ya ce "ya ke
Shuraiba shin baki gani ba ne har alfijir ya keto safiya ta yi".
Koda jin wannan batu daga bakin Za'aratun-layal sai
Shuraiba ta cika da mamaki, ai kuwa sai ta miƙe tsaye ta
domin ta fara shiri kamar yadda sarki Lazwar ya yi masu
bayani.
Wannan shi ne abin da ya faru a masaukin yarinya
Shuraiba.
Kamar yadda ya wakana a masaukin Shuraiba haka
al'amarin ya kasance a masaukin darki Lazwar da gimbiya
mashlira.
A inda Mashlira ta katse labarin bawa sarki Lazwar na matsafi
Sahibul-ukub da mahaifin ta sarki Zammar.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
72
Saboda ganin ketowar alfijir a sararin samaniya.
A ɓangaren masaukin yaro Imran kuwa, ya yin da ya ga alfijir
ya gabato sai ya ɗaura alwala ya shiga gabatar da nafita,
bayan nan kuma sai gudanar da sallar asuba, q lokacin da
hadima khadijat ta bisa a baya a matsayin mamu.
Lokacin da rana da fito ne ta yi haske sai khadijat ta yi
umarni aka kaiwa kowannnen su bahon ruwan wanka, bayan
kowa ya tsaftace jikinshi ya yi kalaci, sai aka ɗunguma izuwa
cikin gari domin gudanar da abin da aka zo nema.
Wannan shi ne abin da ya faru da su sarki Lazwar a
lokacin da aka kai su izuwa masauki.
Babi na sha ɗaya
Lokacin da amarya Munirat ta ci gaba da tafiya a cikin
gidan sarautar birnin Darul-usur bayan ta kuɓuta daga sharrin
magajin gari Yasiran.
Sai ta cigaba da tafiya a cikin gidan sarautar tana ratsa ƙofofi
da dakaru iri daban-daban, zuciyarta cike da matuƙar farin ciki
maral musaltuwa.
Ta na cikin wannan hali sai wannan tsuntsu ya sake bayyana
a gare ta a sama cikin iska
Tsuntsun ya riƙiɗa izuwa wani kyakkyawan aljani mai kyawun
sura, aljanin ya na ɗauke da sura irin ta bil'adama, sai dai
yana ɗauke da fuka-fukai.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
73
Aljanin ya dubi Munirat ya ce "ya ke Munirat ki yi sani cewa da
farko dai suna na Lailatul-azhar kuma ni hidimi ne ga sarkin
musulmin aljanun duniya baƙaƙen fata.
Ubangiji ya bayyana wa sarkin mu halin da ki ke ciki
dama sauran mutanen birnin ku na irin baƙin zaluncin da
magajin gari Yasiran ke yi maku, sannan kuma ya turo ni ne
domin na kawo ƙarshen mulkin zaluncin shi baƙi ɗaya.
Ki yi sani cewa kalaman da ki ka karanta a jikin fuka-fukaina
har kika tsira daga sharrin magajin gari, ba wasu kalmomin ba
face KALMAR SHAHADA wacce duk wanda ya furtata ta da
tabbatar wa a zuciyarshi to ya yi imani da Ubangijin gaskiya
da ya halicci komai da komai.
Idan har kin bayar da gaskiya da Ubangijin ɗaya daya
baki nasara akan magajin gari to tabbas zamu samu nasarar
ganin bayanshi.
Koda jin wannan batu daga bakin aljani Lailatul-azhar sai
amarya Munirat ta cika da matukar farin ciki maras musaltuwa,
ta dube shi ta ce "ina so yanzu ka shigar da ni addinin ka".
Ba tare da wani ɓata Lailatul-azhar ya karanta mata
KALMAR SHAHADA.
Nan fa ya zamana cewa kafin mako guda fiye da mutanen
birnin sun karɓi addinin musulunci a hannun amarya Munirat.
Magajin gari Yasiran kuwa sai ya kamu da wata irin
rashin lafiya, sakamakon wannan wuta da ta ƙona jikinshi,
Nan fa aka rasa wanda zai gaje shi a kan karagar mulkin shi.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
74
'Yan Majalisar suna ganin cewa tabbas yanzu hawa karagar
mulkin Yasiran ana iya kiran shi da SARAUTAR MUTUWA.
Domin su ganin a ko da yaushe magajin gari zai iya samun
lafiya, ko kuma sarki Lazwar ya dawo daga tafiyar da ya yi.
Saboda ba zai yiwu a zauna haka babu shugabanci bisa
dole jama'ar gari suka ɗora amarya Munirat a matsayin
sarauniyar su.
Nan fa jama'a suka fara samun yanci, farin ciki gami da
walwala sakamakon hasken musulmi da bayyana a gare su,
Al'amarin Shuraiba kuwa Lokacin da ta cigaba da tafiya a
cikin birnin Istanbul domin nemo mahaifiyarta sai ta wanzu
tana tafiya babu sassauci, tana cikin wannan hali ne sai ta
hango wajen waɗansu almajirai ke zaune suna bara a
kasuwar, kawai sai ta matsa izuwa daf da inda suke ta shiga
yin nazarin su.
Abu na farko da ya faɗo mata a rai shine shin yanzu ina kike
da tabbacin mahaifiyarki take, ki na ganin cewa mahaifiyarki
zata kasance daga cikin waɗannan almajirai dake yin bara?
An ya kuwa sarki Ladiyas bai mayar da mahaifiyar ki matar shi
ba?
Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenen.
kawai sai ta ɗauki mayafi ta ɗaure fuskarta da rawani, kana ta
ɗauki wani ƙoƙo ta ajiye a gaban ta, sannan ta shiga izuwa
cikin su ta saje da su tamkar ba ita ba.
Zaman ta ke da wuya sai wata dattijuwar almijira dake
kusa da ita ta du be ta ta ce "ya ke wannan yarinya shin ke
kuwa me kika rasa a rayuwar ki da za ki fito bara, baƙya duba
wa ki ga cewa ke yarinya mai karancin shekaru".
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
75
Koda jin wannan batu daga bakin dattijuwar sai Shuraiba
ta cika da matuƙar mamaki ta dube ta ta ce "ya ke wannan
dattijuwa ki yi sani cewa bakomai ba ne ya sanya ni aikata
wannan bara ba sai domin na samu abin da zanyi kalaci.
Mahaifina ya mutu tun ina da shekara bakwai a duniya,
mahaifiyata ce take a raye ina neman ta ruwa a jallo, domin ita
ce kaɗai ta rage min a duniya.
Koda jin amsar wannan tambaya sai dattijuwar ta bushe
da yar karamar dariya ta dube ta ta ce "tabbas yaro yaro ne
kuma duk wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi, na
san cewa akwai muhimmin al'amari daya sanya ki zuwa
wannan waje domin, ban taɓa ganin ki ba tun da nake fitowa
wannan bara tawa".
Koda jin wannan batu daga bakin dattijuwar sai Shuraiba
ta yi dariya ta ce "tabbas da akwai buƙatar hakan da na nema
a wajen wani tun kafin na iso wannan waje, amma tambayar
da zan yi maki wace matsalar dake tattare da wannan waje?
Dattijuwar ta yi dariya ta ce ''ya ke wannan yarinya ki yi sani
cewa bakomai yawan dinaren da mutum zai samu na sadakar
da za a bashi, sai dakarun sarki Ladiyas sun zo sun karɓi
haraji, da ƙyar za ka samu ka tsira da kaso ɗaya cikin goma.
Idan kuwa aka yi rashin sa'a baka samu sadaka ba, to fa sai
sarki ya sanya an kai mutum aikin horo a gidan sarauta domin
ka yi aiki adadin wannan dinare da baka biya harajin ba";
Da jin wannan batu daga bakin almajirar sai yarinya
Shuraiba ta ji ta ƙara tsanar sarki Ladiyas fiye da komai a
rayuwar ta. Sannan ta dubi almajirar cikin alamun matuƙar
tausayin ta ce "tabbas sarki Ladiyas ya cika azzalumi kuma
maras tausayi, yanzu a ce almajirai ma sai sun biya haraji,
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
76
Koda jin wannan batu sai mamaki almajirar har ta buɗi baki da
nufin ta ce wani abu sai a ka hango dakarun sarki Ladiyas sun
shigo kasuwar a bisa dawakai su kamanin ɗari biyu shirye
cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensu ɗauke da waɗansu
murtuka-murtukan kulake.
Nan fa kasuwar ta hargitse jama'a suka dunga kwashe
kayayyakin su suna buɗa wa dakarun hanya, domin idan har
suka iso mutum bai kwashe ba take za su bi ta kan kayan da
dawakan su su tattake.
Lokacin da dakarun suka iso wajen da su Shuraiba su
ke sai suka shiga karɓar harajin a wajen dukkan almajiran
dake wajen, suna cikin karɓar ne suka iso kan wannan
dattijuwar almajira dake zaune kusa Shuraiba.
Jikinta na ƙyarma ta zira hannunta cikin ƙoƙon barar ta lissafo
dinare ta miƙa wa wani badakare, bakinta na karkarwa ta ce
"ga shi ya shugabana har da harajin wannan yarinyar da ke
zaune a kusa da ni,
Kafin hannun badakaren ya kai inda dinaren yake yarinya
Shuraiba ta shammace shi ta gabza mashi wawan naushi a
maƙogaronshi.
Saboda matuƙar ƙarfin dukan sai badakaren ya yi
karanta wa sau biyu a sama, sannan ya faɗi ƙasa matacce ko
shurawa bai yi ba, al'amarin da ya firgitarwa jama'a dake
kasuwar kenan kuma ya harzuƙa zukatan sauran dakarun.
Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya shuraiba a
lokacin da shiga cikin gari domin neman mahaifiyarta.
Al'amarin sarki Lazwar kuwa lokacin da fice da ga masaukin
su ya kutsa cikin birnin Istanbul domin nemo hanyar da zai
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
77
sadu da baiwa Sharifa, sai ya wanzu yana ratsa layu ka da
unguwanni babu sassauci.
Yana cikin tafiyar ne ya hango waɗansu cincirindon al'ummar
a gefen kasuwar, cikin hanzari ya matsa daf da wajen domin
ya ga wata irin waina ake toyawa.
Sa'adda da ya matsa daf da wajen sai ya ga ashe waɗansu
ƙarfafan samari ne guda biyu ke baiwa hammata iska jama'a
sun kewaye su suna kallo.
Idan ɗayan ya gabzawa ɗan uwanshi naushi sai ka ga ya faɗi
kasa tim q matuƙar galabaice, amma saboda naci da juriya sai
kaga ya miƙe tsaye zumbur ya mayar da martani.
A gefe guda kuwa wani badakare ne mai ƙirar
samudawan farko ma'abocin kwarjini da haiba, kallo ɗaya
zaka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance GWARZON
DUNIYA mai ƙarfi na Allah ya isa, yana zaune bisa wata
ƙasaitacciyar kujera ta alfarma, ya zuba idanu yana kallo
yadda artabun ke wakana da alama shine mai kula da gasar
da ake aiwatar wa.
Sarki Lazwar ya matsa daf da wani mutum ya dube shi ya
ce " Wai shin mene ne amfanin abin da waɗannan samari ke
yi na yaƙar junan su?
Koda jin wannan tambaya sai mutumin ya dubi sarki
Lazwar ya bushe da dariyar mugunta ya ce "da alama kai
baƙo ne a wannan birni ko?
Sarki Lazwar ya gyaɗa kai alamar haka ne, Mutumin ya ce "ya
kai wannan baƙo ka yi sani cewa waɗannan da ka gani bayi
ne da aka farauto daga can wata nahiya daban, duk bayan
mako ɗaya mai girma Ladiyas yana sanya a fitar mashi da
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
78
GWARAZAN JARUMI a cikin su da zai kasance ɗaya cikin
masu tsaron lafiyar sarauniya.
Bisa wannan dalili ne ya sanya aka tara su a wannan waje
domin fitar da zakara.
Koda jin wannan batu daga bakin mutumin sai Lazwar ya cika
da matuƙar farin ciki, domin kuwa dama ta samu wacce zata
zamto sanadin kasancewar shi bawa a masarautar Istanbul.
Domin dai ya cika burin shi na saduwa da baiwa Sharifa da za
ta taimaka mashi wajen mallakar abubuwan da zai karya
sihirin tsafin da abokin gabar shi sarki Darwazu ya yi mashi.
A ɓangaren jarumai biyun kuwa tuni labari yasha banbam
domin kuwa ɗaya cikin jaruman ya samu nasara akan ɗayan
Inda ya yi masa jina-jina har layi na ɗibarshi yana faɗuwa
ƙasa.
Nan fa wannan badakare dake kula da gasar ya shiga
ƙyalƙyala dariya bisa ganin yadda ɗayan jarumin ke yin nasara
akan ɗayan, al'amarin da ya fusata sarki Lazwar kenan yaji ya
kamu da matuƙar tausayin jarumin, kawai sai ya dako wawan
tsalle daga inda yake tsaye ya daki ƙirjin jarumin dake samun
nasarar da dukkan ƙarfin shi.
Saboda ƙarfin dukan sai da jarumin ya yi sama yana
mai tsandara ihu sannan ya faɗo ƙasa a matuƙar galabai ce,
hannayen biyu suka karye ji kake ruƙus! Ƙas.
Cikin matuƙar al'ajabi jama'a suka duba domin su ga ko wane
ne, ai kuwa koda suka yi arba da sarki lazwayr sai suka cika
da matuƙar mamaki, domin sun san cewa tabbas koma wane
ne shi baƙo ne kuma ya jifa kanshi a cikin bala'i, domin ba ka
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
79
yi laifin komai ba ma sarkin yaƙi Darusu ya zalunce ma
ballantana ka shiga gonar shi.
Sarki Lazwar ya matsa izuwa inda ɗayan jarumin ke
kwance ya tashe shi zaune ya karkaɗe mashi ƙurar dake jikin
shi.
Al'amarin da ya yi matuƙar fusata sarkin yaƙi Darusu
kenan zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata kone, kawai
sai ya dakawa dakarun shi tsawa suka zare makaman su suka
yi ɗauki kan Lazwar.
Lokacin da aka haɗu sai aka ruguntsume da azababban yaƙi
nan fa artabun ya zamto abin tsoro da kuma ban al'ajabi,
domin ga shi dai sarki Lazwar ba ya riƙe da makami amma sai
ya zamtowa dakarun alaƙaƙai kuma GUGUWAR AJALI suka
rasa yadda zasu yi da shi.
Duk wanda ya gabzawa naushi a wata gaɓa a jikin shi
sai ka ji ta ƙarye ta yi ƙara ruƙus! Ƙas.
Kuma ya wanzu yana zillewa hare-haren dakarun cikin
matuƙar zafin nama JUTIYA DA BAJINTA irin ta ZARATAN
MAYAKA,
Nan fa ihu da kururuwar dakarun gami da ƙarar karafniyar
karafa ta cika dodon kunne, nan fa ya zamana cewa waɗansu
dakarun na daban ya rugawa izuwa kan sarki Lazwar cikin
matuƙar fushi, bisa ganin yadda yake ragargazar 'yan uwan
su.
Kafin cikar daƙiƙa arba'in sarki Lazwar ya bazar da dakaru
fiye da saba'in, dukkanin su sun zube a ƙasa magashiyan
suna nishin wahala.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
80
Nan fa zuciyar sarkin yaƙi Darusu dake tsaye a gefe
guda ta kama tafarfasa tamkar zata fasa ƙirjinshi ta fito waje,
amma kuma wani abu da ya faɗo mashi arai shi ne.
Tabbas wannan baƙon jarumi ya cika GWARZON DUNIYA
yadda ake bukata, kuma tabbas idan na kai shi ga mai girma
Ladiyas zan samu ƙarin daraja da girmama wa, shin me zai
hana ka kama shi a matsayin bawa ga tafi da shi ga mai girma
Ladiyas?
Koda gama yanke wannan shawara sai sarkin yaƙi Darusu
ya shammaci sarki Lazwar ya lallaɓo ta bayan shi ya dunƙule
hannunshi ɗaya ya kirɓa mashi wawan naushi a fuska a
gadon bayan shi. Saboda ƙarfin dukan sai da ƙashin bayan
Lazwar ya yi ƙara ya faɗi ƙasa sumamme.
Cikin matuƙar farin ciki sarkin yaƙi ya yi umarci waɗansu
dakaru suka ɗaure hannayen Lazwar da wata sarƙa suka ɗora
shi a kan doki.
Nan take Darusu ya kama dokinshi ya haye ya sakar mashi
linzami ya durfafi hanyar da zata sada shi da gidan sarauta
dakarunshi suka rufa mashi baya
Waɗansu kuma suka shiga ɗaukar dakarun suka samu
raunuka domin ba su taimakon gaggawa.
Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Lazwar a
lokacin da ya shiga cikin gari domin saduwa da baiwa Sharifa.
Al'amarin yaro Imran kuwa, lokacin da fice daga masaukin
su bayan ya kammala kalaci sai ya wanzu yana ratsa saƙo da
lungu na birnin Istanbul. Domin cigiyar 'yar uwarshi, hakan ya
sanya duk wajen da hango taron jama'a sai ya je ya tsaya,
domin ya ga me ake gudanar wa.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
81
Yana cikin hakan ne ya iso wani waje mai cike da tarin
al'umma, wani dattijo yana tsaye yana yi masu wani jawabi,
kallo ɗaya za ka yiwa mutumin ka fahimci cewa ya kasance
jagoran wani addini.
Kawai sai yaro Imran ya ja ya tsaya yana sauraren
jawabin sa.
Malamin na cikin jawabin shi sai yaro Imran ya ɗaga
hannunshi ya ce "ya shugabana ina da wata tambaya idan ba
za ka damu ba. Koda jin wannan tambaya daga bakin Imran
sai gaba ɗaya jama'ar dake wajen suka cika da matuƙar
mamaki.
Domin ba a taɓa jin wanda ya yiwa matsafi Shamrul wata
tambaya ba akan abin da yake bayani game da bautar gunki.
Cike da matuƙar mamaki matsafi Shamrul ya dubi yaro
Imran da fuskarshi ke rufe da rawani idanuwan kaɗai ake gani
ya ce da shi ''ya kai wannan yaro faɗi tambayar ka ina
sauraren ka".
Yaro Imran ya yi gyaran murya sannan ya ce "ya kai
wannan malami tambaya ta a gare ka ita ce, shin waɗanne
mutane ne suka fara bautar gumaka a duniya kuma mene
dalilin su na yin hakan?
Tambaya ta biyu mene ne ya sanya gaba ɗaya gumakan da
ake bauta mu ne muke sassaƙa su da hannayen mu, to ya ya
abin da mune muka samar da su daga babu a ce kuma su ne
allolin mu?
Koda jin waɗannan tambayoyi daga bakin yaro Imran sai
fuskar matsafi Shamrul sai ta sauya daga walwala izuwa fushi,
kuma ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya kama shi ainun.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
82
Amma saboda kar jama'ar dake wajen su fahimci hakan sai
kya basar.
Abin da matsafi Shamrul bai sani ba shi ne haƙiƙa
maganganu Imran sun yi tasiri a zukatansu baki ɗaya
al'ummar dake wajen.
Tabbas waɗannan tambayoyi da wannan yaro mai hikima ya
yi sune abubuwan da ya kamata kowannen su ya sani kafin ya
kasance cikin wannan addini na bautar gumaka,
Nanfa mutanen dake wajen suka dunga cewa a amsa
masu waɗannan tambayoyi haƙiƙa muna so mu ji ya tabban
malami.
Sautin muryoyin jama'ar ya sake ruɗa matsafi Shamrul, kuma
suna amsa kuwwa izuwa cikin birnin, tare janyo hankulan
sauran mutanen gari suka dunga tuttɗowa izuwa wajen,
sa'adda da matsafi Shamrul ya ga cewa adadin mutanen da
ke wajen yana cigaba da hauhawa, kuma ya tabbatar da cewa
idan ya amsa tambayoyin abin kunya zai faru.
Sai kawai ya yi wuf! Ya shafi wani gurun tsafi a damtsenshi na
hagu, nan take cikin daƙiƙa biyu kacal hadari ya taso gadangadan sama ta yi duhu, a ka fara tsawa, walƙiya gami da iska
mai ƙarfi, nan fa waje ya hargitse jama'a suka fara darewa
suna rugawa izuwa unguwannin su domi kar ruwa ya yi masu
ɓarna.
A bangaren yaro Imran kuwa yana ɗaga kanshi sama
ya kalli hadarin sai ya fahimci cewa, an samar da shi ne ta
sihirin tsafi domin matsafi Shamrul ya kawar da hankulan
al'umma daga amsar tambayoyin da ya yi nashi. Kawai sai ya
yi dariya ya juya ya nufi hanyar koma gida, domin ya tabbatar
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
83
da cewa idan har matsafi Shamrul ya kasa amsa wa mutane
tambayoyin za su juya mashi baya su daina karɓar fatawar
addini daga gare shi, sai da yaro Imran ya bar wajen, sannan
matsafi Shamrul ya daina waigen shi ya na satar kallon shi
Wannan shi ne abin da ya faru da yaro Imran
BABU NA SHA ƊAYA
Al'amarin Gimbiya Mashlira kuwa dukkan abin da wakana
da masoyin ta sarki Lazwar a kasuwa tun daga lokacin da ya
fafata artabu da waɗannan dakaru har izuwa lokacin da sarkin
yaƙi ya yi umarni aka ɗauke shi aka nufi gidan sarautar, tana
tsaye a gefe guda tana kallo.
Koda ganin hakan sai hankalin ta ya dugunzuma ainun,
bisa ganin cewa babu tabbacin za su bar shi a raye, bisa
mummunan laifin da ya aikata. To kenan idan har hakan ta
faru za bai samu damar cika burin shi na saduwa da baiwa
Sharifa ba, harya bayyana mata bukatar shi, wai shin ma ta ya
ya zan iya barci a daren yau matsawar ba na jin motsin
masoyina Lazwar a kusa da ni, bayan cewa zuciyata ta kamu
da matuƙar kaunar shi.
Tabbas zan kasance a tare dashi duk TSANANI DA
UKUBA koda kuwa bazai taɓa gane cewa ni ba ce
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
84
Sa'adda gimbiya Mashlira tazo dai-dai nan a tunaninta,
sai kawai ta dunga bin sahun su sarkin yaƙi Darusu a baya ba
tare da wani ya gan ta ba , lokacin da ta ga cewa an kusa isa
gidan sarauta sai kawai tayi ruf ta rafke ɗaya daga cikin
dakarun, a cikin wani lungu ta maye gurbin tufafin dake jikinta
da na shi, sannan ta kama dokinshi ta haye ta shiga cikin
dakarun ta saje da su ba tare da wani ya gane ta ba.
Wannan shi ne abin da ya faru da gimbiya Mashlira 'yar
sarkin maridai Zammar, bayan ta fice daga masaukin su dake
tsakiyar birnin Istanbul.
BABI NA SHA BIYU
Al amarin yarinya shuraiba kuwa lokacin da ta gabza wa
ɗaya cikin dakarun dake karɓar haraji naushi a magoranshi ya
faɗi ƙasa matacce, sai sauran suka zare kulaken su cikin
matuƙar fushi suka yi ɗauki kan ta.
Ko da ganin hakan sai almijiran dake wajen suka ruga
suka bar wajen domin su tsira da rayukansu.
Ita kuwa Shuraiba sai ta gyara tsayuwar ta tana jiran
isowar dakarun a lokacin da jama'a suka buɗe masu fili mai
faɗi sosai.
Lokacin da suka iso sai aka yi KARON MAZA suka afkawa
Shuraiba da azababban yaƙi, suka wanzu suna kai mata duka
da kulaken cikin zafin nama domin su yi mata kisan farat ɗaya.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
85
Ana fara wannan artabu ne wani abin mamaki ya fara
gudana, domin kuwa Shuraiba ta zamo tamkar shaidaniya a
tsakanin dakarun, ta wanzu tana zillewa tare da hare-haren
dakarun cikin matuƙar zafin nama.
Nan fa ta dunga haɗa karo tsakanin dakarun, suna zubewa
kasa magashiyan.
Amma sai su yunƙurawa su sake afka mata da yaƙi.
Lokacin da aka shafe tsawon rabin sa'a ana wannan
karon batta sai ya zamana cewa Shuraiba da dakarun sun
fara galabaitar da juna
Ana cikin wannan yaƙi Shuraiba tayi wuf ta ƙwaci wani kulki a
hannun ɗaya daga cikin dakarun, ta shiga gabza masu duka a
ƙafafuwansu, kafin lokacin mai tsawo, ƙafafuwan dakarun sun
sage, sun yi tsami gaba ɗayansu su sun zube a ƙasa suna
nishin wahala
Nan fa jama'a suka dunga shewa suna yiwa Shuraiba
jinjina gami da kirari cikin matuƙar farin ciki bisa ganin cewa ta
karya alƙadarin dakarun
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai akaga jiyo haniniyar
dawakai gami da bugun tambura daga can nesa kaɗan,
alamun dake nuni da cewa wani ma'abocin sarauta yana gab
da bayyana.
Koda jama'a suka waiga baya sai suka hango ashe tawagar
gimbiya Lamrat ce.
Cikin matuƙar firgici suka sunƙuiya ƙasa bisa gwiwoyin su,
domin girmamawa a gare ta, sannu a hankali har suka iso
izuwa wajen.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
86
Kawai sai aka ga keken dokin dake ɗauke da gimbiya Lamrat
ya tsaya dai-dai inda yarinya shuraiba take tsaye
Take Waɗansu dakaru mutum biyar suka ruga izuwa inda
Kofar keken take suna masu durƙusawa ƙasa bisa gwiwoyin
tare shimfiɗa gadon bayansu, sannu a hankali ƙofar keken
dokin ta buɗe, sai ga gimbiya Lamrat ta fito ta taka gadon
bayan dakarun ta sauko ƙasa.
Sanye take cikin kariyar alƙyabba da aka yi mata cin
baki da zaren lu'u lu'u da zubar daju, sanye a kanta akwai
wani kambu na sarauta na zinare fuskarta rufe take da wani
mayafi idanuwanta ma'abota kwarjini kaɗai ake gani.
Kai tsaye gimbiya Lamrat ta taka da ƙafafuwanta ta durfafi
inda yarinya Shuraiba ke tsaye wacce ita ce kaɗai bata faɗi
ƙasa domin girmama a gare ta ba.
Lokacin da ya rage saura taku uku a tsakanin su sai gimbiya
ta ja ta tsay, ta kai duba izuwa kan dakarun da Shuraiba ta a
raunata, sannan ta dubi Shuraiba tana mai ƙura mata idanu ko
kiftawa ba ta yi.
Nan take su duka biyun suka ji zukatansu na buga wa da ƙarfi
wani abu ya ɗar su a cikin ta.
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa gimbiya Lamrat mamaki
kenan, ta tambayi kanta a cikin ranta tana mai cewa. Shin
mene ne ya sanya zuciyata ta buga lokacin da na yi arba da
wannan yarinya? Shin ko kuwa hakan na nufin har yanzu 'yata
ƙwaya ɗaya tilo tana raye?
Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenan, kawai sai
ta cigaba da ƙurawa mata idanu.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
87
Daga can sai ta buɗi baki cikin zazzakar murya mai
ɗaɗin sauraro ta ce "ya ke wannan yarinya shin wace ce ke
kuma mene ne dalilin da ya sanya kika zaɓi ki yi bara ki ƙyale
sana'a, wacce za ta ba ki damar ci da sha.
Ko da jin wannan tambaya sai yarinya Shuraiba ta dubi
gimbiya cikin ladabi da girmama wa ta ce "ya shugabata ki yi
sani cewa ni baƙuwa ce a wannan birni, bani da kowa na
shigo wannan birni domin neman mahaifiyata da aka rabu Ni
da ita tun ina yarinya ƙarama".
Da jin amsar wannan tambaya sai gimbiya ta sake jin
zuciyarta ta buga da ƙarfi a karo na biyu
Koda ta sake ƙurawa Shuraiba idanu sai ta taga tana ɗauke
da kamanni iri ɗaya sak da na masoyin ta kuma uban
'ya'yanta sadauki Murrasu.
Nan take abubuwan da suka faru da masoyinta da sarki
Ladiyas ya fara dawo mata a cikin ƙwaƙwalwarta, cikin
ƙanƙanin lokaci zuciyarta shiga tafarfasa tamkar zata ƙone.
Tsananin ƙiyayyar sarki Ladiyas ta ci gaba da ruruwa a cikin
ranta.
Haƙiƙa babu makawa wannan yarinya ba wata bace face 'yata
Shuraiba, wata zuciyar kuma ta ce da ita, amma a halin yanzu
bai dace ki wani yasan da hakan ba, dole ki yi jinkiri ki sake
nazari akai sosai.
Koda gama tunanin hakan sai ta dubi Shuraiba ta ce "ya
ke wannan yarinya idan ba za ki damu ba ina so ki zauna tare
da ni, har izuwa lokacin da zan sa a nemo maki mahaifiyarki".
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
88
Da jin wannan batu sai farin ciki ya kama yarinya Shuraiba ta
ce a cikin ranta, tabbas wannan wata dama ce da zan ɗauki
fansa a kan sarki Ladiyas da kuma gano inda mahaifiya ta ke.
Shuraiba ta ce "na amince da wannan alfarma da kika yi
min, amma nima ina roƙon alfarma a wajen ki da a daina
karɓar haraji a wajen waɗannan almajirai har abada".
Koda jin wannan batu daga bakin Shuraiba sai gimbiya Lamrat
ta cika da matuƙar farin ciki ta dubi wani badakare a dake
tsaye a gefenta ta ce da shi ''daga yau na haramta karɓar
haraji a hannun dukkan wani almajiri dake wannan waje.
Badakaren ya risina ya ce ''an gama ranki shi daɗe''.
kawai sai ta kama hannun Shuraiba ta durfafi inda keken
dokinta yake suka shiga izuwa ciki suka zauna a tare, sannan
badakaren dake kula da keken ya zaburi dawakan kenan ya ci
gaba da tafiya.
Nan fa jama'a suka cika da matuƙar mamaki, almajiran dake
wajen kuma sai sai farin ciki ya turnuƙe zukatansu, suka shiga
yin shewa, kiɗa da rawa bisa