suka zama ruwa, sarƙoƙi da aka ɗaure aljani Za'aratunlayal suka ɓace ɓat!.
Daga can sai tsuntsun ya rikiɗa izuwa wata tsaleliyar
kyakkyawar budurwa, ba wata ba ce face gimbiya Mashlira 'ya
ga sarkin murida Zammar.
Nan fa sarki Lazwar, Shuraiba, sarkin yaƙi da bawa Shaiban
suka cika da matuƙar al'ajabi.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
36
Cikin wata irin zazzaƙar murya mai ɗan karen daɗi tamkar ana
busa sarewa, gimbiya Mashlira ta dube su su duka huɗun ta
ce "yanzu ba mu da lokaci da zamu tattauna domin a
kodayaushe mahaifina zai iya biyo sahun mu, matsawar ya
riske mu ɗayan mu ba zai tsira da rayuwar shi ba.
Ko da jin wannan batu daga bakin Mushlaira sai sarki lazwar
ya umarci aljani Za'aratun-layal ya ɗebe su baki ɗaya,
zuciyarsu cike da matuƙar farin ciki bisa ganin cewa yarinya
shuraiba ta na raye cikin koshin lafiya, kuma gimbiya Mashlira
ta ce ci rayuwar su.
A dai-dai wannan lokaci ne sarki Zammar da
tawagarshi suka bayyana a wajen, koda ya ga dakarun kurku
kwance suna sharar barci kuma babu su Lazwar da 'yarshi
Mashlira, sai kawai ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu, ihun
shi ya haddasa wata girgizar ƙasa da ta sanya gine-gine suka
dunga rushewa, nan fa birnin ya kaure da gujegujen jama'a
domin TSIRA DA RAYUKA.
Sai da sarki ya tsuke bakinshi sannan komai ya samu dai-dai
ta gidaje suka dai na rushewa mutane suka daina hallaka.
Kawai sai ya ɗauko madubin tsafinshi ya shafe shi da
hannunshi na hagu, yana mai karanta waɗansu dalasiman
tsafi, yana gama rufe bakinshi hoton aljani Za'aratun-layal ya
bayyana a kai, yana tsala azababban gudu ɗauke da su sarki
Lazwar da 'yarshi Mashlira.
Koda ganin hakan sai takaici ya ƙara turnuƙe zuciyarshi
har ƙwallar baƙin ciki ta zubo mashi, kawai sai ya runtse
idanuwanshi yana mai karanta waɗansu dalasiman tsafin na
daban, koda kammala hakan sai ga wata irin halitta ta ketowa
daga cikin ƙarƙashin ƙasa.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
37
Halittar ta nunka aljani Za'aratun-layal a girma, muni, da
kwarjini gami da cika idanu.
Ba wata ba ce wannan halitta ba face aljani Durusul-fannar,
Durusul-fannar ya faɗi ƙasa ya yi sujjada ga sarki zammar,
Zammar ya du be shi fuska a murtuke babu annuri, tamkar an
watsa mashi garwashin wuta kan ta.
Cikin kakkausar murya mai ban tsoro ya ce "ya kai
uban hatsabibai kuma kakan kangararru na duniya ka yi sani
cewa, fiye da shekaru dubu ɗaya da ɗoriya rabon da na kira
ka domin aiwatar da wani aiki sai yau, to ina so ka yi sani
cewa na kirowa ka ne domin ka bi sahun su 'yata Mashlira da
ta ci amana ta ta kuɓutar da waɗansu bil'adama da muka
farauto.
Ina so ka kawo min su a raye cikin ƙoshin lafiya domin ni
da kai na zanyi hukunci,
Koda sarki Zammar ya zo nan zancen shi, sai Durusul-fannar
ya sake yin sujjada karo na biyu ga sarki Zammar cikin wata
irin murya mai kama da saukar aradu ya ce "an gama ya
sarkin sarakai, yin biyayya a gare ka shi ne ibada ta".
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Durusul-fannar ya ya
yunƙura izuwa sama domin ya bi sahun su aljani Za'aratunlayal, take ya shiga keta gajimare cikin wani irin masifaffan
gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.
Wannan shi ne abin da ya faru a acan birnin muridai.
BABU NA BIYAR
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
38
Al'amarin su sarki Lazwar kuwa lokacin da suka ci gaba da
gudu a bisa kan aljani Za'aratun-layal, bayan gimbiya Mashlira
ta ceci rayuwar su daga hannun mahaifinta, sai suka ci gaba
da tafiya a sararin samaniya cikin hanzari.
Ana fara wannan tafiya ne sarki Lazwar ya matsa kusa da
Mashlira ya ce" ya ke wannan 'yar sarki ma'abociyar tausayi
da jin ƙai, haƙiƙa ba mu san da wane irin baki zamu gode miki
ba bisa ceton rayuwar mu da kika yi.
Sai dai abin da muka kasa fahimta ni da abokan tafiya ta shi
ne, mene ne dalilin da ya sanya kika biyo mu bayan cewa baki
san daga wata duniya muke ba, kuma baki san ina zamuje ba.
Ko da jin wannan batu sai Mashlira ta yi wani
ƙayataccen murmushi da ya kara tona asirin tsantsar kyawun
surar ta har fararen haƙoranta suka bayyana farare ƙal! Cikin
daddaɗar murya ta ce "ya kai wannan sarki ka yi sani cewa
kafin na fito daga cikin gidan sarautar birnin mu sai da na
gudanar da bincike bisa halarar tsafina, na gano dukkan
labarin ku da duk abin da ya baro da ku daga biranan ku, na
nemo abubuwan da su warkar da kai daga sihirin da abokin
gabar ka sarki Darwazu ya yi maka.
Bakomai ne ya sanya na biyo ku domin gudanar da
wannan tafiya ba, duk kuwa da irin haɗurran dake tattare da
ita sai domin mahaifina ya gano cewa nan gaba zan samu
ɗaukaka mai yawa wacce sai labari na ya yaɗu a duniya, bisa
binciken da na gudanar a yau na gano cewa ta silar ku zan
samu wannan ɗaukaka.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
39
Sannan kuma zan cika burina na samowa jama'ar birninmu
maganin da zai warkar da su, su dawo ainahin surar su ta
bil'adama. Da yake duk wannan tattaunawa da ake yi tsakanin
sarki Lazwar da Mashlira kowa yana saurare, ya yin da aka ji
abin da Mashlira ta furta sai kowa ya cika da matuƙar mamaki
da al'ajabi.
Sarki Lazwar ya dube ta cike da matuƙar mamaki ya ce "ya
sarauniyar kyawawa shin dama jama'ar birninku bil'adama ne
kamar mu ba muridai ba?
Ko da jin wannan tambaya sai idanun Mashlira suka
ciko da kwalla, fuskarta cike da matuƙar damuwa ta ce "Bbsa
labarin da mahaifina ya ba ni ya tabbatar min da hakan, kuma
ya sanar dani maganin da zai warkar da su daga wannan
annoba, akwai buƙatar na sanar da ku labarina a taƙaice.
BABI NA SHIDA
A wani zamani can baya mai tsawo da ya shuɗe lokacin da
jahilci ya yi katutu a zukatan bil'adama, ƙarfi da jarumtaka
suka zamto jari, kuma ake yin gashin dankali wato babba a
sama ƙarami a ƙasa
A wannan lokaci anyi wata nahiya mai ɗauke da
manyan birane guda biyar,
biranen na ƙarƙashin mulkin wani gawurtaccen azzalumin
matsafi da ake yiwa laƙabi da Sahibul-ukub
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
40
Matsafi Sahibul-ukub yakasance GWARZON DUNIYA mai
ƙarfi na Allah ya isa, domin an ce a filin yaƙi yana iya shafe
tsawon kwanaki biyu yana yaƙi ba tare da ya ci ko ya sha ba.
Idan ya je farauta daji kuwa yana iya saɓo giwa a
kafaɗarshi, ya yi gudun sa'a ɗaya da ita ba tare da ya gaji ba,
komai girman bishiya idan ya naushe ta da hannunshi sai ta
jijjigo har saiwarta sannan ta faɗi ƙasa,
Kai wasu lokutan ma idan zai kai farmaki wani birni ko alkarya,
shi kaɗai yake fita ya yaƙi birnin a dare ɗaya ya farauto bayi,
da dukiya mai da ganima mai tarin yawa.
Bisa wannan dalili ne ya sanya duk biranen da suka ji labarin
matsafi Sahibul-ukub zai kawo farmaki, ko da dai su fita su tafi
izuwa gare shi su yi MUBAYA'A kafin ya zo, ko kuma su
tattare ina-su-ina-su su fice daga birnin su yi hijira izuwa wata
nahiyar daban.
Batun ƙarfin sihirin tsafi kuwa, masu bincike da hasashe
sun tabbatar da cewa a halin yanzu babu matsafi kamarshi,
zaluncin shi kuwa ya huce yadda muke tsammani domin
saboda matuƙar zaluncin shi yasa aka gina mashi kurkukun
ƙarƙashin ƙasa da ake bautar da mutane da aljanu.
A rayuwar matsafi Sahibul-ukub bai taɓa yin aure ba
ballantana a ce yana da magaji da zai maye gurbin
karagarshi.
wata rana yana zaune a turakar shi sai kawai a ka ji
ya taƙarƙare ya ƙwala ihu sannan daga bisani ya bushe da
dariya mugunta, bakomai ne ya sanya matsafi sahibul-ukub
ihu da dariyar ba face wani labari da sarki yaƙin sa ya kawo
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
41
mashi, na wani ɓoyayyen birni mai tarin arzikin noma kiwo, da
ma'adanan ƙarƙashin kasa.
Birnin Madinatul-Adfal na yamma maso arewacin birnin
Sin.
Sarkin da ke mulkin birnin yakasance GWARZON
DUNIYA mai karfi na Allah ya isa, yana shugabantar jama'ar
shi bisa adalci da matuƙar tausaya wa, bisa wannan dalili ne
ya sanya kullum tattalin arzikin birnin yake ƙara haɓaka.
Wani abu da matsafi Sahibul-ukub ya gani bisa halarar
tsafinshi shi ne, matuƙar ya mallaki birnin zai zamo
mashahurin attajirin da babu kamarshi a faɗin duniya, kuma a
wannan birni zai gina fadar da take babu kamar ta a duniya
baki ɗaya.
Kasancewar birnin yana ɗauke da dukkanin wani yanayi
mai daɗi da bil'adama ke bukata.
Bayan Sahibul-ukub ya kammala dariyar mugunta, sai ya
juya ya dubi sarkin yaƙin da ke durƙushe a gaban shi tamkar
zai yi mashi sujjada, cikin wata irin kakkausar murya mai
tattare da taƙama gami da BAKAR IZZA ya ce ''ya kai dirkar
birnin Jauraful-harbat, haƙiƙa ba ka taɓa zuwa mii da labari
mai daɗi kamar wannan ba, Amma lamarin ɓoyayyen birnin ya
ba ni mamaki, da har na gasa gano shu bisa halarar tsafi na,
amma ba abin mamaki bane domin masu iya magana na
cewa shi ilimin tsafi kogi ne komai nutson ka ba za ka iya
ɗebe abin da ke cikin shi ba sai dai ka ɗebi iya gwargwadon
ka.
Yanzu abin da nake so shine a tanadar min dakarun yaƙi
guda dubu hamsin, tare da magina dubu goma da kuyangi
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
42
dubu, bayi da barori, a daren yau ina so alfijir ɗin a subahin
gobe ya keto min a birnin madinatul-Adfal, domin wannan yaƙi
na musamman ne a gare ni, ko da jin wannan batu sai sarkin
yaƙi Shamsal ya risina ga matsafi Sahibul-ukub ya ce "an
gama ya shugaba na".
Yana gama faɗin hakan sai kawai ya miƙe tsaye ya fice daga
turakar, domin aiwatar da umarnin da akayi mashi.
A can birnin Madinatul-Adfal kuwa jama'a na gudanar da
ayyukan su cikin lumana, masu saye da siyarwa na yi masu
noma da kiwo na yi, sauran yara kuwa na wasanni a tsakanin
su cikin nishaɗi, hakan kuwa ya faru ne sakamakon saukar
ruwan sama a daren jiya kamar da bakin ƙwarya ƙasa ta
kwanta kuma gari ya yi daɗi korayen tsirrai sunyi luɓ-luɓ
gwanin ban sha'awa,
A na cikin wannan hali ne sai ka ga gari ya yi duhu
dumɗum! Tamakar dare biyu ya haɗu waje guda, kai ka ce
hadari ne ya gangamo zaa ɓarke da da ruwan sama, nan fa
gari ya kaure da gujegujen jama'a gami da ifice-ifice yara da
manya mata da maza.
Ba wani abu ba ne ya haddasa wannan duhu ba face
bayyanar rundunar matsafi Sahibul-ukub da ta iso birnin
Sa'adda gimbiya Mashlira yar sarkin muridai Zammar ta
zo dai-dai nan a labarin ta sai ta yi shiru, bakomai ne yasanya
ta yi hakan ba, sai bisa ganin wata mummunar halitta da ta
bayyana a gaban su, ba wani ba ne wannan halitta ba face
aljani Durusul-fannar da mahaifinta ya turo domin ya farauto
su.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
43
Ko da bayyanar aljani Durusul-fannar sai cikin kowa
ya ɗuru ruwa, hatta shi kanshi aljani Za'aratun-layal da ya
kasance aljani.
Wannan fa shine masu iya magana ke cewa GABA DA
GABANTA wai aljani ya taka wuta, kafin ɗaya daga cikin su ya
yi wani yunƙuri aljani Durusul-fannar ya buda wata irin iska
daga bakinshi, nan take su sarki Lazwar suka kama barci mai
nauyi, kawai sai ya damƙe su ya makale su ajikin fukafukanshi tamkar ya ɗauko 'yan tsaki, ya juya izuwa hanyar da
za ta mayar da shi izuwa birnin muridai.
Tofa ana dara ga dare ya yi.
Lokacin da aljani Durusul-fannar ya tsala da azababban gudu,
ɗauke da su gimbiya Mashlira, sai ya ci gaba da keta gajimare
cikin gudun huce sa'a domin ya isa ga sarki Zammar,
yana cikin wannan gudu ne kwatsam! Bazato babu tsammani
sai ya yi kiciɓus da wani aljani agaban shi, Aljanin ya kasance
ma'abincin kyawun sura fari sol.
Zaune a bisa kanshi wani kyakkyawan yaro ne mai kimanin
shekaru goma sha shida, wanda da kaɗan ya ɗara yarinya
Shuraiba.
Yaron yana sanye cikin fararen tufafi tun daga ƙasa har sama,
a gadon bayanshi yana rataye da wata sharbebiyar takobi.
Kallo ɗaya zaka yiwa yaron ka tabbatar da cewa kyakkyawa
ne na gaban kwatance domin inda za'a ajiye shi daf da
gimbiya Mashlira ba za ka iya tantance wane ne yafi kyawu a
tsakanin su ba.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
44
Sa'adda Durusul-fannar ya yi arba da su yaji zuciyarshi ta
buga da ƙarfi tsoro ya ɗarsu a cikin ta.
A karo na farko a rayuwar shi ya ji wata halitta ta razana
shi, nan fa ya cika da matuƙar mamaki ainun.
Abu na farko da ya bashi mamaki shine duka aljanin bai kama
ƙafarshi a girman jiki da surar jarumtaka ba, kuma wanda ke
zaune a kanshi bil'adama ne yaro matashi.
Kawai sai ya yi ƙarfin hali ya dakawa masu tsawon cikin
matuƙar fushi ya dube su ya ce ''ya ku waɗannan ma'abota
GAJERAN KWANA shin wane rashin tunani ya sanya za ku
tare min hanya? Ba ku da labarin cewa nine GOBARAR
ANNOBA mai tada hankalin duniya, ANNOBA ƊARI mai
shayar da jarumai TASKAR AZABA?
Kafin aljani Durusul-fannar ya gama rufe bakinshi
kyakkyawan yaron ya tari numfashin sa yana mai cewa
''kaicon ka ya kai tsohon mushriki, ka yi sani cewa yau
ƙarshen ka ya zo, kai maza ka miƙo min su sarki Lazwar da ka
ɗauko su domin ka kaiwa sarki Zammar ya hallaka su.
Sannan kuma ina kira a gare ka ka bayar da gaskiya da
Ubangijin da ya halicci duniya da abin da ke cikin ta";
Ko da jin wannan batu sai zuciyar aljani Durusul-fannar
ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone ya sake dakawa yaron
tsawa a karo na biyu, tabbas yaro man kaza, bai san wuta ba
sai ta narka shi, kuma haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya
da suka, tsautsayin akuya gai da kura, rabon da wata halitta
da ɓata min rai yau shekara dubu hamsin, lallai daga kan ku
hakan ba zai sake faruwa ba, domin zan koyar da duniya
darasi akan ku".
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
45
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Durusul-fannar ya yi
ɗauki kan su yana ihu da kururuwa mai firgitarwa, tamkar zai
tashi duniya baki ɗaya,
Ko da ganin hakan sai kyakyawan yaron ya buɗe bakinshi
yana mai karanta waɗansu kalmomi, sannan ya zare
takobinshi a gadon bayanshi ya tunkari Durusul-fannar suka yi
KARON BATTA.
Kaico! Haƙiƙa KARON MAZA babu daɗi, kuma tashin hankali
ba a sa ka mai rana, nan fa aka ruguntsume da azababban
yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro gami da ban al'ajabi, nan fa
yazamana cewa, abin nan da masu iya magana ke faɗi ya fara
tabbata, wato ɗan hakin da ka raina shi ne ke tsoka ne maka
idanu.
Sai ga shi yaron ya zamto wa Durusul-fannar ƙadangaren
bakin tulu kuma alaƙaƙai,
Duka sa'adda da ya kai mashi duka da hannayenshi sai yaron
ya zille gami mayar da martani cikin zafin nama, idan
takobinshi ta taɓa jikin Durusu sai ka ji ya kurma wawan ihu.
Bakomai ne ya sanya shi ihun ba face tsananin zafi da raɗaɗin
da yake ji tamkar ana ƙona shi da wuta.
Abin da Durusul-fannar bai sani ba shi ne takobin yaron
na ɗauke da sirri na musamman, ana cikin wannan artabu ne
yaron ya kaiwa Durusul-fannar wawan sara a kafaɗarshi, cikin
sa'a ya yanke shi, take jikinshi ya kama da wuta, nan fa aljani
Durusul-fannar ya kama ihu da kururuwar neman taimako.
Indai ace mutum ya na tsaye a wannan waje yana kallon
abinda ke faruwa, dola ne ya yi wa Allah godiya bisa ganin
cewa mushriki maƙiyin Allah zai yi mutuwar wulakanci.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
46
Koda kyakyawan yaron ya fahimci cewa wutar zata iya
kona su sarki Lazwar da har yanzu su ke cikin halin barci.
Sai kawai ya ya yiwa hadimin shi umarni da ya kai masu
ɗauki.
Cikin zafin nama aljani ya miƙa hannayenshi biyu ya ɗauko
sarki Lazwar, Mashlira, shuraiba, aljani Za'aratun-layal, sarkin
yaƙi da bawa Shamsal, ya ajiye su bisa gadon bayanshi,
sannan ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luu!. Ya sauka a
turba a dai-dai lokacin da aljani Durusul-fannar ya ƙone
kurmus tokar gawarshi ta sheƙe cikin iska.
Ya yin da ya sauka a turba sai ya sauke su sarki Lazwar a
ƙasa.
Yaron ya koma gefe guda ya share ƙasa yana mai
fuskantar alƙibila ya fara gudanar da ibadar shi irin ta
ma'abota addinin Musulunci, kawai sai aljanin ya tsaya a
gefen shi a yana mai koyi da shi, Sarki Lazwar ne ya fara
farkawa daga barcin, sannan gimbiya Mashlira, bawa
Shamsal, sarkin yaƙi, yarinya Shuraiba aljani Za'aratun-layal a
ƙarshe.
Lokacin da kowa ya wartsake ya dawo cikin hayyacin shi,
suka arba da wannan kyakkyawan yaro da hadimin shi suna
gudanar da Sallah,
sai kowa ya yi turus! Cike da matuƙar mamaki gami da
al'ajabi.
Abu na farko daya bawa ko mamaki shi ne yadda yaron ke
gudanar da ibadar cikin tsafta da tsari mai ban sha'awa,
sannan ya aka yi su ka tsira da rayuwar su? Kuma ina aljani
Durusul-fannar ya ke?
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
47
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kan su kenen,
kawai sai suka zuba idanu suna kallo, har ya kammala ibadar
sannan ya juya ya fuskanci su sarki Lazwar ya ce "ya ku
waɗannan mutane ku yi sani cewa ban ceto rayuwar ku domin
ku saka min da wani abuba, face kawai saboda Ubangiji na ya
bayyana mini ku a cikin mafarki na. Kuma ta silar ku ne zan
samu nasarar gano 'yar uwata da ta ɓace, kimanin shekaru
bakwai.
Bisa wannan dalili ne ya sanya na ce ci rayuwar ku bisa
taimakon Ubangijina, duk da cewa ta mai bautar Allah
maɗaukakin sarki, ku kuma kun kasance kuna bauta wa
gumaka".
Sa'adda su ka ji wannan batu daga bakin yaron sai
kowa ya sake cika da matuƙar mamaki da al'ajabi.
Ita kuwa yarinya Shuraiba sai ta ƙura wa yaron idanu, gami
da yi mashi wani irin kallo da ita kan ta bata san dalilin yin shi
ba, tana mai cewa a ranta.
Shin wai dama akwai wani Ubangiji da ya halicci mutane
bayan allolin mu?
Amma addinin wannan yaro yana tattare da tsafta da
kayatarwa,
Nan take ta ji tana matuƙar ƙaunar yaron a cikin ranta tamkar
ta daɗe da shaƙuwa da shi.
Sarki Lazwar ya buɗi baki ya ce ''ya kai wannan yaro mai ban
al'ajabi shin mene ne sunan ka da labarin ka?
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai yaron ya yi murmushi
da ya ƙara wa fuskarshi kyawu ya ce "Ni suna na Imran ibn
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
48
Nadir na fito daga ƙasar Yemen ne neman 'yar uwata wacce
na rasa ta sakamakon farmakin bazato da aka kawo birninmu,
ita ce kaɗai ta rage mini a cikin jinina, sannan babban burina
shine kuma na yaɗa addini na gaskiya a doran ƙasa, game da
tambayar ka kuwa mene ne labari na wannan hikaya ce mai
tsawo yanzu babu lokacin yin shi sai dai a nan gaba".
Ko da jin amsar wannan tambaya sai sarki Lazwar ya
juya ya dubi sarkin yaƙin shi yana mai yi mashi raɗa a kunne
ya ce "ya dirkar birnina shin yanzu kana ganin zamu amince
da yaro Imran mu yi wannan tafiya tare da shi alhalin ya
kasance mabiyin addinin Musulunci, kuma sanin kanka ne
cewa iyayenmu da kakanninmu mun mutu ne bisa ƙiyayyar
wannan addini.
Sannan ka san babu yadda za'a yi sirrikan tsafi na su yi
tasiri a wannan tafiya matsawar yaro Imran zai karanta abin
da ya shafi addinin su,
Abu ɗaya ma da nake tsoro ya kasance shi ne a koda yaushe
zan iya rasa sirrikan tsafi na.
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai sarkin
yaƙi kara bakinshi dai-dai kunnen sarki cikin ladabi ya ce "ya
shugabana tabbatas zancen ka dutse ne, sai dai wani hanzari
ba gudu ba, baka ganin cewa dukkanin abokan tafiyar mu sun
faɗa tarko da yawa amma sirrikan tsafin ka ba su tseratar
damu ba. Yanzu da wannan yaro bai ceci rayuwar mu ba da
yanzu kuma wani labarin ake yi daban ba wannan ba.
Ni dai shawara ta shine ka ga dai Imran yaro ne ƙarami
babu ta yadda za ayi ya canja tunanin ɗayan mu mu shiga
addinin shi, kawai zamu yi amfani da shi ne, domin cimma
buƙatar mu daga baya sai mu yi watsi da shi".
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
49
Da jin wannan shawara ta sarkin yaƙi sai sarki Lazwar
ya bushe da 'yar karamar dariyar mugunta ya dafa kafaɗunshi
ya ce "an gaishe ka namijin duniya shi yasa dai-dai da sa'a
ɗaya bana son a ce na rabu da kai saboda irin wannan
al'amari,
Ko da gama wannan shawara sai sarki Lazwar ya dubi yaro
Imran ya ce "ya kai wannan Imran ma'abocin taimako haƙiƙa
mun amince mu yi wannan tafiya tare, sai dai bisa sharaɗi
guda, sharaɗin kuwa shi ne iya tsawon wannan tafiya da zamu
yi har ka sadu da 'yar uwarka, ba za ka tilasta ɗayan mu cewa
sai ya yi imani da Ubangijin ka ba";
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai yaro
Imran ya yi lallausar murmushi a gare su ya ce "ka kwantar da
hankalin ka ya kai wannan sarki mai daraja ai addini ba a
tilasta mutum ya shige shi face idan ya yi niyya da kan shi,
Da jin wannan batu daga bakin Imran sai kowa ya gyɗa kai
alamar gamsuwa, yaro Imran ya mayar da duban shi zuwa ga
aljanin shi ya ce "ya kai Hadimul-khair ina mai umartar ka ka
shiga izuwa cikin wannan daji ka samo mana abin da zamu yi
kalaci gami da ruwan sha.
Aljani Hadimul-khair ya risina ga yaro Imran ya ce "an
gama ya shugaba na. Yana gama faɗin hakan ya kaɗa fukafukanshi ya nausa izuwa cikin dajin,
Jim kaɗan bayan shuɗewar waɗansu 'yan daƙiƙu sai Hadimulkhair ya dawo ɗauke da waɗansu nunannnun kayan marmari
da suka haɗar da tuffa, gwanda, ayaba, lemu gami da ibini.
Ya ajiye a gaban Imran,shi kuma Imran ya yi umari kowa ya
ɗebi wanda zai ishe shi, sannan kowa ya shiga kimtsa
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
50
cikinshi, ita kuwa damisar yarinya Shuraiba sai ta kama kiwon
a wajen tana kama kwari da kananan dabba tana lamushe su.
Bayan an kammala ne
an samu nutsuwa sai aka
ɗunguma a ka ci-gaba da tafiya, inda aljani Za'aratun-layal ya
ɗauki sarki Lazwar, sarkin yaƙi, bawa Shamsal da gimbiya
Mashlira, amma sai yarinya Shuraiba ta ki yarda ta hau kan
shi, inda ta nemi alfarma a wajen naaro Imran da ya amince
mata ta hau bisa kan aljanin sa tare damisa Faizur.
Al'amarin da ya yi matuƙar fusata sarki Lazwar kenan ya
buɗe baki da nufin ya hana yarinya Shuraiba hawa kan aljani
Hadimul-khair, amma sai sarkin yaƙi ya dakatar da shi yana
mai yi masa raɗa a kunne ya ce "haba ya shugabana kar ka
manta cewa Shuraiba tana da matuƙar muhimmanci a wannan
tafiya tamu, domin ita ce ta san sirrin birnin Istanbul dama shi
kanshi sarkin birnin, kar tun yanzu ka ɓata kiɗan da rawa, har
Shuraiba ta fahimci cewa kana ɓoye mata wani abu game da
yaro Imran har ta yi ƙoƙarin shaƙuwa da shi ta fahimci addinin
shi.
Idan kuwa har hakan ta faru to kuwa zamu rasa su baki ɗaya
wato Imran da Shuraiba.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi sai jikin
sarki Lazwar ya yi sanyi ya koma ya zauna aka cigaba da
tafiya.
BABI NA BAKWAI
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
51
A can birnin Zawatul-ifdar kuwa, jama'a kuwa sun fara
yabawa aya zaƙin ta, domin magajin gari Yasiran yana yi
masu MULKIN ZALUNCI da ya zarce na sarki lazwar.
Domin ɗan ƙankanin laifi mutum zai aikata sai a yanke mashi
hukuncin kisa ko zaman gidan kaso, yiwa 'ya'ya mata fyaɗe,
ƙwace gami da fashi da makami ya yawaita a birnin Zawatulifdar.
Duk wanda ya yi sabon aure to ba zai tare da matarshi
face an kai ta ga magajin gari Yasiran ya tara da ita sannan
zai karɓi amaryar shi kashe gari.
Yan kasuwa aka matsa masu da karɓar haraji, nan fa ya
zamana cewa hatta 'yan majalisar birnin sun fara ƙosawa da
mulkin zaluncin Yasiran, suka shiga tunanin hanyar da za su
kawar da shi daga kan karagar mulki, duk da cewar a halin
yanzu sun fi matuƙar tsoron shi fiye da sarki Lazwar.
Wata rana da hantsi lokacin zaman fada an cika maƙil da
jama'a babu masaka tsinke, duk inda mutum ya duba
kawunan bil'adama ne rututu tamakar dandazon kiyasai, ana
jiran fitowar magajin gari Yasiran.
Ana cikin wannan hali kwatsam! Bazato babu tsammani sai
aka ji fadar ta kaure da wata irin mahaukaciyar dariya mai ban
tsoro, daga can sai aka ga Yasiran ya bayyana tsulum! A
fadar tamkar an jefo shi daga sama, hannunshi na dama riƙe
da wata sharɓeɓiyar takobi, na hagun kuwa riƙe da wani
mashi an tsire kan wani mutum a jikin shi jini na zuba.
Sa'adda jama'a su kayi arba da kan, sai suka ɗimauce 'yan
majalisa kuwa sai jikkunansu suka kama ƙyarma saboda
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
52
matuƙar tsoro, ba komai ne sanya su ƙyarma face bisa arna
da kan sarkin fada, wato ɗaya daga cikin yan majalisar
magajin gari Yasiran ya ɗaga hannunshi sama fadar tayi tsit!
Tamkar mutuwa ta kawo ziyara.
Fuskarshi a murtke ya ce "ya ku al'ummar wannan fada
mai albarka ku yi sani cewa, wannan shi ne darasi ga duk
wanda baya goyan bayan mulki na a wannan birnin".
Yana gama faɗin hakan sai ya yi jifa da kan sarkin fada a kas,
cikin hanzari wani badakare ya shigo fadar janye da hannun
wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa, tana ta rusa kuka sai ya
iso da ita daf da ida karagar mulki take sannan ya risina ya
zube ƙasa ya kwashi gaisuwa.
Sannan ya buɗi baki cikin ladabi ya ce "ga ta nan na zo
da ita ya shugabana";
Yasiran ya dube shi ya ce "sai ayi hanzari akai min ita
turakata".
Badakaren ya miƙe tsaye ya fice da budurwar wacce ke rusa
kuka tana magiyar a rabu da ita, komai rashin imanin mutum
idan ya ga halin da budurwar ke ciki, dole ne ya zubar mata da
hawaye saboda matuƙar tausayi, da yawa daga mutanen
fadar sai da su ka zubar da ƙwalla sabo da matuƙar tausayin
budurwar.
Wannan shi ne abin da ya faru a can birnin Zawatulifdar