Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
musu kallo sama da kasa. Sannan tace "Or sorry! Dama ku ne kuka tafi makaranta? Ta nuna Nusaiba da tafi ganin damanta, tace "Ke ce Naziyatu? Nusaiba ta girgiza mata kai, ta nuna mata Naziyatu da hannunta. Murja tace "O.k, ke ce Nusaiba kenan? Nusaiba ta kuma daga mata kanta, ba tare da ta bude baki tayi mata magana ba, dan ita Nusaiba a rayuwarta, bata kaunar wulakanci da rainin wayo. Ta kuma fuskanci Murja mai irin halayen ne. Murja tace "To ya kuke? Sannunku fa student." Ta kwalawa Lanti kira. Sai gata ta shigo da sauri. Murja tace "Lanti ki samowa wadannan yaran abin da za su ci. DA SANNU... 93 Duk da dai ba baki bane." Ta jawo wani fingilallen gyale da bai wuce nayi dan kwali da shi ba fari kal! Da shi kamar takarda, tace "Lanti, in nawan ya dawo. Ki fada masa na tafi bakin Asibiti. Na kira Mama mu yi magana. Ni Wallahi wannan bala'in ya fara isata. Mai ake yi da zaman kauye, in ba kaddara ba, ace kana son yin zumunci da 'yan-uwanka. Sai ka fita ka je wai wani bakin Asibiti. Ina amfani haka?Wannan kaddaran tayi yawa. Bari nawan ya dawo. Ni fa kauyen nan ya isheni. Me ake da zaman kauye? Sai lalura. Ni kam na gaji." Naziyatu ta tunzura tace "Ke tsaya fa ki ji. Rainin arzikin naki da walukancinki ya tsaya haka nan. Ya isheki. Na tabbatar da kike wannan kumfar bakin, na san gidan ubanki da yake birni, bai kai gidan ubana da yake kauye ba. Kuma ke ba ki isa ki raina kauye ba, dan nan ne mafarin tsoho da tsohuwa. Dan haka ahir dinki, kada ki kuma neman raina mana kauye. Dan kauye ba abin rainawa bane, ga mai hankali da tunani da asali." Ta nunata da dan yatsa, kamar zata tsole mata ido, tace. "This is the last warning! Sannan ta kamo hannun Nusaiba ta jata suka fita. Ni kaina yau masifar Naziyatu ta birgeni, dan na kan so wanda ke son asalin shi. Na kan kuma so, wanda ke gudun wulakanci da raini arziki. Ba ka zamo saboda abin duniya. Wani ya maidaka wulakantacce ba, ya kuma raina maka arzikin da Allah ya ba ka ba. Ina amfanin irin MAMAN FADILA 94 wannan masu mataccen zuciya? Wanda muddin ba su yi yaki da zuciyarsu ba. To sai dai su mutu a wulakanci. Allah ya ganad da masu irin wannan dabi'u, su guji son abin duniyar da bana su ba, na wani can, don su ke kaimu ga wulakanta da tozarta, har a raina maka naka arzikin da Allah ya ba ka. Dan ko wane bawa da arzikin da Allah yayi ma shi. Ta bangarori da dama. Rashin hakurinmu ne na 'Yan-Adam da har sai mun kai ga inda ake wulakantamu. To Allah ya ba mu ikon tsayawa a matsayin da Allah ya aje mu. DA SANNU... Ba abin mamaki bane wata ran Allah ya kaika ga wani matsayi da mafarkinka da tunaninka. Bai taba raya maka za ka taka wannan matsayin ba. To amma ma sai ka bi da sannu. Babu yadda Allah baya ikonsa. Ya mayar da talaka gawurtaccen mai kudi. Ya kuma mayar da mai-kudi gawurtacen talaka. Tafiyarsu Naziyatu. Lanti ta dunga ba Murja hakuri "Ki yi hakuri, haka halin Naziyatu yake. Babu wanda take ragawa, sai iyayenta da mijinki a cikin gidan nan, ki daina kulata. In ba haka ba rashin kunya zata dunga yi miki." Murja tace "Amma kuwa yarinyar nan zata gane kuranta, za ta raina wayonta."Wayar da dai Murja bata je ta kira ba kenan, tayi jifa da wayarta. Ta shiga rera sabon kuka. Taf! Aiki ko ya sameki. Ni ban iya wannan kissan namu na mata ba. Sai na nufi sasan Hakimi, dan na ga me suke. To ina shiga, na ga Hajiya Safiya. DA SANNU... 95 Tana tafa hannu, tana sallalami "Yanzu Naziyatu zagerancin naki ya kai ki ki je har dakin matar kanin Babanku ki yi sa insa da zuwanki. To zan kuwa bata miki rai ke ma." Nusaiba tace "Hajiya ba fa laifin Naziyatu bane, wai kin ga yadda matar nan ta ke neman raina mana arziki ne. Wallahi ni kaina kiris ya rage in ragargajeta, ke dai kawai Hajiya hakuri za ki yi. Wannan ta faru. Kowa ya kama kansa." Hajiya S afiya tace "To na ji, kada na kuskura na sake jin makamancin haka. Komai ya wuce. Allah ya kyauta gaba." Murja tana daki, ko abinci ta kasa ci, sai aikin kukan kissa da tasa kanta. Magaji ya shigo, ya ci karo da Gaje Zaune a falo. Abin ya so ya ba shi mamaki. Sai bai kula ba. Ya wuce abin shi dakin Murja, yadda ya ganta ya sosa masa rai sosai. Ya je kusa da ita, ya kamata. Yayi lallashin Juniya ta fada masa kome aka yi mata? Amma ta ki yin magana. Sai kawai ya kwalawa Gaje kira "Ke Habiba zo nan." Tayi sallama ta shigo, tace "Sannu, gani." Daga idon da Murja tayi, ta ga irin shigar kwalliyar da tayi, shi ya bata mata rai. Magaji yace ma Gaje "Ke Habiba me ya samu Bebi? Naa Gaje tace "Ni ma ban san abin da ya sameta ba." Da sauri Murja tace "Munafuka, ba ki sani ba kika ce? To uban wa ya turosu, su zo su zazzaga min tsiya." Magaji yace "Su waye suka zo, har daki suka zageki? Murja tace "Su Naziyatu, duka ma suka so su yi MAMAN FADILA 96 min. Lanti ce ta taimaka min. Ba su dakeni ba." Ai da gudu ya fita, ya nufi cikin gida. Naziyatu da Nusaiba suna cin abinci. Suka mike zumbur za su gudu daki. Hajiya Safiya da ke zaune bakin kofar, ta kare, tace "Ina za ku? Sai kun yi ma shi bayani. Babu inda za ku gudu." Magaji ya fallawa Naziyatu mari. Ya kuma daga hannu ya faliawa Nusaiba. Sannan yace "Gaba dayanku, ku ba ku da hankali ko? Hajiya kin san kuwa abinda yaran nan suka yi wa Murja? Suka je zasu daketa. Lanti fa ta hanasu, suna biyewa 'yar kauyen yarinyar nan da bata da hankali. Murja fa ciki ke gareta. Amma kuke kokarin tada mata da hankali. To Wallahi ku bi ta a hankali, kada na kuma samun kun bata mata rai. Dan juna biyu ke gareta." Hajiya Safiya tace "Asibiti kuka je aka fada muku ciki gareta? Magaji yace "A'a ita da kanta ta fada min, wai tana jin kasala, tana kuma yin amai, kuma bata ga batan watanta ba." Hajiya Safiya ta kada kai, tace "Allah ya rabasu lafiya. Ita kuma Gaje fa? Magaji yace "Ita ban yi tsammanin tana da ciki ba." Hajiya Safiya tace "Uhm! To ita ma Allah ya bata." Magaji yace "Amin." Ya nuna su Nusaiba da hannun shi, yayi kawai yace musu "Next time, kada kuka kara." Ya fita da hanzari. Naziyatu tace "Wallahi ga dukkan alamu, maganan Baba Magaji suna cutar gidanku da rowa." Hajiya Safiya tace "Ni ma na ga DA SANNU... 97 5 alaman haka. Amm ku bari zan tambayi Lanti tayi min hayani." Nusaiba tace "Wallahi in har haka ne kafin mu koma makaranta, ita ma Gaje sai ta ba su mamaki." Ita rayuwa ba a mata garaje, komi ka bi a hankali, ka bi shi DA SANNU... Sai ka ga ka kai ga samun duk abinda kake so, kake kuma nema. Murja dai ta gaza sukuni. Ita dole haihuwa take so. Ita ce koyaushe zaryan asibiti kullum yi ma miji karyan ciki. Kuma cikin ya ki samuwa. Ita ce wankin ciki, shan kwayoyi. Ba miji kai a ko wane lokaci, babu hutu. Sai ka ce agogo. Tun Magaji yana zillewa, harya gaji, ya saba, ya fara zame masa jiki. Kamar in fada mata dama ta saukaka musu yin wannan baya kawo saurin daukar ciki, shi ciki DA SANNU... In lokacinsa yayi, to ko akan hanya a tsaye cikin sauri. Ba ma a cikin daki ko kan gado, ko katifa ba. In Allah yayi, lokacin shigar ciki yayi, sai ya shiga. Don haka Murja a jira lokaci. Duk wani gaggawarki ba inda zai kaiki. tunda Hajiya Safiya ta nemi Lanti. Ta kuma gaya mata abinda ta sani. Sai ta samu Gaje tace ta gaya mata gaskiyar lamari. Hatta kuwa shekara dayan data karawa Murja duk sai da ta zayyane mata komai. Ai koda Hajiya Safiya ta ji wannan batu, sai ta ja bakinta tayi shiru. Domin muddin Hakimi ya ji wannan magana. To hatta ita kanta komai zai ruguje mata. Don kullum MAMAN FADILA 98 maganar Hakimi bata wuce cewa ta rika sanya idanu akan zamansu Gaje. Ta tabbatar da cewa dukkansu Magaji bai taka hakkin kowa a cikinsu. Ai babu shiri. Hajiya Safiya ta shiga koyar da Gaje yadda ake zama da miji. Da kuma kishiya. Ta san yadda ake zama da ita. Ta dalilin littafin tauraruwarta A'isha A Tanimu. Mai suna KIRSOSHIN ZAMA DA MIUI DA KISHIYA Lokacin da Hajiya Safiya ta kaiwa tauraruwar tata, Ta tarar ta gama rubutawa. Amma ba a kai ga bugawa ba. Saboda muhimmancin littafin Hajiya Safiya ta gaza hakuri, ta bari a fitar da shi ta dunga magiya akan a taimaka mata ta je da littafin gidanta, ta duba. Sai ta aiko da shi. Abinka da ba karaman mace ha. Akalla ta haifi A'isha. Dole ta cika mata ido ba tare da ran ta yaso ba, ta dauka ta bata, dan bata da nayi. Dan bata haka wani ya karanta mata littafi, ba tare da ta fitar da shi kasuwa ba. Amma tace (Next time) ko Kakanta ce. Ba haihuwarta tayi ba. Ta daina yarda da wannan cika idon. Tunda ga shi har yanzun Hajiya Safiya ta kasa maido mata littafin. Sai fito da wasu sababbi kawai take. Shi ko kirsoshin zama da miji da kishiya. Shiru, wata kila sai A'isha ta je da kanta. Kila ta dawo da abin ta. To dalilin wannan littafi. Gaje yanzun ta sake. Kyar take kallon kowa. Bata da matsala, in dai na iya zama da miji da kishiya ne. Sai dai bata fara aiki da su ba tukuna. Saboda 'yan zamani sun Naziyatu basu gama nasu shirin ba, dan suna ta koyar DA SANNU... 99 da Gaje tsaftar jikinta, iya sa kaya, koya mata girke girken zamani kala-kala. Sannan kuma da koyar da ita hausan nan dai ta fara ganewa. Amma ban da turanci, dan basu da isashen lokaci, saboda lokacin komawarsu makaranta ya karato. Shi kuma turanci, dan son natsuwa ne sosai da isashen lokaci, dan yaren da ba naka ba ne, za ka ara. Cikin ikon Allah, duk abin da su Nusaiba suka koyawa Gaje tana fahimta sosai. Ranan da su Nusaiba da Naziyatu suka koma makaranta. Ranan Gaje ta fara aiki da kirsoshin da Hajiya Safiya ta karanto mata kuma ta fara aiki da koyin 'yan zamani, su Naziyatu. To fa daman 'Ya mace, in har namiji ya nemi juya mata baya. To bata iya kirsa bane da takunta. Ta tsaya sanya ne. Magaji fa ya fara kwadayin matar shi. To amma kuma Murja bata kula ba, dan ita ba wannan bane a gabanta ba. Ita haihuwa ne a gabanta, dan ta kosa ta ga ta zama Magaji. Shi ma ya zama ita. Dan ga alamu, dangin Magaji in har bata haihu da Magaji ba, ta tabbatar ba za ta iya cimma nasaran akan Magaji da 'Yan-uwan shi ba, dan haka yanzun Murja ba wai ta tsaya ga asibiti bane. Hatta magungunan gargajiya. Ita ce jika wannan, ta sha, kwaba wancan, ki sa kafin miji ya sadu da ita. To a haka Mommy mahaiiyarta ta samu wani tsohon Malami da aka yi mata kwatancen shi aka ce su je tare ita da Murja, dan haka Murka tayi wa Magaji karyan an yi musu rasuwa. MAMAN FADILA 100 Na dangin Mamanta a wani kauye. Sai sun kwana biyu zasu dawo. Magaji ya amince mata. Sun tafi. Allah Sarki! Dama Magaji tuntuni yake kwadayin son mata shi Gaje. Ya rasa yadda zai yi ya bullowa lamarin. saba irin takun da Murja ke ma shi. Sai ga shi tayi tafiya, ta bar shi. Magaji ya sakarwa Gaje jikin shi sosai. To amma kuma yayi dauriya, dan ya kasa kusantar Gaje. Har kwana biyun da Murja ta dauka yayi. Shiru babu Murja, bata dawo ba. Ranan kwana na uku. Magaji ya kasa hakuri, saboda Murja tayi masa koyi, ko wane lokaci cikin harkan gamsar da junansu suke. Ya shiga har cikin (Bed room) din Gaje. Abin ya ba shi mamaki, bai yi zaton samun dakin Gaje irin haka ba. Duk abinda Magaji zai yi da Gaje, tunda ya aureta, sai dai ya tsaya tsakiyar falo su yi. Bai taba shiga (Bedroom) dinta ba. Misalin karfe goma sha daya da rabi na dare. Ya shiga dakin Gaje. Amma abin mamaki, sai ya samu tanа sallah. Nan ma yayi mamaki. Ya kura mata ido tana jan tasbaha. Sai yayi mata murmushi. Shi ma ya shige (Birt room) din dakinta, yayo alwala ya fara nafila. Kafin ya fara nafilan, yace "Habiba ina son cikin addu'ar da kike yi, ki sa mu ciki." Gaje ta gama nafila, ta mike ta bude durowa, ta dauko wasu sababbin kayan barci da Hajiya Safiya ta sayo mata da su ka je Saudiya. Tana faman sa kayan barcin. DA SANNU.... 101 Ta kalli kanta a madubi. Sai tayi sauri ta kara daurawa akan kayan barcin da tasa. Sai kawai ta ji Magaji ya fisge zanin da karfi, yace "Daura zanin nana gareki yanzu, babu amfani, dan daren yau ne nake son ya zamana mana darenmu, na farko ni dake." Gaje cikin koyin maganan tsofaffiin hannu irin Hajiya Safiya, tace ma shi "Kada ka manta, ni na kara maka kwana daidai har kwana 365. Ko ka manta ne? Magaji ya rufe ido, yayi dariya, sannan ya bude, yace "Ban manta ba, amma wannan ku ta shafa. Ni ban amince ba." Gaje tace "To mai yasa da ka amince? Magaji ya girgiza kai. yayi dariya har da kyakyatawa. Abin da Magaji bai taba yi a gabanta ba. Sai dai taji shi yana yi a wani waje. Yau ga shi a gabanta yana mata. Ita ma sai ta shiga yin dariya, saboda irin birgeta da sha'awa da ya bata. To ni dai daga dariyar nan, sai kawai na ga suu dare. Sauran bayani na bar wa mai karatu. Dan ni abin ya sha kaina. Ni dai da safe. Na lura da Gaje dingisawa take. Lallai Gaje na san ta ji jiki. Kuma yadda na ga Magaji yana haba-haba da Gaje, baya kaunar ko kuda ya rabu da ita. Na san ba karamin ni'ima Magaji ya samu ba wajen Gaje. Magaji gaba daya ya manta da Murja. Da namiji kenan! Koyausheyana manne da Gaje, ko sasan Hakimi ya hanata zuwa. Hajiya Safiya bata damu ba, dan Lanti ta tsegunta mata komi. Murja bata dawo ha. Sai da ta samu kwana bakwai, sannan ta dawo. Ti-ki-Sa! Boka ya basu MAMAN FADILA 102 magunguna kala-kala. Boka ya fada mata da zaran ta gama amfani da magungunan, to za ta samu ciki. Sun kuma yi alkawari da Bokan. Da zaran ta samu ciki, zata dawo. Kuma ya bata taimako akan kishiyar ta Gaje. Ya mayar da ita nakasashiya da rabata da Magaji. Sam kada su taba jituwa. Dan ta ga alaman Magaji kamar ya fara son matar shi. Da sharadin da Boka ya bata, na wannan maganin da ya bata, cewa in har ta san Magaji ya yana saduwa da Gaje. To kada tayi amfani da maganin, dan reshe zai juye da mujiya. Saboda maganin amarai ake yiwa. A rabasu da mijinsu. Sai ka ga ango yayi sabon amarya. Da zaran ya shiga gonar shi sau daya. Ya fito. To fa ya fito kenan, shi da amarya, sai tsana, har sai sun rabu, zai samu kwanciyar hankali. Koda Murja ta dawo ta ga rawan kafar da Magaji yake yi. Sai ta yake wa, ko ya kula Gaje, bata damuwa, dan tana ganin nesa ta zo kusa. Kafin dare yayi, duk Murja ta gama sarrafa maganin a jikinta, kamar yadda Boka ya bata umarni. Dare na yi, ta matsawa Magaji suka shige daki. Suka fara sarrafa junansu, yadda suka saba. To amma fa yau sam bai ji dadin yadda auratayya tasu ta kasance ba. Amma bai san ko menene dalili ba. To Murja ta gama shirinta, dan haka wai ita zata yaudari Magaji da Boka ya fada mata, duk yadda zata yi, bayan ya sadu da ita. Cikin hadin maganin da tayi wa jikinta, to ta tabbatar kada ta kuma yarda da shỉ, har sai ya sadu da Gaje tukuna. DA SANNU... 103 Sannan kuma asirin zai ci Gaje, dan haka Murja ta fara magana cikin shagwaba "Ni dai gaskiya shekara dayan nan ta isheni. Don haka gobe dakin matarka, wancan yarinyar za ka kwana. Ka bata hakkinta na aure, ka bar tausaya mata kamar yadda kake fadi. Kada mu zama masu tauye mata hakki. Allah ya kamamu da laifinta." Magaji murmushi yayi, yace "Bebi-na ayi haka kuwa? Kin fa sanni jarumi ne. Yarinyar can zata iya min kuwa? Murja ta kashe ido, tace "Haba nawan, kada wannan ya dameka.Yanzu ake kai yara gidan miji, ba su fi shekara sha biyu ba, wani a shekaran ka gansu da goyonsu a baya, ballantana ko da kallon Gaje, in bata kai shekara ashirin ba. To ba kuma zata yi kasa da shekara sha tara ba, dan haka ban jin komi, ni dai nace ka je kawai." Allah Sarki! Murja da kin san abin da ke tsakanin Gaje da Magaji da ba ki yi tunanin tura shi wajenta ba, dan yanzu batun da suke. Gaje na da shigan ciki. Ti-ki-Sa! Wannan fa shine da gamo da kasawa. Wannan ciki shine DA SANNU... Gaje ta sha mamaki da ta ga Magaji ya kwana daya dakin Murja ya dawo mata. Sam bata yi tunanin zai saurin dawo mata ba, sannan abin da ya daurewa Gaje kai, shine yadda suka farantawa junansu rai da gamsar da kansu, ya fi darensu na farko. Shi kansa Magaji abin ya gigita shi. Koda gari ya waye. Magaji ya fita ya shiga dakin Murja. Suna yin ido hudu. Ya ji gaba daya duniyar baya MAMAN FADILA 104 fhi kaunar ya sake ganin Murja. Ai da gudu ya juya da baya, ya koma dakin Gaje. Yana shiga, kamar hadin baki, ita ma suka yi ido hudu. Sai ya ji wani annashuwa da farin ciki. Ya karasa gareta ya rungumeta, yana jin dadi. Tun daga wannan rana. Ruruwan so da kaunar Gaje ya dauwama cikin bargon jikin Magaji. Ita kuma Murja ruruwan rashin son-ta da kaunarta ya tabbata cikin bargon Magaji. Ranan girkinta, sai dai ya kulleta cikin (Bedroom) dinta. Shi kuma ya kwana a falo. Sai ya gama abin da yake. Da safe. Sannan in zai fita. Ya budeta. Cikin wannan halin, su Naziyatu suka dawo. Don sun gama zana jarabawan-(J. S3) dinsu. Shi kuma Auwalu shi ma ya gama (S.S.3). Dukyanzún suna gida. Gaje cikinta sai bunkasa yake, yana gwadawa duniya kansa. Kowa a gidan nan, Gaje yake so. Uban gaiyar kuwa cikin nan kamar ya dawo da shi jikin shi. Auwalu ya shigo yana fadin "Gaje yunwa nake ji." Magaji yana matsawa Gaje kafa da ta kumbura, yace "Kai Auwalu, kada na kuma jin ka kira Habiba, ka ce Gaje. Daga yau dukkanku, ka fadawa sauran nace Anti Habiba za ku dunga kiranta." Gaje tace "Kira min Lanti, ta ba ka abinci." Auwalu bai cika cin abincin cikin gida ba.Ya fi cin na su Gaje. To tunda Murja ta ga yadda abin ya koma. ta san an samu kuskure. Ta kuma san cewa lokacin da tayi tafiya, lokacin Magaji ya san matar shi. Dan haka ta kuma shiri, ta koma wajen Boka. DA SANNU.. 105 Abin da Boka ya fada mata. Asiri ba zai karye ba, har sai ta koma ta jira ranan da Gaje ta haihu. Ta dibo masa jinin haihuwar Gaje, ta kawo ma shi. Ya kuma sadu da ita, shine zai iya karya asirin. Ta dubi yanayin Bokan da wai zal kwanta da ita. Kuma ya zama mata dole ta yarda da shi din, in har zata samu Magajinta ya dawo gareta. Murja ta kema gida, tana jiran haihuwar Gaje. Ta dibi jinin. Murja yaazu bata da katabus a wurin kowa a gidan. Gaje ce kawal he tallafawa Murja. Sam Gaje bata yarda ta wulakanta Murja ba, dan yanzu Murja lallaba Gaje take. Don ta cinma burinta. Kwatsam! Ashe ita Murja ranan da ta sha wankan magunguna. Cili ya shiga. Yana ta karakaina, ya rasa tudun dafawa. in ya shiga nan, ya shiga can. An wayi gari Murja bata san wanda ke kanta ba. Kafin Gaje tayi wani abu. Murja ta suma. Ga shi ta yhwa Magaji magana ya zo su je asibiti. Amma ya i sauraranta. Da gudunta ta shiga sasan Hakimi, tana kuka, tana fada musu halin da Murja ke ciki. Hajiya Saflya ce kawai ta rude, ta shiga dakin Hakimi. Su ke Ya'yan gidan, ko a jikinsu. Sai ma suka dunga yiwa Gaje surutu. "Su Anti masu tausayi. Anti Habiba. Allah ya bar mana ke, tare da Baba Magaji.” Hakimi ne ya fito tare da Hajiya Saflya.Va daka masu tsawa, "Kanku guda kuwa? Kai Auwalu, ka dauhi makullin mota, ka kai su asibiti. Sai ka ga kemi yoyl MAMAN FADILA 106 daidai, sai ka ze ka sanar da mu. In Magajin Hakimi ya dawe zai blyoku, tunda yanzu Gaje tace baya gida. Karyan da Gaje tayi. Allah ya taimaketa. Ashe kawe tona aufa cikin sasa. Shi kuma yana nufa wajen na shi sabgar. Hajlya Saffya da Gaje da wata mai aikin Hajiya Saftya su ne suka tafi da Murja asibiti. Hakimi yay! neman Magaji, ta sake, ta waya. Amma shiru, ba a samu ganin Magaji ba. Nakimi tare da wasu mutanen shi, suka nufi asibiti. Suna zawa. Likita yayi masu bayanin dole za ayi wа Murja tiyata, saboda tana da ciki, amma dan dake cikin nata, ya rasa wajen zama. Dan haka nan da wasu awoyi, in har ba a fede cikin Murja, an kwashe magungunan gargajiya da na asibiti da suka toshe mata inda yaronta zai kwanta. To komai na lya faruwa da ita. Da yaron cikinta. Hakimi da kansa yasa hannu aka shiga da Murja dakin tlyata. Auwalu ya koma gida ya dubo ko Magajiya dawo. Yana kwance da Magazine yana karantawa. Auwalu ya fada ma shi halin da Murja ke ciki. Da sauri yayi jifa da Mujallar hannun shi, yace "Ciki ta he da shi. Ita ma? Ya mike ya wuce, yace "Zo mu tafi asibitin." Sun isa da dadewa. Sannan aka fito da Murja daga dakin tiyata. Kowa a wajen zurun! Tunda haryanzu bata farfado ba, duk suna tsaye bisa kanta. Bayan wani dogon lokaci. Murja ta bude ido, tare da fadin "Kalmar shahada. Tabi kowa da kalio. Sai DA SANNU.... 107 hawaye ke zuba mata. Ta kama hannun Magaji tace "Nawan, ka yafe min, mutuwa zan yi. Ina Gaje? Dan Allah ki yafe min. Na nemi cutar da rayuwarki, ga shi yadda abin ya koma min. Ki yafeni. Ba zan tashi ba. Ina Mommy na da Daddy na? Yanzun zan mutu, ban gansu ba? Hajiya Safiya tace "Ki yi hakuri. Hakimi ya tura a taho da su. Sun kusa zuwa suna hanya. Yanzu suka bugo waya." Tana cikin lallashinta. Mommy da Daddy tare da Direban daya je ya fada masu. Suka shigo. Suna zuwa gabanta. Ta mika masu hannu. Suka kamata. Dariya kawai ta yiwa iyayenta. Sai ta cika. Da kalmar shahada. Allah ya gafarta mata. Ya yafe mata kura-kuranta. Wato da Gaje ta ja dogon salati, sai ta fadi sumammiya. Jini yana zuba. Nan take Magaji ya kuma rude masu yana fadi "Inna-lillahi-wa-inna-ilaihir-raji'una! Duk ni daya, lokaci guda na rasa mata biyu. Da "Ya'ya biyu? Ya zan yi. Ni ma zan bi su, na huta." Da sauri Likitoci suka sa aka shiga masu da Gaje. Suka fara bata taimako. Aka rirrike Magaji da yake ta sambatu. Su Hakimi suka sa aka hada masu Murja aka sakata mota, tare da Magaji. Aka bar Hajiya Safiya da Auwalu jiran tsammanin Gaje. Su Hakimi ba su dade da tafiya ba. Likitaya fito ya sanar da Hajiya Safiya Gaje ta haifi 'Ya mace. Amma wata bakwai ne. Amma duk da haka 'Yar tana da koshin lafiyarta. Haka ma uwar 'yar. Lafiyarta lau. Kodayake MAMAN FADILA 108 tana dai tare da damuwa ne. Amma a basu kwana biyu, zata warware. To yanzu dai kwana uku da mutuwar Murja. An samu kwanciyar hankali. Ganin an samu Gaje da bakwaini. Diyarta kamar ba bakwani ba, sun samu cikakken lafiya. Sun yi kyau abinsu. Ranan suna, saboda mutuwa, ba ayi wani gagarumin taro ba. Amma duk da haka Naziyatu ta je har Zariya ta sanar da tauraruwar marubuciyarta. Dan ta gayyato mata marubuta ta jihar Kaduna, don su yiwa jaririya da Murja addu'a. Ai kuwa tauraruwar tata, ta garzaya, KUNGIYAR MATA MARUBUTA LITTAFAN HAUSA TA JIHAR KADUNA. Watau (WOMEN HAUSA NOVELS WRITERS ASSOCIATION OF KADUNA STATE). Sun kuma amshi gaiyatar tata hannu biyu. Dan sun je mata. Sun dauki jaririya da ta ci sunan Murja. Sun yi mata addu'a. Sannan ita ma Murja sun yi mata Allah ya kai ladan kabarinta. Gaskiya wannan Kungiya ta Marubuta. Sun birge kowa a wajen. Su zama abin sha'awa a wurin. Abin kallo. Shekaru biyu. Sai ga Gaje da tsohon ciki. Zaman Gaje da Magaji, ya zama abin sha'awa ga kowa. Soyayya mai tsafta suke gudanarwa. Murja kuwa ta zamá tasu Nusaiba da Naziyatu. In dai suna nan. To tasu ce su kadai. In kuma ba sa nan, tana like da Hajiya Safiya, ko Auwalu. Da Hakimi ne ba sa shiri, dan bata barin shi sukuni, tana wahalar da shi. Dan haka suke yawan fada. DA SANNU... 109 Shi da ita. lyayenta kuwa, ba ruwanta da su. Sal ta kama. Allah Sarki! Ga shi dal DA SANNU... Gaje, Magaji ya zama nata. Ita daya, sannan kuma ga shiyau ta kuma haihuwa Danta namiji, mal kama da uban shi. Magaji yayi tsalle, yayi murna. Ya ci sunan Hakipi Ibrahim. To ita dama rayuwa. In har ka bi ta da sannu. Sai ka samu duk abin da kake so. Amma da zaran ka ceza ka nuna garaje, ko aikin gaggawa. To kwa za ka ga garaje. Za ka iya samun abin da kake so na dan lokaci. Daga karshe ka ga ba daidai ba. To wannan karon ma an kuma gayyato manyan Marubutan. Dan Magaji ya ji dadin irin addu'ar da suka yi wancan zuwan. Dan ya gani a cikin kaset din sunan Murja. Abin ya ba shi sha'awa. To ni dai ina gefe, ranan sunan, ina kallon irin shigar alfarman da Anti Habiba ke yi, dan ni ma ba zan ce Gajen ba yau. Ihun da tsalle da na ga jama'an gidan sunan suna yi. Suna fita waje. Shi yasa ni ma fita waje. Sai na ga ashe manyan Marubutan ne, suka iso. To ni dal daga nan, sai nayo hanyar garinmu. Dan na sha wuya wancan zuwan nasu. Wajen masu zuwa ganinsu. An

Chapter 6 of 7