abin da
yake mai dadi. Ya rasa da wane fuska zai kalli Murja, ya
ji dadi? Yana cikin wannan hali ne Murja ta shigo da
murnanta, ta fara kawo ma shi shagwaba. "Ka tafi, ka
barni ni daya. Wallahi in har aka kuma zuwa, za a tafi da
kai ba zan yarda ba, sai dai na bi ka mu je tare."
Murja ta fuskanci yadda Magaji ke lallashinta
da akwai abinda yake damun shi. Da hanzari tace "Oч
sorry! Nawan, ka yi hakuri, ban kyauta ba. Don ban
tambayeka dalilin da yasa aka zo aka tafi da kai gida ba
ko? Allah sa dai alheri ne? Yanzun menene dalili.?
Da Murja ta san amsar da Magaji zai bata da
bata tambaya ba. Magaji yayi ajiyar zuciya yace "Dalili
shine, an zo an daukeni ne in je in ga matar da iyaye na
suka auran min ita."
Murja ta daki kirjinta. Ta ja dogon numfashi
tace "Mat.... Bata karasa ba, numfashin da ta ja, bai
dawo ba. Ta yanke jiki ta fadi. Murja bata tashi farkawa
ba. Sai cikin dare, ta ga iyayenta da Magaji suna tsaye
bisa kanta. Tayi ajiyar zuciya, ta sauke numfashinta a
hankali, tace "Mommy! Daddy! Kun ji cin amanan da
nawan yayi min ko?
Mommy ya zan yi, in hakura? Ba zan iya rabuwa
da nawan ba. Na shiga uku." Ta kuma rushe musu da
MAMAN FADILA 76
kuka. Shi ma Magaji hawaye ne ke zubowa daga idansa.
Mahaifin Murja ke ba shi hakuri.
Murja kuma mahaifiyar ta ke bata hakuri,
abinda yasa mahaifin Murja ke lallashin Magaji, saboda
Magaji bai munafunci iyayen Murja ba, duk ya sanar da
su gaskiyar abin da ya faru da shi da sanadiyar shigan
Murja wannan hali.
Dan haka basu ga laifin shi ba. Da lallashi
mahaifin Murja ya dauki Magaji ya maida shi
makaranta, sannan ya wuce gida, suka bar Murja da
Mommy ta. Murja tace "Mommy ina son nawan, son da
ba zan iya yarda wata ta yi kusa da shi ba. Ba zan iya
zama da kishiya ba, ba kuma zan iya fasa auren shi ba.
Mommy ya zamu yi da wannan yarinyar mai
tsautsayi da ta auri mijin da ba nata ba. Meye abin yi a
kanta? Bana son na shiga cikin gidan nawan, na ga
wata 'Ya mace da sunan mijinmu guda.
Mommy ki san abin yi, in ba haka ba, komi na
iya faruwa. Kada ranan da kuka kaini, in banka ma
dakinta wuta, ta kone. Daga ita har kayanta. Don
hankalina ya kwanta."
Jin wannan kalamai da Murja ke furucinsu, suka
sa na tsaya da biro. Na cak! Ina mamaki, ya za ayi ace ki
na budurwa yarinya da ke, ace kin san zafin kishi irin
haka? Dole ne mu da muke zaune da mazajenmu lafiya,
mu dunga gudun kishiya.
Dole su wance da zaran anyi mata maganan
kishiya, ta kan yi kamar ta zare. To ban ga lafinki ba,
dole ki tsorata, dan Allah kanninmu ku yi mana adalci.
DA SANNU... 77
In kun tashi auren mazajenmu, ku dunga zuwa da
zuciyarku guda. Ban da mugun nufi a rai. Da ace ke kika
yi cuta. Gara ace ke aka cuta.
Mommy da take sauraran 'Yarta, tana wannan
mugayen kalaman. Ita sam ko a jikinta, sai ma bata
fuska da tayi, tace "Murja dole hakuri za ki yi, kamar
yadda na fada miki, na gaya miki Malamaina basu da
wani abu da zasu iya yin miki a halin yanzun. Dole sai
kina cikin gidan Abdullahi. Sannan za mu cimma duk
wani buri namu. Ki yi hakuri. Saura kwana nawa ne?
Murja tace "Mommy ina mutukar bakin ciki mu
karasa nawan, ya koma ya zauna da wannan yarinya. An
cuceni Mommy. Wai ma 'yar gidan uban waye ne?
Mommy tace "Za ta wuce 'yar cikin masarautarsu ne?
Murja tace "Za ko ta ci jakar ubanta, ko ma 'yar waye,
kuma Mommy zan riga nawan gama karatu da kwanaki.
Ina gamawa kawai za ku aika maganan
aurenmu. Ni ma in shiga gidan. Ya zo ya sameni, in ba
haka ba, bani da kwanciyar hankali."
Allah Sarki Gaje! Baiwar Allah. Ita a wannan
dare da Magaji ya koma. Dare ne da yayi mata tsawo,
saboda tunaninta, shine yadda za ayi Magaji ya hakura
da ita a mazaunin matar shi.
Gaje ta riga ta yankewa kanta zata ci gaba da
zama da Magaji, duk irin zaman daya bukaci su yi, ba za
tayi ma rayuwar Magaji shisshigi ba, yadda yayi haka
zata bi komi da sannu.
Shi kuwa Magaji a wannan dare. Ya kasa barci,
daga ya juya filo nan, sal ya juya shi can. Sai kuma ya
MAMAN FADILA. 78
mike ya zauna. A haka gari ya waye ma shi. Karfe shida
yana kofar Asibitin, ya samu Murja bata tashi barci ba.
Nan ya zauna yasa ta gaba, yana kallonta, har ta tashi.
Ta bude ido ta gan shi, sai kawai ta juya ma shi
baya. Yayi ta magana. Amma bata tanka ma shi ba, bata
kuma juyo ba. Sai kawai Magaji ya ja bakin shi yayi
shiru. Bai kuma tanka mata ba, balle yayi mata wani
furuci.
Bayan wani dagon lokaci. Murja ta waigo idonta
fal! Da hawaye tace "Nawan, yanzun kai ne da bakinka
da idonka, ka dubeni, ka ce min kana da wata mata,
bayan ni? Kana ko so-na kuwa?
Magaji yace "Ya-Salam! Amma dai ce miki
kawai na yi matar da aka aura min. To mai zai sa ki
damu kanki, har ki shiga cikin wani hali? Aure ne dai
sun riga sun daura min. Na kuma karbeta, na ajiyeta,
kuma zan ci gaba da aje ta. Ki na ina? Kin riga fa kin
dade da sanin ni fa naki ne ke daya, kuma ba ni da wata
mata da ta wuceki.
Bari in fada miki gaskiya, bacin biyayya, habu
yadda za ayi ace in taka waje in wuce. Ita ma yarinyar
nan ta taka. Ke duk abin da zan fada miki, ba za ki yarda
ba. Har sai kin zo kin ganta, za ki jinjina min biyayyar da
na yi. Har na karbi wannan yarinya, na aje ta.
Ni yanzun bani da saura kwancíyar hankali, sai
na budi ido na ganki a cikin gidana, kin zama matata."
Kalaman Magaji sun yi wa Murja dadi sosai. Dalilin
haka. Murja bata san lokacin da ta rungume Magaji ba,
DA SANNU.... 79
tana fadin "Nawan, yanzun ka aje ta, babu ruwanka da
ita, ba wani abu da ya shiga tsakaninka da ita?
Magaji yace "A'uzubillahi. Kada ki yi sabo
mana, kin kuwa ga yarinyar, ko 'yar aiki ba za ki iya
daukanta ba. Ko mutuwa zan yi, ance miki zan iya hada
jikina da wannan kwailar yarinyar nan ne? Ke dai
biyayya dadi gare ta kawai.
Ballantana mu da muka fito gidan sarauta, shi
ya sa na aje ta. Amma in ba haka ba. Duka zan yi mata,
na sallameta, ta koma inda ta fito. Dan ban ma san inda
Baba Hakimi ya samo yarinyar ba. Ni yanzun zan koma
gida, na samu Baba Hakimi, na sanar da shi ya turo
gidanku a gama komi na auranmи."
Duniya kenan! Ta'adanci da shedanci bai da amfani ga
Dan-Adam, kamar yadda ake tunani, ko ta zata.
Yankewa Lamido hukuncin kisa.
To hakan ta kasance. Kotu ta yanke masa
hakunci kisa, ta hanyar rataya. Kauyen 'Yan Warin Daji,
sun yi farin ciki a boye. Sun kuma yi bakin ciki а
baiyane.
To ina ranan haka? Sauran duk anyi musu
hukunci daurin rai da rai. Dan Allah samari maza, ku
daina ta'addanci da shedanci, ku kama sana'a, ku guji
rudin shedan da gatan duniya. Allah kuma ya shiryi
masu irin wannan halayyan.
Rayuwa mai canji. Yanzun Gaje ta zama 'Yar
gidan sarauta, ta saki jikinta sosai, ta saba, bata da
MAMAN FADILA 80
wata matsala, sai safgarta kawai take. 'Yan aikin gida
duk suna kaunarta, sabo da iri halaiyarta. Lanti kuwa ta
zame mata tamkar Uwar.
Ita Hajiya Safiya kuwa, ita daman kowa ma nata
ne a gidan, ballantana kuma matar Magajinta. To
kamar yadda yace zai yi maganan kan aurensu. То
hakan ko yayi. Ranan da ya dawo ya samu Hakimi, suka
gama magana. Ranan ya koma makaranta.
Ya shiga sasan shi, har yayi barcin mintocі.
Tunda Gaje ta shiga, tayi masa sannu da zuwa, babu
maganar da ta kuma hadasu.
Koda zai koma ma, bai yi mata sallama ba.
Dama jikin Gaje bai bata Magaji zai kwana ba, tunda
bata ji ya kira Lanti ya bata umarnin din ta girka masa
kalan abinci da yake so ba. Dan haka da Hajiya Safiya ta
tambayeta, ko Magaji yana nan. Take tace mata ya
koma, dama ta san a komawar nasa. Ta dai tambaya ne.
Dan ta san ya zaman nasu yake.
Hakimi ya ji dadin maganan auren nan, na
Magaji saboda irin korafin auren Gaje da wasu daga
cikin dangi suka dunga yi. Dan haka yanzun ya nemi duk
wanda ta dace. Sun kuma je har can birni, gidan iyayen
Murja. An kuma gama komi. Da zaran ta gama
Diflomanta za a daura musu aure, ta tare a gidan
mijinta.
Hakimi yana zaune. Gaje na durkushe gaban
shi. Hakimi yace "Diyata, mijin ki zai kuma kara mata,
ina fata hakan ba zai canza miki halayyanki na kwarai
da na sani ba tun farkon haduwarmu da ke? nikta
DA SANNU... 81
Ina son halavan na kawai su fi na da. Ki
zama mai juriya haj. kikas ce mai kawaici da
kau d kai, ga abin bahafe ba. Komi kika gani, ki
bi shi da saliliu, Adua ki ce za ki vi garajen cin masa. Bi
she dai da sannuhankali, sai ki cimma nasara.
Dan ha ki kwantar da hankalinki. Allah ya
hada kawunanku ke da ahokiyar zamanki, mijinki kuma
ki ci gaba da hiyayya a gare shi Tashi ki tafi. Allah yayi
miki albarka."
Komai Lomai yana da lokacinsa. Murja ta gama Difloma.
Shirye-shiryen biki kawai ake yi. Abin sai ka ce babu
mafadi. Ango na fama da jarabawa, yana fama da
hidiman biki. Wannan fa shine sa kai, wanda ya fi bauta
ciwo.
Ita kuwa Gaje sai ka ce ba ita za a yiwa kishiya
ba. Ni abin nata bani mamaki yake, yadda na ga mata
suna jigatuwa in aka kawo musu kishiya, duk su fita
haiyacinsu. Sai na ga ita Gaje sam ba haka bane. Kamar
na tambayeta. To amma kuma babu dama. Tunanina ni
dai ya bani ko dan dai Gaje bata san soyayya bane, shi
yasa ita bata damu ba?
Dangi na nesa da kusa sun halarci daurin auren
Abdullahi da Maurjanatu. Haka kuma gidan Hakimi yа
cika, tamkarbabu masa saka tsinke. Taro yayi taro, har
da dangin Gaje da kawayenta.
Hakimi sai da ya kuma gyarawa Gaje dakinta.
Duk dangin Gaje da suka zo bikin, suna shiga cikin
MAMAN FADILA 82
dakin Gaje. Sai su rungumeta suna mata murnan.yadda
dakinta ya zama. Gaba daya su kishiya bata gabansu.
Kyawun dakin Gaje shine a gaban su.
To dada ni ma kaina dakin Gaje na ke, gaba
daya ma sai na shiga tausayawa dakin, saboda ina
ganin kamar Gaje bata san yadda zata sarrafa dakin ba.
Da kyar na iya fita, na nufi dakin amaryar.
Ina lekawa, na ga kayan sanabe kala-kala na
dukiya, an zubasu a cikin dakin Murja. To amma kuma
sai bai burgeni ba sosai. Dan wani karyan.
Da kyale-kyalen in har yayi yawa, sai ya baci. Ko
kusan ince almubazarranci. Dan ba a san ciwon kudin
ba. An rasa yadda za ayi da su, an samesu a sama da
gumin wasu. Da sauri na koma dakin uwargida sarautar
mata. Ina komawa, na samu kanwar Hajiya Asabe
mahaifiyar Magaji tana zazzagawa. Gaje kwandon
bala'i.
"Ni Wallahi ban ga amfaninki ba, tunda na zo
gidan nan, babu abinda kike sai lodawa danginki abinci
kike suna lodawa a cikinsu. Suna washe baki. An zo
gidan akwai. An hadu da abinda ba a saba ci ba, kai tir
da irin ku." Karaf!
Sai a kunnen Hajiya Safiya ta zo ta kawo wasu
baki da za su ga Gaje. Hajiya Safiya tace
"Subahanallahi. Hajiya keda waye haka? Ba dai Gaje
kike fada mata irin wadannan maganganun ba. To
gaskiya kin tafka kuskure, in har da ita kike.
Ki bi a hankali, kada ki gamu da bacin ranki.
Yanzun muddin Hakimi ya samu wannan labari. Wallahi
DA SANNU... 83
ba za ki ji da dadi ba. Ahir dinki, ki rufawa kanki asiri.
Gaje taso mu je can sasana."
Da guntun hawayenta Gaje ta mike. Hajiya
Safiya ta kama mata hannu suka tafi. Suka bar Hajiya
Jami nan sansarai, gwiwarta babu kwari. Hajiya Jami
kanwar mahaifiyar Magaji, ba wani abu yasa ta ki jinin
Gaje ba, sai saboda tilon da 'Yar ta Saratu da take
mutuwar so, ta hada su aure da Magaji. Dan haka take
takurawa Gaje, ta ki jininta. Take kuma son ta ga Gaje
ta bar gidan.
Dan kyar ta shigo, sai ka ce an fada mata Gajе
ce zata hana ta zuwa. Ganin da Hajiya Jami tayi Magaji
ya kara aure, sai take ganin Gaje ce ta jawo hakan.
An gama shagulgulan biki. Kowa ya watse, babu
kowa sai su. Ango kuma yana can wajen zana
jarabawan shi ta karshe.
Murja tayi mamakin ganin Gaje a matsayin wai
kishiyarta. Ta kuma jinjinawa Magaji daya iya karbanta.
A tunaninta dole Magaji yayi kokarin ya ganta ta zama
matar shi. dan abin kunya ne. Ace yana da mata.
A shigo a ga Gaje, dan haka kishin da Murja ta
zo da shi. Sai kawai ta watsar da shi, dan bata ga
shiriritan da zai sa ta bata lokaci tana kishi da Gaje ba.
Mai zata yiwa kishi?
Ga ta da iliminta, na boko, ga ta da kyawu, ga
shi ubanta mai kudi ne. Allah Sarki! Tunanin Murja
kenan! In kika mallaki wannan, kin fi karfin kishiyarki.
To Wallahi ba Haka bane, ba kuma anan take
ba. Kishi, koda mahaukaciya da bata da hankali, wanda
MAMAN FADILA 84
bata san ciwon kanta ba aka hada ku. To kishi ne, babu
zance kin fi karfinta. Ke dai ki iya takunki, kuma babu
ruwan kishi da 'yar talaka, ko 'yar mai mulki, ko 'yar mai
sarauta. Duk kishi guda daya ne. Kowa dai ya san
abinda yake yi kawai.
Magaji duk ya kosa ya kare (Exam). Ya dawo
gida wajen amaryan shi. To Allah ya taimake shi. Ya
gama. Ya kuma dawo gida cikin farin ciki. Hakimi ya
tarasu gaba dayansu a gaban shi. Ya fara "Magajin
Hakimi kamar yadda muke addu'a ka zama kamar
mahaifinmu Hakimi.
Allah ya yafe masa kura-kuran shi, ga dukkan
alamu ka fara kwatanta zama irin shi. Yayi mata biyu.
Kai ma ga shi yanzu kana da mata biyu.
To Allah ya ba ka ikon yin adalci, ka rike kowa
bisa amana. Dan yin adalcinka, shine zaman lafiyan
gidanka, rashin adalcinka, shine rugujewar gidanka,
dan haka ka kula sosai. Ku kuma ke diyata, ke cсе
uwargida.
Dole ki kasance mai hakuri da kauda kanki ga
wasu lamuran. Kada ki zama mai sa ido. Juriya ta ki cе.
Allah ne ya dora miki wannan sarautan. Duk da dai na
yarda da ke, na san ba ki da matsala. Amma dai ki kula.
Ke kuma Murja ke ce amarya. Dole ki yi biyayya,
ki yi koyi da yadda abokiyar zamanki take yi. Kada ki
zama tsagera, mai raini da tijara. Ki bi da sannu. Allah
yayi muku albarka, ya hada kawunanku. Ya baku 'Ya'ya
masu albarka.
DA SANNU... 85
Ke Hajiya Safiya, me za ki ce musu? Hajiya
Safiya tace "Ai duk abinda zan fadi, ka fada. Saboda
haka abin da zan kara maimaita muku, shine ku yi
hakuri da junanku, shine cin ribanku. Allah ya albarkaci
zamanku tare. amin."
Wata sabuwa! Mace shedaniya ce, in taso
shedanci, wato koda suka dunguma suka koma
sasansu. Sai Murja ta shige dakinta tana kuka da
rawan jiki. Magaji ya sameta yana fadin "Murja lafiya
kike kuka? Ranán farin cikinmu. Ranan da muka kosa
Allah ya nuna mana ita."
Ya kamota ya rungume yana lallashinta, "Fada
min Beby na, me ya sameki kike kuka? Dadin kiranta da
bebi da Magaji yayi, shi yasa Murja dada kwakume
Magaji. Kaman zata shige cikin fatan jikin shi. Shedanci
da yaudara irin tamu ta mata, shi yasa Murja dogon
ajiyar zuciya, tace.
"Nawan, dole in yi kuka. A gabanka Danuwanka da matar shi, suka nuna basa kauna ta, har
suna fadin wancan Yarinya ita ce suka san halinta masu
kyau. Suna nufin ni bani da tarbiya kenan? Magajiyace
"No, ba suna nufin haka bane. Bana son ki yiwa zancen
wani zargi.
Ki yi hakuri, tashi mu je mu yo alwala, mu gode
ma Ubangijinmu, mu roke shi, yasa mana albarka a
cikin aurenmu." Koda suka gama nafilarsu raka'a biyu.
Abinka da sun kosa, ba su tsaya wani surutu ba.
Tambayoyin da yayi mata. Ta amsa mai. Wasu kuma ya ci
gyaranta, dan zakuwa ko ma rigar barcin basu nema sun
MAMAN FADILA 86
sa ma jikinsu ba. Da dai suka cire kaya, sai gado. Suka
ja bargo suka kashe wutan lantarkin dakin.
Ni kuma saboda gudun shiga haramcin ganin
sirrin ma'aurata. Sai na yo ribas, na fito da gudu. Na
nufi dakin Gaje. Da shigata na samu Gaje tana ta faman
shirga barcinta.
Nai murmushi, wato ita Allah bai sa ta kasa
barci ba, irin nasu. Wa ke kuka har da su majina.
Saboda yau Maigida yana shimfidan wata? Da abin ya
ban mamaki, sai na koma gefe na kurawa Gaje ido, har
ni ma barcin ya saceni.
Da safe Gaje ta tashi, duk tayi abinda ya dace.
Amma ango da amarya basu fito ba, har rana ta
baiyana. Gaje ta kosa ta shiga cikin gidan Hakimi
kamar yadda ta saba. Babu dama. Tunda bata gaisa da
Maigida ba. Da amarya. Bai kamata su tashi ba su
ganta ba.
Gaje ta gaji da jira, sai kawai ta nufi dakin
amarya, tayi sallama, tana tsaye bakin kofa da kyar
Magaji ya amsa sallamar. Ta gaida shi, ba tare data
shiga ba. Ya amsa mata yana cikin bargo. Ta kuma bude
baki, tace 'Amarya kin tashi lafiya?
Ta ji shiru, babu amsa. Magaji yace "Je ki, bata
tashi ba." Gaje ko a jikinta, ta koma ta nufi inda tafi
auki, tana shiga Hajiya Safiya tace "Kun ga uwargida
sai yanzu muke ganinki. Lale, sannu fa."
Gaje dariya take, tace "Hajiya kun tashi lafiya?
Hajiya Safiya tace "Kalau. Ina fatan dai ke ma kalau
kuke? Kuma babu dai wata matsala ko? Gaje tace
DA SANNU... 87
"Hajiya babu." Ta ci gaba da harkokinta. "Hajiya ni fa
yau kalallaba nake so na yi. Ki na da fulawa, in hada, na
yi."
Mafi yawanci Gaje in ta shigo sasan Hajiya
Safiya, ita ce yin dan wake, gauda, dambu, fate ci ma
dai irin tamu ta gargajiya. Shi Gaje take yi, dan ta ci,
bata damu da ta ci girkin da aka girka a cikin gidan ba.
Wani lokacin Hakimi in yana nan. Ci man Gaje
yake ci, ya koshi, dan ta iya sosai. Gaje na tsaka da yi
tuyar kalallabarta. Magaji suka shigo tare da Murja.
rako ar
Haia Safiya da fara'arta, tace 'Da kanka ka
n? Gaje bata jira ta zo da ita ba." Suka
gaisauji ya fita. Murja ta zauna. Gaje ta miko mata
kai, tace bata ci. Sai ma ta mike tace wa Hajiya
Safiya "Ni zan koma ciki. Ina da aiki." Bata jira jin wani
magana ba, tayi gaba abin ta.
Gaje sai yamma ta koma, ta samu Magaji baya
gida. Sai Murja tana kallon (Nigeria film). Mai suna
(Agumba). Tana ta dariyar tau'raron fim din mai suna
Nkem Owoh.
Yau shine ya gamu da Dan iskan Yaya da yake
lallaba shi. Mai yi a banza. Yau ga shi shi ma ta same
shi. Shigowar Gaje ta gintse dariyar da take. Gaje har
zata shige daki. Murja tace "Ke zo nan."
Gaje ta dawo tace "Ga ni." Murja tace "Ki ji ni
da kyau, ki kuma san abin da kike, dan irinku ne 'yan
kauyen nan, in mutum yayi sake, sai ku kwace mishi
miji, ku bar mutum nan. Daga yau kada ki kuma zuwa
MAMAN FADILA 88
min daki gaidamu, ki bari in mun fito in da halin
gaisuwar, sai mu gaisa. Dan bai zama lalle ba."
Tayi shiru kenan. Gaje ko daki bata shiga ba.
Magaji yayi sallama ya shigo. Da gudu Murja ta
rungumo shi, tana fadin "Nawan, ayoyo. Well come back
to me! Tunda ka fita, ko abinci na kasa ci. Because you
think!
Magaji yace "Ki yi hakuri Bebi-na, wai na ga kin
gaji ne jiya, kada na dawo na kuma matsa miki. Gaje da
ta ga basu da niyyar sakin juna, abin nasu ba na kare
bane. Sai kawai ta kama gabanta.
Zata shiga daki. Ashe duk abin da suke. Magaji
yana lura da Gaje, ba tare da ya waigo ya kalleta ba,
yace 'Ina za ki? Ki tsaya ina da magana da ku." Sannan
ya ci gaba da maganan da turanci, yana fadawa Murja
wanda haka ya nunawa Gaje alama. Koda ba ta jin
turanci cewa da akwai abin da Magaji yake son ya
matsawa Murja akai.
To haka ne. Domin bayanin da Magaji yake
mata, ita tana ganin wannan ba (Reason) bane, wai
yace dole ya hadasu yayi magana da su. Ita fa bata
dauki Gaje kishiya ba. Sun yi ta musayan turanci
tsakaninsu, sannan Murja ta zauna.
Magaji ya zauna kusa da ita. Ya dubi Gaje yace
"Ke ma samu waje ki zauna." Gaje ta samu kan tuntun
dake can gefenta, ta zauna. Magaji ya fara magana
kamar haka "Jiya mun gaji, bamu yi miki maganan
kwanakin girki ba. A yau mun gama kwana bakwanmu,
na amarci.
DA SANNU... 89
Zan ci gaba da yin kwana biyu, ko wane daki."
Murja tace 'Gaskiya kwana biyu yayi min yawa, sai dai
kwana daidai, to wai ke ma ba ki da adalci ne irin na
wasu mata. Da suke yi wa amarya. In anyi masu, su kara
musu wasu watanni. Dan su fahimci junansu."
Gaje bata san dawan garin ba, tace "To kamar
wata nawa zan kara maku? Murja tace "Wasu na ga su
kan kara masu kamar wata shida. Marasa mutunci, ba
sa wuce wata uku. Amma in har akwai mutunci, har
shekara daya ake badawa. Ke ma sai ki zabi wanda kika
ga dama."
Kamar in cewa Gaje ko minti daya ba za ki kara
ba. Karya take. Gaje tace "To ni ma na kara muku
shekara guda Amarya. Allah shi ma Magaji bai sani ba
ko da gaske ne, abinda Murja ta fadi, haka na faruwa.
To ni dai ba zan ce hakan baya faruwa ba, dan
wasu matan su kan karawa amaryan kwanaki da basu
wuce bakwai ba, saboda Allah har cikin zuciyarsu.
Wasu kuma sun kara ma miji kwanaki ko ma
wata, saboda tsananin kishi, ba dan Allah ba. Sai dan a
nunawa miji ko in kula. Amma ita dai Gaje rashin sani
kan yadda abin yake, yasa ta bada nata kwanakin, tayi
musu kari.
Magaji yayi shiru. Gaje ta mike zata koma daki,
yace "Ke dawo." Ta dawo yace "Ina fatan dai kin san
yawan kwanakin da kika kara mana? In har ba ki sani
ba, bari na sanar dake, kin kara mana kwanaki 365.
Kin amince? Gaje tace daga kai, alaman ta
yarda. Sannan yace "Shi kenan, je ki abinki. Allah zai
MAMAN FADILA 90
gyara." "Wai kai mai ke damunka ne? Yarinyar nan fa ko
ta kara mana kwanaki, babu abin da zai shiga
tsakaninka da ita. To ina laifin dana bata hakkinta, ba
mu yi mata fin karfin ba."
Magaji yace "Ni na san babu abin da zai shiga
tsakanina da wannan yarinyar. To amma ya kamata
ranan hakkinta, in kwana ko da a falo ne, dan ya
kasance na haifi shege.
Dan a hakkin wata ake haihuwar shege. To
amma tunda yanzu ita tace da bakinta ta amince da
haka din, shi kenan, babu wata matsala. Wannan abun
yayi daidai."
Kwanci tashi, sun samu wata guda da wasu kwanaki,
suna haka. Babu kuma abin da yake damun Gaje, dan
ba wai tana yawan zaman sasan nasu bane, balle ta ga
bakin ciki. Ita kuma Lanti mai masu aiki, in ta dan zargi
wani abu a cikin zuciyarta. Sai tayi sauri ta watsar, dan
tana gudun hada husuma.
To ita ma Hajiya Safiya tunani ya dan fara
damunta. Anya kuwa babu abin da ke faruwa a zaman
gidan Magaji, ba a cutawa Gaje kuwa? Kullum
tunaninta kenan. Ita ba abni tayi wa Hakimi magana ba.
Ya zama tashin hankali, dan ta san yadda Hakimi ke
tausayin Gaje.
Saboda hakurinta da biyayyarta, kuma
koyaushe tace wa Gaje ba kya cikin takura dai ko?
Amsar da ta ke bata, babu, suna zaune lafiya. Cikin
DA SANNU... 91
wannan hali ne su Naziyatu da Nusaiba suka dawo hutu,
cikin murna Nusaiba ta rungume Gaje.
Ita kuma Naziyatu ta fada jikin Hajiya Safiya ta
dubi Gaje da kyau, tayi dariya tace "Lale, gidanku da
rowa. An waye ke ce da wannan kwalliya haka? Sai ka
ce 'yar jami'a.
Lalle kina tsoron kada Baba Magaji ya auro miki
'yar jami'a kenan. Ba ki san halin Baba Magaji ba.
Wannan kwalliyar ta ki, bata isa ta hana shi ya kara
auro 'yar jami'a ba.
Ki lallabani in koya miki (Dressing) irin ta matan
jami'a. Ke ma ki faso." Nusaiba tace "Tunda ke 'yar
jami'ra ce, ai dole ki koya mata mana." Naziyatu tace
"Ko dai ban je jami'a ba.
Amma na fi wata. Kuma ni babu wata kwalliya ta 'yar
jami'a da sanabe irin tasu da zai gagareni. Sai dai ban
so yi ba."
Hajiya Safiya da take zaune ta bude baki tana
kallon wannan tsagalewa ta Naziyatu, tace “Ko ki so, ko
kada ki so, ki rike (Make up) Da (Dressing) dinki 'yar
jami'a ce Magaji Hakimi ya riga ya aurota, tana can
sasansu."
Nusaiba tace "Hajiya kuka kyale Baba Magaji
ya auro 'yar jami'a. Salon su cutawa Gaje. Gaskiya ba
ayi wa Gaje adalci ba." Naziyatu tace "To ke kin ga
laifinsu? Shi ma adalci aka yi masa? Hajiya Safiya tace
"Au, ko zaku ci ubanku. Na ga abin naku ya fara dawowa
kanmu. Bari na mike yanzun na yi maganinku. Ai kun
MAMAN FADILA 92
dawo kenan." Da gudu suka fita dakin. Kafin Hajiya
Safiya ta mike.
Suna fadin "Mun tafi wajen amarya, mu ganta, mu
kuma ci abincin amarya, mu yini dakinta." Gaje bin su
tayi da ido, tana masu dariya, tace "Hajiya watau in ki
na neman mai sa ido, kika samu Naziyatu, to an gama.
Kin ga dai da dawowarsu ta soma."
Murja na kwance da (Novel) na turanci a
hannunta. Wai shi (Behind the cloud). Ga dukkan
alamu, ta ji dadin kwanciyar da karatun da take yi.
Karan kwankwasa kofar yasa ta tashi cikin yin tsaki da
bala'i, ta nufi kofar, ta bude tana fadin "Wai su waye
zasu matsa min, kamar dole. Sai na bude?
Naziyatu tace "Mu ne 'Ya'yan Baba Magaji.
Dole ne ki bude mu ganki mana." Suka shige suka
zauna. Murja ta kare