An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
HAUSABOOK.COM
DA SANNU
By
AISHA A. TANIMU
DA SANNU
TARE
DA
ALKALAMIN
A'ISHA A. TANIMU
(Mrs ABDULLAHI DAN-FALI)
080-28795375/08-37912542
1
DA
INU
A'ISHA A. TANIMU (MRS ABDULLAHI DAN-FAL
DA SANNU
TARE
DA
ALKALAMIN
A'ISHА A. TANIMU
(Mrs ABDULLAHI DAN-FALI)
080-28795375/08-37912542
1
DA SANNU!
N"i dai Gaje na kan rasa wannan irin kwalliya ta
ki. Ke kenan duk dare in za ki je dandali, sai
kin kwaba fuskarki da zangafur. Sannan ga
wannan kwallin naki da kika kwaba.
Shi yayi ruwa da yawa, ba zama yake a fuskarki
ba, ko kin shafa. Duk kyau irin na ki. Da zaran kin yi ma
fuskarki wannan kwalliyar, sai gaba daya kyawunki,
nema, a rasa. Ke ba ki ko ganin yadda su Lante da
Kandala suke nasu kwalliyar, gwanin sha'awa.
a
Ga su nan da samarinsu a cikin gari. Amma ke
ko har yanzu na gaza samun suruki. Don Allah ki dunga
rage wannan irin shirmen kwalliyar nan ta ki, ko ni ma
na samu suruki da wuri."
Gaje ta aje madubin da ke hannunta ta kalli,
mahaifiyarta tace "Ni dai Umma kin asa min ido akan
wannan kwalliyar tawa. Wai ke an fada miki bani da
samari a dandali ne.
Da sannu fa ake samun komai na Duniya Da
zaran fa mun shiga dandali. Muka fara cashewa, ki zo ki
ga yadda samari suke kallona ina juyi.
Amma sai dai kawai babu mai lika min ko
kwandala. Ni dai bai daman ba, tunda dai ina daukan
hankalin samari. Kwandalansu bai dameni ba. Don
haka wannan kwalliya tawa, abin sha'awa ce ga kowa,."
DA SANNU... 7
Hayaniyarsu Kandala da Lante da suke shigowа,
shi yasa Gaje ta mike da sauri ta jawo gyalenta na dammara, ta tanke cikinta da tsumman, tana fadin "Ga
'yan korafin nan nan, kada su sakani gaba da surutu."
Daga tsaye Kandala da Lante suke fadin "Umma
don Allah ki raba mana gardaman nan da muke yi. Wai
azumi saura kwana hamsim da uku ne, ba saura
hamsim babu daya ne ba? Yanzu Deluwa take fada
mana.".
Umma ta dan dara tace "To ku mai menene abin
musu a ciki? Tunda da akwai saura da yawa, ku bari ya
kara matsowa mana, sai ku gane lissafin. Kuma ai ko
kun yi lissafin yanzu, aikin banza ne, tunda mu dai dole
ne sai mun ga wata za mu dauki azumi."
Gaje da ke neman warin takalminta, ta hango
shi can bakin rijiya, ta je ta dauko dayan can bakin
rijiyar. Tace "Ku dai musu baya muku wuya. Yau kuma
musun naku kan azumi yake?
Kandala da Lante har suna hada baki "To ina
ruwanki? Tunda ke ba ki yi, ki bar mu, mu mu yi abinmu.
Kowa irin ki ne matsoraciya.
Da ba ki iya tabuka komi, kowa ya raina miki
wayo, in an fada miki magana, ba ki iya musawa. Don
Allah mu dal ki zo mu je, tun dazun dandali ya cika, kin
san su Binto ba wai zasu jiramu bane."
Da sauri Gaje ta karisa, suka kama hanyar fita.
Suna fadin "Mun tafi Umma." Da sauri Gaje ta dawo da
baya, ta shige dakinsu da gudu, tana fadin "Na yi
mantuwa."
MAMAN FADILA 8
Duk spk tsaya cirko-cirko suna jiran su ga koо
mantuwar menano Gaje tayi? Gaje ta fito da madubi a
hannu ta rike da wata karaman roba, ta bude ta dantsi
kyalli Madam, ta lilika a fuskarta.
Lante tace "Dama kan wannan kyalkyalin kika
koma ki ka bata mana lokaci? Gaje tayi dariya, tace "Ai
kuwa dole na koma. Ya za ayi na je dandali, ban shafa
birge maza a fuskata ba." Kandala tace "Dama ki na
birgesu mazan ne in kika shafa?
Da sai ki yi tunkaho ke, kenan koyaushe cikin
kwalliya da kwaskwarima, abin baya ko miki kyau."
Umma tace "Ato, ai gara dai kuma ku dunga gwaba
mata, ko ta rage wasu haukan kwalliyar."
****
Sun isa dandati. Ya cika ya batse da samari da 'yan
mata. Dare ne. Amma kaman ba dare ba, ga wutan kara
nan, an hada da a ci balbal. Ya haska dandalin su Binto
da sauran 'yan mata suna tsakiyan fili suna cashewa.
Sai faman gantsarewa suke, samarinsu suna ta
faman musu liki da gudu-gudu su Kandala da Gaje da
Lante suka afka cikin dandali, su ma suka fara na su
cashewa. Samarinsu da suka jima da zuwa dandalin,
basu tsaya bata lokaci ba.
Suka shiga cikin tsakiyan dandali suka fara
likawa Lante da Kandala kudi. Ita kuwa Gaje ko а
jikinta. Ita dai ta na ta faman cashewa, bata ko
waiwaye.
DA SANNU... 9
Lamido da ke can gefe tare da magoya bayan
shi, ya dubi 'yan fada shi yace "Ni kuwa yarinyar can ta
na birgeni, tana kuma ban sha'awa. Ina ganin ya
kamata in latsata, duk da ba irin tamu bace."
Ya keto taro ya kutsa cikin filin dandali. Sai
kallo ya koma kan shi. Da gani wajen wa zai je? Abin
mamaki abin da ba su yi zato ba. Gaje ya nufa, ya dunga lika matá ruwan kudi.
Hatta 'yan matan da suke tsakiyar filin suke
cashewa. Sai da suka dakata da rawan. Suka tsaya
kallon Gaje da ta sake sabon launin rawa wanda haka
ya dada birge Lamido. Har shi ma ya cashe da wasu
baitoci na birgewa da yayi mata. Haka dai dandali a
wannan lokaci ya tashi da surutan Gaje da Lamido.
Kowa ya koma gida, yana mamakin wannan
abun. Ita kuwa Gaje koda ta koma gida, bata sake tuna
abinda ya faru a dandali ba, balle ta sanar da
mahaifiyarta.
Ta dai riga ta san ko da Lamido yayi mata likin
kudi, to ba zai aureta ba. Haka ita ma ko ta rasa miji, ta
san ba za ta iya auren Lamido ba. To ba ma Gaje ba,
hatta sauran mutanen da suka ga abinda Lamido yayi
wa Gaje, ba su yi zargin wai sonta yake yi ba.
"Yan warinDaji kauye ne da yake cikin jihar Zamfara.
Kauye ne daya kunshi dinbin al'umma da suka rike
al'adunsu na gargajiya sosai. Kauye ne mai kyaun tsari
da kyawawan halayya. A cikin kauyen.
_MAMAN FADILA 10
Alhaji Bara'u, shi ne Dakacin wannan kauyen,
kuma shine mahaifin Lamido. Shi kenan masa Dan da
ya haifa, dan haka duk son duniya ya tattara ya dorawa
Lamido. Sai yadda yaso, ya ga dama yake yi a cikin
wannan kauyen.
Babu wanda ya isa yace wani abu akan Lamido.
Sai mutum ya raina kan shi, tun Lamido ya na yaro
karami ya lalace. Shi ne shaye-shaye da dauke-dauke.
Ko a gabanka Lamido ya saci abinka, to ya
zama dole ka yi shiru, ba ka isa ka ce yayi maka sata ba,
kana gani za ka hakura.
Haka kuma kadan yaran shi suka yi maka sata.
Muddin suka je da shi wajen Lamido. To tllas ka dawo
da baya, ka hakura, duk wannan salon iskancin da
Lamido ke aikatawa bai tsaya anan ba.
Yana neman mata. Sai dai wani hukuncin Allah
da kariya ta mahaliccinmu, duk neme-nemen matan
Lamido, baya neman 'yan matan cikin kauyensu, sai dai
ya fita cikin wasu kauyuka ya samu irin 'yan iskan
kauyen. 'Yan matan da suka gagari iyayensu. Ya
kwasosu ya zo da su. In gama zamaninsu ya sallamesu.
Alhaji Bara'u mutum ne daya cika son kansa da
yawa, bai da adalci bayi da mutumci, kada ka sake
rashin mutumci ya shiga tsakaninku, domin za ka
tozarta da shiga matsala.
Mahaifin Gaje. Dan-tani. Mutum ne mai son
abin duniya, kuma yana daga cikin manyan 'yan fadan
Alhaji Bara'u, kuma har mukamin mai unguwar
barayinsu aka ba shi, saboda irin goyawa Alhaji Bara'u
DA SANNU... 11
bayo day
Π
ana dada fasa niaslakan duk abin
3. To daman
a bace.
haka du take. In har
ain arziki Saya bashin sh awara ya dauka.
Sai na batace irin shi, ko kuma mut.m mai kwadayin
abin da yake da shi, ko kuma yake kwadayin wata
daukaka da yake da ita.
Amma wanda da zaran ka rasa wadannan
abubuwan da yaşa yake biye maka, kake yadda ka so,
yake nuna maka wai shi nan kauna yake gwada maka.
Te a lokacin zaka nemi kaunar da yake maka, kа
rasa. Bayan ya kaika ya baro. Kuma kai ma da kanka ka
cutar da kanka da rayuwarka, tun da lokacin da yake
fasa maka kai, ka fi kowa gadara da nuna ka isa da
fadin ran kai wani ne.
Allah ka shiga tsakaninmu da irin wadannan
batattun. In kuma masu ganewa ne, Allah ya ganar
dasu. Gaje ita ce diyar Dan-tani ta farko da ya haifa,
sannan tana da kanni guda biyu, dukkansu maza.
Mahaifiyarsu Gaje macece ta kirki da ta san
abinda take yi, tana da kyawawan halaye da ake
kwatance da ita a cikin kanyensu. Don haka Ya'yanta
dukkansu halayyar uwarsu suke da shi. Basu da rigima.
Da akwaisu da hankali da biyaya da girmama na gaba
da su.
Abu kamar wasa. Da sannu-sannu Lamido yana
ta shigewa Gaje, babu dama Gaje ta shukawa Lamido
rashin mutumci, dan bata gaje shi ba, sannan kuma ta
MAMAN FADILA 12
san gidansu, ko kuma in ce mahaifinta da Mahaifin
Lamido yake tundakoa kauyensu.
Kuma in ma rashin mutuncin ne, ta san Lamido
shine shugaban rashin mutumci. Dan haka take bin shi
da sannu.
Haka mutanen gari da suka kawo na mujiya,
suka zuba musu, babu wanda ya isa ya bincika, ya san
ko meke faruwa tsakanin Lamido da Gaje, wanda ko ita
Gaje ba wai ya fada mata yana son ta bane.
Ita dai suna gaisawa. Gaje ta gaji ta sanar da
mahaifiyar ta irin abin da Lamido yake mata. Mahaifiyar
ta ta gargadeta akan ta bi a hankali, ta san irin huldan
da zata yi da shi.
Ranan juma'a da rana, bayan saukowa daga
masallacin juma'a. Binto da Gaje sun kuro adaka. Gaje
ta baje fuskarta da kwalliyar nan da ta saba. Dukkansu
da kwanukan tallansu a kansu za su nufi kasuwa.
Suna isa kasuwa, suka tarar da Kandala da
Laure suna zaune inda suka saba zama. Binto tace ma
su Lante "To da ba ku jiramu mun zo tare ba, kuka
rigamu zuwa. Ina fatan kun sayar da kayan tallan naku?
Kandala tace "Ko dai bamu sayar duka ba, ai
mun kusa." Lante tace "Ke ma kika bata amsa. Dole ne
sai mun zo a tare? Gaje tace "Kai Bainto, dan Allah mai
yasa kika ta da wannan mana magana?
Tunda sun taho, ai ba laifi suka yi ba, tunda sun
riga mu kammalawa, ai bai kamata su bata lokacinsu
ba, dan haka ba laifi bane.
DA SANNU.... 13
Duk wanda ya riga shiryawa a cikinmu, to ya
tafi. Ba sai ya tsaya jira ba. Dan Allah wannan magana
mu barta, kada ta haifar mana da wasu korafi a
cikimu."
Duk abin nan da ke faruwa. Lamido yana gefe
yana jinsu, saboda haka ya matsu kusa da su ya tambayi
ko kayan tallan na nawa Gaje ta dauko? Gaje ta sanar
da shi. Yace "Na dari da ashirin? Take anan Lamido ya
sa hannu a cikin aljihu, ya ciro Dari biyu, ya mika mata,
yace ki raba ma masu sha'awan ci."
Ya kara gaba ya bar Gaje da kudi a hannunta.
Wata sabuwa! Kowa cikinsu yayi zugun-zugun. Gaje dai
bata iya rabawa kowa kayan tallanta ba. Haka ta koma
gida da kayan tallan nata.
Tana shiga cikin gidan su, ta samu mahaifiyarta
a bakin murhu tana zaune, tana fama da iza wutan kara.
Abinda Gaje ta fara fadi, kafin ta sauke kwanon tallanta
shine "Umma kin kuma ga ta yadda Lamido ya koma
min? Dari biyu ya ban, yace wai in rabawa duk mai
sha'awan cin waran nawa. Ni dai ga waran nan na dawo
miki da ita gida."
Kafin Umma tace wani abu. Dan-tani ya budo
asabari ya fito yana fadin "Ke Gaje, ina dari biyun take?
Lalatacce, kila Dakaci ne ya aiko shi ya kawo min. Shine
zai yi miki haka. Kun san Lamido dan shiririta ne. Miko
min. Ina fatan dai ba ki rabawa kowa awaran ba?
Umma da mamaki ya rufeta, ta ma rasa kome
zata ce. Sai ta cewa Gaje dan haushi, "Mika masa dari
biyun, ko ta rabar da awara, ko bata rabar ba, wannan
MAMAN FADILA 14
kuma bata shafeka ba." Shi dai Dan-tani tunda ya karbi
dari biyu, ya tura ta aljihu, ya nufi kofar gida, yana
sababi.
"Ke dai Lantana ba ki da ganewa ne. Daga
tambaya, kamar nace wani abu. To ko dai dari biyun
kuke so, in bar muku? Ita dai Ummah bata kuma bi ta
kan Dan-tani ba.
Ta maido kanta kan kwanon awara. Ta bude
tace "To yanzu Gaje. Ya zamu yi da wanna awaran? Ga
shi da cikon kudin man gyadan Dela da ban cika mata
ba." Gaje tace "To ai ke ce Ummah, ya za ki ce in ba
Baba dari biyun.
Wallahi ba cewa yayi na kawo masa ba. Shi dai
ya karba ne kawai. Kin san halin Baba da kudi." Ummah
tace "To ban da abinki Gaje, yanzun wa ya isa ya hana
dari biyun? Ke ma kin san muka ja, to ba mu nemi
zaman lafiya ba, yau a cikin gidan nan.
Ke dai kawai yanzun abin da zamu yi, shine ki
dauki kwano awaran nan ki je da shi bakin makarantan
allon Malam Lado. In sun tashi, ki zauna ki dunga sayar
musu da awaran biyu, biyar. Maimakon guda daya biyar.
Kin ga sai mu rage asara."
Gaje tace "Ummah biyu, biyar kika ce? Ai
asaran zata yi yawa. Ki bari kawai na dauka na je bakin
masallaci. Insha-Allahu zai kare. In kawo miki kudinki
daidai."
DA SANNU... 15
Lamido suna zaune gindinwata bishiyar mangwaro shi
da abokan shi. Kuma magoya bayan shi, su kadai suke
ta zuba surutu. Suna shaye-shaye. Shi ko uban gaiyar
zukan sigarin shi kawai yake, yana busa hayaki, baya ko
sauraransu, sannan ga mutane na kauyen da suke
kaiwa da komowa, babu mai kulasu.
Cikin magoya bayan Lamido na kusa da shi,
yace "Oga na ga alaman yarin ar nan tana so na fasa
kwakwalwanka. Ma fi lokuta, muna tare da kai, sai mu
yi tattaunawa akan abubuwan da suke damunmu.
Sal u ga gaba daya kai hankalinka baya tare
da mu. Kuna da ba ma samun irin haka a gareka, sai a
'yan fara huldanka da Gaje. Kuma a tunaninmu mun san
ba za ka iya auren Gaje ba."
Lamido ya kashe sigarin da ya ke hannun shi,
yace "Da waye ya fada maku ba auren ta zan yi ba?
Wannan tunanin da kenan kuke i, ni yanzun auren Gaje
nake son yi. Yarinyar ne ta kasa fahimta. Ka kullum
nuna mata alamomi nake yi. Sai dai bata fahimta."
Cikin magoya bayan shi gu.la yace "To oga ba ka
fitowa fili ka sanar da ita ko kuma ka ba mu izini mu mu
sanar da ita, ko tana so, ko bata so. Dole ta amsa."
Lamido yate "Maganar in baku izini, ku sanar
da ita, duk wannan bai taso ba, dan baso nake ku firgita
min ita ba. Ni da kaina zan sanar da ita, ku kwantar da
hankalniku, ku ban lokaci, ku gani. Yanzu dai mu ci
gaba da abin da yake damun mu."
MAMAN FADILA 16
Kandala da Binto suna kofargida, suna Yar gala-gala
Lante ta sheko da gudu tace Binto. Kandala ku zo ku ga
ikon Allah. Abu ya fara nisa. Lamido da Gaje ga suna
nan suna tahowa tare, ko daga ina suke? Oho?
Kandala tace "Ku mu tsaya anan, kun san
Lamido bai da mutumci, yanzun ya ga mun dubesu da
sunan muna kallonsu, to Wallahi karshenta mu
wulakanta, koda kuwa bai kulamu yanzu ba, saboda
haka mu ci gaba da 'yar gala-galan mu kawai. Mu nuna
basu muke jira ba."
Sun mayar da himma ga yin 'yar gala-gala.
Kaman basu san da wucewar su Lamido da Gaje ba.
Gaje da Lamido suna isowa daidai inda su Kandala
suke. Gaje ta ja birki ta cewa Lamido "Ni fa nan zan
tsaya, dan ni ma gala-galan zan yi."
Lamido yace "To ni zan koma, sai dai anjiman
kenan, zan zo." Su dai su Binto ba su nuna hankalinsu
na wajen su ba. Sun dai ci gaba da yin gala galan su.
Har Lamido ya juya, bai kula kowa cikinsu bа,
tunda shi daman tun farkon shi ba wai yana kula 'yan
matan kauyensu bane. Bayan tafiyar shi da jimawa. Sai
duk suka tsaya da wasan gala-galan da suke.
Kandala tace "Mu dai gaskiya Gaje mun gaji da
sa miki ido, muna kallon ki muna tsoron yin miki
magana, wai ke mai ke tsakaninki da Lamido ne? Kо
sonki yake ne? Lante tace "Gaskiya kan babu mamaki,
kulıum abu sai gaba yake dada yi, ba mu san dalili ba."
DA SANNU... 17
Binto tace "Kuma da kuka fi kusa da ita kenan,
ballantana kuma mu. Ai gara dai ki yi mana bayani, ki fitar damu duhu."
Gaje tace "Allah sarki, in kuwa ni ce zan fitar
da ku duhu akan zargin da kuke yi, to gaskiya ba ko zą
ku ga haske ba, dan za ku dauwama cikin duhu, dan ni
dai babu wata kalmar so da ta gifta a tsakanin na da
Lamido.
Ni dai kawai a nawa ganin Lamido yana yin mu
wasu abubuwa ne, saboda irin dangantakar da ke
tsakanin mahaifina da nása mahaifinsa. Kuma kun san
Lamido irin gogagun 'yan matan da yake kulawa. Ni ba
irin kalan su bane.
Kuma kuma kanku kun san irin mugayan
halayen Lamido, babu yadda za ayi ko da ya furta yana
sona. Ni in kaunace shi. Da in auri Lamido. Gara na
mutu ban yi aure ba, dan haka duk wani tunani dake
cikin zuciyaku da zargi, to dan Allah ku bar shi."
Lante da Binto suka ce "To babu soyayya a
tsakaninku, amma kuma yake sanar da ke cewa sai ya
zo anjima? Gaje tace "Ni ma wannan abu da yace, sai
ya zo ya daure min kai, kuma ban san kome zai kawo shi
ba, dan haka hakuri za ku yi min da sannu har ya zo, sai
ku ji ko menene zai kawo shi. Sai na sanar da ku."
Gaba dayansu suka ce "Shi kenan Allah ya sa
mu ji alheri, ya kuma kareki daga shrrin Lamido." Suka
kama hanya gaba dayansu suka nufi gidan wata amarya
da suke zuwa, suke wasanni a gidanta. Da yake yarinya
ce karama, kuma ba 'yar cikin nan kauyen bace.
MAMAN FADILA 18
Daga wani kauyen aka daukota. Ba wai ta san
mutane sosai bane a kauyen. Mijinta Dan-uwan su
Kandala, ne shi yasa suka saba da amaryan. Dan suna
zuwa su tayata zama.
Safiyar alhamis da sanyin safe. Gaje ta dauki tulu ta
nufi bakin kogi, dan ta dibo musu ruwan. Da za su yi
alwala da wasu aiyukan. Abin mamaki abinda bata tabaа
gani ba.
Wato Lamido ne zaune bisa wani dutse yayi
tagumi shi kadai, sai kuma sauran mutane da suke
zuwa diban ruwa. Kowa yana abinda daya kawo shi. Dan
wasu dai wanki suke yi.
Da hanzari Gaje ta ja da baya, ta tsaya. Lamido
yayi dariya yace "Karaso mana." Ya mike daga inda
yake, ya karasa wajenta yace "Kawo tulun, na dibo miki
ruwan, tunda kin kasa karasawa, ki na mamakin ganina
a bakin kogi ko?
Ya karbi tulu ya shiga daga cikin kogin kadan,
ya dulmiya tulu ya ciko shi da ruwa. Ya fito yace "To mu
je na kai miki gida." Gaje tace "A'a ka bar shi na gode."
Suna cikin tafka gardama. Sannan Lamido yace "To mu
je na rakaki." Da kyar Gaje ta dauki tulun ruwan, suka
tafi.
Sun fara tafiya. Lamido ya karyi wata sanda
yace "Gaje jiya ban samu zuwa gidanku ba, kamar
yadda nace miki. An samu akasin zuwan nawa ne, shi
yasa yauna buga sammako na zo nan, dan na san za ki
DA SANNU... 19
zo. Dama musabbabin zuwan nawa, shine don na zo ne
na warware miki abinda yake damuna ne.
Ina kuma fatan in na sanar da ke, za ki taimaka
min, ki amince min abinda zan fada miki? Ita dai Gaje
cikinta ban da kululu da yake, ba ya komi, duk ta kosa
ta ji manufar tasa. Lamido ya dubeta yace "Ina fata kina
sauraran abinda nake fada miki? Gaje ta daga masa
kai, ba tare da ta dubi fuskar shi ba.
Ya ci gaba da magana "Gaje ina son ki sani, duk
fadin kauyen nan da kauyakun dake suka kusa da
namu, duk na duba, na hanga, na yi tunani, nayi
mafarki, babu wata diya mace da tayi min, ta kuma
dace na aura, face ke kadai Gaje."
Gaje a razane bata san yadda aka yi tulun
ruwan da ke kanta ya tangado kasa ba. Ya tarwatse ba,
duk ruwan ya fancalan ma Lamido ba. Ya jika shi, amma
Gaje bata kula ba, ta rike kugunta tace "Haba Lamido,
ka san abinda kake fadi kuwa?
To Wallahi tunaninka da hange-hangenka da
mafarkinka duk sun raya maka karya, ba su sanar da kai
gaskiya ba. Ni na ma zata dalilin dangantakar dake
tsakanin iyayenmu ne, yasa kake bani kulawa sosai.
Gaskiya tun wuri ka yi gaggawan janye wannan
furuci naka. Na aure a tsakaninmu. Don gaskiya abu ne
da ba zai taba yuwuwa ba, ka yi hakuri, ni ba irin
matarka bace. Ka yi mini hakuri, dan Allah."
Gaje bata jira ko sauraran wata kalma daga
bakin Lamido ba, ta kara da gudu, babu ko waige. Koda Gaje ta shiga gida, tana haki. Lantana mahaifiyar Gaje
MAMAN FADILA 20
tana wanke tukunya. Ta dakata da wankin tukunyar da
take tace ma Gaje da ke kokarin tusa kai cikin daki "Ke
Gaje, menene haka?
Ina ruwan da kika je dibowa? Ba da ke nake
magana bane? Wai ke shin kuwa lafiya kike, na ganki a
rikice kike. Me ya faru ne? Dan ke ba ki da wuyar
rikicewa." Gaje a sargafe tace "Lamido ne?
Da sauri Lantana tace "Me Lamidon yayi miki?
Ta kamata tace "Yi mini magana mana? Ta girgizata
Gaje tace "Cewa yayi wai shi yan sona zai aureni...
Dan-tani mahaifin Gaje da ke cikin daki da 'Yar
Rediyo da ya kunna kamar yana sauraron abinda ake a
Rediyo din. Ashe ba haka bane, su Gaje yake sauraran
abinda suke fadi.
Da dai ya ji Gaje tace "Lamido yace zai aure ni."
Ai bai san yadda aka yi ya tunkude Rediyon da ke gaban
shi ya bankado a sabari ya fito, yana fadin "Allah mun
gode makа.
Diyata zata auri Dan Dakaci. Wannan abu yayi
kyau. Allah yayi miki albarka. Zan je na ga Dakacin da
kaina, na ji ko ya san abinda ake ciki."
Lantana tace "Wai kai dan Allah wane irin
mutum ne da ba ka yin tunani da kallon abinda zai je, ya
zo? To in ma mafarki kake, ka farka, dan ni diyata ba
zata auri wannan yaron mara tarbiya da bai da
kyawawan halayya ko na kwayan zarra ba. Allah ya
kiyashemu da auren irin wadannan. Gidan da ba su da
mutumci." Dan-tani yana mazurai yace.
DA SANNU.... 21
"Lantana kin san abinda kike fada min kuwa?
Ni kike cewa bani da tunani? To Wallahi ba wai hangen
abinda zai je ya zo bane bana yi ba, ko abinda zai tsaya,
ya zauna ne. Muddin Dakaci ya amince da auren Gaje
da Lamido.
To fa dole ba makawa, ba kuma fashi. Ni sai па
daura auren Lamido da Gaje. In ga inda Uban daya
haifan min ita. Ya isa ya hana. Gaje kuka take
Yayin da Lantana ta ga irin yadda Dan-tani ke
ruwan bala'i yana fadan son ranshi. Ita ai sai ta kama
bakinta, bata kuma kula shi ba. Sai ma ta rungume Gaje
tana lallashinta.
Lawai da Sa'idu kannin Gaje suka fito da kwano
daga cikin daki. Hannunsu duk miyar tafasa, suna fadin
"Ummah ki kara mana dumaman tuwan, ba mu koshi
ba."
Gaje kwana biyu ta daina zuwa dandali. Haka
kuma zuwa tallan waran ma, ta daina, sai dai su Lawai
ne suke daukar tallan awaran. Haka ma zuwa yin wasa
wajen kawayenta, shi ma bata zuwa. Su Binto da
Kandala da Lante su na 'yar larakke.
Sai ga