Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
ji da kanka ba ka isa ka auri matar wani ba. Komai mulkinka, dan haka Gaje matar Baba Magaji ce, ko kuna so, ko ba kwa so. Allah ya rubuta, ita matar shi ce. Ku bacin iko na Allah, kun taba tunanin haka zai kasance? To kuma sai ga shi ya kasance. Saboda haka duk wata magana, ku yi hakuri, ku barta, ku jira dawowan Angon." Hajiya Safiya da ke zaune ta kasa cewa komai, sai sauransu da take yi, kowa yana fadin albarkacin bakin shi. Tayi murmushi tace "In ya dawo, ki sanar masa. In dai Magajin Hakimi ne mai nema a duhu. Sannan kuma iyayenmu, in kun gama sharhin, akan abinda aka yiwa Babanku Magaji, kuna iya ku bamu wuri, tunda ku kuka haifemu. Dole ku fada mana ba mu yi daidai ba." Hakimi yace "Ai ni ba ki ji na yi shiru bane. Ai ance shiru ma, magana ne. Ni dai ba wani na yiwa aure ba. Dan-uwana da na isa da shi na yiwa, dan haka babu ruwan kowa, mun fi kusa. Sai kusa ido ya zo ku ga in na isa da shi. Dan haka in kun gama, ku bace min da gani anan." Suna fita. Hajiya Safiya tace "To Ranka ya dade, wai ya aka yi haka ne? Yaran na fa suna da gaskiya, ka kuwa san irin 'yan matan Magajin Hakimi? Kuma ka san DA SANNU... 59 halin shi da son tsafta, ga shi da saurin kushe abu. Amma tashi guda ka yanke masa irin wannan hukunci. To gaskiya duk da ban san dalilin da yasa kai haka din ba. Ni dai shawaran da zan ba ka, shine baba mamaki Magajin Hakimi yana da yarinyar da yake so ya aura, dan haka tun da ka yi masa laifi. To in har ya z0 mana da maganar wata yarinyar. To mu amince masa, ya aurota, ya hadasu su biyu. Kada mu nemi mu hana shi. Ita kuma Gaje da yardan Allah, ni kaina zan dunga taimaka mata ina koya mata wasu abubuwan da bata sansu ba. Bata iya ba, zan kuma sa Nusaiba in sun dawo hutu, ita ma ta dunga taimaka mata, tunda tasu ta zo daya." Hakimi ya ji dadin maganar uwar gidan shi sosai. Da shawaran da ta ba shi kuma. Anan ya bata labarin Gaje, tun ranan da ta zo ganin shi, sannan kuma ya fada mata yadda Allah yayi hukuncin shi, auren nata bai yuwu da Lamido ba. Ya ci gaba da fadawa Hajiya Safiya "Wallahi ni ina tausayawa Gaje ne, ga ta yarinya ce, 'yar kauye. To amma da zata samu wayewa, ba karamin ci gaba za'a samu ba, dan tana da tarbiyya, ga hakuri, ga gaskiya tana kuma da biyayya. Ina tausayawa yarinyar nan, muddin ta auri wanda bai san ciwon kansa ba, duk za a nemi wadannan halayye nata, a rasasu. Sannan ga shi mahaifinta ba wai ya san abin da ya kamata bane, yana iya ya kara hadata da wani wawan. MAMAN FADILA 60 Dan haka ni kuma nayi saurin yanke hukunci, nace ni na hadata da Magajin Hakimi. Kuma in Allah yasa, ya yarda wannan aure da na hada. Sai ya zame mana alheri gaba ki dayanmu. Da yardan Allah ba zan ji kunya ba." Hajiya Safiya tace "Allah ya yarda, to yanzu ya zamu yi, mu da maganan biki? Ka ga ya zama dole dangi su zo wannan biki na Magajin Hakimi. Autan Hakimi, kada ka sa mutanen birni su tsiremu." Hakimi yace "Biki ai ya zama dole ayi shi, а cikin gidan nan. Ni na isa. Daman anan min korafin na ki in koma birni da zama. 'Yan-uwana suna ta korafin na rabasu da Dan-uwansu Magajin Hakimi. Bai ko son zama cikinsu sosai. Komai sai ni ya sani, dan ba sa son gaskiya. Koma a ina muke, ai dole ni ya sani. Yanzu abinda da zamu yi, shine gidansu Gaje su ci gaba da shagulgulan bikinsu su kawo mana amaryanmu. Bayan kwana biyar zan tura a dauko min Magajin Hakimi, in muna masa matarsa da na aura masa. Kuma a lokacin zamu sa ranan biki. Ni da kaina zan je birni na sanar da su, an daura aure. Saboda an samu hatsaniya akan daura auren, in basu hakuri, in sanar dasu taron bikin ranan da za ayi, kin ga sai ku taru ku tashe, ana bikin Auta. Insha-Allahu su ma ba zan samu matsala da su ba. Dan haka yanzu zan sa a gyara can bangaren. Akai amaryan can, kin ga babu ruwanmu da su. Sai dai in sun shigo, ko kuma mu mun shiga. Kin ga mun DA SANNU... 19 basu tazara, babu mai sanin abin da kowa ke ciki. Sai in kai ne ka so a sani." Gajeaje na can ita da kawayenta. Kowa yana tofa mata albarkacin baki shi. Lante ce zaune can bakin kofa, tace "Wai ke ko Gaje ba ki gudun Wulakanci, kika yarda aka daura miki aure da Kanin Hakimi, wanda tunda muke. ba mu taba gani kalan shi ba. Shi kenan kullum vana wajen karatu." Binto tace "Ai ba mu ba, ki ce Yayyinmu ma ba su saniba. k ni fa yadda na ji iyayenmu na fadi, duk Cokin dagin Hakimi babu wanda ya kai shi kasaita. Kо yaushe yana gida. Karewa ma sai ka je gidan, duk ka yi abin ua ya kaika. ka gama ba ka san yana gidan ba. Sai ko in abın va ritsa shi ne zai yanke hukunci. To shine kawai za ka gan shi." Aandela tace To ai ni abin da ban gane ba, shine wai shi ne vace yana son ya aureki? Gaje tace "Ni ma ban sanı ba. Sai dai ku je wajen Hakimi da ya zo ya nemi auren nawa, ku tambaye shi. Kuma ku sani duk ta wahalan da zan sha da wulakanci, ina ganin zai kai na gidan Lamido ba. Da na aure shi." Kandala da Lante, har suna hada baki, suna cewa. "To wai ke shin menene dalilin da yasa aka fasa aurenki da Lamido? Gaje tace "Shi ma ban sani ba. Sai da ku je ku tambayi Dakaci da ya zo, yace sun fasa." Binto tace “Na ma fuskanci abin naki oa rainin hankali MAMAN FADIL.A 62 a ciki. Ai da mun isa mu je, mu tambayesu da ba mu tambayeki ba." Deluwa da bata ce komi ba, tana zaune kusa da Gaje, tayi murmushi tace "Ku Wallahi ban san abin da ke damunku, ba ba za ku daina halayyan ku ba. Inda na barku haka na dawo na sameku." Binto tace "Ai ke fa yanzun tunda a ka je da ke birni, kika dawo kike mana sanabe kala-kala. Sai ka ce ba mu san asalin angulu ba. To Wallahi shege ke rainа mafarin shi. In ma za ki saduda, ki koma asalinki, ki koma." Kandala tace "Da dai ya fi mata sauki. Kuma wai ma me ta sani daga dawowar ta ita? Ba da ita aka shirya komi ba, za ta zo ta dunga mana wani gani-gani." Lante tace "To mu in har mutum yace zai kawo mana raini, ba sai mu dauki mataki a kai ba." Gaje tace "Ya isa haka, duk abin ai kai nan ba. Daga fadan gaskiya. Sai kuma ya nemi zama fada? To dan Allah kowa yayi hakuri." A wannan lokacin Lawal ya shigo, ya sanar dasu ga mai kidan kalangu nan yana kofar gida. Yana kiransu. Kandala ce tace "Ku bari kawai na je na shigo da shi ciki. Ku ku ci gaba da shirinku, da akwai wadataccen fili a gidan su Gaje. Dan haka da aka shigo da mai kalangu, aka yi masa shinfida shi da yaran shi da kuma kujera. Take ya fara kida. Mata 'yan biki suka fara cashewa. Bayan dan takaitacen lokaci. Ita ma amarya da kawayenta suka baiyana a cikin filin suka fara DA SANNU.... 6.3 karairaya. Nan dangi da abokan arziki suka yi zuciya, suka dunga balo lalita, suna fito da dan tsumin su da dabaransu, suna yin kara, suna ta like amarsu. Abin mamaki sai ka ce daga sama. Kowa ya je ya sanar da gidan Hakimi cewa amarya ta fara cashewa? Uhm!. Auwal da Nusaiba da Naziyatu da kuma wasu daga masu aikin gidan Hakimi, duk suka zo suka dunga yin mata ruwan kudi, suna mata liki. Wannan abu ya kwantar da hankalin Lantana. Mahafiyar Gaje, har da ma ita kanta Gaje. Sabo da irin yadda iyalan Hakimi suka nuna a wajen, mussanman ma Nusaiba, ta fi kowa zakewa. Suna gama liki, suka shiga mota. Direba ya tukasu, suka koma gida. Da yamma Hakimi ya tura motoci aka tafi daukan amarya. Naziyatu ta fito a guje ta tsugunna bayan Hajiya Safiya da take zaune, ita da mai aikinta. Naziyatu dariya kawai take. Sai ga Nusaiba ta fito, tana haki, ta doshi Naziyatu da sauri Hajiya Safiya ta tareta, tana fadin "Dakata, haba Damo, me ya hadaki da 'Yar-uwan ta ki? Nusaiba tana hakuri, amma in har ranta ya baci, bata da kyau, dan ga haka Hajiya Safiya tayi saurin tareta. Tana lallashinta, tana kuma tambayarta. Ita dai Naziyatu har yanzun dariya take yi kawai. Nasaiba tana tsaye, ta kasa cewa komi. Saboda takaicin abin da tayі mata. Hajiya Safiya tace "Naziyatu kadan ba ki daina dariyar da kike yi ba, zan yi mugun saba miki. Wannan wane irin sakarcin banza kike yi haka, ki dunga dariya, MAMAN FADILV 64 sai ka ce wacce kika yi gamo. To ki kama kanki. Kuma me kika yiwa 'Yar-uwan ta ki. Da har ta biyoki nan, zaku yi fada? Naziyatu tace "Wai Hajiya tunda muka dawo, na zauna ina ba su Amira da Yakubu labarin irin shigar kwalliyar da gidanku da rowa tayi. Da kuma irin rawar da take yi. Wai dan me zan dunga kwatanta musu, mu na dariya, shine ta haumu da sababi. Ni kuma ba mu fasa dariyar ba. Dan Allah Hajiya, in dai ba neman masifa ba, ina ruwanta? Wallahi in dai kan irin haka ne, to ba ki ga komi ba. Karewa ma ma sai Baba Magajin ya dawo tukuna, dan na san da akwai rigima sabuwa. Gidanku da rowa, ita ce matar Baba Magaji." Hajiya Safiya tace "Wai ke wace irin mutuniyar banzan ce? Shin Gaje ba mace bane kamarki ba? Da me kika fita da kike wani surutu, ki bari ki gani. Sai kin sha mamaki, dan in Gaje ta samu kulawa, ta fi ki. Dan haka bana son na kuma jin wani gutsuri tsoma akan Gaje. Ke kuma Nusaiba bana son kina biye mata, duk ku zama marasa hankali. In har zancen take so, ta je ta samu Babanku shi da ya kulla komi.... ".....Gafaranku dai, ahuwo masu gida. Tare da kaya. Kayan mutane." Masu kawo amarya su ne suka shigo tare da guda. Da sauri masu aiki suka yi musu jagora zuwa bangaren da Gaje zata zauna. 'Yan kai amarya, suna shiga. Nan fa kallo ya koma sama. Ba wanda ya kuma bi ta kan amaryan, sai kallon tsarin dakin da cikin DA SANNU... 65 gidan. Kowa ya nade ka a, ya zauna yace shi ma kwana ya kai a cikin wannan daulan. Su kuwa lyalan leld, tunda smka zo suka yiwа amarya barka de sauka. Da ara kome watwayensu ba. Suka barsu da masu aikin dan. Suka ci gaba da kulawa da su. 'Yan-uwan Gəje sun kwana sun hantse, anyi mata budan kai. Kowa ya watse, an bar amarya da halinta, dangi da kawaye sun koma gida. Suna zunde. Babu ango, tsegumi dai irin namu na mata da baya karewa. To da sh,i ko wacce ta koma gidan ta. Hajlya Sallya ta shigo tara da wata tsohuwar mace. Ba kuma tschuwa con ba. Suka samu Gaje zaune a kasa ta kama kumatanta. Tana ta kuka. Da sauri Hajiya Safiya ta kamate, tana lallashi, tana bata hakuri "Haba Gaje, ki yi hakuri, kowa kika gani, gidan mijinta. Haka aka rabota da lyayenta da dangita. In ban da aure, wa ya isa yayi miki haka? Ki fito gidan kudi, ki fada gidan talauci. Babu kudin, kuma ki zauna dole ki yi biyayyan aure. Abin da ba ki lya ci ba, dole ki iya ci. Aikin da ba ki taba kwatantawa ba, dole ki yi shi. Zanin da kike takama kin karfin daurawa, ki daura, wanda bai kai shi daraja ba. Bayi (Toilet) din gidanku kadai. Sal ya sai gidan da kike zaune da mijin ki da abin da ke cikin shi. Aure kenan. Yakin mata In ba auren ba, wa ya isa yayi miki wannan juyi haka? MAMAN FADILA 66 Kuma aure sai ya dauki 'Yartalaka, wacce basu da kəmi iyayenta ma bara suke. Ya hadata da gidan masu mashahurin kudin gaske. Gidan da suka amsa su masu kudin ne, masu mutunci da suka san abinda suke. Ba gidan mu na da kudi ba. Kudin bai wuce cikin cokali ba. Sun ishi duniya, su masu kudi ne. Iskanci kwando-kwando da isgilanci. Wai suna da kudi. Irin wadannan in har talaka ya shiga cikinsu da sünan aare, ya kai shi, to sai dal ya rungumi kaddara kawał, dan tijara kala-kala. Kin shiga gani ke nan, har sal ran da Allah ya yanke miki. Allah dai ya ganar da irin wadannan masu kudin kece raini, akan talaka. In ko Alah yasa aure ya daukeki, ya kaiki gidan masu kudin arziki, to kiyi hamdala kawai, dan za ki sha mamaki, za ki ga yadda aketaliafawa talakawa. Dangiki kuwa, sai kin zame musu abin alfahari. Saboda haka shi aure duk inda ya kaiki. To ki yi hakuri da juriya, dan haka ki daina kuka. Kinga Lanti nan, na kawo miki ita. Za ta zauna anan bangarenki, tana kwana. Duk wasu aiyukan da ya dace, ita zata yi. Duk wani abin na cikin gidan nan da ba ki sani ba. To ki tambayeta, zata yi miki bayani. KIyi hakuri. Hakimi zai aika a taho miki da mijinki kwanan nan." Kwanan Caje biyar a gidan mijinta. Hakimi ya gama shiryasu Kasailba saka koma makaranta gaba dayansu. Naziyatu tayi korafin komawar nasu da ba su ga zuwan Magajin Hakimi ba. DA SANNU... 67 Dan su ga irin diraman da za ayi. Allah Sarki! Naziyatu tana shirmenta ne, ta manta sarauta, ai ba karya bace. Gidan sarauta ba a ja da su, ba ayi musu gardama. In sun yi magana daya. Ba sa canjawa, dole ayi biyaya. Sun tafi da kwana biyu. Hakimi ya tura aka kawo masa Magajin Hakimi. A lokacin ya rage saura kwanaki ne Magajin Hakimi ya karasa digirin din shi. Rashin sani. Gaje ita da kawayenta su Binto da Kandala da sauransu. Yau ne Gaje ta cika kwana bakwai a gidan Hakimi, dan haka yau ne ranan da kawayenta suka zo mata yini. Bayan sun ci, sun koshi, shine suka baro bangaren Gaje, suka samu zaure su ka zauna, suna 'yar carake, wai suna gudun kada suyi a sasan Gaje, su fasa tayal din gidan, ga shi kuma Lanti mai aiki, bata nan, balle ta sanar da su, bai kamata su je zauren ba. Sun mai da himma, suna carake. Yayin da Gaje ta a je hannunta kasa. Lante tana dunkula hannunta. Tana dakawa bisa tafin hannun Gaje. Daidai wannan lokaci Magajin Hakimi ya shigo cikin zauren. Yana ganinsu, ya ja ya tsaya ya hada giran sama da kasa, ya daka musu tsawa, yace "Kai daga ina kuke, kuka zo nan? Za ku kawo mana sakarci. Maza ku tashi ku bace min da gani." Jikinsu yana rawa, za su yi magana. Ya kuma cewa "Ku rufe min baki, mahaukata kawai. Dubeku, MAMAN FADILA 68 sakarkaru da ku, in har kuka bari na dawo, na iskeku, sai kun gane kuranku." Yayi gaba ya barsu jiki na rawa. Gaje tace "Shi kenan mun shiga uku! Kandala tace "A'a kin dai shiga uku, dan ni daga nan, ko sasanki ban shiga. Ko takalmina ban shiga dauka." Saurąn suka ce "Mu ma din ba shiga zamu yi ba. Tunda ba mu san ko shi waye bane. Da yake mana wannan bala'in. Ke dai da kika jawowa kanki shiga gidan sarauta, sai ayi miki ke kadai, mu kin ga tafiyarmu." Gaje tace "Ni ma ba ni na jawowa kaina ba. Haka Allah ya kaddara min." Deluwa tace "Kin ji Gaje, rabu dasu, wasu mutane ne ki ganin gidan sarauta da akwai tsanani. Rabu da su, babu wani tsanani. Su sakarci ne basu yarda da shi ba. Da shiririta, kuma tun kafin mu zo zauren nan, sai da na fada muku kada mu Z0. Su Binto suka yo min caa! Zan kawo musu iya yi. Ki yi hakuri, mu koma sasan naki, in kwaso mana takalmanmu, in bi su, kada su sakani a dandalin gada anjima. Kuma shi wannan din da ya zo, ya rufemu da sababin, kin san shi ne? Gaje ta girgiza kai, tace "Ni ban san shi ba. Amma anan gidan yake, dan da akwai hoton shi da suka dauka shi da Hajiya da Hakimi da kuma wanda yake shi daya a cikin falon Hajiya." Deluwa tace "To ko shi ne mijin naki? Gaje tace "Ni dai ba su ce min ba. Kuma Insha-Allahu ba ma shi bane, dan in shi ne, ban san yadda zan yi ba, kin ga DA SANNU.... 69 mutum a tsaye, babu alamun sauki a tare da shi. Deluwa tace "Kila ma in ta dauro, ba dan cikin gidan bane, kin san 'yan cin arziki sun fi kankaba da iya, yi." Magajin Hakimi yana zaune kusa da Hajiya Safiya. Sun yi zurficikin hiran da suke. Sai ga Hakimi ya shigo. Da yake shi ya umarci Magajin Hakimi da ya saurare shi anan dakin Hajiya Safiya. Da ya shiga. Ya gaida shi. Hakimi na shigowa. Magaji ya mike tsaye, sai da ya zauna, sannan shi ma. Ya zauna. Sannan shi ma ya zauna. Hakimi yayi gyaran murya, yace "Magajin Hakimi, na aika a zo min da kai ne, dan na sanar da kai na yi maka mata. Satin da ya wuce, aka daura maka aure da ita. Yanzu haka ta na nan gidan. Yanzu zan tura Hajiya ta je, ta zo da ita." Magajin Hakimi, yayi shiru yana sauraran Hakimi. Can dai yayi karfin hali, yace "Yar Sarkin wane gari ne? Hakimi yayi murmushi yace "Ta yaro kyau take, bata karko. Ba 'Yar Sarki bace, ba kuma 'yar Hakimi bace, kamar ka ba." Magajin Hakimi yace "To 'Yar wane attajiri ne? Hakimi yayi dariya, yace "Hajiya Safiya, ki na jina da Danki ko? Hajiya Safiya ta dan murmusa kadan, tace "To ai ba laifi bane, dan yayi tambaya. Ka sanar da shi ko Yar waye." Hakimi yace "Bude kunnenka, ka ji abinda zan fada maka. Sunan Yariyan Habiba. Amma Gaje ake kiranta,kuma ba 'yar attajiri bane, ba kuma 'yar Malami bane, ba kuma 'yar dan boko bane. Ko ma'aikacin gwamnati ba. MAMAN FADILA 70 Gaje 'yar talakanmu ne a cikin kauyen nan. That is end! Magajin Hakimi idon shi jajur, yace "Yanzu Baba Hakimi, kana ganin cikin kauyen nan da akwai yarinyar da ta dace da ni a matsayin matata? Hakimi yace "Ga shi kuma na fada maka. Ai magana ta kare. Ke Hajiya Safiya je ki zo min da Gaje." Hajiya Safiya ta samu Gaje a sasanta, tayi tsuru-tsuru da ita, tace mata "Ke lafiya, na sameki haka? Gaje tace "Dama yanzun nake so na zo na fada miki yanzun nan muna wasa ni da kawayena. Wani mutun ya wucemu, yana ta mana masifa. Yace kada ya sake ganinmu. Su dai duk sun gudu, kawayen nawa, suka barni. Ni ma ina gudun kada ya kuma ganina. Shine zan zo na fada miki." Hajiya Safiya tace "Shigowa yayi har nan ya ganki? Gaje ta sanar da ita yadda ya gansu. Hajiya Safiya dariya tayi, dan ta san kwanan zancen. Ta san aikin Magaji ne. Abin da tace mata, "Shi ne kada ki kuma fita zaure da sunan wai wasa. Wannan ba tsarin gidan nan bane. Duk abin da za ki yi, ki yi shi anan cikin shiyyanki, ki zo mu je mu ga Hakimi." Tunda Hajiya Safiya ta fita ta bar su Hakimi. Magaji dai zaune yake turus! Da shi. Hakimi yana ta ba shi labarin abinda masarautarsu ke ciki. Sannnan Magaji ba fahimtar zancen Hakimi yake ba. Ya na dai amsa masa ne kawai. Suka yi sallama. Suka shigo. Magaji yana daga kai, ya ja da baya, kamar ya ga abin gudu. Gaje tayi gaisuwa ga DA SANNU... 71 Hakimi. Ta kuma yi ga Magaji. Sannan Hakimi, yace "Alhamdulillahi, ala kulli kharin! Yau Allah ya aika cika min burina. Magajin Hakimi. Ga Gaje matar da na zaba maka, na auran maka ita." Magaji yace "Godiya nake Baba Hakimi. Allah ya kara daukaka." Hakimi ya dubi Gaje yace "Diyata, yau ga kanina Abdullahi da muke kiransa da Magaji. Shine mijinki da ba ki san ko waye ba. Duk da dai hala ba za ki rasa sanin fuskar shi a hoto ba. To ga shi nan. Allah ya ba ku zaman lafiya da zuri'a masu amafani, masu biyayya ga kowa kamar ku." Kimi ya kalli Hajiya Safiya, yace "Ko ki na da magar lace "Allah yayi muku albarka, ku ci gaba da hakuti da juna da juriya. Ban da kananan maganganu da kuma yawan kawo kara. Kada ku zama masu tonа asirin gidanku, ku zama masu dangana. Ban da rashin hakuri. Gaje kada ki yarda ace ke kika jawo. Ya zamana ki na vadin ya zan yi? Dan Da namiji abin tunkaho ne, da in har soyayya yayi yawa, sai ya sa ki kasa gane wanda ya fi masoyi, ko kanwa? Kada ku ce na yi kuskure da nace haka. Sai dai Da sannu za ku gane. In Halina ya ja min. Allah sa ku gama da duniya lafiya. Ni magana ta kenan." Hakimi yace "Shi kenan, ku tashi ku tafi." Magaji ya ja ya kuma zama, yace "Ina da magana." Hakimi yace "Ina jinka, fadi maganarka." Magaji yace "Baba Hakimi, ina son ku taimaka min in cika alkawarin da muka yi da wata yarinya a makaranta. MAMAN FADILA 72 Mun yi alkawarin da zaran mun gama karatu, zamu yi aure. Ni da ita yarinyar, tana yin Difiloma ne ita. In har na saba wannan alkawari, ban auri yarinyr nan ba, ina ganin zata iya rasa rayuwarta. Ko kuma ta rasa hankalinta. Dan Allah bisa adalci irin naka, ka taimaka min, kada na kuskure, mu cika burinmu." Hakimi yace "Kada ka damu, in dai wannan ne. Anyi, an gamа. Ai mijin mace hudu kake. Allah yasa ku gama lafiya. Ya baku zama lafiya. Na san halin Diyata. Ina shaidan Diyata, ko ukun za ka karo mata gaba daya, bana jinta. Na san babu matsala a tare da ita." Allah Sarki! Da Hakimi ya san ko wacеcе yarinyar da Magaji suka yi alkawarin aure da ita. Da bai amince masa ba. Sunanta Murja. 'Yar wani Attajiri ne, kuma ma'aikacin gwamnati ne, da bai san ciwon kan shi ba, sai dai ya zauna a cikin ofis ya jira masu kawo cin hanci. Ya karba. Ya ci dubu, sai ceto. A kuma neman mata. Sa 'o'in 'Ya'yan shi. Tarbiyar gidan shi, kalilan ne. Ga shi da son 'Ya'yan shi, yana biye musu yadda suke so. Murja ita ce 'Ya ta farko a gidansu. Sakamakon irin kaunar data kewa Magaji, shine yasa ta dan canza halayanta, ta shiga kama kanta. Murja tana da tsananin kishi, dan ko kawayenta bata yarda su kebe da Magaji ba. Kan dole Murja ke hakuri wata hulda ya hada Magaji da wata 'Ya mace. Ba a son ranta ba. DA SANNU... 73 A ko wane lokaci, suna tare, suna tsara yadda rayuwar aurensu zai kasance. Karewarta ma akwai alkawarin da zaran sun yi aure, babu kuma zancen Magaji yace zai kara aure. Su kadai za su yi ta rayuwarsu, har mutuwarsu. Tirkashi! Gaje ta ki, ta sameki. Ina mafita? Aminiyar kwarai gareki. Ya na iya? Tunda Magaji da Gaje suka fita, suka nufi sasansu, ita dai Gaje baya baya take. Shi kuma Magaji bai ce mata komi ba, ko kallonta bai kuma yi ba. Suka shiga sasan. Lokacin Lanti ta dawo, ta gaida Magaji. Sannan ya shiga cikin dakinsu. Ita ma Ga je ta bi bayansa, ta shiga ta zauna, shi kuma yana tsaye yana kallon tsarin dakin, yana zagayawa. Da ya gama, ya fita abin shi, bai ce komai ba. In da Gaje ke zaune take tunawa shin yaya za ta yi ta iya zama da wannan mutumin da babu alamun wasa a tare da shi? Koda dare yayi. Magaji ya shigo ya ci abinci. Ya kunna kayan kallo, wanda Gaje bata taba tunanin zata kunnasu ba, dan in tana jin kallonta, ta kan shiga can cikin gida ne falon Hajiya Safiya. Koda dare yayi sosai. Ya kashe T.V. Ya kulle kofa ya jawo kushin din kujera, ya kwanta bisa kafet. Barcin da bai yi ba kenan. Da ya rufe ido, sai ya ga Gaje da kawayenta suna carake. Can kuma sai yaga Murja zaune gaban shi tana masa kuka. Ita kuwa Gaje da ke cikin daki tana kwance. Ita ma kasa barcin tayi, ta dunga ji muryan Magaji, yana dawo mata. MAMAN FADILV 74 Cikin tsawa, "Maza ku tashi, ku bace min da gani, in har kuka bari na dawo na iskeku, sai kun gane kurenku." Haka dai wadannan bayin Allah suka kwana. Kwanan Magaji bakwai, babu abin da yake hada shi da Gaje. Sai dai gaisuwa. Bayan nan, ko kallonta baya yi, balle yayi mata mugun kallo. Shi dai harkan gaban shi kawai yake, bai kuma shiga rayuwarta ba. Haka ita ma Gaje tana jin dadin zaman da suke, dan babu ruwanta da shi. Da zaran ta gaida shi da safe. Shi kenan. Abincin shi, sai dai ya zo ya samu inda yake ci. Jikin Gaje ya fara gogewa da shanin, dan Hajiya Safiya tana koya mata tsafta kullum zata yi wanka, tasa kaya, ma fi yawanci tafi yin harkokin ta a sasan Hajiya Safiya. Dan haka ba karamin shakuwa suka yi ba da juna. Ranar da Magaji ya cika kwana bakwai. Ranan ya koma makaranta. Kafin ya tafi. Ya kira Gaje ya dubeta sama da kasa, ya mika mata kudi masu yawa. Yace "Ni na koma makaranta, in za ki kwanta barci, ki kulle kofarki." Gaje tace "Allah ya kaika lafiya." Bai ce mata komi ba, ya fita abin shi. Ita ma ko a jikinta. Kamaryadda Hakimi yayi niyya, in an kawo Gaje su ma zasu yi nasu ruguntsumin biki. To da Magaji ya zo anyi taron biki. Dangi da dama na nesa da kusa sun zo, sun halarci bikin, kuma abin yayi kyau sosai. Sai dai 'yan kananan maganganu da gutsuri tsoma irin tamu ta mata da ba a raba mata da shi. DA SANNU... 75 Magaji yana shiga cikin makaranta. Wayar shi tana kira. Murjan ta shi ce. Ya fada mata ya shigo makaranta ta zo ta same shi. Magaji yana kashe waya. Yayi tagumi, ya rasa

Chapter 4 of 7