gida ba. Lantana dake tsakar gida tana dama
salala. Fadi tke "Ina za ki? Ba dake na ke magana
bane." Amma ina, Gaje bata san tana yi ba, ta riga ta
mika.
Nusaiba tana bakin get, tana magana da wasu
yara, ta hango Gaje da gudu ta nufi wajen Gaje. Tana
fadi "Oyoyo kawata. Daga ina haka? Ko dammara babu,
ballantana gyale." Gaje tace "Ke dai kawa, ko ma yaya
ni za ki ganni. Na zo na ga Hakimi ne. Ya taimaka min."
Nusaiba tace "Wane irin taimako ne, in baifi
karfina ba, na taimaka miki? Gaje tace "Wannan
taimakon ya karfinki, ke dai kawai ki kaini na ga
Hakimi. Taimakon da za ki iya min kenan." Nusaiba ta
kama hannunta ta ce "Allah ya kyauta, mu je na kaiki."
Koda suka karasa cikin gidan, suka shiga dakin
Hajiya suka sameta ita da Naziyatu. Tun kafin su karasa
sallama. Naziyatu ke fadin "Gidanku da rowa. Ke ce da
safen nan, ko (Break fast) ba mu yi ba." Nusaiba tace
"Ke ce kika san wannan. Hajiya kin ga daga
shigowarmu, bata bari ta ji dalilin zuwan ba, zata fara
DA SANNU... 41
ko? Ke fa 'yar rainin wayo ce, ce miki ta yi ta zo ta yi
(Break fast) anan gidan?
Gaje tace "Kawa wai mai take cewa ne? Na zo
nan gidan ba ku yi ba." Nusaiba tayi murmushi tace
"Rabu da ita, wai cewa tayi ke ce anan gidan ko wanka
ba mu yi ba. Kin san ita 'yar kwalliya cе."
Gaje tace "Ai don ma ku ne, mu ba sai ma
kwana biyu, ba mu yi wanka ba. Sai dai in za mu je
dandali ko talla, mu wanke fuska da kafa, mu yi
kwalliya. In kuwa mun yi wanka da sassafe, to sallah ne,
ko biki. To amma yanzun menene abin surutu, dan na zo
baku yi wanka ba. Shine ta damu? To ayi hakuri."
Hajiya da ke jinsu, tana dariya tace "Rabu da
ita Gaje, ita ma iya yi ne. Sai fa ta kwana bakwai bata yi
wanka ba." Naziyatu tace "Kai, kai Hajiya, to Allah zan
fasa kwan." Duk suka yi dariya. Hakimi ya shigo yace
"Amira ta zo tace min ga gidanmu da rowa nan, ta zo.
Shine na taso da kaina in tabbatar."
Nusaiba tace "Zuwan kuma taka ce ba."
Hakimi ya nemi waje ya zauna yace "Ni kaina? To duk ku
tashi ku ban waje." Hajiya tace "Har ni? Yace
"Dukkanku na ce."
Duk suka mike, suka kama gabansu, suna
dariya. Gaje tace "Ai dama ka rabu da su, duk daya ne.
Babu komi." Hakimi yace "To 'ya-ta, ina sauraranki, me
ke tafe da ke? Gaje ta mutsuke idonta, ta fara magana,
tana kuka.
Duk anan ta zaiyanewa Hakimi duk halin da
take ciki. Tana gama zaiyanewa masa, ta kuma rushewa
MAMAN FADIL.A 42
da kuka. Hakimi tunda Gaje ta fara masa bayani yake
tausaya mata, saboda Hakimi yana da tarihin Lamido.
Yana kuma samun labarin irin halayyar
mahaifin Lamido Alhaji Bara'u. Dan yana matukar taka
ma Alhaji Bara'u birki, akan wasu aiyukan, yana takura
masa saboda irin kararrakin da mutanen gari ke kawo
masa, na Dakaci.
Hakimi ya bude baki ya fara lallashinta "Ki yi
shiru, ki daina kuka. Yanzun mai kike so ayi miki akai?
Gaje tace "Hakimi, dan girma irin naka da adalci, da
karama da bin hakkin kowa, ka taimaka min, wannan
aure ka hana.
Ka ceto rayuwata daga fadawa cikin mugun
yanayi da bala'in rayuwa, ka taimaka min. Wailahi ko
wanene, ku canzar min, zan amince na aure shi, пa
zauna da shi lafiya. Ni bana kaunar Lamido Dan
Dakaci."
Hakimi ran shi a bace, yace "Gaje diyata. Ni
Hakimi na san ina da ikon da zan iya sawa Lamido ya
janye hatun aurenki. To amma kada ki manta, kin ce in
sa adalci irin nawa, in har na rushe maganan aurenki da
Lamido. Ban yi masa adalci ba, ki yi tunani, aure fa
sunnan ma'aiki ne. Ya za ayi na zama mai rushe Sunnar
Manzon Rahama?
Gaje ni kaina bana farin ciki da wannan aure na
ki da Lamido, ko lokacin da na zo wajen sa rananku, ban
yi farin ciki ba. Kuma ni ban san haka abin naku yake ba
a lokaci da ba za a kai ga sa muku rana ba.
DA SANNU .... 43
To amma bakin alkalami ya bushe. Ki yi hakuri.
Allah kadai ya san dalilin hada wannan aure naku da
yayi. Allah ya kadara shine mijinki, kuma kila wannna
daman ita ce Allah ya kaddara sanadiyar shiriyarsa.
Kada ki damu da halin shi, ki zama mai biyaya
ga zabin iyayenki, ki zama mai dauriya da halin da
iyayenki suka sakaki, ki yi biyayya ga mijinki, ki zama
mai tattalin shi da ba shi dukkan hakkin shi na aure, ki
zama mai kulawa da duk abinda yake na shi ne.
Yin haka gare shi, sai ki ga Allah yasa ya
karkato gareki, duk wasu mugayen halayyen shi, sai ya
daina. Ki sa dangana, ki yi hakuri, ki zama mai
runguman kaddara Allah mai kyau da mara kyau.
Da zaran kika yarda da hakan, ba za ki taba
tabewa ba, sai kin ga Allah ya musanya miki. Gaje ina
son ki yi min alkawari. Daga yau din nan za ki yi hakuri
da wannan kaddaran aure da Allah ya daura miki, ba za
ki kuma bata ranki ba.
Kuma ki bi umarnin iyayenki, ki kuma yi
biyayyar aure wajen mijinki. Ki yarda Allah ne ya
hadaku, in har kika yi min haka, ki ka daukar min
alkawarin nan Gaje, ba karamin jin dadi zan yi ba. Zan
kuma kasance kullum cikin miki addu'a da fatan sauyi
mai kyau."
Gaje tana hawaye tace "Na hakura da
kaddaran Allah, kuma zan so zabin nasu. Sannan kuma
na amince da duk abin da ka fada min, nayi maka
alkawari, daga yau na yarda da aurena da Lamido."
Muryarta na rawa ta fadi. Lamido.
MAMAN FADILA
t
Ta ci gaba "Na kuma gode da irin shawararka
da nasiharka gareni. Da kuma kaunar da kuka gwada
min, kai da iyalanka, ban taba mantawa da ku. Ni zan
koma. Babu wanda ya san inda na je a gidanmu." Ta
share hawaye. Tirkashi! Tsananin birge Hakimi da Gaje
tayi.
Yasa shi ya dunga sa mata albarka, yana yaba
mata da irin mutunta shi da tayi, ta kasa yin masa
musu. Yace "Gaje diyata, ina son in kin koma gida, ki
sanar da iyayenki, ni Hakimi nace ko tsintsiya kada su
saya.
Gaba daya komi na amarya, tun daga jere da
gara. Ke komai ni na dauki nauyin zan miki shi. Saboda
jin dadin biyayyan da kika yi min, wanda ki 'yar da na
haifa, sai haka. Wata 'yar tawa ma, ta yuwu ta ki yarda
da abinda na fada miki, tashi ki je gīda. Gobe zan ma
zan tura a zo min da mahaifin naki."
Hakimi yace Direba ya mayar da Gaje gida. Tace
"A'a bata son a san ta zo nan. Hakimi yayi mata
alkawarin koda mahaifin nata ya zo, ba zai sanar da shi
ta zo ba. Nusaiba ce kadai ta raka Gaje har bakin get.
Suka yi sallama ba tare da Nusaiba ta kurma tambayarta
ba.
A gidansu Gaje Dan-tani Mahaifinta ya rufe Lantana
mahaifiyarta da ruwan bala'i da masifa. "Abin da za ku
yi min kenan, ki daurewa yarinya ginoi ta gudu.
DA SANNU..... 45
To bari ki ji, ki ma yi shiri ke ma duk inda kika
tura min 'ya, to ki tabbatar kin bi ta, kun dawo tare. In
kuma ba ki ganta ba, ke ma ki shiga duniya. Kada ki
dawo nan. Dan za ki ga tijara da tozarta da gara ke ma
ki shiga duniyar."
Lantana ta bude baki zata yi magana. Dan-tani
yayi mata tsawa, wanda karfin tsawan ne ya ji shigowar
Gaje da gudu a firgice, saboda bata san dalilin yin
tsawar mahaifin nata ba. Lantana ta rungume ta tace
"Alhamdulillahi. Ina kika je ne?
Nayi ta magana, kafin ki fita, ba ki saurare ni
ba? Gaje tace "Mun yi alkawari ne da Lamido, mu hadп
ni da shi da safe. Ban san dalilin da yace min haka ba.
Ni ma na dauka ya sanar ne."
Dan-tani dake gyara baki, yana shirin wani
sabon masifa. Ai da ya ji abin da Gaje ke fadi, sai ya
fasa, ya shiga washe baki, yana fadin "Ai babu komi. Ba
Mijinki bane?
Tuncla an sa muku rana, ba gara da kika je ba.
Kun hadu dai ko? Gaje tace "Na yi ta zaman jiran shi,
bai zo ba, shine na gaji na dawo gida. Dana ga rana tayi
sosai."
Dan-tani yace "Me yasa kika dawo? Gaskiya ba
ki yi daidai ba, sai ki koma ki ci gaba da jiran zuwan shi,
ko zai kai dare, ai kya jira shi. Zan sayo abinci in kawo
miki, ki sarıar da ni wajen." Lantana dake tsaye ta rasa
shin lafiya kuwa Gaje take da har Lamido zai bata uzuri,
kuma ta bi?
MAMAN FADILA 46
Sannan kuma duk ba wannan ba, wai ta koma ta
ci gaba da jiran Lamido. Dan haka Lantana tace
"Gaskiya Maigida ka yi hakuri kawai, tunda yarinyar nan
ta je, bai zo ba, babu amfanin ta koma, babu inda zata
koma."
Ta kalli Gaje, tace "Ke wuce daki, ga kayanki
can ki dauka, ki shiga da shi ciki." Dan-tani yace "Ke јe
ki daki, babu komai, ai yanzun gaskiya tayi halinta.
Na san inda nake samun baraka, mai ruguje min
shiri. Na san dai kin ji kunya, kuma aure babu fashi. 'Yar
bakin ciki. Sakarya kawai."
Ita dai Lantana bata ce masa uffan ba, har ya
fice gidan. Sannan da sauri ita ma ta shiga dakin da
Gaje ke ciki, ta na zaune tana tunani. Lantana tace
"Haba Gaje, me yake faruwa da ke ne? Abin da kika
fada mana, ba gaskiya bane, ki sanar da ni inda kika je?
Uwa ta gari kenan. Da ta san mai take yi. 'Yarta
ta zo mata da maganar karya. Ta yi saurin fahintarta,
kuma ta tsaya cikin lumana ta kama bincike, bata yi
zage-zage ba.
Ita dole karya aka fada mata. Dole a fada mata
gaskiya. Tafdijan! In dai 'Ya'yan yanzun ne, za ko ki yi
bindi, don Wallahi tsiyarki da bala'inki ba su isa ba, sai
dai su kara zurmaki.
Lantana yadda ta bullowa Gaje cikin dabara da
lumana. Shi yasa Gaje zayyanawa mahaifiyarta duk
abinda ya faru tsakaninta da Hakimi, tace Amma don
Allah kada mahaifiyar tata ta sanar da mahaifinta. Gaje
tana hawaye, ita ma mahaifiyar tana hawaye.
DA SANNU... 47
Gaje ke fadin "Ummah na hakura da kadaran da
ta sameni. Na yarda da nasihar Hakimi, ya zan yi? Na
dangana." Lantana tana lallashinta, tana tausaya
mata, tana mata addu'a. Allah ya musanya mata da ma
fi alheri.
Haka ake so, a koyaushe, mu iyaye mata mu
kasance cikin yiwa 'Ya'yanmu addu'a da fatan alheri.
Sai komi ya dunga zuwa ma 'Ya'yanmu da sauki. Allah
sa mu dace, amin.
Alllah sarki! Gaje ta koma rayuwar sai yadda
Allah yayi da ita kawai. Tsakaninta da Lamido, babu
yabo, baku fallasa. Ita dai ga ta nan, tana shawara, ta
saduda haka nan suka ci gaba da hada-hadan sallah da
na biki. Kowa a garin yana mamaki, irin tawakallin da
Gaje tayi.
Sai labari abin ake a boye. Labarin abin ake a
boye, labari har kunnen Hakimi. Hatta iyalan gidan
Hakini da yake basu san komi akai ba.
Don Hakimi bai sanar da su ba. Da labarin ya
iskesu. Sai suka tausaya ma Gaie, duk da dai ana raderadin wai asiri Dakaci ya yiwa Gaje, ta so Lamido.
Koda aka yi shagulan sallah, aka gama. Sai Hakimi ya
nemi Dakaci da Dan-tani. Suka gurfana gabansa. Suka
dan yi korafe-korafe akan wasu 'yan abubuwan da ba'a
rasa ba.
MAMAN FADILA 48
Da suka je birni wasan sallah. Su ce dawakan
Hakimi can garin, sun yi barna. Su ce Yarima wane, bai
yi mana adalci ba.
Kai ga dai su nan. Abinka da marasa godiya.
Hakimi dai ya kwabesu, yace komi ya wuce "Ku jira
babban sallah. Kuma yanzun abin da yasa na taraku,
shine na ga bikin yaranku ya zo, dan haka nake so kowa
na ba shi gudunmawata."
Ya ciro makuden kudade wanda ni dai ban
fahimci ko nawa ne ba, saboda yawansu. Ya mikawa
Dakaci, yace "Allah yasa ayi wannan aure da mu."
Sannan ya dubi Mai unguwa Dan-tani, yace "Kai kuma
taso mu je. Na baka taka gudunmawar." Suka mike
dukkansu.
Suka bi Hakimi a baya. Suka isa wani gareji.
Hakimi yayi umarni aka bude kayan alatu ne, na zamani
kala-kala na dakin amarai, har da su garan abinci. Ni
dai da yake malamaciya ce, ina da son jiki na da yawa,
tunda na kyalla idona hango kayan da ke cikin garejin
nan.
Sai na ja da baya, na koma gafe ina tunanin
inda zan dosa? Dan gaskiya ba zan iya shiga cikin
garejin nan ba, in ce zan iya zaiyane muku abin da yake
ciki ba. Sai kawai na nufi Lamido.
Yana can cikin gona shi da abokan shi, suna zukan
taban wiwi. Da yake ni din ma jaruma ce, sai na kutsa ko
shakkar kada ta bugar dasu. Su dankeni. Wai wa ya ga
DA SANNU... 49
A'isha a hannun kauraye? Ai sai dagewa da addu'a
kaw.. Can kuwa ta fara aiki.
Lamido yace "Kai Bayo, ya ka ganni ranan biki?
Nan Bayo yace "Akwai aiki dai barna daya fi na sallah
da muka yi." Wani kuma a cikinsu yace "Gaskiya fa da
sallah nan mun yi barna."
Lamido yace "Na bikina, sai ya fi haka." Bayo
yace "Sa'a dai, sa'a dai." Lamido yace "Haka nake sonka, kai ma za ka sha romon amarya. Darenmu na farko."
***
DA SANNU..... Bata hana zuwa. Sai dai a dade ba
aje ba, ga shi dai gobe daurin auren Gaje da Lamido.
Ana ta shagulguan biki. Hakimi ya aiko Dakaci ya zo da
sauri yana nemansa. Abin mamaki, koda Dakaci suka
isa gidan Hakimi. Motar 'yan sanda (Police) da ya gani
kofar gidan, shine ya dan sosa masa zuciya.
Abinka ga, mara gaskiya, suna zuwa gaban
Hakimi, suka tarad da 'yan sanda su uku zaune gaban
Hakimi. Ga kuma guda uku tsaye a kansu. Dakaci ya
tsuguna yayi gaisuwa, gaban Hakimi. Ya koma ya zauna.
Hakimi yace "Dakaci an samu matsala a birni wajen yin
bikin sallah.
An samu barna sosai, kuma ana ganin da su
Lamido a ciki. Dan haka yanzu za a tafi da Lamido can
birn. (Police Station). Dan ayi masa wasu tambayoyi.
Da zaran şun gama, zai dawo, kada ka damu, ku
ci gaba da hidiman bikinku, babu fashi. Ka tashi ku je,
MAMAN FADILA 50
ka kai su su tafi da shi. Ni ma daga baya sai mu bi su.
Insha-Allahu babu wata matsala."
Tirkashi! Gaje da kawayen ta suna can bakin
kogi sun je yawon gudu. Sun dawo, sun tsaya wanka
cikin kogi. Da gudu Lawal ya iso yana haki, yana fadin
"Gaje 'yan sanda da yawa a cikin mota, sun tafi da
Lamido can birni." Kandala tace "Ka san abin da kake
fadi kuwa?
Binto tace "To menene sabo? Yau aka fara."
Lante tace "Ku ba su awa daya, in ya dade za ku ga ya
dawo." Gaje da tayi zugum! Tana sauraransu da kyar ta
bude baki, tace "Ku duk ba wannan ba. 'Yan sandan
birni ne aka ce sun tafi da shi fa."
Gaba dayansu, sai duk jikinsu yayi sanyi, suka hada
komatsansu, suka nufi gidansu Gaje da yake da yake
bankar da mutane, sai ka ce ranan ne biki. Koda su
Gaje da kawayenta suka shigo cikin gidan, babu abun
da ya ragu na shirye-shiryen biki.
Sai ma abin da yake karuwa. Haka ma can
gidan Dakaci. Shi ma babu abin da aka rage na shirin
bikin. Duk dalilinsa kuwa na yin haka din, shine 'Yan
sanda sun saba zuwa su tafi da Lamido, ba tare da
daukan dogon lokaci ba. Lamido zai dawo ya ci gaba da
harkokin shi, ba tare da ya sauya hali ba. Allah sarki
rashin sani. Aka ce ya fi dare duhu!
Ni dai dana bi su Hakimi can Birni, sai gamu a
(Police station). Tirkashi! Ni ce da shiga (Police
station). Ofishi 'yan sanda. Ya zan yi? Tunda dai ina
bayansu. Kuma halina ya jawo min na son farantawa
DA SANNU... 51
masu karatu rai. Kuma ina ganin tunda ga Hakimi da
Dakaci, ina ganin ba abin da 'yan sanda zasu yi min.
To ga su Hakimi nan. Dakaci yayi tsuru-tsuru da
shi, fuskar Hakimi da Dakaci babu sauran haske. Zaune
suke kawai gaban shugaban 'Yan sanda (Kwamishina).
Hakimi yace "To wai yanzun meye abin yi?
Kwamishinan 'Yan sanda yace "Babu abin yi, sai
abin da (Court) ta yanke, kuma kun riga kun san
hukuncin da shari'a zata yanke. Wannan abu da ya faru,
na fada muku dama ace dukkan 'yan-matan sun mutu
ne.
Da sai mu yi nasara, mu cire Lamido a ciki,
tunda babu kwakkwaran shaida. Da sai kawai a
yankewa yaran shi hukunci, ba tare da an sa Lamido a
ciki ba.
Kun ga mahaifin yarinyan nan. Lauya ne, dama
ace 'yar lauyar ce kwance a asibiti da abin ya zo da
sauki, tunda ita daya yarinyar ance ubanta tallan gauta
yake a faranti.
Ka ga irin wadannan an saba fatali da
shari'arsu a dannesu. Amma gaskiya hakkin Lauya ba
zai taba dannuwa ba. Ita kenan masa diya mace.
Duk 'Ya'yan shi maza ne, dan haka ina ba ku
shawara, kada ku batawa kanku lokaci. Dole ne
hukuncin kisa ya tabbata akan Lamido. 'Yan mata biyar
fa suka yiwa fade.
Biyu sun mutu, uku suna gadon asibiti, babu
sauki, sai na Allah. Da kyar suke magana. Kuma Lamido
shi ne shugaban yin komi. A hannun shi ma 'yar Lauya
MAMAN FADILA 52
Bashir ta mutu. Allah shi kyauta gaba. Ranan litini za ku
gurfana gaban shari'a.
Dakaci ka yi hakuri. Allah ya jikan yaronka, ya
yafe masa. Ku ke jawo ko ma menene, ku na iyaye.
Yaranku su yi ta jawo rigima koyaushe, kuna tunkahon
kuna da kafa, ko hanya.
Sai dai a sasanta ba tare da kun dauki wani
kwakkwarar mataki akan yaranku ba, tunaninku kuna
da hanya. To. duk hanyarka, wata rana bacewa take,
matukar ka shiga hanyar wasu."
Hakimi ransa a bace yace ma Dakaci "Ka ga
abin da nake fada maka kenan akan Lamido. Sai ka ce
min wai ba ruwan shi da kowa. An dai sa masa ido ne,
halayyar shi suna da kyau. To yanzun ina kyawun yake?
Ga shi zai yi mutuwar wulakanci, sakamakon
halayyarsa. Sai ka tashi mu koma. Allah ya kyauta.
Yanzun kuma sai mu koma mu sanar da gidan mai
unguwar 'yar shi ta hakura. Maganar aure an fasa."
Kwamishina yace "Auren wa za'a fasa? Hakimi
yace "Auren Lamido da 'yar mai unguwa." Kwamishina
yace "Ba iyayenta sun gama komi na aure ba? Dakaci
da sauri yace "Wallahi an gama, ko dan haka a tausaya
man Kwamishinan 'Yan sanda.
Yayi murmushi, yace "Hakimi, tunda iyayen
yarinyar nan sun shirya, to abin da yakamata ku yi,
tunda dai ko kun fasa auren nan a yanzu, dole wani da
ban yarinyar zata aura. Dan Lamido matacce ne, ba
komawa kauyen nan zai yi ba. Sai lahira.
DA SANNU.... 53
Ku je ku nemi uban yarinyar, na ku ce masa ya
kira yarinyar cikin samarin ta ta fito da wani a daura
musu aure da shi. Ina ganin yin hakan shine zai fi kawo
kwancyar hankalin ita budurwan da irin surutun jama'a
da zata fuskanta."
Hakimi yace "Gaskiya ka kawo shawara mai
kyau. Dan ina ganin yin haka zai kawo saukin komi.
Dakaci ina ganin shawaran Kwamishina za ka bi, yanzu
in mun koma, sai ka je ka samu mai unguwa ku
tauttauna akan haka din." Dakaci yana hawaye yace wa
Hakimi "Ka taimaka min, ka aika a zo da mai Unguwa
gidanka, sai mu yi komi a idonka.”
Hakimi ya gyada kai, yace "Babu damuwa, mu
je gidan nawa. Sai in tura a zo da shi din. Kai har ma da
ita yarinyar." Hakimi da Dakaci sun ga Lamido an fito
musu da shi. Abin mamaki da rashin sani. Lamido ya
dauka kamar yadda ya saba dauko rigima awarwareta.
Haka ma wannan rigiman take. Bai san ba haka bane.
Bana 'yar Lauya aka tabo, dan haka fuskar
Lamido babu wani damuwa a cikinta. Sai dan kadan
wanda ba a rasa ba.
Tun kafin su yi masa magana, yace "Baba ina
fatan dai an ci gaba da shagulgulan biki, har can
gidansu Gajen? Dakaci kasa magana yayi, yana zubar
da hawaye.
Hakimi ne yace "Yi mana shiru, mutumin banza
kawai. Wanda baya jin magana. Ai in ba wani iko na
Allah ba, kai da aure, sai a lahira, don rigimun da kake
daukowa, kana yin nasara. To bana ka dauko mai zafi.
MAMAN FADILA 54
'Yar Lauya ka kashe. Dama 'yar talaka ga
Ya'yan Attajirai can bisa gadon asibiti, dan haka
maganar aurenka da Gaje. Babu, mun soke, don ba zata
auri gawa ba. Kai dai Allah ya yafe maka kura-kuranka,
ya kuma gafarta maka. 'Yan baya masu irin halayyanka.
Allah ka shiryesu, ya ganad da su hanya mai kyau."
Ya mike yace wa Dakaci "Ka sameni a waje, ina
jiranka, mu tafi." Ya barsu nan gaban Kwamishina da
kuma wasu (Police) guda biyu, suna tsaye bisa kan su
Lamido da mahaifin shi. Babu wani maganan kirki, sai
kuka da suke yi. A haka aka rabasu, gwanin ban
tausayi. Ko da dai su suka jawowa kansu.
A can kauye kuwa, ana ta ruguntsumin wasannin gobe
biki, har yamma babu ango, babu kuma uban ango.
Nan fa hankula suka fara tashi. Mai Unguwa ya nufi
gidan Hakimi, ko shi ya dawo.
Ya ji yadda abin yake. Faduwa ta zo daidai da
zama. Yana isa kofar gidan Haikimi. Su kuma nasu
motar na isowa. Suka fito daga motar mai unguwa yayi
gaisuwa, ga Hakimi.
Ya shiga cikin gida wajen iyalan shi. sannan ya
fito ya samesu zaune a falo, suna jiran fitowar shi. Koda
ya fito bayan yar gajeruwar magana da suka yi.
Sai Dakaci ya fara wa mai unguwa bayanin
komai. Yana yi, yana zubar da hawaye. Mai Unguwa ciki
jimami da tausayawa yace "Yanzu babu wata hanyar
mafita da za mu samu?
DA SANNU... 55
Dakaci yace "Tunda ka ga mun dawo da
Hakimi, ai babu ne." Mai unguwa, yace "Allah ya
kyauta, bari in je in kirawo ita Gajen, mu ji ko tana da
wanda take so."
Ya fita, ya bar Hakimi da Dakaci, suna dada
tattaunawa kan batun. Ba wani dogon lokaci mai
Unguwa ya dauka ba. Sai ga shi ya dawo tare da Gaje.
Hakimi yace "Ina fatan ba ka tsaya ka fadawa
kowa abin da ake ciki ba? Yace "Babu ma wanda ya san
na taho da Gaje nan." Hakimi ya dubi Gaje.
Bayan ta gaidasu, yace "Gaje diyata, yanzun
idan aka ce an fasa aurenki da Lamido ko kina da wani
daban da za ki kawo mana shi, mu daura muku aure da
shi?
Gaje ta girgiza kai tace "Ba ni da wani." Mai
Unguwa yace "To aure tsakaniki da Lamido, babu shi,
an fasa." Caje bata san Jalilin fasa aurenta da Lamido
ba. ita a tunaninta Lamido kada ya dawo ace za'a daura
musu aure da shi. Dan haka ita ma bata son a daga
auren nata, gara koma waye ta aura.
Yanzu da dai a daga. Da sauri tace "Baba, ni ba
ni da samari, ko daman dan haka na ba ka zabi, ko ma
waye, ka daura min aure da shi, na amince."
Gaba daya sai Gaje duk ta burgesu, dukkansu
suka sa mata albarka. Hakimi yace "Gaje diyata,
sakamakon biyayya irin ta ki. Ni na zaba miki miji.
Kanina Magajin Hakimi, za a daura miki aure da shi.
Ina fatan za ki amince da shi? Da sauri Dakaci
yace "Godiya muke Hakimi. Wannan abu yayi daidai."
MAMAN FÁDILA 56
Mai Unguwa yace "Allah ya kara maka tsawon kwana,
muna godiya. Yarinya ta amince, ta kuma gode."
Ita dai Gaje rufe fuskarta tayi da jin wannan
magana da Hakimi yayi. Yace "Abin da nake so da ku,
wannan magana mu barta anan, kada mu bari kowa ya
santa. Ni kaina cikin iyalaina babu wanda zan sanar da
shi.
Sai gobe. Bayan an daura auren tukuna. Sannan
zan yi musu bayani. Saboda haka kowa gobe in an daura
auren, sai su ji koda wa aka daura auren. A lokacin
koma menene jama'a sai su fahimta."
Ita dai Gaje tafiya kawai take zuwa gida, tana
tunanin wannan aure nata da Magaji. Mutumin da bata
san ko waye ba. Ita bata ma san yana da wani Dan-uwa
ba, sai yanzu.
Anya kuwa shi wannan Magajin, zai amince da
ita a matsayin matar shi? Tirkashi! Ni kaina abin da
nake tunani kenan. Ga dai ni nan biye da su Gaje. Don
haka ta kwana cikin tunanin abinda zai biyo bayan
auren nasu.
Kowa owa ya hallara wajen daurin auren Lamido da Gaje.
Waliyyai su na ciki. Abin da maroki ke fadi, shi ya
gintsewa kowa tunanin shi, yana fadin "An daura auren
Abdullahi da Habiba. Asalin sunan Gaje.
Mata da suke cikin gida, suka fara surutu.
Lantana da yake da safe Dan-tani yayi mata bayani,
saboda irin haka. Abin da Lantana ta fadawa mutane,
DA SANNU... 57
shi ne an fasa da Lamido, yanzu da kanen Hakimi aka
daura. Daga wannan magana, bata kuma furta komai
ba. Ta ja bakinta tayi shiru.
Kowa na fadin albarkacin bakinsa. To haka ma
kofar gida. Su ma da suka fara surutu. Sai aka yi musu
bayanin Allah bai yi da Lamido ba. Da Magajin Hakimi
Allah yayi.
Mutane suna ji, suna gani, suna son su yi
bincike akan abin. Amma babu dama. Sai dai kuskus
suka rika yi, kowa ya watse kafin Hakimi ya koma gida.
Har labari ya iske kowa na gidan.
Zuwan Hakimi kawai suke jira. Hakimi yana
zuwa gida. Auwalu da yake shi ma yana gida bai koma
makaranta ba. Tunda ya dawo hutun sallah. Haka su
Naziyatu da Nusaiba su ma suna gida, basu koma
makaranta ba.
Duk cikin satin nan zasu koma. Shi ma Magajin
Hakimi kwanan shi biyu da komawa. Auwal yace "Baba
Hakimi, wai da gaske an daurawa Baba Magajin aure da
wannan 'yar kauyen?
Hakimi yace "Da gaske ne. Dan birni, kana
mamaki ne? Naziyatu tace "Baba yarinyar nan fa
gidanku da rowa. Amma gaskiya Baba Magaji ba zai
amince ba. Yarinyar da tace sai ta kwana uku bata yi
wanka ba. Ita ce za ace matar Baba Magaji?
Wanda duk kwalliya irin tawa, kusheta yake,
yana cewa ban iya kwalliya ba. Hala dai Baba ba ka taba
ganin hotunan Baba Magaji da yake yi da 'yar matan shi
bane a makaranta. Kuma ma ina ganin 'yan matan
MAMAN FADILA 58
Baba Magaji, ai sun kusa haihuwar gidanku da rowa. Ko
ni fa na girmeta. Taf! Na san zata sha yanka kuwa, don
ba'a iya masa."
Nusaiba tace "To wai ku duk kuna bata bakinku
ne, duk kudinka da mukaminka da