Reading The REGRET by sani Amarya Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?mode=r_c

*NIGERIA*🇳🇬




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.🤌💪




Proudly Nigerian 🇳🇬✅

MY FATHER'S LAND

The Noble Writters

Dedication is our strong 🦚🦚🦚✊✊




Let's dive into the work of fiction 🤝💫



THE REGRET

(Dana sani)🙆🥀🌸



When Love meets temptation 🦚 who survives?

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 🦚
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

Tuna baya a Nigeria

Flash back 🦚💫

2004




Kwance ta ke akan gadonta ta ƙurawa wuri ɗaya ido, wanda kallo ɗaya zaka ma ta kasan cewa tayi nisa
cikin tunanin da ta keyi, idon ta fal ya taru da hawayen dake neman hanyar gangarowa, fuskar ta a
Kumbure yake wanda zai baka tabbacin cewa dukan ta akai.




Bankaɗo dakin da akai ne ya sata tayi saurin tashi daga kwancen da take wani ɗan saurayi wanda bazai
wuce shekara 27 ba ya shigo yana ta muzurai.




Ƙara fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciya cikin shashsheƙa tace " Ya Nabil nayi Alƙawarin bazan ƙara
bijire maka ba amma kasani cewa bazan iya zubar da cikin da yake jikina ba dan Allah kai haƙuri ka barni
da abinda yake cikina....




Bai barta ta ƙarasa ba ya wanka ma ta mari sannan ya ɗaura da cewa"Saboda kin samu wajen arziki
gidan arziki shine zaki cika ni da yara, ban shirya na zama uba ba sai nan da shekaru uku.

Yana faɗin haka yasa kai ya fuce daga cikin ɗakin.
Duk kalmar da ya shigo bakinta furtashi take yi ta rasa ta ina zata fara, ta rasa Mey ke bibiyar rayuwarta
shin wannan aure ne ko ƙaddara batafi shekara 17 ba auren shekara huɗu kenan saboda a gidansa ta
fara jinin ta na al'ada.



In ta tattara ma zata koma gida, can ma iyayenta korar ta zasuyi wai ta ina zasu samu abinci in ba ita ta
taimaka musu ba, tunda ta auri Nabil tun satin farko data tare da taji daɗi har yau bata san mey ne
soyayyar miji ba.




"Ya Allah ka kawo min mafita ni ɗin na kasance baiwace agareka mai ƙasƙantar da kanta ya rabbi kar ka
ganni da laifin zubar da cikin nan da zanyi akaro na shida, ya Ubangijina ka kawo min ɗauki ba dan ni ba,
ya Ubangiji na ka ganar da bawanka ba a ƙurarren lokaci ba ta faɗa kuka na ƙara kufce mata.




Ta shiga rairawa kamar ba gobe mayafin ta ta sanya tunda atamfa ce ajikin ta riga da skirt, tanufi ɗakin
sa ta sanar dashi abinda ta yanke, daman yasan za'a rina kuma yayi farin ciki sosai.




Hanyar asibitin Nassarawa suka nufa akai gwaje gwajen da za'ayi tunda likitan abokinsa ne.

Doctor hafiz numfashin sa ya furzar sannan ya ce" wannan ne ciki na ƙarshe da zaku iya zubarwa idan ta
ƙara wani cikin sai dai ta haifeshi.
Ɗago kanta tayi suka haɗa ido da Nabil, hawaye ta shiga zubarwa bana wasa ba, cikin dasashhiyar
muryarta ta ce" Ya Nabil dan Allah kar azubar da cikin nan ko sau ɗaya ne kaima ka amsa sunan ka a
matsayin uba dan Allah. Wani banzan kallo ya wurga mata wanda ya saka cikinta kaɗawa, a take tayi
shiru kawai ba tare da ta shiryawa shirun ba.

Doctor hafiz ne ya kalli Nabil ya ce " As I said earlier wannan ne ciki na ƙarshe da zaku zubar, sannan ku
kiyaye, duk abinda yaje ya dawo babu ruwana a lamarin nan man.



Daga haka ya tashi ya zaga ta cikin office ɗinshi wani ɗan madaidaicin wuri da aka zagaye da labule irin
labour room komai na wurin is beyond neatness.




Tana ganin ya tashi ita tabi bayan sa dan ta saba yanzu ba sai yace ta shigo ba, shiga ɗakin tayi ta saka
kayan da aka tanada mata sannan yayi abinda zaiyi ya cire cikin daga jikinta abinka da ƙwararren doctor,
sannan ya haɗa mata da wankin ciki.

Sai da aka bata rest bed na awa biyu sannan sukayi hanyar gida a cikin motar ma a takure ta ke motsi
kaɗan in yayi akan idonta ne saboda tsoron kar ya sakar mata ranƙwashi.




Koma warsu gida ke da wuya yace da ita ta shiga kitchen ta dafa mai sakwara da miyar ganye daga haka
ya shiga ɗakinsa ya kulle ƙofar sa.




sai da ta zauna ta fashe da kuka tukunna, saboda inda sabo ta saba amma ai ba'a sabo da wahala.

Sai da tayi mai isar ta sannan ta shiga ɗaki tayi wanka sannan ta dawo madaidaicin kitchen ɗin su, da
ƙyar ta ƙarasa fere doyar sannan ta ɗora yar tukunyar ta a gas saboda ba laifi Nabil nada kuɗi sosai,
sannan ta ɗauki 300 ɗin daya ajiye mata na cefane ta fita kafin ta dawo tasan doyar ya dahu.....



I just started this Novel OOO

I need yah reactions

Allah sarki Ikimat tun banyi nisa a Novel ɗin nan ba na fara tausaya miki🥹
The Regret 🥹 🦋

Is not just a Novel

Buh matsalolin da ƴaƴa mata kan fuskanta agidan mazajen su.



What comes arround goes arround 🥀

Abinda ka shuka shi zaka girba 🌕

Pending Amarya as usual 🇳🇬📜✅



Emotional Vibez 🦋💔🥀https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?mode=r_c



*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.🤌💪



:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::



The Noble Writters 🦚🦚✊

Dedication is our strong 🦚🦚✊



THE REGRET 🙆🥀🌸🇳🇬
when love meets temptation 🦚 who survives?




Rayuwa ta kan zo da sauyi ko wani yanayi🥹

Gwara ka riƙe ƙaddara kan ka shigewa tsautsayi💔💫



NIGERIA 🇳🇬

For Pending Amarya ✍️✍️



NDA DUBDO🦚

My Maiduguri ppl😂




Page 2



★★★★




Zama tayi ta fashe da kuka tukunna saboda inda sabo ta saba amma ai ba'a sabo da wahala.
Sai da tayi mai isar ta sannan ta shiga ɗaki tayi wanka sannan ta dawo madaidaicin kitchen ɗin su, da
ƙyar ta ƙarasa fere doyar sannan ta ɗora yar tukunyar ta a gas saboda Nabil na da kuɗi, ta ɗauki 300 ɗin
daya ajiye mata na cefane ta fita kafin ta dawo tasan doyar ya dahu.......



Tana dawowa kam doyar data ɗaura har ya dahu tayi sauri ta yi jajjage.



Da ƙyar ta gama daka doyar sannan ta samu ta ɗaura miyar ganyen tana gamawa ta zuba su a
madaidaiciyar coolernta ta nufi ɗan madaidaicin ɗakinsa dashi, shigar ta keda wuya ta ganshi zaune
babu abinda yakeyi ya harɗe ƙafar sa, he looks very cute without faɗarsa agareta.




Ƙarasawa ta yi ta ajiye farantin a ƙasa ta ɗurƙusa a dai-dai wurin cikin nutsuwa irin na Ikimat ta ce
"Yallabai ga abincin naka, shin zan iya tafiya ya shugabana (Ni kam yau pending naga iko)(lolz).



Bai ɗago ya kalleta ba sannan shi bai ce mata ta tafi ba, a haka tai ta tsugunnawa a wurin, har sai da
ƙafar ta tayi tsami.

"Miƙo min ruwa" shine abinda ya faɗa ba tare da kuma ya ɗago ba, hannunta na karkarwa ta ɗauki cup
ɗin ta miƙa masa, kaɗan ruwan ya ɗan fallatsa masa ba shiri ya ɗago kanshi ya kalleta idonsa da ya yi jaa
wanda ke ƙara tsorata ta a duk lokacin da ta mai laifi suka kalleta.




Saboda rikicewan da ta yi bata san lokacin da ta sakar mai cup ɗin ruwan ya zubo mai ajikin sa ba.



A gigice ta fara magana "Yaya Nabil dan soyayyar ka da ma'aiki karka dake ni, wallahi juwa nake ji" ta
faɗa tana ƙara fashewa da kukan da bata san ranar dainawar sa ba.



Baiyi mata magana ba sai da yayi mata kallon second biyar, sannan ya ce "Cinye abincin da kika dafa.",
ɗago kai tayi tana kallonsa sosai, ta ga babu alamun sassauci a tattare da maganarsa.
"Ya Nabil Dan Allah Mai na maka? Mai na maka daka tsane ni ?? Mai na maka da baka son jin muryata ko
mu zauna a inuwa ɗaya a tare dani da kai? am hurting billah just say something". ta ƙarasa maganar tana
lulluɓe fuskar ta da mayafinta.



cikin muryarsa na i don't care yace "Ni da ke mun zama Sa'anni da za ki tambaye ni mai kika yi min ko?.''
Ya tambaye ta tare da ƙafeta da idanunsa masu firgitata.




"A'a wallahi Yaya bada kai nake ba dan Allah kamin rai kabarni na huta karka azabtar dani, ba nida
masaniyya akan auren mu dakai Dan Allah yaya". taƙa rashe maganar cikin sanyin murya.




Haka rayuwar ta ta cigaba a gidan Nabil duk ranar da wani na gidan su ko danginsu zasu zo a ranar zasu
yi farin ciki zai zauna a gaban su suyi wasa da dariya da ita yanca koda ta kai ƙara ba za'a taɓa yarda yana
muzguna ma ta ba.



A ranar zasuyi wasa sosai har ta gaggaya masa magana son ranta in sun tafi yayi mata dukan tsiya.



Yanca yake lallaɓata acikin dangi, har cousins ɗinsu mata na crushing akan sa.



Har kishi ya kan bayyana a tattare da su musamman kishi irin na Shuwa Arab

Banbancin kishin su da larabawa kaɗan ne.




March 11 2006
Bayan shekaru biyu




Yau ta ke jummah ta tashi da zazzaɓi ga amai da take ji yana taso mata ta rasa mey ke damunta, ga bacci
da kasala da take yawan yi.



Saukowa yake yi daga matattakalar benen dake cikin falon abinka da masu shi.

Cikin takunsa na isa ya ƙaraso kusa da inda take amai acikin sink ɗin dining area.

Girma ya ɗan ƙaru a tattare dashi, ga jikinsa ya buɗe ba kamar da ba, murtuke fuska ya ƙara yi cikin
muryarsa mai Amo ya ce "Hope is not what I'm thinking?" Cikin Tsananin firgita

Da rashin sanin ya iso wurin da take ta ɗago ta kai duban ta gare shi, ƙamshin turarensa ne ya cika mata
hanci ta ƙara yunƙurawa zatai aman, ta sake shi ajikin sa daga sama har ƙasa, gashi ta kasance jummah
farar shaddarsa ce ajikinsa.




Duk da halin data ke ciki bai hana ya wanka mata mari ba anan ta zube a ƙasa sumammiyya.

Komawa yayi sama ya janza kayan jikinsa.



Ko duba halin da ta ke ciki beyi ba ya saka kansa ya fita daga parlourn.

Sabuwar Mercedes Benz ɗinsa 2006 brand ya hau ya figi motar ya bar harabar gidan zuwa gidansu
Ikimat, wanda ko wani friday ya kanje gaida kawun nasa Sannan siriki agaresa.
Ko da ya isa gidan, ba wani gidan talakawa bane ba sosai da ɗan kyanshi ba laifi.

Bayan sun gaisa da Malam Umaru his Uncle, ya shiga ciki domin gaida mahaifiyyar Ikimat, har yake sanar
mata ai yace su taho tare ta ke faɗin ba zata zo ba.

Mahaifiyarta ta mai nasiha sosai akan rayuwar Aure sai haƙuri, sannan ta ɗaura da zata zo ya sameni.

Daga haka ya ajiye mata dubu biyar ɗinsa yayi mata Godiya ya ƙara gaba.



Ɓangaren Ikimat kam sai da sink ɗin ya cika yayi famm yana zuba sannan Allah ya sa ya ɗigo a fuskarta ta
ja wani dogon numfashin wahala.




Wani kukan baƙin ciki ta saka tana Allah wadai da halin ya Nabil.




Bayan ta gama raira kukan nata jiki ba ƙwari tai hanyar kitchen ta ɗauko sweeper da parker ta share
wurin sannan tai mopping duba da abubuwan zamani sun fara fitowa.



Wanka ta sake yi ta zauna ta na kallon kanta a madubi, Ma Sha Allah shine abinda na furta, ga wife
material amma ba ta faɗa hannun tailor mai kyau ba.

Ikimat kyakkyawar mace ce wanda kowani ɗa namiji ke buƙatar ya gani ya mallaki irinta.

Black beauty irin Kanuri mix with Shuwa Arabi ɗinnan.



Bata wani jin yunwa sosai hakan yasa bata wani damu da tayi girki ba, parking motar da ta ji a ƙasa shi
yayi sanadiyar murza mata ciki kamar wacca ta ga shadown mala'ikan mutuwa.
Ko da ya shigo da bai ganta a parlour ba ɗakin ta ya shiga direct, zaune ya tarar da ita ta zubawa mirror
Ido, idanun ta duk dishe dishen hawaye, zaro idanunsa yayi yace"Wifey what are you crying for?" ya
tambayeta, ɗagowa tayi ta kalleshi dalala, baki sake, ƙarasa shigowa yayi ya ajiye ledar dake hannun sa
Wanda yake cike da Hollandia yourghurt da suya sai ƙamshi ya ke.




"C'mon ta so kici abinda na siyo miki harda favorite drink ɗinki", ya faɗa mata haka yana kallon ta ido
cikin ido wanda itama shi take kallo ta ga reactions da ke cikin zuciyarsa.




Cikin siririyar muryarta tace "Ya Nabil am full bana son cin komai da daddaren nan".



Ran shi ɓace yace"kinga ta lallami na biki ki cire cikin da ke jikin ki ba tare da kin sani ba, amma da ke
daga ƙauyen Maiduguri kika fito bazaki taɓa ganewa ba, kuma Wallahi kinji rantsuwar musulmi ba zaki
haifi cikin nan ba" daga haka ya saka kai ya fita daga ɗakin.



Kuka ta ke son yi amma ta kasa, so ta ke ya barta ta je wurin mahaifiyyarta ta sanar da ita halin da take
ciki ko zata samu mafita a wurin ta amma ta san halin Nabil ba barinta zaiyi ba.

Yanzu duk da doctor yace last cikin da zata zubar kenan tayi surviving da mahaifarta ya Nabil still wants
to abort it.



Wannan wani kalar rayuwa ne, Ya Ubangiji ka kawo min ɗauki ka ramamin cikin gaggawa.
Zuciyarsa na tafasa ya bar gidan wurin ƙarfe 10 na dare shi kansa bai san inda zai je ba , tsayar da motar
yayi yana tambayar kansa Mey yasa yake cutar da yarinyar da bata da nufi akansa sai Alkhairi, maisa
bashida wani buri sai dai ya ga ya baƙanta mata.




Laifi ne dan tace tana sonshi? Wannan wani kalar jarabawa ne? , wani zuciyar ne ya ƙara zugashi tace
"kamanta itace ta shiga tsakaninka da farincikin ka?" daga haka ya ƙara kama hanyar shi direct gidan ya
koma.



Time ɗin har ta kulle ɗakinta da key, because tana tsoron ya shigo ɗakin ya taka mata ciki dan ba yau ya
fara ba.



Kuma babu abinda zai hana ta haifar cikin sai dai in mutuwa tai ko kuma zubarsa daga Allah ya ke.

Dan ta daina zubawa Nabil ido yayi mata abinda ya ga dama....




What's wrong with this guy readers?

Meke damun guy ɗinnan?



Ku dai ki biyo Pending Amarya dan jin yanca zata kaya✍️✍️

Ta tanada muku amsoshin ku

This is just the beginning.




We haven't started yet
This isn’t the end. It’s the beginning of who they must become.

Because the hardest trials... leave the richest scars.



The Noble Writters 🌕 🦋

🦋

Let's end the war together 💔🤝

Kuyimana share sannan

Reactions ɗinku Is All we need the Most 👑🦚



Try your possible best guys 😍



Let the world feel what we have written ✍️✍️✍️



Don't forget with Pending Amarya as usual 🦋 🫠https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?
mode=r_c*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.🤌💪



:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::



The Noble Writters 🦚🦚✊

Dedication is our strong 🦚🦚✊



THE REGRET 🙆🥀🌸🇳🇬
when love meets temptation 🦚 who survives?



💔💫



NIGERIA 🇳🇬

For Pending Amarya ✍️✍️



NDA DUBDO🦚

My Maiduguri ppl😂




CHAPTER ONE :THE STRUGGLE'S 🦋🥀




Page 3




★★★★
Kuma babu abinda zai hana ta haifar cikin sai dai in mutuwa tai ko kuma zubarsa daga Allah ya ke.

Dan ta daina zubawa Nabil ido yayi mata abinda ya ga dama....



Haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya har cikin ta ya girma babu wani cigaba da ta samu a wurin Nabil, in
banda tsangwaman daya fi na daa, kuma har yau bai barta ta je gidansu ba, gashi ba daman tayi girki
yace mata heavy food yake so duk da tsohon cikin ta haka take yunƙurawa ta mai duk abinda yake so.



Ya sha dukan ta ya take mata ciki babu adadi, ita dai abinda tasani shine In Sha Allah sai ta haife abinda
ke cikin ta lafiya.



In yana abu sometimes ta kanji akwai ranar da zai daina, saboda ba ta ce Za'a yiwa yaransa ba tunda
ya'yanta ne itama.

Idan tana jin kwaɗayin abu ta kan gayamai ya taho mata da shi, amma duk lokacin da ya dawo ta
tambaye shi ina abinda nace ma ka zanci, ya kan kalle ta yace mata babu ruwansa da cikin jikinta.



Ta rasa ya zatai da lamarin Nabil ace ɗan cikin ka ba ɗan wani ba.



15 of December 2006

Ranar ta kasance jummah tun safiyar ranar ta ke jin zafi sama sama bayanta gaba ɗaya ya riƙe ta kasa
zaune ta kasa tsaye.



Fitowa yayi cikin sky blue ɗin shaddarsa wacca ta mai kyau, ya tarar da ita sai safa marwa ta ke yi, har zai
wuce sai kawai ya tsinci kansa da dawowa baya.
Cikin muryarsa mai daɗi ya tambaye ta "What's wrong with you? ko baki ganni zan fita ba? baki iya
gaisuwa ba?." Kallonsa tayi still duk da cikin halin da take be hanata kokarin durƙusawa da niyyar gaishe
sa ba, duk da azabar da ta ke ji bata kai ga ƙarasawa ba ta durƙushe a wurin tana yarfa hannu, tsaki yayi
ya wuce tare da furta "Munafuka kullum cikin ƙaryar ciwon tsiya". Daga haka ya wuce wurin da yake
parking motarsa, har ya shiga motarsa yana ƙoƙarin tadawa ko mai yamanta sannan ya dawo cikin
parlourn.




Tana nan durƙushe a yanca ya barta sai kiran sunan Allahn ta ta ke yi da yarfa hannunta.




Kallonta yayi sosai sannan ya ce "ke malama taso na kai ki asibiti". "Bazan iya tashi ba yaya, yaya ka
yafemin mutuwa zanyi" ta faɗa tare da rushewa da kuka.



"Kinga am not ready for this drama, in za ki tashi ki tashi in kuma bazaki tashi ba toh kinga tafiyata".
Ƙoƙarta tashi ta fara yi da ta ga da gaske tafiya zaiyi ya barta.

Sannu a hankali har ta miƙe ta fara tafiya a duƙe.

"Ina kayan haihuwar naki yake?" Ya tambaye ta as usual, "Baka siyamin ba" shine abinda Ikimat ta faɗa.



" Toh mai ya hanaki tambayata?" Ya tambaye ta tare da ƙafeta da ido, "Yaya zafi yake min Dan Allah kayi
haƙuri, Ni tsoron gaya maka nake, kuma nasan inna faɗa ba siya min zakayi ba" ta ƙarasa maganar tana
gunjin hawaye.

"Tun da ke kika yiwa kan ki cikin?".



Tsaki ya ƙara ja akaro na biyu sannan yace "Zakiyi tafiya ko saina ƙarasaki" tafiyan tafara yi sannu a
hankali da ya gaji da tafiyar kawai ya sunkuce ta ya saka ta a bayan sit.



Bai kulle bayan motar da ya saka ta ba ya zauna a driver sit zai tayar da motar, juyowa yayi da kyau ya
kalleta da kyau sannan yace "Kinga in zaki ware jikin ki ki ware ki kulle min ƙofar mota ba akanki aka fara
samun ciki ba, mata nawa ne suke naƙuda basuyi haka ba saike, C'mon kulle min ƙofar motana.
A hankali ta lallaɓo ta kulle ƙofar saboda ita kaɗai tasan wani hali take ciki. Lallai Ya Nabil ya cika maƙiyin
ta wanda kake cikin wannan halin da bai tausaya maka ba ai bazaku taɓa jituwa ba.



Tayar da motar yayi sannan ya ɗauki hanyar Hospital ɗin Nassarawa, basu wani daɗe ba suka ƙarasa
Hospital ɗin.

A kiɗime ya fito daga motar ya ɗauke ta a hannu kamar yar baby yana ta zabga uban sauri (Namiji
hankaka 😏).




kallon fuskanta yayi tayi yana tafiya she looks pale.Mutanen wurin sai tausaya mishi suke, because kana
ganin ta kasan son da yake mata bana wasa bane ba (Nabil ka ji tsoron Allah 😂)



Doctors ne suka duba ta, suka ga ba adai dai kan yaron cikin nata yake ba dole CS za'a mata idan kuma
dole haifar sa za tayi za ta sha wahala ko kuma a rasa ta gaba ɗaya.



Ko da aka samu Nabil aka gayamasa ce wa yayi shi dai matarshi ta rayu (Ni pending Nabil zai min
lahani 😂)




After 5 hours




..Cikin Ikon Allah aka ciro kyakkyawar yarta mai kama da ita.



Jijjiga ta farayi wanda da ƙyar likitoci suka tsayar da hakan.
Nabil aka kira ya kawo kayan baby a gurguje yaje bakin Hospital ɗin ya siyo kaya da

Kayan tea, da dai sauransu.



Bayan an shirya baby aka kawo masa ita Doctor ɗin tace "Here is your pink jet" , murmushi yayi ya ce
"Tnx".

Kallon yarinyar yake wanda a ta ke ya ji wani matsanancin sonta ya ɗirar mai.

Duk da jaririya ce amma hakan bai hana bayyanar da kyawunta ba.




Sai motsi ta ke da bakin ta alamun yunwa ta keji.



Huɗuba yayi mata da sunan late sister ɗinshi FATIMA amma za'a ɗinga kiranta da LIYANA.




BAYAN FOUR DAYS 💫




Yau ne aka sallami su Nabil daga Hospital, kafin suje gida kam kusan rabin familynsu na gidan amma ba
kowa yazo daga Maiduguri ba, duba da yanca Nabil ke da zumunci da son yan uwa.




Ko da suka dawo gida bai yarda ya bar kusa da ita ba Ƙanwar Ikimat tai ta mai mita ya ƙi fita baƙi su shigo
shi mai mata.
Ita dai Ikimat ba abinda ta keyi sai murmushi wanda yafi kuka ciwo.



Dan fatan ta bai wuce ace za'a tattara ta a mayar da ita gidansu ko gidansu Nabil ba.




Bayan anyi suna anci ansha an hantse bata ji alamun za'a ce ta tafi gida ba.

Ashe Nabil ya zaga baya yace ita ta faɗa mai babu inda zata je ta bar gidanta..



Babu wanda ya nuna mata alamar komai bayan taji abinda aka faɗa mata, tayi kuka sosai sannan tayi wa
Nabil Allah ya isa ba adadi, haka rayuwarta ta cigaba kullum cikin ƙunci amma takan samu sauƙi ta
sanadiyyar Liyana.



Idan ya dawo daga kasuwa kam Liyana ya ke ɗauka ya tafi ɗakinsa da ita har sai in kuka take sannan zai
dawo da ita, kuma in ya dawo da ita ɗin zai tsaya akanta ne har sai ta gama breast feeding ɗinta zai
amshe ta ya koma ɗakinsa da ita.



Liyana kam ta fi shaƙuwa da mahaifinta, kyakkyawar yarinya Ma Shaa Allah, bata da hayaniya ko kaɗan.



After 7months



Liyana ke rarrfe a parlour dake ranar Sunday ne bai fita kasuwa ba, ita kuma Ikimat na kitchen tana
haɗa breakfast, rarrafen ta take yi hankali kwance, tana gwarancinta irin na yara jarirai, can jikin socket
kam heater ne ta jona ruwan zafin da zata dama kunu saboda yanayi na mai shayarwa sai da abu mai
ruwa da zai kawo mata ruwan nono.



Sam ba ta ji lokacin da ya ajiye Liya a parlour ba, kawai ita dai taji ihun Liyana tunawa da ruwan zafin da
tayi ta saka a socket, Bata san lokacin da ta yar da wuƙar hannunta ba ihu ta ke yi tana kuka haɗe da
gwarancinta a haukace Ikimat ta ɗauke ta sai taga ashe bata kunna socket ɗinba.
Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta juyo taji an fisge Liyana a hannunta tare da

Please Login or Register in order to submit comment