Reading The REGRET by sani Amarya Chapter 21 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi maganar kamar za ta yi kuka.

Classy Reeda dake zaune kusa da Ammin ce ta ce ''Na biyo ku sisi.?"

Murmushi ta yi tare da faɗin ''Why not.''

Daga haka suka fice daga gidan.
><><><>><><><><>><><><>




Gidan tsaf yake a gyare masu aiki na ta haɗa hadan gyaran shi, ko ina na gidan tsit yake babu hayaniyya,
sai kukan fararen tsuntsaye dake tashi a gidan.



Direct part ɗin Mami suka nufa su ukun cikin shigarsu na abayoyi masu tsadar gaske.



Cikin siririyar muryarta ta yi sallama haɗe da shiga cikin luxury living room ɗin da ƙamshin turaren wuta
mai sanya nutsuwa ke tashi a parlourn.




Ƙarasa shigowa cikin parlourn suka yi Mami na zaune a tamkeken falon cikin wani holland atamfa da aka
ma ta ɗinki na alfarma da shi.



Sultan na daga gefenta kansa akan cinyar Mamin da take ma sa massaging kan na sa, wanda alamu sun
nuna kan nasa ciwo yake ma sa.




Ƙarasa shigowa ta yi ita da ya'n rakiyan na ta kanta a ƙasa har ta ƙaraso wajen da suke haɗe da
durƙusawa ta na mai gaishe da Mamin.



Amsa gaisuwar ta yi, tare da shafa kanta ta na mai sanya ma ta albarka haɗe da amsa gaisuwar su Ilham
ɗin da sai wani nannoƙewa take kamar sabuwar mayyar da ta lashe ɗan kishiyyarta.
''Daughter ya kaɗaici.?"

Murmushi kawai ta yi tare da faɗin ''Mami mai wankin ya miki ne.?" Ta yi maganar zuciyarta na ɗan
faɗuwa.



''Laah, daughter tun jiya da yamma bayan tafiyarki ya min wankin, and kin san da washing machine ne, ai
na gode sosai wallahi Allah ya yi albarka.''

''Amin Mami zamu wuce.''

''Noo wait yau ɗin nan na dafa miki favorite ɗin ki, ina ta jiranki ba ki zo ba, nake faɗawa Sultan zai kai
miki after noon, buh tun da kin zo is better ki tafi da shi.''



Kunya ne ya kamata, dan tun da Mami ta san zancan cikin jikinta, ta koma tarairayarta fiye da da.



Hannunta riƙe da wani tray haɗe da wasu plates aciki dake cike da kayan ciki, sai miyan iwedu da amala
wanda ya yi baƙi ƙirin.

Ji take kamar ta janyo hannun Mamin ta fara cin abincin, a hankali Mami ta sauke abincin tare da ajiye
ma ta shi a gabanta.



''Daughter aci daɗi lafiya, dan ke kaɗai na girka, and I hope you will like it.'' Mamin ta yi maganar tare da
amsar ruwa da lemon kankana daga hannun ya'r aikinta ta na mai dire musu shi.

''In shaa Allah Mami, kin san you're the best cooker ever." Liyama ta yi maganar a ɗan kunyace.



''Aunty Liyana ina wuni.'' Sultan ya faɗa ya na mai k'afeta da idanunsa masu firgita ta.

Ba ta amsa shi ba ta cigaba da cin abincinta.



Ƙarar buɗe ƙofar falon da aka yi shi ya ja attention ɗinsu gabaɗaya zuwa can wurin entrance ɗin. Amir ne
cikin shigarsa na kaftan sky blue da ta ma sa kyau sosai, ya ƙaraso falon haɗe da gaisar da Mamin,
kallonsa ta yi sosai tare da faɗin ''Son ya gida.?" ''Mami Alhamdulillah, daman Mami na ce mu ɗan gaisa
ne tun da hanya ya biyo da ni ta nan ɗin.'' ya yi maganar ya na ɗan daddanna wayar hannunsa ya na
kallon Liyana da ta kasa haɗa ido da shi.




''Mami ayi min package na shi na ƙoshi haka.'' ta yi maganar ta na mai marairaice face ɗinta.



Order ta bawa masu aikinta, Sultan kam silalewa ya yi ya bar parlourn, yayin da Amir ya duƙufa da
chatting ɗinsa, a take wayarsa ta fara ringing, ganin mai kiran na sa ne ya sanya shi tuntsirewa da dariya
a fili tare da ƙara kallon Liyanar.



Sai ta camerar wayarsa ya ƙara yi tare da zooming ɗin kyakkyawar fuskarta dan da ɗan tazara tsakaninsu
ya ƙara ɗaukan pictures ɗinta kusan uku a dai-dai time ɗin da ta ɗago idanunta ta kalli Amir ɗin, tare da
tura ma Hydar da ya addabe shi da kira tun first picture da ya tura ma sa.



Haka nan kawai ta ji da cewa Amir is up to something that will lead her to matsala ko akasin haka, hakan
ya sanya ta tashi tare da faɗin ''Mami sai da safe.'' ta yi maganar a sanyaye.



''Mabaruka, packaging box ya zama allura ne.?" Mamin ta faɗa da ɗan ƙarfi.

''Ga shi Maa.'' Mabaruka ta faɗa tare da miƙawa Mamin.

''Ina wanda na zuba a warmer da nace Sultan ya kai ma ta.?" Mamin ta tambaye su.

''See it here Maa.'' Agnes ta faɗa tare da ƙarasowa wajen da wani lunch box mai kyau a hannunta.



Miƙawa Ilham lunch box ɗin ta yi, shi kuma packaging box ta miƙawa Reedah.



Sannan suka fara harraman tafiyya, tsayar da su Mami ta yi tare da kawo musu wa ta leda dake cike da
turaruka.



''Amaryarmu har za ki tafi.?"
''Eh Yaya Amir, sai anjima.'' ''Okay dear.''

Daga haka suka fice daga gidan.



Tun a ƙofar gate ɗin suka fara dariya, Ilham na ta kwaikwayon Liya yadda take wani sissinne kai kamar
mayya.



Banza ta yi dasu tare da shiga cikin gidan Nenehn da har motarsu Abbhin na pake, alamun sun dawo
gidan.




<><><>><><><><>><><><>><




A kwance yake yau ɗin bayan ya dawo daga meeting ɗin da suka yi da ADAFAR VENTURES na Singapore
akan kayan da suke son a siyar musu da shi, laptop ɗinsa a kan cinyarsa sai wayarsa a hannunsa ya na
kallon wasu reels a Instagram. Sannan ya ga saƙon Amir alamun ya turo ma sa hoto.



A hankali ya ajiye laptop ɗinsa tare da shiga cikin message ɗin, zaune take ta na wasa da hannunta abinci
a gabanta, sai ɗayan kuma ta ɗan cuno baki alamun kamar wasu da portait ya lulluɓesu he can't say su
waye su.
Sai kuma ɗayan ta ɗago fuskarta ta zazzaro idanunta kamar wadda ta yiwa sarki ƙarya.

He just smiled, tare da ƙurawa pictures ɗin idanu, wanda suka ma sa kyau sosai.



Reply ya ma sa da faɗin ''For.???" Emojis ɗin dariya Amir ya turo ma sa tare da faɗin ''Ka dawo ka
kwashi gara my guy, ta dawo yadda kake so wallahi.''

Ganin message ɗin Amir ɗin ya sa wani kalar murmushi suɓuce ma sa tare da ma sa reply ɗin ''Really.?"

''Yeah.'' daga haka suka shiga wani hirar da ban.



Bayan sallar isha ma office ya koma ya duba wasu takardu tare da dawowa gida.




><><>><><><>><><><




Ko da suka shiga cikin falon da Mama Fatuh suka fara cin karo, suna zazzaune kamar ana sulhu.

Can dai suka saki jikinsu gaba ɗaya aka fara hira.



Ƙarfe goma na dare kowa ya watse, dan sai da suka ƙara wani faɗan da Yusrah, sannan ta kamo hanyar
gida ita da Salimah.



Bayan Salimah ta buɗe gate, shigar da motar ta yi tare da ajiye shi a muhallinsa.

Ko ina na gidan shiru, direct backyard ta nufa tare da kunna wutan solar sannan suka shiga cikin gidan,
da ko ina ya wadatu da haske.
Direct ɗakinta ta shige dan ba yunwa take ji ba, dan abincin gidan Mamin sosai ya yi ma ta rana.

Toilet ta shige tare da yin wanka ta fara shiryawa cikin kayan baccinta dan gobe ta na tunanin zuwa
ganin Doctor.




Wayarta ne ya fara ringing hakan ya sanyata ƙarasa k'ulle towel ɗin jikinta tare da ɗaga wani number
ƙasar waje da ba ta san code ɗinsa ba.



Har za ta ɗaga sannan wayar ta katse, in less than 5 seconds aka ƙara biyo kiran, a hankali ta ɗaga tare
da manna wayar akunnenta.



''Assalamu alaikum.'' ta faɗa a sanyaye, amma ba'a ba ta amsa ba, ''Hello.'' ta ƙara magana ta na mai
ɗauke wayar a kunnenta haɗe da mai da shi.



''With whose permission kike fita da mota, and da izinin wa kike fita, bayan school na yarje miki da kije?,
kin fara wasa da ni ko.!?" HYDAR ɗin ya faɗa a ɗan faɗace.



Wani kalar bugawa ƙirjinta ya yi jin muryar na sa a cikin kunnenta, sannan kuma a hankali ta ce ''I'm
sorry, Mami ce ba ta da lafiya, shiyasa nake fita, amma trust me wallahi babu inda nake zuwa bayan
nan.'' ta ƙarasa maganar a sanyaye.



''Shi kuma kwanar badawan gidan ƙanwar ubanki ne acan.?" Wani iri ta ji a ranta da kalar amsar da ya
bata, hakan ya sa ba ta amsa ma sa ba ta yi shiru.

''Ba magana nake miki ba?, kika min shiru.?" Ya yi maganar da ɗan zafi.

Cikin shashsheƙar kuka ta ce ''Yaya dan Allah ka yi haƙuri.'' ta yi maganar a sanyaye.



''Shut that your dirty mouth idan ina magana, ni sa'anki ne.?" Ya ƙara faɗa a tsawace.
Haushi faɗan da yake ma ta ya ba ta dan idan ta cigaba da sauraronsa za ta iya mayar ma sa da martani,
hakan ya sanya ta kashe wayar haɗe da cilli da shi akan gado ta na mai fashewa da kuka.



Cikin shashsheƙar kuka ta ce ''Mai nayi wa kowa ya tsane ni, ni Fatimatu, mai nayi?, ba ga uwar da ta
haifeni ba ba ga kowa ba, saboda zallar tsana da Neneh ta yi min ɗan bariki ta aura min, wanda ba ya
daraja Mahaifina, why me??, why now?, why not later?, ya Rabbi I'm still young for all this, wayyo Allah
na Aliyu zai min lahani, Allah ya ishewa mahaifina kalar cin mutuncin da kake yi ma sa, kai ma Billah sai
an ma ka.'' ta ƙarashe maganar hawaye na fita daga idanunta.....




''Ya Ubangijina ka basu daman share."



Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟

Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂



*THE REGRET*

PENDING AMARYA CE ✍️

JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.




**Pending Amarya 49**



What goes around comes around ⏮️⏩

Every ending is a new beginning 🌕
even if the heart disagrees.✅🌕 🤝🦋



🤍🫧🤧



Not edited 🌟💔🥹



****




Cikin shashsheƙar kuka ta ce ''Mai nayi wa kowa ya tsane ni, ni Fatimatu, mai nayi?, ba ga uwar da ta
haifeni ba ba ga kowa ba, saboda zallar tsana da Neneh ta yi min ɗan bariki ta aura min, wanda ba ya
daraja Mahaifina, why me??, why now?, why not later?, ya Rabbi I'm still young for all this, wayyo Allah
na Aliyu zai min lahani, Allah ya ishewa mahaifina kalar cin mutuncin da kake yi ma sa, kai ma Billah sai
an ma ka.'' ta ƙarashe maganar hawaye na fita daga idanunta.....
Tun da ta yi cilli da wayarta take wani kalan kuka mai cin rai sannan kuma a hankali ta sanya kayan
baccinta haɗe da yin kwanciyyarta.



Ko ta kan wayar ba ta ƙara bi ba wani kalar bacci ya kwasheta.




Washegarin ranar ma bayan ta gama abubuwan da ta saba ita da Salimah, shirye take cikin wani hijjabi
mai kyau da tsada, wanda ya mugun dacewa da fatarta.



Fuskarta ya yi wani haske ya yi kyau sosai, hannunta riƙe da wayarta da car key ɗinta, ta matso tare da
fara ƙoƙarin yin breakfast ɗin dake jere saman dinning.



Fresh milk kawai ta sha wanda Salimah ta dafa ma ta da Lipton da kuma kaninfari, sannan ta wuce tare
da sanya Salimah buɗe ma ta gate ta fita daga gidan.

Sosai ta wataya a school ita da Lily sai da suka sha yawo, dan kalamansa na jiya sosai suka taɓa ma ta rai.



Ko da ta dawo gidanma su Ily da Reedah da Rashanda har da Unaisah duk suna cikin falon suna jiranta.

Hakan ya sanya ta farin ciki sosai suka ɗinga hira har sai da suka ja ta yau tayi post ɗin reel a Instagram,
wanda acikin second talatin sai da ta samu almost 20k likes comments 1k ina ta shiga, sun daɗe ba su
ganta ba( she finds her self again on social media, Dan hakan sosai ya sanyata farinciki).
After 2 months 📚🥀💎




Zaune take fruits na cike taff a gabanta, jikinta na sanye da wani silky gown wanda ya kame ma ta jiki,
har ya yi sanadin bayyanar da ɗan ƙaramin cikinta.



Salimah na gyara falon, ita kuma ta na shan fruits ɗin da take mugun jin daɗinsa.



Wayarta ne ya fara ringing hakan ya sanyata ɗagawa ganin Reeda ce ke kiran na ta, ''Hello Babe.''
Reedah ta faɗa a ta ɗayan ɓangaren.

''Yeah Babe, mai ya faru.?" Ta yi maganar a sanyaye.

''Nothing na kira ki ne mu ɗan gaisa.'' Okay dear I really appreciate.'' daga haka ta katse wayar, dan har
ga Allah yanzu ta tsani magana mai nisa.



''Wai ke Salimah uban mai kike gogewa tun ɗazu a jikin TV ne, duk kin cika waje ke ba ƙiban arziƙi ba.''
Liyana ta faɗa a zafafe dan yanzu kowa ma haushinsa take ji.

Shiru kawai Salimah ta yi mata, dan yanzu wani kalar faɗa Liya ke tsiro ma ta da shi kamar jiƙar Bahubali.

Wayarta ne ya ƙara yin ringing na wani baƙon number da tun kusan mintuna goma da suka wuce yake ta
faman kiranta.



A zafafe ya ɗaga wayar tare da karawa a kunne tare da faɗin ''Wayee?!." Ta yi maganar da zafi duk da
zuciyarta na dukan uku uku.




Cikin muryarsa mai daɗin sauraro ya ce ''How dare you keep me waiting a airport tun ɗazu ina kiranki a
waya?." Sassauta muryarta ta yi tare da faɗin ''Yi haƙuri ban san kai ne ba shiyasa.''

A tsawace ya ce ''Za ki zo ki ɗauke ni ne ko za ki tsaya haukan ki anan wajen.?"
Ba ta bashi amsa ba ta katse wayar tare da ɗauko wani dogon hijabi da ta dawo da shi daga hospital
yanzu, sai safar hannu da na ƙafa tare da ɗaukan mukullin motarsa ta na ƙara jaddadawa Salimah ta ƙara
gyaran gidan sosai.




Ikon Allah ne kaɗai ya kaita zuwa Airport ɗin, ta cikin mudubi ta hangesa, hakan ya sanyata parking
motar na ta ɗan nesa da shi haɗe da saukowa daga cikin motar.



Tsaye yake hannunsa ɗaya a kunnensa wanda da alamu sun nuna waya yake, ɗayan hannun kuma dake
ɗaure da agogon Rolex explorer ll na dafe da trollynsa.

A hankali ta sauko daga cikin motar iska na ɗan kaɗa hijabinta, ba tare da ta damu da hakan ba ta ci gaba
da nufar wajen da yake.




Tun da ta nufo wajen da yake ya fara ƙafe idanunsa da ita, dan da tafiyarta ya gane saboda wani ƙiban
da ta yi, walking slowly ta ƙaraso wajen da yake tare da faɗin ''Yaya, sannu da zuwa.'' ta yi maganar tare
da sauke idanunta a ƙasa.

Ta yi kusan second biyar a hakan sannan ta ɗagoda kanta a hankali, a tunaninta ya na tsaye ya na
kallonta, sai ta ga akasin hakan, because har ya nufi cikin motar , ya na zaune kujerar kusa da driver.




Wani kalar baƙin ciki ta haɗiya, har ƙwalla na niyyar zubo ma ta , gudun kar ya dizga ta a cikin jama'a ya
sanyata ɗaukan trollyn da ya bar ma ta ta nufi bayan motar da shi.
Bayan ta saka trollyn ma wucewa ta yi ta zauna a driver sit ɗin motar tare da yiwa motar key ta na mai
barin airport ɗin.




Acikin motar ma da dukkannin hankalinta take tuƙi gudun kar ta yi mistake da zai sanyata shan mari
yadda ta ƙular da shi ɗin nan.




''By your left hand.'' ya yi maganar tare da ɗan mazewa, ba ta ma sa musu ba ta cigaba da jan motar.




Ƙara tsintar muryarsa ta yi ya na faɗin ''Kai ni wajen da ke da sugar daddies ɗinki kuke zuwa.'' ya ƙarasa
maganar tare da mayar da kujerar motar baya domin ya ɗan fara hutawa.

Shiru ta yi domin ita har ga Allah ba ta taɓa fita da wani sugar daddies ba, parker motar ta yi tare da
faɗin ''Yaya ina ne zamu je?, ban gane wajen sugar daddies ɗin ba.'' ta yi maganar innocently a ɗan
marairaice tare da turo bakinta kaɗan.

Ƙurawa kyakkyawan lips ɗinta ido ya yi, sannan a hankali ya sa hannunsa haɗe da damƙo kanta ya fara
ba ta wani kalar french kiss.



Ba tayi jayayya ba ta bashi haɗin kai acikin motar, jin ana musu wani kalar mahaukacin horn ne ya
sanyata realising cewa akan titi ma ta yi parking motar.



A hankali ya saki bakin nata ba tare da yaso ba, ita ma sam ranta bai so ba, hakan ya sanyata tayar da
motar tare da barin titin.

Wani kalar jaa idanunsa suka yi, murya a shaƙe ya ce ''Hydar's garden, right now.'' ya ƙarasa maganar ya
na ɗauke kansa gefe, dan kallonta kwance ma sa lissafi yake.
Gudu take shararawa a titin a hankali ta na jin yadda kanta ke wani mugun sara ma ta, a hankali ta shiga
cikin tamkeken gate ɗin da ya gaji da haɗuwa, tare da yin parking a wajen da ya dace ta yi.



Sauka ya yi a cikin motar, ita ma ta bi shi, ko ta kan reception bai bi ba ya danna wani kalar remote a
hannunsa wanda hakan ya sanya glass ɗin wajen juyowa ya zama kamar ƙofa, shigewa ya yi ciki, ita ma
ta bi shi, yanayin ginin kaɗai ya isheka ka san da cewa kuɗi sun zauna sosai.

Because ginin penthouse ne, looking very rich, ta cikin glass ɗin za ka iya ganin wanda yake waje,
musamman yadda wajen yake idan ba ku manta ba.




Ta na tsaye ta na kallon kalar yadda gidan ya tsaru, taji mutum ya wani kalar ɗagata sama.



Ba ta musa ma sa ba ta ba sa haɗin kai, then they made love.



Wani kalar jinta yake a ransa, barin ma idan ya tuno kalar ɗawainiyyar da ta yi da mahaifiyyarsa, and
then idan ya tuna a Virgin ya sameta, ya kan ji daɗi sosai.

A kwance take a jikinsa , he can feel the over heat da yake fita daga jikinta wanda shi kansa zafin jikin ya
na affecting na sa, ga wani kalar surutai da take marasa kan gado.



''What's wrong with you.?'' ya yi maganar ya na mai shafa bayanta, ka sa magana ta yi wasu kalar
hawaye na fita daga idanunta.



Jin saukar hawayen a kafaɗansa hakan ya sanya shi mirginota ta koma ƙasan sa tare da kallonta daga
sama har ƙasa, cikinta ya ɗan taso ba kamar yadda ya kusanceta ba aranar farkon su.




Hannunsa ya sanya akan cikin nata tare da ɗan dannasa, saurin riƙe ma sa hannu ta yi cikin muryarta da
ba ya fita ta ce ''Stop.'' ta yi maganar hawaye na sake gangarowa daga ƙuncinta.
''Mai yake damun ki wai ko kin fara hauka ne.?" Ya yi maganar ya na ƙara ƙafeta da ido.

Ƙanƙameshi ta yi da sauri ta na sauke wani kalar ajiyar zuciya, wanda hakan ya ƙara firgita tunaninsa.



''Ki yi wanka mu koma gida.'' still shiru ta yi ba ta ma sa magana ba.

''Liyana!." Ya kira sunanta da ɗan zafi.

Fashewa ta yi da kuka sannan a hankali ta ce ''Yaya, jini na zafi, cikin fata na zafi yake min.''

''Ya na miki hakan ne.?" Ya tambayeta ya na mai ƙafeta da idanunsa.

A sanyaye ta ce ''Just today.''

''Shirya muje hospital, can you dress up ko na taya ki.?"

''Your wish is my command sir.'' ta yi maganar da ƙyar.



Bayan sun shirya, direct nearest hospital suka nufa bayan sun fito daga ƙauyen, test aka yi ma ta,
because it's emargency kuma Hydar ya sakar musu kuɗi, 7 hours aka basu kafin test ɗin ya fito.




7 hours suka yi a hospital ɗin, suna jiran sakamakon, Liyana ce kwance akan gadon emergency room,
hannunta riƙe da cikinta kamar mai tsoron ka da wani abu ya samu abin da ke cikin nata. Hydar na tsaye
hannunsa goye da bayansa yana ta safa da marwa, ya na kallonta a kai a kai.



Ƙarar buɗe ƙofan da ya ji ne ya ba shi daman juyowa da sauri, wa ta matashiyyar nurse ce ta shigo, ta
kalli Hydar ɗin tare da faɗin ''Sir doctor is calling you for the results.''



Sai da ya kalli Liyana da kyau sannan ya matsa kusa da ita tare da shafa kanta ya fice daga room ɗin.
Lumshe idanunta ta yi hawaye masu zafi na gangarowa, sannan a hankali ta ƙara rufe idanunta kamar
mai bacci.




><><><><>><><><>




Doctor Lamil na zaune akan kujerar da aka tanada ma sa ya na duba takardun da sai confusing ɗinsa
suke, kallon giant guy ɗin da ya shigo ya yi sai da suka ƙara gaisawa, sannan a hankali ya ce '' We found
something unusual, the scan bayyana womb...... Amma ba mu ga fetus ba. The cavity is blocked by a
mass, we can't figure out what's actually wrong with your wife Sir.'' ya ƙarashe maganar tare da kallon
Hydar ɗin da idanunsa suka yi ja.



Sai da Hydar ya ja wani kalar numfashi sannan ya ce ''Mass kuma?, mai kuke nufi da Mass ɗin.?"



Sai da Doctor ɗin ya ɗan numfasa sannan ya ce ''Mass a nan na nufin wani abu ne da bai dace ba a cikin
mahaifa, yana iya zama cyst, growth, ko wani abu da ke mamaye wuri. Mass na iya leading to Cancer,
amma ba zamu iya tabbatar da hakan ba tukunna, Wannan shi yasa muke buƙatar ƙarin tests.'' doctor
ɗin ya ƙarasa maganar ya na ƙara ƙafe Hydar da ido.




Wani kalar firgici ne ya ziyarci Hydar ɗin a lokaci ɗaya, cikin wani kalar murya wadda bai san kansa da shi
ba ya ce ''Cancer fa ka ce Doctor.?" Ya yi maganar a ɗan ruɗe...... ''



''Love is blind.''😌
''Ya Ubangijina ka basu daman share."



Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟

Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂

*THE REGRET*




PENDING AMARYA CE ✍️




JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION



The Noble Writers Team.




**Pending Amarya 50**



What goes around comes around ⏮️⏩

Every ending is a new beginning 🌕
even if the heart disagrees.✅🌕 🤝🦋



🤍🫧🤧
Not edited 🌟💔🥹



****




Wani kalar firgici ne ya ziyarci Hydar ɗin a lokaci ɗaya, cikin wani kalar murya wadda bai san kansa da shi
ba ya ce ''Cancer fa ka ce Doctor.?" Ya yi maganar a ɗan ruɗe...... ''



''Bamu tabbatar ba tukunna.'' doctor ɗin ya faɗa tare da gyara eye glasses ɗinsa.



Wani kalar iska Hydar ɗin ya furzar haɗe da ficewa daga office ɗin, direct ɗakin da aka ajiye Liya ya nufa.



Ta na kwance yadda ya barta, ba ta canza position ɗin kwanciyarta ba, a hankali ya tako zuwa inda take
tare da zare first aid ɗin da aka ba ta, ba ta da wani ƙarfin hana sa abin da ya yi niya, saɓa ta ya yi a
hannunsa ya fice daga hospital ɗin ba tare da ya kalli Nurses ɗin dake ta ma sa magana ba.




A hankali yake driving har ya ƙaraso Babban hospital ɗin birnin Kano, wato Aminu Kano teaching
hospital, dake ya san wani doctor a hospital ɗin saboda same school suka yi da shi, hakan ya sa akai
saurin fara gwaje gwajen da ya dace a yi a kanta, tare da ba ta injection domin ta samu bacci, dan har
ƙarfe sha biyun dare ya yi kuma babu wani ci gaba da aka samu.
Around 12:30am results ɗin suka fito, thesame with na wancan hospital ɗin, kuma abin mamaki wannan
na nuna Cancer mai ƙonar da jini ya na yawo a jikinta, wani kalar tashin hankali Hydar ya shiga a wannan
daren wanda bai taɓa ganin kalarsa ba.




Hannunsa ya kai jikinta ya ji wani mugun zafi fiye da na ɗazu, hakan ya sanya shi saurin janyewa tare da
kallon kyakkyawar fuskarta da ya ɗan rame a lokaci ɗaya.



So yake ya kira iyayen su ya sanar da su amma he can't do that duba da yanayin daren da ya tsala.

Wayarsa dake jikin gadon da take kwance a kai ya ɗauka tare da duba notification ɗin telegram ɗinsa tun
bayan da ya yi wa Amir reply lokacin da ta zo ɗaukansa.




Message ɗin Amir ya fara karantawa kamar haka ''Hey Man, barka da shigowa, hope ka huta sosai yadda
ya dace, na je hotel na ka kuma ban gan ka ba, still naje gidanka Salimah ta ce min ba ku dawo ba, hope
say you did nothing to that girl OOO.'' wani kalar jaa idanunsa suka yi tare da dannawa Amir ɗin kira.



Sai da ya yi ring huɗu sannan ya ɗaga, ''Assalamu alaikum, kai ba ka yi bacci ba za ka takura rayuwata
ko.?" Amir ya yi maganar da magagi.



Hydar bai yi magana ba sai wani kalar ajiyar zuciya da yake saukewa, a can ɓangaren Amir wani kalar
bugawa zuciyarsa ta yi, tare da faɗin ''Hydar hope babu abin da ka yiwa yarinyar nan.?"

Still bai yi magana ba ya yiwa Amir ɗin banza ya cigaba da ajiyar zuciyarsa.

''wai wannan wani kalar iskanci ne Hydar, ka yi min magana mana.''

Juyar da kansa Hydar ya yi tare da kallon Liyana da take numfashi da sauri da sauri, idanunta na saukar
da wani hawaye mai zafi, jikinta na wani kalar kakkarwa.
Hakan ya sanya shi fashewa da wani kalar kuka tare da buga kujerar da yake kai ya ce ''Amir zan rasata,
Amir mai sa sai na so Abu nake rasa shi?, why?, Wallahi Amir kai ma ka san kalar son da nake yi ma
Liyana, please talk to

Please Login or Register in order to submit comment