Reading The REGRET by sani Amarya Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanka mata mari, dafe
ƙuncinta tayi ta kalli Nabil da yake kallonta kamar zai ɗaga ta sama, cikin muryarsa mai Amo ya ce "Ba ki
da hankali ba kiga na ajiyeta ba da ban kashe socket ɗinba lokacin da na ajiyeta ba da tuni pink jet ɗina
ta ƙone".



Kallonsa ta ke babu ko ƙiftawa sannan hannunta bai bar ƴar kafaɗar Liyana ba alamu dai kamar baka isa
ka ƙwace min ƴa ba.




"Ba za ki saketa ba?" Cikin muryarta mai sanyi da kuma nuna gajiyawa da halin Nabil ta ce "Kai ka haifa
min ita? Ba za'a saketa ba ɗin kai duk abinda zakayi".



Kallonta ya shiga yi bako ƙyaftawa, sannan ya juya ya ajiye Liyana akan kujera ya bata abin wasa haɗe da
cewa "Lemme deal with your mom little princess" ƙyalƙyacewa Liyana tayi da dariya kamar taji abinda ya
faɗa sannan ta maida hankali kan wasanta data keyi.




Zare belt ɗin jikinsa yayi ya naɗa shi a hannunsa sannan ya fara dukanta dashi ta ko ina ya samu a jikinta
lafta mata yake yi, tun da ya zula ma ta ɗaya ta ke yaya kayi haƙuri amma ina Nabil zaneta ya ke taki ina,
tun tana kuka har ta gaji.



Tsaki ya ja tare da faɗin "mara kunyar banza". Sannan ya ɗauki Liyana yayi sama da ita.




Haka rayuwarta ta cigaba babu wani sabo tsakanin ta da ɗiyarta har Liyana tayi shekara uku a duniya .
Kuma acikin shekaru ukun nan sau biyu ta taɓa zuwa gidansu duk da babu wani nisa tsakanin bachirawa
da hotoro.




Shi zai kaita school shi zai dawo da ita can wurin aiki ma tunda tayi wayo tare suke zuwa tsakanin ta da
Liyana sai dai gaisuwa da shiryata ta tafi school shima ba kullum ta ke shirya ta ba.




Yau dai ta kasance Sunday tun safiyar ranar ya sanar da ita akwai taron family , a gurguje tayi ayyukanta
sannan ta shirya cikin wani after dress Mai ɗan kyau tunda Nabil duk iskancinsa yana wadata ta da komai
na more rayuwa, tayi kyau ba laifi sannan ta riƙe hannun Liyana dake tsaye kusa da Abbanta sai da ta
kalli fuskar mahaifinta sannan ta koma wurin Umminta .



Murmushi ya mata mai nuni da alamun ki je wurinta sannan yayi gaba cikin shigarsa mai kyau.




Sabuwar motarsa kirar Peugeot ya hau 2009 brand new blue color sai ɗaukar Ido take yi.



A hanyarsu na zuwa gidan suna zuwa aka fara gabatar da taro Ikimat kam kamar bare a cikin dangi, Nabil
kuma kamar zai maidata ciki tsabar nuna kulawa da soyayya, cousins ɗinta da ba suyi auren ba sai taɓe
mata baki su keyi.
Bayan dawowarsu gida kam ko kallonta be yi ba ballantana ta sa ran yau Liyana zata ɗan kwana a wurin
ta ta samu taji ɗumin ƴarta.



Ɗakinta ta shiga tayi wanka ta saka kayan bacci mai ɗan kawri saboda yanayin damina dake saukowa a
yan kwanakin nan.



Sai da ta gama shiryawa ta nufi ɗakinsa tsayawa tayi a bakin ƙofar ɗakin tana wasa da yatsunta ɗagowa
yayi sosai ya kalleta na ƴan sakwanni sannan ya kawda kan sa gefe, cikin inda inda ta ce "emm.. Ya ..
Nab...il please zak.......... Kafin ta ƙarasa ya dakatar da ita da faɗin "I'm not in the mood of that
nonsense".



"Ya Nabil that's not what you think, nace dan Allah Liyana zaka bani ta kwanta dani since Last week ko
cikakken fuskarta ban gani b...a" ta ƙarasa faɗar maganar a yanke.



Tsaki ya ja ya cigaba da ordern atamfofin sa daga Ghana, ba tare da ko Kallonta ya sake yi ba.



A kwana a tashi ba wuya Ikimat nada wani cikin, lokcin Liyana shekarunta biyar amma tana da tsawon
ƙafa Ma Shaa Allah.



Laulayin yazo mata da sauƙi amma sam bata iya aikin komai sai dai ta kira ƙannen ta suzo tunda yanzu
ba laifi yana ɗan barinta ta fita amma ba sosai ba......




The Regret wants your Reactions and comments for the person to regret 😂😂

Kaji wani turanci 😂😂

Omo ku biyu pending amarya dan jin yanca zata kaya ✍️🦋

Pending Amarya butterfly writter 🦋

Ɗawisu gidan ado marubuta masu muhimmanci

The Noble Writters Alhaji✍️
What's wrong with this guy readers?

Meke damun guy ɗinnan?



Ku dai ki biyo Pending Amarya dan jin yanca zata kaya✍️✍️

Ta tanada muku amsoshin ku

This is just the beginning.




We haven't started yet

This isn’t the end. It’s the beginning of who they must become.

Because the hardest trials... leave the richest scars.



The Noble Writters 🌕 🦋

🦋

Let's end the war together 💔🤝

Kuyimana share sannan

Reactions ɗinku Is All we need the Most 👑🦚



Try your possible best guys 😍



Let the world feel what we have written ✍️✍️✍️
Don't forget with Pending Amarya as usual 🦋 🫠https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?
mode=r_c




*NIGERIA*🇳🇬

MY FATHER'S LAND

The Noble Writters



Proudly Nigerian 🇳🇬🇳🇬🇳🇬




Dedication is our strong 🦚🦚🦚✊✊



NDA DUBDO THE REGRET FAMILY 💔
😂 🥹🦋

Bana cikin THE REGRET ni kam 🌸🥀🦚

Let's dive into the work of fiction 🤝💫



THE REGRET

(Dana sani)🙆🥀💔🥹

When Love meets temptation 🦚 who survives?

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 🦚



What comes arround goes arround 🥀 💔
Abinda ka shuka shi zaka girba 🦚

Abinda kayi wa ƴar wani za'a yi wa naka 🌚

Duniyar kenan🌕




Is not that easy with you here, buh I know I want you to stay.

See this could be us in a few years 🦋🥀




Chapter two: The past that never let go.

Page 4



:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

Laulayin yazo mata da sauƙi amma sam bata iya aikin komai sai dai ta kira ƙannenta suzo tun da yanzu
ba laifi yana ɗan barinta ta fita amma ba sosai ba.




Tun da yasan daɗin yara kam yanzu yakan kaita scanning ba kamar Liyana ba amma fa Liyana na kusa da
shi Ikimat kuma ita rayuwarta a bayan mota ne.



Tasan wasu daga cikin maƙotanta sosai barimma Ummin Salim maƙociyyarta ta ƙwarai takan shigo gidan
su yi hira tun da ba kullum Nabil ke barinta ta fita ba.



Yau ma kamar kullum tazo tare da kawowa Ikimat Ɗanwake tun da ita gwanar son Ɗanwake ce sosai.

Suna zaune suna hira wanda duk akan mazajen su ne, Ummin Salim ke tambayar Ikimat "Kince za ki
faɗamin sanadiyyar da ya sa Nabil ke muzguna miki kuma har yanzu baki gayamin ba.
Ko har yanzu ba ki yarda da ni bane ba?". Cikin muryarta mai sanyi ta ce "Ko ɗaya wallahi Ummin Salim,
amma bara na baki labari."




Tuna baya



Nabil ya kasance cousin brother agareni ata dalilin mahaifinsa da mahaifina ƴan uwa ne mamansu ɗaya
babansu ɗaya.




Na kanje gidansu Ya Nabil sosai duk da mahaifinsa na da kuɗi sosai bana wasa ba, yawanci acan nakan
cinye hutuna na makaranta tun da bodin school nayi.




Ni kuma Ummi Salim tun da na taso naga Ya Nabil nake jin soyayyarsa araina, wanda har yau duk
muzgunawarsa bai taɓa fita daga raina ba. Lemme just get straight to the point Ummi Salim.



"Yaya Nabil na soyayya da da wata yarinya mai suna Rufaidhat a unguwarmu ta ke muna magana da ita
sosai duk da ni bansan suna soyayya da ya Nabil ba, nikam kawai dan inga ya Nabil ma nakan je gidansu
na cinye kwanakin hutuna, inna zo gidanmu baifi nayi kwana biyu ba na koma school.



Soyayyar Nabil da Rufaidhat kam sai ƙara linkaya ta ke yi saboda zuwa lokacin mutane da dama a dangin
sun sani wanda ni bansan da hakan ba.




Kwatsam ina school lokacin ina js2 ƙanwarsa wadda ta ke ƙawata mai suna Mansura ta sanar dani halin
da ake ciki.
Na sha kuka sosai wanda har na cire rai da aurensa saboda magana na ƙoƙarin zuwa wurin magabata, in
anzo min visiting akan zo da shi amma sai visiting na ƙarshe da za'a min a js2 na tarar ba' a zo da shi ba.



A ta ke na shiga cikin mawuyacin hali sa bo da indai a class ɗinmu kake kowa yasan alaƙata da Ya Nabil
na ƴan uwantaka da ma wanda nake cusa kaina a wurin shi duk da ƙanƙantar shekaruna.




Har akai jarabawa wanda zai kai mu ga js3, mu kai hutu a lokacin shekaruna 13 na dawo gida still gidansu
ya Nabil na sauka, Ummin Salim bazan miki ƙarya ba da ace ni Nabil ke so da nayi dace a duniya, saboda
lokacin da na ke babu aure a tsakaninmu komai ya samu nice duk abinda ya samu ni yake bawa duk
ƙanƙantar abun.




Bayan dawowata da sati ɗaya gidansu a lokacin Ya Nabil na maganar kai kuɗi gidansu Rufaidhat yana
ƙoƙarin sanarwa da Abbana sai shikuma ya sanarwa da Abbinsa.



Toh ranar ta kasance Lahadi kowa na gida muna ɗaki ni da Mansura muna tattaunawa akan yadda zan
cire soyayyarsa pldaga cikin zuciyata, ashe lokacin kuma Ammin ya Nabil ta gama jin duk wani feelings
ɗina a kansa.

Dan kawai tasa ni farinciki ta sayar da farincikin ɗanta dan ta cika min nawa muradin.




Sai a lokacin ta sanar da Abbinsu Ya Nabil yadda taji ina magana harda kuka.

Bai yi ƙasa a gwiwa ba ya kira Nabil ya sanar dashi ya na son ya aureni, babu kunya Nabil ya ce wa
mahaifinsa bazai iya aurena ba saboda ni ƙanwarsa ce sannan shi mai ra'ayin mata ɗaya ne ballantana ya
aure ni ina yiwa Rufaidhat wanke wanke.

A take mahaifinsa ya wanka masa mari wanda a take fushi ya ɗebesa ya zo har inda nake yayi min
barazana akan inna yarda na aure sa.
Ban mai magana ba sannan ban nuna alamar sanin abinda Abbih ke shirin yi ba.



An fi sati ɗaya ana bawa ya Nabil haƙuri mahaifinsa har alƙawarin zai bashi dubu hamsin yayi duk abinda
yake so nan ma ya Nabil yace babu abinda zaiyi da kuɗi, kuɗi bazai iya siyan soyayyar sa da Rufaidhat ba.



Abin ne ya harzuƙa Abbinsa ya ce mai indai har ya auri Rufaidhat ya tsine mai daka cikin ƴaƴansa sannan
in ya auri Rufaidhat ya ajiye duk wani abu da yake da wani abin family ɗin madaki saboda shi Aliyu
Ibrahim ba'a haifi ɗan da zai juya sa ba.




Wannan shine sanadiyyar duk wani muzguna min da yake yi da kuma cin fuskar da yake min".

Ajiyar zuciya Ummi Salim ta yi sannan ta ce "Gaskiya Ikimat kinyi ƙoƙarin da ba ko wacca macace zata yi
ba, kuma har yanzu babu wanda ya sani a gidanku ko dangin ku?"..



"Ummu Salim kenan ai babu wata alama da ya bari, ke da kike kusa dani ga baki ga hanci da ban
gayamiki ba za ki sani?".

Nodding Ummi Salim ta mata alamar a'a.




Sannan ta cigaba da faɗin, "Ko bayan auren Ummu Salim Nabil bai bar ni na cigaba da school ba, sai dai
idan Abbinsa ya tambaye sa yace ai ina zuwa day ya mayar dani.



Ni dai innace ban yafe ba wallahi zai bi Nabil.



One week ka ɗai na san mai daɗin aure wanda har yau kalubalen dake cikin ta nake fuskanta.
Nabil ya taɓa bari na for good ten days ba tare da ya bani abinci ba.



Haƙurin da nayi da Nabil bana fata Liyana ta samu kalar wannan mijin, bana fata wannan kalmar na
abinda kayi wa ɗan wani ya yi ta si ri akan ƴaƴana duk da bansan mai ke cikina da zan haifa ba.



Haka ta gama korowa Ummu Salim duk wani abin da ke damunta irin cin fuskan da Nabil ke nuna ma ta
for good nine years da aurensu.




Ita dai Ummu Salim babu abinda ta keyi in banda hawayen da ke zuba a idanunta wanda nima kaina
pending amarya sai da na zubar da hawayena akan al'amarin Ikimat.




"Innalillahi ƙarfe huɗu yayi banyi girki ba kuma Wallahi yanzu zai dawo tun da da Liyana suka fita".
Ikimat tayi maganar saboda ta kashe zancan duk da ta na son faɗawa wani, amma ba ta son abinda zai
tona asirin wanda duk duniya shi ta ke son ta ƙare rayuwarta da shi sannan kuma ko ba komai shi ɗin ya
kasance uban ƴaƴanta ne.



Da haka ta ƙarasa shiga kitchen ɗin da ke shaƙe da kayan abinci......




Na yau ba yawa manage please 💔
Wacece Rufaidhat?

Wannan ne kaɗai dalilin Nabeel?

Who's the real star the Mom or the daughter?☺️

Who's the one regretting 🌟



Readers mun kusa dawowa labari faa muyi paka paka mu gama mu ɗaura beyond heart break because
nayi missing kowa wallahi 😂✍️



This is just the beginning



We haven't started yet

This isn’t the end. It’s the beginning of who they must become.

Because the hardest trials... leave the richest scars.



The Noble Writters 🌕 🦋

Ɗawisu gidan ado 🦚🦚🦋

Let's end the war together 💔🤝

Kuyimana share sannan

Reactions ɗinku Is All we need the Most 👑🦚



Try your possible best guys 😍



Let the world feel what we have written ✍️✍️✍️



Don't forget with pending amarya as usual 🦋🥀🦚🦋 🫠
> THE REGRET ONLY ON PENDING AMARYA'S BOOK CORNER.



> THE REGRET (Dana sani)



> EXTRA ORDINARY EVERYDAY ONLY ON PENDING AMARYA'S BOOK CORNER 📜 📚
https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?mode=r_c

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.🤌💪



:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::



The Noble Writters 🦚🦚✊

Dedication is our strong 🦚🦚✊



THE REGRET 🙆🥀🌸🇳🇬



when love meets temptation 🦚 who survives?



💔💫



NIGERIA 🇳🇬
For Pending Amarya ✍️✍️



NDA DUBDO🦚

My Maiduguri ppl😂




CHAPTER THREE : RUFAIDHAT 🦋🥀




Page 05




"Innalillahi ƙarfe huɗu yayi banyi girki ba kuma Wallahi yanzu zai dawo tun da da Liyana suka fita".
Ikimat tayi maganar tare da tashi tsaye tana ƙoƙarin shiga kitchen.



"Ikimat ba dai abinci za ki dafa ba?". Ummu Salim ta tambayeta cikin nuna kulawarta a gareta, "Eh
Wallahi Ummu Salim yana hanya kinsan jiya ma haka na shirice ƙarshenta ni na cinye abincin ma".

Dariya Ummu Salim ta yi tare da ce wa "Malama zo ki huta abincin da na dafa da ke nayi ai".

Godiya Ikimat ta mata tare da zama suka cigaba da hira amma ba wanda suka fara ba, har magrib yaya
Nabil bai dawo ba. Sai sannan Ummu Salim ta mata sallama tare da tambayarta yaushe zata cigaba mata
labarin, "Duk lokacin da kike da time ta ce mata". Daga haka tayi mata sallama ita kuma ta wuce sama
tun da har ta jera dambun da Ummu Salim ta ba ta.
Sai ƙarfe 12:00 Nabil ya dawo har Liyana tayi bacci, ƙwanƙwasa mata ƙofa yayi, ya bata Liyana sannan ya
ce ta kawo masa abinci yana jiranta.



Zuciyarta na dukan uku uku ta ƙarasa ɗakinsa da farantin abincin nasa, da ya buɗe ya ga dambu ne ya
mayar ya rufe, sai da ya duba agogon ɗakin sannan ya mayar da dubansa gareta ta re da ce wa "Make
something heavy, and be fast about it". Duk da girman cikinta bai hana ta russunar da kanta agareshi ba
cikin sanyin muryarta ta ce "Your wish is my command sir ". A hankali ta ƙarasa tashi, tayi gaba da ƴar
ƙwallarta a idonta.



Ko da ta shiga kitchen ɗin rasa mai zata dafa masa tayi, kamar tayi kuka, ta fere doya ta dafa mai
pourage yam (faten doya) sai 12:50 ta gama duk bacci ya baibaye mata ido a haka ta kawo mai gabansa
ko da tazo a time ɗin bacci ya ke yi, anan ta ajiye mai abincin sannan ta zauna kusa da shi a ƙasan kujerar
falonsa anan bacci ya ɗauke ta ita ma.



Can cikin bacci ya tashi ƙafarsa ta buge mutum da ke kwance ƙara matsar da ƙafar shi yaƙara yi wanda ya
sauke shi a daidai cikinta, wani Ihu ta saka "zai kashe ni!" A haukace baccin da ke idon sa ya washe
agogon ɗakin ya kalla ya ga 2:56 uku saura, Bai damu da yanca ta ke ba ya ce "Ina Liyana?" Ya tambayeta
a tsawace, kamar za tayi kuka ta dafe cikinta ta ce "Yaya tana ɗakina, yaya cikina zan mutu".



Ko kallonta be yi ba ya shiga ɗakinta sai da ya tabbatar Liyana na nan, sannan ya shiga closet ɗinsa ya
ɗauki belt. Dawowa yayi ya shauɗa ma ta a cinye, a zabure ta tashi ta na hawaye, cikin shashsheƙa ta ce
"Yayanmu Please allow me to rest ba fa akanka aka fara first love ba, Rufaidhat ta riga tayi aure atleast
kai ma kayi moved on mana".




Kallonta yayi sosai sannan ya ce" tun da ke kika aurar da ita, kinci darajar dare ne yanzu amma Allah ya
kaimu da safe za ki san ko ni waye". Daga haka yayi bagging ƙofar ɗakinsa. Kullum da tunanin Rufaidhat
ya ke kwana ya ke tashi, yana sonta amma sai Allah be yi zai mallaketa ba daga haka dai bacci ya kwashe
sa ba tare da ya sani ba.
Washegarin ranar tun da ta tashi ya ke sata aiki sai da ta goge stairs, ta wanke bango, ta goge kujeru, ta
wanke motocinsa kala uku, sai da ta tsaya a bakin gate ya fita da mota ya dawo cikin gidan fiye da sau 10
kuma ba nisa ya ke ba, tana zama daga buɗe mai gate ya ke ƙara fita.



Duk abincin da ta dafa sai ya ce ta sake wani shi heavy food ya ke so, ta dafa abinci yafi kala goma.

A ranar dai Nabil bai je kasuwar kwari ba.



Tun asuba da ta ta shi sai ƙarfe 12 na dare ya barta ta koma ɗaki ta kwanta ga cikinta da ya ɗan fara
girma ba laifi




Tun Ummu Salim na turo almajirinta tana mai yaren kurame har ta gaji.

Ita ma Ummu Salim ɗin ba ta ƙara aiko wa ba.



After one week da lamarin Ummu Salim ta zo ta sanar da ita komawarsu Abuja saboda transfer ɗin
wajen aiki da aka yiwa mijinta.




Bayan ta gayama Ikimat kaɗan ya rage bata yi kuka ba because a ranar zasu tafi, ha ka Ikimat ta yini a
gidan duka bata da wani kuzari, ga shi Abbin Liyana sun fita Shopping na school ɗin Liyana. Sun je Grand
Square siyan chocolates, a sukwane tayi aikin ta da zatayi ta gama, saboda ba ta jin daɗin jikin ta sosai.



Ɓangaren Nabil da Liyana kuwa ko da su ka bar gidan ba su wuce ko ina ba sai Grand Square, suna ciki
shi da LIYANA suna siyayya ta riƙe mai hannu sai dariya ta ke, idanunsa su ka sauka akan wata
matashiyyar mata wacca bazata fi shekaru 25 ba da jaririya a hannunta cikin kaya na alfarma.



Cikin dasashhiyar muryarsa da ta dishe a lokaci ɗaya ba tare da yayi noticing ba ya furta " RUFAIDHAT?
RUFYNA?? Is that you?".
Wadda aka kira da Rufaidhat ce ta juyo da fuskarta cikin shigarta na super holland kyakkyawace amma
ba ta kai Ikimat kyau ba.




Cikin Muryarta mai kyau ta ce "Nabil dama ka na nan". Ta faɗa tare da murmushi.



Murmushi shi ma ya mata ya ƙaraso kusa da ita ya ce " ƴar yaya Nafisat ɗin ce haka?".



"Ƴar yaya Nafisat kuma?, ai wannan ƴata ce ". Rufaidhat ta faɗa ta na kallon Nabil ta re da mai murmushi
mai sanyi.




"Ban gane ƴar ki ba? Haka mukai da ke?? Daman yaudarata kike da niyyar yi?? For almost ten years da
muke soyayya da ke did I deserve this from you?? Na cancanci haka daga gareki Rufaidhat???",
kuma...............




Ba ta bar shi ya ƙarasa ba ta ce "Ban gane yaudara ba Nabil ya zaka na min faɗa kamar wani babana, kai
ba'a kira ka mayaudari ba sai kai ne za ka kira wani da kalmar yaudara?? Kai da kayi aure kafin nayi faa?
Ka haifi ƴa kafin ni na haifa?, babu wanda baya shaidar kalar soyayyar da ka ke nunawa Ikimat.
Bayan auran ka ma ba ka barni ba sai da na ɓata kusan shekaru shida ina jiran ka, kullum ba kada zance
sai you have to zeal something wanda har yau bana tunanin kayi zealing ɗinsa, maƙaryaci, mayaudari. Da
tuni na tsaya jiranka kayi draining time ɗina da energy na wa gari zai waya??.......




> Readers mai makomarsu ? Mai rufy ke nufi da abinda ta gayawa Nabil 🫩🤔



> Tsakanin Uwa da ƴa wace tauraruwa?



> Pending Amarya na ɗauke da amsoshin tambayar da zaku zo mata dasu🤍




This is just the beginning.




We haven't started yet

This isn’t the end. It’s the beginning of who they must become.

Because the hardest trials... leave the richest scars.



The Noble Writters 🌕 🦋

🦋

Let's end the war together 💔🤝

Kuyimana share sannan
Reactions ɗinku Is All I need the Most 👑🦚



Try your possible best guys 😍



Let the world feel what we have written ✍️✍️✍️



Don't forget with Pending Amarya as usual 🦋 🫠




> Pending Amarya's book corner.



> The Regret only on Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋 🥀

https://chat.whatsapp.com/DAqtxT35oDPJgXIGyih8qT?mode=r_c




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.🤌💪
*NIGERIA*🇳🇬

MY FATHER'S LAND



Proudly Nigerian 🇳🇬🇳🇬🇳🇬

Hausa Writter from Igala land 🌸 🥀




The Noble Writters 🦚 🦚 🌟



Dedication is our strong 🦚🦚🦚✊✊



NDA DUBDO THE REGRET FAMILY 💔
😂 🥹🦋

Bana cikin THE REGRET ni kam 🌸🥀🦚

Let's dive into the work of fiction 🤝💫



THE REGRET

(Dana sani)🙆🥀💔🥹

When Love meets temptation 🦚 who survives?

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 🦚



What comes arround goes arround 🥀 💔

Abinda ka shuka shi zaka girba 🦚

Abinda kayi wa ƴar wani za'a yi wa naka 🌚

Duniyar kenan🌕
Chapter four: Her Womb 🥹💔




Page 6




:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::



Bayan auran ka ma ba ka barni ba sai da na ɓata kusan shekaru shida ina jiran ka, kullum ba kada zance
sai you have to zeal something wanda har yau bana tunanin kayi zealing ɗinsa, maƙaryaci, mayaudari. Da
tuni na tsaya jiranka kayi draining time ɗina da energy na wa gari zai waya??.



Kuma Bara kaji na gaya ma ka ina zaune da miji na lafiya fiye da yadda ka ke tunani, na barka lafiya."



Shopping ɗin da ba'a yi ba kenan ya dawo gida jikin sa a sukwane, ko da ya shigo ya ci sa'a ta na falo ba
ta shiga ɗakinta ba.



Sallama yayi ya shigo falon abinda bata taɓa jin yayi ba.
Liyana ya ajiye akan 2 sitter sannan ya ƙarasa three sitter ya zauna, jikinta na rawa ta ce "Yaya sannu da
zuwa" da wani irin sauri ta ƙarasa kitchen ta ɗauko bottle water duk da tsohon cikin ta haka ta tsugunna
agabansa wani kalar runtse idanunsa yayi ya miƙa hannunsa zai ƙarɓi ruwan already daman ta riga ta
buɗe bottle ɗin, sai ruwan ya fallatsa masa ajiki.




"Yaya dan Allah kayi haƙuri wallahi i didn't do it intentionally." ta faɗa ta re da ɗaukan tissue jikinta na
kakkarwa alamar tsoronsa ta ke ji.




"IKI" ya faɗa da kakkausar murya, runtse idanunta ta yi, saboda yanzu an doshi 10years da taji sunan nan
a bakinsa, is she still dreaming?", ta tambayi kanta, because har yanzu ba ta yarda da abinda take ji
kuma take gani in her present ba, not even her past life wan da daman kullum da imagination ɗin past
life ɗinta take bacci take tashi sannan kuma take rayuwa.




"Ikimat am sorr........ Ka sa ƙarasawa yayi kawai ya ta shi daga wurin zuciyarsa na masa ɗaci.




Ha ka rayuwarta ta cigaba da tafiya a gidan Nabil har ta haifi ƴar cikinta wanda shima Cs aka mata, ta sha
wahala sosai because mahaifarta ya sami matsala an juyar mata da shi , ta yi kuka ta godewa Allah,
kamar maye sai da ya kira Rufaidhat ya sanar da ita.(Soo Sad🥹💔)
Seven Years later 🌟💫



A kwana a tashi girman mutum ba wuya Liyana ta na Jss2 in da ɗayar yarinyar mai suna Maimuna amma
ana ce mata Ilham ta ke primary 2 rayuwar su gwanin burgewa an ƙara renewing gidan nasu komai ya
zama na zamani.

Zuwa yanzu kam driver ke kai Liyana da Ilham school wanda duk girmanta sai tayi kukan Abbih ne zai
kaita.

Akwai shaƙuwa sosai tsakaninsa da Liya wanda ko a gaban waye ba ya ɓoyewa.



A school sai labari ake da LIYANA wacca kowa a class ɗinsu ke son mata magana da kuma son aga ta na
hulda da kai saboda kuɗin Abbinta, yau friday ko da aka tashi ba ta wani ɓata lokaci ba ta nufi primary
section ta ɗauko Ilham ta re da riƙe mata hannu suka fito daga school compound ɗin.



Hannunta sar ƙafe da na Ilham har wani motan da ta ke sa ran na Abbine ya iso wurin, ƙirar Mercedes
Benz s class 2018 sai sheƙi ya ke a hasken rana, fitowa yayi daga motar yana murmushin sa mai kyau ta
re da karɓan jakar hannunta...




Abbih" Sannu da zuwa" ta faɗa da siririyar muryarta, mai daɗin sauraro.

Nabil kam girma ya zo mai a tattare da shi amma baifi under 40s ɗin shi ya ke ba, wannan wankan da
ƙwalisar na nan, fuskarsa da ya ke murtukewa kaɗai ne ba ya nan shi ma ban san ko dan babu Ikimat ba.

Sai dai fa su muke kira da saurayi magidanci, he's soo calm ƙarasa saukowa yayi daga motar da
murmushi a fuskarsa ya ce "Ƴammatana! Ƴammatana"Liyana da sai kumbure kumbure take taƙi juyowa,
Tana tsaye a wuri ɗaya tayi folding hannunta, Ilham da zafin rana ya dameta, cikin muryarta na yara ta
ce "Abbih Dan Allah ka buɗe min ƙofa na shiga mota ni nagaji da tsayawa."
Nabil ne ya juyo ya

Please Login or Register in order to submit comment