Reading AURE KO BOKO 3 BY TAKORI Chapter 7 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki na kwanikar data sameta. Amma kamar Hashim itama Zarah kwantar mata da hankali tayi, ta ce “ki godewa Allah Besty, nawa ne suke nema da kudin su basu samu ba har suke zuwa asibiti ayi musu artificial? Ba sai mun je da nisa ba akan haihuwa ko Hanan ta ishe ki ishara”.
Tun daga ranar Halima tayi wani kyakkyawan kuduri a zuciyarta wanda bata gayawa kowa ba.
Bayan sun dawo gida ta daidaici lokacin da Hashim yake cikin kyakkyawan yanayi, sai ta zo ta zauna a jikin sa, ta kwantar da kai bisa kafadarsa. Cikin wata lallausar murya take magana;
“Cheriè, ka yi min alfarma in hada kayan Zarah in kaiwa Hanan ita gobe -goben nan, amma ba hutu irin wanda take zuwa ba, na barwa Hanan ita halak-malak, amincewar ka cikin dimbin alfarmomin ka da basa karewa a gare ni nake nema”.
A hankali Hashim ya dago fuskarta cikin tafukan sa, sai ya ga hawaye fal a idon ta, tana tsananin tausayawa ‘yar uwarta matsalar rashin haihuwa. Yace “C’mmom Halima shine sai kin yi kuka? Kin fi karfin kowacce alfarma a gareni in har inada ikonta. Allah ya taya su riko, Zarah ta zama ‘yar su ko dama rabin rayuwar ta ai yafi yawa a hannun nasu”. Halima don farin ciki sai ta makale shi tana kuka sosai.
Hanan sai ganin Her Excellency Halima tayi a washegari a gidanta, da kayan Zarah rankatakaf ko pant daya bata bari ba. “Ga ‘yar ki mun kawo miki duniya da lahira, Safeeyah bai iya bada ita amma ga Zarah mun baki”. Hanan ta kifa kai a cinyar Halima tana kuka, ta rungume Zarah. Shima Daddy da yaji abinda Halimah da Hashim suka yiwa Hanan sai da ya ninninka albarkar da yake sanya musu a kullum.
(Allah ka hada kanmu da ‘yan uwan mu, ka fidda hassada da ganin kyashi tsakanin mu da su, ka sa zumunci ya zame mana silar shiga Aljannah- Takori).














MURFI
Engnr. Hashim ya gama tenure din sa with much success, yayi mulki irin wanda ba’a taba yi na farar hula a Kano ba, ya bar tarihi wanda ya tsaya a zuciyar Kanawa. Don haka ne yana gamawa basu barshi ya sauka ba suka sake tsayar da shi karkashin jam’iyyar NRC.

Ita kanta NRC ta kara daukaka a dalilin farin jinin Hashim. Don haka wannan karon basu sha wahalar kamfen ba Hashim ya sake lashe kujerar gwamnati a Kano.

Bayan karewar tenure ta biyu, shekaru takwas kenan akan karagar gwamnati, sai shugaban kasa na lokacin wanda dan jam’iyyar su ne ya bashi Minister of Youth and Sport. Wanda shine mukamin da yake kai a halin yanzu. Don haka su Halima sun yi kaura da jimawa sun koma Abuja a unguwar Ministers’ Hill Colorado Close.

Hanan sun samu sauyin wurin aikisun koma Lagos, can ta hade da Salima suke zumuncinsu diyar Hajja Falmata. A lokacin Zarah ta gama primary a hannun ta.

Zumuncin Halima da Zarah Datti, wani irin kawance ne mai wuyar samu a wannan zamanin, sun tashi daga kawaye sun koma ‘yan uwa, kuma sirrin juna, bata banbanta Zarah da Hanan akan komai, musamman bayan rasuwar Alhaji Datti, Hashim shi ya zamewa su Zarah babban Yaya ya rungume komai nasu ita da mahaifiyar ta. Shi yake musu komai a bayan ran alhajin duk da cewa ya bar musu gado mai yawa.

Haka rayuwa ta cigaba da mika musu incredibly. Da kyakkyawan zumunci abun koyi.
****





BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYU

(WEST OF ENGLAND SCHOOL FOR THE BLIND, EXETER).

“Safeeyyah Hashim! Safeeyyah Hashim! Safeeyyah Hashim!”.

Kawai kawai kake ji ya na tashi a loudspeaker, ranar yaye daliban kwalejin makafi ta garin Exeter, England.
Komai itace ta farko, best in Braille (wato rubutun makafi), best in music, best in sport, best in english literature sannan ta karbi kyautar wadda tafi kowa da’a da iya guiter (garaya).
Safeeyah ‘yar baiwa ce ba tun yau ba, Allah da ya halicce ta (visually impaired) bai barta haka ba. Sai ya yi mata karamomi masu yawa wadanda mai lafiyar idanu ma bai da su. Kwakwalwarta na matukar ja, sannan tana matukar so da tausayin iyayenta. Ta shiga ran mahaifin ta fiye da duk ‘ya’ya takwas da Allah ya bashi. Tunanin sa a kullum yadda zata yi coping a gidan aure ne, ko wane miji ne zai aure ta ya rike masa ita da daraja ba wulakanci babu gori?
A kullum in yayi wannan tunanin hankalin sa yana tashi, ya gwammace ya ajiye ‘yar sa yayi ta ilmantar da ita yana kula da rayuwar ta. To amma shi al’amarin
Ubangiji ba haka yake ba. Ya riga ya rubutawa kowa rayuwa tun zuwan sa duniya. Ita Safeeyah a karan kanta bazata iya rabuwa da iyayenta zuwa gidan aure ba.
Tana kammala sakandire West of England School for the Blind Exeter ta yi sponsoring karatun ta na jami’a zuwa ‘Royal Blind College’. Bayan kammalawar ta ta dawo gida tana da shekaru ashirin da daya.
Sai ga Muhammad Mujtaba, Da na fari ga Zarah Datti, wanda ke karatu a Aviation School, Zaria. Ya tuburewa mahaifiyar sa Safeeyah yake son aure. Zai iya da dukkan lalurorin ta a yadda Ubangiji yake son ganin ta. Kwatakwata shekaru uku ya baiwa Safeeyah.
Zarah ta rasa ta inda zata bullowa Muhammad domin da gaske yake yaki komawa makaranta yace sai ta je ta fadawa Aunty Halimah an tsayar da magana zai yarda ya koma. A karshe Zarah da maigidanta Barr. Zahraddeen suka samu Minister Hashim da kokon barar su, tare da alwashi iri-iri na zasu rike Safeeyah a gidan auren ta tamkar tana gaban sa.
Hakika Hashim ya shiga tsaka mai wuya a wannan dan tsakanin, bashi da niyyar aurar da Safeeyah ga kowa, don guje mata halin maza sabida lalurar ta. Amma Zarah tafi karfin komai a wurin su in har suna da iko. Itace tsanin duk wani mataki da suka taka a yau. Don haka bai iya ya juyawa wannnan bukata baya ba, amma yace har sai Muhammad ya gama karatun sa.
Shekaru biyu bayannan akayi auren Safeeyah da Mujtaba. Kuma a yadda Zarah ta fada din, a gidan su Safeeyah da mijin ta ke zaune don dai ta kula da ita, kuma Mujtaba ya nuna shi dan halal ne bai hada soyayyar Safeeyah da komai ba. A nakashen da take.
Ba jimawa Safeeya ta samu gurbin karo karatun digiri na biyu a jami’ar Exeter.
Ta zamo abin kwatance a kasar mu Nigeria, duk wasu jami’o’I da suke da Special Education a Nigeria nema suke Safeeyah ta zo ta koyar tare da su.
Kwalayen ta abin kwatance abin alfaharin iyayen ta.
Daga shekaru Talatin da Biyu, Safeeyah tana kan ‘Professorial Chair’.
“Nakasa ba kasawa bace. Ba nakasashshe sai kasashshe”. Inji gidan radiyon BBC a lokacin da suka sako programme din su akan rayuwar Prof. Safeeyah Hashim Ismael Yakasai.

Masha Allahu laquwwata illa billah.

Nan na kawo karshen littafin AURE KO BOKO?
Kuskuren da ke ciki ku taya ni rokon Allah ya yafe mini, alkhairin da amfanin da ke ciki, Allah ya raba mana ladansa ni da ku bakidaya.

Sumayyah Abdulkadir ke cewa;
Mu hadu a sabon littafi na MASARAUTAR MU!......
Wanda tare suka fito da Aure ko Boko na 3. Yana nan shima a kasuwa.
Nagode muku bisa dimbin kaunar ku gareni. Allah ya bar mu tare cikin Alherinsa…. Har zuwa ranar da muka daina numfashi.

MASARAUTAR MU!!!
BAN TABA RUBUTU SOLELY AKAN GIDAN SARAUTA BA, SAI A LITTAFIN MASARAUTAR MU! GARZAYA KI NEMI NAKI DON YA BANBANTA DA GABADAYAN LITTATAFAN TAKORI DA KIKA KARANTA. DON JIN LABARIN HARGITSIN RAYUWAR ‘SA’ADE’ A GIDAN SARAUTAR ASKIRA.

SUMAYYAH ABDULKADIR
07030137870
WHTSP ONLY
(MATA KAWAI)

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment