Reading AURE KO BOKO 3 BY TAKORI Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ji lafiyar yaran ya dade da saving no.dinta, kafin ta yi fushi ma sam ta daina kiran. A cewar ta in 'ya'ya ne itama Allah ya bata, Zubair Numan, ya jika nasa ya shanye.

Sai yanzu da Hanan ta bude masa wuta kan ya hadata da su ne kuma da yake shiri yake nema da 'ya 'yan nasa helter-skelter sai bai yi musu ba, ya bata lambar Hajja Falmata tare da bata hakurin abinda yayi musu a karo na sau ba adadi. Ita kam Hanan in don wannnan ban hakurin ne na Daddy ta gaji da jin sa, ta haddace duk wata kalma dake cikin sa, hatta da yadda zata yi ta isa gidan ta inta je Maiduguri Daddy ya gaya mata.
Hanan in don ita ta dade da yafewa Daddyn tana fata Halima ma ta yi hakuri ta yafe masa. Amma ta lura Halima har gobe ko zancen Daddy bata so ayi mata.
A hankali ta san watarana zata huce, domin kamar ita tafi cutuwa da matakin da Daddy ya dauka akan su bayan auren su.

Ya kaita wata rayuwa wadda bata taba sanin akwai a duniya ba, idan ya kwace kudin da yake mallakin sa kwalayen karatu fa ai gumin su ne! Haka kulawar da Allah ya dora a wuyan sa ya watsar bisa ganganci da son zuciya. Halima ta cancanci tayi fushi da mahaifin su amma in tayi la'akari da hakkin haihuwa ya kamata tayi hakuri ta bashi dama ya gyara kurakuransa kamar yadda yake son yi a halin yanzu.
Motocin suka yi parking a kofar gidan da aka kwatanta musu wanda ke unguwar (Hausari). Hanan da Halima zasu iya rantsewa har wani irin contentment suka ji ya tsirga a zuciyar su lokacin da suka shiga gidan da aka ce anan ne kanwar mahaifiyar su take aure. Lokacin da suka shiga mayalwacin falon ta wanda ya ji komai saisa-saisa alamun akwai rufin asiri amma babu tarin arziki. Suka yi arba da ita tana saukowa daga matattakalar benen dake cikin falon alamun daga dakunan barcin dake sama ta sauko.
Waya ta ke yi amma da Halima ta daga ido ta dubeta suka hada ido, bata san sanda ta saki wayar hannun ta fadi kasa ba, sabida gani tayi kamar Yayarta marigayiya Safeeyyah ce tayi wankan kuruciya ta tsaya a agabanta tana kallon ta.
Hanan ce ta karasa ta russuna tana tsince mata wayar data yi filla-filla. Ta dago ta mika mata, bata karba ba sai ta tsaya kamar mutum-mutumi tana kare musu kallo a tsanake. Halima ma ta taso ta jeru a gefen 'yar uwar ta Hanan, suka tsaya a gaban Falmata su biyu.
Hajja Falmata zata yi shekaru hamsin da doriya amma tsabar kula da lafiyar jiki bai fi ka bata 40 a idon ka ba. A hankali tasa fuskar Halima cikin tafukanta, sannan ta ambaci sunayen su a hankali ba tareda sun gabatar da kan su ba.

"Hanan & Halimah!"

Ta fada cikin sassanyar murya, basu yi wata wata ba su kuma suka tafi zuwa jikin ta suka rungume ta.
Ita kuka su kuka. Sun yi shi har sun ji babu dadi. Ba mai lallashin wani, kasancewar a falon zaure suka baro su Hashim. A karshe Hajja Falmata ta tambayesu yadda aka yi Prof. Ya yarda yanzu ya barsu suka zo garetaàà, tace "ni dama na san in dai Safeeya ce ta haife ku, to watarana sai kun kawo kan ku gare ni, shiyasa na hakura na rabu dashi na tura masa aniyar sa".
"Amma ko a boye ba sai ki neme mu ba Hajja? Tunda kinsan zuwa yanzu dai duk inda muke mun yi hankali da hangen nesan sanin cewa muna da dangin da muke bukata a jikin mu? Bazamu rayu da Daddy shikadai ba kasancewar sa uba a garemu kuma namiji tilo a cikin mu. Adda in bamu yafe muku ba kuma kuna da hakkin mu…....". Halima ta fada cikin kuka sosai.
Hajja Falmata ta janyo su suka zauna a tare bisa doguwar kujera, tana shafa bayan Halima da hannun ta tace "ko me zan gaya miki bazaki gane ba, har gobe baki gama sanin babanki ba, ba kankanin abu ke canza masa ra'ayi ba. Marigayiya ta sha wahala akan sa ba kadan ba. Ka rabu da shi in ya ce ka rabu da shi, shi ya fiye maka alkhairi, in ba haka ba zai wulakanta ka".
"Duk da haka for our sake hujjar ku ta kyale mu kwata-kwata tayi rauni Hajjah" Halima ta kalubalanta. Hajja Falmata ta kara jan ta cikin jikin ta sosai, kamshin turaren bare-barinta ya ratsa Halima, tace.
"Na karbi kuskure na Halima and Hanan, I apologize ku yi hakuri ku yafe mini, bacin rai ne, akwai sanda yayimin korar kare tun daga bakin gate don nace zan dauke Hanan, wallahi kullum da ku nake kwana da ku nake tashi a rai na. Ku yi hakuri ku yafe mini, amma ina matukar son sanin yadda aka yi kuka san ni, ya kuma bar ku yanzun kuka zo".
"Mu fara yin sallah tukunnna, dogon labari ne, and please Hajja ki samawa Baban Safeeyah abinda zai ci, bana barin shi da yunwa". Halima ta fada cikin kulawa, a fuskarta kauna da soyayyah ne a kwance zallah. Hajja ta kai mata rankwashi a tsakar ka tace "uwar ki nake, ba abokiyar wasan ki ba" Hanan tace "in dai Halima da Hashim ne zaki ga fin haka. Zasu iya rungumar juna su sumbaci juna a gaban ki" Halima ta kai mata duka ta goce, Hajja na dariya ta ce "that's wonderful. Love is overall".
Hajja Falmata tasa aka budewa Hashim da Salim falon mijin ta sannan ta shiga hidimar abincin su. Sai da sukayi sallolin dake kansu sannan ta shiga suka gaisa, tayi identifying kanta matsayin kanwar mahaifiyar su Hanan ta gaya masu tarihin komai tun bayan rasuwar Safeeyah da dalilin ta na barin yaran.
"Yanzu da Allah ya nufa suka girma ai gashi sun biyo ni da kafafun su".
Inji Hajja Falmata, ta fada musu ita kadai ta rage a dangin mahaifiyar su sai 'ya'yan ta bakwai dake gidan aure maza da mata. Sai wani Yayan su a kasar Togo. Gobe duk zasu zo su ga 'yan uwan su. Na Togo kuwa zata saka lokaci ta rakasu wajen sa shima ya gan su.
Ta yaba kwarai da kamalar mazajen 'ya'yan nata musamman Hashim, wanda da ganinsa ka ga responsible gentleman. Shi kuwa Salim ka ga dan gata irin Hanan. Ta fita ta barsu tareda matan nasu suka ci abinci sannan su Hashim sukayi musu sallama kan zasu je su nemi masauki. Ya sumbaci Safeeyah yace "Sophy goodnite" ta shafa fuskarsa da hannayen ta tace "goodnite Daddy, gobe in zaka zo ka tahomin da kuli-kuli" yace "kuli-kuli kuma Safeeyah?" Tace "eh, mai sukari ba! Irin wanda Anty Sa'a ke kawomin" yace "an gama my princess".
Ya daga ido yana kallon Halimah, wadda ke yiwa Safeeyah dariya, fararen hakoranta gabadaya a waje, kullum da abinda zata kirkiro mai wuyar samu tace uban ya kawo mata, shi kuma ko zai yi yaya sai ya nemo shi. Yanzun ma yace "kice ma Hajjah don Allah a nemo mana kuli-kuli mai sukari, ko nawa ne zan biya" zai rike ta, tayi saurin ja da baya, juyawar nan da zai yi sai ya ga Salim da Hanan na kallon su, sai ya shafa kai ya cira kafa yana fadin "goodnight sweetheart". Salim dai burgeshi suke, basa taba gundura da juna. Kullum kamar sabon aure, to aure ne da aka gina bisa doron soyayyah ta saboda Allah wadda tayi karanci a wannan zamanin. 80% na auren zamanin nan an gina shi ne for worldly materials. Shiyasa baya karko kuma baya zuwa ko'ina ranar da babu worldly materials din, ko ayi ta zaman hakuri da juna. Hanan ta ce "ai kawai ki hakura da hira da Hajja daren yau ku tafi kya dawo da safe".
Ta fadi haka ne ganin yadda idanun Halima da Hashim ke ragaita da ya juya zai tafi. Hashim din ya sake juyowa, sai idon sa cikin na Halimah, sai kuma Halima ta ji kunya tayi saurin shigewa cikin gida. Murmushi yayi sannan suka fita shi da Salim suka tadda escourts din su suka tafi cikin gari suka kama masaukin da zasu kwana zuwa gobe.

Kusan kwanan zaune aka yi tsakanin 'ya'yan da Antin nasu. Duk labarin rayuwar su sai da suka warware mata. Ita kanta Hanan sai yanzu ta ji wani abun game da rayuwar da Halima ta yi a birnin Kano, sai da suka yi hawaye dukkan su don bata san Halima ta je Abuja neman gafarar Daddy ya yi mata korar kare da mugun baki ba sai yau da Halima ta fada da bakin ta. Ta tabbatar Halima ta fi ta shan wahalar rayuwa, don dai ta kasance mai zurfin ciki da wadatar zuciya ne.
Hajja Falmata ta kara janyo Safeeyah jikin ta jin cewa makauniya ce. Bata raba daya biyun mugun bakin da Prof. Yayi wa Halima ne ya sauka akan 'yar ta. Ta ce "Yaa Ilahi! Shin? Ina Zubairu zai je da hakkin Halimah!"
Ta tambaye su su duka biyun.

"Shin kun taba cin kayan gyara na mata?" Su duka suka hada baki suka ce "menene kuma kayan gyara na mata?" Hajjah Falmata ta aje kunya tayi musu bayani dalla-dalla, cewa suka yi su basu taba sanin wannan abun da ta ke fada ba sai yanzu. Hajja Falmata dai cannot control her tears. Ta yi kuka sosai a gaban su ta zargi kanta da butulci ga 'yar uwar ta da cin amanar zumunci. Halin Uban su bai zama hujja ba na wannan kyaliyar data yi musu a gabadayan rayuwar su. Rokon Halima da Hanan kawai take kan su yafe mata in ba haka ba Allah ma ba zai bar ta kan wasarere da zumuncin nan ba. Tace.
"Na san mahaifin ku yana son ku, kuma yana da halin da zai kula da ku, kuma baku bukatar komai daga gare ni, amma kulawar 'ya'ya mata sai UWA mace. Na yi kuskure dana biyewa bacin zuciya da halin baban ku. Don Allah ku yafe mini".
Halima ta ce "ni kam komai ya wuce a waje na Hajjah, idan Allah ya rubuta abu zai faru babu dan adan din da ya isa ya kankareshi" Hanan ta zumburo baki tace "ni sai kin bani kayan mata din zan hakura, ko na kara samun soyayyar Salim tunda maman shi so take a yi min kishiya".
Hajjah ta ce in don wannan ne kin zo godan sa Hanan, sana'ata kenan gyaran mata, daga gari-gari zuwa ake wajena, balle ku 'ya'ya na na kaina, ai sai na ga abinda ya turewa buzu nadi".
Washegari 'ya'yan Hajja duk suka zo gidan, sabida wayar data yi musu kan zuwan su Halima, Habiba itace babba, yaranta biyar, anan Maiduguri take aure, sai Salima mai bin ta tana da yara uku, ita kuma tana aure a Lagos. Sauran duk maza ne su biyar, daya ma'aikacin banki ne yana da aure wato Saifullahi, sauran ukun Yunus, Suraj da Alkali suna jami'ar Maiduguri, autan Hajja Usman da suke kira (Danzaki) yana ajin karshe a sakandire.
Yau Hanan da Halimah sun wuni sur cikin su Aunty Habiba da zumunci rin na dangin uwa wanda biro yayi kadan ya bayyana shi. Habiba tayi musu dilke da halawah ta yarfa musu kananan kitson bare-bari yiri-yiri yakai kusan guda dari uku, tun zuwan ta gidan bata huta ba tana ta gyara su, ita kuwa Hajja cewa tayi gyaran da bata yi musu na aure ba shi zata yi musu yanzu don haka dole su kara kwanaki a Maid koda su Hashim zasu yi gaba ne su bar su. Ita da kanta zata maida kowacce har gidan mijin ta.
Hashim ya so yayi gardama Salim ya taushe shi, ya nuna masa muhimmancin ya bar su din, wani experience da basu taba samu a rayuwar su ba.
Hashim da Salim suka tafi a ranar, cike da kewar matan nasu, suka bar Halima da Hanan wajen Hajja Falmata da 'ya'yan ta.
Ai kuwa Hajjah bata tsaya sanya ba, gyara take musu na musamman kamar yau zata kai su dakin aure. Hatta Safeeyah ta sha kitso da lalle wajen aunty Habiba. Ta kuma yi musu guzurin wanda zasu tafi dasu.
Sai da maigidanta Alhaji Buba ya dawo ta nemi iznin sa, na dukkan su itada yaranta da surukarta Bintu zasu raka su Halima gidajensu. Salim shi ya yankar musu tiket na zuwa Porthearcourt dukkansu, shi kuma Hashim ya yanki na Kano.
Sati guda kenan rabon Halimah da Hashim, wani lokaci ne da basu taba dauka ba tare da juna ba tun auren su. Don haka yau da suka dawo in ka ga rawar jikin da Hashim ke yi sai ka tausaya masa, yana da meeting a Abuja amma fasa zuwa yayi, ya kuma kasa controlling kansa gaban surukar sa Hajjah Falmata da yaran ta, bai san sanda ya ce,
"Ke ce kuwa Leemah? Kin zama very young, your skin is glowing.... Hajjah me kika shafa ma Maman Safeeyah haka?"
Dariya duk suke masa domin kuwa ya kama Halima kam-kam ya rike a gabansu, yana kokarin sumbatarta tana gocewa. Ba shiri duk suka zaizaye suka bar musu falon. Ai kuwa da ya sunkuci Halima bai direta ko'ina ba sai a gadon barcin su.
A wannan daren, a wanna ranar, a wannan mintocin, al'amuran da suka gudana tsakanin ma'auratan masu tsauri da nauyi ne a zuciya da ruhin su. Daga Hashim har Halimah sai da sukayi hawaye domin kaunar junan su; tamkar Hajjah ta kara ma auratayyar su wani maganadisu ne mai jan zuciya da ruhi. Hashim bai iya daurewa ba, sai da ya jirkito da Halima saman sa, cikin wani irin shauki ya ce.
"Leemah, you became a virgin, menene wannan sirrin? Don Allah ki gaya mani? I’m perflexed (na rikice)".
Hajja ta ja kunnen ta ba'a fadima miji irin wannan sirrin, amma Halima da Hashim sai Allah! Ji tayi bazata iya boyewa Hashim ba, ita fa ko tari ta yi, ya kuma tambayi dalilin jin sa ba yadda ya saba jin sa ba, to zata fayyace masa bazata boye ba, balle wannan babban al'amarin da itama ya gigitata, bata san haka auren ya ke ba sai yau. Duk da tana jin kunya amma bata jin akwai wani sirri da ya saura tsakanin ta da Hashim; they are not ordinarily mata da miji; su abokan juna ne kuma sirrin juna.
"Actually..... Hajja ta bani wani abu na ci…" ta fada tare da saurin rufe idon ta, ta kuma kifa kanta a tsakanin kafadunsa. Kunya kamar ta yi yaya! Dariya yayi, ya sumbaci idanun dake rufe. A hankali yace "Hajjah deserves an accolade, Allah ya bamu sa'ar zabe insha Allah sai ta maimaita Hajjin ta a dalilin wannan babban gata data yi mani".
Kwanan su Hajjah Falmata uku gidan Halimah suka wuce Porthearcourt ta airport din Malam Aminu. Suka raka Hanan, can ma suka kwana uku, sannan suka koma Maiduguri, amma kullum suna makale da waya, kamar masu tsoron.....kada kaddara ta sake giftawa ta nesanta su da juna.
*****






















ABUJA
Prof. Zubair Numan, na zaune a makeken falon sa abin duniya ya ishe shi. Shi daya tal! Kamar tsohon maye a tafkeken gidan sa amma kamar marayan da bashi da wani gata. Kwanan nan kuma tarin fuka ya sanya shi gaba (tuberculosis). Daga shi sai ma'aikatan sa da hadiman sa wadanda duk maza ne kabilu. Ya soma tunanin to ko shima auren zai yi ne irin na Hanan da Halima ya samu mai debe masa kewa da miko-miko?
To amma idan yayi aure yanzu at the of 70 yaya sunan auren nasa? In dai ba wadda zata yi masa takaba ta cinye dukiyar da ya wanzar da rayuwar sa yana tarawa Hanan da Halimah zai aura ba?
Yana nan zaune yana tufka da warwara shi da zuciyar sa ya soma jiyo wani irin hucin zafi, ya kuma rasa daga ina zafin ke fitowa, kan a jima kuma yaji atmosphere na dakin na sauyawa da wani irin kauri mara dadi. Mikewa yayi da kyar yana tari yana rarraba idanu cikin son fahimtar abin da ke faruwa, kawai sai ya ga ashe daga na'urar sanyaya daki ne (A/C) hayaki kawai take fiddawa da wani irin kauri, baya raba daya biyun wuta ce aka karo mai tsananin karfi ta janyo sanadin hakan. Kafin yayi wani action A/C din ta kama da wuta ganga-ganga, sai kuma gabadaya wayarin na lantarkin gidan ma ya kama jikake taratsa-tsa....lantarki na haduwa da dan uwan sa yana bada feshin wuta daga inda duk wata wayar wuta take a falon.
Kan ayi haka kwan lantarki yayi bindiga, duhu ya mamaye falon, sai hasken tartsatsin wuta. Da gudu ya soma neman hanyar tsira cikin tsananin gigita, amma kasancewar dare ne kuma kwayayen lantarkin falon sun yi bindiga sun tarwatse sai ya rasa hanyar kofa. A lokacin ne ya fara salati yana kiran yaran sa "Jonathan.......Jafaru.....Solomon.." da iyakacin muryar sa, amma ina! Basu ji shi ba sabida suna can baskwata, sun gama ayyukan su na yau, ga wuta ta kama ganga-ganga har ta fara cin kujerun falon, labulaye da kayan kallo.
Da gudu ya dinga lalube har yaji hannun sa ya kama marikin kofar da bai san ko ta ina bace, ya murda ya shige ciki yana salati hadi da ihu, ashe dakin barcin sa ya fado. Nan ma tuni lantarkin dakin ya laso wutar, hayaki ya turnike har ba ya iya ganin komai. Amma ya san duk wasu muhimman takardunsa da kadarorin sa suna cikin dakin nan. Wani salati da ya saki mai kamar ihu ya nufi kwabar da yake adana komai ya soma kokarin budewa. Tsabar rikicewa tasa ya manta password din.
Prof. Numan bai san sanda ya fashe da kuka ba, ya daina hangen dukiya ya koma tunanin yadda zai yi ya tsira da ran sa. Gabadaya bai san inda ya jefa wayoyin sa ba. Ya fi tunanin ya baro su a falo ne bisa centre-table daidai inda ya kwanta dazu.
Ya tabbatar in ya cigaba da tsayuwa yana tunanin hanyar tseratar da dukiyarsa to zai kone ne ayi biyu-babu shi da dukiyar. Hatta takardun Halima da komai nata suna cikin kwabar.
Dabara ta fado masa....ya afka toilet, ya taka masai ya bude tagar ya danna kai, amma karafan da aka yiwa tagar makari dasu suka hana ko rabin kafadun sa shugewa. Haka ya dirgo daga kan tagar zuwa cikin bahon wanka. Karar da kashin kafarsa ya bayar ya tabbatar masa in ba karyewa ba to tsagewar kashi. Sai ya tuna da kan telephone din cikin bandakin.
Da rarrafe ya isa inda telephone din yake, hannun sa na rawa ya daga, yayi dialling code din kiran maigadi, yana jin maganar maigadin a kunnen sa yace.

"Seun, ina ciki zan mutu.....gobara a daki na......ku kawo min dauki na rasa hanyar fita…. ina toilet....".
Daga haka ya saki kan wayar sakamakon hayaki da tarnaki da turirin wuta da ya sarke shi. Ya soma tari yana kokawa da numfashin sa wanda ke neman daukewa gabadaya. Ba abinda yake son gani a wannan lokacin sai HALIMAH don ya fidda rai da rayuwa......!!!

Seun, bai yi wata-wata ba ya kira 'fire-service' wadanda aka fi sani da 'yan kwana-kwana. Duk ma'aikatan gidan sun fito da gudu jin ihun Seun. Da wutar da komai Seun ya danna kai cikin gidan don kubutar da ubangidan sa. Kasancewar ya san kan gidan sosai haka ya danna kai da kayan sojojin sa ya zagaya ta kofar baya zuwa sassan Prof.
Ya fiddo shi daga toilet rai a hannun Allah. Shi kansa Seun wuta ta fara cin kayan jikinsa, Prof.kuwa hayaki da tururin wuta ya shidar da shi tuni. Fatar kafarsa ta salube.
Dai-dai lokacin da jiniyar 'yan kwana-kwana ta shigo layin. Kafin a shigar da shi Ambulance ya daga ido da kyar yana kallon yadda dankareren gidan sa ke cin wuta....gidan da ya narkar da biliyoyi ya gina domin 'ya'yan sa Halima da Hanan...ya kuma kwashe tsayin shekaru biyar yana gina shi.....Gidan da yayi rayuwa da Safeeyah.....Gidan da ya kunshi duk wani tarihi na rayuwar 'ya'yan sa...... dukiyoyin da ya tara cikin sif ya hanasu ci........yau gashi wutar duniya na lashewa a banza.....!!!


Please Login or Register in order to submit comment