Reading AURE KO BOKO 3 BY TAKORI Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a tsakanin ‘yan jam’iyyarsu ya haye saman Inusa da Aliyu Sardauna da kaso mafi rinjayen magoya baya.
Wannan yasa jam'iyyar NRC (Northern Region Congress) ta kara baiwa Hashim tsaro a duk inda zai shiga haka a gidan sa dama iyalin sa.

*****

ABUJA
GIDAN PROF. ZUBAIR NUMAN

Lokacin da ya shigo gida magriba ta kawo jiki, Prof. Har wannan lokacin haka nan yake zaune kwal shi kadai a tafkeken gida kamar tsohon maye, sai tarin arzikin da ya fi karfinsa kamar ya kashe shi, neman mata kam ya dade da dainawa tunda ya fahimci tsufa ya fara kama shi, kayan alatu na fita hankali har ya rasa yadda zai yi da su a gidansa saboda babu masu mora. Ga tsufa da ya fara cin karfinsa. Domin tenure din sa ta dade da karewa daga NCC. A yanzun shi retired ne daga aikin gwamnati. Zaune yake a gida baya aikin komai. Sai pansho da garatuti da yake karba. Baya zuwa ko'ina sai cin dukiyar da ya tarawa 'ya'yan sa shi kadai ransa.

A kujerar falon shan iskarsa ya zauna ya kwantar da kai a masangalin kujera yana lumshe idanunsa. Kwanannan ba tunanin da yake yi sai na Halima. Ta tsaya masa a rai har mafarkin ta yake cikin kyakkyawan yanayi. Wayarsa ya dauka a karo na sau ba adadi ya kira Hanan, wadda ke gidan mijin ta a garin Porthearcourt, ita kam Hanan har ta fara jin tausayin Daddyn nasu, a bisa damuwar sa akan son sanin inda Halima take, ta fara karaya, amma in ta tuno gargadin Halima sai ta kara sarewa.

"Idan kika fadawa Daddy kinsan inda nake Allah ya isa Hanan ban yafe miki ba".

Ta kuma tuno muguntar da shi Daddyn ya yiwa Haliman. Sai ta ga cewa Halima ta fi ta gaskiya, bata bukatar Daddy a halin yanzu cikin rayuwar ta. Bai ji kanta a lokacin da take neman jin kansa da gafarar sa ba!!!

“Yanzu Hanan ba za ki tausaya min ba? Duk soyayyar da na ba ku kin manta, ba za ki gaya min ina Halima ta ke ba sai ranar da na bar duniya ban ganta ba ko? Hanan ki tuna ko waye Daddynku, shi ne mahaifin ku mai sonku da kula da ku, wanda ya yi muku komai da uwa ke yi wa ‘ya’yanta. Na karbi kuskure na kun fi ni gaskiya, ba za ki afuwan ta min ki hada ni da ‘ya ta ba?”
Ya soma wani irin tari kuful-kuful, maganar ta sarke ta kasa fitowa, alamun rashin koshin lafiya ya bayyanar da kansa a tare da Farfesa.
Hanan couldn’t keep it, ta yi shiru tana hawaye. Ba za ta iya kirga wannan shi ne karo na goma sha nawa da Daddy ke rokonta ta hada shi da Halimah ba.
“Daddy sis Leemah ba ta cikin Abuja fa, nima nemanta nake yi ruwa a jallo. Amma insha Allahu zan kara zage damtse wajen neman ta, kuma zan gaya maka da zarar na samu labarin ta”.
Ta kashe wayar ba tare da ta jira cewarsa ba. Kada ya karya sauran lagon ta ta karya alkawarin data yiwa Leemah. Sannan a take ta kira Halimah, ta gaya mata komai kan damun ta da Daddy ke yi wajen neman ta.
Halimah wadda ke hakimce cikin luntsumemiyar kujerar leather ta falonta, ta yi murmushi ta kwantar da kwayan idon ta kasa tamkar Hanan na kallon ta, sanna tace da kanwar tata.
“Kyale Daddy kin ji Hanan, har yanzu bai fara nadama ba, kadaici ne ya ishe shi. Yake neman abokin taya zama, tunda kema kin tashi. So yake na koma mu ci gaba da zama ko? To ni da igiyar AURE za'a kai ni kabari na insha Allahu".

****






Hanan Zubair, ta fito daga dakin ta da gudu jin 'yar ta Yusra na callara kuka, sai ta hangeta tana mirginowa daga matattakalar dogon benen su har ta kai kasa... jini ya soma malala kamar an sunce famfo. Wata kara da Hanan ta saki ita tayi sanadiyyar fitowar Saleem a guje shima daga kitchen din falon, kafin Hanan ta idasa saukowa ta cimma 'yar, Saleem ya riga ta.
Ya girgizata ya girgizata amma babu alamun akwai sauran rai a jikin ta. Ta rasu!.
Hanan da mijin ta Saleem sun shiga wani mawuyacin hali, na rashin yarinyar, duk da ba ta hanyar halal suka sameta ba suna son ta kamar yadda iyaye ke son kowanne da. Babban tashin hankalin su ba'a fi kwana biyar ba kenan da yiwa Hanan check up a asibiti bayan wani zubar da jini da tayi ta yi mara yankewa, likita ta tabbatar musu Hanan bazata iya sake conceiving ba (daukar ciki). Mahaifar ta ta yi rauni.
Tun daga lokacin kuma Hajiyar Saleem ta bude masa wuta kan sai ya kara aure, tunda shegiyar ta mutu, kuma an ce bazata sake haifar na halali ba.
Da wa zata yi sharing wannan abubuwan alhinin da suka sameta tunda su ba su da uwa? Sai Haleemah kadai.
Watakila Halimah ta tausaya mata ta bata Safeeyah ma, ita kuma ta yi alkawarin yi mata kyakkyawan riko fiye dana diyar data haifa.
Saleem bai hanata zuwa Kano ba data ce masa zata je wajen Yayar ta Halimah. Duk abinda zai sa ta farin ciki a wannan dan tsukin shi yake yi. Washegari ya yankar mata tikitin jirgin Azman mai zuwa Kano daga Porthearcourt.
*****




Hanan ta sauka a Kano da yamma lis, daga nan ta dauki Adaidaita zuwa unguwar data san su Halima suke wato Yakasai. Bata gayawa Halima zata zo ba, surprise take son yi mata.
Saidai katon kwado ne yayi mata sallama. Wani dake tsaye daga gefe ya ce da ita. "Ai tunda aka tsayar da Hashim takarar gwamna suka tashi suka koma Nasarawa".
Hanan tace "no, ba wadannan ba dai, ko suna ne ya zo daya" yace "in dai Hashim mijin Halima mai kwan kaji ne to shi nake nufi".
A take Hanan ta fiddo waya ta kira Halimah. "Sis, gani a kofar gidan ku ana gaya min wai kun tashi" Halima tsabar farin ciki da zuwan Hanan kidimewa ta yi, tace da Hanan ta tsaya anan kofar gidan sun yanzu zata turo direba ya dauketa.

Hanan sai ta kara sakankancewa da al'amarin Ubangiji. Ba jimawa direban ya faka a gabanta ta shiga suka nufi Nasarawa.
Halima da Hanan suka wani irin rungume juna kafin Halimah ta saketa ta tambayi baby Yusra. Hanan ta nemi waje ta zauna tana share hawaye da gefen mayafin ta, lokacin ne Halima ta lura da tsananin ramar da Hanan din ta yi. Jikin ta yayi mugun sanyi, ta zauna gefen Hanan tana kara tambayar ta ina Yusra?
"Ta rasu!"
Hanan ta fada tana kifa kanta a kafadar Halimah. Tare da rushewa da kuka.
Tiryan-tiryan ta bata labarin yadda Yusra ta fado daga bene ko shurawa bata kara yi ba, da matsalar mahaifarta sannan da halin data ke ciki da mahaifiyar Saleem a yanzu.
Halima bata san yaushe ta fashe da kuka ba suka hada goshin su suna ta yi. Bazasu daina dakacen rashin rayuwa tare da mahaifiya ba. Wani tunani ya zo wa Halimah.
Hashim ya dade da yi mata alkawarin sada ta da dangin ta na uwa da uba, tana ganin babu lokaci mafi dacewa da hakan irin yanzu, ga ta ga Hanan in Salim ya amince su je tare.
"Lokaci yayi da zamu nemawa kanmu gata Hanan, mu tashi mu nemo dangin mu na uwa da uba, mu bar Daddy da halin sa shi kadai don bazai taba canzawa ba".
Hanan tace "wallahi ya canza Leemah, ya dade da canzawa. Sune dai suke fushi da shi. Amma ina bayan ki kan mu mu neme su. Kuma a daidai wannan lokacin".

Halima ta mike tana kiran Hashim a waya wanda ke can Abuja a lokacin wajen harkokin Campaign dinsu, ta gaya masa zuwan Hanan da shawarar da suka yanke. Hashim ya ce "i'm sorry Sweetheart, ban cika alkawari na ba tuntuni amma yanzu zan cika. Ina nan dawowa gobe, in mijin Hanan zai bar ta tayi kwanaki tare damu sai mu shirya tafiyar da zarar na dawo gobe". Halima tayi godiya, sannan suka yi musayen kalaman soyayyar su da bata ginsar su….
"I'm missing you sweetheart….."
"....missing you is all i do Cheriè. Stay blessed".
Suka yi sallama. Hanan na kallon ta tana murmushi, ta yarda Halima ta yiwa kanta kyakkyawan zabi a rayuwa. Zabin da bazata taba dana-sani ba! Arziki ba shine kadai kwanciyar hankali ba. In kika cire babun tasu Halima ta fita sa'ar aure. Ga babun ma na neman zama tarihi a gare su.
Halima ta gaya mata yadda Zarah ta taimaki Hashim ta hada shi da Baban ta. Da position din da suke kai a yau. Hanan tace "Zarah ai mai son ki ce, she will do more than that. Daddy fa ya dawo min da takardun mu na karatu, tare da asusunan bankunanmu, daga wancan lokacin zuwa yanzu kada ki so kiga abinda ya karu akai. Ni tsoro kudin cikin bankunan ma suka bani. Ya bani nawa yace duk ranar da Allah ya sake hada ku zai baki naki. Sis Leemah kiyi hakuri ki yafewa Daddy, he really regretted".
Halima tayi wani murmushi mai ciwo, tace "Hanan bana bukatar komai a halin yanzu don ba aiki nake nema ba, i'm a total house-wife (ni tabbatacciyar matar aure ce). Duka lokutana da lafiyata na sadaukar dasu ga AURE na da iyali na. BOKO na riga na bashi baya, kuma ni Halima in na baiwa abu baya, bana sake waiwaye.
Bana bukatar takardun makaranta a halin yanzu da duk wani abu da ya shafi boko. Kudi kuwa wallahi in zai kai su baitul-mali ko ya bada su sadaqatul-jariya ga mabukata gara yayi hakan ya fiye masa alkhairi, amma ni Halima bana bukata."
"Sis Leemah, yaushe kika koyi taurin rai ne? Shikenan zan baki mamaki watarana".
Safeeyah ta fito daga daki tana laluben bango, tana kiran Halima. Da gudu Hanan ta karasa gareta, ta jima da sanin matsalar yarinyar daga bakin Halimah. Tace "Doty, gani na zo me zan samu?" Ta fada tareda daukanta suka dawo kujera suka zauna gefen Halimah. Yarinyar ta sha ado cikin kaya 'yan kanti ruwan hoda, gashin kanta ya sha gyara don da Halima da Hanan duka ba baya bane wajen gashi. Ubansu bafillace uwar su kuma shuwa.
"Aunty Hanan ce?"
Safeeyah ta fada tana shafa fuskar Hanan yadda take yi in tana son gane fuskar mutum. Hanan ta lumshe ido ta dafa hannun nata tana fadin "i look so much like your mother, zaki bi ni Porthearcourt? 'Ya ta ta rasu, ke kadai kika rage mana".
Safeeyah tace "idan na tafia wa zai zauna da Mom da Daddy na?" Da sauri Hanan tace "Mom zata haifo wani baby.., nikuwa bazan sake haifowa ba, I have only you”. Halima tayi murmushi ta wuce ciki ta bar su don samawa Hanan abinda zata ci, ta barta suna ta tafka musu itada Safeeyah kan tafiya Porthearcourt. Komai ta ce sai Safeeyah ta yi gardama. Bata ce komai akai ba don ta san Hashim ba zai taba bari ba.
Mai raba shi da Safeeyah sai Allah! Balle Hanan da tun fil azal jinin su ba gamuwa yayi ba.
*****

Tun yammacin ranar suka fara shirye-shiryen tafiya Maiduguri da Numan ta jihar Adamawa. Salim ya ce ko sati ne Hanan tayi ba komai, watakila shima yayi joining dinsu ta jirgi in sun isa Maiduguri. Hanan ta bawa Halima lambarsa ta hada shi da Hashim, nan da ban abota ta kullu.
Washegari suka shiga kasuwar kantin kwari don sayen tsaraba, komai kwasowa suke tun daga kan kayan abinci da na masarufi da suttura. Sai da suka cika boot din motoci uku sannan suka koma gida gefen maghriba.
Suna zaune a falo da daddare sun kunna tv suna sauraron labarai suna shan soft-drinks, Safeeya na bisa cinyar Hanan tana bata lemon, tashar ARTV ta Kano ake nunawa. Abokan hamayyar Hashim ne ake programme da su inda suke ta bankado sirrikan Hashim na baya duk don su bata shi a idon talakawa. Jam'iyyar adawa ta tabbatarwa manema labarai cewa shi tsohon ma'aikacin NCC ne wanda Commission din ya kama da laifin sama da fadi da kudi masu yawa na ma'aikatar shekarun baya aka kore su shi da matar sa.
Sannan Hashim ba ba-kano bane cikakke tunda kuwa uwarsa Basudaniya ce. Ya sato 'yar uban gidan sa ya aureta bada sanin mahaifin ta ba... maganganu dai gasunan barkatai na tozarci da kage wadanda baka raba 'yan adawar siyasa da irin su.
Hanan mikewa tayi ta kashe talbijin din tana tsaki, tace "'yan media sai Allah ya gyara wajen yada abinda basu da tabbas akan sa. Sara da sassaka dai baya hana gamji tofo, don haka ya rage nasu su fadi duk abinda suke son fada".
Halima bata ce komai ba amma tabbas ta girgiza da wannan sharrin da aka yi musu akan NCC. Hanan ke kwantar mata da hankali tana gaya mata siyasa ta gaji haka, sai in baka shigeta ba.
Washegari da daddare Hashim ya dawo cikin wani yanayi, har da jini a goshin sa da jikin kayan sa. Halima ta kidime ta shiga tashin hankali tana tambayar sa ko lafiya? Murmushi yayi yana share goshin sa da hankicin sa sannan yace "kada ki damu Sweetheart, ana bibiyata ne, so suke su kashe ni amma Allah yana nan.
Sun tare mu a kan hanyar Kaduna da kyar sojoji suka kwace mu. Ana zargin ‘yan PRP ne kuma hukuma ta shigo cikin maganar. Sannan an zuba tsaro sosai yanzu a gidan nan. Don haka tafiyar jirgi zamu yi gobe zuwa Maiduguri, daga can ma zuwa duk inda zamu je jam’iyya zata dauki nauyin kula da mu". Halima na kuka tace "No Cheriè, ka bari sai after election ma je, na fasa, ina tsoron kada wani abu ya same ka acan din". Hashim ya rungumota yana fadin kada ki damu, Allah na tare damu, after election ne zuwan zai yi wahala, gara muje yanzu mu huta. Ai kuna da address din duka na Adamawa da Maidugurin ko?"
Tana share masa digon jinin ciwon goshin sa tace " Hanan ta karbo addresses din duka wajen Baban ta" Hashim yayi dariya ya ja dogon karan hancin ta "wato baban ta ita kadai, banda mu?" Ta sunne kanta a kafadar sa tana fadin "na yafe mata shi".
Hanan tace ita a dakin Safeeyah zata sauka, don haka tun kan Hashim ya shigo sun kuke a daki itada Safeeyah sun kwanta. Hashim kuma wanka Halima ta taimaka masa yayi, ya ci abinci ya sha maganin ciwon jiki sannan suka soma tsara yadda tafiyar su ta goben zata kasance. Kafin a koma fafatawa a fagen soyayya.
******
















WASHEGARI
ADAMAWA, Nigeria
Gidan Modibbo Hussaini Muhamad Numan ba boyayye bane a garin Numan ta jihar Adamawa. Tunda suka shigo Numan suka yi tambaya sau daya aka yi musu jagora har gidan Modibbo Hussaini, Modibbo Hussaini dattijon bafullace talaka likis, kani yake ga mahaifin Alh, Zubair Numan. Yana da matan aure hudu da 'ya'ya bila adadin da jikoki duk a gida daya.
Kusan ace Modibbo Hussaini shikadai ya ragewa Prof. A dangi, daga shi sai wata kanwar kakarsa Goggo Iyami. Bata tsufa cancan ba kuma yaranta duka mata ne sun yi aure duk sun hayayyafa. Sauran manya a zuri'ar su duk sun rigaye mu amma 'ya'yan su matasa suna raye a nan Numan.
Salim kusan tare suka sauka da shi a Adamawa, tare suka hadu a filin jirgi Shuwagabannin NRC na jihar Adamawa su suka zo da motoci suka dauke su zuwa Numan, kasancewar dan takarar gwamnan Adamawa ma dan jam'iyyar su Hashim ne.

Modibbo ya fito zai tafi gona, sai gani yayi ana faka masa dindima-dindiman motoci a kofar gida. Dakatawa yayi cikin tsoro yana kallon motocin wadanda dukkansu tinted ne. Mai tsaron lafiyar Hashim shi ya fara fitowa ya bude masa kofa, sai da ya fito sannan Salim ya fito, sai matan nasu guda biyu da Safeeya a hannun Hanan.
Dukkan su suka karasa gaban dattijon suka tsugunna, shikuma cewa yake "maraba - lale ku shigo daga zaure in shimfida muku tabarma".
Duk suka duru a dan karamin soron na Modibbo, hannu ya baiwa su Hashim amma suka ki, suka gurfana irin na surukuta suna gaishe shi. Modibbo yace.
"Nafi ganewa ku bani hannu mu gaisa, shine abinda muslunci ya yarda da shi kun ji?"
Duk sai suka mika mai hannun.
"Samari da 'yammata daga ina? Ban waye da ku ba".
Halima ce ta wakilci Hanan, wajen yi masa bayanin ko su waye su. 'Ya'yan Zubairu Muhammadu Numan na garin Abuja. Kafin ta rufe baki Modibbo ya fara kuka, ya kama hannun Halima da Hanan yana fadin "na gayawa 'ya'yana duka ko bana raye, ko bajima ko ba dade zaku zo ne!".
Tausayin dattijon yasa Halima kuka, tace "wallahi Baffa mun dade muna so mu zo, Allah ne bai yi ba. Life's hustling and bustling (kujuba-kujubar rayuwa) bata bar mu ba sai yanzu. Kuyi hakuri ku yafe mana". Hanan tace "Daddy ma yayi nadamar rashin neman ku da baya yi, yace ba da jimawa ba zai zo shima" Modibbo sai yayi murmushi kawai yace.
"Ki kyale babankin nan kin ji? Ko ya nememu a halin yanzu neman bashi da amfani. Wanda ya tozarta zumunci da sannu Allah zai tozarta shi. Ku dai tun da kunyi hankalin zuwa neman mu mun gode Allah, mun kuma ji dadi kun kawo kan ku gida".
Ya tashi ya shiga gida, ya fitowa dasu Hashim kwarya cike da damammiyar fura da taji nono kindirmo, nan suka jefa ludaya suka hau sha cikin marmari shi da Salim, Hanan da Halima kuma yayi musu jagora zuwa cikin gidan wajen matan sa.
Yawancin 'ya'yan Modibbo manyan maza ne, sai auta mace wadda itama tayi aure. Har gidanta aka kai su wato Abuwa. Daga nan aka dinga raka su gidan 'ya'yan Modibbo daya bayan daya da kuma gifan Goggo Iyami. Ita kam kukan farin ciki ta saka ta rungume su Halimah.
Hashim yasa aka shishsshigo da duk tsarabar suka yo musu a bayan motocin su. Nan suka wuni sur, shakuwa ta shiga tsakanin Hashim da Saleem, da magriba ta kawo jiki bayan sun yi sallah tareda Modibbo suka yi masa sallama kan zasu shiga cikin Adamawa su kwana, gobe da safe zasu biyo su dauki su Halimah.
Halima da Hanan dakin goggo Iyami suka kwana, ta kwana basu tarihin iyayen su da kakannin su na wajen Uba, tace gara da baku biyewa Ba-amurken uban ku ba, in bai yi wasa ba sai rashin zumunci ya kai shi wuta. Hanan dai hakuri take basu tana gaya musu Daddy ya canza, shi ya batta adireshin su da kan sa, kuma kwanannan zai zo ya nemi gafarar su.
Halima in an yi zancen Prof. Bata cewa komai akai, shiru take yi, don a ganin ta itace mai tabon Prof. Numan fiye da kowa.
Kudade masu yawa Hanan tayi ta rabo, ta kuma cewa Baffa da goggo iyami nan bada jimawa ba za'a buge gidajen su ayi musu na zamani. 'Ya'yan su kuma idan akwai wadanda sukayi karatun zamani a bata guda uku zata tafi dasu Porthearcourt ta sama musu aiki. Goggo Iyami tace “daga Auwalu sai Basiru sune sukayi wannan abun digirgir a cikin Adamawa, sauran iyakarsu sakanni in dire. Na ko ji suna batun neman aikin nan”.
Shikuwa Hashim cewa yayi duk wadanda basu yi karatun ba a bashi, bayan zabe idan Allah ya sa yayi nasara zai dauke su ya basu ayyuka tare da shi.
Yau dai gidan Baffa Modibbo kamar an musu bushara da shiga aljannah, haihuwa mai rana, abinda Zubairu bai yi musu ba a shekaru talatin yau gashi 'ya'yan sa sun musu a rana daya.
Washegari da wuri suka kama ha yar airport, bayan motar su taf da tsarabar Numan, wadda aka yi wa kyakkyawan packaging, inda suka hau jirgin da zai kai su Maiduguri. Don ganawa da dangin mahaifiyar su marigayiya Safeeyah.
******











A Maiduguri
Daddy ya gayawa Hanan akwai kanwar mahaifiyar su Hajja Falmata a raye, tana aure a cikin Maiduguri, har lambar wayarta ya bata, ashe dama ya san da wanzuwar kowa ya kuma san inda suke, ra'ayin sa na kada a rabe su shi da 'ya'yan sa balle su raba shi da su ne ya hana shi dangana su da su.
Suma kuma dangin marigayiya Safeeyah daga baya fushi sukayi suka bar masa 'ya'yan sa.
Saboda sun sha zuwa takanas tun daga Maiduguri tun yaran na kanana don su gansu baya bari, haka zasu zo su koma wutsiya a zage ko ruwan gidan sa basu sha ba. Musamman Hajja Falmata. Da yake ta sha kiran sa a can baya don

Please Login or Register in order to submit comment