Reading AURE KO BOKO 3 BY TAKORI Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Duk tarin wahalarsa na NCC yana cikin sif dinnan, komai ya kone kurmus! Hatta kwalayen karatun Halima da ya kwace basu tsira daga konewar wuta ba...

Idanun sa suka shiga wani irin lumshewa a hankali yana fadin "YAA SALAMU SALLIM!". Wani bangare na zuciyarsa na ta amsa-kuwwar fada masa "....this is the end of Zubair Numan.........da tarin dukiyar sa da izzar sa........" wani bangare na musantawa da cewa ".... kana da sauran dama ta neman Lahira tunda da sauran numfashin ka....... Rai dai! Aka ce baya taba rabuwa da rabo, sai dai idan ya kare!
Daga haka idanun sa da kwakwalwar sa suka rufe suka tsaya da aiki gabadaya. Bai kara sanin me ke faruwa a duniya ba.....
****

Zabe na kara karatowa, al'amuran siyasa da kalubalenta na kara tsanani ga su Halima. Abokan hamayyar siyasa sun sanyoshi gaba, duk wani siririn zare na rayuwar sa saida aka zaquloshi na nuna yayi sama da fadi ne da wasu kudade a NCC shine dalilin da Zubair Numan ya kore shi, ya rufa masa asiri ne sabida yana auren diyar sa da ya sato ya aura.
Amma da yake an ce Zakaran da Allah ya nufa da cara..ko ana ga muzuru ana ga Shaho sai ya yi. Jam'iyyar NRC ta sanyawa Hashim tsaro yadda ya kamata shi da iyalin sa. Sannan daga shi har matar sa Halima masu karar da rabin dare a tsaye ne cikin Ruku'i da Sujudi. Don haka zamu iya cewa; hassadar masu hassada bata taba siyasar Hashim da komai ba, tamkar taki take zame masa. Wanda ya rike Allah da Manzon sa ya kuma yi riko da gaskiya to zai yi ta yin gaba ne komai sharrin mai sharri. Kullum farin jinin sa karuwa yake a idon al'umma, sunansa kara tambari yake a jihar Kano.
****

RANA MAI DIMBIN TARIHI
Rana mai dimbin tarihi ga Halimah da Hashim itace ranar da aka gudanar da zabe (secondary election) a tsakanin duka jam'iyyun Nijeriya. Inda a kowacce mazaba jam'iyyar (Northern Region Congress Party) wadda aka fi sani da Jam'iyyar talakawan Arewa ita ce kan gaba, tun daga presidential har gubernatorial. Al'ummar jihar Kano musamman matasa maza sun fita kwan su da kwarkwatar su sun dangwalawa YAKASAI (sunan sa kenan a Siyasa). Tun daga sanda suka ji missions and vissions din sa a BBC debate na ‘yan takarar gwamnoni; cewa shi akan cigaban matasa zai tsayar da administration dinsa domin sune future din Nigeria. Ban taba ganin Engnr. Halima Zubair Numan ta yimin kyau irin na yau ba. Ban taba ganin fuskarta na fesar da annuri irin na yau ba. Tana tsaye a polling unit na Kano-Municipal tareda Hashim da Safeeyah rike a hannun ta, cikin jikin ta ya girma sosai. Sanye take da laffaya koriya shar mai ratsin fari wato kalar tutar Najeriya. A cikin rumfar da suke zaune akwai Dr. Rabiah da mijin ta, Sa'adatu da mijin ta Lawal. Ta bangaren Halima kuma mutanen Numan ne kwansu da kwarkwatar su, ga kuma Hajjah Falmata ma sun zo da dukkan 'ya'yan ta. Hatta Salima dake Lagos ta zo don tsayawa da Halima a wannan muhimmiyar rana mai dimbin tarihi a gareta.
Bayan kammala zabe suka dawo gidan Halima dake Nasarawa. Kowa yayi mamakin rashin ganin Hanan don tun kan su taho filin zabe suke jiran isowar ta, da lokaci ya kure dole suka taho babu ita don wayoyin ta duka sun ki shiga.
A daren ranar kafafen yada labarai suka sanar da zababben gwamnan jihar Kano wato Engnr. Hashim Ismail Yakasai. Za'a rantsar dasu nan ba da jimawa ba.
*****


Likitoci rankatakaf! Suka rufu a kansa don kakarin nemo ran sa. Hayaki da turirin wuta ya salube duka fatar kafafun sa. Ya kuma yi lahani a mashaqar numfashin sa. Prof. Zubair Numan, yana raye ne kawai amma bai san a duniyar da yake ba, har tsayin kwanaki uku.

Seun, shine tare da shi, tun ranar da abin ya faru yake gwada wayar Hanan amma bata shiga, shi kuma bai da layin mijin ta, sai a rana ta biyar ne yayi sa'ar samun ta.
Hanan ta yi shirin tahowa Kano, anko suka yi na laffaya ita da Halimah sai kala daya banbanta, nata purple ne light and dark, don tsayawa tareda Halima ranar zaben mijin ta, wayar Seun ta risketa, "where have you been Hanan? Daddyn ki na kwance rai a hannun Allah a asibiti, gidan ku ya kone kurmus! Sai abinda ba'a rasa ba ya saura.......".
Tsananin tashin hankali yasa Hanan mancewa da batun tafiya Kano ta wuce Abuja kai tsaye daga Porthearcort.

A yadda Hanan ta samu jikin Daddy sai zuciyar ta tsinke. Komai ya kwace mata. Ta kifa kai a kan kirjinsa tana kuka. Amma ta yanke a ranta bazata gayawa Halima a yau ba, kada tayi spoiling farin-cikin ta. Zata bari sai hada-hadar siyasa ta lafa. Ko Hasheem bata gayawa ba yau ranar farin-ciki ce a garesu kuma sun cancanceshi komai kankantar sa. Duk da Halimah na fushi da Daddy ai Uba-Uba ne. Dole hankalin ta ya tashi in taji abinda ya same shi.
Hanan na can Abuja suna jinyar Daddy itada Salim da Seun, Halima da Hashim na Kano suna celebrating victory din su, ba tare da sun san abinda ya faru a Abuja ba. Salim ma bai fada masa ba. Ba jimawa kuma aka rantsar dasu Hashim suka yi hijira zuwa "Government House Kano State". Karkashin rakiyar babbar aminiya Zarah Datti Giade da dukkan iyalin Alhaji Datti Giade da 'yan uwan su na jiki da makwabtansu na Yakasai da abokan arzikin Inna Haajar da na unguwar da suka fara zama a Kano.
Da Halima ta nemi ba'asin rashin zuwan Hanan, cewa tayi ita da Salim sai daga baya zasu zo taya murna, sun yi tafiya mai muhimmanci zuwa jihar Calabar.
"Kowanne irin muhimmanci ke da tafiyar, yakamata a ce a wannan ranar babu ke tare da ni Hanan?". Halima tayi korafi.
Hanan ta daga ido ta dubi Daddyn su, wanda ke kwance kafafu a salube sai juya kai yake saboda azaba, hawaye masu dumi suka cicciko idon ta. Tsakanin shi da Halima bata san wa tafi tausayawa ba yanzu. Halimah has gone through a lot. Yau ce ranar girbar hakuri da sadaukarwar ta, ranar farin-cikin ta bazata lalata wannan farin-cikin data tsinkaya a muryar Halimah ba. Ta kakalo murmushi ta ce.
"Your excellency, First Lady of Kano, kai na bisa wuyana. Amma tunda nace miki tana da muhimmanci to ki yarda tana da shi din. Ina nan tafe bada jimawa ba, bani Safeeyah in mata "congratulations".
Dariya Halima tayi jin sunan da kanwartata ta kira ta dashi. She's indeed Kano first lady after being Kano last lady! Tace "Safeeyah na can cikin yara, yau ta manta bata da ido. Harka kawai take yi da mutane kace-kace" Hanan tayi murmushi cike da kauna da kewar yarinyar sannan suka yi sallama.
Hajja Falmata da Goggon Numan ne suka shigo karamin falon da Halima ke zaune tana waya da Hanan, suka shiga lissafin abinda za'a sallami bakin Numan da shi da na Maiduguri Halima na amsawa tana bada order ta wayar hannun ta. Kwanaki bakwai sur ba abinda ake a gidan gwamnati sai hidima da bidirin farin-ciki kala-kala. Halima da His Excellency basu samu kansu ba sai daren ranar asabar da kowa ya tafi, bangaren nasu ya saura daga su sai Safeeyah, hatta ma'aikata sun nabba'a a bangaren su. Hashim ya mikar da Halima dake zaune ya ja ta cikin jikin sa a hankali.
"Words are not enough to express my gratitude, for your being with me through light and dark, through struggles and obstacles, for your sacrifice and infinite love,....Halimah you are my life and source of every happiness of today, i assure my love, heart and everything in my possession. I LOVE YOU with all my heart… HALIMAH!"
Halima ta zama wordless, kalaman Hashim sun gama kashe ta, kawai sai ta tafi cikin slow-motion ta kanannade a jikin sa kamar macijiya. Dare ne da suka gudanar da wata irin sassanyar soyayya wadda hasken zuciya da yalwar farin-ciki ne ya jagorance ta. Contentment da sukunin zuciya ya kawatata yayi mata ado da alharini, domin sun kasa bayyana iyakar kaunar da suke yiwa juna a daren yau da kuma dimbin godiyar su ga Ubangiji.

Watanni biyu bayan tabbatuwar Hashim a kujerar gwamnatin Kano Halima ta haihu, ta haifi 'yar ta mace lafiyayya, tun a asibiti da Hashim ya dauki yarinyar Halima ta roke shi ya sanya mata sunan ZARAH DATTI.
Ai kuwa daga jin wannan albishir Zarah ta dauko hanya ta taho daga Bauchi, da akwatunan kayan barkanta damkam, da ita aka yi radin sunan takwarar ta. Still Hanan na bada uzurin basu dawo daga Calabar ba, wani muhimmin aiki ne ya rike su, zuwa yanzu kam Halima ta fara zargin akwai muhimmin abin da Hanan ke boye mata.
*****

Watannin Prof.kusan uku kenan a asibiti, ya murmure sosai, konannun kafafun sa sun kame sun zama tabo, amma ya rame sosai, kullum hirar sa dai HALIMAH ce, da rokon Hanan ta nemo masa Halima kafin ta Allah ta kasance da shi akan gadon nan bai ga Halima ta yafe masa ba.
Ya tabbata hakkin ta ke bibiyar rayuwar shi. Hanan sai dai tayi zugum ta kasa ce masa komai, don ko jiya Halima ta jaddada mata in ta fadiwa Daddy ta san inda take Allah ya isa bata yafe mata ba! Kuma har abada bazata yafe mata ba".
Yau Salim ya zo ya dauki matar sa suka fice, suka bar Daddy shikadai a daki, amma kafin ta fita sai da ta kunna masa talbijin don ta taya shi hira, kasancewar bata kunna masa sam sabida gudun kada ya ji sunan Hashim a kafafen yada labarai. Yau kuma Salim ya janye hankalin ta da soyayya yayi tagiya ne ya dawo, kuma Seun yayi nisan kiwo, ta kunna masa tv tace.
"Daddy, bazamu jima ba, zamu je mu sha fresh-air mu dawo”. Murmushi yayi mata yace.
"Allah yayi miki albarka Hanan, ke da 'yar uwar ki a duk inda take".

Wani programme da ake haskawa ne ya dauki hankalin sa a NTA Abuja, misalin karfe tara da rabi na dare aka sako shirin a takaice ba gabadaya ba. Debate ne na 'yan takarar gwamnonin jihar Kano na dukka jam'iyyun Najeriya wanda BBC Hausa ta shirya kafin ranar zabe. Kowanne dan takara aka kira zai tashi ya yi bayanin missions and visions dinsa da ya tanadar wa al’ummar Kano idan ya samu nasarar hayewa kujerar gwamna.
Dan takara na biyu da ya mike daga jam’iyyar talakawan Arewa jam'iyya mai farin jini (NRC) shine Engnr. HASHIM ISMAIL YAKASAI, ihu da sowar mutane kadai (in applause) abin burgewa ne. "Sai GWAMNAN MATASA......." Shine inkiyar sa, camera ta hasko kyakkyawar basudaniyar fuskarsa ta ruwa biyu, sosai tayi fresh ta cika allon talbijin din.
Ya soma magana cikin tsararriyar Hausarsa mai accent din Kanawan Usul. A takaice ga bayanin nasa; shi gwamnatin sa ta matasa ce, don su suka tsaya suka zabe shi, don haka su zasu fi kowa cin gajiyar ta, bai tsaya siyasa ba sai don taimakawa matasa marassa aikin yi wadanda suka samu damar yin ilmin zamani da ma wadanda basu samu ba don tsamo su daga afkawa laifuffukan da ake yi a kasar mu Najeriya a yau. Babban mission dinsa shine gina future generation. Samar da aikin yi da sana'o'i ga matasa da kuma kawar da cin hanci da rashawa da koyawa matasa tsayuwa akan diga-digan su.....

Prof. kara matsowa ya yi gaban talabijin din don ya tantance fuskar wa yake gani haka… it's so familar...... haka muryar ma.... hakan bai ishe shi ba sai da ya dauki medicated glass dinsa ya manna. Nan ya tabbatar ba kowa ba ne, P.A din Halima ne, Hashim Isma’eel Yakasai, kuma mijinta a halin yanzu.
Ba jimawa kuma aka hasko shi a matsayin zababben gwamnan jihar Kano ya je bude wani sabon asibitin jiha......an kira sunan sa sau ba adadi, an kuma nuno shi sau ba adadi...ba wani bane Hashim Yakasai ne.

Jikin Prof. ya mutu murus, daga inda yake zaune, bai san sanda ya miki tsaye ba, ya kuma koma jabar! Ya baje cikin kujerar da ya tashi. Ya rasa inda zai sa kansa da mamaki da tu’ajjibi. Zama ya yi kamar wani zararre, shi kadai sai safa da marwa yake a dakin asibitin. Nadama mai tsanani na huda zuciya da bargon sa. Ya yarda wani bai isa ya azurta wani ba, kamar yadda wani bai isa ya talauta wani ba. Ya tuna kalamai na karshe da Hashim ya gaya masa, rana ta karshe da ba su kara takowa kofar gidansa ba bayan korar karen da yayi musu da mugun baki, har zuwa inda yau ke motsi ko inwar su bai kara gani ba.
“ALLAH NA KOWA NE!”. (Inji Hashim).
Tabbas yau ya yarda Allah na kowa ne!!!
Allah shine kadai mai azurtawa kuma mai talautawa ba dai mutum ba!!!

"WA MAN YATTAQIL-LAAHA YAJ’ALLAHU MAKHRAJA.
WA YARZUQHU MIN HAITHU LAA YAHTASIB, INNALLAHA BAALIGU AMRIHI- QAD JA’ALLAHU LIKULLI SHA’IN QADRA’'

Fassara;
“Duk wanda ya ji tsoron Allah zai ba shi mafita, Ya azurta shi ta inda ba ya zato. Hakika Allah mai isarwa lamarunsa ne, Allah ya sanya wa kowanne abu gwargwadonsa”.
****





Daddy bai gayawa Hanan da Salim ya san inda Halimah take yanzu ba, ya gama gane boye masa suke yi amma sarai sun san inda take. Ko abinda ya gani a talbijin bai fada ba. Shiru yayi ya cigaba da kwanciya a gadon sa kamar mai barci lokacin da ya ji dawowar su. Zazzabi mai zafi ne ya rufe shi wanda nadama ce mai tsanani silar zuwan sa. Kallo daya suka yi masa suka gane jikin sa na karkarwar zazzabi suka kira likitan sa ya zo ya duba shi, yayi masa allura sai ya samu barci.
Bayan sayi biyu da yin haka aka sallami Daddy daga gadon asibiti. A gidan sa bangaren ma’aikata ne kawai bai kone ba wato baskwata da harabar waje da wajen adana motoci. Ko rigar sanyawa bai tsira da ita ba. Amma motocin sa suna nan. Don haka Solomon da Jonathan da Jafaru suka bar masa baskwatan su suka koma bangaren Seun. Amma Hanan sai ta kasa tafiya ta bar Daddynta a wannan muhalli cikin wannan yanayi. Zuwa yanzu ta san hankalin Halima ya gama kwanciya is high time ta san halin da mahaifin su ke ciki. Hanan da Salim suka roki Daddy kan zasu tafi da shi gidan su a Porthearcourt kafin asan abin yi a kan gidan sa shima kuma ya kara samun kulawar Hanan ya karasa warwarewa.
Da kyar Daddy ya yarda, don cewa yayi ina aka taba haka? Uba da zama a gidan ‘yar sa? Sai da Minister wato Baban Salim ya sanya baki yace “yadda zan je in zauna a gidan Salim idan lalura ta kama haka kake damar ka je ka zauna a gidan Hanan, kafin ka kara samun sauki a san yadda za’ayi da konannen gidan”.
Hanan ta kira Baffa Modibbo Hussaini bayan sun isa Porthearcourt, ta gaya masa duk abinda ya faru da Daddy cikin watanni ukku. Aka ce naka-sai-naka! Modibbo cewa yayi cikin kidima ga shinan zuwa Abujar. Tace basa Abuja sun wuce gidan ta da shi a Fatakwal zata turo masa tikiti ya zo shi da duk wanda ke son zuwa. Hakan kuwa aka yi.

Daddy bai san hawa ba bai san sauka ba, sai sallamar Kawunsa da ‘ya’yan sa da Goggon sa Iyami ya ji akan sa, yana zaune falon Hanan sanye da farar yar shara da wando na shan iska wanda Salim ya dinka masa da yawa, Hanan na gefen sa tana firfita masa shayin na’a-na’a kasancewar garin yayi lumshi an tafka ruwa. Sabida tsabar kunya da jin tozarta sai ya fashe da kuka.
Ya gurfana gaban Baffan sa Modibbo Hussaini yana bashi hakurin watsar da su din da yayi (don ba su da komai), ya manta dan uwa shine suttura, shine mutunci duk kudin ka duk mukamin ka. Akidar sa ta BOKO mara amfani ce bata amfana shi da komai ba, ya yiwa BOKO gurguwar fassara. Yanzu kam duniya da yake makaranta ce ta koya masa darasi kala-kala.
Modibbo Hussaini murmushi yayi, ya dago shi daga durkuson da yayi a gaban sa suka zauna tare. Ya ce da shi “in Allah ya baka ‘ya’ya to ya baka komai na rayuwa, ka kula da su ka rike amanar su. Ka godewa Allah da ‘ya’yan da ya baka ka wulakanta su. Yau gasu sune kadai marufar asirin ka su suka tallafi kowa naka, a lokacin da kai ka watsar dasu ga duniya. Auren nasu da baka so shi ya suturta ka!
Zubairu mecece duniya? Wallahi aikin banza ce. Ka dauke ta da zafi don kurum Allah yayi maka falalar rayuwa. Ka yi ta istigfari domin kuwa aure sunnar Annabi ne, kuma ya ce wanda ya ki sunnnar sa baya tare da shi…..hakika ka nesanta kan ka da Manzon Rahma (SAW) tunda kana adawa da sunnar sa. Kai baka yi ba, sannan ka ce ‘ya’yan ka ma bazasu yi ba? To lasisin aikata zina ka basu ko me?”
Haka Modibbo Hussaini ya cigaba da lugwigwita zuciya da ruhin Prof. Numan da wa’azi da nasiha mai shiga jiki, baya cewa komai sai hawaye da “astagfirullah” a fili. Baffa yace “afuwa ta da kai Zubairu guda daya ce ka nemi kamilar mace cikin dangi ka aura, ga nan Saddiqa diyar Goggon ku iyami mijin ta shekarar sa guda da rasuwa bata taba haihuwa ba, ka rufawa kanka da ‘ya’yan ka asiri ka mutunta kanka da tsufanka ka aure ta. Sannan zan taimaka kayi tattaki zuwa ga HALIMATU ka nemi gafarar ta.
Hakika ka cutar da ita, ka wahalar da ita, ka wulakanta amanar marayu da Allah ya baka. Bar ganin kai ka haife su, su kan su ‘ya’yan daka haifa amanar Allah ne a hannun ka. Wadda idan ka ci ta tun a duniya sai Allah ya tuhume ka kafin ma aje lahira idan basu yafe maka ba………”.
Daddy kuka yake ta yi sosai yana fadin “don Allah a tashi a rakani wajen Halimahtus-Sa’adiyyah, na riga na ji a talbijin tana Kano koda sun boye mani, kuma ko a kafa zan kai kaina Kano daga nan Fatakwal”.
Hanan a yadda ta ga yanayin Daddy ta san yana nufin abinda yake fadi. Tsoro ya kamata kada ya faki idonta ya tafi Kano a kasa. Ita Allah ya isan da Halimah ta yi mata take ji. To gashi ya ce already ya san komai. Gwamna kuwa ba boyayye bane a kowacce jiha balle gidan sa. Ko ta kai shi ko basu kai shi ba zai iya kai kansa, don haka ta yarda zata dauki Allah ya isan Halimah ta kai Uban ga ‘yar sa, in ya so daga baya ta nemi gafarar ta.
Sun shirya tafiyar ne dukkan su familyn har Baffa Modibbo da Goggo Iyami, don dai su cikawa Halima ido ta amshi mahaifin ta. Salim ya ce “wannan family matter ne don haka ba zai bi su ba, ya kaisu filin jirgi ya sanya su a jirgi mai zuwa Kano. Sannan ya koma bakin aikin sa.
Suna sauka Kano Hanan ta kira His Excellency (yadda take kiran Hashim) ta gaya masa suna filin jirgi itada su Baffa ya aiko a tafi dasu. Bata gaya masa yau har da Daddy-Professor suke tafe ba.
Nan da nan kuwa sai ga motar gidan gwamnati irin doguwar civilian dinnan, ta zo ta kwashe su zuwa Governmnt House.
Tun daga bakin get na farko da shirgin sojoji masu bakin kaya da bindigogi suka tare su zasu yi bincike suka samu waya daga ofishin cikin gida kan cewa bakin na ‘Her Excellency’ ne kuma bisa iznin mai girma gwamna kada a bincike su.
Daddy baya komai sai sharar hawaye, ya daga kai yana kallon duniyar da Halimah ke ciki, her humble abode, kuma duk wadannan matakan tsaron don kare lafiyar ta ne data ‘ya’yan ta da mijin ta. Lallai Allah baShi da abokin tarayyah! Kuma shine mai daukakawa da kaskantawa da azurtawa da talautawa a lokacin da ya so, ba dai mutum dan adam ba!!!
Imanin sa ya karu a yau, taqawa ta kara dabaibaye shi.


Please Login or Register in order to submit comment