dan ni a ganina ban yarda ba ka zauna a Haka, the world is changing Mata sun fantsama cikin business Dan Haka kema ya kamata a dama dake, ya kamata ki duba kiga me Zaki iya Yi, be an independent Lady, saboda BAHAUSHE yace " Me kwadayi shi yasan gidan me rowa" idan kin nema na kanki bazaki saka Rai a kayan wani ba.
Washegari wajen goma na Gama shiryawa cikin wani cotton and soft material kalan light purple dinkin skirt da riga, na daure gashina da ribbon na nannade shi, na dakko cleanser ta na goge fuskata sosae sannan na goge fuskar da face wipes sannan na shafa powder nasa kwalli, fuskata Banda sheki Babu abinda take, Anna na yawan cewa duk abinda nake samu a gyaran kaina take karewa, Kuma hakane saboda i always want to look good. Na daura dankwali, Ina jin Nuzla na cemin gayu ma a gurin ki ya Kare, Dan duk wani sabon trend na dauri ko wani Abu na iya, kafin ya baza gari se nayi yadda nayi na koya, na Gama shiryawa sannan na zura takalma na fito, Anna na zaune a kitchen tana girki, tace da kanta take son girki Wai mu huta tunda ba zata fita ba. Ina shigowa ta dubeni da murmushi a fuskar ta tace
" Mashaaa Allah! Adda kinyi kyau"
Nayi murmushi Nima nace
" Nagode Anna"
Purse dinta ta janyo ta bani 500 na saka jakata ban manta Yi Mata godiya ba, ta bani tsaraba akan na Kai gidan su Zuhra Kuma kada nayi dare. Ban Jima ba na samu napep mukai ciniki ya kaini har kofar gidan, tunda muka Shiga unguwar nasan na masu dashi ne, gidaje kankararru ga Kuma shiru baka m ganin wulgawar mutane, na sauka na sallame shi sannan na Isa gate din nayi knocking a hankali, security ya bude yana kallona kasa da sama yace
" Gurin wa Kika zo?"
Na gaishe shi sannan na fada Masa, se ya Kara tambaya ta ko Zuhra tasan da zuwana na girgiza masa Kai alamara a'a, se yace to na kirata, ni Kuma bana son hakan so nake kawai ta ganni, Amma se na Ciro wayata da niyyar kiranta, se naji honk a bayana, da sauri na matsa, Yaya Man ne shi da wani me yanayi da Saif sede daga gani ya girmi hatta Yaya Man din. Aka bude musu gate ya danna Kan motar ciki, me gadi ya mayar ya kulle, se Kuma ya buden yace
" Ki shigo inji oga Man"
Na saki ajiyar zuciya na shiga na samu Yana fada musu
" Akan wannan da kuke gani zaku iya fara takun saka da Zuhra, ku ganeta saboda next time"
Se Kuma Suka fara bani hakuru Wai Basu gane ni ba, to da sun sanni ne? Na ayyana a raina, karasawa nayi na gaida Yaya Man da Kuma na gefen shi, Yana murmushi yace
" Yau gidannan Babu Zama finally Unaisa tazo"
Wanda ke gefen busy with his phone yayi saurin dauke Kan shi daga wayar yace
" She's Unaisa?"
Ya fada yana kallona from head to toe, na tsani irin wannan kallon Amma a ganina ai duk waccan Yar hau din ce ta jamin, idan kana zuzuta Abu da zancen shi kowa zai so yaga abun. Tare muka Shiga har parlon da ya gaji da haduwa, Ina tsaye ya kwadawa wata Kira daga ganin yadda tazo kasan me aiki ce ya Bata umarnin ta raka ni wajen Zuhra. Na bi bayanta muka haura stairs nanma parlon Dana samu se da yayi putting na kasan to shame. Daki dake gefe ta kwankwasa sannan ta tura tace min ki shiga kilan Bata tashi ba ma. Na Mata godiya na wuce ciki, komai na dakin peach ne, it looks lovely, dakin yayi duhu saboda ko Ina a kulle yake se AC dake aiki Babu kakkautawa, na karasa gaban gadon inda ta kudundune na yaye tare da bubbuga gefen gadon, ta bude idonta se Kuma ta rufe, se ta Kara budewa kafin ya Mike a sukwane, ta rungume ni, se ta sake ni ta shige toilet. Nayi dariya na kunna Kwan dakin na ninke Mata duvet din na gyara gadon na zauna Ina fadawa Anna na samu gidan, ta bani sallahun na gaishe su na Kuma dawo da wuri. Bata Jima ba ta fito sanye da bath robe ta zauna gaban dressing mirror tana fadin
" Unaisa naji dadin zuwan ki, Wai Dan kwatancen da na Miki har kin gane kenan?"
Na Harare ta ta Gama shiryawa sannan ta ja hannuna muka fita,tana ta mini Hira tun Ina murmushi har na saki jiki mukai ta Hira,dakin Dada mukaje, kana kallon matar kasan bafullatana ce, kusan tsayin su daya da Anna, for some unknown reason se nake ganin kamar Anna, bawai Kama suke ba Amma kawai se nake ganin yanyain Anna a tare da ita. Tunda na shigo ta kafe idanun ta cikin nawa, har na tsugunna har kasa na gaishe ta, tana ta kallona Wanda yasa naji I'm uncomfortable itama ta amsa tana nuna min gefenta na zauna, tace
" Ina Maman ki? Yau dai Unaisa tazo mun huta da mita"
Nayi murmushi nace
" Tace a gaishe ku"
Ta danyi murmushi amma se Naga yanayin ta kamar tana cikin damuwa, ta dubi Zuhra tace muje mu gaida Abba. Muka Mike shi har yafi Dada Wasa da barkwanci, ya dinga min tambayoyi Ina amsawa sannan muka koma dakin Zuhra, ta kunna Mana kallo wani film da ban ma gane a wacce kasa bace, they're more of Chinese. Se tace min ai Koreans ne and I began to think yadda ake take gane su Bayan kusan duk Kamar su daya. Wasa Wasa kafin mu tashi a kallon Nima na fara gane su.
A parlon Dada muka je cin abinci, tana zaune tayi shiru da abinci a gabanta, se Yaya Man da wannan Dana gani. Muka zauna shi din yace ma Zuhra
" Finally yau munga Unaisa"
Nayi murmushi, ita Kuma tace
" Yaya Muhammad ka ganta kyakyawa ko? Wallahi tafi Ya bilkisu kyau"
Na zungure ta ta kalleni na Harare ta, shi Kuma se dariya yake, Bayan mun Gama lunch din Dada tace min
" Unaisa ku Yan wanne gari ne?"
Nace
" Masaya, Anna tace a Birnin kudu yake"
Dada ta gyara zamanta tace
" Baku taba zuwa ba"
Na danyi shiru Ina son tuna last da muka je, se na tuna time din da aka cewa Anna mu ba Yayan Baba bane,idanuna suka ciko da kwalla na danyi kasa da kaina nace
" An dade, bazan ma iya tunawa ba"
Se ta gyada kanta I was hoping kada ta Kara min wata tambayar Kuma, Amma se tace
" Dangin Maman ki fa?"
Na danyi shiru nace
" Anna Bata San iyayen ta ba, kawai dai akwai yayarta Inna Zulai a gurin ta tashi, se tace Wai kamar sunada wata yaya Kuma, I'm not sure yadda abin yake"
Ban taba maganar da wani ba Amma bansan me yasa nayi maganar da Dada ba, kawai naji ya kamata na Bata amsa, Bata Kara zancen ba Amma she looks disturbed, tace naje wajen Zuhra Dan daga ni se ita mukai maganar, na koma bayan laasar na koma na Mata sallama se tace min
" Inna Zulai din tana nan?"
Se na girgiza Kai nace
" Ta Jima da rasuwa"
Daga Haka ta bani Kaya sosae, Abba ya bada kudi a bani na dinga godiya se gida.
Dadas' POV
Bayan fitar Unaisa da tafiyar ta, Dada ta mike zuwa window Wanda yake katoto Yana Kuma baka damar hangar duk wani Abu Dake faruwa a parking space din gidan, a hankali Unaisa ke takawa, kana kallon ta kasan ta Kai shekarun Yan matanci, a hankali take tafiya me cikeda karsashi kuma, bayanta Zuhra Dake dariyar da Bata San me suke fada ba, jiyowar Unaisa da sakin murmushin ta yasa Dada matsanancoyar faduwar gaba, hakan ba zai taba yiwuwa ya Zama coincidence ba, Dole duk inda Unaisa ta fito ta hada iri da tsatson Inna, a hankali Unaisa ta shiga waving hannunta ma Zuhra se taga tamkar ranar da Inna ta juya tana daga Mata hannu bayan an kaita dakin ta, wannan tafiyar ita ce ta karshe daga ranar Babu labari Babu Kuma dawowar su, daki ta koma ta bude safe dinta Bayan ta Danna passcode ta Ciro wani karamin hoto Wanda ba se an fada maka ba dadewar tashi ta Isa, hoton ya kunshi Fulani guda biyu, wadda macen tamkar Unaisa ce a tsaye sede kasancewar ta hoton Fara ce yayinda Unaisa take baka, Haka Kuma se Dada da Abba cikin shiga ta alfarma, se wani a tsaye Wanda mahaifin Dada ne, da Kuma karamar yarinyar shekara takwas zuwa Tara. Ta jujjuya hoton ta cigaba da shafa fuskokin dake hoton musamman fuskar photocopy din Unaisa!
Unaisa is not free! Pay N300 to 3091721807 Aisha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
[5/14, 10:41 PM] Hauwa Galadima: *K*
Sunsan yadda Dada wasu lokutan Kam Jima ita daya a daki yasa Koda sukaga Bata fito ba Zuhra ma Bata neme taba, se wajen maghrib Zuhra ta fito bayan ta idar da sallah Dan zuwa Kama aiki a kitchen kamar yadda suka saba, tana Shiga ta Kai idanunta Kan stool din Dada ke Zama tana monitoring yadda ake hada abinci, taga wayam, ta dubi Baba ladi tace
" Dada Bata fito bane?"
Baba ladi tace
" Eh Amma tace Zaki zo ayi Dake"
Zuhra ta zauna har ishai aka Gama komai sannan ta nufi dakin Dada, Bata parlor se a bedroom ta sameta,
" Dada wani abu ya faru ne? Kinzo daki kin kwanta Kuma"
Ta Dan dago da fuskar ta me cikeda damuwa tace
" Babu komai, kiyi ma Abba setting table Zan shigo"
Ta danyi Jim kadan tana kokarin karantar Dadan Wanda fahimtar hakan yasa Dada tambayar ta ko Bata ji abinda ta fada Mata bane, se ta juya cikin damuwa tayi yadda tace Mata, tana cikin hadawa Abba ya shigo shi da Yaya Man da Kuma Yaya Muhammad, Faisal baya gari Yana Yola inda yake karatu.
" A'a auta Ina Dada ne?"
Muhammad ya fara tambaya Dan shidai seka tunanin Dan Dada ne, in har Yana Kano to tabbas daya daga cikin abinci uku da ake ci a Rana to a gidan Dada ne nashi, tun Mamaa na damuwa har ta zuba Masa idanu, a iya zuwan sa yasan wannan aikin Dada ne Bata Bari wani ya jerawa Abba abinci,
" Tana dakinta"
Abba da Bai Kai ga zama ba yace.
" Daki Kuma? Is she fine?"
Yaya Man Dake zaune yace
" Na sameta daki Bayan tafiyar Unaisa, she seems disturbed though nayi nayi tace ba koma"
Abba ya gyada Kai yace Zuhra ta kwashe kayan abincin zuwa bedroom din Dada, lokacin tana toilet har Zuhra ta Gama jera abincin, zata fita Dada ta fito ta kalli carpet din sannan tace
" Ina nace kikai abincin"
Abba Dake shigowa yace
" Ni nace a kawo nan"
Ba tace komai ba Zuhra ta fita shi Kuma ya karaso ciki Yana fadin
" Naga yau Jan aji ake min shi ne na kawo kaina"
Ya fada Yana dariya Wanda Dole ita ma yayi lightening mood dinta, seda Suka ci abinci sannan ya dubeta yace
" Me ya faru ? Wani Abu akai bayan fita ta?"
Ta girgiza Kai alamar Babu, sede ta kasa hada idanu dashi
Yace
" In six days zamuyi shekara talatin da aure, Zainab ko da hannu kike tafiya nasan kafar Dake Miki ciwo, ki fada min me ya faru?"
Tace
" Unaisa"
Se ya Dan kalleta da mamaki yace
" Me Unaisa tayi?"
Se tace
" Baka ganin kamar In Maharazu ce ta Haifa Unaisa? Abba kamar ta baci, Abba ni nasan Unaisa tsatson Innar maharazu ce"
Se yace Mata shima hakan ya gani tun a mota, to Amma yasan Allah ke halitta kuma Bai son ace yasa ta hopes dinta high shiyasa yake bincike. Nan Dada ta fada Masa yadda sukai da Unaisa yace zaiyi bincike.
Bayan laasar na karasa gida, da sallama dauke a bakina na Shiga, gidan shiru Babu kowa a tsakar gida hakan yasa na wuce inda muke aje containers din ruwa na daura alwala, dakin mu na wuce se na same su dukkan su a can, banma lura da tsohuwar Dake zaune gefen katifa ba, na gaida Anna sannan na amsa sannu da zuwan da suke min na zura hijab na tada sallah. Cikin sallar naji bakuwar murya na fadin
" Hassana da ace kinsan mahaifiyar ki da kin tabbatar da kamar da Unaisa ke Yi da ita. Allah me iko ai kamar tasu ta baci"
Anna tace
" Allah sarki! Ai tun tana karama idan Inna Zulai tazo Haka take fada, tace Kama suke sosae"
Matar tace
" Ai kamar ta baci hassanah, ko ku Baku Kama da ita kamar yadda take Kama da ita"
Lokacin na idar da sallah, na juyo na gaishe ta, fuskarta a sake ta amsa tana cemin nazo, Babu musu na karasa gurin ta, ta rike hannuna tana kallon Anna tace
" Duk sun girma mashaaa Allah!"
Anna tayi murmushi sannan tace min mamar babanmu ce, na tsura Mata idanu se Kuma Naga hakane fa ga Kamar su sosae ta bayyana. Na Kara gaishe da ita ban masan wazan tambaye ta ba. Se tace
" Hassana Babu Wanda ya tambayi Baban a cikin su"
Anna dake duba kayan da nuna Mata an bani daga gidan su Zuhra tace
"Eh saboda dama Basu Saba dashi ba, shiyasa"
Se tayi shiru, ni Kuma karfin halin ta nake gani, me ya kawo ta? Bayan shekara da shekaru se yau aka gadamar waiwayar mu kenan. Na mike na fita tsakar gida na shimfida tabarma, daya Bayan daya su Badi'a suka biyo ni, muka fara Hira kamar yadda muke, se itama Anna ta fito ta zauna damu tana sauraron dukkan abinda tace. Da daddare dukka munyi Shirin kwanciyar Anna tace na barwa Baba Fiddau katifata nazo dakin ta mu kwanta. Na shirya na dauka wayata da hijab Dina na musu sallama zuwa dakin Anna, already ta kwanta Nima na kwanta gefenta, Bayan na Gama addua nace
" Anna Wai me tazo Yi?"
Ta danyi murmushi da naji sautin shi tunda duhu ya mamaye dakin tace
" Wai tazo ta ganku ne"
Nace
" Uhmmm! Kuma se yau? Kinga Anna idan Kika Basu fuska zasu ta zuwa ne, zasu manta duk abinda Suka Miki"
Tayi dariya batace Dani komai ba, Nima se ban Kara cewa komai ba na lumshe idanuna a Haka bacci ya daukeni. Washegari Babu makaranta Babu me fita se bamu tashi da wuri ba se wajen goma, ni na fara tashi na fito tsakar gida, seda na tsorata da farko, tana zaune ta zabga tagumi hannun ta rike da casbaha da ba lallai tasan me take ja ba.
" Ina kwana?"
Ta saki murmushi tace
" A'a takwara kin fito?"
Se na fahimci Nuzla take nufi, na gyada Mata Kai na wuce toilet nayi wanka sannan na shirya lokacin kowa ya tashi,kaida se mun gyara gida munyi wanka sannan zamuyi breakfast, Anna ba ta Hana ba tace muyi yadda muka Saba, muka gyara gida kowa da aikin shi, Ina jin Badi'a da Nuzla na fadin
" Kalli yadda take Hamma kamar zata cinye mutane'
Badi'a Dake wanke mopper tace
" Kinsan a kauye 6am anyi breakfast Dole ai taji Yunwa"
Na danyi gyaran murya Dan su San Ina jin su, Nuzla ta kalleni tana dariya na girgiza musu Kai alamar su daina, se Sha daya na Gama breakfast muka baje kowa Yana cin abinci, ta dubi Anna tana fadin
" Hassana Haka kuke cin abincin safe da Rana tsaka? Ina ai Banga gurin Zama ba"
Badi'a tace
" Dan Allah Baba ki zauna ya Zaki tafi"
Na saki Baki Ina kallon makirar yarinyar nan, Basu Jima da Gama gulmar baiwar Allah nan ba"
Nuzla cikin turanci tace
" Badi'a what's this? Abeg allow this old woman to leave"
Anna ta Harare su, da gaske muna Gama Breakfast ta dauki Kaya muka Taya ta se bakin titi ta samu napep sannan ta tafi, da muka dawo Anna ta cemin gashi cikin ruwan sanyi anyi maganin ta, munafurci ya kawo ta tazo taga halin da muke ciki, Kuma tazo taga a yadda muke, wani me kudin Bai Isa fada Mana Jin dadin rayuwa ba.
Bayan sati daya Shirin tafiya hadejia kawai nake, duk abinda ya kamata Anna na siya min a hankali kafin lokacin tafiyar yayi. Kudin registration shima ta aje min tun da naci pre test, saboda kada nazo tafiya a samu matsala. Har na kwanta wayata ta fara ringing nasan Zuhra ce Dan ita daya nake anticipating Kira daga gare ta. Ina dubawa Naga ita dince kuwan, na dauka ina fadin
" Zuhra"
Ta amsa muka gaisa Amma se naji yanayin excitement din dake cikin muryar ta a Koda yaushe Babu shi. Na tashi na zauna nace
" Zuhra akwai wani abun ne? Naji muryar ki kasa kasa"
Ta danyi shiru se tace
" Dama Dada ce, tunda Kika tafi to gata nan dai dukka Bata Jin Dadi"
Nace cikin rashin jin Dadi
" Subhannallah! Me ya faru?"
" Wallahi Kinga tambayar ki zanyi, Anna tana da wata Yar uwa da Bata sani ba?"
Nayi shiru Ina tunani Dan ni a yadda na sani Anna Inna Zulai ce kawai Yar uwarta Bata taba Mana zancen wasu ba, nace
" Wallahi bansani ba Zuhra, just tell me me ya faru ne?"
Ta saki ajiyar zuciya me nauyi tace
" Ita Dada Fulani ne, to Kuma irin masu yawo dinnan ne Dan ita tace bata masan asalin garin su ba, tasan tana da Yaya namiji tun suna Yara ya tafi karatu, se kanwar ta Zulai Wai, to suna yawon sukazo Jahun, kinsan Abba Dan Jahun ne. Se baban shi kakan mu kenan se ya ganta se yace ya kamawa Abba, kafin su tafi akai aure su Kuma suka Kara gaba. To Kuma Basu Kara dawowa ba, Bata San inda suke ba ko sauran Yan uwan nata ba, tunda ita bayan auren Abba zai tafi karatu England ya tafi da ita acan tayi karatu"
Se naji ai irin labarin Inna Zulai ne, ga Kuma sunan Inna Zulai ya fito, nace
" Allah sarki Dada, to yanzun me ya faru?"
Tace
" Bayan kinzo kunyi magana kin tafi tace wallahi kamar ku daya da Babar ta, Kuma kema kinyi maganar Inna Zulai ai"
Nace
" Zuhra ki cewa Dada tazo ta samu Anna suyi magana, it can't be a coincidence all this, tunda ance da kakata maman Anna nake Kama, ga Inna Zulai"
Ta saki ajiyar zuciya cikin jin Dadi tace
" Allah yasa hakanne, I can't wait duk hankalin mu a tashe yake, duk ta damu"
Nace
" Ai dole, yanzun Zan cewa Anna kawai Dada zata zo, idan sunzo se suyi maganar"
Da wannan mukai sallama, naji Dadi na Kuma Yi adduar Allah yasa hakan ya kasance da naji dadin gaske, Dan Ina son Nima Naga munada Yan uwa. Aikuwa washegari na fadawa Anna cewar Dada zata zo, tayi niyyar fita clearing kayan ta da Suka iso Amma se ta Bari, mukai girki sosae na tarbar ta. Karfe daya Suka iso itada Yaya Man da Zuhra, har waje naje na taro su, tana ganina ta rungume ni se nake Kara ganin yanayin Anna a tare da ita, wallahi har jikin su iri daya ne. Tare muka shigo har Yaya Man da da farko yaki seda Dada tace ya shigo kafin ya shigo, Anna ta fito ta tarbesu, Ina ganin kallon da sukewa juna. Zuhra na tama Anna surutu itama tana biye mata se can muka Basu guri Dan suyi magana. Dada ta dubi Anna tace
" Maman Unaisa bansan ta Ina Zan fara ba, Amma dai Bari ki gani"
Ta fada tana Ciro wani tsohon hoto daga jakar ta, Anna ta karba ta tsirawa hoton idanu kafin Kuma tayi saurin mikewa ta nufi bedroom dinta ba tareda tace komai ba, Amma yadda take tafiya tana hardewa shows she's nervous, ba jimawa se gata ta dawo da irin hoton itama, ta mikawa Dada, Dada ta karba tace
" Ke kanwa tace Maman Unaisa, ke jini na ce, Ina Zulai?"
Anna se hawaye Shar a fuskarta tace
" Inna Zulai ta rasu, Yaya hafsatu Ashe kina da rai, Ashe kina nan? Har ta rasu duk lokacin da zamuyi magana da ita se ta tambaye ni ko na hadu dake? Allah me iko Ashe kina kusa"
Dada tana kuka tana jajanta rasuwar Yar uwarta, hoton anyi shi ne ranar bikin Dada, a hoton akwai Dada, Inna Zulai da Kuma mahaifiyar su Anna. Seda Suka daina kukan se Kuma Hira ta barke, ita Dada Bata masan an haife Anna ba, ba Kuma tasan rasuwar iyayen ta ba, wayar ta ta dakko ta Kira Abba ta fada masa labari me dadi, Yaya Man na zaune se ya Kira mu muka zauna, nace
" Amma Anna Baki taba fada Mana cewar kina Neman Yan uwanki ba"
Tayi murmushi tace
" Unaisa kenan"
Dada ta hada mu mu hudun ta rungume mu Jin irin wahalar da muka sha, har seda ta saka ni kuka se nake jin abin banbarakwai, Wai yau ni ce na samu wata matsayin yayar mahaifiya ta. Basu tafi ba se bayan sallar ishai, Yaya Man ne ma ya fita da Hunainah da Badi'a da Nuzla, mu Kuma Muna daki Hira. Dukka muka rakasu akan zasu saka Rana suje Masaya Dan Dole aje aga yaran Inna Zulai dukda sun watsar da Anna Suma.
Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels