Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
Dole ranta ya baci" Daga Haka na tsaya nayi alwala Ina Shiga naji tana ma Nuzla fadan sun Bata Mata gida,su kamar ba Mata ba Basu San yadda zasu gyara gida ba. Nidai na tada sallah sannan na idar na fita tsakar gida muka hadu da Nuzla muka gyara gidan tas sannan ta zubo Mana abinci, Anna na daki na bita nace " Anna kizo kici abinci, kiyi hakuri an gyara gidan" Ta Gama saka top din dake hannunta tace " Yanzun fisabillilahi Adda ya kamata ace sun bar gidannan kacakaca Haka Kamar bola?" Nace " Kiyi hakuri ba zata Kara ba" " Wannan me kunnen kashin zata ji ne" Haka na lallaba ta mukaje muka ci abinci sannan muka zauna Hira. Haka rayuwan yake tafiya har aka Kira mu zuwa pretest a danbatta. Wannan karon ni kadai naje nayi sannan na dawo. Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258. [5/11, 9:05 PM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕 *H* Ayshatuuu *Have you paid for Unaisa? If no then hurry and do so as we only have two pages to take down the free pages. Thank you for the patronage.* Bayan sati biyu ranar asabar na shirya tafiya zuwa hadejia, Dan yin exams dina. Tun dare Anna ta sallameni da komai Nima na hada komai da zanyi amfani dashi. Hatta kayan da Zan saka seda na dakko Dan Haka da sassafe Ina tashi nayi wanka sannan na dakko atamfa red me adon spring sea green da purple. Seda na shafa powder nasa khol fuskar nan tawa smooth saboda yadda nake kula da ita bana son ko Abu daya ya taba ta, kurji daya idan ya fito min se na tadawa kowa hankali da korafi, shiaysa nake maintaining jikina musamman fuskata. Na shafa balm Wanda yasa lebena kyalli na yafa veil na zura flat shoes Dina na dauka folder se jaka. Anna na kokarin fito damu Koda kayan mu basuda tsada Amma tana iyakar kokarin ta akan mu, shiyasa ba zaka taba ganin alamar ko muna cikin wahala ba, balle yanzun ma Babu wata wahala da muke Sha, Anna na samu sosae se godiyar Allah. Seda ta rakani Tasha na hau mota sannan na ta koma gida, shi ne lokacin farko da nayi tafiya me tsawo ni daya Dan Haka duk bayan mintina ashirin se ta Kira taji Ina Ina, gashi ni bansan hanya ba se tace na tambayi driver din mana, tun Yana fada min har yace Wai na ishe shi Haka. Wani Dake gefena yasha kufta ya kafa hula zanna bukar ya dubeni Yana murmushi yace " Alama baki taba tafiya ke kadai ba ko?" Na Dan Bata fuska tare da gyada Kai na, yayi murmushi yace " Dama kyawawa irin ku ai treasure ne" Wannan karon ban kula shi ba, na saukar da kaina Ina Kara haddace formulas din physics. Muna zuwa hadejia aka sauke ni a Tasha, shima gayen ya sauka ya dubeni Ina kokarin matsawa gefe yace " Ina zakije?" Na Dan yi shiru se Kuma nace " School of nursing zanje" Ya gyada kan shi sannan ya samar min napep, bayan na Shiga ciki shima ya shigo ya zauna gefena, duk surutun da yakeyi ko uffan bance Masa ba Amma shi din Bai gajiya, he's so annoying na ayyana a raina. Har gate din school Suka kaini, na sauka Ina Nemo Masa kudi yace ai na bayan ya biya, na kalleshi nace " Nagode Allah ya saka da alkhairi!" Ya gyada Kai ya min waving tareda bani card yace na kirashi. Na gyada Kai Suka wuce ni Kuma na nufi cikin makaranta, banma tsaya wani duba card din ba na wullar dashi cikin katon drum din shara. Screening aka farayi se venue aka bani na exams din, ana bani questions dina na fara Babu Wasa. Tun Ina cikin exams din Naga alamar hadari ya hado, sede is More of iska than hadarin ruwa, gashi duka garin ya daure yayi dum Babu dadi yanayin. Se na fara attishawa da Dan karamin tari, a Haka na Gama nayi submitting sannan na fito, Amma se naji kirjina yayi min nauyi har numfashina suna ciccikowa, ga gajiya ga Kuma Yunwa, ga fargaban hadarin dake hadowa, kafin wani lokaci duk na gaji Amma a Haka na cigaba da tafiya zuwa gate, Ina zuwa mutane anata tafiya ga motoci na lodin garuruwa, na nufi inda naji ta Kano Dan shiga na tafi se naji an dafa ni, nayi saurin juyowa se Naga wannan Zahra din, tana min murmushi tace " Yayar Hunainah!" Nayi murmushi Nima nace " Zahra ko?" Ta Dan Bata Rai tace " Gaskiya I'm hurt! Kin manta sunana?" Na rufe fuskata da hannayena nace " I'm sorry! Tuna min Dan Allah" Taja hannuna tace " Sunana Zuhra Ismail, nazo nan pre test. I just hope kema Haka?" Na daga Mata folder nace " Of course! I'm Unaisa Yahya" Ta danyi Jim tace " Usaina?" Na girgiza Kai nace " UNAISA! Unaisa" " I've never heard of your name fa" Nayi dariya a hankali nace " Nima ni kadai na sani me sunan" Ta kamo hannuna tace " Wuce muje Yaya Man na jira mu tafi, har na shiga mota yace min wai kalla wata kyakyawa, shi ne na dago se kawai na ganki." Na danyi murmushi nace " Wai kyakyawa" Tayi dariya tace min ai ita ta Jima Bata ga me kyau Irina ba, inata dariya na Ciro wayata daidai lokacin da take cewa " Kizo mu tafi Mana" Na nuna Mata wayata nace " Zan Kira Anna na fada Mata" " Wacece Anna? Your Mom?" Na gyada Kai Ina Kara wayar tawa a kunnena, Anna ta dauka tana fadin " Adda kin gama?" Kafin nayi magana ta kwace wayar a hannuna ta Kara a kunnenta tana fadin " Anna Ina wuni? Sunana Zuhra, kin tuna min hadu daku a mota wancan month din?" Banji me Anna tace ba Amma daga Murmushin da Zuhra keyi nasan ta samu, " Yawwa Anna zamu taho da ita, na Miki alkawarin har gida zamu kawo ta nida Yaya Man" Inata kallon ta Ina ayyana bazan iya abinda tayi ba, I'm not friendly sosae, ni din ban fiye sakin jiki sosae da mutane ba, shiyasa ko a secondary banyi kawaye ba, Babu wata wadda zatace ita din kawata ce shakikiya, karatu kawai nakeyi tunda shi aka kaini nayi. Shiyasa Anna kullum na yimin fadan na dinga sakin jiki da mutane, kalli yadda ta saki jiki da dai zakai tunanin ni da ita munsan juna ko Kuma irin mu Saba dinnan sosae, ta saki jiki sosae damu. " To Anna nagode se nazo " Haka ta Miko min wayar ta ja hannuna muka nufi wata Ash din Benz, Kai ba se an fada maka ba, kana kallon kayanta kana kallon ta kasan Yar masu kudi ce. Kuma kana kallo kasan arziki a cikin shi ta tashi, Dan kuwa Wanda ya tashi cikin arziki ya jiku dashi zakaga bashi da girman Kai Amma Dan talaka se karya da hura hanci. Su biyu ne a motar dukkan su a gaban mota, daya Yana sanye da black trouser da Ash top, fuskarshi sanye da brown shades, dayan Kuma clad in Ash shadda se maiko takeyi, Kan shi Babu hula Amma Kuma tana aje Akan dashboard din motar. Ina Zama na gaishe su dukda a dadare nake, Suka amsa " Wannan shi ne Yaya Man, he's Yaya Suleiman" Na danyi murmushi nace " Sannu Yaya Man" Ya juyo tare da cire shades din fuskar shi yace " Sannu! Ya exams din?" Nace alhamdulillah sannan ta dubi dayan tace " He's Yaya Saif, shi nake bi" Nayi murmushi na gaishe shi sannan muka dauka hanya, sunata Hira Kuma duk ciki se ta saka ni a ciki Dan na ware Amma still nayi shiru Ina jin numfashi na Bai Gama daidaita ba. Seda muka shiga Kano nayi Masa kwatance har kofar gida, na dubi Zuhra nace "Zuhra nagode sosae, ku gaida Mama. Yaya Man nagode" Wani kallo tayimin tace " Tare zamu je, se na gaida Anna ai. Yaya Man just five minutes" Saif ya dubeta yace " Wallahi zamu tafi mu barki banza uwar shishiggi" Ta bata Rai Amma taki sakin hannuna tace " Yaya Saif Babu ruwanka! Yaya Man Bari na Shiga na fito" Bata ma jira su ba su amsa Mata ba ta bude muka fice, da sallama muka shiga ciki, dukka suna zaune Anna na buga lissafi cikin karamin littafi yayinda Nuzla ke dama fura. Da murmushi Anna ta tare mu, Zuhra ta rungume Hunainah bayan ta gaida Anna, tace " Hunainah kin tuna ni?" Ta girgiza Kai tana tsotsan alewa, Zuhra ta dubi Anna tace " Anna Kinga Bata gane ni ba Wai" Anna tayi dariya tace " Ai halin Unaisa ne da ita, zauna Kisha fura" Ta kalli Nuzla tace " A'a jirana ake Anna, Zan dai dawo na yini" Anna ta tada Nuzla ta dakko jug ta juye Mata furar ta kulle a bakar Leda sannan aka dakko flask an soya awara nasan saboda ni ne, ba karamin so nake yiwa awara ba, tayi Murmushin jin dadi tace " Anna nagode Ina son awara wallahi. Kai Anna nagode" Anna tace " Banda abinki Zuhra wa kikaga Yana yiwa uwarshi godiya" Ta mike na rike flask din ita Kuma ta rike jug din furar, Nuzla da Badi'a Suka biyo bayan mu har mota muka rakata mukai exchanging contact ta wuce na dawo gida. Se lokacin na zauna na mimmike kafa nace " Anna Kinga tana da kirki ko?" Nuzla tace " Wallahi ni na fara sonta, she's very wise kiga kamar ta Dade da sanin mu" Anna tayi murmushi tace " Dama hakane ai, Allah ya Mata albarka daku Baki daya. Adda oya kici abinci" Na bude flask din na zauna naci sosae sannan nayi wanka nazo mukai ta Hira. Se dare sannan Anna tace min na Kira zuhra naji yadda taje gida, na dauki wayata nayi dialing number dinta bugu daya ta dauka " Unaisa! Yanzun nake bawa Dada da Abba labarin ki, shi Abba ya manta ki Wai" Nayi murmushi nace " Zuhra kenan! Ta Yaya zai tuna Dani. Come-on ya kikaje gida" Karshe dai seda ta kaiwa har Abban ta muka gaisa dashi Haka ma mahaifiyar ta Dada. Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 First Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258 [5/12, 10:10 PM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕 *I* Ayshatuuu Lokuta da dama mukan dauka cewar choice din mu ne haduwa da mutane, Amma idan muka nutsu mukai tsam da ranmu zamu gane cewar komai a rayuwar Dan Adam is destined, it's written. Kuma dukkan Wanda aka hadu dashi akwai manufa da Kuma hikimar hakan. Haduwata da Zuhra na dauka kawai choice Dina ne da na kulata har ta Zama kawata, Amma Bayan lokaci me tsawo se na fahimci through her akwai abubuwa da Allah ya tsara Wanda ni ban sani ba. Zuhra mutuniyar arziki ce. Bayan Anna ita ce mutum ta farko da na fara bude Baki na Kira da kawata, duk da halayen mu by far sun banbanta nesa ba kusa ba, ita din mutum ce carefree and friendly yayinda nake akasin hakan, ni mutum ce me wahalar sabo kamar inada kin yarda, ko Kuma Ina tsoron been attached to someone Kuma ya tafi ya barni. Kullum Rana idan na tashi to se Zuhra ta kirani Wai kawai taji yadda nake, sede nayi dariya kawai nace ai lafiyata kalau, wani lokacin Kuma idan ta Kira se ta ce min wai banji komai ba Akan exams dinmu, har ranar nace ta jira Zan Kira Yaya Yusuf na tambaye shi, ko Dana Kira shi se yace min ai Yana Hanya zai zo gidan. Dan Haka na fito na fadawa Anna, ta dubeni tace " Ni Wai meye ne tsakanin ki da Yusuf din Anty Nanah ne?" Na bude Baki da mamaki nace " Anna menene tsakanin mu kuwa? Kawai na Kira shi naji maganar makaranta ne saboda Zuhra ta takura" Ta nuna min gefenta alamar na zauna, na samu guri na zauna gabana nata faduwa, tace " Unaisa ba takura muku nake ba, Amma kinsan yadda komai ya kasance a rayuwar ku, Ina son ki manta da zancen wasu samari ki maida hankalin ki kiyi karatu, lokacin aure zaizo, lokacin da zakiyi samari Yana nan zuwa. Ni ki kalleni shekara ta Sha biyar akai min aure ko yadda zanyi sallah daidai ban Gama sani ba, ki kalla irin abinda na tsinta a aure me naci riba, Dan haka kudinnan komai da nake jurewa saboda kune, ki daure kuyi karatu kinji Adda?" Na gyada Kai na Ina goge hawayen fuskata da tuni na fara kuka nace " Allah Anna ki yadda Dani Babu wani Abu tsakanina dashi, ban taba tsayawa da wani..." Tayi saurin katse min rantse rantsen da nakeyi tace " Na sani Adda, kawai dai Ina tuna miki ne. Kin gama girkim?" Na girgiza Kai tace to naje na karasa, na Mike da sauri na fita kamar Zan kifa, na shiga kitchen na karasa stew din sannan na jujjuye na gyara kitchen din. Ina gamawa Badi'a da Hunainah na shigowa, na dube su duk sun gaji nace " Sannun ku, kuje ku cire uniform kuzo kuci abinci" Badi'a ta saki murmushi tace " Kai wallahi Adda kamar kinsan Yunwa nakeji" Hunainah ta tsaya tana hura hanci tana tambayata abinda aka dafa, nace ta wuce ta bani guri, ta tafi tana bubbuga kafar ta. Babu jimawa se gasu sun fito daidai shigowar Nuzla, Dake Shirin fara waec, shiyasa take dawowa daban da kowa. Ta dubeni " Adda an Gama abinci" Anna dake fitowa daga bedroom tace " Haka dai kullum kamar kamun Yunwa" Tayi dariya ta wuce ciki, tray na dakko na hada Mana dukka Dan yawanci tare muke cin abinci, dukka tare muka zauna muka fara cin abinci, Bayan mun Gama Anna ta zauna tana bamu labarin yarintar Nuzla dukda wani abun na sani, tunda Zan iya tuna yarintarmu tare, Muna ta Mata dariya ita Kuma ta hade Rai tana fadin " Allah Anna so kike Badi'a ta dinga tsokanata ko" Anna ta dubi Badi'a wadda har ciki take rikewa saboda dariya tace " Kayya ba gwara kowa akan nata ba, ita me kukan Madara ma" Ai fa se muka fara dariya, ta mike ta dauke tray din, Anna tayi dariya tana binmu da kallo me cikeda farin ciki da kauna, wannan matar ladan ta a gurin Allah ne shi daya, tunda Baba ya saka kafafun shi ya tafi Bai Kara waiwayar mu ba Haka muma ko da Wasa bamu sake maganar shi ba, ni ce ma lokaci zuwa lokaci nakan tuna dashi bawai Dan ya dawo ba a'a se Dan mamakin karfi Hali irin nashi da nake da Bai taba juyowa ko ba Dan Anna ba danmu Yayan shi, gaba daya rayuwar nan se a hankali se yasa nake Kara tsoron attachment a rayuwata. Se dare sannan Yaya Yusuf yazo, ya kawowa Anna scholarship din da ya samu zuwa Sudan Dan yin karatu, gaba daya muka taya shi murna anan yaci abincin dare sannan ya Kara nanata min nayi karatu da kyau Dan makarantar da zanje kora suke Babu ruwan shi. Bayan sati daya Ina zaune Ina saka wani set din kayan sanyi na babies da aka kawo daga makwabtan mu danta ya haihu suna hada kayan barka, na Gama saka riga da wandon da hula, se shawl din da socks kawai suka rage, Badi'a na gefe tana hada hulunan da Nuzla tayi, Hunainah Kuma ta fita da Anna se Nuzla na girki. Kamar daga sama se Jin sallamar Zuhra nayi, na aje knitting pin din Ina mikewa se kuwa gata ta shigo, na saki murmushi Ina jin Dadi, ta shigo ta zauna tana fadin " Wallahi wayarki batada amfani, kinsan irin Kiran da na dinga Yi Miki kuwa?" Na dubi Badi'a Dake gaisar da Zuhra nace " Badi'a Ina wayata?" Ta mike nace da Zuhra " Ayya ai bansani ba tun dazun ta dauka sannu da zuwa, sannu Ina Dada da Abba?" Ta gyara zamanta tace " Duk suna lafiya suna gaishe ki, Ina Anna? Ko Dan tace min taje unguwa ko?" Na gyada Mata Kai, Sega Nuzla tazo suka gaisa ta kawo Mata ruwa sannan ta Bata hakuri Akan an kusa Gama abinci, murmushi kawai tayi muka cigaba da Hira, tace " Wai duk sakar nan ke kikayi? Gaskiya you got talent Babu abinda na iya se surutu" Aikuwa na kwashe da dariya jin tayi admitting cewar ita din me zance ce, ta Ciro wayatta tace Wai albishir tazo tayi min, na aje pin din na karba dogon list ne na Wanda sukai nasarar cin entrance exam din da mukai, na saki hamdala ganin sunanta sannan na tafi lalubar nawa se kuwa gashi, na rungume ta Ina fadin " Alhamdulillah Zuhra we made it!" Ta gyada min Kai tana dariya tace " Kinga da Abba yace na Bari kawai naje Nile University nayi BSC acan saboda can Aseey zataje" Se naji banji dadi ba, na aje wayar Ina sauraren ta " Amma nace ni fa can hadejia zanje gaskiya, na riga na hadu dake" Se nayi murmushi nace " To me Abba yace?" Ta yaye veil dinta ta aje can gefe tace " Ya yadda of course, Aseey zata wuce wani satin ita" Na gyada Kai dukda bansan wacece Aseey din ba, ban Kuma tambaya ba. Nan muka ta Hira har Ina mamakin kaina sannan muka ci abinci, se yamma Anna ta dawo da dealolin gwanjo da aka Aiko Mata, me napep din ya shigo dasu, ta zauna a gajiye Zuhra ta kawo Mata ruwa tana Mata sannu da zuwa, seda ta nutsu sannan ta fada Mata cewar ai munyi making exams dinmu, ba karamin Dadi taji ba. Tana zaune aka bude dealer farko wadda duk blazers ne, skirts da Kuma tops, muka Taya Anna ta shirya su se yamma sannan aka kirata akan anzo daukar ta, ta dubeni Bayan ta tashi tace " Ina jiran ki kizo kema" Na dubi Anna da tayi murmushi tace " Zata zo Inshallah" Da idanu Anna ta nuna min ledar ta ware Kaya ta min alamar na bita dashi, na dauka muka fito muka tarar da Yaya Saif ne yazo tafiya da ita, muka gaisa dashi sannan mukai waving juna bayan na wulla Mata ledar a backseat nace inji Anna, nayi ta dariyar hararar da take min na Zan Kama ki dinnan. Seda taje gida taga kayan sannan ta kirani tana ta godiya ta Kira Anna na. Rana daya akai Mana fixing ranar da zamuje interview, tun dare kamar yadda na Saba idan zanyi tafiya na hada kayana har credentials Dina, washegari da wurwuri nayi wanka na shirya cikin Ash din atamfa me design din pink a jiki, dinkin skirt da riga, ban daura dankwalin ba se na saka hula Dan hijab nake son sakawa, awara na.soya na hada sauce na Kuma juye cikin flask sannan na dawo Kan fuskata, nayi scrubbing na wanke ta tas se glowing take sannan na shafa Mai da powder, nasa kwalli na gyara gashin kaina da Kuma na gira, na duba madubi Naga I'm good to go! Ina saka hijabi na Se naji sallamar ta, ta shigo sanye da bakar Abaya me wasu sparkling stones, ta rufe kanta da veil din, "Bari na gaida Anna nazo mu tafi" Anna ta fito.da sauran yaran Dake midterm break, Suka gaisa sannan muka wuce, wannan karon driver ne muka gaisa dashi sannan muka dauki Hanyar hadejia. Muna zuwa ana farawa, se wajen Sha biyu aka Kira sunana, na gyara zaman hijab dina, na dauka file case Dina na shiga, kowannen su a zaune, wasu sun manyanta yayinda wasu suke a young age din su, na gaishe su aka min tayin kujera na zauna, na Mika musu takaddu na kamar yadda suka bukata, wasu na going through yayinda wasu Kuma ke jefo min tambaya. Ina ta amsawa se a karshe suka tattaro min takaddu na Suka ce naje, Haka na juya da karfin gwiwa ta na fito bayan na musu godiya. Se bayan azahar Zuhra ta shiga Tana fitowa mukai sallah muka tafi mota muka ci abinci sannan muka dakko Hanyar dawowa gida. Duk yadda muka kwaso gajiya Bai hanata shigowa ta gaida Anna ba, dama tun a hanya take min korafin ni naki zuwa na gaida Dada, a gidan su kullum se anyi Mata dariyar har yanzun ban zo ba. Na danyi dariya nace " Zan zo fa" Tace " Se yaushe?" Na danyi shiru kafin nace " Zan kiraki idan zanzo" Se ta gayda Kai ta fara rubuta min address din cikin note din wayata, tun a hanyan take bani labarin su " Mu Yan Jahun ne, Abba engineer ne ita Kuma Dada accounting tayi, tana aiki itama, Yaya Man shi ne babba se Yaya khulthum ita tayi aure da wani cousin din mu, se Yaya Faisal se ni" Nace " Wow auta! To wannan da kuke video call dazun fa?" Tace " Oh! Yaya Ahmad he's a cousin. Baban shi yayan Abba ne Abiey. He's my favorite cousin" " Dada fa? Ita Yar Ina ce somehow kina min Kama da Fulani" Tayi dariya tace " Abin mamaki Dada bata San asalin garin su ba, kinsan kakkani na are very funny, Wai kawai sunzo wucewa Suka yada zango garin su Abba suka bada auren ta, guess what Basu Kara dawowa ba" Na bude idanuna see a similar story to that of Anna, nayi dariya Nima nace " Haka family Anna sukai, ba fulanin daji bane? Ai su dai se su" Muka hadu muka saka dangin Anna da dangin Dada da duk sauran fulani a tray muka tsuye su, not minding mu dinma fulanin ne, nakan ayyana dama Zan iya Dana fada Mata namu labarin Amma bazan iya ba, na cika zurfin ciki da rashin yarda. Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258 [5/13, 2:49 PM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕 *J* Ayshatuuu *Last free page* Ban cika alkawarin da na daukawa Zuhra ba na cewar zanje gidan su, ni din bame yawan son fita bace balle Kuma har naje gidan su Zuhra da ko skin dinta ka kalla ba se an fada maka cewar ita din Yar masu kudi bace, kana kallon ta kasan hakan, to ni bana son na fiye shishigge mata sboda inada gudun wulakanci. Tun tana korafi har ta fahimci bazan je bane se kawai ta kyaleni, Amma Kuma Bata Kara zuwa gidan mu ba Haka Kuma ta daina Kirana Wanda hakan ba karamin abin mamaki bane, hakan sabon Hali ne data zo dashi, hatta Hunainah seda tayi jigiyar ta. Da yammaci Ina sanye da skirt da top na gwanjo, kaina a barbaje Ina tajewa Ina ta yatsina fuska saboda yadda ya Kara tauri, Dan tun asali Kan nawa tauri ne dashi, seda na Gama Ina jin kamar nayi ihu saboda dukan Kan ya daure hatta scalp din ciwon tazar yake. Na daura Leda a hannuna na fara diban home made hair mayonnaise, dukda warin man shanun dake bugata Bai dameni ba as long as kaina zaiyi laushi an wuce wurin, na Gama sawa tas hannuna har ya kage saboda yawan gashin, Anna ta fito lokacin Ina zura bakar Leda a Kan Dan ya Dan narke. Ta samu kujera ta zauna tana fadin " Har kin gama? Ai da kin sakawa Hunainah Dan itama irin gashin ki ne da ita" Na kalle ta tana zaune acan gefe tana Wasa nace " Seda nace tazo na saka Mata yarinyar nan ta gudu" Anna ta girgiza Kai kawai tana murmushi tace " Wai kin fasa zuwa wajen Zuhra dinne?" Na Dan yamutsa fuska nace " Ni fa kawai bana son zuwa,kada aga kamar kwadayi ne" Anna ta gyada kanta tace " Kinyi magana kema, Amma ya kamata kije say daya daga nan shi kenan. Zuhra ai mutum ce" Se na yadda Akan zanje washegari, na wanke kaima tas seda naji baya wari kwatakwata sannan na dauraye shi, wasu a gidajen su powder su ce ke saurin karewa yayinda mu a gidan mu shampoo dinmu ke fara karewa saboda yadda muke taadin shi da Kuma yanayin gashin mu. Comb na dauka da man kitso na daure Kan na tafi can wani gida Dan nesa da namu amarya ce Bata Jima da tarewa ba take wankin Kai da dasu stretching, na Jima a tsaye Ina kwankwasawa kafin tazo ta bude min, fuskar ta da murmushi tace " Nuzla sannu da zuwa!" Nayi murmushi saboda Nuzla tafi sani Dan tafi kowa zuwa, muka shiga cike se sannan nace ai yayar Nuzla ce, se tace min wallahi duk Kama muke Kuma sunana wahala yake Mata, nayi dariya kawai. Har stretching akai min sannan na biya ta na koma gida. Yadda Mata ke sanaa cikin gida a wañnan zamanin burgeni yake,

Chapter 4 of 5