Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
Babana, ban taba ganin ta saki jiki idan tana tare dashi, gashi ni yarinya ce me bin kwakwaffi, I observed kamar spy Haka nake. Akayi aure Anna da Baba, da farko se ya ajeta a masaya tayi wajen sati uku se ana hudu sannan ya tattara ta Suka dawo sauna. Anna Bata son shi yadda me karatu bazai dauka ba, a masaya sukance idan yazo zance se da itace me bakin wuta Inna Zulai ke korata, Kuma saboda sanin batada kowa se Inna yasa ta hakura ta aure shi. Bata fi watanni uku ba Sega ciki ya fito, gidan da take zaune gidan haya ne daki daya ya Kama ya biya kudin shekara biyu, cikin na wata biyar ya fara Shirin komawa saudia kamar yadda ya saba, da ya fada Mata se tace ita ta yadda ya maida ita masaya tunda nan Babu wani Dan uwa da take dashi. Yace shi baiyi niyya ba Kuma ita Bata Isa ta saka yayi hakan ba, Haka kuwan ya tafi ya barta anan, ko hanyar masaya ma Bata sani ba. Haka ya barta ya tafi wata uwa duniya. Guzurin da ya bar Mata Bai Kai lokacin haihuwa ta ba ya Kare, zuwa lokacin tayi sabo sosae da makwabta Dake Kuma ta iya sakar hannu se tunda tazo Bata zauna ba take saka, wannan kudin sakar take sakawa cikin banki a Haka har Allah yayi ta haihu. Wata makwabciyar dakinta dattijuwa ita ta zauna da ita har ta haifeni, kafin ya tafi ya fadawa makwabcin shi yadda zaayi a sanar a masaya cewar Anna ta haihu. Washegari kuwa se gasu sunzo yuya guda. Inna Zulai kamar ta Yi me saboda farin cikin haihuwata. Ranar suna aka saka min Unaisa kamar yadda yace Mata. Ragon suna da koami daga can Suka zo dashi. Kama nake sosae da Anna Amma Kuma fatata se tayi duhu irin ta mahaifina. Se ya kasance ni ce daban da sauran, Dan dukka kannena farare ne tas dasu. Bayan tayi arbain aka kaita Masaya ta kwana biyu sannan ta dawo, shiru Babu Baba Babu dalilin shi, kowa yasan kayan sanyi suna ci ne kawai lokacin sanyi sede idan kana da wani da kake bawa, hakan yasa ciniki ya tsaya cak, ta fara tunanin da me zata zauna wannan dattijuwa Baba Rakiya Anna na fadar ta, tana yawan cewa ita din ba karamar taka rawa tayi a cikin rayuwar ta ba. Ita ta fara koyawa Anna yadda zata tashi a tsaye, tace Mata tunda mijin baya nan bazaiyi ba to ita Anna ya kamata tasan yadda zatayi ta nema na kanta. Shi ne ta fara wankau, ka kawo kayan ka ta wanke maka se ka biyata, dashi zata yi cefane ta Adana wani. Idan ka kalleta se kasa Baki ka hureta saboda Rama, wahala da talauci. Haka tayi rayuwa har na shekara da rabi, lokacin kudin haya ya Kare kwatsam Sega Baba ya dawo, ku kalla wajen shekaru biyu. Ya siya kayan abinci, ya Kara biyan kudin haya baiyi ko wata ba ya Kara komawa, a wañnan Karan Bai dawo ba se Dana cika shekara uku lokacin Anna Sanaa take iri iri Dan ta biya min kudin makaranta, a cewar ta yadda batayi karatu ba, Bata San dadin karatu ba to nidin bazan Yi Haka ba. Wata private school cikin unguwa ta sakani tana biyan kudin. A Haka ya dawo shima kamo shi akai aka dawo dashi, to wannan shine yayi shekara daya Bai koma ba Yana hada kudin da zaiyi igama idan yaje. Kafin ya tafi Anna ta haifa Firdausi Nuzla. Ko arbain ba tayi ba Baba ya shura takalman sa ya koma. Ko zaman da yayi na shekara bana yarda dashi kamar ma tsoron shi nakeji, komai nawa Anna ce, ko nazo zanyi Mata magana muka hada idanu dashi to tabbasa na fasa maganar. Bayan ya shekara hudu ya sake dawowa, kuyi imagining duk wata wahala da bawa zai iya Sha, to Anna Tasha akan mu, ya maida ta tamkar Baby making machine, idan yazo Yana tafiya ciki zai bayyana. Bayan ya dawo min Kara girma ya Kara komawa ya Barta da ciki, shi ne aka Haifa Badi'a. Bai dawo ba seada ta shekara biyu lokacin Anna ta samu cikin Hunainah. Wata safiyaKafin mu Gama shiryawa se gashi ya fito daga daki, Nuzla da Badi'a Suka gaishe shi Amma ni Kam ko kallon shi banyi ba seda Anna ta zungure ni hade da harara ta sannan nace " Ina kwana?" " Lafiya Lau Unaisa! Har Kun shirya zuwa makaranta?" Nace " Mhm!" Yace " To Allah ya bada saa, kafin ku dawo na koma no" Nidai bance komai ba har muka gama na dakko jakunkunan mu zamu tafi, na kalla Anna nace " Anna zamu tafi, jiya kin manta Baki bawa Badi'a kudin crayons din ba" Ta mike da sauri tana fadin " Mantawa nayi wallahi,Allah yasa baa dake ki ba?" Ta gyada kanta, ta wuce daki Dan dakko min, Baba ya saka hannu a aljihu ya Ciro uban kudi Yan 500 notes da se Dana zare idanuna Dan mamakin yawan su. Ya zaro daya sannan ya maida sauran ya Miko min daya yace " Gashi nan kuje ku saya sauran se ku saya Abu a Hanya" Na girgiza Kai nace " A'a" Se ya tsaya sororo Yana kallona yace " Amshi Mana!" Na Kara girgiza Kai daidai fitowar Anna se ta tsaya tana kallon mu, Nuzla tace " Anna tace kada mu dinga karbar Abu a gurin mutanen da bamu sani ba" A take Naga fuskar shi ta canja, he looks embarrassed, yaa kalla Anna sannan ni se Nuzla se Badi'a, Anna ta Mika min tace " Adda ku tafi kinji, ayi adduar fita daga gida sannan Dan Allah ana tashi ki dawo kunga yau laraba akwai hadda a islamiyyar" Na gyada Kai na Ina fadin " To Anna inshallah se mun dawo" Ta bi bayan mu tana fadin Allah ya muku albarka. Haka kullum take ita din uwar arziki ce. Bayan ta dawo yayi Mata rashin mutunci sannan ya tattara kayan shi ya tafi. Ko da muka dawo se muka cigaba da harkar mu Babu Wanda ya tambaye ta inda yake a Haka rayuwa ta tafi, abin bakin ciki tafiyar shi da wata Tara ta Haifa Hunainah, wannan karon Babu Wanda yazo ko daga masaya ma, itama batayi taron suna ba, a cikin mu Babu wadda ta samu less kulawa ma irin Hunainah, duk yadda muka shaku da Badi'a to abin ya wuce tsakanina da Hunainah, ni ce komai nata, wanka goyo, feeding dinta da komai ni ce. so da ta fara magana ma da suna na ta fara fada, take cemin Amie. So akwai wayanda har muka girma Yar Amie suke ce Mata Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 First Bank of Nigeria A'isha Hassan kwalam and send evidence of payment to 09063467258. [5/11, 5:55 AM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕 *F* Ayshatuuu Kafin ya tafi ya canja Mana gida, sede saboda tsadar gidan Bai bar Mata kudin abinci ba yace ai an fada Masa tana Yan buge buge Dan haka ta samu ta ciyar damu. Wannan abubuwan su Suka Kara harzuka Anna akan tsanar Baba, Bai taba sauke nauyij shi da Allah ya daura Masa ba, shi ya kasance kawai head figure ne a wañnan gidan. Anna kullum cikin Neman abin da zatayi da zai kawo Mata kudi take, ita ba gata ba balle ace wani zai kawo Mata dauki, duk duniya Inna Zulai kadai ke gareta, ita dinma Kam tana ta kanta. Kwatsam ana haka ta samu kwangilar yin rigunnan sanyi zuwa wata makaranta, Dake tunda na fara wayo inhar zata aje kwarashi to se na dauka na gwada tun tana hanani har ta kyaleni, ta siya min idan na Gama assignment dina se na dauka inayi. Wannan sanaar ma Bata ishe ta ba se take siyarda seasonings da spices Haka. A Haka nayi wayo Nuzla ma Haka, se ta saka ta a makaranta, idan muka dawo se mu tafi makaranar islamiyya. Dake na fara wayo idan na dawo se na dinga tambayar ta " Anna Ina Babana? Anty tace zaayi PTA meeting kowa Baban shi yazo" Se tace min nayi hakuri zaizo. Ana Haka Baba ya dawo da mummunan labarin rasuwar Baba Zulai. Anna kamar zata haukace saboda tashin hankali har yau Ina iya tuno kukan da ta dinga yi, a wañnan karon mukaje Masaya to zuwan ma ba me dadi ba mukai, seda muka kwana bakwai kafin muka dawo, ban manta ta taba Danni inada wayo sosae Kuma inada rike Abu ba nida mantuwa, of all my life lokacin na dauka ita ta Haifa Anna, kowa ya bude Baki zaice Hassana ce abar tausayi, ko Yayanta baa tausaya musu ba kamar Anna, dama su biyar ta Haifa dukka Masa Kuma duk sun girma, har da me zuwa Lagos. Tunda muka dawo Anna ta kwanta jinya shi Kam Alhaji Yahai dama can muka barsa, a wañnan jinuar da tayi min Sha wuya, da rokon Allah aka samu ta dawo Kan dugadugan ta ta daura daga inda ta tsaya. A islamiyyar da Anna ke zuwa tayi wata kawa Anty Nana, wannan Anty Nana kusan kullum tana gidan mu saboda Allah ya Mata yawo, danma ita Anna ba Zama take ba Dan ta koma harkar Saida gwanjo, Amma Kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen ganar da Anna hanyar da zata bi, ta Kuma nausar da ita yadda rayuwa take a wañnan zamanin. haihuwar Hunainah wadda ta kasance auta Kuma ta hudu a gurin Anna, Wambai take zuwa tayi tsince tsince ta dawo gida ta siyar daga baya Kuma da likafa ta cigaba se ta siyo Kaya sosae ta jibge a gida, a shekarar da Hunainah ta cika biyu Ina Anna ta Zama wata daban Dan kuwa dealer Kaya take budewa ta siyar ta hada kudin ta. Ga saka da muke Mata, wadda makarantu da dama a kusa damu mu muke musu saka ni da Nuzla, Allah ya albarkaci kasuwancin matar nan se gashi ta hada kudi ta siyar da wani fili da ta taba siya acan bayan mu ta saya gida ta saka Yan haya. Wannan Anty Nana tace Mata ta Kara hada kudi ta saya gida idan ba Haka ba watarana zata rasa inda zamu zauna, kamar Wasa Anna ta hada komai da take dashi ta siyar tabi shawarar Anty Nana ta saya gida Amma a wañnan watan abinci ma se da kyar take iya siya Mana, dole ta samu wani gida take musu girki, idan zata dawo zata taho Mana da abinci muci. Mun Sha wahala sosae ba da Wasa ba, bana mantawa da weekend idan ta tafi gidan aikin ni Kuma se na karbo wankin mutane na zauna nayi na Kai can gidan na shanya su bani kudi, Wanda nake amfani dashi na siyawa Badi'a da Hunainah abinci da rana, mu Kuma se mu hakura har se ta kawo, ga Badi'a da son Madara yadda Bata San Babu ba, Duk abinnan Bata sani ba se watarana ta dawo unexpected ta sameni nida Nuzla min zage muna wankau, ranar seda ta fasa min jikina saboda dukan, a cewar ta ita zatayi Fadi tashi ta samo Mana Abu Amma mu we don't have that right, tun daga ranar ban sake wannan gigin ba. A wañnan shekarar komai yayi tsanani, sau da dama Zan ganta tana kuka idan Hunainah na kukan Yunwa a Haka a daddafe wata ya cika kudin aikin ta Suka iso ta siya Mana kayan abinci, da aka Bata kudin hayar gidan ta se ta koma sanaar ta ta gwanjo, rayuwa ta Dan Zama a bit stable. Inada shekara Sha biyar, Nuzla nada Sha biyu, Badi'a na da tara ita Kuma Hunainah nada bakwai Haka muke. Wani safiya ta asabar anyi hutu both islamiyya da Boko. Tunda muka tashi Anna ta bar min sallahun ta tafi gidan aikin ta muyi abinci muci, duk Wanda yazo nemanta muce ta tafi ungiwa Dan ba kowa yasan tana aikatau ba, an dai San tana fita tun safe se yamma take dawowa. Hakan yasa muka dakko holiday homework din mu, na fara koyawa Hunainah tracing kafin na koma Kan Badi'a, na Gama da ita na dawo Kan Nuzla da tace min ta kasa composing poem da aka saka ta tayi, na zauna da kyar na Mata sannan na koma Kan nawa, Haka abin yake kullum, Allah ma yasa dukkan mu kokari ne damu shiyasa wahalar take raguwa. Bayan mun Gama Nuzla ta hado kayan da mukai amfani dashi kanana ta wanke mana tas ni Kuma na daura Mana danwake da zamuci for breakfast, kawai se muka ji sallamar Baba, dukka muka amsa ya dawo bayan shekara da shekaru. Muka Masa sannu da zuwa ya shige daki abin shi ya barmu. Nuzla ta dubeni tace " Adda ya zamuyi Anna Bata nan" Nayi shiru Ina tunani nace " Kawai muce ta je suna ko?" Se muak gyada Kai, seda na sauke abinci sannan na bawa Badi'a ta Kai masa, se yace tace min nazo, na saka hijabi na Dake Kan igiya na Shiga dakin Yana zaune Yana ta jefa danwake a bakin shi, a raina nace kamar ya bada kudin flour se wani ci yake. " Ke Baki San kice min sannu da zuwa ba? Yara duk Babu tarbiyya" Nayi kasa da kaina Ina jin Babu dadin yace min bamuda tarbiyya, a ganina duk kokarin da Anna keyi ganin ta tarbiyantar damu daidai Amma shi da ko kadan Bai bada gudunmawa ba zaice Haka, se hawaye ya fara zubo min, Bai ma lura ba yace " Ina iyar ku?" Na dan diririce Ina share hawayen fuskata nace " Ta...taje suna can Brigade" . Ya gyada Kai yace na tafi, Babu musu kuwa na fice Ina sakin ajiyar zuciya. Seda muka Gama cin abinci sannan Badi'a tayi wanke wanke a hankali kamar marar laka, Haka take ita din ajebo ce of highest order! Shiru shiru Anna Bata dawo ba har shida shi Kuma se tambaya ta yake Yi se yaushe zata dawo nace ai bansan me yasa Bata dawo ba. Hankalina ya tashi ganin har Bayan ishai, har Hunainah da Badi'a sukai bacci Bata dawo ba se wajen Tara naji sallamar ta, nayi wuf na tafi zaure , a matukar gajiye Haka fuskarta ta nuna nace "Anna me ya faru yau kin dade?" Ta danyi tsaki tana Mika min kayan hannun ta tace " Wallahi aikin ne se a hankali, me gidan ne yayi Baki Dole seda muka Kara daura wani abincin" A hankali nace " Anna wannan mutumin ya dawo" Tace " Waye?" Nace " Baba fa" Se ta dafe kirjinta nace " Amma nace Masa suna kikaje, mu shiga Kar yaga na Dade" Mun jiyowa se muaki kicibis da bawan Allah ya nade hannun sa Yana kallon mu, ya saka hannu ya kwada min marin da shi ne karon farko Kuma Karo na karshe da aka marenu, kafin nakai hannuna, Anna ta riko ni tana fadin " Me yasa zaka mare ta? Laifin me tayi maka" Ya Mata wani bansan kallo yace " Ke kin Isa kice wani Abu, mayaudariya Maci Amana. Dama ance fita kike Yi idan bana nan. Ga Yara nan dukka sunyi wata irin Kama.." " Yahai! Ka tsaya da duk abinka akai na Amma karka Bata min nasabar Yara na, me yasa bazan fita ba? Ka bar Mana abinda zamu ci ne? Ka tafi uwa duniya ka barni da Yara da auren ka. Wallahi Yahai ko zaka Fadi ka mutu a gabana bazan taba yafe maka ba" Ya daga hannun sa ya dauke ta da Marin da seda ta sake ni, na saki kuka Ina rike hannun ta ji nayi duk duniyar tana juya min, " Na fada Yahai, bazan yafe maka ba Koda shi kadai ne abinda zaka je aljanna wallahi se de kaje wuta, idan kana ganin banida gata banida kowa ka sani Allah shi ne gata na, Kuma zakI daka sanin abinda ka Mana" " Tunda har kinsan na fada ki fada to se ki je na sake ki saki daya, saki biyu!! Babu ni Babu ke, ki tafi can da Yayanki" Wannan shi ne mafarin komai, shi ne silar bunkasar mu yayinda ta Zama ta rushewar sa! Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258 [5/11, 6:00 AM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕 *G* Ayshatuuu Se lokacin ta gane abinda Anty Nana je nufi da maganar ta, ta Kama hannuna muka shiga ciki Ina kuka, tana Yi Nuzla nayi, ta kwashe kayan mu Ina Taya ta, a Daren bamu runtsa ba ta kwashe kayan ta, ta Jirge gado da komai nata asuba nayi Muna sallah ta dauki mayafin ta ta fice, kafin bakwai ta dawo da me mota da Kuma Anty Nana se makwabciyar mu umma da suek shiri ta shigo, munata baccin gajiya a parlor, seda ta kwashe komai nata tas sannan ta kwashe mu muka tafi, Allah ya rufa Mana asiri ta saya wannan gidan da sede muje karkashin gada mu zauna. Muka koma sabuwar unguwa anan cikin Kano, gidan karami ne me dakuna biyu se bandaki da Kuma kitchen kwaya daya, se shago Wanda kofar shi take a waje. Anna tasa aka rufe kofa aka dawo da kofar ciki, tsakar gidan karami ne da rijiya ta ruwa. Haka Suka Taya ta ta shirya komai da se yamma lis sannan aka Gama Suka tafi. Daki daya tasa kayan gadon ta da wardrobe, dayan shagon tasa kujerun ta, se dayan tasa Mana katifar mu da jakunkunan makarantar mu. Da daddare muka kwanta, duk farkawar da nake tana zaune a sallayya tana kuka, seda mukai wajen kwana uku sannan ta hada kanmu muka tafi Masaya bisa shawarar Anty Nana. Muna zuwa ko karasawa gidan dagaci bamuyi ba, aka dinga Mata Ihu tsintacciyar mage Bata mage,Ashe dama mu din ba yayan Yahai bane yawo takeyi, Haka ta dinga kuka muna Taya ta ta juyo muka dawo Kano. Ka guji macen da akai wa laifi. Kafin mu koma makaranta ta rage damuwar ta, ta samo Mana makaranta sabuwa kusa damu, kullum ta zauna se tace Mana " Unaisa, Nuzla, Badi'a da Hunainah.." Wadda ba lallai tana fahimtar maganar da Anna keyi ba. "...Duk wannan abinda nakeyi Dan ku nakeyi, Ina son kuyi karatu ku fitar Dani kunya, Ina son yadda mahaifin ku ya wulakanta ku, dangin shi Suka ki karbar ku, kusa su zo da kansu su roki gafarar ku Yayana, ku wanke min bakin cikin shekara goma Sha shida na kunsa a wajen mahaifin ku. Daga yau ni kawar ku ce, ko menene kuzo ku fada min" Wannan kalaman nata seda muka haddace shi a kwakwalwar mu, se ya zamana rayuwata gani nake Dan ita nake, komai nake se na tuna wannan maganar tata. Ance zafin nema baya kawo samu inji BAHAUSHE, gaskiya ba Haka bane Dan kuwa kafin shekara ta rufa Anna tayi gaba se de ka tada Kai kallo, mussamman kasancewar mu farkon tarewa a unguwar ya zamana kusna ta kafa kanta a Sanaa. Kayan gwanjo har daga saudiyya ake Aiko Mata ta Zama babbar mace mu kanmu se rayuwa tayi afuwa sosae, Amma kullum tana tuna Mana kada mu manta wahalar da muka Sha, kada Kuma mu manta kanmu. Bayan shekara uku Na cika shekara goma Sha takwas, na zama young adult which always wanted to, kullum so nake ace min ai shekara ta Sha takwas. Na Gama secondary school Dina tsaf na Kuma fita da flying colors dan kuwa kaf set din mu Babu Wanda ya samu grades din da na samu a waec. Dama banyi neco ba. Saboda Anna tace tana da yakinin zanci neco. Sede inda aka samu mistake banyi jamb ba, seda Dan Anty Nana Yaya Yusuf yazo sannan yake tambayata nace ai banyi ba, bana mantawa shi ya siyo min form din school of nursing hadejia da Kuma form din school of midwifery Kano. Yace naje nayi pretest da interview duk inda naci kawai se naje nayi. Na girma sosae, na Zama yanmata wadda dauke idanu akaina se Wanda yayi da gaske, banida tsayi sosae Amma tsawona is average, no macece chubby saboda ni ba a rame nake ba, hips dina tamkar Wanda aka hura shi Haka yake abinda ke daukar hankalin maza da yawa suke nuna suna Sona, and I hate that fact. Ba laifi I'm busty dukda ba sosae ba Amma ba zaka ce bani dashi ba, ni din macece cikakkiya. Fuskata nada tsawo, inada gashi me yawan gaske sede tauri ne dashi sosae, banida goshi Dan ta gefen gira ta gashin kaina a hade suke, gashi ne kwance a forehead Dina Wanda ko Yaya na daura dankwali se ya fito, gashin baya rufuwa, inada asalin kamanni na Fulani, dogon hanci, matsakaitan idanu farare tas, bakina bashida girma Kuma ba karami bane, hakorana farare ne tas a jere kanana, a jiki inada wushirya siririya. Ina da sanyin Hali, banida hayaniya ko tashin hankali, duk wani Abu Dana ga zai bani matsala Ina koakrin ganin na kauce Masa. Bana fada zaiyi wahala kaga ance anyi fada Dani Amma Kuma inada ruko na gaske, I forgive but I don't forget, inada saurin kuka Wanda ake cewa it's a sign of Innocence, hakane indai nai kuka to inada gaskiya Amma idan nayi shiru to gaskiya nayi laifi, ni mutum ce me sallah, a ibada sallah na daya daga cikin abinda nake finding joy and peace a yinta, Amma azumi da kyar nake sitta shawwal bayan Ramadan. Wannan gaba daya itace Unaisa. Anna ta dawo na nuna Mata forms din da na riga nayi filling na Kuma Yi attaching dukkan credentials din daake bukata a ciki. Ta karba ta jujjuya sannan ta dauki wayar ta ta Kira Yaya Yusuf tayi Masa godiya sosae. Washegari ni da Anna da Hunainah muka je Danbatta mukai submitting da sati ya zagayo mukaje hadejia muka Kai. Mun fito daga school din muka wuce tasha, muna zaune cikin tashan Hunainah Tasha guava t Bata min veil dina, tunda Anna ta kalleni ta gimtse fuska, na Bata Rai nace " Saboda Allah Anna kiga abinda yarki ta yimin?" Hunainah ta saka hannun ta tana goge min Bata San Kara Bata min take ba, na saki karamar Kara nace " Anna kiyiwa Allah ki ce yarinyar nan ta Bari Mana" Ta dubemu tana dariya tace " Hunainah daina kina batawa Adda mayafinta" Ta kalleni da idanun ta irin nawa tace " Sorry Adda!". Na shafa kanta nace " It's ok Darl" Anna ta dubeni tace " Wacce kike so a ciki makarantar?" Na danyi murmushi nace " Idan Zaki yarda nafi son hadejia, nayi nursing kawai" Se tayi murmushi tace " Nasan a duk inda kike Zaki kula da kanki Dan Haka Babu damuwa Allah ya sa ki samu wadda kike so din" Nayi murmushi nace Amin. Se hirar mu ta katse saboda shigowar passengers guda uku, babban mutum Haka shekarunsa sunfi arbain se wani guy da yake a late 20s dinsa, da Kuma Yar budurwa da Bata fi saa ta ba. Sukai sallama suka shiga, seat din dake gaban mu na mutum hudu yace ya siya Dan Haka akace mota ta cika Dan muma Anna seat din baya ta siya, ga dama akwai passengers biyu a gaban motar. Budurwar ta fara juyowa ta gaida Anna hakan yasa nima na gaida Wanda nake tunanin mahaifinta ne da Yayanta. Sunata Hira har muka Isa Kano, tun kafin mu Isa guy din ke waya Yana fadin " Ahmad kazo park mu wuce, wallahi motar mu ce ta samu matsala tun a hadejia" So ana aje mu duka muka sauka, tazo ta taba Hunainah tana murmushi tace " Ya sunan ki baby?" Ta kalleni tace. " Yar Amie" Nayi dariya nace " Sunanta Hunainah" Se ta shafa kanta daidai lokacin Baban kece Mata " Zuhra Ahmad yazo" Ta Mana waving hannunta Suka shiga katuwar mota baka wuluk Suka wuce, na lumshe idanuna na tare Mana napep sannan muka wuce gida. Muna zuwa Nuzla tayi girki ta Gama Amma gidannan gaba daya upside down. Tunda muka shiga Anna ta hade fuska, Badi'a tana zaune da wayata Dana bar musu Koda zasu kira mu ko mu Kira su. Tana ta danne danne ga Waka ta Kure volume tana ji. Tana jin sallamar mu ta mike Dake Anna ce a gaba tayi kanta zata rungume ta, wata harara data sakar Mata yasa ta tsaya, se ta sunkuyar da Kai " Anna sannu da zuwa!" Bata amsa ta ba ta wuce ciki,na dubeta nace " Badi'a ya gidan" Ta Bata fuska tace " Kuma Anna se Bata Rai takeyi" Na kalli tsakar gidan nace " Ki kalla yadda kukai da gidan

Chapter 3 of 5