zaune lafiya nake, last time da na sani balai take akan zaa auro ni, to gashi Kuma ta karbe ni hannu bibbiyu, ta hakura ta saduda, Amma akwai abubuwan da bazan manta ba. Ranar da aka Yi kwana bakwai akai addua a karkade, aka cire tampons Dake waje, wasu Suka gyara Mana gida sannan aka baje, Anna, Dada da Zuhra Wanda suka kasance tare dani duk ranar suka tafi, har mutanen hadejia ma, Anty Aisha ta tafi tun ranar uku Amma ana bakwai dinma tazo. Wannan tafiyar tasu yasa nayi ta kuka mussamman da Abba yace anan Zan zauna ba se na koma gida ba, Haka na yini a daki Ina kuka, har Anna ranar se da tayi kuka, Ina ganin rayuwata a garari take, musamman da nazo kwanciya Naga Babu Zuhra da zata raba dare tana lallashi na, da Kuma min Hira Koda bazan amsa ba. Abokan shi Wanda ya kasance Senate president, da sauran senators tunda shima elected senator ne in office. Seda suka saka aka cika Mana store da duk wani nau'in kayan abinci sannan suka shigo suka Kara gaida mu ya aje kudi ya juya ya tafi su Muhammad Suka raka su. Washegari gidan Babu kowa, Jin shirun da gidan yayi yasa na kasa fitowa Bayan na idar da sallah na zauna Ina jin kewar shi a dukkan sassan jikina, kwana uku kawai mukai dashi Amma kwanakin bazan manta dasu ba, sun kasance masu dadin gaske, ya sakani farin cikin da nake mamakin yadda mutum zai iya hakan, Na lumshe idanuna hawaye sun wanke min fuska ta, na saka kaina tsakanin cinyoyina Ina kuka tun karfina, Ina cikin kukan se wayata ta fara ringing, na saki ajiyar zuciya tare da janyo wayar Naga Anna ce me Kiran, cikin sauri na goge hawayena na dauka Ina fadin
" Anna Ina kwana?"
" Lafiya Lau Unaisa! Ya kike Ina fatan bakya kuka"
Na saka hannu na dauke hawayen dake cascading a kuncina, na danyi sniffing nace
" Na daina Anna"
Ta Jima tana min nasiha sannan tace nayi wanka na fita na taya Mamaa aiki. Daga Haka mukai sallama na Mike jikina ba karfi nayi wanka sannan na shirya cikin wata bakar riga wadda Babu ado ko kadan a jiki. Hulata na cire Dan saka sabuwa anan naji yadda kaina ya damkare guri daya. Comb na dauka na taje shi Ina runtse Idanuna saboda yayi tsamu. Na zauna a nutse nayi kitso biyu na hade jelar na saka a hula sannan na dauki katon veil na yafa a jikina na fito parlor. Ba kowa se masu aiki sunata fama, muka gaisa suna kara min gaisuwa, Ina tunanin murya ta Mamaa taji ta fito, idanun ta sunyi jawur Wanda ya tabbatar min kuka tayi, na gaishe ta, ta saki fuskarta tace
" Ya Kika tashi Unaisa?"
Nace
" Alhamdulillah Mamaa"
Muna zaune shiru, tunda ba sabawa muaki ba balle muyi magana, plus Ina Kama kaina, Ahmad ya shigo ya shirya zai tafi aiki, muka gaisa sannan ya nufi kofa zai fita se na dubi Mamaa nace
" Bazai ci abinci ba"
Tace
" Ahmad abinci fa?"
Ya girgiza Kai, ta dubeni sanann tace
" No dawo ka zauna, Bari kasha ko tea ne"
Haka ya zauna aka kawo tea din yasha sannan ya tafi ita dama Aseey ta wuce gidan ta tun Daren jiya, Haka Muhammad ma da Bilkisu matar shi sun koma Gombe tun jiya. Se ya rage daga ni se ita, aka hado abinci Wanda naci kadan se naji zuciyata na tashi kawai se na Bari, ta dubeni
" Ko akwai abinda kike so ne?"
Na girgiza Kai Ina Dan murmushi nace
" Kawai bakina daci nake ji"
Ta gyada kanta kawai ba tace min komai ba. A hankali kwanaki suke shudewa, kullum Rana Yana Kara kwanaki a cikin kabarin shi, duk lokacin da na kebe se nayi kuka musamman idan na tuna yadda mukai rayuwa dashi, ranar da muka fara haduwa da irin artabun da akai kafin na aure shi, Amma Ashe Babu ma rabon zaayi doguwar rayuwa tare, kwata kwata kwanaki uku kawai mukai dashi ya tafi ya bar zuciyata da tabon rashin shi. Na goge hawayena Jin muryar Mamaa tana fadin
" Unaisa dakko hijabin ne Haka?"
Na dauki hijab din da wayata na fito, ta dubeni tace
" Kuka Kika Yi ko?"
Kamar ta zuga ni se wani kukan ya Kara kwace min, ta janyo ni jikin ta tana lallashi har nayi shiru sannan muka nufi asibiti. Ahmad na tsaye sanye da labcoat Yana jiran Karasowar mu. Muna zuwa office din shi muka zauna, da kanshi ya dauka sample sannan ya cike forms ya Kai Lab, seda ya dawo Mamaa tace
" Ahmad dama scan kawai akai ko?"
Se yace Yana shafa Kai
" Wallahi mantawa nayi. Anty Unaisa sorry na bula ki"
Nayi murmushi ba tare da nace komai ba Dan har lokacin na ksa sakin jikina dashi ba duk yadda yake kokarin ganin na saki jiki, Yana Kuma kokarin wanke laifin shi a gurina, Amma Wanda yasa yayi min laifin ma Baya duniyar, meye abin fushi, kawai dai Ina iya takuna ne, Kuma dama bahaushe yace baa Bari a kwashe daidai. Tare muka fita zuwa scanning room din cikin asibitin, an cika sosae a gurin, ya Shiga Babu jimawa ya fito yace na shiga, Ina Shiga na kwanta dukda naji Babu dadi Ina Kuma ganin hararar da ake wurgo min ta kowanne guri, nasan munyi chancing dinsu. Gel ya shafan a ciki Bayan yayi min gaisuwa sannan ya dauki probe din ya fara gogawa a ciki na zuwa marata, yanayi suna magana da Ahmad da yayiwa screen kuri da idanu.
" She's pregnant Doctor!"
Nayi saurin duban fuskar Ahmad se Naga ya saki fuska Yana murmushi yace
" Alhamdulillah! Mamaa zata ji dadi. GA din fa?"
Yace fuskar shi a washe
" 20 days ne"
Shi Kuma a ranar kwanan shi Sha takwas da rasuwar, a raina na ayyana kenan ranar da muka fara having affairs a ranar na samu ciki. Na tuna ranar daurin aure friend Dita tace
" Kina zuwa Zaki samu ciki tunda ovulation kike yau"
Na harareta nace
" Ki gani akan ki, se na huta tukunna"
A hankali hawaye suka gangaro min na sakko daga gadon Bayan ya bani tissue na goge ciki na, na fito ganin hawaye na tsere a fuskata wani na korar wani, Mamaa tayi saurin tasowa tana fadin
" Ya akai Babu cikin ne kike kuka?"
Kaji Mamaa da wata magana, kawai Dan babu cikin se na dinga kuka, na karasa inda take tsaye har lokacin Ina kuka ban Bata amsa ba, Ya fito Yana fadin
" Mamaa akwai Mana"
" To meye abin kukan Unaisa? Kiyi murna Mana"
Na rike hannunta nace
" Haka zaa haife Babyn Bai masan mahaifin shi ba"
Se Naga duk jikin su yayi sanyi suma, Ahmad yace
" Haka Allah ya tsara, Allah ya jikan Abiey!"
Nace Amin, bamu koma office din ba muka koma gida, da kanta ta Kira Anna ta fada mata, Anna tace Mata
" Kinga rabo"
Mamaa tace
" Wallahi kuwa, ni kaina abinda nake fada kenan. Allah ya inganta"
Ta Kira Abba ta fada Masa da daddare kuwa se gashi yazo shi da Dada ya duba mu, Asiya ma ta kirani tana fadin
" Nasan nayi Miki laifi Unaisa kiyi hakuri"
Ina zaune dirshan akan gado na Gama Shan kunun tsamiyar da Mamaa ta dama min Kiran nata ya shigo wayata, na dauka ko gaisawa bamuyi ba, na danyi murmushi kadan Dan a kwanakinnan Murmushin ba sosae nakeyi ba. Nace
" Asiya magana ai ta wuce, komai ya wuce tunda Wanda akai komai Dan shi dinma ya rasu"
Se ta danyi shiru kafin tace
" Dan Allah Unaisa, ba Haka zakice ba, nasan baki manta abinda ya faru ba"
Na sauke ajiyar zuciya nace
" Asiya ya wuce wallahi, nasan fushi yasa kikai komai, Amma yanzun Ina fata kin fahimci dalilin da yasa Allah ya tsara na aura Baban ki ko? Rabo ne Asiya. Wanann cikin Dake jikina"
Ta jinjina Kai tace
" Na fahimta Unaisa, Dan Allah find a place in your soft heart and forgive me"
Nayi murmushi nace
" Ya wuce na yafe miki kada ki Kara tada maganar, mu fuskanci abinda ke gaban mu"
Ina jin dariyar ta saboda Jin Dadi ta Dan tsokane ni kamar yadda muke da sannan mukai sallama kowa yayi nashi wajen.
Kwanaki suka cigaba da tafiya, har Rana ta zago mukai Masa sadakar arbain, a wañnan lokacin annual leave Dina da na dauka ya Kare haka Kuma na Mamaa. Dan Haka na fara hada kayana Dan komawa aiki. Da yamma ranar asabar na Gama komai na fito daga toilet se na tsaya gaban madubi Ina kallon fuskata, na rame Rama ta ban mamaki, idanuna sun tashi daga asalin farare sun rine saboda yadda kullum se nayi kuka, Haka lips dina duk sunyi cracking kamar bani bace wannan Unaisar da kowa yake kwatancen gayunta, kaina tun wannan kitson biyun da nayi ban Kara ba. Ya kamata na gyara jikina na ayyana. Na cire kayana na dakko shaving cream, da shampoo na shga wanka, seda na wanke jikina da kaina tas sannan na fito, wata ajiyar zuciya na sauke Jin wata iska na shigata ta ko Ina, na zauna na gyara kaina sannan na shafa Mai, na saka turare me sanyin kamshi Wanda nasan bazaa ji ba, na zura wani bakin material dinkin A shaped gown. Anan na Kara tabbatar da ramar da nayi. Na daura dankwali na yafa katon veil na fito parlor. Suka suna zaune, Aarif din Asiya nata tsalle tsalle, Bilkisu na ma yarinyar ta magana. Ko rasuwar nan Bata min gaisuwa ba, Bata taba min magana ba Haka Nima ban taba Mata ba, ko abubuwan aurennmu Yaya Muhammad Bai taba shiga ba, Amma ita tafi Mamaa kishi, Muka gaisa da Muhammad sannan na koma daki Dan Mamaa da Asiya sun fita. Se yamma Mamaa ta dawo, Asiya ta fara shigowa tana fadin
" Kin nane a daki kamar me takaba"
Na tashi na zauna daga kwancen da nake nace
" Da me nakeyi idan ba takaba ba"
Se ta rufe bakinta tana dariya ta shigo, muka gaisa sosae tac e
" Da nazo ai Mamaa tace bacci kikeyi"
" Bana iya bacci da daddare"
Se Naga fuskarta ta Dan canja tace
" Me yasa? Wani gurin nayi Miki ciwo ne?"
Na girgiza Kai na nace
" Kawai abin duniya!"
Se ta Bata fuska tace
" Ya kamata ki Dan sararawa zuciyar ki Unaisa, mutuwa ba yadda zamuyi, we so much missed him wallahi"
Na gyada Kai na ba tareda nace Mata komai ba, se ta kawar da wannan hirar ta dakko wata.
Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First Bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.
[5/11, 5:55 AM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕
*D*
✍️ Ayshatuuu
Ranar lahadi da sassafe na fito a wanka , na Gama shiryawa cikin doguwar riga coffee Ina yafa veil naji sallamar Mamaa, na amsa se gata ta shigo na gaishe da ita, ta zauna gefen gado sannan na zauna tace
" Har kin Gama shiryawa se tafiya kenan?"
Na gyada Kai na Ina Dan murmushi kadan
" Allah ya jikan honorable!"
Na amsa da Amin sannan tace
" Zaki dinga zuwa ko? Ko Dan Zan dinga zuwa Ina ganin ki. Ki kula da cikin jikin ki Dan Allah, kada ki Bari damuwa tayi Miki yawa, ki sani komai shiryayye ne daga gurin Allah, sannan kiyi hakuri abubuwan da suka faru a baya, bansan me yasa nayi Haka ba, bansani ba"
Nayi saurin riko hannun ta ganin idanun ta na cikowa da kwalla nace
" Ai ya wuce Mamaa, Inshaaa Allah Mamaa ya wuce, "
Ta aje min kudi tana min godiya, nayi saurin dubanta Ina girgiza Kai nace
" Mamaa inada kudi Dan Allah ki barshi"
Ta dube ni na Dan lokaci sannan tace
" Karki damu hakkin ki ne ai, kawo Mana akai kin manta"
Ban tuna ba kawai se na gyada Kiana na zura kudin a jaka Ina Mata godiya, tana murmushi tace
" Nagode da Kika zauna Dani na wajen kwanaki hamsin, nagode sosae duk abinda kike bukata ki sani hakkina ne na Nemo Miki shi, Allah ya jikan Honorable ya gafarta Masa ya kyautata namu zuwan"
Inada saurin kuka, wannan maganar tata tasa na fara kuka, ta rungume ni a jikinta tana lallashi, seda ta saka ni a gaba naci abinci sannan ta janyo akwatina na biyo ta da karamin da Kuma handbag dina. Suna zazzaune dukkan su a parlor suna breakfast. Ina shigowa Muhammad ya saki murmushi yace
" Anty Unaisa Ina kwana?"
Nace
" Lafiya Lau Yaya Muhammad, ya Islam?"
Ya dubi Islam Dake cinyar Maman ta yace
" Gata nan me kukan dare"
Nayi murmushi, Ahmad ma ya saki fuska sosae muka gaisa yace
" Babu matsala ko? Ba wani Abu?"
Na girgiza Kai nace
" Babu komai!"
Dan gaskiya nakan manta cewar ciki ne dani, bana laulayi ko kadan ko craves dinma ba nayi. Asiya ta dubeni muka gaisa na karbi Aarif a hannunta. Amma Bilkisu ko kallona batayi ba tana spreading chocolate spread akan slice bread a gaban ta. Idon Mamaa yasa nace
" Bilkisu Ina kwana!"
Muhammad ya kalleni sannan ya kalleta Bai ce komai ba, Mamaa tace
" Bilkisu kinada matsala da Unaisa ne? Na lura ko magana bakya mata"
Ta girgiza Kai Bata ce komai ba, Mamaa se tayi shiru, Ahmad ya Mike tareda Jan trolley na yace
" Anty Unaisa mu wuce ko?"
Na mike Ina gyara lullubi na na dubi Mamaa data mike nace
" Nagode Allah ya saka da alkhairi"
Ta rike hannuna muka fita harda Asiya me min kashedin na dinga cin abinci, se Dana shiga mota sannan Muhammad ya karaso mukai sallama dasu Mamaa na Mana Allah ya kiyaye Hanya. Tunda muka dauki hanya mukai shiru se karar radio Dake aiki har muka karasa kofar gidan mu, ya samu guri yayi parking yace
" Zaki Dade naje wani gurin? Ko Dan Zan dawo nan da 2 hours. Is that ok by you?"
Na gyada Kai nace
" Yayi, seka dawo"
Daga Haka na shige gida yayi reverse ya bar unguwar, da Hunainah na fara Karo ta fito daga kitchen dauke da plate din abinci, tana ganina ta aje plate din ta taho ta rungume ni tana fadin
" Anna ga Adda Unaisa tazo"
Kafin Anna ta fito tuni Nuzla ta fito tana ihun
" Adda Unaisa oyoyo"
Itama ta fado jikina, karon farko da nayi dariya tsakanin da Allah tun Bayan rasuwar shi, bayan sun sake ni na hangi Anna a tsaye tana murmushi, rabo na da ita tun ranar sadakar bakwai, tayi kokari Bata Kara komawa ba, su Nuzla ne Suka jemin wajen sau uku, Zuhra duk sati se tazo, Dada da Abba ma sunzo har bazan iya irgawa ba, Baffa Dake baya nan akai rasuwar ranar da ya dawo daga China, ko hadejia Bai he ba ya taho gidan, ranar nayi kuka da ya saka ni gaba da lallashi, da nasiha. Rayuwa kenan!
Na karasa da sauri na rungume ta, itama ta rungume ni tana sakin murmushi, sannan ta ja hannuna muka shiga parlon Dake kunshe da dakuna biyu, daya mallakin Anna daya Kuma namu mu uku, Dake ba kasafai muka Faye Baki ba shiyasa gidan Bai Mana kadan ba. Na zauna saman carpet nace
" Anna Ina kwana?"
" Lafiya Lau Unaisa! Nayi tunanin se yamma Zaki tafi"
Na girgiza Kai nace
" Bana son nazo nan a tsatsaye shiyasa Naga gwara na taho da wuri"
Se ta gyada kanta, sannan ta mike tana tambayata abinda zanci, na danyi shiru Ina tunanin kafin nace
" Kawai Anna ki bayar a siyo min awara"
Tayi murmushi tace
" Aikuwa nama manta har nake tambayar ki"
Ta shiga daki Babu jimawa ta fito da note din dari biyar ta bawa Hunainah tace taje can makwabtan mu ta siyo min, Amma ta dauki food flask Bata son Abu a Leda. Hunainah ta mike yayinda Anna ta fita ita Kuma, se ya rage daga ni se Nuzla Dake danne danne a wayatta se sakin murmushi takeyi. Na dubeta nace
" Nuzla whatsup?"
Tayi dariya tace
" Nothing! Tare zamu tafi ko?"
Nace
" Abinda Anna tace"
Se ta aje wayatta ta matso kusa Dani tana magiyar nace ita Dan Allah, na Harare ta nace
" Saboda me Wai? Me yasa kike son Bina Wai"
Ta langwabar da Kai tace
" Kawai Kinga strike akeyi Ina bukatar fresh air"
Na tabe baki nace
" Ni Kam su Baffa Me gishiri Basu San anyi min rssuwa ba"
Anna dake shigowa tace
" Ki kyalesu, bawani Abu bane Dan Basu zo ba"
Na dubeta na gyada Kai, Nuzla da bakinta baya shiru tace
" Amma Anna ai sunzo biki, har yayan shi na aure seda suka zo cin shinkafa Amma gaisuwa sun kasa..."
Me zanyi Banda dariya, Anna ta wurga mata Parker Dake aje a gefenta tace
" Ubanki Nuzla! Bakin ki baya shiru ko"
Ta mike tana dariya tayi ciki, na Mike kafata daidai sallamar Hunainah, ta shigo da kwanon ta aje sannan ta mikawa Anna kudin da baa fasa ba tace
" Anna Baba Delun tace Wai ba zata karba ba tunda ta Adda ce, tace tana Miki sannu da zuwa zata shigo"
Nayi murmushi Ina yin godiya Haka ma Anna, plate ta kawo min na zuba ga lettuce da tomatoes data yanka min na hada, tana ta kallon kofa kamar me jiran Abu, hakan yasa nace
" Anna kina jiran Abu ne?"
Ta gyada min Kai tace
" Naman da kike so na bayar a siyo Miki Kuma har yanzun baa kawo ba"
Nayi murmushi Ina ayyana that's my Queen mother! Ina kaunarta Dan kuwa ita din ita ce komai namu, Fadi tashin da Anna tayi Akan mu bazai fadu ba, ko uban mu haifar mu kawai yayi, Amma cin mu da Shan mu, sutura da komai bamu it's ce, se ya kasance maganar ta a gurin mu it's kadai muke ki, saboda a ganin mu it's din ta cancanci every of our loyalty! Har na Gama ci kuwa ba a kawo Naman ba, na dubi agogon wayata saura awa daya kawai Ahmad ya dawo, na dubi Anna nace
" Anna Kinga har yanzun Badi'a Bata zo ba, Kuma lokaci na tafiya"
Hunainah tace
" Zata zo kuwa, Dan dazun ta Kira Adda Nuzla tace zata zo"
Na gyada kaina kawai tare da Dan kwanciya na Mike kafata, Anna tace
" Da waye Zaki tafi a cikin yaran nan, munyi magana da Dadar ku tace tana Neman dattijuwar da zata zauna dake kafin ki haihu"
Nace
" Duk Wanda kikace Anna daidai ne"
Ta dubi Nuzla tace Mata ta hada kayanta, tayi wani Murmushin jin Dadi ni Kuma na girgiza Kai. Badi'a Babu jimawa tazo, da yaranta biyu Nasrin me sunan Anna se Wahida me sunan Dada. Mun Sha Hira har Ahmad ya kirani akan ya dawo, Haka Dole muka rabu, Anna nata min nasiha akan hakuri da juriyan, ta nuna min Allah ke tsara komai Dana gani. Na share hawayena na fito, Yana tsaye ya harde hannayen shi a kirji, his father's look alike, na tuna lokacin da yake kawo Zuhra gidannan, lokutan da suke zuwa da Aseey, wansu lokutan yazo shi kadai, idan na fito shigowa da su yayi ta tsokana ta Yana cemin Wai daga ni gayu ya kare, zai so yaga mijina. Wani lokacin yace min Kar na sake na auri Wanda bashi da kudi bazai iya jurar necessities Dina ba. Amma haduwata ta karshe dashi shi ne Wanda yazo ya zazzage ni har gida, ya cimin mutunci , ya kirani da macijiya me cin Amana me kwadayi, bayan yasan baban shi Yana neman aure na. Wannan ranar nayi kuka har seda Anna tayi fushi Dani. No a lumshe idanuna ganin yadda rayuwar take sauri, Wai har anyi an Gama? Anyi bikin har ya rasu? Su Kuma Dake ba halin su bane har sun hakura, Yana ganin Anna ya tsugunna ya gaishe ta sannan ya bude min kofar din baya na shiga, Nuzla ta zauna gefen shi muka dauki hanya, seda muka biya gidan Dada sannan muka tafi, nan ma seda nayi kuka saboda nasihar da Abba kemin. Tunda muka tafi nake kaartun qurani cikin wayata har mukaje Dutse. Har kofar gida ya aje mu ya fito Mana da Kaya,
" Ka shigo kasha ruwa"
Ya girgiza Kai yace
" Zan dawo dubaki Inshaaa Allah! Dan Allah ki kula ki Kuma Yi hakuri da dukkan abinda Suka faru Dan Allah"
Ina iya hango nadama da Kuma kunya ta a idanun shi, Nayi murmushi Wanda mahaifin sa ya kance Wai shi ne abinda ya fara capturing zuciyar shi. Nace
" Ya wuce. Allah ya kiyaye Hanya ka gaida Mamaa"
Daga Haka na wuce na saka key na bude kofar parlon, na barshi tsaye da Nuzla. Katon parlon da aka tsara shi, na tsaya a tsakiyar Ina tuna ranar da aka kawo ni, ya shigo ya sameni zaune Kan daya daga cikin kujerun na takure, ya zauna gefena ya yaye min veil din da ya rufen fuska, tare da fadin
" Amarya bakya laifi ko kin kashe Dan masu gida!"
Kamar wani video Haka na cigaba da rewinding duk wani moment da muka kasance tare dashi, na zauna jagwab cikin kujera Ina sakin matsanancin kuka, in between sobs din Ina fadin
" I missed you!'
A Haka Nuzla ta shigo ta sameni, ko Bata tambaya ba tasan mijina na tuna Bata cemin komai ba, se da nayi me isata sannan na wanke fuskata a sink din dining na dauka wayata na Shiga bedroom dina, ban taba kwana a ciki ba na zauna na Kira Anna, Mamaa da Kuma Dada na sanar dasu munje. Kowannen su seda ya bani Baki a karshe Abba ya kirani ya Jima Yana min nashiha sannan mukai sallama. Zuhra ce kawai ban Kira ba, Dan na San tahowa zatayi.
Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
[5/11, 5:55 AM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕
*E*
Ayshatuuu
Nasan zuwa yanzun Kun kosa kusan asalin Labarina, zaku so kuji wacece Anna? Haka Mamaa Haka Dada? Su Ahmad da dukkan role dinsu cikin rayuwata. Sunana Unaisa Yahya, mutane da yawa sukance Wai a gurina Suka fara jin suna Unaisa, ni kaina Bayan ni me sunan baifi sau biyu na Kara jin me irin sunana ba.
Mahaifina Dan wani kauye ne ko Kuma nace gari a Masaya Dake karkashin Birnin kudun jihar jigawa. Mahaifina sunan shi Alhaji Yahya tun Yana saurayi sunan shi kenan, Dan bashida aikin da ya wuce yaje Saudi Arabia yayi shekara uku, hudu har ma biyar sannan ya dawo. Hakan yasa duk garin kowa Alhaji Yahai ake ce Masa memakon Yahya din. Mahaifiya ta sunan ta Hassana tace Mana ita Yan biyu ce Amma abokin tagwaita Kar tata shi ya rasu. Su biyu ne gurin iyayen su itada Baba Zulai a Wanda ta sani. Tace Mana dukkan Yan uwan ta idan aka haife su rasuwa suke, Amma akwai yayun su biyu Wanda Suma Basu San su ba, ba Kuma ta San inda suke ba, su biyu kadai Suka rage. Iyayen Anna Fulani ne Wanda ke yawo a duk inda Suka samu shanun su zasuyi grazing. Suna tafiya Allah ya kawo su Masaya lokacin Zulai Bata fi shekara goma Sha biyu ba, da suka zo sukai camping can bayan gari ita Kuma tana Dan shiga gari da sauran Yara a Haka dagaci ya ganta ya aure ta. Lokacin ana goyon Anna, da lokaci yayi suka kada shanu suka tafi Suka barta. Se bayan shekara hudu lokacin Yayanta biyu sannan suka dawo, sunzo wucewa, . Zasu tafi dagaci ya samu da kyar ya karbe Anna with the hope cewar idan Anna na nan zasu dinga zagayowa suna ganin su. Suna tafiya baa fi kwanaki uku ba Wanda dagaci ya aika ya gano hanyar da Suka dauka ya dawo yace iska akai sosae wadda tasa da yawa Suka rasu Kuma ciki harda kakkanin mu. Wani maganar ta girgiza kowa se Anna ta tashi hannu Inna Zulai ita ce uwarta da ubanta da komai nata. A Haka ta girma hannun su Babu makaranta da aka saka ta har ta shekara Sha biyar aka dinga zancen Bata samu miji ba, Anna kyakyawa ce ta gaske tana da gashi Haka Kuma karamin jiki me da ita kamar yadda Inna Zulai take. Kana kallonta kaga bafullatanar asali. Fara ce tas har yellow yellow take. A shekarar Alhaji Yahai ya dawo daga saudiyya Bayan ya shafe shekaru acan. Dagaci Baffa ne a gurin shi, da kakata da ta haifi Yahai da dagaci uwa daya uba daya suke, Kuma ita din uwar dakin Inna Zulai ce Dan Haka Yana neman auren Anna Babu wani ja aka hada su auren. Har muka girma nasan Anna Bata son