Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 5
daga gidan" Ya yunkura da karfi wanda hakan ya yi sanadin da ya watsar da ni gefe guda. Waje ya fito, ya dauki tabarya, ya koma dakin amma ina! Bai tarar da su ba kamar yanda ya yi buri, sai ya fara huce takaicinsa akan kayan jere da ke dakin kafin wani lokaci ya yi kwatsa-kwatsa da vidio da television. Saitin mai ros kuwa ya dagargaza da dama daga cikinsu, na isa dakin domin dakatar da shi aiwatar da danyan aiki, amma abin ya ki yiwuwa. Sai na nufi dakin Jimmai domin na nemo a gajinta. Yau ce rana ta farko da na ke shirin yin magana da ita. Kwance na sameta a kan gado tana yin barci, na tattabata har ta tashi "yaya akayi ?"ta nemi ji " maza ki kawo agaji babu lafiya" ban tsaya jin abin da zata fada ba na yo waje. Dakin na sake komawa ina ba shi baki amma ko yanzu ya daina to dainawar bata da amfani ya riga ya gama kwankwatsa duk wani tarkace da ke dakin. Sannan ne Jimmai ta shigo tana mai zazzare ido""me ne ne ke faruwa haka Sakinah?" "ke dai mu samu mu janye shi daga baya kin ji" Muka nufi Abdul gaba daya, ya kallemu a fusace " wallahi duk wadda ta kuskura ta kusanto ni sai na buga mata tabaryar nan" sai muka tsaya cirko-cirko. A gabanmu ya gama kwatsa kwatsa da kayan dakin daga bisani sai ya fito yana huci. Waje ya fita da sauri na san yunkurinsa shi ne ya hau mota ya bi su. Sanin zai yi hakan ya sanya tun sa'ar da ya suma na dauke mukullin na boye. Bayan wani lokaci sai gashi ya dawo ya fara dudduba mukullin a dakinsa. Rashin ganinsa ya sanya shi dawowa gare ni "Karimah ba ni mukullin mota ta da kika dauke. Na girgiza kai " banga mu kullinka ba Abdul" 50 "Karya ki ke ke ki ka dauka ki ba ni makullina ko kuma ranki ya Baci" "ban gan shi ba Abdul " na sake maimaitawa sai ya nufo ni a fusace. Sanin cewa komai na iya faruwa ya sanya ni guduwa faki da sauri, Amma ina!. Kafin na kullo kofa ta ya danno da karfi ya rutsa ni a kusurwar daki, Idanunsa ya yi ja kamar garwashi. Ya miko min hannu " ba ni makullina nace da ke" Na marairaice " to dan Allah Abdul ka zauna kar ka bi su " Ya sharareni da mari "surutun banza na tambaye ki ko kuwa mukullin mota?" Marin ya yi matukar shigata. Na dauko masa mukullinsa na ba shi, ya sake ficewa cikin huci. A tsakar gida na sami Jimmai rike da kugu. Ta dubeni "wai dan Allah me ya faru Karimah?" Na girgiza kai, "ni ma ban san ko me ne ne ba. Na dai jiyo Abdul yana farfasa kayan dakin ne" "to ina ita Sakinar?" "ina ganin unguwa ta tafi ko" Ta kalle ni cikin rashin gamsuwa da bayanin da na yi mata. Da alama ta fahimci cewa ina so ne na boye mata. Ta sulale a hankali zuwa dakinta gami da fadin" Allah ya kyauta" ni ma sai na nufi nawa dakin na ci gaba da sauraron dawowar sakamakon lamarin. Zancen abin da ya afku duk ya bi ya cika gari. Hakan kuwa sai bayan da "yan sanda suka shigo zancen, sakamakon zuwan da Abdul ya yi har gida ya ci wa uwar Sakinah mutunci, doke-doke su ka yi shida ita. Sakinah kuwa ko ina ta gudu ba a dai sake jin duriyarta ba ita da Laurat. Sanin cewar Abdul ba shi da kwanciyar hankali a halin yanzu ya sanya ni rabuwa da shi, na ma kauda kaina daga abin da ni ya ke damuna a kashin kai na, shi kuwa ko kasuwa sai ya daina zuwa, a 51 ko yaushe yana zaune a cikin gida cikin halin zurfafa a tunani, sati guda ya shude cur! "yan sanda suna binciken Sakinah domin tura maganarsu kotu. A ranar da satin ya cika ne Zuwairah ta zo gidan, tun daga soro ta fara bambami "banzan mahaukaci duk ka tara matan banza a gida, daga barauniya sai mai neman mace 'yar'uwarta" A wannan halin ne Jimmai ta san abin da ya faru, ta zo ta sameni a daki " Karimah da ma Sakinah "yar neman mace ce shi ne ki ka boye min?" Na yi shiru, ban ce mata komai ba, ta ci gaba " to wai ke kuma me ya sa take ce miki farauniya ?. Shi ya sa ma kika ga gaskiya ko kula ki bana yi " Hawaye ya zubo min " Jimmai ni wani sharri aka kulla min da babu damar na fita. Ana biki a gidan su Abdul aka saka min kayan wasu a jaka, shikenan kuma aka ce nice na sata, to amma abin lura sai a ce barawo sau daya kawai aka kama shi da kayan sata?" Ta girgiza kai " ba zai yuwu ba, da akwai dai wani kullin Kasa" a Zan tukan Zuwairah suka dakatar damu"Abdul wallahi Hajiya tace ko dai ka saki barauniyar can ko kuma babu ita ba kai. Dole nema ka sakewa rayuwarka tsari, ba zai yiwu ba kullum mutane suna ganinka a banzace saboda matan banza daka jajibo ka zuba a gida, ka hakura da Jimmai kawai ta isa" A sannan ne na jiyo maganarsa da alama tuni ya gama fusata "ya isheki Zuwairah, zancen 6arauniya ya fita daga bakinki, duk wanda yace Karimah ta yi sata ko waye karya yake yi " Ta rike baki a lokacin tuni idona na kansu "yanzu Abdul ni kake fadawa irin wannan maganar? Idan kai kanka ba ka yarda ta yi satar ba me ya sa kawatsar da ita ?' 52 Eh wannan ra'ayina ne, dan ta kashe min 'ya da ganganci na yi watsi da ita, amma maganar sata kururuwarku ce ta mata ta banza da ta wofi' Ta tsagalgale " to ai dai har da uwarka a maganar, in kuma ka се karya ne har ita ka karyata kenan" Ya mike tsaye a fusace " Eh na karyata ta din, maza ki fice min daga gida ko kuma ranki ya baci yanzun nan" Ta tsaya kikam tana kallonsa, ya sake daka mata tsawa " ki fice min daga gida nace yanzunnan, idan ba haka ba kuma zaki sha mamaki" Ta nuna shi da yatsa " wai kai ba nice yayarka ba za ka yi min rashin kunya?" Ya Kara hasala "yayar banza yayar wofi, ko ke uwata ce dole ne ki fice min daga gida. Da kina rike girmanki da ina ruwana da ke? Da dole na baki respect, amma yanzu ni da ke ba wani batun sassauci" Ta jinjina kai 'lallai wuyanka ya yi kauri Abdul' Kau! Ya zabga mata mari "I say find your way out" Ta rike kunci gami da kurma ihu " shike nan Abdul ka ci min mutunci a gaban matanka, to wallahi sai ka gwanmmace ba ka yi ba" sai ta nufi waje tana kuka Nan da nan tausayin mijina ya kama ni, wani hawayen nadama ya fara zubo min, ashe shi kansa baya goyon bayan sharrin da aka yi min. Ashe dai matsalaersa it ace mutuwar Hamidah. Ban zarge shi ba akan wannan, na sani yana son Hamidah kamar rai, tsautsayi ya zo ya hadu da ganganci har ta mutu, idan kuwa haka ne zan yi kokari na shawo kan mijina. Sai na cigaba da zubar da hawayen bakin ciki. Na farka cikin dare wajen karfe biyu da rabi, a sannan ne na fito domin yin alwalla, a wannnan kwanakin haka na ke yi domin mikawa ubangiji kukana. .............. 53 Sai na gurfana a gabansa na sunkuyar da kai, tsahon lokaci ban ji wani abu ya faru ba, babu zato sai na ji ya yi jifa da wukar, sai kuma na ji hannunsa ya rike hannuna, a sannanne na dago kai na dube shi, hawaye na ga yana fitowa daga nasa idanun. Ya bude hannayensa biyu " come on Karimah" Sai na ta so da sauri na shige, shi kuma sai ya mayar ya rufe, hannunsa ya cigaba da zarya a cikin gashin kai na " na yafe miki Karimah, na yarda da cewa haka Allah ya so da lamarinsa, da sannu zan sake komawa da ke irin rayuwarmu ta da. Nima Karimah ina mai takaicin rashinki a kusa da ni, sawun giwa ne dai ya take na rakumi rashin Hamidah ne ya sani daukar wannan mataki, kin yi gaggawa da yawa, ba zan taba yarda ba Karimah a ce kin yi sata, akan haka kuma ina iya batawa da kowa. Sai dai kash! Kin yi saurin yanke hukunci da ki ka hau babur a matsayinki na matar aure, wanda hakan ya yi sanadin rasuwar 'yata da na kwallafa raina a kanta " Na kara kwantar da kaina a jikinsa, har yanzu ban daina zubar da hawaye ba. "kaya fe ni mijina, kuskure ne na riga na yi, kuma zan yi kokarin kiyaye irin haka a gaba" ya dora habarsa a kaina " na yafe miki duniya da lahira Karimah, Allah kuma ya maye mana da watae Hamidar " Na dago fuskata daga jikinsa cikin farin ciki, muka zurawa juna ido tsahon lokaci, daga karshe sai ya kamani muka mike tsaye, a tsarin lissafi wannan rana tace. Shimfidarsa'muka zarce kai tsaye. Sallolin da ban yi ba kenan a ranar, maimakon haka sai na nemi ladan a wani bangaren daban. Muka kwana muna farantawa juna rai ni da Abdul. A washegarin shiryawar mu ne da Abdul yayarsa Zuwairah suka zo da mahaifiyarsa. Tun da suka shigo na fahimci ran Hajiya a bace yake. Na durkusa na gaiđa ita, amma ko kallona sai ta ki yi. & Kai tsaye ta zarce dakin Abdul, yana shiye-shiryen fita ya fara gaida ita, amma shima sai ta kI ta amsa. " ka ga ba wai zuwa na yi ka gaishe ni ba, gaisuwar kánnenka na gída ma ta isa, zuwa na yi ka rubuta takardar saki a gabana. In kuma kai ba za ka saki matar can ba to ni zan sake ka" Ya koma ya zauna akan kujera "hajiya ke fa babba ce, bai kamata ki dinga biyewa zantukan su Zuwairah ba, in har za ki biye musu sai su bata tsakani na da ke" Zuwairah ta taso kamar ta cinye shi "wáto mu ka mayar da mu shaidanu ko ? Har ma da mari na jiya akan 6arauniyar can" Ya tashi tsaye a kufule " look Zuwairah kar ki sake cewa mata ta 6arauniya, wallahi a kan ta zan bata miki rai" "na fada barauniya" ta maimaita Tuni idanunsa suka rufe, yama manta da cewa a gaban mahaifiyarsu yake, jika ke kau! Ya kwada mata mari. Hajiya ta fashe da kuka " yanzu Abdul dan rashin mutunci a gabana zaka mari yayarka ? To wallahi ba ka isa ba dole nema ka rabu da waccan ballagazar yarinyar" Ya dubi mahaifiyarsa cikin nutsuwa " Hajiya me ya sa ki ke biyewa wannan matar? Lokacin da tana shukawa mijinta rashin mutunci na taba tsoma baki? Bance uffan ba har ya ga ji ya sake ta, to ni kuma yanzu sai tace dole na rabu da mata ta? To wallahi babu in da mata ta za ta je, ko "yar fashi ce ba barauniya ba ina son kayana, kuma dole a yi hakuri a bar mu tare." Hajiya ta dafe kirji "yanzu Abdul ni ka ke fadawa wannan maganar?" "hajiya kin san bazan taba fada miki magana ba, kuma ni na sani Zuwairah ce ta ke zuzuta lamarin. Kuma wallahi sai na yi maganinta " Ta nuna shi da yatsa " ka ga ba wani batun Zuwairah, umarni na ne kuma dole ka cika, dole ne kayi duk yanda nace ina so, idan ba haka ba kuma wallahi na tsine maka" 56 Ya girgiza kai cikin jimami "haba Hajiya, kefa mahaifiya tace na sani ba za ki taba so kiga na shiga wani hali ba, to dan Allah ki kyale su Zuwairah da hayaniyarsu" Ta daka masa tsawa. "zaka bi umarnin ko kuwa tsinuwar ka zaba? Dole ne a yi daya a cikin wadannan" Ganin abin zai yi muni ya sanya ni matsowa da sauri " Abdul yi hakuri ka bi umarnin mahaifiyarka, iya abin da Allah ya hukunta na zamanmu kenan" Ya girgiza kai "ba zan sake ki ba Karimah, in kuwa har na sake ki to zan saki Jimmai ma, kuma ni da aure har duniya ta tashi" Uwar ta zura masa ido " ai kuwa ko gwauron dutse za ka zama sai ka sake ta, in ka sa ke ta in ya so ka zauna haka" "to shi kenan Ummah haka ki ka ce ko?" "Eh haka nace"" Sai ya zaro biro da takarda daga aljihunsa, take anan ya rattaba ya miko min, da karba na dora hannu aka ina kururuwa" "Eh sai a kwashe kaya " zancen Zuwairah Ni kuma sai na nufi daki ina kuka, tashin hankalima ya hanani duba ko saki nawa aka yi min. Abdul ne ya fara fita daga gidan cikin fushi, daga bisani saі Hajiya da Zuwairah ma suka fice, ni kuwa na yi ta rusa kuka a daki, na kai rabin awa ina yi, sai na jiyo takun kafa na zuwa ciki. Ban daga kai ba balle naga kowaye, sai na ji an dafa bayana "Karimah yi shiru ki saurare ni" muryar Abdul ce ta fadi haka Na dago cikin takaici '" shi kenan Abdul an raba mu, wayyo Allah na shiga uku!" Sai na dora hannu aka. Ya tarairayo ni jikinsa "kiyi shiru nace ki ji Karimah, duba takardar kiga saki nawa na yi miki?" Na dauko takardar cikin mutuwar jiki, ina mai girmama tashin hankalin da zan fuskanta yayin karanta takardar. Ya rubuta 6aro-6aro" ni da ke mutu ka raba Karimah" ban san sa'arda na jefar da takardar ba. Na rungume shi, na ajiye wani irin numfashi, "amma Abdul ka cece ni, da a ce sakina ka yi yaya zan yi ?" 57 Ya kara rike ni a jikinsa "ba zan taba sakinki ba Karimah, da zan sake ki da na aiwatar tun sanda Hamidah ta mutu, a sannan ma na kasa ballantana yanzu?!" Sai ya jona bakina da na sa. Kaunarsa ta kara ratsa zuciyata. Ya sake ni " kin san yanda za'a yi yanzu Karimah ?" Na girgiza kai " sai ka fada' "to ki shirya ki tafi gida, zan sa bayan kwana biyu a zo a kwashe kayanki, ni na san inda zan mayar da ke, in ya so duk ranar girkinki sai na dinga binki can muna more rayuwarmu, ko yaya ki ka gain? Dan yanzu idan Hajiya ta san ban sake ki ba to za ta iya tsine min din, ni kuwa ina shakkar iya rayuwa babu ke" Sai na kara lafewa a jikin Abdul "to mijina nagode, Allah ya bar ni tare da kai har abada" Yanda Abdul ya tsara haka din a ka yi, yasa aka kwashe kayana, gidan wani abokinsa aka kai, a can muka ci gaba da more rayuwarmu ta aure. Kusan nace yanzu mun fi more rayuwa fiye da da, kullum Abdul ba shi da zancen da ya wuce na taimaka na sake haifo masa wata Hamidar kuma wai ni ya ke so na fara haihuwa kafin Jimmai, ni kuwa ina ganin wannan ai wani lamari ne daga Allah, yaushe matar da ka ke kusantarta kullum kace wai wata ta rigata haihuwa, lamari dai sai a barwa Allah. Da safe bayan mun tashi na hada mana shayi, muna cikin sha Abdul ya dube ni " Karimah dan Allah idan Allah ya kuma ba mu bebi ki kula mana da hi sosai, saboda duk duniya babu matar da za t haifa min da na kauna ce shi dari bisa darikamar ke, ina ga hakan yana da nasaba da irin kaunar da na ke yi miki Karimah, ban da Allah ya riga ya halittani a sahun.maza na matakin farko da babu yanda za'a yi na auro wata mata bayan ke" Ya kamo hannuna ya rike "bari na fada miki gaskiya, duk wata mata da kika ganni da ita muna zaune ne kawai, amma a 58 zahirin gaskiya na fi kaunarki, ni ina zaton ma ran mu daya da k e, watakila ma lokaci guda za mu mutu" Na kwantar da kai na a kan tebur "to Abdul ai babu komai, abokiyar zama in dai ta gari ce ai babu matsala, ni dai irin su Sakinah na ke gudu". Sai naga ya saki hannuna, fuskarsa ta canza a lokaci guda, nan da nan hankalina ya tashi. Na taso da sauri na tsuguna a gabansa " Abdul me ne ne kuma ya faru?" Ya girgiza kai cikin jimami "Karimah kin taso min da bakin ciki ne, a duk da sanda na tuna halin da na ga Sakinah da kawarta na kan fita daga hayyacina. Ina mai neman gafara ki Karimah bisa hadaki aure da na yi da wannan Kazamar, sai dai tun farko laifi na ne da na boye miki gaskiyar lamari, a gaskiya Sakinah ba 'yar mai gida na ba ce, 'yar wata mata ce da ta ke zuwa siyayya rumfarmu, duk sanda zata zo tare suke zuwa, kuma babu abin da ya ja hankalina da ita sai siffofin jikinta da na ke gain, idona ya rufe akan son naga na aureta, na 'manta da cewa ba bu yadda za'a yi "yar mutunci ta kasance haka, shikenan nakama fadi tashi, ban sami nutsuwa ba har sai da na kwaso ta, daga baya kuma kinga abin da ya faru, wai kuma sai sannan na ji cewa ashe ma shegiya сe" Sai ya dafe kai " kaitona! Karimah na yi matukar cutarki. Dan Allah ki yafe min," Sai naga yana zubar da hawaye. A hankali na kai hannuna zuwa fuskarsa na fara kokarin kwantar masa da hankali. Hannaye na kuma na masu share masa hawaye " kar ka damu Abdul ita rayuwa gaba ki dayanta tana tafiya ne bisa kaddarar ubangiji, duk kuma abin da ya hukunta sai ya afku, kai dai Allah ya kiya ye gaba" Sai ya bude hannayensa, ni kuma na taso da sauri na shige, ya mayar ya rufe da ni " ina kaunarki Karimah irin kaunar da bakina ke gaza bayyana miki" Na kara kwantar da kai na a jikinsa "ni ma ina kaunarka mijina kaunar da zuciya ta ta gaza kwasheta duka" Muka kasance haka cikin kaunar junanmu Ina zaune da rana a tsakar gida domin shan iska, ba wai iskar kawai na ke sha ba ina haďawa ne da tunanin irin rayuwar gudun hijira da muke yi ni da mijina, to yanzu ranar da mahaifiyar Abdul ta gane ya ya za mu yi ken an? 59 A wannan hali ne a kayi sallama, muryar da na dade ban ji ta ba ce. Asme'u ta shigo sanye da kayan aikinta na asibiti. A guje na ta shi na je muka rungume juna. Rabo na da ita tun ranar sunan Hamidah "wail Ashe rai kanga rai " na fada sa'arda na ke rike da habа " wallahi kuwa, ai cewa na yi tunda ke kin ki zuwa bara ni na zo, ban ma san kun tashi ba sai da na je matar gidan ta ke shaida min." Na ja ta daki muka zauna, muka sake gaisuwa ta musamman da ita, sannan na yi mata Allah sanya alheri akan aikin da ta samu. Ni dai duk kunya ta ishe ni da ban je har gida na yi mata murna ba. Ta dubeni " in ce ko dai ba siyar da gidanku ku ka yi ba Karimah?" Na girgiza kai " ba siyarwa muka yi ba, za mu sake komawa can bayan wani lokаci" su wadancan sai su tashi kenan? Na gama ai na şan matar, tana zuwa asibitinmu" Na dubeta "to ta tashi ta je ina, bayan ita ma gidan sune?" "ban gane ba" ta fada cikin wani yanayi da ke nuna yanda lamarin ya daure mata kai Na yi murmushi " ai mijinmu daya da ita, kishiya tą ce wadda Abdul ya auro daga baya" Ga mamakina sai naga jakar hannun Asma'u ta sullube, ta gwale idanuwa gami da dora hannaye biyu aka, sai kuma ta fara sallallami. Na kalleta cikin kidima "me ne ne ya faru Asma'u ?" Ba amsa ta ba ni ba, maimakon haka sai ta kife kai a kas. Na iso gare ta da sauri, hannu na sa na dago kanta " dan Allah me ne ne Asma'u?" Ta kalleni kallon da ke nuna irin firgicewar da ta yi, ina iya-ganin idanunta kamar su fito saboda tsabar tsoro. Ta fara magana da wani irin lafazi " ta faru ta kare Karimah, wannan yariyar tana daga wani tsari da muke da shi a asibiti. A duk wata tana zuwa karbar magani " Ta sassauta murya "Karimah wannan yarinyar cutar kanjamau (Aids) ce da ita" Dan Allah "yan'uwa makaranta a yi hakuri sai a tara a littafin kwashe kwashen miji na biyu. Na gode taku Rufaidah 60 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 5 of 5