da abokanan zamanta biyu, sannan
muka gaisa da yayyen Abdul mata su biyu Binta da Zuwaira daga bisani muka gaisa da amarya Maimunatu har na dan yi mata tsiya. Sauran Kanne kuma suka zo suka gaida ni. Daga haka na kaiwa daya daga iyayen Abdul Hamidah. Na ajjiye jakata gami da canza
25
kaya sannan na zo na shiga sahun masu girke-girke. Mun yi ta yin abubuwa da dama, kama daga yanka nama, yankan kayan miya har
ya zuwa wanke farantan abinci. Daga nan muka hau girki gadan- gadan. Fage ne na yara mata masu ji da kwarewarsu a kicin.
Waccan ta kawo tata gwanintar wannan ta bayyana ta ta. A haka muka hada kwarya-kwaryan abinci mai dadin dandano. Babu shakka yau mata za a yi santi in aka yi wasa wata har sai bayyana tuggun da ta shirya ta kori kishiya. Da muka kammala
dafa abincin ne mu ka shiga raba shi. A lokacin kuwa kowanne sashi na gidan a dankame yake da mutane, wasu ma har såida suka tafi makota.
ta
Muka yi ta aikin raba abinci daga karshe mu ma 'yan girki mu ka ja namu farantin bayan da muka tabbatar kowa ya wadatu.
創
Muna kammalawa na bawa Hamidah ta'sha, na sake mayar da
ita ni kuma na shiga wanka, wanda hakan ya sake fito da ni a
matsayjna na wacce ta zo biki. Na sake daura atarnfar anko dina.
Ai fa sai na koma dakin imu-imu. Hira ta kaure babu kakkautawa.
Anar yammaci ya.riske nu aka fara shirye-shiryen watsewa.
Na dubi Sakninah bayan da'na mike tsaye na goya Hamidah
"zo mu tafi gida Sakinah"
"au Abdul din ya zo ne ?" ta tambaya.
Na girgiza kai"bai zo ba, akwai abin da ya sa ba za mu jira shi ba"
cewa ya yi kar mu jira shi?"
"a'a ba haka yace ba, ke dai wani abu ne da bam, bari idan mun
fita zan fada miki"
Itama ta mike tsaye. A sannan ne wata budurwa ta fara cigiyar
takalminta da ya yi laya a kofar daki. Abin har yana shirin sata
kuka kamar yadda ta fada mai tsada ne kuma yau din nan ta fara
sashi.
Har ma ta fara kuka muka sa namu takalman alamun da suka
nuna mu namu ba su 6ata ba.
Mun nufi dakin mahaifiyar Abdul kenan domin yi mata
salláma a kayi kiranmu. Sai mu ka sake komawa. Wata mata muka
26
gani a tsaye ta yi zuru-zuru. Wai ita kuma Jakarta aka
Kamar yadda ta fada 'yar karama ce, akwai kudi naira dubu uku a
ciki baya ga na'urar sadarwa. Na dubi Sakinah " to mu tafiya bata
same mu ba "
Wata matar ce ta fara Magana " to gaskyi ya 'yan'uwa hakuri
za ku yi a caje kowa kun san dai mu kadai ne muka zauna a dakin,
tun da babu wadda tatafi kunga ai an yi babar sa'a" sai aka fara caji daga jaka har zuwa wanin jaka hatta zani sai mace ta kwance duk
dai dan gudun kada ta Boye a ciki. Ni dai na zura ido ina ganin
ikon Allah. A haka har bincike ya iso kanmu ba tare da an ga ko da allura ba
Sakinah aka fara cajewa sannan ni. Na ajiye jakata a kasa "ku tsaya
na fiddo muku da komai a hankula saboda akwai fidar yarinya a
ciki "
"a'a Hajiya ai kowa ma dubawa akayi ba wai shi ya dubawa kansa ba. Da kowa zai dubawa kansa da sai a ce kowa ya bincika a gida "
Jin haka ya sanya na sallama musu suka fara binciko kayan daya da daya, kayan da na yi girki dasu ne a sama. Ana debe su sai
abin da yafi kowanne daure min kai a duniya ya afku. Cikin zakuwa da saurin hannu matar tafi to da duk abin da ake nema
guda biyun. Daga jakar har takalmin duk gasunan a ciki. Sai na sami kaina cikin daukewar numfashi. Bakina kuma ya rasa kalmar da zai fara furtawa
"haba gaskiya mana ta ke ta hankoron su gudu, mijinsu ma cewa
ta yi kar su jira ashe dai ta san abin da ta shirya kenan'"
Zancen matar da ta ke da jakar kudin kenan " amma dai kin bata wayonki" inji wata dabam. Anan fa hayaniya kala-kala ta tashi kowacce macen da ke dakin tana wadai da ni. Kamar wutar
lantarki sai zancen ya game kowacce kusurwa ta gidan wai an kama barauniya. Ni kuwa har yanzu bakina ya kasayi min alfarmar da zance wani abu,Sai kawai na fashe da kuka.
Cuncurundon matan aure da "yan mata suka rinka zuwa kallona, wani abin takaici har da surukaina, mahaifiyar Abdul da ta zo taga wai nice barauniyar sai ta fashe da kuka " amma yariyar
27
nan
hannu
kin ba ni kunya, yanzu me mijinki yagaza yi miki har za ki sа ki dauki kayan mutane? To wallahi bada mu ba" Ni kuwa a wannan lokaci uban kukan da nake cima bazai bari kalmomisu fita daga bakina ba. Nan na ji wasu suna cewa kyau a
yi mini dukan tsiya.Wasu kuma cewa su ke a bari kunya ma kawai ta ishe ni. Sai dai ni da za su nemi zabina a lokacin babu abin da zai hana nace gara su kashe ni: Babbar yayar Abdul ma ta fara na ta bambamin " amma Allah ya isa Karimah kin dai rigaya kin bata mana sunan zurui'ah amma wallahi sai mun dauki mataki a kanki, bari dai Abdul din ya zo, in har za mu fada masa ya ji to kuwa........"
Ta yi shiru bata karashe ba. Na san dai ba zai wuce tace ya sake niba.
Sai sannan na dan sami bakin magana " wallahi niba ni na dauka ba, sai dai idan sharri ake son kullamin"
"ke rufe mana baki, idan da ba ke ki ka dauka ba me ne ne na ki na
son tafiya gida alhali kuma kinsan mijinku yace kujira shi? Kowa
ai ya san kokarin ki tsira da sune"
"wallahi ni akwai dalilin da ya sa za mu tafi bai zo ba "
"to wane dalilin ne ?" yayar Abdul ta tambaya.
Sai na rasa ta cewa, ni dai ba abin nace cewa ya yi za mu
yi masa kiss ba da dai kunya na fadi hakan, kuma ba na zaton
akwai mahaukacin da zai karbi wannan a matsayin uzuri, duk
kuwa da cewa bisa gaskiya haka lamarin yake. Nan na ci gaba da
kuka.
Banga wasu alamu da suka karfafamin guiwa za'a daina
zuwa kallona ba. Zuciya ta kuwa ina ji kamar zata kama da wuta,
yayin da kaina ya ke min yekuwar cewa darewa zai yi gida-gida.
Na yi karfin halin kai idona ga laluben Sakinah, amma sam bata
tare da ni da alama tana jin kunyar a danganta tada ni ne.
Da na ga cuncurundon bamai karewa ba ne sai na nufi
bandaki. Nufi na na shige can na ci kukana. Amma cikin rashin
sa'a na samu cewada mutum a ciki, ga kuma wasu jerin mutum
ukunnan duk da butoci ahannayensu suna jira afito su shiga.
28
Duk duniya sai tayi min kunci. Ina ji araina inama kasa
zata yarda ta dare na shiga, inyaso na amince ni na shiga nawa
kabarin ke nan. Da zai yi wu kuma sai na tashi sama irin na
tsunutsaye wanda hakan zai rage min kunan rai wanda na ke fama
da shi sakamakon idanu wanda su ke kallona rututu. Hatta gindin
bandakimma bi yoni suka yi. Yau fa na gamu da gamona.
Daga karshe sai na yanke shawarar na nemi hanyar gida.
Nasani hakanne kawaizai kawo karshen namujiyar da ake zuba
min. Ba taro da na yi sallama da kowa ba sai na nufi waje gadangadan. Na kama hanyar da zata kai ni titi. Sai dai kash! Ashe ban
sani ba hakan ya fi muni fiye da komai. Sai da ni ci rabi na ji
kururuwar yara a bayana
" ku da ke ta"
"Garauniya"
'Metasata?"
"6arasuniya"
"takalma"
'Barauniya"
'Da kudade"
'barauniya"
Sai na kara fashewa da kuka, wanda hakan kamar yiwa
mutane shela ne akan cewa nice barauniyar da yaran suke nufi.
Mun yi ta wuce mutane akan hanya ciki har da abokan
Abdul da suka dade da sani na. Har bakin titi yaran suka raka ni
kamar an saka su. Wakar da suke rerewa sai ta hana na sami mota,
duk wanda ya tsaya da zarar ya ji abin da yaran suke cewa sai ya yi gaba. Lamarin ya zame min kunci kan kunci. Babu arziki na
yanke shawarar da ni kai na bata yi min dadi ba a raina. Dan acaba
na tare na hau, domin kuwa shi ka dai ne zai iya daukar kaddarar daukata. Sai dai raina bai so haka ba. Ko sanda ina budurwa ban
taba hawa dan acaba ba. To amma gashi yau na hau saboda larura.
Wasu daga yaran har sai da suka daddakeni kafin babur,din yayi gaba. Ni dai ba ni da ta cewa. Haka mai babur din ya yi ta zabga
29
gudu da ni gab yake da ya kai ni kiyama, amma sam ban kula ba,
domin kuwa tashin hankalin da na ke ciki ya wuce na mutuwa.
Gab da zamu wuce wani junction fan sanda mai ba da
hannu ya daga mana hannu, amma mai babur din cewa ya yi bai ga
abin da zai dakatar da shi ba. Kara murde totur din ya yi har,
Karshe. Wannan ya tabbatar min da cewa dan arufta na hau.
Tuni mai bada hannu ya baiwa na daya titin hannu.
Sa'arda muka zo tsakiya ne wani mai mota akori kura ya
yayumemu jikake kayanı!
Da babur din da ni da dan acabar duk kowa sai ya nufi
nahiyarsa daban, hatta goyon Hamidah da ke bayana 6allewa ya yi
Tuni "yan sanda suka gaggauta kawo agaji. Na yi kokarin
da zan yi domin na mike amma ina! Gabaki daya garin gani na yi
yana wulwulawa. Sai na sake komawa na fadi. Ina iya jin wani
sanyi sanyi a goshina, alamun da suka tabbatar min da cewa jinine
yake zuba. Ban sami "yar nutsuwa ba sai da aka dauki lokaci, a
sannan ne abubuwa suka fara bayyana a gare ni filla filla.
Yunkurina na farko shi ne na gano "ya ta Hamidah. Tana rike
a hannun wani dan sanda, idan har ba gizo idona ya ke yi ba zanin
da na goyata wanda yanzu dan sandan yake rike da ita da shi a jike
yake da jinni. Na yunkura na nufi wajen dan sandan. A sannan ne
idona ya gane min abin da ya fi komai munana a gare ni. Kan
Hamidah neyake zubar da jini sakamakon rabewa biyu da ya yi
ya mafi munin ranar da na taba gani tun bayan haihuwa ta! "
Wata irin kara na fasa cikin kidimewa. Jijiyoyin jikina suka saki
lakwas, hakan ya sanyani faduwa ragwaf! Daga sannan duk abin
da na kara na yi karya.
Ban tashi sanin halin da nake ciki ba sai bayan da na jini
kwance a cikin katifa. Da farko nayi zaton dakina ne, to anma daga
baya sai na fahimci asibiti ne. Tunanin halin da naga "yata shi ne
ya fara fadowa a raina. Ko da yake ina da yakini akan cewa ta
30
mutu, amma duk da haka zucuyata sai ta ci gaba da zolaya ta akan
na dai bincika. Na dan juya kaina kadan wanda ga dukkan alamu
adaure yake tamau, ba kuwa da komai aka daure shi ba illa da
bandeji sakamakon raunin dana ji a goshi.
Sa'ilinnan ne wata ma'aikaciyar jinya ta nufo gadona. Da
zuwa tatsaya a kaina " dan Allah baiwar Allah ina "yata?"
Tambaya ta farko kenan da na fara da ita
"yarki tana nan lafiya" ta bani amsa
Shakka ba bu matar ta cika makaryaciya wai ba ma
maganar rai ba ita lafiya take cewa.
Na kalleta cike da zargi "Hajiya haka ba za ta yuwu ba,
yarinyar da na gan ta kanta ya dare biyu"
Ta girgiza kai "ba haka ba ne baiwar Allah, ba a hankalinki ki
ka ganta ba ne, amma ba na zaton cewa ta ji wanirauni ba ya
gawata "yar tsaga a gefen kunnenta, ita ma na bari ana dinkewa"
Har yanzu ina shakkar abin da matar ta fada " Hajiya kina
nufin kice "yata tana da rai ?"
Ta gyada kai "kwarai kuwa ni nan na bata madara da
hannuna"
Sai na ji wani farin ciki ya kamani, ba na zaton akwai albishirin da
aka taba yi min da yifi wannan dadi. Da ace Hamidah ta mutu ni
kaina ina shakkar ci gaba da zama na tare da Abdul zan iya cewa
yana son ta fiye da ni, to ashe kuwa babu abin da zai hana shi cewa
ganganci na ne ya kashe masa "ya.
Ni kai na na san cewa hawa acaba bai dace da matar aure ba
to amma ni gashi dole ta tilastani hawa. Sai dai bana zaton Abdul
zai karbi dolen tawa a matsayin uzuri. Da kuwa Hamidah ta mutu
da zamanmu yazo karshe.
Koda yake a yanzunma ina shakkar yi yuwar ci gaba da
zaman, a yanda na bar yayyensa da babarsa ina zaton za su
tilastashi ya sake ni. Sai dai har idan Abdul ya sake ni na gama
mutuwa, domin kuwa jininsa ya dade da cakudewa da nawa.
Shima kuma ina shakkar ya iya sakina din, domin Abdul yana
yi min kauna ta mutuwa, sai dai duk da haka sai idan da gaske
31
'yarsa tana nan da rai idan kuwa ta mutu to ni ma sai a shirya binne aurena.
dakatar
A
da
wannan
ita "
halin ne na ga Nurse din tana shirin tafiya. Na dan Allah baiwar Allah taimaka ki kawo min ita na gani
Ta bata fuska " ke da na fada miki cewa na baro ana dinke mata rauni, da zarar an kammala komai ai za'a kawo miki "yarki" Na yi shiru da bakina ita kuma ta fice daga dakin. Bayan fitar ta da wani dan lokaci sai kuma wasu mutane suka
Gaban
shigo suna sanye da kayayyaki irin na kungiyoyin agaji. gadona suka zo suka tsaya. A sannan ne suka fara da yi min tambayoyi.
" Baiwar Allah ya ya sunanki?"
"suna na Karimah" na amsa musu tambayarsu
"ba mu sunan iyayenki ko mijinki"
"sunan mijina Abdul muna zaune a rukunin gidaje na kundila" Suka nemi lambar gidan na fada musu duk suka rubuta sannan dayansu ya fara yi min bayani
"dama mu ne muka kawo ki asibiti, yanzu kuma za mu je ne musanar da mijinki. Idan kuma kin san lambar wayarsa ta tafi da gidanka sai ki fada in har yana da ita"
"Eh yana da ita " nace da su. Ina maganar ne kamar kaina ya tsage saboda tsabar radadi. Dayansu ne ya zaro tasa ya nemi da na bayyana masa lambar. Na fada masa ya shigar, sannan ya tsaya jiran a dauka'a can.
Ba'a dauki lokaci ba layin yashiga inajin sa'adda mutumin yake shaida masa lamarin a takaice, daga bisani sai ya nufoni dawayar
"ga shi yana so ya yi magana da ke' "Karimah"muryar abdul ta fito ta cikin wayar Na amsa da "na'am Abdul"
" sannu Karimah, a wane hali Hamidah ta ke ciki ?"
"Hamidah tana nan lafiya " na ba shi amsa
Ina jin sa'adda ya ajiye wani dogon numfashi a wayar 'to
alhamdulliilahi ki saurare ni zan zo nan da minti goma "
"to sai ka zo Abdul "na fada
Mutumin ya janye wayarsa " to shi ke nan ma mun huta zuwa bari
mu jira shi anan ya zo." sai suka zauna akan kujeru
Mintuna goman da Abdul ya diba ba su cika ba ya iso. Tun katin
ya iso na fahinci irin gigicewar da ya yi. Da zuwa ma'aikatan
agajin suka fahimci shi ne gaba ki dayansu sai suka mike tsaye.
Hannu suka fara mika masa, daga bisani sai suka nufo inda na ke
tare.
Ya dube ni cikin tausayawa " sannu Karimah ya ya lamarin ya
afkune?"
Daya daga ma'aikatan agajin ya fara yi masa bayani
"akan dan acaba suka yi hadari"
"dan acaba kuma ?"Abdul ya tambaya cikin mamaki
Shiru mutumin ya yi kamar dai yana shakkar amsa masa
tambayar
"to yanzu ina yarinyar da ta ke goye?"
Mutumin ya sunkuyar da kai "ai yarinya sai dai ace Allah ya
rahamshe ta domin kanta ne ya dare biyu"
Da mutumin ya san bala'in da zai biyo bayan bayanin na sa
da bai ma fara jarraba yin sa ba.
Duk hannaye biyu Abdul ya diba ya dora aka " Hamidah ta
mutu?!" Ya mai maita.
Babu zato sai ya nufo inda na ke a kwance a guje. Kwalar
rigata ya kama, ya shake ni ya kuma fara jijjigani da karfi bai kula
da halin da na ke ciki na rashin lafiya ba
"Karimah kin cuce ni kin kashe min 'ya babu abin da zai dakatar da
ni kai kararki kotu. Wallahi sai an bi min hakkina Karimah"'
Nan ma'aikatan agajin suka taru a kansa. Kokari suke yi iya
yinsu domin su bambare shi, amma ina! Babu wasu alamu da suka
nuna zasu ci galaba, tamkar dai Abdul yanayi ne da karfin aljanu.
Ni kuwa in banda kuka babu abin da na ke yi. Nadamar
abin da ya hau da ni babur ta baibaye ni, ina ma a kasa na dabo har
33
gida duk kuwa da cewa tafiya ce mai tsayi in ya so in duk garinnan ne zasu yi min kallon barauniya su kalleni. Na dai tabbata zai fiye min sauki fiye da halin bala'in da na tsinci kaina a ciki yanzu gashi dai har yanzu a matsayin barauniyar na ke, ga shi na rasa "yata, ni kaina kuma babu lafiya, sanhan ga babban bala'in rashin jituwa mai karli da ta 6ullo tsakani na da mijina Ya mafi kasancewar ranar bakin ciki tun ranar da aka halitta
ni! To wai duk me nene silar faruwar haka? Silar dai ita ce kayan da aka zuba min a jaka. To waye ya zuba min kayan kuma da wacce manufa?"
Sanin kowaye sai Allah munufar kuwa ita ce na shiga
garari. To ga kuwa gararin nan na shiga, gararin da na tabbatar ya
zarce yanda ya tsara a tsarinsa. Anya kuwa ko wuta naga zata kamashi zan iya yafewa?
Tsahon lokaci ma'aikatan agajin suna kokarin bambare ni daga jikin Abdul. Sai da kyar suka ci nasara, bayan da duk na bi na galabaita, suka yi waje da shi sa'ar da ya ke cin alwashin bin hakkin "yarsa da na kasha. Na kara fashewa da kuka sakamakon
faruwar wannan lamari da ya dage wajen jibge min buhuna masu
toliya na tashin hankali.
1
1
1
Sati guda na karar cur a asibiti ina jinyar da tazame min
mafi rudani da muni da farko dai bakin cikin dake cin raina, abu na
biyu kuma mijina da yaki ya leko dai dai da sakon daya.
Tun bayan da dai ya yi zuwan farko a ranar hadarin.
Mutane da dama sun yi ta zuwa duba ni, ciki kuwa har da
kishiyata Sakinah. Wadda ita kanta na fuskanci cewa na rage kima
a idonta.
lyayena da sauran "yan'uwa da kawaye sun yi ta zarya a
asibitin, amma dangin Abdul sai dai na hana rantsuwa. Hakan
kuwa yana nuni ne da yadda suka kule da ni. Sa'ar da aka sallame
ni daga asibitin ne lamarin ya zama kiki-kaka, shin gidan iyaye za
34
S
a nufa da ni ko kuwa gidanmiji? A bakin titi aka samar da "yar
Karamar majalisar dattawa, kowa yana fadin ra'ayin sa, a kan abin
da ya ke ganin ya fi. Daga karshe ra'ayoyin da suka karkata akan a
nufi gidan iyaye da ni in ya so daga baya bayan daidaita lamari sai
na koma gidan miji. Hakan aka yi muna shirin tsayar da motar
haya sai ga kanin mahaifina, shike nan muka hau motarsa. Ko da
ya ke an sallame ni ne daga asibiti bisa ikirarin cewa na warke, to
amma ni na san yanzu ne cuta mafi illa zata da baibaye ni. Shin
yaushe ne damuwar rashin "yata zata fita daga raina?
Bayan sallar la'asar ne aka zaunar da ni a daki, mahaifina
da mahaifiyata suka zagaye ni "Karimah muna so ki zayyana mana
duk abin da kika sani dangane da lamarinki daga farko har karshe"
babata ke nan take umarta ta. Na sunkuyar da kai a lokacin hawaye
ya fara zubowa daga idona. Cikin karfin hali na bayyana musu duk
abin da ya faru daki-daki ban rage komai ba.
Da na gama yi musu duk bayani, mahaifina ya numfasa "to
me ne ne dalilinki na matsawa akan ku tafi gida alhali kun yi da
mijinku cewa zai zo ya dauke ku?"
Zubar hawayena ya dadu ina ga abu mafi a'ala shi ne na
kawar da kunyar da na ke ji gefë guda, na fadi hakikanin abinda da
yasa. To amma da na yi wani tunani sai na ga gara na yi shiru da
bakina, dan bana zaton da akwai wani mahaluki da zai yadda
wannan shi ne kadai hujjata, kuma da na ke ta ikrari cewa sharri
akayi min waye ya yi min sharrin ke nan ? Ni dai babu wani
mutum dana rika. Mahaifina ya katse min tunani " baki ba ni amsa
ba Karimah"
Nasa gefen mayafi na share hawaye, "Abba shi Abdul din
ya san abin da ya sa na yi hakan, in ka tambaye shi zai ce ya san da
maganar "
"to ke me yasa baza ki fada min ba ?"
Na yi shiru ban ce komai ba. Da yaga bana shirin fada sai ya
rabu da ni. Daga bisani ya ke shaida min cewa ya aika a yi kiransa.
Ina nan zaune kanina ya shigo, ina zaton kuma shi aka tura wajen
35
Abdul. Na kara tabbatarwa bayan da na ji zancen da ya shigo da shi.
"Abba wai yace ka yi hakuri ba zai iya zuwa ba"
"kuma ka ce ni ne na ke kiransa?"
Habib ya jinjina kai "na fada masa haka"
yanzu a ina ka baro shi ?"
"yana gida "Habib ya bayar da amsa
Sai mahaitina tashi yasa hula, ya dubi mahaifiyata "Hajiya zan je na same shi da kai na" sai ya dauki makullin baburinsa ya fita. Na zauna nan shiru cikin tagumi. Na sani ba abu ne mai dadi
a dinga bin miji a gindi a gindi ba, sai dai duk da haka ban gano illa ba da ake neman tarar da Abdul. Ba dan komai ba kuwa sai dan yadda na ke kaunar mijina.
Kusan awa biyu mahaifina ya karar kafin ya dawo ya dube ni "ki shirya ki tafi gida, na tattauna komai da shi"
"ai kamata ya yi a rakata" zancen mahaifiyata
"ah haba! Sai kace dai wacce ta yi yaji? Ki fa tuna ba yaji tayo ba"
A haka na mike, na shirya tsaf, sannan na yi wa iyayena sallama, na kama hanyar gidan mijina.
Hakika ina mutukar son komawa gidan, amma ina shakkar irin kallon da Abdul zai yi min sakamakon rashin Hamidah. Bayan
wasu "yan mintuna na iso kofar gidan. A zato na ina zuwa zan ga motar Abdul, to amma zaton nawa bai tabbata ba. Nasa Rafata a
gidan zuciyata na dakan uku-uku, kai kace zuciyar wani
matsoracin da ya je satar dan zaki. Sallama na yi sa'ar da na kure
soron, a tsakar gida na tarar da Sakinah. Wani kallo ta yi min da
ban san manufarsa ba. Daga bisani sai tayo masa rakiya da
tambayar raini " au har kin dawo?"
A iya rayuwata ban san da irin kalmar da ake amsa irin wannan
tambayar ba. Sai na ari " Allah ya hukunta"
Nasa mukulli na bude dakina ina shiga kura ta yi min maraba.
Wannan kuwa domin tulin kwanakin da ya dauka ne babu shara.
Kamata ya yi na fara daukar tsintsiya na share dakin. To amma ba
hakan na yi ba kujera nafada cikin tagumi.
36
:
A wannan halin ne na hango gadon Hamidah. Wata damuwa
da bakin ciki suka da baibaye ni, sai na fara ragewa kaina su ta
hanyar kukа.
Abdul bai ta shi dawowa gidan ba sai can dare, yana dawowa
kuma ya shige daki. So nayi na je na same shi to amma sai na ji ya
rufo kyaure, ya kuma danna sakata bias wannan dalili na hakura
sai da safe.
Da asubah ina idar da sallar asuba na nufo dakin Abdul. Ga
mamaki na, sai na same shi arufe. Nan na shiga tunanin to wanne
kenan daga biyu, shin fita ya yi ko kuwa har yanzu tashi ne bai yi
ba?
Domin amsar tambayar sai na koma kofar daki na zauna. Ina
nan zaune har lokacin da rana ta kori alfijir, haske ya bayyana
sosai. A wannan lokacin na tabbatar da cewa fita ya yi to amma me
yasa zai yi sammakon fita haka? To me yiwuwa da wani uzuri ya
kwana. Sai na tashi na koma daki da nufin sai ya yi dawowar
yamma.
Ina nan zaune na ji sallama, da jin muryar na gane mai ita
Zuwairah ce yayar Abdul. To me ya fito da ita da wuri haka? Ada
dakina na yi zaton zata shigo, to amma sai na ji ta zarce dakin
Sakinah. Ina jin sa'ar da ta ke tambayarta Abdul " ya fita tun
asubah"
"to me ne ne ya fitar da shi da wuri haka ?"
"baya so ne su hadu da waccen"ta bata amsa.
Sai gabana ya fadi ras! Ashe ni Abdul ya gujewa kenan. Gano
hakan sai ya sani fashewa da kuka. Na sani da wuya idan Sakinah
ta san ina jin abin da suke fada. Sai suka ci gaba da hirarsu kai
tsaye.
Zuwairah ta ci gaba "ni kai na ai akan matsalarta na zo,
Hajiya ce tace kada ya kuskura ya maido da ita. Ashe 'yar nacin
tuni ma ta dawo. To amma duk da haka ba ta baci ba, anan din ma
37
dole ne ya sallame ta. Ba zamu bari haka kawai a Bata mana sunan Zuriya ba. Tuni zance ya game ko'ina cewa matar Abdul