Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
ta yi sata. To ina dalili wallahi sam! " Duk wadannan maganganu ana yin su ne a kunne na. Ba su haifar min da komai ba illa bakin ciki da hargitsewar zuciya. To da wane zan ji? Da satar da aka kala min ko kuma da mutuwar "yata? Ni dai abin ya zame mun shege da hau ka. Bayan wani lokaci sai Zuwairah ta fito ta tafi, ba kuma tare da tayi kokarin kula ni ba. A daki na yini ina cin kuka. Rannan na fara ganin wani cin mutunci wai abincina ake shaida min cewa an bar shi a tukunya, saboda haka sai dai na je na debo kenan. Sai dai abin da bata sani ba, ni sam abinci ba ya raina. Abdul bai dawo da yamma ba kamar yadda ada yake al'adarsa. Da daddare ma ba shigowa yayi cin abinci ba, yaro ya aiko ya karbar masa. Da na ga dare ya dan fara tsayi, sai na fito daga dakina. kofar dakinsa na zo na tsuguna, na san dai idan yazo budewa aj zai ganni in yaso da ya bude sai nafada dakin. Kaga sai mu daidaita lamuranmu cikin sauki. Anan na kasance tsugune tsahon lokaci, ga sanyi ana yi, amma sam ban damu ba. Ni dai burina na kai gasa min biyan bukata. Sai can wajen sha biyun dare Abdul ya shigo. Na daga kai na kalle shi, ya yi matukar rama da baki. Cikin karfin hali na yi masa sannu da zuwa. Bai ko kale ni ba balle ya amsa. Sai yasa mukulli ya bude dakin. Kafin yasa kafarsa nayi kundunbala ciki. Ya daga labule ya kalle ni cikin daurarriyar fuska sai ka ce ba ita ce fuskar da take kasancewa cikin fara'a ba. Fuskar da bakina ya yi zarya a kanta fiye da sau cikin kwando " fito min daga daki" ya fada da wata kakkausar murya. Muryar da ada na ke shaukin ji to amma gashi yau tana ba ni tsaoro "ki fito min daga daki" ya sake maimaitawa. Sai na fara kuka " dan Allah Abdul ka yi hakuri, ka gafarce ni wallahi kuskure ne na yi" 38 A sannan ne ya sako kafa dakin, a zatona hakura yake shirin yi, amma ga mamaki na sai naga ya dauko bargo. Na sha gabansa da sauri " dan Allah Abdul ka tsaya ka ji" Wani kallo ya yi min wanda ina zaton a wajen soja ya koya. Nan da nan jikina ya dauki rawa. Na kai hannu na ya zuwa rike hannunsa har yanzu kuwa ban daina kukan ba. Hannu daya ya sa ya bangaje ni na tafi taga-taga na hadu da bango, har kai na sai da ya amsa kum! Amma ko waiwayowa Abdul bai yi ba. Sai yasa kafa ya fita. Na daddafa bango na mike cikin jin jiki. Sannan nima na kama hanyar fitowa daga dakin. A kofar dakin Sakinah na hangi Abdul yana bugawa, ba'a dauki lokaci mai tsaho ba, na ga fitilar dakin ta kama. Na ji ya yi magana sai kofar ma ta bude. Na hango ta sanye da kayan barci, jan hannun Abdul ta yi zuwa ciki. Sai aka sake kulle kofar kafin daga bisani fitilar ma ta sake mutuwa. Na ji juwa ta debe ni, na ji tamkar na fasa kara. A haka na daddafa bango zuwa nawa dakin. Ina zuwa na fada kan kujera anan na ke sa ran cinye nawa daren da ni da sabon mijin da ya aure ni, wato azababben kuka. Na ci gaba da kasancewa tsahon kwanaki cikin halin da ban san a matsayin da Abdul ya a jiye ni ba. Ni dai bai ce a ba ni girki ba, ita kuma Sakinah ba ta ba ni ba. Ko kuma shi ne yace kar tabani? To ni dai ban sani ba. Kullum sai dai idan ta gama abinci ta turo min nawa kofar daki. An dai mai da ni kamar wata tunkiyar da ake kiwatawa. Ni kuma gashi yanzu sam ba ni da kima azuciyar Abdul. Da ace ina da kima ma sai na yi magana. Amma yanzu sai dai na yi hakuri da duk cin kashin da zan gain. Na yi iya kokarina domin ganin cewa na shawo kan Abdul amma abin ya ci tura. Saboda ni ya ke ficewa da wuri, kuma 39 saboda ni yake kin dawowa da wuri. Bias wannan dalilin sawun Zuwairah uku ba ta samun sa. Ni abin na ta sai na keganin kamar da biyu. Ko kuma dan na ta auren ya mutu ne ni ma ta takura akan sai an sakeni "? To me yi wuwa haka din ne. Sai na ci gaba da mika lamura na ga mahalicci. Ina zaune a tsakar gida na ji sallama na daga kai domin ganin kowa ye. Laurat ce kawar Sakinah kallona kawai ta yi ta kau da kai, daga bisani cikin wata murya mai ciki da iyayi tace " sannu ko". Hannu kawai na daga mata domin hakan shi ne dai-dai da amsar gaisuwarta. Ina mamakin yadda take tafiya cikin wata irin rangwada ita ba wani kyau ba. Gashi kuma duk kurajen fumfus (pimples) sun bata mummunar fuskarta. Ta tube takalmanta za ta shiga fakin Sakinah "kai! Kai! Shigo da takalmin ki" Sakinah kenan ta ke gargadinta Wani abu ya zo ya kulle min zuciya, wato an mayar da ni barauniyar takalma saboda haka a shiga da su kar na dauke. Anan bakin ciki ya ci gaba da kwakular zuciyata. Da abin ya yi yawa sai na tashi na shiga daki, a can na ci gaba da tunanin lamurrana. Bakin cikin da na ke fuskanta duk yabi ya ko dar da ni. Ni kai na san cewa mun bambanta da inda na ke a wani katon hoto a sannan ina amsa sunan Karimah, ba kamar yanzu ba da na zama Kayima. na Ba zan iya kiyasce adadin mintunan da su Sakinah suka karar adaki ba. Kuma in ma har sun yi hira to kasa kasa sukayi ta. Bayan lokaci mai tsaho sai Laurat ta fito kawarta ta tayo mata rakiya har zuwa soro sannan suka yi sallama tatafi. Ni kuwa na ci gaba da kasancewa cikin halin tunanin mafita. Wani lokaci sai naga ko dai zuwa zan yi gida nafada, to amma sai na ji tsoron kan hakan ya harzuka Abdul, a karshe kuwa auren namu da a halin yanzu yake jone-jone ya karasa ballewa. Ni kuwa na fi son ko rabuwa za mu yi da Abdul to mu rabu cikin mutunci. Halayar da ya ke nuna min sai ta tabbatar min da cewa lallai kunyar Abba kawai ya ji yace na dawo. Amma sam ba na gabansa. Sai dai abin tambaya shin Abdul shima ya amince ne da cewa na yi sata ko kuwa duk haushin mutuwar "yarsa ne?. 40 Amsar dai sai nace Allah masani. Agogon bango ya nuna karfe goma sha biyun rana, a lokacin ni kuwa na mayar da hankalina kan karatun Alkur'ani mai tsarki wannan kuwa domin ragewa kaina bakin ciki da takaici ne. A sannan ne Nusaibah ta shigo, sallama ta yi a dakina, ganin cewa ina karatu ya sanyata yin shiru, ta sami kujera ta zauna. "yan mintuna suka shude wadanda su ka ishe ni kawowa inda ya kamata na tsaya bayan na yi addu'a sai muka shafa tare danusaibah sannan na dube ta da "ina kwana?" Ta amsa min gaisuwata cikin lalaci da kasala wannan kuwa na san saboda ramar da ta ga na yi ne. Ba ta iya jurewa ba sai da ta lambaya "Karimah yaya na ga duk kin rame?" Na sunkuyar da kai " ke dai bari Nusaibah ina fuskantar wani babban gararin rayuwa ne" Ta gwale ido cikin tsoro " me yake faruwa Karimah?" Na warware mata duk halin da na ke ciki da kuma dalilin shiga halin. Ta yi shiru tana tunani daga bisani ta dube ni 'To Karimah kewa ki ke gani ya sanya miki kayan a jaka?" Na girgiza kai " ni babu wani mahaluki da na ke zato, Allah ne dai kawai ya sani" Ta sake tambaya ta " to ke dawa ki ka san ba kya jituwa a wannan lokacin ?" Na girgiza kai "babu wani mutumin da da mu ke takun saka da shi a iya sani na" "har kishiyarki?" "har ita, bayan kin ga irin zaman da muke da ita" Nusaibah ta yi shiru tana tunani, daga bisani sai ta dan yi wani tsaki "kai Karimah akwai alamar tambaya, ni na san kowa ye, amma ki ba ni lokaci zan yi bincike. Ina ganin akan ki zan fara jarraba kos (course) dI na" Na yi murmushi "To Allah ya taimaka Nusaibah" 4 Ta amsa " Amin" ta sake dubana " kuma da gaske duk yanda na sanki da, da Abdul yanzu baya kulaki?" Na jinjina kai " wannan gaskiya ne Nusaibah, dan ni nan da ki ka ganni ajingi ne nake" "kamar yaya a jingi ne ?" Ta nemi bayani da sauri ni kuma na fara haskaka mata. "kin ga đai da farko ko girki ba na yi, sannan kuma babu wata alaka tsakanina da shi. Kama daga maganganu har zuwa hakkin aure. Kuma na yi iya yina akan na lallabe shi amma ina! Rannan ma da na same shi a daki baro ni ya yi acan" " Ya baro ki acan ya tafi ina?" Na sunkuyar da kai "shi dakin abokiyar zama na ya shiga" "To wai ita yanzu wane irin zama kuke yi da ita?" Na dan kada kai " to kin sani, muddin miji bai dauke ka da muhimmanci ba, to ita kanta abokiyar zama da wuya ta kula da ke ko kuma ta dauke ka wani abu" "wato itama yanzu ta juya miki baya ken an ?" Na gyada kai "tabbas" to shi ke nan Karimah ki rabu da shi har na kamala bincike na, in yaso sai mu san hanyar da za a bullowa lamarin. Amma dan Allah ki futar da damuwa a ranki. Hakurin da ki kayo kuma tun farko ki daura a kansa. Kar ki kuskura ki kai labarin abin da ke faruwa gida domin da zarar kin yi haka kin gama dagula lissafi. Na jinjina kai alamun gamsuwa Karimah zan koma amma ki ba ni tsahon sati daya da yardar Allah a sannan zaki ji komai " Nima na tashi ina murmushi "to Nusaibah nagode Allah ya bar mana zumunta" Na rakata sannan na koma daki. Hirar da muka yi da ita sai na ji ta sama min nutsuwa aria. Sai kuma na ke hangen cewa duk da wasu matasaloli da na ke ciki sun kusa warwarewa. Saboda haka na sake komawa ga karatuna na Alku'ani mai tsarki. .. Ina zaune a cikin daki da rana sai na ji shigowar Abdul gidan. Na yi mamakin abinda a yau ya dawo da shi a wannan lokaci. To amma sai na hadiye mamakina yayin da na ga wani mutum kaса42 kaca da fenti biye da shi. Bayan sun yi "yan dube-dube da "yan maganganu sai suka fita. To me kuma zai sa a yiwa gida fenti yanzu? Kwata-kwata dai bai fi wata uku ba da auro Sakinah ashe kenan da akwai alamun shakku ace Abdul aure zai kara. Ni dai ina nan tunane-tunanen har wani lokaci. A sannan ne mai fentin ya sake dawowa. Wani katon bokitin roba ya shigo da shi. Dağa bisani sai ga wasu yara suma da nasu bokitan. Sai dai na tabbata su fenti ne a ciki. Bayan "yan share-sharen bango da tsintsiya sai aka fara shafa farar kasa. Daga wani daki da babu komai acikinsa aka fara, ni dai na kasance a nan cikin tunani lallai lamarin yana da rikitarwa. Badan-badan ba da sai na je na nemi bayani a wajen Sakinah. Babu shakka ita za ta sami lábarin kome hakan ke nufi. To sai dai me ne në nawa na'tone-tone ni da a halin yanzu an riga an jingine ni. Sai dai wani abu da na kudurta a rai shi ne muddin dai ya zamana amarya Abdul ya yo, kuma ya ci gaba da watsi da ni to zan nemi takarda ta. Gara na koma can gida gaban iya da wannan zaman na bakin ciki. In ya so idan Allah ya taimaka sai na sake samun mai Kaunata na aurа. A kwana daya kacal me fantin ya gama yiwa duk inda aka nemi ya yi. Washe garin ranar kuma sai naga ana kawo kaya. Lamari ya tabbata kenan. Ai kuwa wata washegarin sai ga amarya an kawo. Wai ita " Jimmai ". Daki na shiga shiru na yi tagumi. To shi wannan lamari wane iri ne? Abdul yana nufin madadina ya kawo kenan? In kuwa haka ne ai gara na hutawa kaina. Sai na kasance cikin shirin da ya dawo na tarar da shi. Gara dai a yi ta ta kare a yau din nan. In yaso nima sai na huta da da kwanan bakin ciki da takaici. Na kudure wannan a zuciya ta, sai kuma na tuna yadda muka yi da Nusaibah lallai ya kamata na dakata har ta zo, tun da kwanaki biyu kawai suka rage ta zo. 43 Ina sallama nan dai zaune cikin bakin ciki aka bankado dakina ba, ko dabbobi na daga kai domin ganin wa nene me hankalin kace wata haka. kishiya Zuwairah na ga ni yayar Abdul rike da kugu, sai kishiya. mai zafin kishi da ta ke nufin buga kokawa da Ta fara magana cikin daga murya "to sarkin naci kinga dai madadin ki nan Abdul ya kawo, gara ma tun wuri ki sauwakewa kan ki, ki kama hanyar gidanku. Abadan ba za ki kara kima ba а wajen Abdul da danginsa " Ni dai na yi shiru kawai ina ci gaba da kwararar da hawaye ita kuwa sai ta ci gaba "kin rigaya kin cuce mu, kin bata mana sunan zuriya, kin ja labari ya ba zu a gari cewa dan'uwanmu ya na auren barauniya. To mu da ke sai dai Allah ya isa A sannan ne hawaye da na ke zubarwa ya koma cikakken kuka sai na fara musa abin da matar ta ke fada "ni wallahi Allah ni ba 6arauniya ba ce gara ma tun wuri ku nemi barauniya" Ta nuna ni da yatsa" karya ki ke yi munafuka ke 6arauniya ce. Bayan Allah ya toni asirinki a tsakiyar taro, to mu dai sai a yi waje aure dai ba da jininmu ba. A yi ta haifa mana 6arayi, wadda ta mutum ma wa ya sa ni ko wacce iri ce" Wayyo Allah! Kai na ne ya yi wata irin sarawa. Ba ma a wai yi min ba. A gaba na ba a taba ciwa wani mutumci kamar haka ba. Sai na fado ragwaf! Daga kan kujera. A zababben kuka kuma ya ci gaba da gallabata. Lallai ko dan irin wannan cin mutumcin ya kamata na hakura da zaman gidan. Bai kamata a gaban kishiyoyina a rinka ci min mutunci haka ba. Kwanaki biyu suka shude da tarewar amaryar Abdul Jimmai. Kawayenta sun yi ta zuwa ganin daki. Sai dai abin takaici duk gayyar da ta zo Sakinah kan shawarce su da su shiga da takalmansu. Wannan abu ba Karamin kona min rai ya ke yi ba. Shin wai me ya sa a halin yanzu Sakinah ta tsane ni hakaka? Duk amincin da ke tsakaninmu da ita ada, yanzu ya zama tsana. Ina zaune a daki na dukufa karatun alkur'ani mai tsarki na ji sallamar Nusaibah. Kusan kullum haka na ke bin dare da rana, karatun alkur'ani domin ragewa kai na takaici. Ba da jimawa ba Nusaibah ta isa kofar dakina, ganin cewa ina karatu ya sa ta shigo babu sallama, ta sami kujera ta zauna. Ni kuma na ci gaba da karatuna har zuwa inda na ke so na tsaya, sannan na roki ubangiji gami da shafa addu'a. Na juyo ga Nusaibah "ina wuni'?" nace da ita ina murmushi "lafiya lau"ta amsa gaisuwar da wata fuska da ke da bambanci da tawa "waccan kuma da na ke ga ni fa Karimah ita kuma wace cсе?" Na sunkuyar da kai kasa "waccan amarya ce Abdul ya karo" "amarya kuma?" Ta nemi tabbaci Na gyada da kai "kwarai kuwa " Ta bude baki cikin mamaki "to wai kwata-kwata ma wata na wane da yin aurensa da Sakinah?" "ba'a fi wata uku ba" na bata amsa "to ke yanzu ya dawo yana kula ki? Na girgiza kai ina shirin fara zubar da hawaye "ba ya kula ni Nusaibah ita kanta wannan amaryar sai dai na ga an kawota, amma sam ban san da zancenta ba" Nusaibah ta daga kai tana tunani daga bisani sai ta sauke kasa "Karimah duk irin son da ki ke yi wa Abdul ya kamata ki hakura da shi, domin ba na zaton zai sake juyo da hankalinsa zuwa ga re ki. Wannan wani hannunka mai sanda ne akan cewar ya ma ye gurbinki" Nasa gefen zani na na share hawaye"" ni kai na na san haka Nusaibah, kuma yayar sama ta fada tace a matsayin madadina Abdul ya auro Jimmai " 45 "ita Nusaibah ma kuma ta sunkuyar da kai cikin takaici daga bisani sai ta dago wannan a ina ya samota?" Na girgiza kai "ni dai kam ban sani ba " "to Na Allah ya kiyaye, Allah yasa ba irinsu daya da dayar ba " dayar yaya dubeta ta cikin bukatuwa ya zuwa ga gamshasshen bayani "ita ke ne Nusaibah ?" Ta zura min ido "dayar labarin samuwarta ya munana. Ke mijinki cewa ya yi da ke "yar mai gidansa сe ko?" Na jinjin kai. Taci gaba "to sam lamarin ba haka ya ke ba. Abdul ya boye miki gaskiyar lamari. Yarinyar "yar gidan wata hajiya ce abokiyar cinikayyarsa, kuma ina mai bakin cikin shaida miki cewa matar irin karuwan nan ne ma su bin ofisoshi da rumfunan 'yan kasuwa. Tarihin matar a baya ya munana. A halin yanzu ma girma ne ya yi mata cikashi. Kuma ina mai sanar miki cewa a kwararo a ka yi cikin yarinyar. Shegiya ce da bata da uba, kamar kuma yanda na sami Labari marar kunya ce ita takin karawa. Sa'arda tana budurwa bata da wata surtura da ta wuce irin mai dame jikin nan tana bayyana tsiraici. A hakan babarta ta dinga zuwa da ita wajen Abdul siyayaya. Kin kuwa san wasu mazan da maita. Ganin siffar yarinyar kiri-kiri shi ya ja ra'ayin Abdul har ya kai ga aurenta. Amma ki yi nazari kawayenta masu zuwa zaki iya gane yanayinta a wajensu.' Na yi shiru cikin tagumi babu shakka biri yayi kama da mutum. Da irin kayan da ta taba zuwa lokacin da Abdul żai nuna min ita. Kuma shakka babu kawarta Laurat bata da suturar da ta wuce wadannan. Sannan ni na san yanda maitar mijina ta ke dangane da mace, & i. Ina iya cewa an halitta shi ne halittar mutum mafi bukata. Wanda duk irin wannan sai dai Allah ya ki yaye. To shi Abdul sai ma a yi murna da Allah ya tsayar a nan, domin wasu sai sun hada da bin haramtacciyar hanya a waje. Sai dai ina shakkar Abdul ya san cewa shegiya ya aura, duk yanda aka yi kudundune masa lamarin a ka yi. 46 Nusaibah ta ci gaba "to Karimah kin dai ji kowacece Sakinah kokarina na gaba shi ne na gano yadda aka yi har aka zuba miki kaya a jaka. Amma kisa ni ko da a sannan kin rabu da Abdul sai mun bi hakkinmu. Dole ne a wanke sunanki da ya riga ya ya yi damama" Ta mike tsaye " ki taya ni addu'ar cin nasara, domin kuwa aiki ne da zai ba da "yarwuya" Na gyada kai"to Allah ya taimake mu" " shikenan zan tafi Karimah sai kuma na dawo wani lokaсі" Na rako ta soro mu ka yi sallama ta ta fi, ni kuma na dawo muhallina na bakin ciki da kadaici. Zugum na yi ina tunanin labarin da Nusaibah ta ba ni. Kowanne minti daya zancen mai girgizawa kanyi zarya a Karin fiye da sau ashirin "Sakinah shegiya ce" Na yi iya yi na domin na bude wani shafin da ban a kwakwalwata amma abin ya gagara. To na ji Sakinah shegiya ce kuma ga abin da ya ja ra'ayin Abdul har ya kai ga aurota. To ita kuma Jimmai fa wace iri ce? Kuma me ya ja ra'ayin Abdul dangane da ita ?" A halin yanzu dai ba zan ce na san irinta ba, amma idan na yi la'akari da ra'ayin Abdul to abin da ya ja ra'ayinsa a bayyane ya ke Jimmai duk ta fi mu irin jikin da Abdul ya ke so. Abinda ya ja ra'ayin Abdul kenan. Wanda kuma har ya kai shi ga kara aure watanni uku kawai da yin wani. Sai dai in har na yi kyakkywan nazari na yin aure saboda ra'ayi irin na Abdul kawai cike yake da matsala ga kuma irinta nan ta fara faruwa ya kwaso ahegiya ya kawo gidansa. Sai dai ba a ji mutuwar sarki a baki na ba. A halin yanzu ni ma na ji da tawa matsalar. Ada shiri na shi ne na sami Abdul idan ya dawo da daddare, to amma ga mamakina sai ga shi a gidan da rana gatse-gatse. Dakinsa ya bude ya shiga ba tare da ya cewa kowa uffan ba, ni kuma da dakina ya ke kusa da na sa, Ni kadai naga dawowarsa ragowar 47 matan kuma duk suna na su dakunan sakamakon rana da ta sauka ako'ina. Cikin mutuwar jiki da kasala na nufi dakin bayan da ya zauna. Na yi sallama ni ma na shiga fakin. Kai kawai ya daga ya ga kowaye daga nan ko uffan bai ce da ni ba. Sai ya mai da hankalinsa ga laluben wami abu a durowa. Ada sa'arda taurarona ya na tashe duk sa'adda ya shiga irin wannan laluben to wani rasiti ya ke nema, yanzu ma ba na zaton lamarin zai wuce haka. yi Na tsuguna a gefen guda a sannan ne na fara magana kamar zan kuka "dan Allah Abdul wajen ka na zo" Ya waiwayo a fusace "waye yace ki shigomin daki?" "yi hakuri Abdul ni so na ke yi ka a fada min a inda ka ajjiye ni Abdul, duhun gara na san matsayina maimakon kullum ina zaune cikin kаi" Wata "yar dariya ya yi "ke ki ka so ki sanya kanki a duhun kai, duk matar da miji ya kau da kansa gareta, ai yana nufin ba shi da ra'ayinta. To ki sani nima kin gama yayi a wajena, sam ba kya raina kuma ba na zaton ki sake da wowa raina din" Wani dunkulallen takaici ya tarwatse a zuciya ta, wanda hakan yasa hawayena ya kara yo ambaliya "yanzu Abdul kana nufin ka ce ka yarda kai ma ni barauniya се?" Ya nuna ni da yatsa " look a wajena kin wuce barauniya ke gawurtacciyar "yar ta'adda ce, a duniya ma kaf ana yaki da ta'addanci nima kuma na daura aniyar yakar naki" Sai ya fice fuu daga dakin Na yi zaton kasuwa zai koma amma sai na ga dakin Sakinah ya nufa ga alama bai ga rasit din da ya ke nema ba ne. Hargitsewar da zuciyarsa ta yi sakamakon "yar muhawarar da muka fara. Ita ta mantar da shi yin sallama da zuwa ya bankada labule ya sa kai "yan dakiku da ba su wuce goma ba da faruwar hakan sai na jiyo wata irin kururuwa. Da alamar muryar Abdul ce kuma mai yi. Wani tunani ya yo dirar mikiya a kwakwalwata, mai yi wuwa wutar lankartarki ce ta ja shi. 48 Kururuwar ta sake fitowa a karo na biyu take a nan tsohuwar söyayya ta motsa. Na ji ina mai mutukar son taimakawa Abdul. Idanuna suka rufe na nufi nahiyar dakin da gudu da nufin koma me ne ne zai kashe Abdul sai dai ya hada har ni. Da zuwa na bankada labule. Ba a nan Abdul ya ke ba ga alama yana kuryar daki. Har ciki na tura kai ba kuma tare da na dauki wani madoki ba d a zai taimaka min. Mutum uku ne cirko-cirko tsaye a dakin Abdul da ke tsaye dafe da kai, sai kuma Sakinah da Kawarta Laurat da ke can makure a kurya. Idanuna ba su yi maraba ba da irin ganin da na yi musu. Ee wacce to ke eenye ko da dan feto a ciki. Tsirara su ke haihuwar iyayensu. To me ken an haka?. Amsa ita ce neman junansu su ke yi. Asara, tabewa da tsinuwa su tabbata ga masu aiwatar da irin wannan mummunan aiki, nima firgicewa na yi na rasa me ya kamata na yi. Na dade ina jin ana cewa maza suna neman maza. Ko kuma mata masu neman mata "yan'uwansu. To amma ban taba ganin ko da mutum daya ba da aka ce yana gudanar da harkar, to yau ga shi idanuna sun nuna min biyu. ka Ya tabbata ke nan duk sanda Laurat zo wajen Sakinah su shiga dakin ta suka dade wannan kwamacalar su ke yi. Amma Sakinah ta cuce ni, a haka ta ke kwanciya da miji na sannan ni ma ya kwanta da ni. Sai wani bakin ciki ya taso min a rai. A sannan ne na ga Abdul yana shirin yanke jiki ya fadi. Cikin gaggawa na isa na tallabe shi sharaf ya fado jikina. Da na kula sai naga ya rigaya ya suma na kwatartanta ciccißarsa amma ina! Abdul ya rigaya ya yi min nauyi sai na yi wata dabara. Hannunsa na kewayo da shi ta kafada ta. A haka na yi ta jansa har dakinsa. Na kwantar da shi akan doguwar kujera sannan na dawo gabansa na durkusa ina firfita. A wannan hali ne na jiyo takun kafafu da gudu Sakinah ce da kawarta suke kokarin barin gidan. Na kallesu cikin tsana da rashin kauna. A haka suka fice da gudu. Bayan lokaci mai tsaho ina yi wa Abdul fifita sai ya farfado. Zumbur ya yi kokarin mikewa daga 49 kwanciyarsa, Abdul bari na daddanne shi gami da ambaton sunansa " kwanta ka huta" kyale ni Karimah idan har ban kashe wadancan ba to ni kashe kaina zan yi" Na kara rirrikeshi "yi hakuri ka kwanta sun gudu

Chapter 4 of 5