me ne ne Abdul ?N
"dauki ki kai daki tukunna, idan ki ka dawo sai na fada miki"
Na zura masa ido tsahon lokaci daga bisani sai na yi yanda ya се
din, na kai dakin na dawo" to gani na dawo me ne ne ?"
Ya dan lumshe ido gami da sudar le66a "Kanwa zan kawo
miki Karimah"
18
Nan da nan kirjina ya yi wani irin duka kai ka ce mata ne su ke lugude a gidan biki." me ka ce Abdul, za ka kara ąure?"
Ya gyada kai " haka na ce Karimah "
Sai na fara kokarin kuka "yanzu Abdul me na yi maka da za ka yo min kishiya? Ko kana nufin ka ce kaunar da na ke nuna maka bata gamsar da kai ba ?"
Ya kama hannuna "wallahi Karimah babu abinda ki ka yi min, kuma hakika kina nuna min duk irin kaunar da na ke nema"
"To idan haka ne me yasa kuma zakayo min kishiya Ko kuma dan ka na nufin na tsufa ne tun da na fara haihuwa?"
Ya sa hannu ya toshe bakina "ya subhanallahi! Me ya sa ki
ke irin wannan zancen Karimah? An fada miki ni irin wadannan
mazan ne?"
Na Kara marairaicewa "to Abdul idan ba haka ba me ne ne
dalili?"
Ya jawo ni jikinsa ya rike "Karimah yarinyar "yar maigidana
ce, kuma shi ne ya matsa akan sai na aureta. Ni kuma da na ga tana da hankali da ladabi sai na amince, ina mai tabbatar miki da cewa
za ki ji dadin zaman ku tare da ita, dan Allah kar ki damu Karimah
Hawaye ya zubo min ba da jimawa ba kuma hawayen ya koma
kuka, hakan ya rikita Abdul. Ya kara matseni a jikinsa. "Karimah
bai kamata ki tashi hankalinki akan wannan maganar ba, ke fa
Karimah malama ce kin sani Allah bai haramtawa mutum yin mata
sama da daya ba"
Cikin shasshekar kuka na fara magana "Abdul ba wai kishiya
ce ban a so ba, tsoro na ke ji kar ta zo ta rikita mana zama. Muna
zaman mu lafiya ta rusa mana shiri"
Ya girgiza kai sa'ar da yake share min hawaye "haka ba za ta
faru ba Karimah, kuma ma babu wadda za ta taba ki mu shirya da
ita, ki kwantar da hankalinki'
Na yi shiru da kukan a lokacin ya matso da fuskarsa kusa da
tawa " to ba ki yi addu'ar fatan alheri ba Karimah"
14
Na yi shiru ban ce komai ba, zura masa ido kawai na yi ya
nuna damuwarsa a fili. "Dan Allah ki yi addu'a Karimah idan ba
haka ba sai na ga kamar ba ki amince da magana ta ba ne"
Na fara motsa bakina cikin karfin hali "Allah ya tabbatar da
alherinsa Abdul"
Ya yi murmushi "Amin Karimah, to ko ke fa kinga yanzu
hankalina sai ya kwanta" sai ya sumbaci kumatuna.
+
Ina zaune a falo shiru cikin tagumi kai ka ce wadda aka
kawo mata sakon mutuwa. A wannan hali ne mahaifiyata ta shigo,
a karo na biyu ke nan da ta tako gidan tun sa'ar da a kayi bikinmu
da Abdul. Ta kalle ni a tsorace " ke kuma me ke damun ki ki ke
faman tagumi?"
"babu komai Ummah "na ba ta amsa sa'ar da na mike tsaye a
hankali, ta shigo ta zauna akan kujera ni kuma firij na nufa na
dauko mata ruwan sanyi na dawo na ajiye mata, sannan na fara
gaisheta." Ina wuni Ummah?"
"Lafiya lau ya ya mai gidan na ki?"
"yana nan lafiya"
"to madallah, dama unguwa naje shi ne nace bari na biyo na gan
ku, nama dauka cewa zan sami mai gidan dan sau biyu yana zuwa
bana nan"
Na sunkuyar da kai " ya fada min gashi kuma yanzu shima bai dawo ba "
"to ai shi ke nan idan ya dawo sai ki gaida shi"
"to zai ji Ummah "nana gyara zama
"kina da labarin zajKara aure Ummah?"
Ta karkace kai "A 'tha zan ji? To ko dama zuwan da ya ke yi ken
an?"
"Eh ina ga haka din ne"
Ta gyara lullubinta " to Allah ya tabbatar da alheri yasa kuma abokiyar zama ce "
15
Ba haka na so na ji Ummah tace ba dan haka na fara kokarin
bijiro mata da abin da ke raina "ni wallahi Ummah duk hankalina
ya tashi akan lamarin"
Ta kalle ni da sauri "au shi ne na ga kina ta faman tagumi ?
Ai kishiya ba abin gudu ba ne Karimah, kishiya abokiyar zama ce
mai taimakawa a lokacin bukatar taimako mai kuma debe kewa a
lokacin kadaici, saboda haka kar ma ki damu kanki, ki yi farin ciki
da faruwar haka"
Na yi tagumi " to ai ni Ummah ba wani abu nake gudu ba illa
kar ta zo ta rikita mana zama, kin ga dai yanda mu ke zaune lafiya
ni da shi"
Ta karkada yatsa "sam kar ma ki da mu kowacce da halinta
zata zauna, idan halinta ba mai kyau ba ne a kan ta zai kare, ke dai
ki yi kokari ki tabbatar da cewa kin gyara na ki halayen" ta mike
tsaye
"To ni zan tafi, idan ya zo sai ki ce ina yi masa fatan alheri "
Ni ma na tashi na rakata har soro sannan muka yi sallama ta
tafi. Ba 'a fi minti talatin ba Abdul ya yi sallama, fita na yi domin
na yi masa irin tarar da na saba to amma sai naga wata yarinya ce
take biye da shi a baya, sai na ja na tsaya turus. Na yi masa sannu
da zuwan fatar baki kawai, shi ne ya karaso ya kama hannuna
zuwa falo muna shiga ya dube ni, Karimah dan Allah ki yi hakuri
kanwarki ce na kawo ku gaisa gashi kuma na manta sanda zan fita
ban fada miki ba"
Na yi shiru kawai ta riga ta faru saboda haka ba ni da
abinda zance masa, ya sake dubana " ba ki ce komai ba Karimah"
"to me zance abdul? Da dai ka fada ai da na yi mata wani
tanadi, amma yanzu kaga ai kusan yadda tazo zata koma "
"karki damu da wannan itama ta san ban fada miki ba "sai ya
nemi da ta shigo "sakinah" ya kirawo sunanta. Ta matso a hankali
gami da yin sallama. Ni ce na tare ta da fara'a " sannu da zuwa
Kanwata ai ban san ke ba ce, laifin Abdul ne da ya ki sanar da ni
cewa za ki zo"
Ba ta ce komai ba murmushi dai ta ke yi, na ja ta har 4
kujera na zaunar da ita sanan na bude fridge na debo tufla da
tataccen ruwan lemo(juice) na kawo gabanta na zuba "To sai a yi
hakuri da dan abin da muka tari bakin da shi, da dai na san da
zuwan ai da an yi muku girki "
"babu komai" ta fada tana murza yatsun hannu ta. A sannan
ne na kare mata kallo, babu shakka kyakkyawa ce ita ma kuma na
tabbatar kyawun ta ne ya kai Abdul ba wai kyawun hali ba kawai,
kamar yanda ya fada to ashe kenan za a sha gwagwarmaya
musamman ma idan Abdul yayi irin abin nan da wasu maza ke yi
na fifita amarya akan uwar gida.
Ina yanka mata tufar nima sai na sami waje na zauna. Abdul
ya dubeni "to karimah gadai kanwarki nan, ya kamata kusan junan
ku tun yanzu da fatan kuma za ku zauna lafiya idan Allah ya kawo
lokacin, kuma dama haka na ke sa ran tunda da ke da ita duk nasan
babu mai san fitina"
Mun dade muna hira gaba daya daga bisani Abdul yamike
tsaye "to zan mai da ita gida naga yamma tayi sosai"
Na mike tsaye"to ina zuwa" wasu turaruka guda biyu da
sinkin sabulu, sai kuma man shafawa na zuba su a leda na kawo
mata. Ta karba tai godiya sannan nayo musu rakiya har soro muka
rabu-cikin fara'a. Bayan awa
daya ne da tafiyarsu Abdul ya dawo tun kafin ya zauna ya fara
magana "amma Karimah kin yi matukar birge ni yanda ki ka karbi
yarinyar nan, kin ga ita kanta zata tabbatar da cewa wajen me
tallafa mata za ta zo"
Na sunkuyar da kai "to saura dai ya rage gareka idan muka
zauna lafiya da kai, kai ne ka yi adalci idan kuma aka ji muna fada
laifin ka ne"
Ya girgiza kai "Allah ma ya kiyaye Karimah da yardar
Allah zan yi kokari wajen ganin cewa na yi adalci. Nima idan kuna
rigima ai hankalina ba zai kwanta ba"
17
Watan dawowar alhazai aka daura auren Abdul da Sakinah.
Shikenan ni ma na yi kanwa, kuma in har zaman mu da ita ya
daure kamar yadda mu ka faro, to na iya cewa ba sunanta kishiya
ba sunanta "yar'uwa.
Muna zaune ni da ita a falo wata guda bayan tarewarta babu abin da mu ke yi illa aikin kallon fina-finan Hausa, a kullum haka
muke karar da lokaci tare da įta muna kallo. Zan iya cewa na yi marhaban da zuwanta domin kuwa yanzu na daina zaman kadaici,
sai dai dole ne na dan ji canji, a da ni ce ke da ikon mai gida
kullum amma a halin yanzu sai dai bayan kwana biyu.
Sakinah ta mike tsaye bayan da kaset din da mu ke kallo ya kare "ya ya kawo Hamidah na yi mata wanka"
Na mika mata yarinyar wacce ta ke ta kai wa iska naushi
cikin wasa irin na jinjirin da ya fara wayo.
Sakinah ta shiga raina saboda yanda ta ke kulawa da "ya ta.
Ta saba Hamidah a kafada sannan ta fice da ita daga dakin. Bayan
shudewar tulin mintuna sai ta dawo gare ni "yaya kawo wasu
kayan a sake mata"
Na mike tsaye"tsaya na bude kwaba na debo mata". Bayan
wani lokaci sai ta dawo falon da ita yarinyar ta yi fes da ita, ba
miko min ita Sakinah ta yi ba zaunawa ta yi anan ta na yi mata
wasa na kan kasance a farin çiki matuka duk sa'ar da na ga "ya ta a
cikin walwala.
Sakinah ta kale ni sa'ar da ta rungume Hamidah a kirji
"yaya ki ta ya ni addu'a ni ma Allah ya fara ba ni 'ya mace"
Na yi murmushi " to Allah ya ba ki Sakinah"
Ta kara mayar da hankalinta wajen yiwa Hamidah wasa.
A wannan lokacin ne Abdul ya shigo, shi ma waje ya samu ya
zauna, mu duka mu ka yi masa sannu da zuwa ya amsa cikin fara'a.
Sannan ya dubi Sakinah " an gaida ke babar Hamidah "
T a yi murmushi "yawwa sannunka dai"
Mu duka ukun mu ka ci gaba da hira da alama shi kansa
Abdul yana jin dadin yadda ya ga mun hada kanmu. A cikin hirar
ne Sakinah ta ke neman iznin zuwa dubo marar lafiya gobe, kamar
8
yadda ta fada yayar aminiyarta ce tare ma za su ta fi, sun yi da ita
ta biyo mata idan za ta tafi. Abdul ya amince mata. Ta miko mini
hamidah " to ya ya karbeta zan shiga ban daki" Na miko hannu, na
karbe ta cikin fara'a "an gaida ke, Allah ya bar zaman tare". Ba
fita ta yi ba da wuri sai da ta dan yi wa Hamidah wasa, ta hanyar
daga mata hannu, Hamidah ta yi dariya wai ala dole ita abin dariyar ta ga ni.
Da karfe goma sha daya na rana ne kawar Sakinah mai suna
Laurat ta iso. Ita sabanin Sakinah ce "yar baka ce gajeriya, tana da
dan kauri da ke sata kwaikwayon doya. "Yar faffadar fuska mai
dauke da hanci da ya shimfide kamar tabarma. Mu ka gaisa da ita
cikin fara'a, sannan suka shiga daki tare da Sakinah. Sun dan bata
lokaci a ciki wanda ya isa Sakinah ta kammala shiryawa, daga
bisani sai suka fito bayan ta yi kwalliya har ta ratayo jaka ta kalle
ni"To ya ya mu mun tafi, sai mun dawo"
Na kai ido na ga kyauren dakinta daga bisani na juyo da su
inda ta ke a tsaye "Sakinah ai kin manta ba ki kulle dakin ba"
Ta yi murmushi "yanzu ya ya dan za ni unguwa sai na wani
kulle daki? Sai ka ce dai wani waje da ake zaman rashin yarda "
Na girgiza kai "ai ba zancen haka ba ne Sakinah ina dai
gudun kar wani ya shiga ne lokacin da ayyuka suka yi mini yawa,
ko kuma na shiga bandaki kin ga ai abin da ba a so zai iyya afkuwa
"
Kyakyacewa ta yi a inda ta ke "ni wallahi har kin ba ni
dariya, ya ya za a yi wani ya shigo gidan nan da rana gatse-gatse.
To ni dai ba wata kullewa da zan yi dan na san za ki kular min da
shi fiye da yadda za ki kula da dakinki"
Da fadin haka sai ta yi gaba kawai na yi na yi da ita a kan ta zo
ta kulle amma ta ki ta saurare ni sai dai ta bini da " sai mun dawo
din ya ya"
19
Na rike kugu cikin takaicin faruwar haka, ban so ta tafi ta bar dakin a bude ba to sai dai babu yadda na iya. Katin ta fice na yi mata adawo lafiya tare da rokon a gaida mai jiki. Ta amsa da cewa
za ta ji. Bayan fitar ta ne na shiga dakina na dauko kwado, zuwa
na yi na jawo kyauren fakin Sakinah na datse mata shi, sannan na
sa kujera a tsakar gida ina tunani to ita Sakinah wacce irin yarinya ce? Ga alama dai ta amince da ni fiye da zato. Sai na tuno shirme
na gkan kukan da ha yiwa Abdul akan wai zai karo aure, da lokacin na san da cewa haka matar za ta zo da babu abin da zai
sani yin barnar hawayena maimakon haka sai na dage wajen
Kartafa masa gwiwa da kuma kokarin kwadaita masa abin a rai. Mintuna da dama sun shude min anan a zaune wadanda a cikinsu
ne kawata Nusaibah ta shigo. Cikin fara'a da walwala na tashi na
tare ta, mu ka dunguma daki gaba daya. Gaisawa muka fara yi
kafin daga bisani mu nutse a hirar duniya. Nusaibah dai har yanzu
ba ta da aure cewa ta yi sai ta karbi kwali mai kwari tukunna, shi
ya sa har yanzu tana karatun ta a jami'arbayero.
Natarkata mata kayan sanyi a gabanta ni ma na zauna muka
ci gaba da hira, ta dube ni "Karimah ina kuma kanwar ta ki ne?"
Na yi murmushi gami da karkace kai "ta tafi unguwa wata
marar lafiya ta tafi dubowa a asibiti"
Ta kurbi lemon "to ince ko ta kirki ce ba kwashe-kwashen
miji ba"
Na girgiza kai gami da tabe baki "ko kusa wallahi Sakinah
"yar kirki ce dan ni har Allah na yi wa godiya da ya kawo min ita,
dan baki ga yadda mi ke rayuwarmu ba gwanin sha'awa"
Ta ajiye cup din dake hannunta "to madalla kin san wasu
mazan basa yin nazarin mace in zasu aura, sai dai da sun ga kirar
ta birge su shi kenan sai su zo su hadata da matar da su
zaman lafiya a gida shikenan kuma lamari ya hargitse"
ta ke
"Nima dama haka na guda da farko to amma sai Abdul ya
tabbatar min da cewa yarinya ce tagari, gashi kuma nima naga
hakan da idona dan in dai har irin su sakinah ce to nan gaba a karo
biyu mu zama hudu
20
Nusaibah ta kale ni da sauri "amma Karimah baki da hankali an
fada miki cewa lallai ne itama ku dore a haka har abada? Kan
kajerinki da kuma surutun tsiya sai sun kai ga jefa ki ramin da zaki
gaza fitowa"
Nai murmushi "ai gani na yi muna zaune kalau Nusaibah ni ba
ma abinda tafi birgeni dashi irin yadda take kulawa da "yata.
Nusaibah ba ta sake cewa komai ba akan batun sai ta canza hirar
da wata "kin san cewa Asama'u ta fara aiki a asibitin zana?" na
kalleta baki bude yaushe ta fara aikin Nusai bah ?"
"satin da ya gabata ta fara aiki yanzu itama ta shiga sahun
ma'aikatan jinya (nurse) da ke asibitin "
Na rike haba " Shegiya Asma'u sai da dai ta kai ga cimma burin
da ta ke bukata, zan kywa taka har gida na sameta na yi mata
murna tun da dai yanzu zuwanta gidannan sai abin da hali ya yi,
sau biyu ta taba zuwa dama"
Na mike tsaye bayan da agogo ya nuna karfe dayan rana
"Nusaibah bari na dora mana girki na dawo" sai na fice na barta
anan ta na duba wani littafi. Rabin awa kacal abincin ya yi ya dahu
na zuba mana a faranti ni da Nusaibah, sannan na ajiyewa Sakinah
na ta a food flask. Na kawo mana namu daki muka tasa a gaba.
Doguwar robar ruwa da kwalin tatacciyar abarba na halarto mana
da su ta yanda za muji dadin dibar gishara kasan halinmu dai muna
diba muna hira, bayan kammalawar mune muka shirya yin sallar
Azahar hakan kuwa muka yi. Bayan idarwa Nusaibah sai ta fara
shirye-shiryen tafiya gida a sannan ne Sakinah ta yi sallama ta
shigo. Dakina ta nufo kai tsaye tana tafe tana murmushi.
Na yi mata sannu da zuwa gami da tambayar mai jiki. Har
yanzu murmushin bai fice daga fuskar taba" mai jiki ai mun samu
ta warware domin ana saran sallamarta a yau ko gobe "
"to madallah" nace da ita. Ta sunkuyar da kai ya zuwa kallon
yadda ta ke bude Jakarta. Ba tare da ta dago kai ba ta fara tambaya
ta "ina 'yata ta ke Karimah?" na yi murmushi"yarki tana can
tana barci ni yau har mamakin irin baccin da ta ke na ke yi wajen
awa biyu kenan bata farka ba" kamar mun tsokano ta sai muka jiyo
2
kukanta. Mu duka ukun muka fashe da dariya " To kin ji "yar halak din ba " zancen Sakinah kenan. Ta ratsa dakin har inda gadon Hamidah na jirajirai yake ta tsamo ta, sannan ta dawo gare mu tana mai yi mata wasa, daga bisani sai ta fiddo abin da ta ke son fiddowa daga jakarta "yaya da ma wani dan takalmi na gani ya birge ni shi ne na siyo mata shi" Na kalli takalmin mai mugun kyau a hannunta. Take Kaunar
Sakinah ta sake shiga raina. Ta zauna akan kujera gami da zaunar da Hamidah ta hanyar jinginata da jikinta. A haka ta sami damar gwada mata takalmin. Takalmin kuwa ya hau sosai. Na yi mata godiya gami da bayyana farin cikina.
Ta miko min ita "bata tasha tukunna sai na zo na karbeta na yi
mata wanka " ta tashi zata fita: Na kirawota na bata makulli. Tа
karba dauke da alamar tambaya " na me ne ne shi kuma?" Na yi murmushi " ai kulle dakin na yi saboda muna nan ciki ni da bakuwa.
Ta kada kai gami da yin murmushi "yaya kenan!" sai ta fice ta bar
ni makale da kaunarta a raina.
Nusaibah ta dube ni ta jinjina kai "lallai Karimah kya yaba
yarinyar nan ni ai bana zaton na taba samun labarin kishiya mai
hali irin nata, ah! Abin sai son barka"
Na yi murmushi "to ba shi ne abin da nake fada miki ba, ai
kadan ki ka gani daga lamarin Sakinah" ta mike tsaye "to ni
Karimah ni zan wuce sai kuma abin da hali ya yi "ni ma na mike
rungume da Hamidah a kirjina bayan da ta dukufa tsotson mama.
A haka muka fito daga dakin. Nusaibah ta yi wa Sakinah sallama
sannan na rakota har soro, daga nan muka yi sallama ta tafi. Ni
kuma na dawo daki na zauna. Har ya zuwa yanzu kuwa mama na
ke bawa Hamidah. Na kai hannuna na shafi kan ta zuciya ta cike da
tunanin cewa zan more suruki shekaru sha masa zuwa domin
kyakkyawar fuskarta kyawun jikinta zai sanya samarin lokacin yo
rige-rige kasan kuwa sai na zaba na darje.
22
YAYA AKAYI HАКА?
Lissafin ranaku yau Asabar, yayin da watan bature kuma ya zama
hudu ga watan Maris (March) wanda kuma ita ce ranar da ake yin
cincirindo a gidansu mijinmu Abdul domin yin bikin kanwarsа
Maimunat. Tun karfe goma dai dai na safe muka gama shiryawa ni
da Sakinah Abdul kawai mu ke jira ya kwashemu a motarsa. Bada
jimawa ba kuwa ya iso. Gabaki dayanmu muka yo waje muna
sanye da atamfar ankon da mijin mu ya dinka mana. Sakinah tana
rataye da karamar jaka, yayin da ni kuma na ke dauke da irin dingimemiyar nan mai kama da buhu sai kace mai shirin zuwa
sayayyar kayan miya kasuwa, sai dai ko ba komai ita ce jaka mafi
dacewa da mace mai goyo, domin ta kan ji dadin zuba komatsanta
ba tare da damuwa ba, Da fitowar mu mu ka duru a motar Abdul
kirar Toyota samfurin Baby Starlet shi kuma ya ci gaba da
gurgurawa da mu bayan da mun ka riga muka kulle gidan Abdul
mutum ne mai barkwanci saboda haka a motarma ba shiru ya yi ya
rabu da mu ba, ya dan waiwayo gare mu sa'ar da danja ta tsayar
damu "to ku hado min kudin kunan " mu duka mu ka bushe da
dariya "kudin me kuma?" Sakinah ta tambaya
"kudin mota mana" ya bata amsa cikin daure fuska sai kace da
gaske. Ta kale ni " to yaya kawo kudin mota a ba shi"
"ke rabu da shi wane dan tasi( taxi)
Yaga yana karbar kudi kafin ya sauke fasinja ai a ka'idar tasi
bayan kudi sai kafafun fasinja sun taba kasa"
"to wa ya fada muku tasi ce ?" zan cen Abdul
M
au, to Bus ce?"na nemi ji
" I mana da idan ba Bus ba ce me ce ce? Bus kuwa kun san kafin
taya ta yi juyawa goma a ke karbar kudi"
A dai dai lokacin aka ba mu hannu. Ya daga ya tafi a lokacin da ni
kuma na ke cewa " to nuna mana karen motar sai mu ba shi"
"kun ga Hajiya ni babu Karen mota na ke aikina saboda haka ku
hadomin kudl na kawai"
23
Yana maganar ne kwatankwacin yanda mafadatan direbobin motocin haya ke yi. Hakan bai sama mana komai ba illa sakamakon dariya abin har sai da ya kai mu ga tafawa. Cikin wannan rahar muka kusa da gidan. Bamu karasa ba ya yi fakin. Mu dai bamu san dalili ba. Ya waiwayo garemu "kun san dalilin tsayawata anan ?"
bamu sani ba " muka ba shi amsa. Ya ci gaba wani katoton adalci na yi muku mai matukar rahusa. An yi ta nuna ni akan hanya ana cewa ni direbanku ne, saboda haka ba zai yi wu na ajiyeku haka kawaiba. Duk mai son tafiya to na gaggauta jin bakinta a
kumatuna"
Sai ya daure fuska. Na kalli Sakinah cikin zazzare ido " mu fa yau ta mu ta same mu dan Allah Abdul ka yi hakuri kaga nan kan hanya ne"
Ya harare ni " to ni ina ruwana amma idan kun fi so mu karasa gabansu Ummah sai mu karaşa, ni dai kun san babu abin da zai ba
ni kunya "
Sakinah ta kalleni " ni dai yaya ba ri na yi masa yanda yake so
na huta"
A hankali ta kai bakinta ga kumatunsa anan ta bar masa shacin
jan baki ya rike min hannu gami da daga mata kujera ta fita " to ke kuma fa?"
Na marairaice "ni dai gaskiya Abdul wallahi zan yi maka
kuka""
Ya jinjina kai " tafdijan! Ai kuwa da kin jawa kanki, kin san
dai babu wanda zai ce sato ki na yi kuma da an tambayi dalili zan
fada "
Abin ya ba ni dariya " to dan Allah yi hakuri idan muka koma
gida zan yi maka goma"
Ya girgiza kai " ban lamunta ba na yanzu kawai na ke so guda
daya, idan ba haka ba kuma zan kulla miki sharriі"
Na zazzare ido "wane irin sharri kuma Abdul?"
"duba kumatuna har gaban su Hajiya za ni a haka, kuma kin
san ina da abokan wasa duk wacce za ta yi min tsiya sai na ce
24
jarabarki ce hana ni fitowa ki ka yi daga mota wai sai kin yi mis kiss"
Na rike baki " na shige su! Dan Allah Abdul ka yi hakuri kaga yanzu Sakinah har ta shiga gidan kuma na san an fara tambayarta ni"
Ya kada kai "ah to, ai laifin ki ne, har fa sai da na shigo lungu
domin da saukake muku, da wannan surutunma da tuni kin yi
tafiyarki"
Babu yanda na iya na kai hannayena domin kamo kansa ta
yanda zan ji dadin sumbantarsa a kumatu
ນີ້;
tsaiton iokad dags blegny" to ko ke fa ba shi ke nan ba
ya sa hankici ya goge fuskarsa sannan ya kai ni har kofar gida. Na
fito rungume da Ha midah. Ya kalleni ya tuntsure da dariya. Ni
kuma na harare shi cikin wasa. Ina juyawa ne na ji muryarsa
"kinga" na waiwayo " There will be some more when going
back"(za'a sami dadi ya yin komawa)
Na sake harararsa " ai ba ka isa ba, amotar haya zamu koma"
Ya yi kwafa""na ga wanda bai isan ba tsakanin ni da ku"
"kai ne baka isa ba " na maida martini. Sai ya bude kofa da sauri, a
guje ya zo har inda na ke a tsaye, a lokacin da ni kuma na ke
Kokarin tserewa.
"wallahi za ki jawa kanki zan rike ki har gaban Hajiya "
Na sani cewa kadan kenan daga aikin Abdul sai na shiga
hadashi da Allah da Annabi akan ya yi hakuri. Da kyar na samu na shawo kan sa
Ya sake ni ya koma mota, ni kuma na shiga daga ciki. Duk da
cewa da wuri muka zo amma gidan ya fara karbar baki. Na san kuwa wadanda za su girka abincin rana ne suka zo
Na je na gaida Hajiya