Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kasa kallon cikin idon sa don alkawarin da yayi min bai cika shi ba, ya ce zai lallashi Abba kada a yimin auren dole amma yayi hakan? Shirin angwancewa yake yi. Da ya ga ba zan gaishe shin ba kamar yadda na saba sai yace "kada ki damu fa Boddo ni ba bakon zafi bane, it's a promise bayan auren mu ba zan zo inda kike ba, I mean... I mean ba zamu hada shimfida ba don na fahimci damuwar ki kenan. Zan yi hakuri zan jure har sai ranar da kika karbe ni as a husband don radin kan ki. Ranar ne zaki banbance da banbancin da ke tsakanin Aya da tsakuwa; soyyayyar Yaya da ta wani bare da kike underestimating dina a kan sa. Zaki tabbatar soyayyar gaskiya ba a mafarki take gudana ba, a zahiri take; from theory to practice. Na tabbata Dream Man din naki, bai fi ni komai ba, haka bai fi sauran maza mazantaka ba, watakila ma.....watakila ma.....ya kyabe baki kafin yayi kasa da murya kada wani ya ji abinda zaya ce, kamar cikin rada ya ce, "watakila Boddo ko kwakkwarar sumba wannan (kissing) bai iya ba sai shegen tsayi kamar falwaya da bakar kalar sa dana fahimci sune abubuwan sa da ke rudar ki!". Hannaye na biyu na saka na toshe kunnuwa na na fita daga madafin ina mamakin sa. A baya in wani yace min Ya Umar zai iya irin wannan maganar ba zan taba yarda ba. Sabida kallon wani kasurgumin shaihin malami nake masa. A raina nayi murmushin tausayin sa, sabida ya gama amanna da ya same ni ya gama. Shi yasa bazai damu da abinda nake gudun auren sa a kan shi ba, tunda ya san ko ba dade ko bajima zai zama nasa ne. "Ya Omar da muguwar rawa gwanda kin tashi. Zamu ga wa za'a kai gidan ka balle har ayi batun hada shimfida ko akasin ta. Bana yin magana don yaudarar kowa amma tunda an zo wannan gejin zan yanke hukuncin da zuciyata ta fi amincewa da shi. Lokaci ya kure min da zan nemo ka Dream Husband, kamar komai ya kurace min muddin na bari aka daura min auren nan, suna maganar daurin aure nan da kwanaki uku. Omar ba zai taba saki na ba muddin igiyoyi na suka shiga hannun sa. Damuwa ta daya ce a ina zan nemo ka?" Anti ta gama shiryawa tsaf, shirin tafiya Mambila a washegari, inda za'a fara gudanar da bikin mu yadda Al'adar garin Gembu ta tsara. Na tabbatar muddin na saka kafa a Gembu, dakin Ummati aka shafa min lalle; aure na da Ya Omar ya gama tabbata, mai iya raba Omar Gidado Gembu da igiyar aure na kuwa sai dai mutuwa balle in yi fatan zan shiga ne in fito a sanda nake so, ko in Dream Husband ya bayyana kan sa, in bar Omar in koma masa, a halin yanzu kuwa bana bukatar auren kowa na fi so in bar duniyar bakidaya in huta da azabar soyayyar dana ke dandana, tunda bani da nasara a kan ta, da zai bayyana da ya bayyana haka kafin lokaci ya kure mana. Da in ganni a gidan Ya Omar matsayin matar auren sa gara in bi bayan mahaifiya ta, ko na samu cikar buri na a aljannah, ko mayi aure da wanda nake so a wata duniyar ba wannann tamun wadda muke ciki ba, tunda ya ki bayyana a duniya har gashi za'a yimin auren dole a dalilin (SAKACI) NEGLIGENCE irin nasa...... "FIYA-FIYA TANA TSINKA HANJI IDAN TA SHIGA JIKIN DAN ADAM. DON HAKA UMMATI KADA KI KARA AJIYE FIYA FIYA A DAKI SABIDA YARAN MAKWABTA DA NAKI JIKOKIN KANANA DAKE SHIGOWA SUNA DABDALA A TSAKAR DAKIN KI". Na tuno wata magana data taba gudana tsakanin Anti da Ummati a zuwan da muka yi mata yawon Arba'in din Nadiya, Maryam Jamila ta dauko wata kwalba akan talbijin tana tambayar Ummati ko turaren Dan Duala ne a ciki? Ummatin ta ce "a'ah fiya - fiya ce maganin sauro guba ce, maza ajiye ki je ki wanke hannun ki". Abbana ya ce wai ko gawata ce a kai gidan Umar, kafin a wuce da ita makabarta, to watakila ya fada da bakin mala'iku ne. Domin furucin iyaye karbabbe ne shi yasa ake so a kowanne lokaci su dinga tauna kalaman su a kan 'ya'yan su. Na zabi in sha fiya-fiya a kan dai na je zaman aure gidan wanda bana yiwa so na soyayya.....!!! (A wasu lokutan idan baka barwa Allah lamarin ka ba, idan ka zabi ya barka da dabarar ka sai ya barka din. Babban kuskure na ni Siyama, tunda na fara mafarkan nan da shi ban taba neman zabin Allah a kai ba, ban taba cewa idan soyayyar da nake yiwa wannan bawan Allah daidai ce da addini na, tarbiyya ta da lahira ta, kuma alkhairi ce a gare ni da addinin Allah, Allah ya sada ni da shi cikin hikima, buwaya, mulki da iyawar sa da tsarkin mulkin sa. Ni na san tun farko da ace wannan addu'ar na dukufa ina yi tsahon shekarun nan dana fara mafarkan sa, na tabbata da tuni na rabauta cikin zabin Allah. Amma a yanzu lamari na yana hannu na ne kacokam! Kuma shedan ya yi min kyakkyawar jagora yana gaya min rayuwa ba tare da shi da na kallafawa rai ba aikin banza ce, don ba zan taba jin dadin ta ba. Na daga kwalbar fiya-fiya na rufe ido sannan na yi kalmar shahada, ban sani ba ko Allah zai karbi shahadar nan tawa? Tunda ni nayi nufin yin ta da hannu na bata Allah da Annabi bace?? Ko kuma shan fiya fiya don gujewa auren dole daidai yake da kashe kai??? Gara in taimakawa Abba ya cika burin sa ya kai gawa ta dakin Ya Umar, sannan a zarce da ita makabarta. Shi kuwa Dream Husband dina bazan taba yafe masa ba, duk ranar da ya gama yangar sa ya ga damar bayyana kan sa gare ni, ya samu labarin na gaji da jiran sa na kashe kaina a kan sa he will then take it for granted.... I would love to see his reaction a lokacin da ya samu wannan labarin. Reaction din sa na samun labarin mutuwa ta a dalilin sa, shi zai nuna girman matsayi na a zuciyar sa..... shi zai bayyanawa mai karanta labari na cewa shima yana so na ko ni kadai nake koshin wahala a kan sa? Duk da 90% na zuciya ta na tabbatar min our hearts are jointly connected internally by the creator..... Ba ni kadai nake wannan suffering din ba. Na hango kaina Abba na binne ni yana kuka yana cewa da na sani na taimaka miki kin nemo shi Boddo, ba wanda ba zan iya nemowa a duniya ba idan na saka kaina, da na sani ban yi gaggawa ba wajen yanke hukuncin yi miki auren dole, da na sani ban ki bin shawarar likita ba da ya ce a tsahirta, da na sani Omar ya zabo duk macen da yake so da kan sa, in ya so na aura masa ko wacece koda zan rasa banten daurawa....Da na sani din da Abba zai yi a kan hukuncin da yayi wa rayuwata tana da yawa..... Amma me? Wani bangare mafi rinjaye na zuciya ta ya ki amincewa da hakan, cewa yake dani cikin amsa-kuwwa.... "Abba ba zai taba yin dana sani ba, don hukuncin sa bai sabawa Allah ba, ke ce zaki yi da kin sani, kece zaki dawwama cikin sa, kuma ki tabbata cikinsa daga nan har karshen rayuwar ki muddin kika aikata abinda zuciyar ki ke umartar ki a yanzu". Amma hakan bai sa ko kadan na fasa abinda nayi niyya ba, a ganina hanyar tsira daga auren dolen da Abbana zai min kawai kenan wanda zai zamo shinge/katanga ga tabbatuwar mafarkaina da wanda nake so. Da in rasa wadannan mafarkan nawa gara na rasa rayuwar dungurungum bakidayan ta. Love is real, kuma nawa baya karbar uzurin kowa face na samun wannan soyayyar gaibun dana ke so. Na soma tittila ruwan fiya-fiya a baki na ina hango DREAM HUSBAND dina, yau kam tar-tar nake ganin sa cikin idanu na ba kamar kullum da a fizge kawai nake iya ganin sa ba; those beautiful eyelashes sun kwanta sosai a saman lumsassun idanun sa, that cool man's pride da ke dimauta ni, wanda ya tafi ya zagaye habar sa ya kwanta lambam a kan kyakkyawar bakar fuskar sa sai sheki da salki gami da walkiya yake yi. Hakika Ubangijin halitta ya kyautata surar sa a cikin bakaken mutanen Africa, ya qawata min shi a zuciya da ruhi fiye da duk wani da namiji mai numfashi a duniya. Gani nake kamar ya bude min hannuwa yana min murmushin da ya lotsa gefen kumatunsa guda daya yana jiran isowa ta. Na amince Allah ne ya hada mu ba don komai ba sai don mu rayu tare, rayuwa ta har abada amma a wata duniyar daban, ba wannan tamun wadda muke ciki ba!!! ******** MAI RABON GANIN BADI....... A cewar Hausawa ko ana ga uzuru ana ga Shaho sai ya gani. Allah ne ya kawo Wasila a daidai wannan lokacin, wanda yayi dai-dai da zuke kwalbar fiya-fiya da nayi, idan Allah ya ce kwanan dan adam bai kare ba to babu abinda zai kashe shi sai kudura da iradar Ubangiji. Na yarda da hakan a yau a kaina domin tabbas na san na sha kwalbar fiya-fiya, daga nan sai shigowar Wasila da ihunta da na ji a kaina, bayan wannan ban kara tantance meke faruwa da ni a duniya ba. Na bude ido ne na ganni akan gadon asibitin Nizamiye, inda anan file din duka 'yan gidan mu yake, sauran abinda ya biyo baya mai ban tausayi ne domin kuwa Abba ba ta jinya ta da Wasila ke yi ya ke ba shi, bata tabbacin da likita ya bashi na nasha guba an samo ni da kyar da taimakon Ubangiji yake ba a'ah, ta shirin daurin aure na yake yi ko in mutu ko in yi rai. Koda na farfado na yi ido hudu da Abba ban iya kara yi masa kallo na biyu ba, sabida yadda fuskar sa ta koma ta tsantsar bacin rai ban taba ganin sa cikin kwatankwacin irin wannan halin ba. A gefe Wasila na share hawaye, Umar na gefenta ya kura min ido harde da hannayen sa a kirji, gabadaya yayi wani zuru-zuru kamar wanda ya mutu ya dawo. Ina jin bai taba gamuwa da tashin hankali da bacin rai a rayuwarvsa irin na wannnan lokacin ba. Da Abba ya tabbatar na dawo cikin hayyaci na sai ya ja kujerar zaman 'yan dubiya gaba na ya zauna. Ya kura min ido yace "Siyama! Anya Siyamar dana sani na kuma haifa tareda Asshe ce wannan ko kuma dai Nos din data karbi haifuwar ki ta musanya min tawa Siyamar da wani jinin daban? Ina mamaki! Domin dai nawa sanin. Jinin malam Dalhatu Abdullahi Gembu ba zai taba aikata kisan kai ga kowa ba balle ga karan kan sa a bisa sani kuma, ba zai so ya zo duniya a banza ya koma a hofi ba. Haka ba zai so ya mutu kafiri ba. Akan wata kankanuwar bukata tasa ta duniya. A matsayi na na uba bazan ce ban so kika kubuta ba, amma na so ki cika burin ki kije lahira ki dandana azabar wuta kona wuni daya ne sannan ki dawo, watakila zaki fi sanin cewa iyaye ba abin wasa bane. Kuma duk wanda ya zabi son zuciya yayi SAKACI dasu yana tareda dawwamammiyar nadama. A karshe ina sanar dake cewa har yanzu ina nan akan baka na na cewa Omar na zaba miki, kuma jibin dana saka don daura muku aure ba zan fasa ba. Wannan karon sai ki sa wuka ki farke cikin ki don kifi mutuwa da sauri, a mika gawar ki gidan Omar kafin a wuce da ita makwanci.....". Abba ya fada cikin wani mashahurin bacin rai da ban taba gani a tare da shi ba. Daga bayan sa Ya Omar yayi gyaran murya cikin karaya ya soma rokon Abba "Abba don Allah.... na roke ka ka janye kudirin ka, ka bar Siyama ta nemo wanda take so ka aura mata. Abba rayuwar Siyama cikin farin ciki ta fiye min auren ta. Abba tunda har Siyama zata iya iya yunkurin kashe kanta a kaina Abba na hakura da Siyama na haramtawa kaina ita. Ina rokon ka kaima kayi hakurin musulunci kada ka yi fushi da ita, ka bata dama ta auri zabinta, don Allah Abba". Omar ya fada cikin despair da kuma karaya da al'amarina bakidaya. Anti tace Abba tunda har Umar ya hakura kaima kayi hakuri. Rayuwar Siyama gaba take da komai don Allah Abban Siyama..." Anti ta fada cikin hawaye, don hakika ta shiga tashin hankali irin wanda bata taba shiga a rayuwar ta ba, da tazo ta same ni ina shan fiya-fiya kuma babu jimawa na bi kwalbar muka zube a kasa, kumfa na fita daga baki na. Allah ne ya so Omar na falo a lokacin, da gudu ta fita tace "Siyama ta kashe kanta Omar, ta sha poison, ban san a ina ta samu ba". Irin zaburar da Omar yayi kamar ta fitar kibiya ya kuma daukoni a kafadar sa yasa a mota Anti ta shiga gaba basu zame ko’ina ba sai Nizamiye. An karbe ni a emergency likitoci suka rufu akaina don ceto raina. A lokacin ne Anti ta samu sukunin iya kiran Abba wanda bata san ina yayi ba a ranar. Hakika akwai kwararru ba na wasa ba a Nizamiye, watakila kwarewar su ce ko kuma ince Astagfirullah Allah bai yi kwanaki na sun kare ba kawai shi ya cece ni. Amma an kashe kudi ba na wasa ba. Sannan daga farfadowa ta Abba ya bi ni da wadannan muggan maganganun. Wanda suka nuna ko kadan suicidal attack dina bai sauko da shi daga kan dokin kudirin sa ba. Anti da Ya Omar suka dukufa roko, rokon Abba suke akan ya janye ya kyale ni in yaso duniya ta koya min hankali don wanda nake so din ma fa babu shi babu dalilin sa cikin duniya, imagination ne kawai nake yi. "Ai kuwa zata mutu cikin hasashe" inji Abba. Sannan ya juya ga Omar da ke durkushe a gaban sa, ya ce "Omar ba ka son Boddo?" A firgice Omar ya daga kai ya dubi Abba, Abba ya ce "amsa nake so eh ko a'ah ba wani dogon turanci ba". Omar ya rasa inda zai kansa, ya ce "it does not matter Abba son da nake yi wa Boddo tun tana zanin goyo, tunda ita bata so na na yafe soyayyar dana ke mata, na sadaukar da tawa soyayyar don farin cikin ta da kasancewar ta cikin kwanciyar hankali". Abba yace "magana ta kare Omar bana son jin karin komai. Ka tashi mu tafi, gobe zamu wuce Mambila ko sun sallameta ko basu sallameta ba a daura muku aure". Omar zai sake magiya Abba ya daka masa tsawar data gigita shi. Ya kuma sa kai ya fice a dakin asibitin. Dole Umar ya bi bayan sa don mukullin motar Abban na hannun sa. Yana fita yana waiwaye na. Gani yake kamar bazai dawo ya tadda ni a raye ba. A lokacin na lumshe idanuna bansan ya akayi ya akayi ba, kawai naji kwallar tausayin Umar sun wanke min fuska. Ni da Anty muka kwana duk wani motsi da zan yi a kan idanun ta nake yin sa, don tsoron ta na ko zan sake wani attempt din na salwantar da rayuwa ta. Akwai maganganu fal a bakin Anti amma ta adana su zuwa in samu lafiya. Bakin cikin abinda na aikata ya hana duk wani masoyi na sukuni a zuciyar sa kuma babu wanda na baiwa tausayi banda Ya Umar. Ita Anti da zata samu dama so take ta dan yi min shegen duka ko zata huce tashin hankalin dana jefa ta. Kwance kawai nake da ledar karin ruwa a jikin hannu na nida ita mun zama tamkar kurame ba mai ce da dan uwan sa uffan. Sai likitoci da ke ta shige da fice a kaina don tabbatar da aikin su na tafiya daidai. A daren Umar Faruq ya kasa barci, ya tabbata in har ya wayi gari jibi a gidan mu Abba ba zai fasa abinda zai zo yana nadama ba, idan a da yana ganin abin na Boddo wasa ne yanzu ya tabbata Boddo da gaske bata son sa, koda za'a dora mata wuka a makoshi bazata zauna da shi ba, tunda har Boddo zata iya kashe kanta a kansa shi kuwa meye ribar sa a cikin auren ta??? Wane farin ciki ko alheri zai tsinta a cikin auren matar da ke kin sa har haka? Matar data zabi shan guba fiye da hada shimfida da shi. Tausayin Abban mu kadai ya ishe shi amma ya yanke hukuncin da yake ganin yafi masa alkhairi. Ya kuma fi zama maslaha ga Abba sannan ya fi zama kyautatawa a gare ni. Washegari tunda safe likita ya sallame ni, Anty ta dauko ni muka taho gida jikina duka babu karfi. A falo muka cimma Abba yana saukowa daga matattakalar bene cikin shirin sa tsaf, da gani yayi shirin wucewa Mambila ne daurin aure na a gobe, don sun yi waya da Anti kafin mu taho ta gaya masa an sallame mu yace to yana jiran mu zamu wuce Gembu yanzu. Don haka muna shigowa Anti ta wuce dakin ta don dauko kayanta, nima na wuce nawa dakin kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ina hawaye, ganin irin kallon tsanar da Abba ya jefa min yau. Anti ta fito jaye da akwatin ta ta nufo daki na don ta hada min nawa kayan don ta san ba hadawa zan yi ba. Ita ta daukarmin komai ta hada cikin akwati sannan ta kama hannu na muka tadda Abba a falo, yana ta faman gwada layin Ya Omar ya ki shiga don shi zai ja mu a motar. Bayan tun daren jiya sun gama magana ya kuma gaya masa karfe goma na safe zamu kama hanya ko an sallame ni ko ba'a sallame ni ba, in ya so in karasa mutuwa a hanya. Amma gashi yanzu ana gaya masa layin Omar a rufe yake bakidaya. "Ban san ina Omar ya yi ba, ki duba min dakin sa ko bayan gida ya shiga" Abba yace da Anti. Anti Wasila tabi bayan Omar amma haka ta dawowa Abba tace bata gan shi ba, kuma bata ji motsi sa a bayan gida ba. Abba da kan sa ya tafi BQ neman Umar Anti ta rufa masa baya. Babu inda basu duba ba a dakin ba Umar babu mai kama da shi. Sai a lokacin ne ma suka lura babu kayan sa na sanyawa a dakin sai daidaiku. Akan chest-drawer Anti ta hango wata takarda da rubutun Umar ya dora biro a kai alamar bai jima da ajiye ta ba. Kawai sai ta dauka, ganin sunan Abba a jiki baro-baro yasa ta mika masa cikin kidimewa. -ABBAN MU Samun mutum irin wanda zumunci ne silar shigar su aljannah tamkar namu Abban na tabbata zai yi wuya a wannan zamanin da muke ciki. Hakika baka nufin komai a kan mu ni da Boddo sai zumuncin da kake so ya dore a zuri'ar Ummati har 'ya'ya da jikoki. Amma Abba ba kowanne mafarki da buri ne da muke da shi yake iya zama reality ba. Wasu mafarkan a mafarkai suke tabbata musamman idan Ubangiji ya san cewa ba alkhairi bane a gare mu. Hakika Abba ka yi duk iya kokarin ka na kulla wannan alkhairin a tare da mu, amma kaddara ta riga fata Boddo ta kamu da son wani na wanda take ganin zai hana ta yimin biyayyar aure, maimakon a nemi lahira da auren sai ya zame mata mujazar fadawa halaka. Na fahimci Boddo anan. Ba zan jagoranci ragamar wargajewar rayuwar ta ba sabida nawa farin cikin. Ni dan ka Omar ina bayan kanwata Boddo, and i will always stand by her, zan taya ta neman wanda take so cikin duniya kuma bazan aure ta bisa tirsasawa ba. A karshe ina baka hakuri Abban mu hakuri kan hakuri, na san na bata maka nima, akan hukuncin dana yanke. Bani da zabi ne Abba sai hakan don ka ki ka fahimce mu. Na bar gida Abba zuwa duk inda kaddara zata kai ni sai idan ka janye maganar aure tsakanina da Boddo ne zan dawo bayan shekaru uku masu zuwa in Allah ya kai mu. Idan har lokacin baka janye ba Abba zan ci gaba da zama a duk inda kaddara zata kai ni. Ni na san tunda inada kai to ni ba maraya bane Abba, amma idan na auri Boddo zan koma maraya idan na rasa soyayyar ta. Ina baka hakuri Abba, Abba Allah ya huci zuciyar ku. Ka yafewa Boddo ka kuma sa mata albarka ba don ni ba don Allah Abba. Daga Yayan Boddo Umar Gidado. Gumi, zufa, iri-iri suka ketowa Abba Dr. Mamman Gembu. Omar ya gudu! A dalilin Boddo bata son sa. Kuma yana ikirarin idan har Abba bai janye ba ko bayan shekara ukun da ya ambata ne ba zai dawo ba. Jikin Abba yayi mugun sanyi, ya saki takardar a kasa kawai sai ya juyo, da ni muka yi ido biyu idanuna a bubbude domin na fuskanci abinda ke faruwa Ya Omar ya zabi ya bar gidan mu akan dai Abba ya tursasa ni ga auren sa, kafin na ankara Abba ya yo kaina, ya soma duka na ta ko'ina da hannaye da kafafun sa iri dukan na huce bacin rai. Anti ta sa kuka ta rufu a kaina ta ce "gara kayi

Chapter 9 of 12