bar amsa-kuwwa a kunnuwa na ba, yana maimaita kiran suna na cikin shauki na soyayya wanda miji kadai zai iya yiwa matar sa magana cikin wannan yanayin da na gan mu cikin sa.
Na kasa fita in taya Anty hada breakfast yau kamar yadda na saba a dalilin zazzabin da ya ci karfi na ya rafke ni a kan gado, na koma cikin duvet na cigaba da kwanciya ina kakkarwa. Na kuma tabbata a yanayin dana samu kaina wankan janaba ya kamani, janabar da na san ban aikata ba. Shin ko dai aljani ya aure ni ne wanda nake jin ana cewa haka suke auren bil adama? Sai gani yau ina kuka rurus ina neman agajin Ubangiji a kan wannan Jinnul Aashiq.
Tsoro mai tsanani ya shige ni. Ina wankan ina jin kunyar hakan kamar na aikata zunubin da gaske. Maimakon in yi addu’ar Allah ya raba ni da shi sai na bige da addu’ar Allah ya bayyana min shi kawai muyi aure, ko aljanin ne INA SON SA HAKA!
Da farko Anti ta kyale ni bata neme ni ba don itama a kule take da ni kan maganganun dana gayawa mahaifi na jiya wadanda ita kadai ta san cewa basu bar shi yayi barci ba.
Yau din ta kasance Lahadi kuma ta kama rana ce ta hutun Ma'aikata (international worker's day) daga Abba har Anti duk suna gida, data ga shiru - shiru bata ji motsina ba har ta gama hada abin kari sai ta biyo bayana tana tambayar.
"Lafiya dai ko Siyama?”
Daga kwancen da nake dukunkune cikin Duvet na bata amsa.
“Anti kai na ke ciwo da zazzabi” maimakon ta tausaya min kamar yadda na san ta da tausayi akan ciwo, sai ta kyabe baki ce “sabida an tuna miki maganar da tun haihuwar ki kin san da ita, tuna miki kawai aka yi ba sabuwa bace, shi ne kika sakawa kan naki damuwar data haifar miki da ciwo? To Allah ya sauwake, inda alkawari dai ruwa bazai dafa kifi ba!”.
Tasa kai ta yi ficewar ta ta barni da tunanin ma’anar Karin maganar ta..
“In da halacci da amana ba za ki ki dan uwan ki Umar ba!" Ko "in da alkawari Abban ki bai cancanci wannan rashin biyayyar ba?” Dayan biyu, haka Anti take nufi ko me?.
To ni na ce ina kin Ya Umar? Ai ina jin bayan wadda ta kawo ni duniya sai Abba sai shi a wadanda nake kauna, sai Ummati sannan kowa ma ya biyo baya.
Ba zasu taba yarda da hujjoji na ba. Ko sun gane din ba zasu basu muhimmancin da ni na basu ba. Ba kowa ya san banbancin kauna ta 'yan uwantaka da kauna ta soyayyar aure ba. A sani na Namiji zai iya auren wadda baya so, ya zauna da ita for the satisfaction of his sexual desire kadai, mace kuwa ba zata iya auren wanda bata da sha'awa ta aure ko kankani a tare da shi ba, and that's exactly my point.
Aure da Omar bazan iya ba gaskiya, ko duk duniya zata taru a kaina because i've no desire for him.
A gareniSoyayya daban, kaunar ‘yan uwantaka daban. Omar can never be my choice of a husband, ban taba yaudarar Abba ba duk sanda yayi zancen nan ai gaskiya nake fada cewa Yaya na ne, bazan auri biologicalbrother na ba don babu banbanci kona haihuwa a tsakani na da Omar.
Ban taba dai gaya masu ina da wanda zuciya ta ta afu gare shi ba sai jiya dana yi subutar baki. Sabida bani da tabbacin mutum ne ko aljan. Allah kadai ya san nufin Sa na sako shi cikin mafarkai na har na saba da shi har haka, na ke jin duk duniya bani da miji sai shi, wanda na tabbata ko bajima ko ba dade mafarkan nan zasu zama gaskiya...
Mutumin nan baki, dogo siriri, mai tarin gargasa a fuska da giran ido, mai murya irin ta Asians mai sassarfar magana don junan mu aka halicce mu.... kuma yana gab da bayyana kan sa gare ni komai daren dadewa.
******
VOA - HAUSA
S
hirin su na safiyar yau Lahadi, wanda ya kasance (live-program) ne daga mita 0900 UTC (VOA-Muryar Amurka, Hausa). Shi Abba ya kunna a falon kasa ya kure sautin, yayi filo da hannayen sa bisa doguwar kujera yana sauraron labaran duniya daga bakin tauraruwar sa Grace Alheri Abdu. Tun bakwai na safe yake sauraren VOA har zuwa karfe tara lokacin da aka gama, kuma lokacin karya kumallon su yayi shi da iyalin sa.
Grace Alheri Abdu na gama nata shirin, akayi taken VOA mai dadi, har Abba zai kashe rediyon sa shirin "HANTSI LEKA GIDAN KOWA" ya rufawa sallamar Grace baya, wato ya maye gurbin nata shirin.
"Hantsi Leka Gidan Kowa" Sabon shiri ne daga gidan rediyon VOA wanda ya ta'allaqa kacokam ga zaqulo fitattun mutane na Afrika da suka shahara a fannin su wajen baiwa kasashen Afrika gudunmuwa a kafatanin fannonin rayuwar su ta bangarori daban-daban da suka hada da kiwon lafiya, tattalin arziki, ilmi, rubuce-rubuce (literature), tarihi, wasanni, siyasa ko zamantakewa.
"A yau shirin mu na "hantsi leka gidan kowa" yana tafe ne tare da tsohon marubucin Najeriya Farfesa (Noble Laureate) Wole Soyinka, wato Shakespearn Najeriya, wanda muka fassara wa masu saurare zuwa harshen Hausa (live) daga gidan rediyon VOA-Amurka Hausa a safiyar yau Lahadi, Ashirin ga watan Aprilu, tare da ni …… HAMZAH....ALMUSTAPHA....MAWONMASE........!!! (Ya fadi sunan nasa dalla-dalla yana sama yana kasa da sautin sa kamar cikin rhyme). Tare da cewa; Ayi saurare lafiya......".
Iyaka abinda ni Aisha-Siyama na ji kenan a safiyar yau, safiya mai dumbin tarihi, safiyar da ta juya ta kuma wulwula rayuwata bakidaya. Muryar ta fito ne kai tsaye daga radiyon Abba ina kokarin fitowa daga daki na don halartar tebirin karin kumallo. A karshe ya yi wa masu sauraren sa bankwana da cewa daga wannan lokacin, daga wannan hirar da zai yi da Soyinka, za’a jima ba’a ji shi ba don zai tafi karo kwas na wasu watanni kafin ya dawo.
Nan take jiki na ya karbi wani irin quickreaction na extremeshock, kafin zuciya ta tayi tsalle ta fado kasa daga cikin kirji na ta karbi wani irin coolness duka a lokaci guda. Tamkar na narke a inda nake tsaye.
Numfashi na yayi sama yana dambarwa a tsakanin kirji da hanci da kuma baki na. Tamkar mai fama da ciwon asthma sakamakon yadda shaqar numfashi ya koma cikin hunhu na ya gagare ni. Domin muryar da na gama ji ce a daren jiya a mafarki na nake jin ta yanzu a rediyon Abba, muryar mutumin da ya haifar min da zazzabi da wankan janaba na babu gaira babu dalili a safiyar yau. Ko ko ince; muryar da na girma na kuma rayu sama da shekaru bakwai ina jin ta cikin kunnuwa na, a cikin yanayin barci (mafarki) da yanayi na ido biyu (imagination) a wasu lokutan. Ta yaddda ta riga ta samu kyakkyawan matsuguni a kwanya ta; a koina na ji ta zan gane ta.
Na sako kafa ta a falon kenan zan wuce diningroom don na san duk irin ciwon da nake fama da shi ban isa in ki fita cin abinci ba musamman da yake yau tare da Daddy ne a karshen mako, yana gida don haka tare muke cin three square meal, amma sai na dan dakata ina saurare, iya abinda na ji kenan a kan shirin amma na gama tantance muryar DREAM HUSBAND dina ce. Kawai kuma ba zato ba tsammani na Abba ya kashe rediyon sa domin Wasila ta zo ta tsaya a kan sa tana faman gaya masa "Breakfast is ready!".
Su duka suka juya a tare jin Yiiipp! An fadi a bakin entrance na shigowa falon, Siyama ce dake shigowa ta zame ta fadi kasa, gabadaya suka yi kaina a guje suka daga ni suna faman kiran sunana amma ina! Sun nemi bakin 'eye balls' dake cikin idanun kowannne dan adam sun rasa a tare da nawa idon.
Wasila na fadin Baban Siyama maza dauko mukullin mota" shi kuma yana fadin "ki nutsu, mu fara bata taimakon gaggawa tukunna, kawo min ruwa mai sanyi" kafin ya rufe bakin sa Anti ta fita da gudu neman ruwa Abba kuma ya hau karanta min addu'a yana tofawa, Maryam Jamila ta na gefe tana kuka tana cewa "Anty Siyama!"
Abba na shafa min ruwan da mintuna biyu na yi ajiyar zuciya mai nauyi, kamin in lumshe idanuna bakin kwayar cikin su ya dawo. Hawaye ya gangaromin ta gefen ido, na soma sambatu ".... Abba na gaya maka dama yana raye, mutum ne ba aljani bane. Allah ne ke nufin mu da wani al'amari mai girma da ya shallake tunanin mu". Abba a kidime ya ce "Waye?" Na ce "Dream Husband dina, na rantse maka da Allah Abba yau na ji maganar shi a zahiri ba'a mafarki ba...... saura ganin sa ya rage min...." nayi - nayi in tuno sunan dana ji ya ambaci kan sa da shi kuma na kasa, tamkar anyi formatting memory dina mai alhakin tuna abubuwa, ko kuma don ban taba jin suna irin sa bane?.
Abba sabida takaicin dana ba shi sai ya sakar wa anti Wasila ni yayi tafiyar sa dining ya zauna yayi jugum, sai kuma ya hada shayi amma ya kasa sha. Tsaki yayi can ya tashi ya dau mukullin mota ya bar gidan ya manta jallabiyya ce a jikin sa sai gajeren boxer daga kasan ta. Shi kansa bai san ina zai je ba".
Anti Wasila ta ciccibe ni ta kai ni dakin ta, ta koma ta hado shayi mai kauri ta kawo min, a baki ta bani duk da zafin sa haka na bude baki na sha sosai don jiya ban ci abincin dare ba na kwanta.
Saida Anti ta tabbatar na samu nutsuwa, barin da jiki na ke ta yi na yunwa da shock ya ragu, sai ta sanya tafukanta cikin nawa ta matsa a hankali. Tace "Yau dai sai an gaya min wanene wannan Lucky din da ke neman sheka min 'ya barzahu, ya hada ta da fushin mahaifin ta babu gaira babu dalili".
Wani matsiyacin kuka ya zo min, na ce "Aunty Wasila kin san ba zan miki karya ba ko? Ba zan iya boye miki komai ba ko? To wallahi duk duniya shikadai nake so, Allah ya riga ya nuna min shi tun kafin ya bayyana min shi" cikin mamaki Anti tace "a ina ya nuna miki shi din?""A cikin mafarkai na Anti, rana dai dai ne bana kwana in tashi ban ganshi cikin barci na ba, har ta kai ta kawo zuwa yanzu na haddace kamannin sa da sautin muryar sa". Idanun Anty was like irin "Siyama ta yi gamo, aljani ya aure ta". Abinda na gani a cikin idanun Anti tsabaragen tsoro ne zallah. Ta ce "kwanta ki huta, in Abba ya dawo zan masa bayani abin ba na fushi bane Siyama kina bukatar taimako".
Taimakon da ban gane wane iri take nufi ba.
Da Abba ya dawo daga zagayen da yaje yayi a mota don neman nutsuwar yanke hukunci akan lamarin 'yar sa Siyama, sai da tayi kokari ya sha tea da chips kadan, sai ta karkace ta soma lallashi.
"Baban Siyama fushi da Siyama ba naka bane, na fahimci gamo tayi". Abba ya dakata yana kallon matar sa Wasila da kankance ido da sakakken baki, ta ce "kwarai gamo ne, ina kyautata zaton namijin dare (jinnul aashiq) ya aure ta yana zuwa mata cikin mafarki, yau kuma ta ganshi maybe a cikin bangon falo ido da ido". Jikin Abba yayi sanyi ya ce "kin tabbata ba salon iskancin ta bane?" Anty ta yi rantsuwa akan abunda take zargi ta ce kuma idan aka samo malamai na gaske da suka iya rukiyyah zasu iya raba ni da shi, (a distant cousin of hers) ta yi fama da (similar problem) kuma da iyayen suka dage da neman magani an rabu lafiya yanzu har ta yi aure.
Dole Abba ya yarda da Wasila amma wani bangare na zuciyar sa yana tababar yiwuwar hakan. A tsari da kafin da yasa aka yiwa gidan nan nashi kafin su tare wani shaidanin aljani bai isa ya shigo ba har ya samu matsugunni a jikin iyalin sa. Shima Gidado ne ya bashi wannan laqanin kafin rasuwar sa.
Amma don kore shakku haka ya dauko malamai nagari masu fitar da jinnu daga jikin bil adama suka saka ni a gaba aka banka min turare sannan suka fara karatu. Baka jin komai sai tari na lokaci - lokaci sabida rashin dadin turaren nasu, amma har suka gama Suratul Baqarah ras nake, sai ma kafa danake canzawa position don karatun yana min dadi, na dade ban yi tilawar surah Baqarah ba sabida sakaci irin nawa. Ni na san bani da wani aljani amma na isa in yi jayayya? A je a hakan. Watarana da kan su zasu yarda da ni cewa, na san abinda basu sani ba.
A karshe malaman suka gayawa Abba gaskiya babu shaidani a tare da ni, watakila dai na saka wani saurayi a raina ne shiyasa nake yawan mafarkin sa yake kuma yi min gizo a kunnuwa na.
Abba ya kawo sadaqa ya sallame su. Bai ce komai ba ya bi matattakala zuwa saman bene Anti Wasila ta rufa masa baya.
Tun kafin su karasa daki ya ce "kin ga abin da nake gaya miki ko. Salon iskanci ne kawai irin nata don ta gujewa auren dan uwanta, Omar bai ki Siyama sai ita ce zata ki shi har haka? Na rantse da Allah sai na aura mata Omar sai dai ta mutu da kiyayyar hakan..." Anti bata taba ganin fushin Abba a fili irin na yau ba. Tace "to tunda ta ce yana raye a duniya ka nemi ta kawo shi, in ta kasa sai kayi abinda ya dace" yace "babu wanda zan saurara akan Siyama, ni addini ya baiwa damar zaba mata miji kuma na zabar mata, ya rage nata tayi min biyayya ko ta bada min kasa a ido babu wani shirmen ta da zan kuma saurara".
A daren ranar Anti ta sameni a daki dauke da indomie da dafaffen kwai guda biyu, ina kwance ne kawai ina fiskantar ceiling tunanin duniya ya addabe ni, kunnuwa na ba abinda suke son sake ji sai muryar sa da sunan sa, takamaimai bansan daga wane gidan radiyo bane don tsakiyar zancen na tsinta babu farkon sa.
"Inaga zaki iya cin wannan tunda baida nauyi" ta fada tana zama a gefe na. "Bana jin yunwa Anti""nikuma bazamu yi magana ta fahimta ba sai kin ci abinci, tashi zaune a baki ma zan baki" ta debo abincin ta nufo bakina da shi, na kauda kai, sai ta hau yimin wakar da take yi wa Shukra-Nadiya idan ta ishe ta da rigima.
"Hayya bina yaa Nadiaa, kam sa'atan laki na'imah!"(Tashi haka ‘ya ta Nadiya, awannin ki nawa kina barci?)
Dariya ta bani sosai don wato nufin ta yau ni da Nadia yar watanni shidda bamu da maraba a wurin ta.
Dole na karbi lomar abincin daga hannun ta, loma uku nayi nace don Allah ta kyale ni kada in yi amai.
Da Anti ta fahimci na dan ware sai tace dani.
"I want to see him!"
Da alamar tambaya na dubeta ina juya hannu wato ina son sanin wa take son gani din?
"I want to see our Dream Guy, in yi magana da shi ta gemu da gemu. Idan na gamsu dashi zanyi kokari in gamsar da Abba duk da na san ba karamin aiki bane mai sauki na daukowa kaina ba.
Amma a matsayi na na 'yar uwa mace na san illar auren dole don haka zan taimaka miki, ki fada masa gobe ya zo ina son ganin sa a office dina"
Sai na rasa abinda zan ce mata, anya idan na kara maimaita mata cewa nima ban san shi a zahiri ba, ban taba ganin sa ba, ban kuma san a ina yake ba zata manna min hauka ba? Tunda dai ta ce in kawo shi zata taimaka min to abinda zan yi yanzu shine in nemo shi, a duk inda yake, in kawo mata shi ta rarrasar min Abba ya karbe shi.
Siyama kina da tabbacin shi yana son ki zai kuma iya auren ki? Haka ake soyayyar baka san mutum ba baka san halin sa ba baka san komai akan shi ba? Bai ce yana son ka ba sai ka je ka ce masa zo ka aure ni? Idan ma kin same shin kenan. Ko kuwa shi yace miki yadda kike mafarkin sa shima haka yake naki mafarkin? Lamarin is complicated amma ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare. I vowed to find him, a duka gidajen radiyon jiha dana tarayya. Kuma zan ke ta kasa kunne a duka gidajen radiyo da talbijin ma tunda na fahimci mijin mafarkin nawa Professional Radio Presenter ne. Ba zai min wuyar riska ba.
Da Aunty ta ga nayi nisa a duniyar tunani sai ta mike tana fadin "sai ya zo. Ki fada masa daga karfe tara na safe zuwa sha biyu na rana zai iya gani na a HumanitarianAffairs".
Daga haka ta fita, tana kara cewa "kinsan dai WAEC da NECO ne a gaban ki, ki ajiye komai ki fuskance su in kina son gina future din ki yadda ya kamata, idan zaki bari soyayya ta zama priority din ki a rayuwa kin kade har ganyen ki".
Nisawa na yi bayan fitar Anty ina cewa ni kam ai har fadowa kasa warwas na riga na yi daga kan bishiyar karewar kadewar ganye indai a kan sa ne. A yadda nake jin karfin soyayyyar sa a raina zan iya bashi rayuwata, zan iya batawa da kowa in dai har zan tsira da shi. In na ce kowa ina nufin KOWA!
*******
A
unty ta fito daga matattakalar bene inda dakin barcin ta yake zuwa daki na rike da 'yan mukullan motar ta "Siyama na fita, zani Wuse Market kayan cefanen mu sun kare, da dai-dai kike da na nemi rakiyar ki, to duk kin bi kin susuta kan ki akan da namiji, kin susuta min Abban ki babu gaira babu sabar na kasa gane kan sa. Ga nan Nadia ki kula da ita kafin na dawo".
Ta fada tana miko min ‘yar autar mu Nadia, babu kiwa ba komai yarinyar ta taho zuwa gare ni tana bangale baki, ta bani jakar jegonta mai dauke da abincin ta na frisco cream da kayan canjawa da su pampers din ta.
"Sai kin dawo Anti, in kin ga radio please ki sayo min, latestone".
"Radio kuma? Yaushe kika koyi sauraron radio naga dai da bata dame ki ba?"
"Ina neman abinda zai ke debe min kewa ne ya hana ni tunanin auren dolen da ake son yi min".
Aunty ta gyada kai kamar kadangaruwa ta sa kai ta fita tana mamaki. Ita bata ga aibun Omar ba, yaro saurayi matashi jazur da shi kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba, ga tsafta ga addini, a irin shakuwa ta da shi bata taba zaton haka zata faru ba in aka fara maganar auren mu. Duk da na dade ina cewa ai Yaya na ne.
Zata so kwarai ta ga wannan dream man din na Siyama, ta ga shin me ya taka har haka da ya narkar da zuciyar Boddo-Siyamah a murya da mafarki kadai? Ta san dai ba fin Omar kyau yayi ba yaro kamar Balaraben kasar Kuwait. Kuruciya ce kawai take damun Siyama ta ke neman kai ta ta baro, to wanda ya ki bin maganar mahaifin sa ai kuwa ya kai kan sa ya baro.
Anti da ta tashi dawowa ta sawomin Radio mai quality kirar LG wadda babu inda bata kamowa gida da waje. Na yi mata godiya mai yawa sosai. Na ji kamar ma na hadu da shi na gama. Tamkar ta cikin radiyon nan zai bullo ya cimmani, ya wanke tsatsar kaunar sa da soyayyar sa da ke zuciyata.
Tun daga ranar na yi mata saitin kamo tasoshin ko’ina, na dukufa sauraren tasoshin radio daban - daban na gida Najeriya, da ban kara jin muryar dana ke nema ba sai na karkata ga sauraren International Media masu magana da Harshen Hausa, nice kullum BBC ke har ma da VOA dana fi karfafa zaton a can naji shi, kuma ita ce major din Abba, da wuya ka ji yana sauraron wata tasha ba VOA ba, amma abun kamar delusion na samu a waccan ranar. Don kuwa ban kara jin waccan muryar ba ko mai kamar ta, ko sunan da ya ambaci kan sa da shi wanda na yi ta kokarin in tuna na kasa, sai a mafarki na kuma.
Ni dai na tabbata na ji ta real a Radiyon Abba, saidai ban samu naji ko daga wace tasha bane, in na yi kamar in tambayeshi "Abba kwanaki wace tashar rediyo ka kunna ranar dana fadi dinnan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 12