An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
SAKACIN WAYE?
Sumayyah Abdulkadir
takorikabara@gmail.com
babbangoro2015@yahoo.com
`GORON SABUWAR SHEKARA` (2023).
TARE DA NI;
SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI.
1 GA WATAN JUNAIRU, 2023.
2023
HAKKIN MALLAKAR LITTAFIN DA DUK ABINDA YA KUNSA NA MARUBUCIYAR SHI NE SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI). A GUJI KARANTAWA A YOUTUBE KO SARRAFA SHI TA KOWACCE HANYA BA TARE DA RUBUTACCEN IZNI NA BA.
“GEMBU”
(GARIN MU DA BABU KAMAR SA A SANYI A FADIN KASAR NAJERIYA)!!!
G
arin Gembu, kamar yadda na samu cikakken labari daga bakin Ummati, da sauran bincike na na ilmi a kan tarihin yankin namu, kasancewa ta wata irin mutum mai son sanin Tarihi da bin ussin salsalar ilmin abu, yankin Gembu wani babban birni ne ko kuwa in ce alkarya da ke a yankin Duwatsun “MAMBILLA” a jihar Taraba a Najeriya, shine babbar Hedkwatar karamar hukumar Sardauna wato (Sardauna Local Government) da aka fi sani da “Tsohuwar Mambilla” a jihar Taraba.
Sunan Sardauna Local Government ya samo asali tun daga zuwan Alhaji (Sir) Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto yankin mu na Gembu a shekara ta (1956).
Mutanen Mambila ko Mambilla suna zaune ne a Tudun Mambila (Mambilla Plateau). Garin yana kusa da Boda wato iyakar da ta raba kasar Najeriya da kasar Cameroon. A wasu lokutan masana tsaunin Mambila kan kira tudun na Mambila da ‘Heaven on Earth’ wato (Aljannah a duniya), wannan ya samo asali da kasancewar garin Gembu gari mafi kyawun yanayi na sanyi mai ban mamaki a arewa maso gabashin Najeriya.
Masana ilmin labarin kasa (Geographers) sun tabbatar da cewa a kasar Najeriya bakidaya babu gari mai irin kyawun yanayi na sanyin Gembu. Sannan gari ne mai cike da albarkatun kasa wanda da gwamnati zata maida hankali wajen bunkasa shi da ta samu arzikin kudin shiga mai yawan gaske a kan sa, sakamakon yadda garin ya ja hankalin masu yawon bude ido na ciki da na waje. A Gembu akwai wasu manyan Dams guda biyu wato ‘Barup Dam’ da ‘Tunga Dam’ masu tsohon tarihi tun tana ancient town of (Bommi), garin Mambila na zaune a matsakaitan duwatsu tsayin kusan mita 1,348 (4,423 ft) sama da matakin Teku, yana daga cikin manyan biranen Najeriya.
Gembu na da habakar kiwon shanu, tumaki, awakai da Buffalo. Tuntsayen gida kuwa Allah ya yi albarkar su a Gembu, wanda ya sanyawa garin albarkar nama da abinci mai lafiya, duk da cewa sun fi kiwon dabbobin su fiye da cin su.
Abincin da ya fi yawa a Gembu shine kayan marmari (fruits) wanda ke taimakawa kwarai wajen kasancewar mutanen garin cikin koshin lafiya, yawan shan ‘Piya’ ya maida fatar mutanen Mambila wata irin danyar fata mai taushi da sulbi kamar larabawa.
Gembu gari ne da Allah ya halicci kyawawan mata, in na ce kyau, to ina nufin tsurar kyau na halitta fiye da na sauran duka kabilun fulanin Najeriya. Akasarin ‘yan Gembu (musulman cikin mu) zaka gan mu dogaye haka sirara masu cikar zati da kamala, sirantakar dake kara mana kyau, matan Gembu masu asalin dogon hanci da doguwar fuska ne, masu sassanyan kyau da babu fulanin da suka mallaki irin sa a fadin kasar Najeriya.
Wadannan din dana ambata ba dukkan su ne ‘yan kabilar Manbila ba, mutanen Gembu sun fito ne daga rukunin kabilu daban - daban wadanda suka hada da; Mambilla, Kaka, Kambu da Panso.
Yaren garin Gembu shine fulatanci ziryan din sa, Hausa bata da tasiri sosai. Yaran da aka haifa a Gembu ko “zo in ka she ka” da hausa basu sani ba sai wadanda suke fita ko suke ta’ammali da bakin haure.
Matan Gembu wasu irin kyawawan mata ne na bugawa a jarida kamar sun hada iri da larabawa, sabida tsananin sanyin garin basa ta’ammali da fanka ko A/C. Mutanen da aka haifa a Gembu basu taba ganin fanka ko A/C a zahiri ba sai a talbijin ko a littafi.
Sabida karfin harshen fulatancin su hatta a Choci da fulatanci a ke sermon kasancewar kiristocin su kusan sun fi musulmai yawa.
A wancan lokacin dana ke magana a kai mazan Gembu na fita cikin jihar Taraba don yin karatun boko amma matan Gembu basa karatun boko sai daidaiku, wadanda a wannan karnin da ake ciki ne ma suka dan fara karatun boko, shi yassa ake fadin cewa matan Gembu ‘yan kabilar Mambila basu da wayewar kai kamar na sauran fulanin Jalingo. Amma kuma suna bada karfin su a kan neman ilmin muhammadiyya wanda yasa bazaka taba kiran su jahilai ba.
Sana’ar matan Gembu sakar kayan sanyi da zannuwan gado na rufuwa masu kauri, wadanda suke sakawa don amfanin kan su sabida yanayin garin su. Sai ko kiwo da noma.
Sunan yaren garin ne “Mambila” sunan garin kuma shine “Gembu”. Kamar yadda na fada a sama Gembu shine birnin Mambilla wanda ke karkashin karamar hukumar Sardauna.
Gabadayan garin da sauran kauyukan da ke makwabtaka da shi a kan Duwatsu suke tsugunne, wato (Mambilla Plateau).
“Mambillah, the coolest wheather in Nigeria - (Wikipedia-Britannica)”.
Mambilla ya zama tourist attraction na jihar Taraba sakamakon ni’imar sanyi da Allah ya yi wa garin da sauran albarkatun kasa da bazasu lissafu ba.
Geographers da yawa sunyi rubutu a shafin wikipidia a kan tsaunin Mambila, haka masu binciken albarkatun kasa (soil scientists) sun tabbatar da cewa akwai Zinare da Shudin Yaqutu (Gold and Blue Sapphire) kwance a cikin kasar Mambilla Plateau, wasu marubutan ilmi kuma sun yi ittifaki a kan garin Mambila wanda sam gwamnati bata maida hankali akan albarkatun sa ba, da cewa; da gwamnatin Najeriya zata maida hankali a kan sa da ya tabbata “Heaven on Earth” din da ake kiran sa da shi ko kuwa ya zama tamkar kasar Dubai a Najeriya.
Hanyar zuwa garin Mambilla kan shi a kan dutse yake, wanda ya taho daga garin Jalingo. Mambilawa wato ‘yan asalin Gembu basu cika ji ko yin yaren harshen hausa ba musulmin su da kiristocin su. They have a very strong Fulfulde accent wanda ya bambanta dana dukkan fulanin Najeriya.
Kauyukan da ke yankin Gembu sun hada da; Tunga, Maisamari, Yelwa, Gurgu, Sabon gari da kuma Nguroje.
Kafin zuwa garin Gembu sai ka fara isa Numan ta jihar Adamawa, sannan ka dauki hanyar Taraba, tafiyar awanni biyu a tsakani kafin ka iso Jalingo, daga nan ne zaka dauki hanyar da zata kai ka Gembu, tafiyar awanni takwas a tsakani kafin ka samu isa Gembu.
Don haka tafiya daga Kano ko Kaduna zuwa Gembu tafiya ce mai nisa ta tsahon awanni 21-22, tafiyar kwana daya kenan cur, idan har ba mutum ya yi transit (matsaya) a garin Jalingo ba.
Kasashen turawan yamma sun maida Gembu ‘tourist destination’ na Taraba, ba ka raba Gembu da bakin jar fata lokaci-lokaci suna daukar hotuna a cikin motocin su masu budadden sama. Ba turawa kadai ba duk ma wanda ya san ni’imomi da albarkatun da ke tattare da Gembu kuma ya ke da halin zuwa to kuwa zai so ya kai kan sa yawon bude ido wannan gari namu mai dimbin albarka, don hutawa da karin fadadar ilmi, musamman in ka kasance mai son karin ilmi a kan geographical setting na kasar Najeriya.
Gembu na kusa da wata karamar hukuma mai suna Gashaka, inda a can ne ‘Gashaka Gumti National Park’ ya ke.
- GEMBU; Garin da ya tara tsala-tsalan ‘yammata mafiya kyawu a Najeriya - (Saliadeen Sicey).
Da zarar ka fara haurawa kan tsaunin Mambila daga wani tsauni da ake kira ‘Mayo Selbe’ da ke karamar hukumar Gashaka, zaka hangi Tsaunin Mambilla mai tudun gaske lullube da korran ciyayi da wasu irin dogayen bishiyoyi da yayyafin hazon kankara ya yi musu mayafi, don wasu lokutan kankara har zuba ta ke.
Dalilai da yawa zasu sa ka son ziyartar Gembu; na farko zaka so ziyartar garin Gembu ko don ka ga tsala-tsalan matan da Allah ya halitta a can, in kai mai son zane-zane ne har ka so ka zana su da alkalamin ka, ka sha fruits nunannu iyaka shan ka (musamman Piya), ka sha danyar madara da nono kindirmo iyaka yunwar ka, ka ji ni’imar sanyia jikin ka da zuciyar ka iya ka jin ka, ka ji kamar ba a kasar Najeriya ka ke rayuwa ba, ka kuma amfana da tarin albarkatun kasar da ke tattare da garin, ka kara girmama girma da buwayar karfin ilmin halittar ubangiji.
*****
UMMATIN MAMBILLAH!
U
mmati, sunan Kaka ta kenan wadda ta haifi mahaifi na. Sunan ta na asali Saudatu, ni na saka mata suna (Ummatin Mambila), kasancewar ita ta raine ni, daga madarar shanun ta mai dumi da gardi da ta zama makwafin nonon uwa a gare ni a wancan lokacin. Ban taba sanin dumin jikin mahaifiya ta ba sai na Ummati, na san fuskar ta dai a hoto kan wani tsohon farin hoto marar kala daukar zamanin da, da Ummati ta taba nuna min, sai naga ba maraba da tawa fuskar banda kuruciya dana fi ta, duk da cewa sanda aka yi hoton ma da tarin kuruciyar ta don bata cika shekaru ashirin ba. Kuma Ummati ta sha gaya min da kuruciyar ta ta rasu.
Sunan Ummati da na lankaya mata tun ina koyon magana shi ya bi ta a bakin ‘ya’ya da jikokin ta, dama jama’ar garin Mambila baki daya, ita da kan ta ‘Ummati’ ta ke kiran kan ta da kanta, Saudatu ya dade da bacewa a bakin kowa.
Ita da mijin ta mai rasuwa Malam Dalhatu ‘yan asalin garin Gembu ne, iyayen su da kakannin su sune tushen kabilar Mambila, wato wadanda sune ‘yan asalin garin Mambillan tun daga iyaye da kakannin su, aka kuma haife su a nan, suka girma suka yi aure suka rayu tsayin rayuwar su a nan.
Malam Dalhatu Abdullahi Gembu, ya rasu ya bar matar sa Ummati da ‘ya’ya maza guda uku, Gidado da Mamman wadanda shekaru biyu ne kawai a tsakanin su sai suke tamkar tagwaye a idon mutane, sai kuma autan Ummati wato Baffa Adamu wanda suka baiwa ratar shekaru kusan bakwai.
Wadannan zaratan ‘ya’ya maza guda uku na Ummati duka sun tashi sun girma tare karkashin kulawar ta da jajircewar ta a kan kiwo da sana’ar saka da ta ke yi don ta tallafi maraicin su a bayan ran mahaifin su. Ban taba ganin jarumar uwa irin Ummati ba. Wadda ta tsaya tsayin daka wajen hada kan ‘ya’yan ta da daukar dawainiyar su ta yadda basu taba kukan basu tashi tare da mahaifi ba.
Lokacin da ta tashi yi wa Gidado da Mamman aure sai ta yi takakkiya ta tafi har makwabtan su garin da ake kira kauyen Gashaka, ta nemo musu auren Yaya da kanwa ‘yan asalin Gashaka masu nasaba mai girma sabida tsoron ta na kada mace ta raba mata kan su.
Asshe da Hassu ‘ya’yan wani attajirin bafillace ne a Gashaka, in aka ce miki attajirin mutum a Mambila to fa ba tsabar kudi ko tarin dukiya ya bashi wannan sunan ba, a’ah; yawan dabbobin ka da gonakin ka na gado sune arzikin ka a Mambila.
To ita kam Ummati ba ma wannan ta duba ba wajen aurawa Gidado da Mamman Aisha da ake kira (Asshe) da Hafsatu da ake kira (Hassu) illa duk fadin garin Gashaka su ne yaran da aka tabbatar sun sauke Al’qur ani sun kuma haddace shi kafin su cika shekaru goma-goma. Hassu da Asshe ‘yan biyu ne masu kamanni daya basu taba yin karatun boko ba sai na addini. Wanda ya sanya suka zama ‘yammata masu nutsuwa da tarbiyyah ababen rububi a wajen samarin Mambilla, kowanne uba da kowacce uwa fatan su a auro musu zuriyar Muhammadu Jauro, ga kuma kyawun sura da Allah ya basu.
Gidado da Mamman ra’ayi ya banbanta a kan abinda suke so a rayuwa, yayin da ilmin boko ya kunno kai a Manbila wasu sun karbe shi da hannu bibbiyu musamman kiristocin cikin su, wasu kuwa musaman musulmi suna tababa a kan amsar shi, wasu da yawa sun yi hannun riga da shi ne da cewa sakon missionaries ne.
Mamman dai ya karba da hannu bibbiyu ya shiga makaranta yayi firamare da sakandire yana kuma hadawa da kiwon shanun su na gado da noma duka bai bar Gidado da wahala shi kadai ba, Gidado ya yi wa kansa Allah ya kiyaye da boko ya maida hankali wajen kula da mahaifiyar su, daga noman da kiwon babu wanda ya dame shi ya fi gane ya tara yara a a zaure yana koya musu karatun Al’qur’ani, a kowanne karshen sati iyayen su su bashi sadakar kudin Laraba. Da haka ya zama malami sosai har manya yake karantarwa littafan addini a Alhamis da Juma’ah.
Dan autan Ummati kuwa wato Baffa Adamu har ya fi Mamman son boko, Ummati kuma ta basu dama kan kowanne ya yi abinda yafi so in dai ba sabon Allah bane.
Ta sadaukar da shanun gadon su masu yawa kafin a bawa Gidado da Mamman auren Asshe da Hassu. Gidado ya auri Hassu, Mamman ya auri Asshe. Gidado shi ya fara samun rabo shekara na zagayowa Hassu ta haifa masa Umarul-Faruq. Yaro tamkar khaki (photocopy) na mahaifin sa Gidado.
Asshe kuwa shiru, tun ana saka rai har an hakura, da abin ya dame ta duk inda ta ji mai bada maganin haihuwa sai ta je a boye ta karbo sassake don idan ta bari Gidado ya sani zai sata a gaba ne yana mata wa’azin Allah kadai ke bada haihuwa, ta yarda Allah ke bada haihuwa amma shi ya ce tashi in taimake ka.
Lura da damuwar Asshe da Ummati ta yi a kan haihuwa. Da Faruq ya isa yaye sai Ummati ta dauke shi ta baiwa Asshe. Don farin ciki Asshe saida tayi kuka a lokacin ita Hassu goyon ciki na biyu take yi.
Asshe ta dauki Umar ta rike da dukkan kaunar duniya da kulawar data fi wadda yake samu a gun mahaifiyar sa. A wajen haihuwar na biyun ne sai ya zo da karar kwana Hassu ta rasu tare da abinda ke cikin ta.
A wancan lokacin zautuwa ne kawai Malam Gidado bai yi ba sabida mutuwar matar sa uwar dan sa abokiyar rufin asiri, Hassu. To kuma ina ga ‘yar uwar ta da suka fito daga mahaifa guda suka yi yarinta da kuruciya da aure tare?
Da kyar da kuma rokon Allah har da rubutun dangana Ummati ta samo kan sa, ya koma karantarwar sa kmar yadda ya saba. Malam Muhammadu Jauro wato mahaifin su Hassu ya ce “inama ina da wata diyar! Da na baiwa Gidado, domin ban taba yin surukin da ya san darajar mace kamar sa ba, amma duka na aurar da su”.
Tun daga lokacin Baba Gidado ya dauki soyayyar duniya ya dora a kan Ya Umar, Inna Ashe kuma ta goya Umar - Faruq goyo na amana bata da lokacin kan ta sai na Faruq, bata da hidimar kowa sama da tasa ko mijin bata bashi lokacin da ta ke baiwa Faruq, koda yake ai dama Dan ta ne tunda kuwa shaqiqiyar ta ce ta haife shi. Wadda har ta rasu tana gaya mata a kullum “ke na haifawa Umaru dan ki ne halak malak”.
Auren Asshe da Mamman ba jimawa gurbin karatun sa da ya nema a jami’ar Jos ya fito, ya tattara ya tafi Jos ya bar Asshe tana goyon Omar-Faruq a gaban mahaifiyar sa Ummati. Sai da Omar ya shekara bakwai cikin ikon Allah buwaya gagara misali rana daya (bayan ta riga ta fidda rai), sai gashi Allah ya dubi hakurin ta da zumuncin ta a kan maraya ya bata nata rabon, wato ta haife ni.
Lokacin da na fara tasawa sai mutane ke cewa ai babu wanda nake kama da shi duk cikin iyayen mu, Ummati da ma dangin mu na wajen uwa dake Gashaka sai da Omar kadai. Dukkan mu kuma da iyayen mu mata muke kama don haka jama’a da yawa da basu san tarihin mu ba sun dauka uwa daya uba daya muke, musamman yadda Omar yake taya Asshe raino na tun ina mitsitsiya ta ya ke goya ni, yaje makaranta da ni goye a bayan sa.
Tun ana korar sa kan ya mayar da ni gida ya dawo, sai malamin ya ga ya tsaya a bakin tagar ajin su ya ki tafiya yana leke yana sauraron karatun daga bakin taga, dole malamin su yake jin tausayin sa ya kyale shi yake zuwa karatu da ni. Don ya lura kaunar da Ya Omar yake min tana da yawa.
Wannan ya faru ne a sanda na fara wayo. Wani abun jimami da ya biyo bayan murnar haihuwa ta shine tun bayan haihuwar Asshe ke fama da matsalar zubar jini, an yi yawon neman magani iri-iri har babban asibitin jihar Taraba inda likitoci suka tabbatar da cewa magunguna masu karfi data yi ta sha na gargajiya don neman haihuwa su suka lalata mahaifar ta, Allah ne ya rubuta zan shaki iskar duniya shiyasa har ta iya ta haife ni.
Aka saka ranar da za’a yi mata aikin cire mahaifa don a samu zubar jinin ya tsaya ta huta ta samu lafiya gabadaya amma babu batun sake haihuwa.
Da ranar ta zo aka yi komai lafiya aka gama lafiya, ana ta murna wahala ta kare, ashe kuwa da gaske babbar wahala ta kare domin kuwa Inna Asshe, bata farfado daga allurar anaesthesia ba.
******
MAMMAN
“
Kina nufin Hassu da Asshe duka sun shigo rayuwar mu ne ni da Yaya Gidado halan don kawai su haifa mana marayun ‘ya’ya su bar mu da kananan marayu su koma?
Me kike nufi da cewa ta zarce a cikin allura??
Kina nufin, nima ni kadai zan raini ‘dan nan/'yar nan kamar yadda Yaya Gidado yake rainon Omar Faruk shi kadai???
To shin da wanne nonon kike nufin zan raine shi/raine ta?
Ai gara Umar ya sha nonon uwa har na tsayin shekaru biyu ko ba komai ya san dumin jikin uwar sa, ki ji tausayin halittar Allah baiwar Allah ki fada min gaskiya cewa wasa ki ke….. k ice min mata ta Asshe barci take yi a cikin allurar yanzunnan allurar za ta sake ta ta tashi mu tafi gida ta shayar da Dan ta”. Sai hawaye wasu na korar wasu suka biyo bayan maganganun da zaka tabbatar cikin fita hayyacin sa yake yin su.
Abinda Baba na ya fadawa Nos din da ta gaya masa rasuwar mahaifiyata kenan kafin hawaye su cigaba da tsinke masa, ya kuma kasa karbar jaririn da take ta faman bashi kamar ya ce mata "ki musanya min shi da mata ta Asshe. Zata iya kara haifa min wani, amma ita bazan kara samun kamar ta ba!!!"
Nos dai bata gane sambatun wannan mijin mai tsananin son matar sa me yake nufi ba, ta dai san zafin mutuwar matar sa ne ke bugun sa ya kuma fidda shi a hayyacin sa, sai hakuri
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 12