Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kada mukullan motar hannun ta, tayi shigar ta islamically kamar kullum ta hanyar yin rolling da bakin mayafi akan doguwar riga samfurin kasar Oman ruwan kwaiduwar kwai data ke sanye da ita. Tunda Hamzah ya gama shirin dana ke saurare, ba matsala zan iya raka ta. Don haka nace Aunty bani mintuna biyu in dan watsa ruwa, nima ina son fita in motsa jiki na, yau kwana goma kenan ban je koina ba". "Sai sauraren Hamzah Mawonmase!". Anty ta fada cikin kirjin ta har sautin maganar ta ya dan fito. Na juyo daga kofar toilet bayan na zari towel daga ma'ajiyar sa, nace "na'am Aunty magana kike yi ne?" Ta girgiza kai tace "Oh! Ban ce komai ba fa. Yi maza ina jiran ki a mota". A gurguje nayi wankan na fito wani wajen ma kumfa bata fita ba, a haka na saka jacket wadda ta kai min har kasan guiwa da wandon Jeans baki. Na saka hijab wanda iyakacin sa kafaduna, na dauki wayata da 'yar karamar jakata 'Chanel' na bi bayan Anti zuwa mota. ***** "NASARA ALKALI" (MY SECOND LIFESTYLE INFLUENCER) M una kan hanyar mu ta zuwa ‘Walmart Supermarket' dake kan titin Riggs Road, South Dakota, inda a can Anti Nasara ke yin duk wani provision din kayan abincin mu dana amfanin ta. Anti ta dube ni da wutsiyar idon ta. Kafin ta maida hankalin ta kacokam kan tukin data ke yi cikin gwaninta. Sannan ta kira sunana cikin siga mai nuna muhimmiyar magana take son yi da ni. "Sai yanzu na gane dalilin da yasa Abban ki ya zabi yayi fushi da ke har ya kore ki Siyama. Nima kuma ina gab da yi; fushi da kora". Na zaro ido ina kallon Anti cikin tsoro da razanar maganar ta. Me nake shirin ji haka ni Siyama! Aunty Nasara bata damu da reaction dina ba kan maganar ta, ta cigaba da cewa. "As long as mace zata bari wani namiji da ba mijin ta na aure ba ya shiga zuciyar ta, ya shiga cikin rayuwar ta yayi kane-kane irin haka ya hana ta cigaba, ya hanata wani tunani bayan nasa, ya shiga tsakanin ta da iyayen ta, ya yi galaba a kan karatun ta, ya dauki ragamar zuciyar ta daga kan turba sahihiya, wannan mace macen sunan ta sorry domin mara hankali ce, kuma wadda bazata iya fighting da emotions din ta ba. Maimakon hakan, it's the emotions that drives her, not her own humble self, su suke jan ragamar ta tare da wannan namijin. Musamman wanda bata cikin rayuwar sa, ba kuma son ta ya ce yake yi ba". Anti ta dakata ta yi kwana ta dauki titin Walmart Supermarket, ta bar kalamanta na ragargaza ni, sannan ba tare da ta damu dani ba ko halin da ta jefa ni ta cigaba da cewa, "Siyama kin dauki hanya ta ruguza rayuwar ki, kin bar emotions suna driving din ki. Kin bar ALLAH Siyama tunda kin bar koyarwar AL'QUR'ANI, bayan cewa sune kadai abinda idan ka rike komi na rayuwa zai zo maka da sauki". Jiki na bakidaya ya saki, gwuiwoyi na sun yi sanyi kalau. Buri na kawai Aunty Nasara ta dauki hanya dodar kai tsaye ta gayamin me nake yi har haka da har take tunanin na bar ALLAH na dau hanyar rusa rayuwa ta. "Amsa ga tambayar da kike yiwa zuciyar ki a yanzu Siyama, yaushe rabon ki da karanta littafin Allah, yaushe rabon ki da yin sallahr dare don gayawa Allah bukatun ki da rokon sa a kan ya sassauta zuciyar mahaifin ki? Siyama kin fadi WAEC kin fadi NECO amma ba abinda ya dame ki sabida kin saka soyayya a zuciyar ki, soyayyar da bata da madafa don kuwa Hamzah Almustapha na gidan Rediyon VOA; BA MUSULMI BANE CHRISTIAN NE (Ahlil Kitabi) dake bin Addinin CHRISTIANITY." Don haka in zaki shiga hankalin ki ki shiga, in zaki dawo hayyacin ki ki dawo. Ki kama Allah ki kama iyayen ki. Ki maida hankali wajen gyara kuskuren da kika yiwa mahaifin ki, ya fiye miki alfanu duniya da lahira akan bibiyar shirye-shiryen Hamzah dare da rana, ya fiye miki alkhairi ga cigaban rayuwar ki, ya fiye miki maslaha da Ubangijin ki. Yara mata irin ki sun fi goma dana samu labarin sun yi RIDDAH a kan soyayyar wannan mushrikin a Najeriya. Don baiwar iya magana da ta halitta Allah yayi masa karshe, amma arne ne Siyama, ba addinin ku daya ba, ko kusa bai cancanci soyayyar ki ba. Siyama Gembu, 'yar musulmai ce rainon musulunci. Umar Faruq shine mijin da ya dace da rayuwar ki kamar yadda Abban ki ya hango miki, abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala da gwauron dutse ba zai hango ba. Shiyasa aka ce ta yaro kyau take amma bata taba yin karko. Don haka Siyama a matsayi na na UWA ba MARIKIYA ba nake baki shawarar ki kama abinda zai amfane ki ki manta da Hamzah, ki manta da Mawonmase, har yanzu ke yarinya ce da take kan gabar gina rayuwar ta. Baki kai ga cimma komi a rayuwar ki ba. You are still a Teen. Na sama miki islamiyyah school a New York na gama komai zan kai ki gobe, a tsayin watanni shidda kacal ake haddar Al'qurani, ta wasu musulman Canada ce Dr. Ismail Memon da dan sa Dr. Shaykh Ibrahim Memon Madani, su suka bude ta a birnin Buffalo, New York. Kafin watanni shidda nake son ganin Hafizah Siyama a gabana, in ga sabuwar Siyama mai Qira'ar Madani, wadda iyayen ta zasu yi alfahari da samun ta, kasancewar ta mahaddaciyar Al'qur'ani. Idan kin kammala wannan makarantar zan maida ke aji shidda na sakandire da sunan transfer daga Regent, ki sake zana jarrabawar kammmala sakandire sannan ki fara karatun Jami'a. Wannan shine tsarin da na yi miki nake kuma fatan ki bani hadin kai a kan sa, ko in mayar da ke Mambillah!!!". ****** MURFIN LITTAFI NA DAYA Ban iya tsayawa kallon yanayin da Siyamar mu ta fada ba na ajiye Biron, ba don komai ba sai don nafi Siyama kidimewa. Abinda ban sani ba; Shin SIYAMA zata bi tsarin uwardakin ta Nasara don a zauna lafiya da ita? Ko kuwa a'ah itama zata bi sahun masu yin RIDDAH ne kamar sauran matan da aka yi ittifakin sun yi RIDDAH a kan sa??? Tunda dai mun ga har fiya-fiya ta sha don ta tsira da shi da fantasie din ta a kan sa??? Sanin hakikanin wannan amsar sai ita kadai ‘yar mutanen Mambillah; Aisha-Siyama Mamman Gembu. Don haka mu biyo Boddon mu-Siyamar mu a littafi na biyu don jin yadda zata wakana tsakanin ta da ‘Dream Man' din ta. Shin da gaske Hamzah kafirin ne ko kuwa shaci-fadi ne irin na Nasara don ta samu hanyar raba Siyama da emotions din ta??? SAKACIN WAYE? 2 TARE SUKE DA LITTAFI NA DAYA. TAKU HAR ABADA SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI). In kinji tashin hankali, razani da kidimewar da suka sameni a wannan dan tsakanin da nasara ta dauka tana magana to guda daya kenan. Na shiga abinda ake kira bewilderment8 na zuciya da ƙwaƙwalwa. Na shiga coma ba dan na kwanta a kwance ba, sai don kasancewar ilahirin gaban jikina sun daina aiki na kame a kujerar da nake zaune.wani bangare na zuciya kuma yana Mai gasgata kowacce kalma da kowanne harafi dake fita daga bakin anti na. Na yarda iyakar gaskiyar da kowacce uwa zata fadamin kenan, iyakar mataki da kowacce uwa ta gari zata dauka kenan don tseratar da 'yarta daga fadawa halaka, shi nasara ta dauka take Kuma aiwatarwa a halin ynz. Ban tashi tare da mahaifiyarta ba amma Sai Allah ya hada Ni da wasu irin matan uba na gari wadanda irin su sun yi ƙaranci a wannan zamanin da muke ciki, wadanda Kullum burin su shine su dora ni akan hanya kuma turba sahihiya idan na karkace, in kasance yarinya ta gari abin koyi, abin alfahari gare su da mahaifina..iyakacin rudani na shige shi a wannan ranar, rudanin daya kusa fiddani a hankalina. Ba musulmi bane a ina ya samo sunan sahabin manzan Allah kuma baffansa sayyidina Hamza (A.S)? Ina ya samo sunan shugaban halitta (Almustapha) a surname din sa??? Duka wannan ma idan an bi salsala ai basu da wani amfani a wuri na, ba kuma zasu amfane Ni da komai ba.Tunda kuwa hamza bai taba sanin da wanzuwata a duniya ba,Hamza bai ce yana son siyama ba, Hamza bai Sanni ba....A takaice Ni kadai nake kida na, nake kuma taka rawa ta iri - iri akan sa, cikin wata duniya ta fantasy and imagination wadda ban taba jin mai irin taba sai ni. Amma kuma ina tababa hadi da waswasi a cikin al'amarina da wannan bawan Allah, tabbas akwai wani BOYAYYEN SIRRI wanda Allah kadai ya san shi, ya kuma ke nufi a kaina dashi hamzan, in ba haka ba ta ina ya kutso ya shigo cikin mafarkaina, na rayu shekara kusan goma ina mafarkinsa, na kuma Ganshi exactly a talabijin yanda nake ganinsa a mafarki da imaginations dina??? "Ya Allah taimakeni kafin na haukace!" Na fada a fili, cikin kama kaina dake neman rabuwa gida biyu saboda sarawar da yake min, ina girgizawa da karfi ina qara girgizawa da karfi ko hakan zai rage nauyin daya yimin. Anty tace mata dayawa sun yi RIDDAH wato sun bar addinin musulunci akan hamza, wanda ke nufin ta san shi farin sani, ta kuma san duk abinda nake ciki Akan sa, domin har zana shi nayi da pencil na kafe a cikin Frame din gefen gado na, sannan cikin wayata da laptop dina duka hotunan Hamza mawonmase ne,wanda nake saukewa daga cikin hotunan sa na shafukan social media, ga kuma kona mata girki da nake tayi akai akai tun daga lokacin da young Abba ya mallaka min waya, sannan a fili nake kunna Muryar tasa sautin na tashi daga Radio na, ko talabijin din gidan dake falo, in kura masa ido kamar tsohuwar mayya data ga Nana ko kuwa kamar mai shirin hadiye shi don so. A zahiri duk wata uwa indai mai kula ce akan al'amarin 'ya'yanta to tabbas zata yi saurin gano inda na dosa akan HAMZA VOA, ba wai labaran nasu nake kallo ko nake saurare ba, tunda kuwa in bashi yake labarai ba ai bana ko tsayawa in kalla ko in saurara An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 12 of 12