Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 6
a tsakiyar falon Jiddah ce ta ce "Wallahi Yusra ki bani ni bana son haka" gwalo ta mata ta na cigaba da wulla taddy da ke hannuta ganin sun dage su na gudu akan taddy ya sa Ammi yin magana "Wai nikam dan Allah bazaku barni ba haba tun ɗazu kun sani gaba" gudunsu su ka cigaba dan su bama jin abunda ta ke faɗa su ke ba "Ai shikenan tunda na ce ku bari kunƙi bari na kira yayan ku na faɗa masa" da sauri su ka karaso gurinta suna rungumeta "Am sorry Ammi mun daina" A"u da kuna jina kenan shaƙi yanci ya sa kuka ƙi magana" Zuwa ta yi ta aje masa kan table ɗin har lokacin kuma idanunsa a rufe ya ke murmushi ta yi ganin kamar ya yi bacci ta sa ka hannuta ta na wulwulawa a wajan fuskarsa shiru ya yi kamar mai bacci, murmushi ta yi "Tunda dai ya yi bacci bari na tafi office ɗin Aunty Suhailat" gyaran murya ya yi, da sauri ta juyo ta na zare idanu Ina ma'abota son littfin a wani Company na ce shin kunsa dacewa littfi na na kuɗine shin me kuke jira saura ƙiris fa na gama free page har yanzu ba muyi komai ba cikin tafiyar littfin a wani Company ki hanzarta yin payment yar uwa saboda kar ayi wannan tafiyar babu ke kin san dai daɗi littafina da kuma ma'anarsa ba sai na faɗamiki ba shin kin shirya yin payment na littfina idan kin shirya 2318541707 Hauwau Umar Abdullahi UBA Bank Kowane mutum ance da ƙaddararsa Tabbas haka ya ke kamar yadda ƙaddara Ayrah ta fara da wani Company mai ɗauke da mabanbanta mutane masu halaye da ban da ban Ayrah ta haɗu da masoya wanda su ka nuna mata soyayya sai dai cash ashe wannan soyayyar zata zama matsala a cikin rayuwata Sister ki hanzarta kiyi payment ni na tabata bazaki Dana sani ba *Karku manta sunan littfin* *A WANI COMPANY* [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ A WANI COMPANY BY HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS Fallow my account Arewabook@hauwauomar Page_18_19 Da sauri ta ƙarasa shiga cikin ɗauki idanunta na zubda hawaye, jijigata tafara yi ta na kuka. Buɗe idanunta ta yi da ƙyar wanda su ka ma ta wani irin nauyi. kallonta Mama ta yi, menene ya faru da ke Mama? dan Allah ki tashi shine kawai abinda ta ke faɗa idanunta na tsiyaya da ruwa kama hannu ta yi tana matsewa a nata "Fatima" ta kirata cikin Normal sunanta "Ki yi haƙuri da rayuwa Fatima ki kula da rayuwarki ko ba na raye, kimin alƙawarin kare mutuncinki Fatima ina matukar ƙaunarki, ina jin kamar bazan tashi ba sai dai a kullum ina kuka rashin iyayena dan da na son in da su ke da komai zaizo mana da sauƙi ina matukar ƙaunarki Zarah" ta faɗa tana lumshe idanu "Mama dan Allah ki daina faɗar haka Insha Allah zaki tashi" murmushi kawai Mama ta yi da dugu ta shiga cikin ɗakin ta ɗako ledar magani ruwa ta ɗibo ta zo ta na bata gyaramata kwanciya ta yi bacci ne ya ɗauketa da sauri ta miƙe ta nufi bayi dan ɗauro alwala sallah t ayi raka'a biyu ɗa ga hannuta ta yi sama ta na kuka da roƙan Allah ya bawa Mamata lafiya Ta na idarwa ta kwanta a gefan Mama bacci ne ya dauke ta Washegari Alhmdllh Mama ta ɗan fara samun sauƙi Ayrah shara gidan ta yi tass kunu ta dama mu su bayan sun gama sha Mama ta kalleta "Ayrah ya kama ta ace kinje aiki" girgiza ma ta kai ta yi "Ki daure kije kinji insha Allah babu abunda zai faru da ni" babu yadda ta iya miƙewa ta yi ta nufi ciki ɗakin dan shiryawa ta na gamawa ta fito da hajjab har ƙasa murmushi Mama ta ma ta "Allah ya tsaremin ke a duk inda ki ke" "Ameen Mamana" ta faɗa ta na sumbatarta a kumatu tsaye ta ganshi a jikin motar da alama kuma dama ita ya ke jira tuntuni, tunda ta fito ya ke binta da kallo wani irin kallo ya kemata Wanda bai taɓa ma ta shiba dube-dube ta fara yi a jikinta dan ganin ko wani abune da sauri ya kawar da kansa ya na shiga cikin motar shiga itama tabyi yaja su ka tafi su na isa ya fito ya yi ciki ko left yau bai hauba ya nufi stap.. Shiga ya yi cikin office ɗin, dafe kansa ya yi ya na furza da wani wahalala numfashi shi kaɗai ya san abun da ke damunsa tabbas yau ce rana da ya kamata ya aiwatar da abunda zuciyarsa keson ya aiwatar ɗin. Da Salama ta shiga cikin office ɗin ɗaga kai ya yi ya kalle ta, nufar gurin haɗa Coffee ta yi da sauri ya dakatar da ita "Kije kawai bana bukata" ba ta damu ba ta nufi hanyar fita daga office ɗin ƙasa ta sauka wajan Aunty Suhailat ƙarasawa ta yi fuskarta ɗauke da murmushi "Ke Jiddah Jiddah ki tashi fa na ce" turo baki ta yi gaba tana jin haushin tashin da'a kamata wai Ammi sai ina bacci ki ta tashina" banza Ammi ta mata ta nufi kofa tai fucewarta a hankali ya ke sakowa daga bene Ammi ce ta tsaya ta na kallonsa murmushi ya yi lokacin da ya ƙaraso guri "Ammi kallon fa?" "Ai dole na kalle ka son yau na ga abun da ban taɓa gani ba, kai ne wai yau ka sa ka manya kaya? kuma ba karamin kyau su ka maka ba" dariya ya yi sosai wadda ta kara masa kyau Ammi dai kice sokike ki ce bana sa wa" "Da toh sawar ka ke ne" murmushi kawai ya yi "Anya babana ba wajan wa ta zaka ba?" haɗe rai ya yi kamar bai taɓa dariya ba dan in da abun da ya tsana a rayuwarsa toh bai wuce amasa maganar mata ba shi ya yi soyayya ma ya ce ya yi me shifa gaskiya har yau baiga wace ta isa ya sota ba, ganin ya haɗe rai kamar baya dariya ya sa Ammi cewa "Allah dai ya shiryaka Babana wai ni kam kai kullum idan aka maka zance budurwa sai ka sauya fuska shikenan sai kayi ta zama ba kai aure ba, kai kasani yanzu ka yi duba da Sa'a nin ka duk sunyi aure wasuma har ya'ya gare su" "Ammi su su kaga zasu iya wahala" ya faɗa ya na wucewa murmushi kawai Ammi ta yi tai gaba abunta dan yau ne Abieey zai dawo Nigeria Momy ce zaune a cikin bedroom ɗinta ta na waya sheƙewa ta yi da wata dariya "Ke dai bari kawai kawata ai komai na shirya shi yanda ya kamata yoh Allah na tuba taya zanyi sanya da wannan aiki idan kika ga ban aiwatar ba toh kice ni zainab an buneni ne a rami kinga a lokacin ai babu abunda zan iya" ta faɗa tana ƙara sakin shu'umin murmushi Yusra da ke tsaye a bakin ƙofar ɗakin duk taji abun da mahaifiyartata ta faɗa hawaye taji na zuba a fuskarta shin yaushe ne Momy za ta gane ta dai na irin wannan abubuwan? da sauri ta bar bakin ƙofar gudun karta fito ta ganta.. Cikin murna Fahad ya fito ya na murmushi ganin abokin na sa dan baitaɓa tunani da gaske zaizo gidan na saba kama hannusa ya yi su ka shiga cikin parlon zaunar da shi ya yi akan kujera ya nufi cikin bedroom ɗin ya na kiran Samha fitowa ta yi da fara'a "Badai har babban baƙon namu yazo ba?" "wallahi kin ga ko ya karaso' murmushi ta yi tana fita a ɗakin drinks ta ɗako da sincks ta nufi kan centar table ɗin ta ajiye ma sa "Ina yini brother" murmushi ya yi ya na kallonta "Lafiya qlau Samha ya gida" "Alhamdulillah yau dai Allah yayi munganka a gidan mu" "Ai kuwa dai" ya faɗa a taƙaice zuba ma sa juice ɗin ta yi ta na miƙe ma sa godiya ya ma ta ya na karɓa Suhailat ce ta dubeta "Kinga Ayrah bari naje office ɗin H.o.d na kaimasa wannan file kinji, yanzu zan dawo" "Toh aunty Suhailat sai kin dawo" fita ta yi ta barta a office ɗin haɗe hannuta biyu ta yi akan kuncita tun ɗazu babu abinda ta ke tunawa sai Mamata ko wane hali ta ke ciki yanzu lumshe idanunsa ya yi ya na jin wani irin ya na yi a jikinsa gaba daya jijiyoyin kansa sun tashi, p.a ce ta turo kofar tashigo sai da ta ambaci sunansa sau uku bai ɗago ya kalleta ba hakan ya sa ta ajiye file ɗin da ke hannuta ta yi ta fita ta na tunani ko menene ya faru da Mdee zama ta yi akan kujera da ta kasance mallakinta Shin kodai taje ta faɗawa Mdee tana son zuwa gida Saboda Mamata bata da lafiya? a'a gasky bazata iya ba tashi ta yi ta fita dan zuwa cikin lambu da ke Company, tana zuwa ta zauna kan fararen kujerin da ke gun lumshe idanunta ta yi ta na jin wani irin ya na yi shiba damuwa ba shi ba farin ciki ba "Ya Allah ka sa Mama ta na cikin ƙoshin lafiya" ta furta hawaye na bin gefan fuskarta "Ameen" taji an ambata a bayanta da sauri ta buɗe idanunta wanda su ke kawo ruwa Oga Abdul ta gani tsaye ya haɗe hannusa biyu akan ƙirji murmushi ya sakar Ma ta ya na zama akan kujera da ke gefanta fine girl ya faɗa ya na murmushi da shi kaɗai ya san ma'anarsa kawar da kanta ta yi da sauri kuma ta miƙe ta nufi hanya fizgota ya yi ta faɗa jikinsa, ƙoƙarin kwacewa ta ke amma ina gaba ɗaya ya ruke ta cizo ta gartsa masa da sauri ya saketa ya na dafe gun da gudu ta fita a wajan ta na haki dafe ƙirjinta ta yi ta na ambata sunan Allah Office ɗin Suhailat ta shiga ganin har lokacin bata dawo ba ya sa ta saki ajiyar zuciya mai ƙarfi zama tayi akan kujera shin wananan wane kalar bala'i ne Motoci ne yan uban su guda biyar ke shigowa cikin katafaran gidan da wani irin gudu Jiddah da ke tsaye a jikin window da gudu ta sako zuwa ƙasa a hankali ya sako ƙafarsa zuwa waje kyakyawan dattijo farine tass kana ganinsa zaka san cewa shine mahaifin Abrad saboda ya na yin Kamar su dai dai da kwayar idanunsu iri ɗaya ce rungumesa ta yi ta na murna "Oyoyo Abieeyna" "Oyoyo Mama" Abieey ya faɗa shima ya na rungumeta Yusra ce ta nufo gurin itama da buɗe hannusa ya yi ta faɗa jikinsa a hankali ya saki ajiyar zuciya ya na jin wani irin kewa da kaunar ya'ya na sa Momy ce ta fito ita da Suhaima itama rungumesa ta yi Murmushi Momy ta sa ki "urwelcome Sir" Murmushi ya ma ta ya na kallon Ammi da ke fitowa daga part ɗinta wani irin sanyi yaji na ratsasa lumshe idanunsa ya yi da sauri ta ƙaraso ta faɗa jikinsa, a tare kuma su ka saki ajiyar zuciya mai ƙarfi haushine ya ya turnike Momy da sauri ta wuce abunta, Bunta Suhaima ta yi ita ko Yusra taɓe baki tayi alamar ko a jikinta waige-waige Abieey ya fara yi tuntsirewa Jiddah ta yi da dariya dan ta san mai yake nema juyawa ya yi ya kalleta "Mamana lafiya daiko"? "Abieey na san fa wa ka ke nema toh sai dai kayi haƙuri dan ya Abrad dai bayanan tun ɗazu ya shirya ya tafi zance" ta faɗa ta na karayin dariyata mai kyau da sauri kuma ya juya ya kalli Ammi ya na son jin da gaske ne abunda Jiddah ta faɗa taɓe baki Ammi ta yi "Kadai san yarinya nan da shirma kawai dai bai san zaka dawo bane yau shiyasa ya fita kuma kaine kace kar'a sanar ma sa zaka masa bazata" baice komai ba ya kama hannuta su ka nufi ciki bunsu su Jiddah su ka yi a baya Yusra ce ta ce "Wai ke yarinya nan yaushe zakiyi hankali ki daina shirma?" turo baki ta yi gaba "Duk randa kika daina nima zan daina" Mtss Yusra taja tsaki dan gaba ɗaya Jiddah shirmanta ya ma ta yawa suna isa parlon ya haura sama dan hutawa bunsa Ammi ta yi "Nifa Ammi nasan yanzu kin daina kulamu saboda Abieey ya dawo ko" murmushi kawai ta yi tai gaba abunta dan ta san halin yaranan Suhailat ce ta shiga office ɗin ta zauna "Kin jini shiru ko siste" ɗaga ma ta kai ta yi alamar eh "Wallahi muntsaya wani aiki ne shiyasa ni kaina duk na gaji, ta so muje muyi sallah" babu musu ta miƙe tabi bayanta su na isa masjid ɗin su ka ɗaura alwala shiga su ka yi ciki, bayan sun idar Ayrah ɗa ga hannu tayi sama ta na rokan Allah akan ya bawa mahaifiyata lafiya ganin tana hawaye ta na addu'a ya suna fitowa Suhailat ta tambayeta lafiya ta ke kuka? rungumeta ta yi ta cigaba da kukan "Please Ayarh kiyi shiru ki faɗamin karki sani nima cikin damuwa" "Aunty Suhailat Mamana Mamana" "Menene ya faru da ita" "Bata da lafiya jiya da na je gida ko buɗe idanunta ba ta yi" "Ya salam shine kuma kikazo aiki yau Ayrah why' "Itace ta ce na zo yau saboda jikin na ta da sauƙi" "Okay toh kiyi shiru kinji kar mutane su ga kina kuka Insha Allah Allah zai bata lafiya" goge ma ta hawayen da ke fuskartata ta yi "Smile" ta faɗa duk dan ta sa ta cikin farin ciki murmushi ta yi _Yawwa Hajiyata ko ke fa kinga yadda ki ka yi kyau? da dariya nan kamar wa ta Ashwariya 😁" "Kai Aunty Suhailat ni ina na isa na zama Ashwariya" "Allah har kin fita Ayrah ki godewa Allah ke ɗin mai kyau ce" "Kinga zomu shiga ciki" binta ta yi su ka nufi ciki office ɗin Insha Allah anjima page 20 zai sauka wanda ya kasance page na karshe a free page shin me kike jira yar uwa har yanzu baki payment ba kin san dacewa yanzu nema wasan zai fara ohh ya rabbi Allah sarki Ayarh ko zataci jarabawoyin da suke bibiyarta sai dai muce Allah ya bata ikon cinsu Ayrah baiwar Allah *Littafi* *A wani Company* *₦300 babu tsada idan kinyi shirin biya* *9165855674 hauwau umar Abdullahi opay* *Zaki turo evidence ta wannan Number* *09165855674 * *Jinjinata agareku masoya na ina matukar ƙaunarku.❤️ Sosai kamar yadda kuke ƙaunata *MUCH LOVE LOVER'S* *_~MEEYRAT CE~✍️_* [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ *A WANI COMPANY 🏬* *HAUWA'U OMAR* Cute Meerat. *MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*. # SQUAD 2024. Page_20 *Last free page* Juyi yake cikin haɗɗaɗen office ɗin mai kamada fadar shugaban ƙasa idanunsa a rufe suke dan mutum na iya zaton cewa bacci yake a hankali ya furzar da nunfashi lokacin da yake buɗe idanun nasa wowwwww!! Masha Allah Mdee Suhail kenan cikakken matashi mai ji da kansa tattausan hannunsa ya sanya ya janyo telephone pole ɗin dake gefensa wasu ƴan nambobi ya danna sannan ya kai kunne cikin wata irin kasalalliyar murya mai nuna buƙatuwa akan wani abun ya furta "Ayrah!" Abinda ya iya furtawa kenan sannan ya ajiye wayar, P.A ɗin ta fahimci abinda yake nufi hakan yasa ta mike dan kiran wacce ya ambata ɗin. Wani irin kallo ta bisu dashi kamar na nuna ƙasƙanci sannan ta taɓe baki kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta ce" keee!... dukkanninsu suka fuskanceta dan basu san da wacce take a cikinsu ba, haushine ya turniƙeta hakan yasa cikin fushi ta ce"kee ba dake nake magana ba Ayrah?" kallonta Ayrah tayi da lulu eyes ɗinta bata ce komai ba dan yawan magana ba ɗabi'arta ba ce "Mdee na kiranki Malama" ta fice daga office ɗin a fusace. Numfasawa Ayrah tayi sannan ta miƙe jiki babu kwari tayi waje. Turo ƙofar ta yi a hankali ta shiga gaba ɗaya bata jin wani ƙwari a jikinta ganin idanusa a rufe ya sa ta karasa ta zauna akan kujera murmushi ya yi wanda shi kaɗai ya san ma'anarsa sai da ya kai kusan five minute a haka kafin ya buɗe idanunsa da su ka yi wani irin ja tsoro ne ya kama ganin yanayin idanunsa ya sauya launi, miƙewa ya yi bai ce ma ta komai ba ya nufi bakin ƙofar ganin yasawa ƙofar luck yasa tsoro ya kamata dan hakan bai taɓa faruwa ba juyowa ya yi ya na kallonta ya ɗau tsawan lokaci ya na tsaye kafin ya cije laɓansa wani irin abu ya ke ji wanda bazai iya misaltawa ba shifa yau yaci alwashin cimma burinsa kuma tabbas zai bi zaɓin zuciyarsa. "Sir!! Sir!!" Murmushi ya yi lokacin da yake sake tunkarota har sannan kuma bata fasa kiran sunansa ba idanunta sun kaɗa sunyi jaa zallar tashin hankali ya wanzu akan fuskarta inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun wace irin mummunar ƙaddara ce ke neman tarwatsa rayuwarta me yake shirin faruwa ne??, Jin da tayi ta gagara yin baya ya tabbatar mata da cewa tazo ƙarshen bangone yayinda Suhail ke gabanta so close wanda har suna iya jin numfashin juna. Zufar da tagama wanketa take ƙoƙarin gogewa amma abun ya faskara bakinta sai rawa yake da alama akwai abinda takeson furtawa amma harshenta yayi mata nauyi hannayen Mdee da taji yana yawo akan fuskarta shine abinda ya ƙara tayar da hankalinta me Mdee ke ƙoƙarin aikatawa ne?, Daman ƙaddarar data kawota Companyn kenan?, wane wanda zai ceceta cikin wannan mummunan lokaci ya Rabb Ayrah ta furta cikin ranta, iskar da yake hura mata ita ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data shiga ashe da gaske ba mafarki take ba! Da gaske *A WANI COMPANY* ne haka ta faru?, da gaske ita Ayrah ke cikin wannan mawuyacin halin?, Me zatayi wanda zata kuɓutar da kanta daga wannan masifar? Tamkar a mafarki haka zuciyarta ta ayyana mata wani abu wanda lokaci ɗaya ya yi tasiri cikin ranta har ta ɗauki hakan matsayin hanyar da zata kuɓutar da ita hakan yasa ta kalli gefenta hankali tashe glass cup ɗin da ke kan table ɗin ta janyo nufar wuyanta ya yi ya na shin-shina lumshe do yayi saboda wani ƙanshi turare da yaji wani zafin nama taji ya zo mata da sauri ta ɗaga kofi ta sauke ma sa aka da sauri ya ɗago ya na kallonta da runani idanunsa kafin ya yanke jiki ya faɗi agun dafe ƙirji ta yi tana zare idanu "Nashiga uku ni Ayrah me na aikata haka" da sauri kuma ta buɗe kofar ta fita da gudu ta wuce p.a ta sauka zuwa ƙasa ganin ta fito da gudu ya sa p.a ta shiga cikin office ɗin ihu ta saki ta na kuka "Nashiga uku ta kashe shi fita ta yi zuwa ƙasa ta na ƙwalawa security ku tareta karku bari ta fita ta kashe Mdee Inna lilahi" abun da ke fita a bakinta kenan lokacin kuma tuni Ayrah ta daɗe da fita gaba ɗaya daga Company dan gudu karma a ganta ta get ɗin baya tabi... Wani irin azababben gudu ya keyi dalilin kiran da aka yi masa tuƙin kawai yake amma a zahiri tunaninsa baya wajen sosai kwakwalwarsa ta shagaltu da tunanunnuka wanda suka yi masa ƙawanya cikin ransa,kyakkyawar bugawar da zuciyarsa ta yi ya sanya ya ja wani uban burki ji kake ƙiiiiiiiiiiiiii! a matuƙar tsorace da kuma tsananin tashin hankali yake kallon gabansa gabaɗaya tunaninsa ya tsaya cak meya aikata ne haka?, something fishy!. *_Kowacce ƙaddara tanada mafarinta kamar yanda ƙaddarar Ayrah ta kasance ƙarƙashin WANI COMPANY wanda yake da mabanbantan mutane masu mabanbantan halayya da kuma ɗabi'a Alhmdllh wannan page shine karshan free page hajiya ta ki zo ayi tafiyar da ke dan ni nasan bazaki dana sani karanta Novel ɗina ba... Shin ina Ayrah ta tafi? Mdee na raye ko ya mutu? dama Mdee ya na da wa ta manufa kenan akan Ayrah? Idan kinyi shirin biya. 9165855674 hauwau umar Abdullahi opay Sai ki turomin evidence ta wannan Number 09165855674 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6