murmushi ta yi "Daddy yaushe ka dawo?" murmushi shima ya mai da mata yanzu nan dawowa ta kenan daughter" "sannu da zuwa" "yawa daughter ina zaki yanzu" "zani ƙasa ne office ɗin su aunty Suhailat" "Masha Allah Allah ya taimaka" "ameen dad" "maza ki je kin ji" nufar hanya tayi shikuma ya shiga da Salam ya karasa shiga cikin office ɗin zaune ya taddasa ya na latsa lapton ɗin dake gabansa zama yayi akan kujera gaisawa su kayi da Suhail "dama ba komai ne yasa na ce idan ka dawo kazo ba sai chanjin wajan aiki da ka samu zuwa Austiralia" murmushi alh hadi yayi irin nasu na manya "amma ko wani abun ne ya faru"? "A'a babu abunda ya faru mun yi duba da yanda kake gudanar da aikinka tabbas kai ɗin mai amana ne, wannan dalilin yasa muka yanke hukunci haka" yalwatace murmushi ne ya subuce masa "ina matukar godiya da wannan shaidar da Kuka min da kuma ƙarin girma sai dai wani hanzari ba gudu ba shin idan na bar ƙasarnan wanene wanda zai dinga ɗako Ayrah?"
"Karka damu da wannan Insha Allah za'a san yadda za'a yi" godiya ya masa kafin ya miƙa zuwa waje dan lokaci tashi yayi har ya akai bakin ƙofar ya dakarmtar da shi "idan ka tashi tafiya karka damu da jiran Ayrah zan kai ta gida" godiya ya masa sosai sannan ya fita a office ɗin
Fitowa yayi zuwa ƙasa dai-dai office ɗin da Ayrah ta ke ya tsaya ya na nocking ta sowa tayi dan buɗe ƙofar ganin Mdee tsaye a jikin ƙofar ne ya bata mamaki murmushi ya sakar mata "muje ko" shine abunda ya ambata kallon Suhailat ta yi taga ta sakar mata murmushi fita tayi ta bisa abaya.
Dai-dai grand towers mall suka tsaya "muje ciki" gyaɗa masa kai tayi alamar a'a dan gaba ɗaya tsoro ya kamata "kina jin tsoron ne" ya faɗa dai-dai kunnanta ƙara gyaɗa masa kai tayi "a'a ni kawai kuje ku dawo inan" shima kwai-kwayar maganr tata yayi "a'a ni dai sai mun tafi tare" wata irin dariya ta tin tsire da ita dan ita abun ma dariya ya bata ganin yayi magana kamar wani yaro shima dariya ya ke yana kallonta. "Maza ki buɗe muje" buɗe murfin motar tayi tafita suna shiga kai tsaye ya nufi wajan wasu dogayan riguna yan uban su jida ya dunga yi kamar babu gobe wata Black ya hango cen nesa da shi sai walwali ta ke mai adon golden karasawa yayi ya ɗakota ya saka cikin basket ɗin ita dai Ayrah ta zama yar kallo dan babu abun da ta ke sai kallosa yana gama kwasar abayar ya nufi wajan Englishwest ya shiga jidar su suma yanda kasan zai haɗa lefa Ba karamin kaya Suhail ya jidaba har dangi su bra da pant sai da ya ɗibe su kafin ya nufi bangaran chocolate da beskit suma ya jida bayan ya biya kuɗi wanda a ƙala sun kai sama da 2m security gurin su ka ɗauka ledojin su ka samasa a mota a hankali ya ke takowa inda take dan ita dai ta zama mutum-mutumin tun lokacin da taga iyayen kuɗin da ya kashe hura mata isakar bakinsa yayi ya na kallonta murmushi kawai tayi ta nufi waje, shima binta ya yi a baya zuwa wajan motar, suna tafiya ta na kallonsa jin muryasa ta yi yana cewa "Shikuma kallon na menene" sadda kanta ƙasa ta yi don har ga Allah ba'tai zaton ma yana ganinta ba
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ
A WANI COMPANY
BY
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS
Fallow my account
Arewabooks@hauwauomar05
Page,07.
Suna isa ƙofar gidan na su da kansa ya buɗe murfin motar ya fito, drive ya sa ya ɗeba kayan zuwa soran gidan. "Amma sir naga ana shiga da kayan gidan mu aje maka zanyi ne?" murmushi ya yi ya na dubanta. "A'a ba jemin zaki yi ba mallakin kine, zaro idanu tayi waje tana kallonsa "To ni ina zan kai wainan kayan?" murmushi ya yi kawai ya shiga cikin motar su kayi gaba, tsayawa tayi ta na kallon motar har su ka ɓace mata cikin sanyi jiki ta shiga gidan tana kiran Mama Mama fitowa tayi da sauri dan gani menene ya faru Ayarh ke mata irin wannan kiran. "Lafiya Ayrah kike kira... Kasa karasa maganar tayi ganin uban ledojin a cikin soran, "Ina muka samu wainan ledojin kuma?" "Mama ki kama mu shiga ciki idan mun zauna zan miki bayani" babu musu Mama ta kama ledojin suka dinga shiga da su cikin gidan. zama ta yi akan kujera ta na sauke ajiyar zuciya, zu ba mata ido Mama tayi tana kallonta "Kefa na ke jira kimin bayani" bata labarin duk abun da ya faru ta yi, shiru Mama ta yi ta na mamakin wannan lamari kafin ta ɗago kai ta kalleta "Kina gani kuma ya miki hakan bada wata manufa ba?"
tasowa ta yi ta ƙaraso in da Mama ta ke ta kwanta akan cinyarta. "Mama ki tamin addu'a inaji ajikina babu wata matsala" "Allah ya sa" "ameen" ta ce ta na rufe idanunta saboda wani irin bacci da ya ke fuzgarta
Yau ta kama asabar kasan cewar babu aiki yau zaune ta ke cikin ɗakin hannuta ruƙe da beskit tanaci, Mama ce tashigo cikin ɗakin ta na kallonta "Hajiya shan zaƙi yau ansamu abunda ake so" sun kuyar da fuskarta ta yi ta na dariya "Ma za ki tashi muje gidan alh hadi, tin ɗazu ya aiko mu zo kina bacci" murmushi ta yi ta miƙa ta na gyara zaman riga dake jikinta hijjab ta saka na riga su ka fita suna tafe suna hira har suka isa gidan. a parlor su ka samu hajiya da sauri Ayrah ta ƙarasa wajan Hajiya sarai ta na murmushi ita ma murmushi tayi "A'a yau ma'aikata ne a gidan namu? sannu da zuwa lale marhabu da daughter" karasawa ta yi ta na rungumeta habib da shigowarsa kenan cikin parlor ya yi gyaran murya "Nifa na fahimci Momy kamar kinfi son Ayrah akaina Allah" ya faɗa ya na turo baki gaba kamar wani karamin yaro. tin tsirewa Ayrah ta yi da dariya ta na nunasa wollah ya habib da ka yi shagwaɓɓa ka yi kyau sosai" murmushi kawai ya yi, ya na karasa shiga cikin parlon
Gyaran murya alh hadi yayi ya fara basu labarin yadda sukayi da Suhail fashewa Ayrah ta yi da kuka "Yanzu Daddy idan ka tafi ni yaya zanyi kuma dawa zan dinga tafiya"?karki damu daughter Mdee ya ce za'a san yadda za'a yi insha Allah komai zaizo da sauƙi" Allah ya sa" anan alh hadi ke faɗa musu Insha Allah ranar Monday za su wuce Austiralia kuma shi da iyalinsa za su tafi, ba karamin damuwa su ka shigaba jin haka amma babu yadda za su iya "Shikenan alh Allah ya kaiku lafiya" Ameen ya ce ya na miƙewa dan yana son ya je wani waje Saboda shirin tafiyarsu
Suna isowa gidan kai tsaye Ayrah ta nufi ɗakin, ta na shiga ta kwanta gaba ɗaya sai tajima aikin ya fita kanta.
Zaune ya ke akan sujerun da ke garding ɗin hannusa ruƙe da cup ɗin juice ya na sha jin gidana ya yi da kujera ya na lumshe idanunsa ji ya ke ina ma yau ba ta zo a sturdy ba, gaba ɗaya zaman gidan ya ishe shi gashi babu wani wanda ya sani bare yaje in da yake. Ayrah shine abunda zuciyarsa ta faɗa masa tabbas gidan su Ayrah ya kamata ya je har ya miƙa kuma wani tunanin ya zo masa shin idan yaje gidansu ya ce mata me? kai ina bazaije ba gaskiya, gwara ya yi zamansa shi kaɗai. tashi ya yi ya nufi cikin gidan ya na shiga ya janyo lapton ɗinsa dan kiran Daddy ɗinsa.
Da fara'a dad ya ɗaga wayar murmushi ya yi ya na kallon mahaifinnasa "Allah dad ni na fara gaji da ƙasarnan, idan fa babu aiki sai dai na yi ta zama a gida kamar wani mara gata, ya faɗa cikin shagwaɓɓa" murmushi Daddy ya yi dan yasan rigima Suhail ce ta motsa "Ka yi shiru dad, yaji murya Suhail ta katse ma sa tunanin da ya tafi "Haƙuri zakayi son tinda kaga tunda ka dawo Nigeria ba'a kara samun wa ta ɓannaba, na san kana ƙokari kuma nima ina matukar kewarka. amma Insha Allah inan zanzo na kawo maka ziyara da zarar na gama da aikin dakenan" murmushi jindaɗi ya yi "Promise dad" "I promise you son"
cigaba sukai da wayar ta su cikin farin ciki da kaunar juna su na gama wayar ya kashe lapton ɗin ya na lumshe idanunsa tabbas ya na natukar son mahaifansa baya iya haɗasa da komai
Tashi ya yi ya nufi ciki dan ya samu yayi bacci.
Cire kayan da ke jikinta ta yi ta nufi bayin na su ta watsa ruwa ta na fitowa ta tsaya a gaban wadrop ɗin ta su ta na kare mata kallo tinani kayan da za ta saka ta ke, ganin har kusan takwas ta yi ba ta fito ba ya sa Mama ta tashi ta shiga ɗakin tsaye ta ganta a jikin wadrop ɗin ta zu ba mata idanu murmushi ta yi kawai ta karasa ta na taɓata, da sauri ta dawo da kallonta kan Mama "Ke kuma lafiya? ki ke ta kallon wadrop Kamar kinga sabon abu" turo baki ta yi kamar zatayi kuka kafin ta ce "Ni to ba rasa kayan da zansa na yi ba" "Tofa yau nabanu wai Ayrah yaushe zaki daina wannan halayyar taki? ace kullum mutum in ya yi wanka sai ya ta ruwan ido, kafin ya sa kaya" Mama ta faɗa ta na janyo wata marron ɗin abaya cikin abayoyin da Mdee ya siyamata "Ingo wananan ki sa ka" karɓa ta yi ta na murmushi zura riga ta yi a jikinta wow Masha Allah yanda kasan dan ita aka yi riga, ba karamin kyau ta mataba ƙarasawa wajan mero ta yi ta shafa tirare da leps glows a bakinta kama kanta ta yi dan ɗaurewa tin ta na yi ta na ganin za ta iya harta fashe da wani irin kuka mai cin rai. ƙarasowa Mama ta yi ta kama kan ta na ɗaure mata da wani white ribom mai kyau, hula riga ta sa ka white sai belt na riga shima white ta yi rolling dashi, takalmi ta zura plat. ba ƙaramin kyau Ayrah ta yi ba yadda kasan yar turai. fitowata yi ta na ɗagawa Mama hannu. Fita ta yi waje ta na tunani ta yadda zata tari abun hawa ya kaita Company. Turus taja ta tsaya ganin wata arniyar mota kirar pontic gto(1964). Tsayawa ta yi ta na kallon motar a hankali ya sauke glass ɗin ya na sakar mata murmushi, murmushi itama ta yi ta na nufar wajan motar. Da sauri drive ya buɗe mata tashiga, godiya ta masa ta zauna "Good Morning sir" "Morning" "how are you today" "fine" ta bashi amsa a taƙaice
Su na isa cikin Company ta buɗe murfin, "Ba kiji ba"ya faɗa a hankali juyowa ta yi ta na kallonsa, ganin idansa har yanzu a lunshe kamar bashi yayi magana ba "Kinyi Kyau sosai" "Thank you very much" ta faɗa ta na fita a motar shima fitar ya yi ya nufi hanyar da za ta sadashi da left, sai murmushi ya ke shi kaɗai kamar wanda akaiwa bushara 😂
Ya na shiga ya nufi office ɗinsa da fara p.a ta gaidasa ko kallon inda ta ke baiba bare ta sa ran zai amsa mata. Jiki a sanyaye ta karasa kan kujerata ta zauna hawaye ne ya fara zarya akan kuncinta. Turo kofar ta yi ta shiga bakinta ɗauke da salama da sauri ta goge hawayenta ta na gallawa Ayrah harara, sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tai gaba abunta ta na shiga ta nufi wajan haɗa coffee dan ta san zai bukacesa zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda ta ke komai cikin nutsuwa samun kansa yayi da sakin wani murmushi wanda shi kansa bai son manufar yinsa ba
"Sir" "Sir" gaba ɗaya ya faɗa duniyar tunanin baima san ta na masa magana ba sai da ta bibuga table ɗin sannan ya dawo hayyacinsa karɓa ya yi ya na kaiwa baki ƙara lumshe idanunsa ya yi ya na kai kofin bakinsa sai da yasha sosai kafin ya ɗago ya kalleta. "Yau baki tawo da abinci Mama ba?" gyaɗa ma sa kai ta yi alamar eh "Dama ina son na maka godiya da kayanan nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, Mama ma ta ce na maka godiya" "Babu komai na yi dan Allah so dan haka ni aganina ba abun godiya bane." "Sannan daga yau duk abunda da na baki ba na son godiya kinji" ya faɗa ya na kafeta da idanunsa ma su matukar kwarjini saurin sunkuyar da kanta ƙasa ta yi dan bazata iya jurar kallonsa ba.
Da salama ta shiga ciki office ɗin wanda baida wani girma samunsa ta yi zaune ya haɗa hannusa biyu akan fuskarsa da alama wani abun yake tunani. Murmushi ta yi ta na karasawa ciki, hura masa iskar da ke bakinta ta yi "Lafiya kai kuma ka ke ta fama tunani?" murmushi kawai ya yi ya na cije leɓansa na ƙasa "Hmm wallahi har yau na kasa mantawa da abunda Mdee ya min akan yarinyar nan" "Kaima kenan daba wani abu ya maka ba" "Ni tozartani ya yi agabanta😥 "Ni da na ke matsayin p.a ɗinsa amma ko ta ni bayayi, sai wata ƙaramar yarinya" tsaki ta yi mai sauti dan a duk lokacin da ta tuna wa ta irin wutar tsanar Ayrah ke karuwa tabbas ta yi alƙawarin sai ta wahala da yarinya wahala wadda ko aljan sai yaji tausayinta bare mutum. "Wai me ki ke tunani ne? ina miki magana kin min banza kin san fa ba na ɗaukar wulakanci ko" Abdul ya faɗa a hasale "Kaifa daɗina da kai rashin haƙuri ina tunani yadda zan wahala da yarinya ne, da yadda zan rama abunda tamin" wa ta irin dariya ya sheƙe da ita ya na kallonta "Ina jinki me kike tunani kenan?" murmushi ta yi ta na gyra zamanta akan kujera. Matsawa ta yi dab da shi ta raɗa masa wani abu akune wata irin dariya su ka sheƙe da ita su duka, su na tafawa "Sai yanzu na kara yadda da ke wace" "Kai dai kawai ka kasance cikin shiri dan a koda yaushe zakajini na nemaka" "Angama shugaabar mugaye duniya" wata dariya ta karayi ta na fita a office ɗin
rungumeta Hajiya ta yi su na kuka "Idan Ayrah ta dawo kice ma ta mun tafi" gyaɗa kai Mama Ayrah ta yi har sun shiga mota Habib ya fito "Aunty idan Ayrah ta dawo kice zan yi kewarta sosai, ki gayama zanzo na ɗauketa mu koma Australia tare" murmushi Mama ta yi ta na goge hawayen da ke fuskanta..
A hankali ya tashi ya nufi cikin ɗakin da ke office ɗin sai da ya kusa shiga kafin ya tsaya ya na duban Ayrah "Kije office ɗin su Suhailat, kuma bayan nan ban yarda kije ko ina ba" gyaɗa ma sa kai ta yi alamar toh fita ta yi da ga office ɗin kanta a sunkuye ganin p.a ba ta office ɗinta ya sa ta sa ki wa ta irin ajiyar zuciya mai ƙarfi, dan gaba ɗaya ba ta son ganin Suhailat
Da murmushi Suhailat ta tare ta "Yau sai yanzu ake ganinki" zama ta yi ta na gaidata amsawa ta yi cikin sakin fuska "Ina kika shiga yau?" "Babu ko'ina ina office ɗin Mdee" "Okay" Suhailat ta ce ta na chanza hira "ki na son wani abu ne?" "A'a Aunty Suhailat na ƙoshi" to ai ba cewa na yi nima baki ƙoshi ba, ina nufin kamar beskit chocolate da dai sauransu" murmushi Ayrah ta yi jin an ambato kayan kwaɗayi
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ
# SQUAD 2024
A WANI COMPANY
BY
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS
Fallow my account
Arewabook@hauwauomar05
Page_ 8_9
Ana tashi ta fito harabar Companyn don tafiya gida,ko office ɗin Mdee ba ta koma ba. fitowa wajan get ɗin tayi sai da tayi kusan 5minth bata samu abun hawa ba, hakan ya sa tashiga takawa da ƙafa ta na tafiya dafe kanta tayi saboda wata rana da ake gashi ko rabi bata yi ba, jin horn a bayanta ya sa ta yi saurin juyawa zuge glass ɗin motar ya yi ya na mata wani irin kallo, sunkuyar da kanta tayi ƙasa da sauri ta na wasa da yatsun hannunta
Nuna mata motar yayi alamar ta shiga, babu musu ta shiga kuma har lokacin kanta na ƙasa suna isa ƙofar gidan na su ta buɗe ta fita ko magana bai mata ba yaja motarsa yayi gaba jiki a sanyaye tashiga cikin gidan na su ganin bataga Mama a tsakar gida ba yasa tayi cikin ɗakin, samunta ta yi zaune ta na karatu al'Qur'ani mai girma zama tayi ta na murmushi.
Yana shiga gida faɗawa yayi saman kushin ɗin gaba ɗaya yau ya gaji lumshe idanunsa yayi ya na sauke numfashi tinani rayuwarsa ta baya da ta yanzu ce ta shiga dawo masa hawaye ne ya fara zarya akan kuncinsa tabbas bashi da wani gata sai na mahaifinsa mahaifiyarsa ta tafi ta barsa tin baisan ma menene duniyar ba haka ta watsar da shi ta tafi kawai dan basu da kuɗi alokacin. Allah kenan mai azurta bawansa a sanda ya so mahaifiyarsa taci amanar Daddysa taje ta auri abokinsa kawai dan shi baida kuɗi alokacin bata damu da rayuwar da zasu shiga ba haka ta barsu kuma har yau bata wai wayesu ba tuna irin waɗannan abubuwan ya sa ya kara fashewa da kuka mai cin rai idanunsa sun yi wani irin ja abun ka da fari nan da nan fuskarsa tayi ja a hankali ya kwanta ya na wani irin numfashi aduk sanda Suhail ya tuna waɗannan abun tofa yana shiga cikin wani irin hali ne . Tun yana numfashi a hankali har ya nemin fun ƙarfinsa miƙewa yayi ya shiga bathroom ya sakarwa kansa ruwa mai sanyi yana fitowa ya goge jikinsa da towel ne ɗaure a jikinsa ya kwanta yana rufe idanu kuma har lokacin hawaye bai daina zuba akan fuskarsa ba
Wanene Suhail?
Suhail Arif shine ai nayin sunansa asalin mahaifansa bature ne haka ma mahaifiyarsa
Austiralia. Calvary public hospital
Ihu ne ke tashi a dai-dai room 003 dake cikin hospital ɗin a hankali kuma ihu ya fara disha shewa kyakyawa mutune tsaye a bakin ƙofar idanunsa a rufe da alama yana cikin yanayi na damuwa jin kuka jariri da yayi ya sa yayi saurin shiga cikin ɗaki kwance take akan gadon na marasa lafiya daga ganin yanayi yadda take bacci zaka tabbatar da cewa a wahalce take da sauri ya karasa ya ɗauki jaririn dake gun yana rungumesa tsam a jikinsa kamar wani zai rabasa da shi sun kai tsawan muntina 20 a haka kafin ya ɗago ya kalli matar da ke kan gadon wani uban harara ta watsa masa tana jan tsaki nufar idan da take yayi da sauri ta dakatar da shi da hannunta "karka sake ka kusanci inda nake Arif saboda baka da wani amfani a gare ni cikin dake jikina ne na haife maka kuma na barmaka shi har abada bana fata ka faɗa masa yana da wata uwa wadda tai kaman ceceniya da ni talaka kawai wllh nayi nadamar auran matsiyaci kamar ka kuma ina so kasani aurena da Mahabub babu fashi" ta faɗa tana tashi daga kan bed ɗin ko damuwa da ciwon da jikinta ke mata bata yiba ta nufi hanyar fita da sauri ya karasa gabanta ya na haɗa hannuwansa biyu alamar taji tausayin su ratsesa tayi ta fita tana jan tsaki durkushewa yayi ya na fashewa da wani irin kuka mai cin rai tabbas Mahabub ya cuceshi ya ci amanarsa yanzu da gaske dama Sarah zata iya barinsa saboda kuɗi shin me yasa bata ji tausayin ɗan da yazo duniya ba yau duk wannan maganganu shi kaɗai ya ke yinsu kamar wanda aka tsikara ya miƙe ya ɗauki jaririn nufar hanya futa yayi daga hospital ɗin gaba ɗaya
Haka rayuwa ta ciga da tafiya Suhail ya taso wajan mahaifinsa kullum shi yake kaisa makaranta ya ɗaukosa bayaso ko wani ƙwarzane ya taɓa masa ɗa watarana ya dawo daga school ya nufi parlon su jun haya niya yasa yayi saurin tsayawa ya na saurare "Arif kenan ban fa na zo ne dan na tambayi ya kake ko ya ɗanka ya ke ba a'a nazo ne dan naji ance kayi kuɗi shine nazo dan kabani nawa kasan tunda dai dani akasha wahala" da wani kallon ya watsamata "Tabbas baki da imani Sarah baki ko tambaye ni ya ɗan ki ba sai Maganar dukiya abar banza wannan damuwarka ce ni koma ya yake bai dameni ba to bazan bayar ba Sarah ina lokacin da bani da kuɗin gudu na ki kai kuma ki maza ki fita a gidanan kafin nasa security su fitarmin dake" ganin da gaske ya ke babu wasa yasa tayi ƙwafa tana fita a ɗakin Suhail da idanunsa ke zubar da hawaye ya tsaya yana kallonta tsaki taja tayi gaba abunta da gudu ya shiga cikin parlon yana faɗawa jikin dad ɗinsa numfashinsa ne ya fara sarƙewa da gudu dad ya ɗauke sa zuwa hospital ɗin dake cikin gidan tun daga wannan lokaci Suhail ke fama da ciwo a zuciyarsa har izuwa wannan lokaci.
Wannan kenan.
Sai kusan la'asar ya tashi a bacci miƙewa yayi yana ambaton sunan Allah, bathroom ya shiga ya ɗauro alwala ya gabatar da Sallah.
Mama ce ta dubeta tana murmushi "yau kin daɗe Ayrah lafiya?" murmushi tayi tana bata labarin abun da ya faru "ke yanzu taya zaki iya zuwa gida dama a ƙafa karki kuskura ki ƙara wannan ganganci" "tom Mama insha Allah". "Kin san kuwa su Habib sun tafi yau ya ce na ce miki zai yi missing ɗin ki sosai kuma wai yanan zaizo ya ɗaukeki ku koma cen tare" murmushi "Allah sarki ya Habib nima zanyi Miss ɗinsa sosai Mama".
Washegari da wuri ta fita dan karta ɓata masa lokacin tana fita kuwa ta gansa cikin mota ganin kamar babu drive yau ya sa abun ya bata mamaki buɗe baya tayi zata shiga jin muryasa tayi yana magana "kenan niɗin drivern kine da zaki wani shiga baya?" fasa shiga bayan tayi ta buɗe gaban ta shiga.
"Dole ne kayi taka tsantsan saboda kar Mdee ya gani ta camera" murmushi yayi "haba wai bana ce miki na kashe camera office ɗinsa ba" murmushi kawai tayi suka cigaba da zuba abun ya a hankali ya buɗe office ɗinsa ya shiga itama shiga tayi ta nufi kujera ta zauna "kawomin coffee" miƙewa tayi dan kawo masa jin ta kasa tashi akan kujera sai ƙokarin tashi take amma abu ya gagara ganin tana ta ko kawa ya sa ya ce "me yake faruwa?" ɗago idanunta tayi wanda ya fara zubda ruwa "na kasa tashi" "what kin kasa tashi kamar ya ba yanzu kika zauna ba?" "Allah da gaske nake" ta faɗa hawaye ne ke ambaliya a fusakarta ganin tana kuka yasa ya miƙe dan ganin meke faruwa saka hannunsa yayi ya janyota amma ya ga ko motsi bata yiba durkusawa yayi dai-dai kujera yana dubawa murmushi kawai yayi ya nufi cikin wata drowa hannusa ruƙe da wata roba ya dawo ganin ya na zuba mata ruwa a jiki yasa ta fashe da