ruƙe ya ke cikin na haka suka jera suna tafiya gwanin ban sha'awa suna isa bakin motar aka buɗe musu suka shiga kai tsaye kata faran gida dake maitama hills estate ya salam gidane iya gida girman gidan ya zarce misali gaba ɗaya gidan zagaye yake da security ta ko ina mai gadi ne ya buɗe get ɗin da jerewa motocin suka yi zuwa cikin gidan tun kafin su gama parking ta fito da gudu ta na ihu duk da tsakanin cikin gidan da pearking lot da nisa amma hakan bai sata ta howa da gudu ba ta na murna "Oyoyo Ammina Oyoyo ya Abrad" shine kawai abun da take furtawa ta na gudu murmushi yayi kawai ya kalli Ammi itama kallon na sa tayi da sauri ta faɗa jikin Ammin ta na murmushi cen kuma hawaye ya fara zuba akan fuskarta "Ammi shine kuka tafi kuka barni ni kaɗai ko?" "ohh Jiddah toh yanzu kuma menene abun kuka ai gashi mun dawo ko?" gyaɗa kai tayi ta na kallon Abrad jan hanci ta yayi ya na cewa "rigimama Ammi" murmushi tayi ta na turo baki "nifa fushi na ke da kai" "kaina bisa wuya na idan kikai fushi da ni ina zan kama" ya faɗa ya na yin gaba abunsa dan shi bai cika yawan magana ba wananan ɗin ma yayi ta ne kawai wani haɗaɗan falo ya shiga mai tsanani kyau irin falon nane da ko gidan shugaban ƙasa ba a samunsa a hankali ya zauna a kan kujera da ke gun ya na lumshe idanunsa wani irin sanyi ne ke ratsa masa zuci yau dai gashi ya dawo Nigeria duk da badan Ammai taje ta tawo dashi bana babu abun da zai dawo da shi
Ammi kama hannu Jiddah tayi suka shiga na su apartment ɗin sai surutu ta ke kamar redio dan Jiddah badai magana ba
Ayrah fitowa tayi cikin ƙanan kaya masu kyau da shaƙi kallonta Mama tayi tai murmushi "kin yi kyau sosai" murmushi tayi ta na zama akan tabarma "wallahi Mama na ƙagu gobe tayi naje aiki saboda za'a bani salary na" murmushi Mama tayi "waya ga su Ayrah da salary" wata dariya tayi mai cike da nuna zallar farin ciki ta
Tashi yayi ya haura sama ohh ya rabbi ashe ba komai na gani a ƙasa ba dankareren falone shima na alfarama bedroom ya shiga dan watsa ruwa
Ɗaure ya fito cikin white towel iya gwiwa hannusa na ruƙe da karami wanda ya ke tsane kansa da shi
Wani irin taunar cingom take mai bada sauti kallon wata ƙarama yarinya tayi wadda baza ta fi Sa'ar Jiddah ba "kinji na gaya miki wallahi kika sa ke kikaje wajan mutsiya tan cen ranki sai ya bacci sakara kawai" "rabi da ita Momy ita yarinya wallahi na fahimci tafi son Ammi" "eh ɗin nafi sonsu kuma ni wallahi duk abinda zakuce sai dai muce haka kuri ni dai wallahi Momy akullum ba zan daina faɗaminki kiji tsoran Allah ba kuma kisan zaki mutu" da sauri Momy ta bige mata baki "zaki rufemin baki ko kuwa sakarar yarinya sai anyi magana ki farawa mutane wa'azi angaya miki mu bamu san abunda ya dace ba ne?" tashi tayi ta haura sama tana ƙunƙuni
"Na fahimci yarinya nan sai na shiga dukanta zata dawo hankalin ta" "kema ce Momy tutuni nagaya miki ki kaita wajan durfus kawai ya rufe miki bakinta wallahi idan ba haka ba duk wani shirinki sai ta tarwatsa sa yanzu gashi su ya Abrad sun dawo Nigeria kuma da kince ance miki ba zai taɓa dawowa ba" shiru Momy tayi ba tace komai ba dan itama al'amarin duk ya ɗaure mata kai
Niko nace Allah kenan babu wani wanda ya isa yayi abunda Allah bai ba hajiyata[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ
A WANI COMPANY
BY.
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT.
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS
Fallow my account.
Arewabook@hauwauomar
Page_16_17
Be ce mata komai ba ya buɗe idanunsa "Kin ɗauka na yi bacci ko shiyasa zaki gudu" girgiza kai ta yi alamar a'a "Jeki toh idan an kusa tashi sai ki dawo" "Okay sir" ta faɗa ta na fita dan zuwa office ɗin Suhailat
Ana tashi ta fito dan nufar office ɗin Mdee a hankali ta tura ƙofar tashiga ganin baya cik i ya sa ta zauna ta na jiransa. Fitowa ya yi cikin wasu fararan cuz masu kyau, tsayawa ta yi tana kallonsa ganin da marron ɗin cuz ce a jikinsa yanzu kuma ya canza kenan da wasu kayan ya ke zuwa Company? ta faɗa ta na cigaba da kallonsa zuwa ya yi dab da ita ya sunkuya "Madam shi kuma kallon fa na menene?" murmushi ta yi tana saurin kawar da kanta "Tashi muje ko?" babu musu ta miƙe tabi bayansa, suna fita su ka shiga cikin motar kai tsaye ya gida su ka nufa. Suna isa ta fita dan shiga gida "Baki jiba" juyowa ta yi danjin mai zaice "Ki gaidamin da Mama" "Toh insha Allah zan faɗamata"
Tsaye ya ke ajikin window apartment ɗinsa, sanye ya ke cikin treecotar black da white riga mai kyau haɗe gashinsa ya yi ya ɗaure guri guda idanunsa a lumshe ya ke wani irin jindaɗi yanayi ya ke garin lileɓe ya ke da hadari mai tafiya da iska mai sanya nishaɗi da gudu ta shigo cikin bedroom ɗin ta na kwala masa kira dafe kansa ya yi wanda ya ji ya sara masa "Ohh ya rabbi wai Jiddah yaushe zakiyi hankaline?" turo baki ta yi Kamar zata yi kuka "Toh ni ba Ammi ce ta biyo ni zata dakeni ba dan na ɗauka mata waya shine na zo gurinka, ka hanata dukana amma ka ke min faɗa ko ya Abrad" ta faɗa hawaye na zuba akan fuskarta "Dan Allah kiyiwa Allah kimin shiru Jiddah" banza ta ma sa ta cigaba da kukan ta tsawa ya daka mata, da sauri ta fita a ɗakin ta na kuka
Ammi da ke nemanta ganin tana kuka ya sa ta tambayarta lafiya? karasawa ta yi ta rungumeta "Wai ke lafiyarki ne kike min kuka?" "Ba ya Abrad bane ba ya yi min faɗa" "Da ya miki faɗa ke me kika masa"? "Ni Ammi babu abun da namasa ki tambayesa"
"Naji maza ki wuce ciki kiyi shiri islamiyya" babu mu su ta nufi bedroom ɗinta dan shiryawa ajere su ka fito ita da Yusra drive ne ya ƙaraso yana buɗe musu motar, shiga su ka yi hannusu ruƙe dana juna. Suna isa Jiddah ta dubi Yusra ta na dariya hararata ta yi "Mie kikewa dariya ke kuma?" "Babu komai kawai ina tuno darun da zakuyi keda ya Ustaz ne" "Toh ina ruwanki nifa Allah bana son gulma" gwalo ta ma ta ta na fita a motar da gudu, bunta ta yi itama da gudu su ka shiga gudu a makaranta Ustaz ne ya ƙaraso gurin ya na mu su magana tsayawa sukayi su na suraransa "Wai ku kullum sai kun shigo kuna gudu haba ya kamata ace kunsa kun girma fa" Jiddah ce ta turo baki "Ni dai Allah ya Ustaz ku daina cewa mun girma nawa mu ke ne nida Sis za'a na cewa mun girma" dariya ya yi kawai yai gaba abunsa dan yasan idan ya biyesuu sai sun bashi ciwon kai.
Ayrah na shiga gida ta sa ki ajiyar zuciya ta rasa mai yasa a yanzu idan ta na tare da Mdee ta ke rasa nutsuwarta ganin sai murmushi ta ke kamar wata zautaciya ya sa Mama da ta ƙaraso gun ta dafata firgigit ta dawo hayyacinta "Ke kuma lafiya kike murmushi?" "Babu komai ni kawai ji nayi ina cikin nishaɗi" "Toh Allah ya kyauta" "ameen" ta ce ta na nufar cikin ɗakin na su kwanciya ta yi saman tabarma ta na kallon silin ɗakin da ya sha wuya ya ke bukatar taimako. Abincin Mama ta ajiye mata "Ki tashi kici abunci kinji" miƙewa ta yi ta na janyo yar karama samira shinkafa ce da wake da mai sai salat da aka yanka, ba Ayrah ba ko ni sai da na yi sha'awar cinta😁 bismillah ta yi ta fara ci dama wata irin yunwa ta ke ji lumshe idanunta ta yi "Wollah Mama wannan abunci na ki ya yi daɗi sosai" murmushi Mama tayi "Kodai na sa miki waigi ne" dariya ta yi ta na cigaba da cin abunci
Su na tashi su ka fito dan tafiya ruwa ne ya fara zuba da sauri Jiddah ta karasa ta shiga motar jan luck ɗin ta yi ta rufe, Yusra da karasowarta kenan ta yi ta yi ta buɗe ta kasa drive ta ce ya buɗe ma ta wani kallo Jiddah ta watsa ma sa "Wallahi idan ka buɗe ma ta ko hmm" shiru ya yi ba ce komai ba "Wai sani me keke nufi ne ba cewa na yi ka buɗemin ba" dariya Jiddah ta yi ganin ruwa na ta dukanta, ganin jikinta ya fara rawa ya sa ta buɗe ma ta, da sauri ta shiga ta na ƙanƙame jikinta ko buntakan Jiddah ba ta yiba sani ne yaja motar su ka tafi. Suna isa gida da sauri Yusra ta fita ta yi apartment ɗinsu ta na shiga ta ga Momy zaune ita da Suhaima da gudu ta yi sama ta na isa ta cire kayan da ke jikinta ta sauya wasu faɗawa kan makeken gadon ta yi ta na sauke numfashi
Washegari da wuri ta fita zaune ta samesa ya na danna waya zama ta yi kan kujera ta na gaidasa amsawa ya yi cikin sakin fuska suna isa suka fito a jare zuwa cikin Company tun da su ka jero p.a ke kallonsu ita ma zuwan ta kenan ta na pearking mota ta ga fitowarsu, ji ta yi hawaye ya gangaro ma ta Allah ya sa ni ta na son Suhail shiyasa bama ta so wani ya raɓesa shin ta ya zata raba Ayrah da Suhail? shine tambayar da taiwa kanta
Ƙwafa ta yi ganin ta rasa mafita ta fito itama dan shiga ciki .Coffee ta aje masa akan table ɗin mug ɗin ya ɗauka ya na kaiwa baki, miƙewa ta yi dan barin office ɗin "Ina zaki" ya tambaye ta "Am dama zanje wajan Aunty Suhailat ne" "Shine kuma ba ki tambayeni ba" girgiza mai kai ta yi da sauri alamar a'a "Shikenan ki je amma karki daɗe dan anjima akwai inda zamu" "Thank you sir" ta faɗa tana murmushi
Da sauri ta ke sauka daga kan stap ɗin ta na sauka ta ga p.a da Oga Abdul tsaye da'alama wani abun su ke wani kallo ya watsa ma ta ya na tsaki da sauri ta ratsa ta gefe ta yi wucewarta "Munafuka ce yarinya nan wallahi" p.a ta faɗa cikin hasala tana isa ta sameta zaune ta na dube dube a laptop.
Zama tayi a kusa da ita murmushi Suhailat ta yi "Jiya ina ki ka shiga ban ganki ba" "Da wuri mu ka tafine shiyasa" "Ohk wai ni kam na tambaye ki man" "Eh ina jinki" "Kina zuwa sloon kuwa?" girgiza ma ta kai ta yi alamar a'a "Gaskiya toh ya kamata yau na kai ki saloon naga idan angyara miki gashi ya zaiyi" murmushi ta yi kawai mikewa ta yi tana kama hannuta "Zo muje kinga mu tambayi Mdee ko zai bari" tashi ta yi tabita su ka fita, su na isa Suhail ya ɗago ya na kallonsu "Sir dan Allah idan ba damuwa zamu fita da Ayrah" wani irin kallo ya ma ta da sauri ta sunkuyar da kanta "Idan kunfita kuje ina" taji ya ambata "Saloon" ta bashi amsa shiru ya yi na wani lokaci kafin ya ce "Shikenan muje na kaiku murmushi jindaɗi su ka yi su na kallon juna
Baya suka buɗe za su shiga su duka "Ni ɗin drive ku ne da zaku shiga baya" "Sorry sir" "Ayrah ki shiga gaban kinji" "A'a Aunty Suhailat ke ki shiga" wani kallota ma ta wanda ya sa ta saurin buɗe gaban ta shiga, murmushi gefan baki ya yi dan dama hakan ya ke da buƙata beauty saloon su ka isa da ke garin abuja babban gurine na musamman wanda ya kayatu, akwai wajan saloon da lalle, wajan make up duk agun, fitowa su ka yi su ka nufi wajan saloon ɗin zama ya yi a gurin su kuma su ka karasa cikin wani glass "Madam gulo ce ta fito ta na tambayarsa abun da ya ke so nuna ma ta su Ayrah ya yi dake zaune cikin glass "Ki tambayesu" ya faɗa ya na ɗora kansa a jikin kujera lumshe idanunsa ya yi wani irin bacci ke fusgarsa
Suhailat ce ta basu umarnin su yiwa Ayrah saloon mai kyau sannan ida sun gama su ma ta kalba kanana zaro idanu ta yi ta na turo baki "Allah ni Aunty Suhailat kar'amin kitso kedai kam anyi raguwa wallahi" "Dan Allah Aunty Suhailat" ta faɗa cikin shagwaɓɓa "Allah fa ke daina marairaice wa dan sai an miki" shiru ta yi kawai ɗago idanunsa ya yi dai-dai lokacin da ake warware mata kai masha Allah ya ambata cikin cool voice ɗinsa, cikin muntina da ba su wuce 30 ba aka gama mata komai bakaramin kyau kalba ta ma ta ba zubawa kan nata idanu ya yi tabbas yarinya Allah ya yi mata baiwa kala- kala "Sir" da sauri ya kalleta ya na mamakin yaushe ta iso nan? mikewa ya yi su ka nufi ƙofar fita su na shiga kai tsaye su ka sauke Suhailat a gida kallon Ayrah ya yi "Kin yi kyau sosai da wannan kitso" murmushi ta yi tana mamakin yaushe yaga kitson na ta "Kina mamakin yadda nagani ko?" ɗaga ma sa kai ta yi dan har ga Allah ta yi mamaki
Buɗe murfin ta yi ta shiga ɗa ga ma ta hannu ya yi ya na murmushi, ta na shiga gida ta ga babu kowa a tsakar gida karasawa cikin ta yi Inna lilahi wainna ilayi rajiƙun
Mai ta ke gani haka
Ina ma'abota sun littfin a wani Company na ce ko kinsan har yanzu ba'a fara wasan ba ko kinsa cewa yanzu ne ƙadarorin Ayrah za su fara ohh ya rabbi ki hanzarta biya danjin yadda zata kaya
Idan kinyi shirin biya
9165855674
Hauwau Umar Abdullahi opay.
Ki turomin evidence ta wannan Number
09165855674
Karki bari a baki labari yar uwata.. littfina ₦300 ne babu tsada
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ
A WANI COMPANY
BY
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS
fallow my account
Arewabook@hauwauomar05
Mikiya writer's Allah ya cigaba da haɗa kanmu sharin mutum da Aljan Allah ka tsaremu tabbas farin jini jama'a Allah ne ya bamu kuma muna alfahari da haka domin mu masoyan mu akullum sune mu mune su masoyan mu abun alfaharin mu.
Page_14_15
"Good morning Ammi good morning ya Abrad" "Morning dear" Ammi ta faɗa. Ta na gamawa ta miƙe da sauri tana sumbatar Ammi fita tayi waje, samun Yusra ta yi tsaye ta na jiranta hararata ta yi "Wai ke kullum sai mutum ya ta jiranki?" "Sorry sisna ta faɗa ta na kama hannuta, drive na isa ta fito da sauri ko jiran Yusra batai ba.
Tana gama shiryawa tafita. A ƙofar gidan ta ga motar Mdee da sauri ta buɗe ta shiga murmushi yayi yana kallonta suna isa ya fito zuwa cikin Company
A hankali yake ziro santala-santalan ƙafa funsa daga kan makeken bed ɗin sanye ya ke cikin fararan sleep dress white masu matukar kyau da shaƙi badroom ya nufa dan watsa ruwa.
Yana fitowa ya nufi wajan mero tabbas Abrad kyakyawa ne farine tass ƙwayar idanunsa blue sai bakinsa da ya kasance ƙarami pink color girarsa ta haɗe da sajen fuskarsa, yana da fafaɗan ƙirji jikinsa a murɗe Kamar mai gym lotion ya ɗako masu kyau da ƙanshi shi kansa salon shafa man abun kallone a wajan Abrad. Ya na gamawa ya taje kansa White ribom ya ɗako ya haɗe kansa dashi
Yana gama shiryawa ya fito kai tsaye part ɗin Ammi ya isa tana ganinsa ta saki murmushi da sauri ya ƙarasa ya na kwanciya akan cinyarta wata irin nutsuwa yaji
tana ratsasa shafa kansa Ammi tayi "Son ya kamata kaje wajan Momy ku ka gaidata" shuru yayi kamar bai jiba "Da kaifa na ke" "Please Ammi nifa bason shiga sabgar matarcen nake ba" "Naji ni dai nace kaje idan kuma bazaka jeba kai kasani ta faɗa tana turesa" "Sorry Ammina Insha Allah idan na fita zanje" murmushi tayi "Yawwa ko kaifa"
Company
Tura ƙofar office ɗin ta yi ta shiga ɗa ga idanu ya yi ya kalleta zama ta yi ta na gaidasa bai amsaba ya ciga da abun da yake. Kirane ya shigo cikin wayarsa ganin ya na murmushi ya sa da sauri kuma ya miƙe ya na yin gaba kobin takan Ayrah baiba ya kara gaba abunsa kai tsaye ya nufi airport da gudu ya karasa alokacin da jirgin ke sauka farin dattijo ne ke sakowa daga matata kalar jirgin da gudu ya nufi gun ya rungumesa "Oyoyo dad" murmushi dad yayi ya na shafa kansa kama hannunsa yayi suka nufi wajan motar, kai tsaye gida suka wuce dad zama yayi akan kujera Suhail yayi murmushi "Amma wallahi dad kamin bazata" "Ai dama na gaya maka ba zata zan maka" hira suka shiga yi "Dad amma dai nasan akwai abun da ya kawoka ko?" "Nazo ne kawai na ga ka my son Sannan akwai maganar da zamu yi da wani ne anan so ya ce min shima zai dawo daga uk yau shiyasa na zaɓi nazo nan saboda na ganka kuma naga yadda kake gudana da aiki a Company" tunawa ya yi da Ayrah da ya bari a office, da sauri ya miƙe yayi hanyar waje "Ina zaka kuma son?" "Ina zuwa dad company zani akwai abunda na manata acen ɗin" "Okay sai ka dawo" dad ya faɗa yana miƙewa dan haurawa sama
Buɗe ƙofar part ɗin ya yi, ya shiga zaune ta ke ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya sai taunar cingom ta ke baƙace mai jiki ta na da katon baki amma saboda gyara da kuma wadata ya sa idan kaganta ba zaka gane hakan ba gefanta kuma wata yarinya ce wace aƙalla bata fi shekaru 22years a duniya treecotar ne ja a jikinta sai white riga mai adon ja yar karama hula ce akanta ba laifi yarinya ta na da kyau sai dai ita chocolate color ce. Zama ya yi akan kujera "Momy barka da safiya ya ku ke ya gida" ya faɗa duk lokacin ɗaya wani banza kallo ta masa kafin ta ce "Lafiya qlau ta na yatsina fuska, wani kallo ya watsawa suhaima da sauri ta duru kasa "Yaya barka da safiya" banza ya yi bai bata amsa ba Yusra ce ta shigo cikin falon da gudu sancewar dawowar su kenan daga makaranta ta na ganin Abrad ta karasa da sauri ta faɗa jikinsa ta na dariya shima dariya yayi "I miss you ya Abrad" "Miss you too baby ya school ɗin?" "Alhmdllh" "Masha Allah har yanzu baki daina wannan guje gujen ba ko hmm naga Ranar da zaku girma ya ranan" dariya ta yi ta na miƙewa da nufin haurawa sama tashi ya yi shima ya fice abinsa ko magana bai karawa Momy ba ya na fita taja tsaki da sauri suhaima ta miƙe ta zauna kan kujera "Wallahi Momy bakiji yadda najiba da naga ya Abrad ohh" ta faɗa ta na sauke numfashi "Ke dallah rufemin baki sha-sha-sha kawai duk ba tsoransa da kuke jibane ya kawo haka wallahi na tsani yaranan ita kuma Wannan shegiyar yar kullum ina nuna mata abunda ya dace bata ganewa" ita dai Suhaima shiru ta yi dan ta fahimci Momy ta ɗau zafi da yawa
Ya na isa Company da sauri ya fito ya na shiga left, Zaune ya sameta akan kujera murmushi ya yi kawai "Ta so mutafi" babu musu ta miƙe tabisa, suna fita cikin mota ya shiga shiga ta yi itama yaja motar su ka tafi. Ya na sauke ta a gida ko magana bai mata ba yaja motarsa dan babban burinsa ya isa wajan dad ɗinsa tabbas ya san yau zai kwana cikin farin ciki gashi ga mahaifinsa
"Ammi" "Ammi" shine abunda Jiddah ke faɗa ta na futowa daga bedroom "Menene haka Jiddah kike min irin wannan kira? wai ni yaushe zaki girma ne?' "Turo baki ta yi toh ni ba Abbey ne ya ce ya kira wayarki baki ɗaga ba shine ya ce na kawomiki" "Amma Jiddah fisabililahi sai ki dunga min irin wannan kiran" miƙa mata wayar ta yi ki sauri ki gama wayar Ammi ni game na ke" banza Ammi tai mata ta na ɗaga wayar sai da su ka daɗe su na waya kafin ta miƙa ma ta lokacin Jiddah ta cika fam kamar ta yi kuka, miƙewa ta yi za ta haura sama Yusra ce ta shigo cikin parlon da salama sanye ta ke cikin riga har ƙasa mai matukar kyau ba laifi Yusra kyakayawa ce sosai fara tass dan suna matuƙar kama da Jiddah gashinta ta zubo har baya, karsowa ta yi ta na faɗawa jikin Ammi "Oyoyo daughterna" "I Miss you Ammina na yi kewarki sosai" "Nima haka daughter na yi kewarki" tsaki Jiddah ta yi tai wuce warta kyale-kyalewa da dariya Yusra ta yi "Uwar kishi kawai wai Ammi ita Jiddah sai dai kita kulata ni banda ni" ta faɗa kamar zatayi kuka "Rabuda ita daughter ai bata isa ta raba ya da uwa ba"
"Kinga ta so ni kiraka ni" tashi Suhaima ta yi su ka fita "Amma Momy drive zaki sa ya kimu ne?"
"A'a wane irin drive dama kinga ina irin wannan tafiyar da drive ne" girgiza kai ta yi buɗe motar ta yi su ka shiga cikin sauri taja motar wani irin gudu ta ke akan titin tun su na cikin gari har su ka bar gari gaba ɗaya.
"Ayrah" "Ayrah" ki tashi fa karki makara yau wane irin bacci ki ke haka sai tashinki na ke kinƙi tashi?" buɗe idanunta ta yi wanda har yanzu su ke ɗauke da bacci "Wallahi Mama yau wani irin bacci na ke ji" "Toh ya zakiyi ki tashi kar mutum yazo ya yi ta jiranki" miƙewa ta yi dan watsa ruwa. Ta na fitowa ta shirya miƙe ma ta kunu da ƙosan da ke gun Mama ta yi atsai tsaye ta ci ta fita dan tafiya ta na fita taga drive zaune acikin motar ƙara sawa ta yi ta shiga ta na gaidasa su na isa ta sauka ta yi ciki. Zaune ta samasa ya na duba wani File ƙarasawa ta yi ciki ta zauna "Good Morning sir" "Morning" tashi ta yi dan haɗamasa coffee "Ayrah" taji ya ambaci sunanta dawowa ta yi ta zauna dan tasan tunda ya kirata akwai wani abun ɗagowa ya yi ya kalleta harya buɗe baki zaiyi magana sai kuma ya cije laɓe ya na murmushi "Kawai jeki haɗomin coffee ɗin" miƙewa ta yi ta na tafiya cikin tafiyarta mai kyau da burgewa lumshe idanunsa ya yi ya na kallonta bazaka taɓa cewa ita ya ke kallo ba
"My man kude ba'a ganinku sai shekara shekara" murmushi Abrad ya yi ya na kallon abokin nasa "Ina ta magana kamin shiru kaifa daɗina da kai mutum ya yi ta ma ka magana ka na jinsa" kwanciya ya yi ajikin kujera ya lumshe idanunsa ko kaɗan Abrad bai da yawan magana idan kagan shi ya na magana toh da Ammin sa ne ko kuma Jiddah da Yusra ya na matukar ji da su. Sai kuma dad ɗinsa wanda ya kasance sanyi idanunsa
Gudu su ke kawai