falo,
da kyar yana faman huci.
"Humaida! Humaida!!"
Ya dinga kiran sunanta cikin daga
murya.
Ta bude ido ta mike zaune tana
hamma tare da mika.
"Me ye ka ke tashina haka?"
Ta fada a kufule.
"Humaida, ki ji tsoron Allah,
wannan wace irin rayuwa ce ki ke son tsiro
da ita? Irin wannan rayuwar ko a tatsuniya
119
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
ban taba ji ko ganin an yi irinsa ba, ta ya
ya za ki ce wannan murdaden gardin ya
shiga dakin bacci ya gyara miki?"
Ta yi murmushi cikin kada kai.
"Wallahi har ka sanya gabana
faduwa haba mijina kwantar da
hankalinza babu komai a ciki, an kawo shi
ne saboda irin haka...
A zafafe ya katse ta.
"Ke! Rufe min baki, wallahi ba zai
yiwu ba".
Ya maida kallonsa ga John.
"Daga yau na kara zuwa na ganka a
dakinta sai na mika ka ga 'yan sanda".
Ya yi tsaki ya hankada shi, ya shige
dakinsa.
Da gudu Humaida ta rufa masa baya.
Ta zauna a gefensa idanunta cikin nasa.
"Na fi son kullum in ga murmushi a
kan fuskarka, na fi son na ga kana
walwala".
120
リ
KA AURE NI=2
Ya buga mata harare.
BILKISU H. MUHD
"Irin wannan rayuwar da ki ka tsiro
ban taba ji ko ganin inda a ke yi ba, ki
gaya mini ya sunan wannan auren namu?
Humaida kin sake, kin sauya, ina tartama
wannan ba Humaidata ba ce. A yau na yi
tir da auren wannan Humaidar".
Ta yi matukar sanyaya murya.
"Irin wannan rayuwar duk wani dan
Adam ke fatan cimmawa. Na taso a
gidanmu ban san don me ya sa ka kasa
fahintata ba. Haba mijina ka zauna za yi
nazari".
Ya mike a fusace.
"Nazarin me ki ke so na yi? Babu
wani abin da zan yi in ba ki gyara ba,
komai zai iya faruwa tsakaninmu".
Ya ja dogon tsaki ya yi waje yana
faman mita. Binsa ta yi da kallo kawai
cikin tabe baki.
"Lallai akwai rigima a gaba".
121
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ta ga alama Mu'allim namijin
duniya ne, sam ba shi da alamar risinawa a
gare ta a matsayinta na 'yar gata yana son
tun ba a je ko ina ba ya nemi dora mata
hawan jini.
*** *** ***
"Ango ka sha kamshi”.
Kirarin da Yusuf ya dinga yi masa ke
nan, ya ci gaba da fadin.
"Ai ni ban sa rai da ganinka nan
zuwa wata daya ba, anya ka kyauta wa
amarya kuwa?"
"Haba, zaman gida sai mata".
Mu'allim ya fada.
"Ban da abinka abokina, ai kai kuma
ana nema maka hutu kana nuna kai dan
wahala ne, ai Alaji kawai ka nade a dafa a
kawo maka ka ci ka tada kai, ka tsoma
biyar ka cire goma".
122
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Murmushi kurum Mu'allim ya yi,
ringin din wayarsa ne ya katse Yusuf.
Lambar Dad ya gani, wato surukinsa. Ya
kara a kunne bayan ya danna malatsin
amsa kira. Muruar surukin nasa ta ratsa
dodon kunnensa, da sauri ya dan risina
kamar yana gabansa.
"Barka da yamma”.
"Barka ka dai Mu'allim, ya
Humaida?"
Ya ce, "Tana nan kalau”.
"Da kyau, am Mu'allim ya kamata
gobe a fito ofis".
Iya abin da ya fada ke nan ya kashe
wayar.
"Yusuf ni zan wuce".
Da sauri Yusuf ya sha gabansa.
"Haba Alaji ai ba ka isa ba, ka
mance yanzu ka girma hakan ni ma a dan
jika ni".
123
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ya dube shi shekeke da wani uban
takaici.
"Me ka ke so na yi maka?"
Ya tambaya a kufule.
"Ina nufin ni ma ka dan dandala
min... O.k bari na yi maka gwari-gwari,
wallahi garin ne ya yi zafi".
Ya rasa wacce irin amsa zai bai wa
Yusuf, domin shi kansa rabonsa da ya ga
naira dari a hannunsa tun kafin a daura
aure.
masa.
"Yusuf ban fito da komai ba".
Ya sa hannu cikin aljihu yana nuna
"Ka yi hakuri”.
Haka suka rabu Yusuf na faman
mita. Kai tsaye ya nufi gidansa.
John ya gani zaune da rimot a hannu
yana kallon talabijin.
A fusace ya karaso inda John ke
zaune, murya a kausashe ya ce.
124
KA AURE NI=2
ko?"
BILKISU H.MUHD
"Ba ka ji kashedin da na yi maka ba
Yà kai hannu ya damko shi tare da
mikar da shi tsaye, ya kai hannu ya tsinke
shi da mari ya kuma tankada shi. Ya yi
taga-taga zai fadi, ya yi saurin dafa bango.
"Wa ke wa mutane ihu haka?"
Humaida da ke kokarin fitowa daga
kicin ta tambaya.
"Don Allah ka saurara masa, kana
son takura wa mutumin nan me ya za ba za
ka yi harkarka shi ma ya yi nasa ba?"
Bai saurare ta ba idanunsa sun yi
jajir, jikinsa har tsuma ya ke, yana huci.
"Ka fita na ce". Ya ce wa John cikin
daga murya da nuna masa kofa.
Ita ma ta bude murya bakidaya.
"Koma ka ci gaba da kallonka, babu
inda zai fita ka ga Malam wai me ka ke
nufi ne? Ni yanzu John ya fi ka amfani a
gurina, domin zai gyara kuma ya dafa in
125
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
ci, kai ko Dad shi ne kadai na ke wa
amfani in kuma ka musa ka banar da
amfanin me ka ke yi min, wallahi ka yi
magana ka yi shiru babu ke nan ko to
tunda babu ka bar mini mai aiki ya sake".
Zuciyarsa ta dinga tunzurashi a
kanta, ya kai hannu kamar zai mare ta, ya
fasa ya maida hannun yana maimaita.
“Innalillahi'.
A zuciyarsa, ya juya a fusace ya bar
gidan, ita ma ta shige nata dakin shi ko
John ya hau doguwar kujera ya mike
abinsa.
A can harabar gidan ya zauna rike da
kai komai ya kunce masa, son Humaida ya
zame masa illa, da zai iya da tun yanzu ya
tsinke igiyoyin aurenta. Yanzu kam yadda
ya ke ji ba zai iya rayuwa babu ita ba, ko
da a ce babu daula zai iya jure duk wani
tijararta.
126
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Wai ashe haka so ya ke da zafi?
Sonta ya sanya ba zai iya zartar da kowane
irin hukunci ba. Ya dinga kada kai.
"Humaida kin yaudare ni, kin
shammace ni".
Bai koma ciki ba sai daya tabbata ta
yi baci.
Lokacin da ya doshi gidan gabansa
ya ji ya tsananta bugawa, ya yi sallama
cikin rashin kuzari.
Kawu ne mutum na farko da yake
burin son dora idanu a kansa. Umma na
zaune a tsakar gida, tankaden gari ta ke.
Da sauri ta dube shi tana kokarin ajiye
rariyar, ta mike tsaye tana yi masa wani
irin kallo.
"Me ya kawo ka gidan nan? Ka fita
ba mu bukatar ganinka, mun dade da bar
wa duniya kai".
Ya rude ya dube ta.
127
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Umma kuka ki ke yi? Don Allah ki
daina, zan fita amma kafin nan ki saurare
ni don Allah".
Da sauri ta daga hannu ta nuno shi.
"Dakata! Kada ka soki zuciyata sau
biyu, ya zama dole idanun iyaye su zubda
kwalla don sun zama cikin bakin ciki
saboda cutarwar 'ya'yansu".
Gabadaya jikinsa ya gama yin sanyi,
ya yi tattaki zuwa gabanta ya durkusa ya yi
bala'in kaskantar da kaicikin sanyayyar
murya.
"Umma ina son ki sani Allah ya tsara
Humaida matata ce in ba haka ba ban taa
ketare abin da Abba ya tsara mini ba. Ke
ce shaida, ke ce ya kamata ki fara
fahintata, ban yi niyyar na
ketaremaganarsa ba, don Allah ki fahintar
da shi ke ce kawai za ki fahintar da shi ku
yafe min".
128
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ta juya masa baya ta sarke
hannayenta a bayanta ta yi dan tattaki ta
sassauta murya.
"Babana mahaifiyata kalmomin da
suka fi dadin fadi aMebe, babu wani
matashin kai komai taushinsa da ya kai
tausayin uwa balle lallashin uba, hakika su
kan rasa bacci don kai ka yi, sukan koka
don kai ka dara".
Ta juya gabadaya tana fuskantarsa,
ta yi matukar kaurara murya.
"Yau na tsane ka na tsani ka kira ni
da wannan sunan Umma ko mahaifiya,
saboda ba ka amfana mana komai ba
lokacin da muke neman ka janye wata
bukata taka ka juya mana baya".
Kukan da ya ci karfinta ya sa ta dan
dakata da maganar.
Maganganunta sun gama rikita shi,
ya girgiza matuka, zai yi magana ta katse
shi da fadin.
129
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Biyayya ga iyaye fitila ce da ke
haskaka hanya zuwa aljanna, rana ce da ke
haska farin ciki a zukatan iyaye, kuma
biyayya ga iyaye na debe maka kewa
yayin da ka tsufa".
Ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa
cikin cizon lebe, ta sake numfasawa.
"Duk ka rasa wadannan, ka rasa
Mu'allim, ka shiga uku! Tun tasowa ta ban
ga dan da ya sanya mahaifansa zubda
kwalla ba sai kai, dan da mu ke tutiyar
mun ba shi tarbiyya, tir! Ka kuma tashi ka
fice kada Malam ya dawo ya riske ka a
gidan nan, ka fice na се".
Ta sake fada cikin daga murya,
yadda ya ga tsanarsa a kwayar idonsa ya
tabbata in kukan jini zai yi ba za ta saurare
shi ba, tilas ya bar gidan.
130
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ta maida kai gurin duba agogon da
ke manne a jikin bangon sitroom, karfe
tara na dare, ta koma zanceń zuci.
"Shin ina Mu'allim ya shiga, ba dai
tun fushin jiya ba ne? Kai karfin sona ba
zai bar shi ya yi fushi ba".
Ta nufi daya sitroom din, John ta
gani ya mike a kan kujera yana kallo.
"Sannunka madam za ka fita ne?"
John ya ce da ita. Ji ta yi kamar ya
tunzurata, ta hau yayyafa masa ruwan
bala'i ta inda ta shiga ba ta nan ta ke fita
ba. Ya zuba mata ido kurum yana kallon
ikon Allah. Karshe ya ga abin ba na kare
ba ne ya mike.
"Madam please, ka yi hakuri..."
Ta watsa masa wata uwar harara.
"Ka yi mini shiru ka kuma fice min
daga gida ba na son ganinka yanzu”.
Sum-sum ya yi waje.
131
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
Ta dauki waya a kan talabijin ta
shiga laluben Dad dinta.
"Dad, Mu'allim shiru har yanzu bai
dawo ba".
"Shi ne duk ki ka tada hankali haka?
Yana tare da ni, aiki ne ya sha masa kai,
kuma zai ci gaba da dawowa a irin wannan
ララ okacin.
Ta shagwabe murya kamar za ta yi
kuka.
"Haba Dad, ya za ka ce haka? Shi ke
nan ba shi da lokacina sai dai na zauna ni
kadai? Haba! Gaskiya ni ban yarda ba,
wannan ai shiga hanci da kudundune ne, ni
da mijina a raba ni da shi?"
Dad ya yi murmushi irin mai cin rai,
ya koma yа се.
"Ina kayan kallo, ina jaridu, ina
kuma John duk ba su ishe ki hira ba?"
Ta yi saurin cewa.
"Dad me ka ke so ka ce mini?"
132
KA AURE NI=2
Ya daka mata tsawa.
BILKISU H.MUHD
"Ki yi mini shiru, kina tunanin zan
dauki diyata na ba shi ya ci bulis? Ko
kadan ba na tunanin yin haka".
Ya ja tsaki ya katse kiran a zuciye.
Ta cillar da wayar ta dora hannu a ka
ta kwalla kara ta koma ta zube a kan
kujera tsawon lokaci ta kasa motsawa.
Motsin tahowa ta ji, ta yi saurin
mikewa ta nufo bakin kofa. Mu'allim ta
gani, ta yi saurin shan gabansa.
"Ina ka shiga, me ya hana ka
dawowa da wuri?"
Bai bi ta kanta ba ya wuce abinsa ya
zauna a kan kujera, ta tsaya kawai tana
dubansa, komai na Mu'allim mai kyau ne,
duk sai kallonsa ya gama kashe mata jiki,
ji ta ke kamar ta je ta fada jikinsa, sai dai
tana tsoron aikata haka, zai sa ya rainata, ta
matse lokaci daya ta daure fuska ta nemi
133
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
daya daga cikin kujerun ta zauna ta yi
bala'in basar da shi.
Ya mike ya nufi firij ya dauko tuwa
ya koma ya zauna, ya tsiyaya a kofi ya sha
ya koma ya kwantar da kai a jikin hannun
kujera, sam ba shi da niyyar kulata saboda
abin duniya ya sha masa kai, ya rasa komai
na farin cikinsa.
Tilas ta karya billenta cikin shan
Kamshi ta ce.
"Mu'allim magana fa na ke maka, ka
bude baki ka ba ni amsa.
Ya ja tsaki ya mike tamkar bai san
da zamanta ba, bedroom dinsa ya shiga.
Da gudu ta mike ta rufa masa baya. A
tsakar dakin tsaye suke carko-carko.
"Mu'allim kana son maida ni 'yar
iska a gidan nan, kana neman ka raina min
hankali, kana neman wuce makadi da
rawa, saboda tsabar rainin hankali ina yi
maka magana kana wani tafiya? To ka sani
134
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
ko Dad na ke wa magana ba ya yi mini irin abin da ka ke yi min! Yau ka 6ata min rai".
Takaici da bakin ciki gami da dariyaа gabadaya suka dinga cinsa, a fusace ya ce.
"Ki je ki tambayi mahaifinki!"
Ya yi saurin barin dakin.
Yana zaune a kan mota yana faman
lallatsa waya, wasu muryoyi ya ji a kusa da inda ya ke. Jin ana fadin sunansa ne ya sa
shi maida hankali ga abin da suke fada.
Samari ne su biyu ba su wuce sa'anninsa ba, daya yа сe.
"Me' ya sa ba za mu latsa Mu'allim
ba, na san ba zai hana mu ba”.
Dayan ya ce, "Kai don Allah rabu da shi, ba ya mikawa sai yawan gaisuwa".
Dayan ya sake cewa, "Kada mu yi
saurin yanke hukunci sanin da na yi masa
mutum ne mai son yin alheri".
135
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Whm da ke nan, lokacin da bai san
dadin kudi ba, amma yanzu ya dandana ya
san zakinsu".
"Me ya sa ka ce haka?" Dayan ya
sake tambaya.
"Kai kanka ka dube shi ka gani, da
da yanzu daya ne? Wanne ya fi kyan gani?
Dubi fa yadda ya fige ya lalace lokacin da
yana talaucinsa bai yi irin wannan ramar
ba"..
Ya sato kallon gurin da Mu'allim ya
ke, da sauri Mu'allim ya basar, ya maida
kai ga abokin nasa.
"Tabbas na yarda da kai, to amma
abin da ban mamaki”.
"Ba abin mamaki ba ne, yawanci
dogon buri ne wanda har abada ya ke hana
su gode wa Allah a kan abin da ya ke
samu, idan kuma ya fara samu za ka same
shi mai kyamar jama'a, kuma shi kansa
mawahalci ne ba ya iya daukar wani abu
136
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
daga cikinta don ya wadatar da kansa da
iyalinsa, wai duk don gudun kada dukiyar
nan ta kare".
"Na yarda da kai, tabbas Mu'allim
ya sauya a da mutum ne shi mai yawan
fara'a, ga son jama'a yanzu kam kullum in
ka ganshi za ka ga fuskar nan a daure tamau".
Daya matashin ya dora da fadin.
"Wannan shi ne dalilin da ya sa a ke
samun wadansu attajiran suna fama da
yunwa abin da ya fi muni duka shi ne idan
ka ki yin amfani da dukiyar nan ta hanyoyi
masu kyau yana yiwuwa bayan ka mutu a
batar da ita wajen aikin banza, babu
shakka kuwa komai ka bari gobe kiyama
za a tambaye ka bayanin hanyar da ka bi
כל ka samu abin nan...
Bai iya tsayawa jin karashen
maganganunsu nasa ba ya dimauce ya
gigice, tabbas ba wannan ne karo na farko
137
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
da ya taba jin ire-iren maganganun nan ba,
amma yau abin ya yi muni.
Ya diro daga kan mota ya shiga ya
tada ita, da kyar ya ke iya ganin gabansa,
ikon Allah ne kurum ya kai shi inda za shi.
Kamshin da ya dinga shaka ne ya
tilasta masa kutsawa bedroom dinta, tana
zaune a gefen gado sanye da rigar
bacci.zumbur ta mike tana kallonshi.
"Lafiya?"
Bai ce komai ba ya maida kofar zai
rufe, ta dako tsalle sai ga ta a gabanshi.
"Me ka ke son aikatawa?"
"Na zo gurin matata don karbar
hakkina".
Ta dube shi shekekeş ta ce.
"Hakki? Wane irin hakki kuma?"
Ya ce, "Ke ba karama ba ce, kin san
abin da na ke nufi".
Ya fada yana kallonta.
138
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
"Humaida na gaji, ke halalina ce ba
zan iya ba, please".
Ta dan ja da baya.
"Ai na gaya maka ban aure ka don
wannan abin ba, shi ya sa ma na zabi na
zauna da kai a ganina ba za ka taba tirsasa
ni ba, ka gane ko?"
"Me ya sa za ki yi min haka
Humaida? Kin sauya mini tamkar ba ke
ba".
Ta murguda baki cikin yanayin
tsiwa.
"A rayuwa babu abin da na tsana irin
haihuwa, ban shirya mata ba, ba yanzu ba.
Har nawa na ke? Ba zan iya ba".
Ya katse ta da fadin...
"Humaida, kina da ilimi, kin san
abin da aure ke nufi..."
"Mu'allim na ce da kai ka kyale ni,
me ya sa ka ke son maida ni wawuya? Ni
fa ban yi aure don namiji ya juya ni yadda
139
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
ya ga dama ba, yauwa kai kanka ka san na
fi karfin ka zo min da wannan rainin, ka
bar ni na mori rayuwata ni kadai ba tare da
wani yaron ya rage mini jin dadinsa ba,ba
kuma na bukatar wani guri a jikina ya sami
tawaya, ba zan haifa ba balle na shayar, ka
gan ni kawai ka kalle ni na burge ka, ka
dinga jin ka fi kowa sa'a domin ka tsinci
dami a kala. Yanzu in na haihu kai kanka
ba za ka so kallona ba, yanzun nan zan
tsofe na yakune, da fatan ka gane nufina?"
Ta gama kular da shi karshe, cikin
daga murya ya ce.
"Saboda haka na ce da ke, ke
mahaukaciya ce tuburan, sam ba ki da
hankali, ke gabadaya ma ba ki cikin jerin
mutanen da za a kwatanta su da masu
hankali, ke jahila ce wadda ba ta san me ta
ke ba, banza! Bailagaza! Sauna! Kuma ki
ji da kyau, wallahi ba ki isa ba, dole ne na
juya ki, dole ne na yi yadda na ga dama da
140
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
ke, don ni na ke aurenki ba ke ki ke aure
na ba. Bari ganin ina daga miki kina duk
iskancin da ki ka dama, ba wai ba zan iya
tsawatar miki ba ne, ina so ne ki saba da
rayuwar a hankali, amma tunda na lura
kwalwar kifi ce da ke zan saita miki
دو
zama...
Kusan daskarewa ta yi a gurin
saboda tsananin mamaki, ta nuna shi da
yatsa.
"Mu'allim ni ka ke ci wa fuska
haka? Ni ce jahilar? Wace irin tarbiyya ce
iyayenka suka ba ka da ba su koya maka
tattalin mace ba? Ko haka ka ga tsoho na
y...
Tabdijan! Humaida ta ballo ruwan
dafa kanta. Mu hadu a littafi na uku don
jin yadda za ta kasance.
Bilkisu H. Muhd.
141
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
DANDANO DAGA
'YAR BABBAN GIDA
Ya kutsa kai dakin da yake jiyo kukanta, ya
hango ta a takure a sakon gado lamarin ya yi matukar
taba masa zuciya musamman da ya yi mata ganin a
hargitse babu gyara. Kwalliyar nan tata mai jan
ra'ayinsa yau kamar ba a taba yin irinta ba a jikin
Sa'adah ba, tun kayan barci ne na daren jiya. Fuskar
nan ta koďe ta jeme, idanuwan sun yi luhu-luhu, ga
ruwan hawaye da ya y kaca-kaca a fuskarta, gabadaya
yanayinta ya sauya sai ya ke ganinta kamar ba
Sa'adan tashi ba 'yar kwalisa mai iya daukar kwalliya
da iya zuba dressing irin na daukar hankali ba.
Tausayinta mai yawa ya tsirga masa, tabbas an shiga
babin da zai iya salwantar da rayuwarta, ta sha fada
masa. "Wallahi Mahmood gara na mutu kafin na ga
ranar da za ka yi min kishiya".
"To wai wa ya ja? Ita ce silar komai".
Ya zauna gefenta cikin tattausan lafazi ya ke
magana a gare ta. "Me ya yi zafi har irin haka
Sa'adah? Ashe ke din ba za ki daure ki zamo jaruma
a cikin mata ba? Yanzu saboda Allah irin wannan da
ki ke yi me sunansa? Wa zai dube ki a yau ya fahinci
ke ce Sa'adahr nan ma'abociyar ado da kyalkyali?
Dube ki yadda ki ka mayar da kanki dalilin wani abu
142
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
da bai taka kara ya karya ba har ki ke neman sukurkurta kanki, ki ke son ki zamo abar kallo da nuni a wajen sauran mata...?"
Ya sa hannu ya ke jawo kanta da ta tura tsakankanin cinyoyinta, ya ke fada mata. "Ki sa hakuri da juriya a ranki, ki zamo jaruma sai ki ringa rayuwa shi wannan din wani lamari ne mai girma da ya zo gare ni daga Ubangiji, ba wai niyyar kaina ba ne, ko nufin muzanci a gare ki, a'a yi wa lamarin kallon shirin Allah ne. In ba Allah ba Sa'adah shirin ya zo daga gare Shi ya ni da na ke da kamar ke zan jawo wata cikin rayuwarmu? Haba! Haba! Ai wannan da gani kin san ba yina ba ne, yin Allah ne. saboda haka maza share hawayenki, ki zamo mai hamdala a
gare Shi, don ba mu sani ba kila wata rahamar ce ya yi shirin yenta a gare mu, shi ya sa ya aiko da hakan a
gare mu".
Ya sa hannu yana share mata hawayen. Tа ture hannayensa daga jikinta, ta ke magana a gare shi da muryarta da ta dushe don azabar kuka. "Babu wani furucinka da zai yi tasiri a gare ni, domin na riga na gama fahintar lamarinka game da ni, nid in na zamo abin ki a gare ka..."
Da sauri ya katse ta. "Wa ya fada miki ke kin
zamo abin ki a gare ni?"
"Kai ka tabbatar min da haka tunda har za ka
iya raba soyayyata zuwa ga wani fangaren". Ya fada
143
KA AURE NI=2 BILKISU H.MUHD
mata cikin lallami. "Ki dauki aurena kaddara
Sa'adah, ba wai wani batu da ke fita a bakinki ba".
Ta juya kafada da girgiza kai ruwan hawayen
na ci gaba da kwaranya daga idanunta, ta ce. "Babu
batun kaddara a maganar kishiya, ka ci zarafina irin
wannan ka zauna a gabana kana fada min wai
Kaddara? Ina! Wannan sam ba kaddara ba ce, son
zuciya ne kawai da son muzanci a gare ni".
Ya ce, "To idan ma ba kaddarar ba ce Sa'ada
wa ya ha? Kar ki mance fa komai ya faru ke ce
sanadi, da a ce kina tare da ni a kan kowane ra'ay
nawa kina biyayya a gare ni, da yin rayuwa
kyakkyawa irin ta sauran ma'aurata ta ya za a yi irin
wannan ya faru? Amma ki yi duba ki ga mene ne na
Gatanci bai faru daga gare ki zuwa gare n da tallafin
mahaifnki ba..."
Ta katse shi da alama ranta ya kara hauhawa a
6aci. "Na yi maka alkawarin gyara halayena da binka
sau da kafa, da yi maka duk yadda ka ke bukata,
amma kai ma ka yi min alkawarin bayar da saki aa
gare ta tun kafin ta kai ga shigowa cikin gidan nan".
Murjanatu Muhammd Dan-Guru
144
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels